Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fahimci Atine yarinyace mai lura da saurin fahimta, da zata je makaranta, da anga kwaruwar yarinya. A daren kadai ta haddace A-Z sai dai rubuta su ke wahalar da ita.
Washegari kamin ya fita sai da ya jaddada min in haddace rubutun su kafin ya dawo, in har ina son sabon darasi.

***


N
ayi wanka kamar yadda Talatu ta koyar da ni, wato sai an zuba abubuwan roba a ruwan wankan (turaren wanka, dettol da sauran abubuwan kashe kwayoyin cuta), sai naji fatata har wani santsi take, wani danko-danko da wani maiko-mako da nazo da shi na kauye, duk ba ko kadan.
Haskena ya fara fitowa, na taje dogon siririn gashina na kallabe shi kalba daya, ta sakko har dokin wuyana na nufi sassan uwargijiyata.
Sanye da farar karamar riga da ruwan bular siket mai fadi, yau ma waya take, amma kwance a cikin kujera…….. “wallahi na sa Tom ya dinga bata abinci sau uku a rana …me? In yi hira da ita? In ji ko tana da matsala? Tab, kaima kasan this’s impossible (ba zai yiwu ba….) ban bata aikin ba tukunna, sai na gama tsaftace ta…kayi hakuri nace ko?
(Ta sassauta murya) ai yau zan bata dama, ni kaina dattin ya isheni, dakina har yana ta soma taruwa..” tayi tsaki ta yi cilli da abin maganar “stupid kawai”.
Nayi mata sallama ta juyo, na zube a kasa na gaisheta, ta amsa kamar tayi bal da ni cikin kufula da daga murya tace
“sai yanzu kika ga damar tashi? To nan ba hutu kikazo ba, kinji mai kafar shanshani? Ba a banza zaki ci kudin aikin ba, sabida muma wuni muke muna nemowa, muna aiki da lafiyar mu, lokacin mu da ilimin mu, mu hana idanun mu barci mu tafi nema.
Ki bar ganin komi baja-baja kamar na banza, a kididdige yake cikin gidan nan. Na fiki sanin muhimmancin ‘naira daya’ sabida ni aiki nake tun safe har dare, yanzu haka da kika gani a gida, hutun haihuwa na ke.
Don haka in zaki yi aiki, ki mike kiyi azama. In banda Fulani ta kawo ki, ke din nan baki isa ki yi mun aiki ba, ke duk ‘yan garin ku ma wallahi baku isa ba.
To ba yadda zanyi, tunda na auri Dan da Uwar sa ke juya al’amuran shi. Daga yau karfe bakwai zaki dinga tashi musamman in na koma aiki, kizo ki gyara mun daki da sassana gabadaya, ki wanke min toilet ki canza min zanin gado kullum. Peter zai zo ya nuna miki yadda ake komi.
Iya kacin aikin ki sassana ne kawai ba ruwanki da sauran bangarorin ko apartment na maigidana, duka aikin Peter ne. A sanda muka ci abinci a sannan ake wanke kayan ba sai an bar su sun bushe ba, kina jina?”
Na daga kai da sauri
“Yaya sunan ki?” “Atine shine sunana” “meye kuma Atine? Atini ciwon kashin yara da naji ana fadi?” “A’ah sunan rana ne” “to meye na daren?” “Nima ban sani ba sai iyaye na, tunda na taso, Atine suke ce mini” “to na ji, ni a wurina bazan iya fada ba, domin yana tuna mini da kashin yara.
Daga yau sunan ki a gidannan ‘BLACK’. Sai ka’idodin zaman gida na.
Da farko dai bama rasa abinci, duk abinda kike so Tom zai dafa ya baki. Iyakacin yawon ki daga nan sassan da zaki dinga gyarawa sai can dakin girki wajen Tom inda zaki dinga yin wanke-wanke.
Babu ‘yar aiki mace cikin gidan nan balle ki sami kawa, su Tom duk kiristoci ne da Inyamurai, don haka ki maida hankali kan aikin ki kadai, ko tsinke bana son gani cikin sassana.
Zakiyi wanka sau uku a rana, safe rana da dare don karki ke canza mun atmosphere na daki kamar farkon zuwan ki. Ki kula da fesa anti-perspirants dake cikin kayanki a hammatarki.
“Ba yawo, ba kawa ba kazanta”. Sune ka’idodi na. Idan miji na yana gari, kada ki sake in ganki a hanyar sassannan, don in ya ganki, amai zai yi. Ko zaki zo kwasar kwanukan abinci, sai kin tabbatar ya tashi.
Duk ranar da tsautsayi yasa ya tambayeki, ko ina kyautata miki? Kika ce ba haka ba, wannan dogon jelan gashin da ke reto a wuyan ki zan cinnawa gass da ashana, kin ji abubuwan da na gaya miki?”
Na gyada kai “to Hajiya”.
“Uwarki ta kauye yaushe ta je Makkah da har kika sa mata Hajiya? Suna na, MUBINA, anan ‘yan aiki na suna ce min “Madam”, amma ke tunda ‘yar wanke-wanke ce zaki ce mun Aunty”. Na sake gyada kai don tabbatar mata na ji abinda tace, na kuma dauka.
Ta zaro ido tace “ya sunana?” “Anty Mubina” “ke kuma fa?” “Atine ‘yar gidan Maikalwa”, ta mike “nace miki ‘BLACK’ kin ce ATINE’, sunan da na tsana a rayuwata. Har da bayanin gidan ku ko daddawa ce gidan ku na tambayeki? Bari in baki maganin mantuwa, shige mu je”.
Na bita a sanyaye, duk jikina ya mace. Tafiya muke lungu-lungu har muka zo kayataccen dakin da zuciyata ta gaya min kichin ne, ba don nasan amfanin kayyakin dake wurin ba, illa don ganin tukunyar girki da nayi.
Ta bude wani farin abu kato mai fadi, iri biyu ne da dogo da gajere, ko ince dana tsaye dana kwance mai fadi, to mai fadin ta bude wai in shiga, bayan ta fidda lemunan dake ciki.
Tsoro ya kamani, jikina ya soma kyarma, ta daka mun tsawar data firgita ni, nayi kundumbala na yi tsallen albarka na fada, ta rufe kif, duhu ya mamayi ganina.
Wani irin sandarewa naji tsokar jikina nayi, in shaki numfashi, in ji kamar ana tura min kankara a hanci. Nayi kara ba murya, sai can ta bude ni na fito, duk na sandare ji nake tsokata kamar ba tawa ba, da kyar in gudun jini ma, bai daskare a jikina ba.
“Gobe in kara cewa sunan ki “Black” ki ce “Atine”, in kara gaya maki abu ki manta, shige ki tafi”.
Jikina sai bari yake da karkarwa, na kunna tafasahshen ruwan nan na surka kadan na shiga ciki na kwanta na soma kuka, jikina yayi min dadi naji ana kwankwasa kofa, na maida kayana na fito.
Tom ne ya shigo yace “maza-maza in je in yi wanke wanke, ta gama karin kumallo, idan kuda ya hau mata kwano, komi tsadar shi a shara take sakawa”.
Tun bai rufe baki ba, ni tuni har nayi nisa da gudu na, dariya ce sosai ta kamashi, ya tabbatar ba karamin tsorata nayi da Aunty Mubina ba. Na kwaso kwanukan na fara wankewa.

*****
C
ikin wata guda kacal na fahimci Aunty Mubina kakaf. Irin mugayen ‘yan gayun nan ne da har gayun ya so ya shafi ingancin addinin su. Tana son duniya, kuma ta sameta a yadda take so, tana cin karenta babu babbaka, cikin katafaren gidan ta kuma babu wulakantacce kuma kaskantacce gareta kamar dan aikinta.
A wurin ta dan aikin ta dabba ne kurum, da idan taga dama, zata ce ya kwanta ta taka shi ta wuce. Gogaggiyar mace ce ‘yar duniya kuma ‘yar boko, ‘yar gata kuma wadda ta dauki auren ta a suna kawai.
Abin nufi, komi da ke gaban ta yafi auren muhimmanci, haka rayuwar auren su da mijin ta, irin rayuwar auren nan ce ta kayi gabas inyi yamma, kowa ya je ya nemo nasa, ba mai jiran dan uwan sa ya zo ya bashi.
Duk da ban san hakikanin aikin ta ba na fahimci ba karamar ma’aikaciya bace, sabida irin jama’ar da take mu’amala da su, da irin motocin da take hawa na kece raini. Babban abinda yake bani mamaki da uwargijiyata shine duk gayunta, ballagaza ce, bata da kintsi ko kadan.
Hatta panties din ta da bra in ta tube nan tsakar dakin take cillarwa, ni zan dauka in wanke in adana mata. In kuwa zata shirya, sai ta hautsina bakidayan dakin ta rikirkito da dukkan sitturun ta dake cikin sif.
Komi ta dauka, haka zata cillar da shi komi tsadar shi, sai ni in bi in gyara, haka ko kayanta masu datti, bata san ta fitar ba a’ah, ni zanyi tunanin ai tasa wadannan jiya, in zauna kullum in ware mata masu dattin.
Sannan duk iya kokarina kullum aikina baya gamsheta, bayan sau dubu zan gyara, sau dubu zata bata, barin ma in bakin ta sun zo sunyi ciye-ciyen su, ni kuma a ranar ba dai hakarkarina yaga katifa ba.
Zagi kuwa da aibatani da take a cikin su, har ya zame min jiki. Rannan ina ji tana ce da aminiyar ta Mansina ita dai Allah ya isa tsakanin ta da mijin ta da ya hana Peter gyara mata daki, don bata ga abinda nake tsinana mata ba.
Rannan kuma naji tana koka mata bakin cikin ta akan wannan cikin da take dauke da shi, don bata son tayi (losing shape) dinta, kuma ko ta haihu bazata shayar da jaririn ba, kada mamanta su rankwafa. Nanny zata dauko daga turai.
Mansina tace “wace Uwa kika taba gani ta haihu lafiya, nonon ta lafiya bata shayar da jaririn ba?” Ni dai nayi gaba ina ta mamakin hali irin na Aunty Mubina.
Domin halayenta gabadaya irin na nasara ne, ta dauki tsarin rayuwar yahudawa ta dora rayuwar ta akai, itakuwa cikakkar bahaushiya ne gaba da baya kamar yadda Tom ya gaya mani.
A ganina girman kanta ta ya yi yawa, domin bata aje kanta anan kusa ba, hatta ‘yan aiki ba kowa takan so yayi mata aiki ba, daga Inyamurai sai Nupe, da ake debowa daga Jihar Neja, rayuwar ta mai tsada ce sosai fiye da ta su Mansina.

Ranar wata lahadi ina canza mata zanin gado lokacin ta shiga wanka, na jiyo ta tana nishi da wani irin wahalallen numfashi, na saki zanin da gudu na je ina kwankwasa kofar nace “Anti ki bude” da kyar tace in murda kofar a bude take.
Na murda na shiga sai na ganta kwance male-male cikin ruwa da karnin dana tabbatar na haihuwa ne, domin a irin yananyin naga Amarya lokacin da zata haifi Sadiya.
Na karisa da gudu na kama ta nace “Anti haihuwa zakiyi” duk da halin da take ciki sai da ta dallamin harara cikin karaji tace “kirawo min Peter” nace cikin mamaki “Anti to gyara zanin ki” wani kofin wanka ta wawura ta maka min a goshi, ba shiri na fito a guje neman Peter, mukayi karo da Tom yana jera mata karin kumallo.
Cikin kaduwa na gaya mishi Anti nakuda takeyi tace a kira mata Peter, bai kira shin ba ya dauki waya anan falon ya kira likitar da ke zuwa yi mata awo gida cikin mintuna goma sai gata ta iso, wata nurse biye da ita ta riko mata kayan aiki, da saurin su suka shiga toilet din da Anti take.
Shiru-shiru, in kai gwauro in kai mari a tsakiyar kayataccen falon. Allah ya gani, ina matukar tausayawa iyayen mu mata a yayin haihuwa. Duk da ban taba yi ba, nasan ba karamar hikimar Allah ce a cikin ta ba. Don haka na daga hannu ina nemawa Anti Mubina sauki cikin nakudar ta, ban san sanda hawayen tausayi suka zubo min ba, duk gayu irin na Anti, in ka ga yadda ta koma lokaci daya sabida azaba, dole ka tausaya mata.
Ihun da take kurmawa, da zagin da take narkawa mijin ta abun babu dadin ji, data lailayo wani ashariya ta yarfa mishi sai da gidan bakidaya ya amshi kuwwar, fadi take ai sai da ta gaya mishi bata shirya haihuwa ba ya sace mata pills din ta, ya hada ta da jangwam, ya tsallake ya barta, amma anyi na farko anyi na karshe ita da shi sai a lahira. Tun da ya fuskanci watan haihuwar ya kama ya gudu yana hutawar shi a turai ya bar ta da bala’in da ya kunsa mata.
Babu kiran sunan Allah babu na Annabi ita dai ya jawo mata ya gudu ya barta, tsakanin ta da shi sai Allah ya isa.
Tom yayi tsaki ya juya ya fita bayan yasa yatsun shi biyu ya toshe kunnuwan sa yana cewa, bazai iya jurar tozarcin da ake wa Ubangidan sa ba. Sai kace a kanta aka fara haihuwa.
Sai karfe hudu na yamma su Anti aka sami kai da kyar. Jariri ya canyara kuka da zazzakar muryar shi kamar gyare, yana gaya mana ya iso gidan Ubansa. Jaririn da ya juya rayuwata dama rayuwar gidan bakidayanta.

Tunda Anti ta haihu bamu zauna ba, hidima muke da karfin mu da lafiyar mu kamar babu tsokar nama a jikkunan mu. Baki ne ke ta barkowa daga ko’ina cikin Abuja duka ta bangaren Anti, amma ko kuda na lura babu daga masarautar Karaye, wato dangin maigidan
A kullum Tom ya daura tukunya ya sauke akalla sau goma. Ni kuwa shara, wanke-wanke da goge-goge kamar in ji don ma yawanci komi da inji ake yin shi.
Akwai wata kanwar Anti mai suna Mimi har fargabar zuwanta na keyi domin in ta soma “ke Black dauko mun kaza, karbo mun kaza, miko min kaza har sai kafafuna sun sare. Ana i gobe suna kuwa kafafun ta tasa a ruwa wai in goge mata kaushi, taje wajen wanki kaushin sun tashi gashi gobe zasuyi luncheon din suna.
Cikin mamaki na dubeta, ba tare da ko dar ba nace “wannan ba aikina bane.
An dauko ni shara da wanke-wanken Anti, amma ba a ce da Ubana zan dinga yin gugar kaushi ba”. Daga hannun nan da zatayi sai fauuuu! Ta dauke ni da mari tace bari in je in ji idan ita maijegon ne tace ki dinga yi mun rashin kunya.
Ai dama da ganin idanun nan naki kwala-kwala nasan yarinyar nan ke nan gaba abin tsoro ce.
Ina daki ina ta kuka Anti ta fado dakin ta soma surfa min zagi, tace daga yau Mimi ta sake sani aiki nayi mata musu, to a bakin aikina.
Bayan sunan da aka yi shi da sati biyu ga yadda na fahimta maigidan ya dawo, aka sake wata walimar a rockview, wadda Tom ya kawo mana jarida mai dauke da hoton Anti da Babyn da fuskarshi ke kunshe cikin farin shawul matar shugaban kasa na mika mata kyauta, nade cikin wata leda mai kyalkyali, cikin mamaki nace
“yaya Baban Babyn bai shiga hoton ba?”
Yayi wani irin murmushi mai nuna matukar kauna da gimamawa ga wanda na ambata (charismatic devotion) yace
“Ogan mu, ba daya yake da sauran mutane da kika sani ba!”.


T
unda aka haifi Dan nan bamu san kalar shi ba, sabida yadda ake kulawa da shi ko kwai sai haka, sai dai mu hangoshi daga nesa a hannun baki masu zuwa, wadanda kallo daya zakayi masu kasan sune jama’ar Anti Mubina, wato daga matan ministoci sai na manyan ma’aikatan Banki abokan huldar ta, da basu san me ake kira talauci a rayuwar su ba.
A wata asabar ce Anti da Mimi sun baje kyaututtukan da Babe ya samu suna hira, ni kuma ina durkushe gaban t.v ina gogewa, Mimi ta dube ni tayi tsaki tace
“wallahi Anti ko kadan yarinyar nan ba ta dace da aikin ki ba kwata-kwata ba ajin ki bace, wai baki san ko ‘yan aikin yanzu ba kowanne irin kwashi-kwaraf ake dauka a Abuja ba?
Kin dauko yarinya sai tsayi zankankan da manyan ido kaman ta cinye mutane, ni wallahi duk sanda na daga ido na dubeta sai na ji gabana ya fadi, sabida tsoron da idanun ta suke bani”.
Anti ta yarfar da hannu, tace “oho! Fulanin Sarki ta aiko da ita kema kin san ban isa in maida ta ba, dama kadan ake jira a aibata ni, don ita ta zuge shi wai bai dace Peter ya dinga shiga uwar daki na ba…”
Mansina ta jirkito daga cikin kujerar da take kwance, ta dubesu daya bayan daya tace cikin mamaki.
“Wadanne idanuwa ne suke baku tsoro, kodai suke saku kishi? Ku dubi idanuwa sparkle (masu walkiya) kuce suna baku tsoro?”
Ni dai jikina na rawa nayi hamzarin fita na barsu batare da na ji amsar da Antin ta bata ba, ban san yadda suka kare ba. Sai dai daga ranar na fahimci Anty ta kara daure mini sosai haka duk wata kafa ta hutu, ta toshe mini ita a gidan.

Baby nada wata daya, rannan ina wanke kwanukan da aka ci abincin rana, Tom yana tsaye daga can baryar sa yana kiciniyar daura tukwanen dare. Wata murya muka jiyo daga can kofar shigowa tana kiciniyar shigo da akwati tare da nemen iznin shigowa falo.
Ba muryar matar ne ya samu fitowa dukkan mu ba illa yaren da take magana da shi. Ni dai nasan wannan ba hausa bane ba kuma yarbanci ba haka ba fulatanci ba.
Wata yamusashshiyar baturiya ce, da alama ko cikin turawan wannan babu wata wadata ajikinta, tana tura akwatuna masu taya guda biyu (trolley), gashin kanta ja ne irin turawan nan masu jan gashi da ake kira ‘blonde’, zatayi shekaru arba’in.
Tom ne ya amsa mata yayinda ni kuma na saki baki ina kallonta, shi yayi mata jagora zuwa falon Anti, can anjima Anti ta rika kwala min kira na je na tsugunna a gabanta, tace
“kwashe shirgin ki daga dakin ki, ki maida su dakin da ke kusa da shi, wannan falle dayan, Tom zai kwashe injinan sharar da ke ciki, na bayar a sayo maki karamar katifa” nace “to” murya ta abin tausayi.
Ina kwashe kayan ina hawaye don ba karamin sabawa da dakina nayi ba, duk da cewa shima wancan dakin cikin bangaren Antin yake, amma babu toilet, don haka na koma na tambayeta ko da wane toilet zan dinga amfani?
Ta kunduma min ashar tace ai talaka bai iya samun wuri ba, a gidan Ubanki ba a filin Allah kike kashin ba?
Kamar in ce da ita ai in ma a filin Allahn ne, akwai kasar da zamu haka mu bizne, nan kuwa fa? Da tangaren shine abin takawar ku? Sai da taga dama tace in dinga shiga dakin muna amfani da shi mu biyu.
Daga baya ne Tom yake gaya mani mai raino ce baturiya Aunty ta dauko bada sanin Oga ba, sabida a gobe ne zata koma aiki, tuni ta so ta dauko ta tun Baben yana sati biyu sabida hutun da aka deba mata ya cika.
Yace Oga yayi-yayi ta aje aikin nan ta kula da yaron ta taki, nonon ma da take bashi, wanda ba kullum ba, ba karamar badakala a ka kwasa da ita ba kafin ta yarda ta dinga ba shi sau uku a rana, sai da yayi karar ta gun Baban ta tukunna.
Don tana tsoron Baban ne yasa take bashi amma ita tana ganin rainon yara bai dace da ita ba a wannan lokacin dai da take kan gabar kuruciyar ta, haihuwar ma Allah ne ya kaddari yaron mai numfashi ne a doron kasa, amma bata shirya mata ba, ba kuma kokarin da bata yi ba don zubar da cikin abin ya ci tura, karshe dole ta hakura, don har kasar waje ta je a fitar mata sun tabbatar mata ko dai ita a rasata ko mahaifar ta gabadaya, sabida cikin ya girma sosai a lokacin shiyasa ta hakura. Nace
“amma da ta haife shi ai gashi nan tana son shi, ko kuda bata bari ya taba mata shi”. Yace “wannan ne dai kuma bani da tabbaS a kai (tana son shi ko bata son shin?)”.

Tun zuwan Elizabeth bama jin dadin zama da ita, kwata-kwata ta maida mu ‘yan aikin ta sai kace itama ba ‘yar aikin bace. Ita aikin Baby kawai take wanda nake ganin kullun ta sa shi cikin wani keke ta tura mai fankon fida a baki (kan fida kawai babu fidar da turawa ke sarrafawa don hana yaro yin kuka) ko ta dau keken goyon jarirai ta hada da bayanta ta kulle, bayan ta sanya shi a ciki, tana harkokin ta ko kallo bamu isheta ba. Wani zubin kuma sai ta sashi cikin wani irin lilo mai kamar gado tana cillawa a hankali, hatta madarar da take bashi a kididdige take, sai ta auna, ko kusa ko da wasa bata bari wani cikin mu ya je ko kusa da shi.
Duk abinda Tom ya dafa sai tace bai yi mata ba, ya sake dafo mata wani. Wata rana kuma taje kasuwar Wuse (Wuse-Market) ta sayo kaguwa da dodon kodi tazo ta soya, yawancin abincinta kwari ne, in ta so kuma ta aiki Peter manyan gidajen cin abinci dake cikin Abuja ya sayo mata abincin kasarsu, wanda duk rabin sa tsutsotsi ne da ganyayyaki.
Ranar da na fara ganin ta tana loma da tsutsotsin nan, wuni nayi ina kwarara amai sabida kyankyami, daga ranar kuwa ko plate ta taba bana kara cin abinci da shi, ita kanta ma tsantsamin ta nakeyi.
Gata da kazanta a toilet, sai ta cire auduga (pad) batacciya ta ajiye a kan bahon wanka, sai dai ni da abin ke daga min hankali in dauke mata. Ko ta jika kaya taki wankewa sai sun yi tsami haka tun zuwanta bandakin mu yake wani irin zarni.
Ni dai na ji ance turawa suna da tsafta, amma wannan ko a cikin kazaman turawan ma ta daban ce. Ko brush tayi bata san tasa ruwa ta wanke kumfar daga cikin sink ba haka zata barta ta bushe, ko kuma ni in wanke mata. Gata da fadin ran tsiya. Tom boyi-boyin ta, Peter dan aiken ta, ni kuwa ‘yar aikin ta.
Ejiro da baya sakar mata fuskar har da zata raina shi, shi ta mayar makiyin ta, kullum cikin bata shi take a wajen Anti, don dai Antin na son aikin sa ne kawai da tuni tasa an sallame shi.

Tsaye muke nida Tom a kichin kowa na aikin sa, yayi kwafa yace “nifa zaman matar nan ya ishe ni Tine” nayi dariya nace “da yake kai ka ajiye ta ba?” yace “Allah ba zancen wasa ba, kiga kullum sai na gama abinci ta zo tace bai mata ba, in sake, an gaya mata aikin ta nake, Allah ko Oga na ban taba yi mai girki yace bai mishi ba, sai wannan matar, who the hellshe thinks she is, tana ‘yar raino ina kuku, matsayin me ta fini?”
Nayi murmushin da ya kara kular da shi don ni kadai nasan hakurin da nake da Elizabeth, shi nashi shafar mai ne “kome takeyi daurin gindi ta samu daga Uwar-gijiyar ta, amma da bazata yi ba”.
Tom ya kuta yace “ban ga dama ba ne, na rantse da tuni ta bar gidannan, don Oga bai san da zaman ta ba, a tunanin shi Aunty na tafiya da Babyn wajen aiki ne” nace “akan me zaka fada mishi? Ina ruwan ka da sha’anin su, kai dai kayi aikinka na kuku, a biyaka ba shike nan ba?
Ni ka ganni abin da Allah bai daura mun ba kenan, shi ga abin da babu ruwa na. Idan ba so kake Anty tayi sanadiyyar lalata hanyar abincin ka ba”.
Bai yi magana ba, amma yanayin fuskar shi ya nuna maganata tayi tasiri a tare da shi.
Rannan Anti ta tafi aiki, Elizabeth na wanka ta bar Baben yana ta kyanyara kuka, ba tun yau ba ina kallon ta idan har ba Anti na gidan ba bata wani mai da hankali kan yaron, sai ta bar shi yayi ta kuka har Allah ya gajishshe shi.
Naji bazan iya jure kukan da yaron ke yi ba, domin kuka yake har cikin kwakwalwata. Na lallaba na leka dakinta naga bata fito ba, na shiga da sauri na sungumi Babe nasa a bayana, na dau towel din da aka nade shi da shi na goye shi tam, a bayana, ina zagaye dakin da shi ina jijjiga shi.
Wannan shine babban buri na a rayuwa; in ganni goye da jariri, ina jijjigashi, ina yi masa rawa ina cilla shi ina cafewa. Rabona da goyon jariri tun ina rainon Jafaru. Don haka yau na jini cikin

Please Login or Register in order to submit comment