Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Babanku, ko bai san ku ba, balle kuma ya san ku, an ce MaiKalwan, ba Maikalwar bane? Ance maki mai kafar muburgin ko ba tsigigiyar bace? An kuma ce waye Ubankun? Wanda duk yace zai ja da Saraki, ai kuwa sun tambaye shi waye Ubansa?”
Na mike ina kumburi nace “Allah banda ni, babu wanda zai zagi Babana akan idona inyi shiru in kyaleshi, ko Wazirinne, balle wata tsiya, Bello, don kuwa Babana, na tabbata bai taba zuwa roko wajen su ba”.
Goggo tace “gaskiyar ki Atine, nima ina bayan ki, ku kare mutuncin talaucin ku a ko ina, mulki da abin duniya duka Allah ke badawa, babu kuma wanda yayi mai rawa ya bashi.
Jeki dauraye jikin ki duk kin cika mu da doyi, akwai wata kalwar zan daurawa Rabi’u ya kaiwa malam Ladan din”.
****
Kwana biyu ina juya tambayar Bello a raina, na kasa mantawa, nayi-nayi in mance na kasa. Ba wai ciwon abinda ya mana ke damuna ba, don kuwa nima na rama, na kuma tabbata ya ji ciwon sharewa (bagararwa) yayi.
A zahiri, ni karamar yarinya ce, shekaruna basu fi goma sha uku ba, ko kirgen dangi irin na Atika ni ban soma ba. Don haka ba zan ce son Bello na ke ba, amma ya dameni, kyawun surar shi da cikar kamalar shi abin so ne ga kowa.
Ba ga surar shi kadai ba, yanayin shi ma abin so ne, tsari da zubin halittarshi abin burgewa ne, balle ga mu, kauyawa. Ban taba ganin shi ba, banda ranar, sai dai na sha jin labarin shi da irin karimcin shi.
Dana ganshi, sai na ga ashe ya fi yadda ake tsammanin shi. Watau dai ganin sa yafi jin sa. Na kuma fahinci ashe macijin sari ka noke ne; ba shi da mutunci ga wanda bai san shi ba, ga wanda ya san shi, shi mai masifar mutunci ne.
Kenan idan har da gaske ina son sanin hakikanin wanene shi, kamar yadda zuciyata ta nace da son sani, dole ne in binciko tambayar shi ta shin waye ne BELLO WAZIRI KARAYE? To a ina zan bincikan? Oho!

Motsin dawowar Awal na ji a zaure, na bashi lokaci na tabbatar ya gama duk abinda ya saba, na je rumbu na fiddo masa abincin ranar sa, gudun kurna ne muka yi da miyar taushe.
Nayi sallama ya amsa, yana zaune bisa kwayar tabarmar karaunin da ke dakin, a hannun shi littafin boko ne yana ta rubuce-rubuce, na aje akushin na zauna gefensa nace “sannu da aiki Yaya, rubutu kake tayi, kullum baka gajiya da rubutun nan dai” ya aje biron yayi murmushi yace
“assignment ne aka bamu nake ta kokari, wallahi naso ace Baba ya yarda an sa ku makarantar boko, babu abinda ya fi ilmin zamani dadi Atine, zaki rubuta, za’a rubuta miki bayani ki fahimta kamar da baki ne ake gaya miki….”
Awwal zuba yake, a yayin da ya fahimci ido nake binsa da shi kurum, amma zuciyata bata tare da shi, tana ga wani dan matsakaicin hoto cikin firem da ke aje can gefe; Bello ne, rungume da Yayan mu Sani, suna sanye da kayan kwallo na ManchesterUnited kungiyar kwallon kafa da Sani ke maitar so.
Kullun ya dawo kasuwa, kallon kwallo yake tafiya can bayan gari, sai da yasan yadda yayi ya takurawa Goggo ta bashi kudi, ya kukkulla da taimakon abokai ya sayi irin kayan su.
Hankalina ya dawo ga kalmar da naji Awwal ya ambata yanzun nan, wato assignment, tabbas na so na ji ta a bakin Bello, ranar daya zageni, ban san ma’anar ta ba, illa zuciyata ta fassarata yadda ta ga dama. Nace
“Yaya menene assignment?” “Assignment aikin gida kenan, kamar wani aiki da za’a baki ace ki je gida ki yi a nutse, a karbi sakamako washegari, kin gane ko?”
Na maida ido na ga hoton, a hankali nace“dama Sani ya san Bellon gidan Waziri?” “Waye bai san shi ba? Ai yaron, yana da mutunci sosai, ga son mutane, ga faran-faran, ga ilmi, Bello zakka ne, a Karaye baki daya”.
Nayi zugum, a raina nace “ikon Allah! Mutumin da ke zage talaka, ya ci mutuncin iyayensa, shine kowa ke so? Inda ranka kaga da yawa. Wannan kadai ya isar mani amsar tambayar wanene BelloWaziri??? Amsar da kowa zai bani kenan.

*****






S
ati biyu suka shude, ban ji duriyar, dan gidan Waziri ba. Zuciyata, cike ta ke da begen, son sake ganin wannan kasaitacciyar fuskar rashin mutuncin. Ina tsoron idan har ba asiri mutumin yayi mini ba, tunanin shi ya hana ni zaman lafiya, duk na sauya, na rage walwala na zama tamkar ba ni ba; babu kuzari babu karsashi aduk abinda nake aikatawa.
Hatta Jafaruna, ya san uwar dakin sa na cikin damuwa, damuwa da wanda bai san tana yi ba.
Kulawar da nike mai tayi rauni, ga Atika ma, kullun hirar ta Bellon gidan Waziri, Bello, Bello…. Kusan kullum sai ta bi hanyar gidan Waziri da Maimartaba, Sarkin Karaye, wai ko zata sake ganin sa, burgeta yake. Ta tambayi Sani, yace shima kwana biyu baya ganin shi ya je filin Ball, da kyar in bai koma Jos, inda yake karatu ba.
****
Muka wayi gari Goggon mu ba ta jin dadi, tun safe take kwara amai, zuwa yamma sai gudawa. Hankalin mu ya tashi ainun, barin ma ni da bana hada muhimmancin al’amarin Goggo da na kowa cikin gidan.
Awwal ya je kemis ya amso mata ja da yalo ta hadiya amman ba sauki, sai wurin Allah. Abu sai gaba ya ke, Baba da Amarya, sai jike-jiken saiwoyi suke mata tana kwankwada.
Naji ana fadin wai kwalara (cholera) ne, amai da gudawa, idan ba’ayi saurin dauke marar lafiya ba, duk gidan sai sun kama. Awal ya shawarci Baba akai Goggo asibitin Murtala dake cikin garin Kano (a zamanin kauyen Karaye ba asibiti, sai dakin shan magani).
Baba yayi shiru kamar yayi kuka yace “asibiti da ake kashe kudi masu yawa Awal, wa zai bamu? Ina za’a nemo?”
Awal yace “Baba asibiti akwai na kudi, akwai kuma na gwamnati, shi wannan na gwamnati ne, ba’a kashe kudi, kyautaake ganin likita, sai sayen magani kawai.”
Baba ya amince, ya kukkulla ‘yan canjin shi ya ba Awal ya hada da na shi da cinikin Omo da kayan kullin Goggon da akayi yau duka.
An shirya Auwal da Amarya ne za su tafi da Goggo ko don a samu saukin wahalar kudin mota, Inna ta zauna ta kula da gida da yara, mu kuma mu saida kayan Goggo, a samu karin kudi. Ba mu san kowa a birni ba don haka ko abinci sai sun saya.
Tun ranar da suka tafi suka aiko mana an baiwa Goggo gado, banda kuka ba abinda nake da kuma yiwa Goggo addu’ar neman sauki. Atika ce mai karfin zuciyar sai da omon, Inna ko sabgar ta take ba abinda ya dame ta da ciwon Goggo, tana girki tana ‘yan wake-wakenta irin na wanda gida yayiwa dadi.

Da daddare wurin karfe takwas, garin Karaye, hadari yai holoko, sama tayi fari fat da kwantaccen hadari, sai iska da tsawa gami da cida ke kadawa kunnuwan ‘yan adam ganga.
Wannan bai hanani sulalewa in fice zuwa gidan kakana Liman ba, wai in amso addu’o’in da ya ce in zo in amsa bayan sallar isha’I in yiwa Goggo na, daren Juma’a ne ana yin dace da samun karbuwar addu’a.
Tafe nake faram-faram, iska na kada ni inda duk ta ga dama, dama gani jiki kamar sillen kara, siririya ce ni sirit kamar haihuwar bakwaini, koda ya ke Goggo ta ce a BAKWAINI aka haife ni. Fuskata ma siririya ce, doguwa, mai dauke da siririn dogon karan hanci kamar shape din karas, wadatattun manyan idanu, kullum yanayin su kamar na mai jin barci, zubin su kamar kwan kazar hausa, a takaice, komai nawa siriri ne maras kauri irin na Inna na, Amarya.
Jin taku nayi a baya na, ga layin ba kowa, hasken farin wata da hadarin yasa ina gano inuwar, dogon mutumin da ke bina, kamar mai gadi na.
Na kara sauri akan nawa na da. Iska ta yaye dan yalolon gyalen da nike yafe da shi, ban tsaya ba, sai na kara da sauri-sauri gudu-gudu, shima dankwalin yayewa yayi, ina ganin in na tsaya bin shi nima iskar, dauke ni zatayi. Bakin tufkakken gashi na ya shiga fidda sheki da kyalli cikin hasken farin watan. Sai na daura dukkan hannuwa na a ka, wai in suturta kan.
Kaurarrar muryar, wadda na tabbata duk Karaye, mutum daya ne mamallakinta, dai-dai sanda na sa kai kofar gidan Liman ita ke kiran “A-ti-ne”.
Nayi hamzarin juyowa, Bello ne, ban ce komi ba, illa na ja na tsaya, sai na tuna bani da ko mayafi balle kallabi. Na shige gidan da sauri na daga Asabarin dakin Luba, duk a tsorace nake, Luba tayi salati tace “ke lafiya, ba dai Indo ta rasu ba?”
Nayi ajiyar zuciya mai karfi “a’ah Inna Luba! Iska ce ta dauke mayafin, ta dauke dankwalin, nima sauran kadan ta dauke ni. Ga kuma wannan dogon mutumin, wa ma ya ke da suna? Dan gidan Waziri yana ta bina, muryar shi abun tsoro ce, Inna, don tana firgita ni”.
Luba ta yi dariyar da ta fiddo wawulon bakin ta tace “Atine zauna nan,” na zauna, tace “ki nutsu, nasan halin ki kinji? Ki saurari Bello dan gidan Waziri yaron kirki ne, ba zai cutar da ke ba, Baban ki da Malam za su ji dadi idan baki wulakanta shi ba. Ba yarinyar da Bello ya taba cewa yana so, duk fadin Karaye, haka duk dangin su. Maimartaba ma ya bashi diyar shi yace baya so, idan kika samu ya so ki, Allah ya taimakeki, mutum ne dan asali, dan babban gida, mai gawurtacciyar nasaba, mai ilmi sosai, Atine na, kin ji?”
“Inna baki san wannan ba, shine ya zagi Baban mu, ya….” ”ni ba wani abu nace ba, kurum cewa nayi ki saurare shi, ki ji me zai ce da ke?” “Shikenan Inna, Malam ya kwanta ne?” “Ya jiraki tun dazu baki zo ba, ya rubuta ya bawa Sani ya baki, nake jin mantawa yayi (Sanin).
Ta bani mayafi na yafa na fita. Har yanzu yana tsaye jikin dakalin gidan, sai naji tausayin shi. Ni mutum ce mai tsananin tausai don ko kiyashi, bani iya kashewa da gangan balle in wulakanta mutum.
Sanye yake da wata irin jibgegiyar rigar ruwa ta kare jiki daga dukan ruwan sama, sai kyalli take kamar leda a cikin hasken hadarin. Ya harde hannuwan shi bisa kirjin shi, ya kurawa hadarin ido kamar mai son karanto wani boyayyen al’amari a cikin sa. Jin motsin fitowa na yayi saurin sauke kai. Biyo ni kurum yayi bai ce komi ba, kazalika nima.
Hadari ya gama gangamowa, sai yayyafi ya soma sauka yaf-yaf a jikin mu, da kan runfunan kwanon da ke layin karar babu dadin ji. Na dukunkune hannuwana cikin tsananin razana, alamun tsoro, zane baro-baro cikin idanuna masu haske. Da ni kadai ce zurawa zanyi da gudu, shiko ko a jikin sa yace
“Atine, bakya magana, baki gaida na gaba da ke, why? Na lura in za’a kwana ana tafe da ke bazaki yi magana ba” nayi shiru, ya sake cewa
“Atine, ba kya gudun ruwan nan ya taba mun lafiyar ki?”
Nayi hamzarin dago ido na dubeshi ta wutsiyar ido, kallo na yake da idanuwan shi masu kwarjini, wani abu na ji ya tsirga har cikin kwakwalwata. Ban ankara ba na ji yana rufa mun wani abu mai dumi. Suman tafe nayi, shidewar wucin gadin razana.
Sai da na dawo dai-dai na fahimci cewa, jibgegiyar rigar turawan ce cikin jikina, ni Atine Mamman Maikalwa.
In banda wani irin lallausan kamshi, ba abinda ke tashi cikin rigar. Dai-dai sanda muka kawo kofar gidan mu ruwan ya jike shi sharkaf, amma bai ko damu ba. Na mika hannu zan zare mishi rigar shi, hannun shi na dama yasa ya danne nawan yace
“No, ajiya ne na baki Atine, zan karbi kayana idan na dawo. In an tambayeki thick-coat na wanene, me za ki ce, Atine?”
Iyakar rudewa na gama rudewa, tuni fitsari ya cika min mara fam, na sunkuyar da kai jikina na kyarma yayi hamzarin dauke hannun shi a nawa da sauri yace
“Atine, zan tafi, tunda bazan samu alfarmar kalma ko daya a bakin ki ba. Shin kin nemo amsar tambaya na na kwanaki? Da nace ki binciko wanene Bello Waziri? Na san kin binciko amma amsar ta yi miki sabani da tunanin ki?”
Yayi murmushi, duk da ba shi nake kallo ba, tafin kafata na kurawa ido, na ji sautin murmushinsa a hankali, a zuciyata ina gasganta zancensa, kwarai naji sabanin abinda nayi tsammani, amma hakan baya nufin na yarda, tunda ni ban ga hakan akan kaina ba.
Ba kuma tare da ya kuma neman jin komi daga gareni ba yacigaba da cewa
“Yau ma ga newassignment, ki je ki ki binciko, menene yasa Bello Waziri ya sa maki rigar shi? Abinda bai taba yiwa wata yarinya a fadin garin Karaye ba? Mene yasa kika kasa dubar kwayar idanun Bello Waziri ko kadan, sabanin kwanakin baya da kike gaya mai magana son ranki? Atine, na barki da wannan, sai da safe!”.
Nafi mintuna biyar tsaye a wurin kamar an kafe ni, kamin in dawo hayyaci na in shiga gida, su Atika tuni sunyi barci Baba ne dai nike jiyo sukurniyar shi a turakar shi. Na zare riga a hankali, na janyo aci bal-bal na kyasta ashana, haske ya gauraye dakin.
Na dubi riga da kyau, ta hadu ta burge ni iyaka rayuwata ban taba ganin riga mai kyawun ta ba. Wannan kamshi, ni’ima ne ga ma’abocin shi. Na samu kaina da rufa riga a kaina ina shakar kamshinta ina murmushi a hankali. Wai shi wannan bai san ni yarinya bace, yake cika mini kwakwalwa da maganganun da suka fi karfin hankalina? Ni ina nasan wani dalilin sanya mani riga? Ba ruwa ake ba ya taimake ni? Wanda kuma duk ya taimaki wani ai Allah zai taimake shi shima.
Ya hada yatsun mu, don kar in ciro riga mana ina na san wani dalili bayan wannan? To amma ni kaina nasan yau na ji ni cikin wani bakon nishadi, ga farin ciki ya baibayeni kamar ance mun Goggo na, ta warke sumul.
Na linke riga na janyo wata tsohuwar akwatun Amarya na tura, na rufe na mayar.

Washegari Atika kallo na take kaman taga aljana tace “Atine, jikin ki tashin kamshin Aljannah yake, shin ko kin ga Annabi a barci ne da Malam yace mana ana gani, in anyi dace?” Na yi dariya na bi ta
“eh”.
Yammacin ranar mun yi ciniki mai tarin yawa, na hada kudi na baiwa Baba, ya tafi Kano. Washegari da safe nayi wanka na saka atamfata mai dan daman, print ce ruwan bula, ni bana kwalliya sam ko vaseline in ba lokacin sanyi ba bana shafawa, na goya Jafaru nasa kibiya ina tsefe kaina ina tajewa. Sani ya shigo, baki har kunne, a duk sanda ya zo min irin haka nasan ya ciyo kudin wani karikicen abokin sa ne, wai zai hada mu, na tsuke fuska kuwa iyaka.
Ya samu jijiyar bishiyar dalbejiyar da nake zaune a karkashinta ya zauna jikin sa har rawa yake yace
“wai ke Atine, baki gajiya da tsifar kai?” Nace “unh!” ya lankwashe kai yace “shin kin san Bello,Yallabai Bello dan gidan Waziri?” Nan ma nace “unh” na sake tsukewa, Sani ya dabarbarce, yama rasa ta inda zai faro, da gani ba kudi ya ci ba yau mutuncin ya gani, ya kare kwane-kwanen sa yace
“ki je yana kiran ki, Baba ya san da zuwansa, ya kuma ce in gaya maki muddin ya ji wannan dabbancin naki, sai na kabari ya fiki walawa”. Ya haura takalman sa ya mike nace “in dai rigarsa ce da ya ara min, ban roka ba, balle a biyo ni har gida a ci mun mutunci, tana nan bari in dauko maka” Sani ya fice abinsa ko saurare na bai yi ba.
Murna kaman in yi tsalle. Ni kaina nasan, na kamu da son mutumin da ba tsara na bane ta fannin komi, amma Allah shaida na ne kan ba ni na daurawa kaina ba. Surutu ne nasan za’ayi shi a garin Karaye har a gode Allah, oho, za su gaji su bari ne.
Tun daga zaure nake jiyo kamshin, ina gaba yana kara dosa ta. Dan farin wankakken hijabi ne a kaina hannayena rungume da riga, na hange shi shida ‘yan iskar abokan sa, dan tsamirmirin nan da dan gajeren.
Sanye yake da karamar riga da dogon bakin wando mai kauri na ‘yan birni, kyakkyawar fuskar shi tayi kyau a cikin hantsin kamar kullum. Na kara cuske fuska, a nutse na gaida su fuskata ba annuri, ita kanta gaisuwar ba don gargadin da Sani yai min ba da ba zan yi ba.
Dan tsamirmirin ne yace “ranki ya dade, Uwar gijiyar mu, Yallabiyar mu tuba muke!” Ba tare da wata maganaba na mika mai riga nace
“ga rigar ku!”
Sukayi murmushi a tare yace “bar zancen riga tukunna, nace maki mun zo tuba ne….” nace “da kuka yi wacce shirka? Ai ku saraki ne, masu mulki, don haka ko mi kuka yiwa talaka a hanyar garin Karaye, baku yi laihi ba, tunda garin ku ne to amma nan cikin gidan Maikalwa, kalwa ta daddawane, mallakin sa ne daya gada tun iyaye da kakanni, babu wanda ya bashi cikin masu mulkin Karaye.
Don haka ba wanda ya isa ya zage shi anan mu kyale. Ga rigarku nace” na dangwarar ta anan na juya abina.
Sai bayan dana dawo na shiga tambayar kaina “maiyasa na yi haka?” Don me ban saurare su na ji uzurin su ba, ko Ubangiji muna yi mai laifi, mu rokesa gafara ya gafarta mana, balle ni wata tsiya ‘Atine’. Koda ya ke na nuna martabar Baba na, mai girma ce a gareni. Sai dai ina wahalar da kaina ne a banza; son Bello nake, son shi ke wahalar da ni a ‘yan kwanakin nan.

Kwanan Baba ukku kamin ya dawo har hankulan mu sun tashi, ya dawo cike da farin ciki raina yayi fari kal don na tabbata Goggo ta samu sauki kenan.
Da yamma Baba ya kirani dakin shi, munyi hirarraki da dama game da lafiyar Goggo kamin ya gangaro maganar da ban tsammana ba, yace
“Atine naji dadi kwarai da kuka shirya kanku da yaron nan dan gidan Waziri, domin yaron mutunci ne, dan babban gida mai ilmin da duk fadin garin nan babu saurayi mai ilmin sa, wanda in banda ikon Allah, ba abinda zai yi da ke, idan kika yi la’akari da matsayin mu na talakawa likis, wadanda basu aje ba, basu kuma ba wani ajiya ba.
A cikin rufin asirin Allah muke daura tukunya bisa murhu, mu daura sittira dai-dai karfin mu. Allah ya bamu wadatar zuci kuma kowa ya sani, bamu kwadayi, balle ace kwadayin mu ne ya hada mu da su Waziri.
A jiya yaron nan ya je Kano, ya biya duk basussukan da ke kanmu, ya sayi magungunan da muka kasa saye, ya sanjawa Goggon ku asibiti zuwa na larabawa masu mutunci da sanin hakkin bil adama. Ya sayawa Goggon ku duk abinciccikan da likita ya bukata ta ci wanda ni a rayuwata ban taba jin su ba ma, ya kuma yi umurni ga wata ‘yar uwar shi da ke karatu can Kanon kullum ta dafo abinci safe, rana da dare ta kawo mana. Su zauna muyi hira su zaga da mu gari, yau din nan Waziri da kansa ya je ya duba Goggon ku, tare ma muka dawo a motar dan Maimartaba, nan da kwana biyu za’a sallami Goggon ku.
To mutanen da suka yi maka wannan karimci akan suna son naka, basu kyamaceka ba duka da yadda Allah ya yi ka, ai bai dace ka ki amsa bukatar su ba da take ta alheri a gareka.
Don haka ni na gaya masu tuni na basu ke, duk sanda suka shirya su fito ayi aure, waccan solobiyon ma in ta gama ruwan idon ta fiddo daya cikin tarin samarin da take tara mun a kofar gida, a hada ku lokaci daya”.
Shiru nayi, kaina a duke, nayi mutuwar zaune, ina sauraron Babana cikin abinda nake ji kamar a mafarki ko kuwa (almara); an bada ni ga Bello Waziri? Abin ma abin tsoro, bayan duk wulakancin da nayi masa? Shine ya biyo Babana da siyasa irin tasa ya aure ni, ya rama duk wulakancin da nayi musu kenan.
Hawaye suka cika min ido taf. Buri na na karatun RAINO ya karye ban cimmasa ba. Burina na zuwa makarantar boko ya bi ruwa shima. Auren wuri, abinda na ki jini a rayuwa ta. To amma me?
Da wanda na tabbatar ruhi, kalbi, tsoka da gangar jikina duka suna mutuwar so da kauna; Bello Waziri. Daya da daya a mazan Karaye bakidaya. Wanda yai ilmi, mawuyaci ne ya hana matar shi yin ilmi.
Na rattaba haduwar mu da Bello, a matsayin kaddararrah daga Allah! Ita kanta haduwar, bata dadi bace, babu wata kalmar arziki data taba hadamu balle kalmar SO, amma gashi har manya sun shigo cikin maganar.
Na tabbata ina son Bello, amma ina shakkar kaunar sa gareni. Idan na tuna farkon haduwar mu kafana kamar muburgi ya ce, to mai zai yi da ni, in ba yaudara bane?
Yanzu yadda Babana ya gama saki da al’amarin su Waziri, wane bayani zan mai ya gamsu? Bama wannan ba, in nayi hakan na yi butulci wa alkhairin da suka yi wa Babana, suka maisheshi mutum mai darajjah cikin su har suka damu da ciwon Goggon mu, wadda bani da kamarta duk fadin duniya, Goggo na fa, Goggona ka taimakka fa…….”.
Na dubi Baba da yayi shiru yana karantar yanayi na. Kallo daya zaka yi mishi ka fahimci cike ya ke da tsoron, rashin amincewata.
Ni kam koma da wane nufi Bello zai aure ni, na amince domin Babana, darajja Babana da Waziri yayi. Su basu kyamace mu ba, me zan yi wa kyama, tattare da Bello Waziri???
Baba ya fiddo ido kadan yace
“Uwata Atine, kada ki bada min kasa a ido, kada ki mayar da ni karamin mutum a idon mutanen da suka darajjani, suka martaba ni, suka girmama ni ta hanyar da wani dan adam bai taba yi min ba….” Sai hawaye.
Na rarrafa ga Babana, nayi murmushi, idona cike taf da kwallah, “na amince Baba, dama ina son Bello, ina dai jiye mana wulakancin gidan sarauta ne, tunda mu ba mu da komi, ba wasu bane face talakawan gari”.
Baba yayi murmushi.
“Bana gini, ban duba filin wurin ba, Atine, bazaki wulakanta a gidan Waziri ba, in dai kin kasance mai;
- Gaskiya
- Amana
- Hakuri
- Juriya
- Kawaici
- Gudun duniya da kyamar abin hannun mutane.
Ki zama mai bayarwa ba mai karba ba, wannan shine babban makami na zama da kowace irin al’umma, a ko’ina, komi mulkinta.
Talaka kan zamo wani abu, idan yayi riko da wadannan makamai. Mai mulki kan kaskanta, idan ya rasa wadannan makamai har a darajja talakan da bashi da komi fiye da shi.”
Kaina a sadde nace “Na amince Baba, Insha Allah zan gina tubalan ginin rayuwata ne a kan kalaminka, ko babu komi, bazan taba tabewa ba na tabbata idan na bika”.
Hannunsa nadama yadauraa kaina “Allah yayi maki albarka Atine, Allah ya daukaka ki da daukaka ta buwayar sa” “Ameen Baba”.




S
hara nake, na ji an zugure ni, dagowar nan da zan yi sai na yi arba da Goggona, tsaye da kafafunta, na rude na kidime na yada tsintsiya na ruga na rungume Goggo su Amarya suna ta dariyata. Na dubi Goggo duk ta rame, da alama har yanzu jikin ta da saura, na kama Goggo na zuwa daki har gadon bunun ta.
Hira ta kaure a dakin na labarin asibitin da aka mayar da Goggo, wai a bandakin asibitin har da wani inji makale da
zaka danna sabulu mai kamshi da laushi ya zubo, a wunin ranar zungur, hirar kenan.
Baba ya shigo

Please Login or Register in order to submit comment