Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani sabon nishadi.
Shi kuma jaririn da na tabbata ba’a taba goya shi ba, tunda uwar sa ta haife sa, sai yayi tsit daga kukan da yake, yana ajiyar zuciya. Sai naji tausayin yaron ya kamani.
Tausayin sa nake, ba don bashi da gata ba, yana da gatan komi, amma ya rasa gatan da yafi komi amfani da muhimmanci a gareshi, watau dumin jikin Uwa, a dai-dai lokacin da yake tsananin bukatar shi.
Na tabbata ba kukan komi ya ke ba tunda babu yunwa a tare da shi, illa kukan jin sa shi kadai ba tare da da kowa ba, balle Uwar da zai laluba ya rungume har ya samu damar tsotson abin da yafi komi dadi a gareshi, wato nonon Uwa.
Ban san sanda Elizabeth ta fito ba sai jin ihunta nayi a kaina tana afi tana kakabin a kawo mata agaji “Help! Help!! Help!!! The Baby will die” wato Dan zai mutu.
Nayi saurin sauke mata shi sabida yadda ihunta ya kidimani ya gigitani. Wai ashe duk wannan ihun da take na goya shi da nayi ne, da gudu tazo tana tattaba kafafun shi ta gani ko na karya shi?
A sukwane Ejiro ya shigo ta shiga gwada mishi tale-talen da nayi wa Baby har tana daukar filo tasa a bayan ta da zani, yayi tsaki ya fice nima na fice yana ta yi min korafin ni me ya kaini shiga shirginta.
Ashe bata bar zancen ba domin Aunty na dawowa da gudu ta kai mata dan ta tana kuka wai bazata iya zama ba tana gani in kashe shi a daura mata laifi, ta gwada mata yadda nayi mishi Antin takira ni tasa ni a gaba, yau ma a firji ta sani, wai karambani na yayi yawa, gobe in kara goya mata Da.
Don haka washegari na tashi da matsanancin zazzabi ko gani bana yi sosai, musamman da yake a watan Fabrairu muke, sanyi yayi tsanani ainun. Aka kuma sani a firinji, na kwana hancina na yoyo, kuma a cushe ta yadda hatta numfashi ta baki nake iya furzar da shi.
A haka na rarrafa na shiga dakin Anti don ka’ida ne kafin ta fito na gama da falo, da zarar ta fito sai in shiga cikin dakunan barcin in gyara mata. In banda rawar dari ba abinda nakeyi duk da riga (suwaita) mai kauri da ke jikina, ina yi ina hutawa in na jiyo motsi in yi saurin mikewa, in cigaba.
Sama-sama na jiyo muryar Anti daga ‘dining’ wato kwararon da aka zagaye da farin labule da makeken tebur, domin cin abincinsu wanda ke gefe guda na cikin falon, tana lissafo kudin aikin ma’aikata na wannan watan, da alama da Maigidan ta take magana.
Yana magana ne a hankali don haka bana jin me yake cewa, sabanin ita da take da karfi, don daga baya ma fada-fada ta koma magana wai babu inda Elizabeth zata, waye zai dinga kula mata da Babyn sai dai in shi zai dinga goya yaron yana tafiya nashi ofis din, amma ita bazata bar aikin data bata shekaru goma tana wahalar karatunsa ba, sabida wani yaro can (unwanted Babe) da ya zo mata ba’a sanda ta shirya haihuwarsa ba.
A fusace kuma cikin fada yace “ina yarinyar da ke maki aiki da Fulani ta aiko daga KARAYE? A bata Babyn ta dinga kula da shi, amma wannan matar yau zata tafi, bazan biya wadanan makudan kudaden ba, sabida ba’a kasa na ke tono kudin ba.
Idan kuma kina ganin hakan bai maki ba, to zan dauke shi in kai shi gaban Fulani, tunda ke da kika haife shi, kika fi kowa sanin ciwon sa, bazaki zauna ki kula da shi ba.
Kina kiran shi (unwanted Baby) Mubina, a gareni yafi ki, ya fi min komi na duniyar nan da abinda ke cikin ta.
Don haka idan zaki aje aikin ki bashi kulawar uwa da ta dace, to, idan kuma bazakiyi ba, to cikin biyun da na baki zabi dole zaki zabi daya”.
Ga yadda tayi shiru bata kuma magana ba, maganganun nasa ba karamin kada ta su kai ba, jin an ture kujera baya za’a taho falon nace kafa! Me naci ban baki ba, kada su ce ina masu labe, bayan kuma ba haka bane, aikina ne ya kawo ni har ga Allah bani da wannan halin.
Kafin azahar ba sai muka ga Elizabeth ta turo akwatunan ta ba tana ta zobara baki, Ejiro aka dankawa nemo visar ta yana tsaye rike da passport dinta a hannu, yace tabar akwatin, tafiyar sai jibi wajen visa za su je. Ni da Tom har tsalle muka yi a daki don murnar tafiyar Elizabeth, Anti kuwa ta cika tayi fafam, kiris take jira ta fashe don haka muma muka shiga taitayin mu ba wanda ya nuna ya san abinda suke ciki.
Na shiga aiki washegari, da misalin karfe bakwai na safe, na tadda Anti tayi shirin tafiya aiki, tana zaune cikin luntsumemiyar kujerar falon ta, tana cika tana batsewa. Ita wannan sabida tsabar son aikin ko in ce son kudin, duk wani ma’aikacin banki takwas take masa a ofis amma ita Anty sabida tsabar zafin nema bakwai da rabi abankin su take mata, Da da miji kuwa ko oho, don shi kan sa Oga tana riga shi fita.
Tom ya gaya min cewa Anti Manajar Banki ce guda don haka in daina mamaki, tace “ajiye tsintsiyar kizo nan” da sauri na ajiye na zo na russuna agabanta “kina da masaniyar gobe ne Elizabeth zata tafi?” “Ban sani ba Anti” “to in baki sani ba gashi na gaya maki, don haka zaki dinga kula da JAWAD kamin in dawo aiki, don bana son Baban shi ya maida shi Karaye, kina jina?” Na gyada kai da sauri.
“Daga yau karfe bakwai nake fita aiki, don haka zaki zo ki dau Jawad kiyi mai wanka, ki shirya shi yadda nursezata zo ta koya maki, duk kayan shi dakin ki zasu koma bana son rainon Babe.
A rana sau uku zan gan shi, in bashi nono sau uku; da safe kafin in tafi, da yamma idan na dawo da kuma da daddare kafin ya kwanta barci. Idan kuma na yaye shi, a wurin ki zai dinga kwana.
Ki cigaba da wanka sau uku a rana, kamar yadda na gaya maki a farkon zuwanki don kar ki shafawa dana datti. Aiyukan da kike a da, gabadaya an dauke miki Peter zai cigaba da yi, dama shi yakeyi.
Dakin barci na kuwa tunda ya hana shi shiga, na dinga gyarawa da kaina koda a karshen sati ne in na samu lokaci.
Don haka ki maida hankali bisan aikin ki na yanzu kadai, KULA DA JAWAD.
Ba’a goya min da, kada a karya masa kafa domin siriri ne. Akwai gadon shi, akwai abin shan iskar shi duk za’a kawo su wurin ki. A rana zaki canza mai ‘pampers’ sau shidda. Ki kwaso kayanki ki koma dakin ki nada idan Elizabeth ta tafi gobe”.
Nayi godiya na mike na fito duk jikina babu kuzari. Daga wanke-wanke kuma na koma ‘Nanny’ babu yadda rayuwa bata yi da dan Adam. Ta wani fannin kuma ni dama RAINO NA FI SO A RAYUWATA.

Dana gayawa Tom yadda mu kai da Anti, bude baki yayi cikin mamaki, ya kuma fi mintina biyu bai rufe ba “Tine, ka lissafa kanka cikin masu sa’a a duniya. Uwar-goyon Babe Jawad? Zaka ji dadi wurin Oga in ka ba Jawad kulawa mai kyau. Yana son Jawad, fiye da komi a rayuwar shi.”

Ina wanka da safe naji ana kwankwasa kofa, na sanya wasu sababbin riga da siket jajaye cikin irin kayan da Talatu ta hada min ne.
Na bude kofar ba tare da na tambayi ko wanene ba, wata macece mai dan jiki gajeriya, tana sanye da fararen kayan asibiti, da alama mai kirki ce tayi min murmushi tace “ke ce mai rainon Jawad ta yanzu ko?” “Eh” “ni sunana Sister Sadiya Danladi, (nurse) ce, an turo ni musamman domin in koyar da yake yadda ake yiwa yaro wanka, da yadda ake ba shi abinci bisa ka’ida da sauransu don haka zauna ki saurare ni”.
Tayi min bayani tiryan-tiryan har na gamsu na yi mata godiya ta tafi.
Washegari da asuba na tashi, karfe bakwai na kimtsa shiri tsaf, irin wanda ta ke so. Na je falo na jira ta har ta fito cikin shirin fita. Na gaisheta bata amsa ba ta miko min jaririn. Na sa hannu biyu na amshe shi cike da dukkan kulawa.
“Sai karfe biyar nake dawowa, ba’a soma bashi ruwa ba tukunna, sai yayi wata shidda, yau watannin shi hudu, zaki fara shayar da shi madara yadda sister Sadiya ta gaya miki, an kai miki kayan tun jiya sai na dawo”.
Na zauna bakin gadona na sanya Babe Jawad cikin ni’imtaccen gadon sa, na kura mishi ido kurrr! Allah gwani tsatstsarka, daya nufi mummunar mace kamar Aunty Mubina da haifar kyakkyawan yaro irin Jawad; Fari ne sol, sumar kanshi mai yawa baka wuluk, hancinsa dogo zirit, labban sa jazur ‘yan kaurara, kanana, yana da cleft da kyawawan yatsun kafa da hannu. Ban taba yi masa wani kyakkywan kallo ba sai yau.
Kaunar yaron ta tsirga mani tun daga tsakar kaina, zuciyata, bargona, kasusuwa har yatsar kafata. Na fiddo shi daga cikin gadon na rungume shi tsantsan a kirji na, tamkar na tsaga kirjin na sanya shi, in haifo shi ya zan mallakina.
A haka barci ya sure mu, motsin shi na ji cikin barcin yana shafa ni yana neman nono kenan. Na tashi na farke katon din da ke ajje a gefe, na fiddo wata irin madara wadda jikina ya bani ko a cikin madarar yara, wannan ta musamman ce. Hoton kyakkyawan Babie ne a jiki, amma sai naga bai fi Jawad dina kyau ba.
Na debi adadin da Sister Sadiya ta ce min, na duba iya lambar da ta nuna mini a jikin feederna tsiyayi ruwan dumi da ke cikin flask na hada na jijjiga sosai, na bar shi ya dan sha iska, na zaunar da shi a cinya ta, nasa mai kan fidar a baki, ya ko kama da karfin sa, kadan yaki shanyewa.
A raina nace haka kawai a ce bazan ba dan Adam ruwa ba, sai yayi wata shidda? Don bani da imani ko don me? Yaran gidan mu an basu ruwa tun a ranar da aka haifesu, kuma sun rayu lafiya, don haka sai na ba, Jawad ruwa.
In Tom zai kawon abinci, yakan hado da wani ruwa da naji yana cewa FORMOSA table-water, na je kichin na dauko mara sanyi, na zuba a murfin fidar kadan, na daura mai a baki, yaro ya kwalkwale ruwa da sauri, na kara cika murfi, ya shanye, na karamar, ya rage rabi, yana dubana da kyawawan idanun sa ya shiga bangala mani dariya, nima sai naji dariyar, ta kamani.
Na sa shi a bayana da tawul din sa na goye shi cike da matsananciyar, kauna. Ko Uban wa ya ce mata goyo na karya kafar siririn yaro? Ni har bakwaini na goya, na kuma sauke shi lafiya.
Daga goya shi sai barci ya dauke shi, na kwanta rub da ciki da shi a bayana. A haka Tom ya cimmana, hannun sa rike da bakar leda, bai san sanda ya saki ledar a kasa ba “lalala! Ka goya dan kwan gidannan? Babu goyo, babu goyo, Anti zata zage ka Tine”
“Tom mu Hausawa da goyo muka rayu, itama uwar ta ta goya ta, akan me zata ce bazata goya nata ba? A kan wani dalili maras tushe da asali? Kayi hakuri bazan bari ta gani ba” ya kyabe baki, daga bisani yayi dariya, nasan mamakin karfin hali da karambani na yake.
“Is not my own business” “me kenan ka ce?” “Nace (babu abinda ya shafe ni), I brought to you something special (na kawo miki wani abu na musamman) wanda nasan zaki yi murna da shi”.
Ban ji me yace daga farkon ba, illa naga ya zaro wasu littattafai iri-iri daga ledar da da ya shigo da ita, duk na koyon karatun turanci da rubutu, irin na ‘A for Apple’ da suran abubuwa da sunan su ya fara da A, haka ya tafi har Z, kowanne da hoton abin radau cikin kala, muka shiga karatu, ko abinci bamu ci ba.
Karfe hudu ya tashi ya kawo min, farfesun gudar kazar gidan gona, da biredi, wai inyi maneji kamin ya gama girkin dare.
Nayi Sallar la’asur sannan na sauke Jawad, sai ya bude ido, na sake dama mai madara, wannan karon har da nutriend din da tace kar in bashi wai ya wuce shan shi, abinda localyara ke sha ne, na kuma bashi ruwa, na kaishi cikin robar wankan shi na fidda mai pampers, wadda bai yi komi a cikin ta ba sai gumi. Nayi mai wanka da wani irin tsadadden sabulun Babies dana gani cikin kayansa, bayan na zuba duk wani abu da Sister tace in zuba.
Ina sanya mai kayan sanyi Tom ya shigo dauke da tray, na ce “da ka koma da shi, wannan ya isheni sai ko ‘dinner’ naji kana cewa ko?” Ya yi min tafi“Yauwa, haka nake so Tine, ka dinga rike, duk abin da na fadi cikin turanci, da haka zaka saba. Daga sati biyu masu zuwa, ka daina magana ‘in Hausa’.

Sati ya zagayo, na soma yara turanci da Tom, ya dinga kunna min labarun BBC, labarun kasa da sauran su, suna yi da babban turanci yana bani bayani cikin sassaukan turanci, rubutu kuwa na iya rubuta su Ant, Ball, Cup. A satinne ta kara turani saloon, da wurin gyaran akaifa, don wai taga alamar yakushi a wuyan danta, bayan shi ya yakushi kan sa. Wannan karon da Tom ta turani.
Wani yammaci bayan ta fita, na gama dirkawa Jawad abinci na goyashi, na tadda Tom da Ejiro a Kichin, suna ta kiciniyar kwabin ‘coconut-sandwitch’ da ‘beef burger’ And shawarMah, abin ya burgeni, ya kuma bani sha’awa, ganin komi da inji suke yi, ba wahalar komi sai ta tsayuwa.
Nan na zauna kallon su har suka kare. Na tabbatar abin ya zauna a kaina, ko yanzu aka ce in yi yadda sukai, zan iya kamantawa.
Daga ranar duk sanda suke girki, in dai Maman Jawad bata nan, sai in goya shi in je in zauna in ta kallon su, muna hira suna kara min bayanin komi.
Watarana nace da Tom don Allah ya samo min waken suya (soya-bean), ya tambaye ni abin da zanyi da shi nace wani kamu ne muke sha a kauye.
Kullum sai in yi kamun waken suya mai tsabta, in shige da shi dakina in kulle, in yi ta durawa Jawad, shiko komi na bashi ya shanye shi tas. Bana bari yayi awanni biyu ban bashi abinci da ruwa ba, ba ruwana da wani kididdige, shiyasa yake yawan fitsari da kashi, in fidda in wanke shi tas in canza masa. Cikin watanni biyu kacal da dawowar shi hannu na, yaro ya shiga wata irin kiba da wayo mai ban mamaki.
Wani marece Tom yake ce da ni “Tine ka iya raino mai kyau, hannu ka mai albarka ne. Dubi yadda Babe ya koma daga zuwan shi hannu ka, yaro dan siriri ya koma ‘Bouncing Baby”.

Washegari ranar naga sun fiddo na’urorin gyare-gyaren gidan, dukkan ma’aikatan sun kasa zaune, sun kasa tsaye aiki suke cikin kuzari da zafin nama tamkar ana yi masu allurar kuzari. Ga wani nishadi na babu gaira babu dalili, tattare da kowannen su.
Maman jawad ta iske ni har daki na tana daga shi da kyar, don wai bata iya daukar shi yanzu kada ya sata ciwon kirji.
“Yau Abban Jawad zai dawo daga tafiyar da yayi Kasar Canada, idan ya nemi Dan sa, ki je ki kai masa, ki tabbatar kin gyara shi sosai, in ya nemeni ki ce ina gidan kwamishina Mansina ce ke fama da mura, amma zan neme shi a waya anjima”. Na amsa da “to”.
Ina sallah, nayi sujjadar karshe ina sadar da bukatu na ga lillahi, Tom ya shigo, ya-zauna-ya-zauna har ya gaji ya tafi, can kuma ya dawo “Tine pieous (wato mai Ibadah), ni zani (lecture) sai biyar zan dawo. Mun gama shiryawa Oga Spanish-Lunch, idan zai ga Jawad zai nemeki da kansa, ba ruwan shi da matsantawa irin na Anti”.
Na rungume Jawad a kafaduna da ya soma kokarin tashin daga barci nace
“yauwa! Dama tuntuni ina so na tambayeka Tom, tun da nake, ban san dan aiki yana da ‘yancin zuwa makaranta ba, har ya fita sanda yake so, ya dawo sanda yaga dama? Imagine!”
Ya kyalkyale da dariya sosai yace.
“Ogan mu, mutum ne da baya dannewa dan Adam hakkin sa ko kadan. Mutum ne mai masifaffen Ilmin boko. Ba kowadanne Iyayen gida ne irin Ogana ba!.
Bai zama da wanda bai ilmi, shi ba mazauni bane haka matar shi da muke zamanta bata faya zama ba. Mu biyar ne duk maza, ita ta kawo mu ba shi ba, amma yace lallai tun da mun yi sakandire, mu tafi makaranta.
Zama a karkashin sa baya nufin bamu da ‘yancin sauran abubuwa masu muhimmanci a rayuwar bil adam, musamman Ilmi. Ni da Ejiro, muke kuku, don haka muke karantar ‘catering’, Peter da Joseph da ke kula da gida, tattalin gida suke karanta, Samson da ke kula da shukoki yana karantar ilmin tsirrai (Botany) a Jami’ar Abuja.
In daya nada darasi, daya baya da shi, zai yi aikin gida kamin daya ya dawo koda ba aikin sa bane, wanda yawanci, mu ke cinye abinda muka dafa domin ita bata cin abinda ya hau wuta, sai na gongoni.
Shi kuma Oga, asalin shi kauye, bai son wannan tsarin, in yana nan zai bamu odan muyi masa tuwon semovita miyan danyen kubewa da busasshen kifi, yace kunun aya yace kunun zaki. Wallahi in kinga abinda yake ci, sai kin raina mishi. Matsayin shi; Minister ofForeign Affairs, ( Ministan huldar Nijeriya da kasashen waje).
Sun yi artabu da Anti akan zuwan ki, domin a da, Peter ne ya keyi mata dukkan aiyukan da kike yi, Oga ne yace bai lamun ta ba, katon namiji ya dinga yi mata hidima, ya gaya wa mahaifiyar shi cewa a sama mata ‘yar aiki mace, kuma karamar yarinya, haka sunyi artabu akan cewa da yayi ke ki dinga kula da Jawad, tunda ta dage bazata bar aikin ta kan rainon yaron ba.
Domin Anti ta dauko mai raino daga Brussels can cikin kasar Belgium (Elizabeth) da zai rika biyan ta tsabar dalar Amurka dubu dari da hamsin a kowanne wata, shi kuma ya dage, wanda ba dan AREWA ba, ba kuma dan masarautar su ta KARAYE ba, ba zai rainon mishi dan jinjirin shi a duniya ba.
Ita tana ganin Bahaushe kazami ne, sai kace ita ba bahaushiyar bane. (‘Yar asalin garin Zaria ce).
Ya kara da cewa “Ki saki jikin ki da Oga mutum ne mai saukin kai, zaki ji dadin zama da shi fiye da Anti, domin suna aure ne amma halin su daban-daban. Sai dai kada ki yi mata abinda bata so ko kadan, zata ci miki mutunci daga ke har shi, don bata darajashi sam.
Talaka da dabba a wurin Aunty basu da maraba balle kuma dan aikin ta. In kinga yadda shi kuma yake jan mu a jiki, yana jin damuwar mu, kamar kannen shi da suka fito ciki daya, wadanda ta haramta masu zuwa gidannan sam, kiyi takatsan-tsan da Anti, “bata da mutunci”. Ya fada ya kara maimaitawa har sau uku, domin kara tsoratar da ni ga kowace ce Uwargijiyata (Aunty Mubina).

Bayan tafiyar Tom, na dade ina sake-sake, gami da jinjina abin da na ji a raina, ba a jima ba naji dirin ribda-ribdan motoci, na dau Jawad cikin nutsuwa nayi mai wanka, na fiddo sabbin kayan shi da ban taba sa masa ba zubin su kakin sojoji, na saka mishi, na zura mai sabon takalmin shi, rufaffe sak dana sojoji mahadin kayan, na taje yalwatacciyar sumar shi na mulke ta da mai mai kamshi, sai kyalli take ta kwanta lub a dokin wuyan shi. Na dauko turarukan shi ‘Dune’ da ‘Calcutta’ na feshe shi sosai.
Na dura mai kamu na na goge mai baki, na bashi ruwa ya sha ya koshi yayi gyatsa, ga yadda yake mun rigima nasan so yake in goya shi yadda na sabar mishi bayan cin abinci. To amma ta yaya zan goya shin? Uwar sa ta hana balle Uban sa?
Na sashi a kafaduna nayi ta jijjiga shi amman ya ki yin shiru, kuka harda digon hawaye.
Ejiro ya shigo “A’ah Jawad, kuka, why? Papa ya dawo” ya karbe shi
“Nanny Tine, Oga wanna see his son, gashi yana kuka” nace
“goyon da nake mai yake so, gashi bana son su san ina goya shi, kai dai kai shi hakan, watakila in ya ga uban yayi shiru”. (An dan jima Ejiro ya dawo)
“ki zo ki goya shi yace”.
Gabana ya fadi dam! Zuciyata ta tsinke, na fiddo’yan idanuwana hantar cikina na murdawa, muryata abun tausayi nace
“Haba Ejiro? Meyasa ka ce ina goya shi? Idan ya gayawa Anti fa?”
Ejiro ya kyalkyale da dariya, yayi mai isar sa ya gaji.
“Tine, Oga ke biyan ki ba Anti ba, shi yace kiyiwa Jawad rainon AREWA, shima dan garin ku ne ya san goyo. Shi da kan sa yace in kiraki, ki goya Jawad yayi barci. Ya kuma tambayeki, me kike ba Jawad yayi girma mai ban mamaki, cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba?”
Gabana tamkar ana luguden kirjina da tabarya, doguwar rigar Jeans ce a jikina mai kauri, cikin kayan da aka sai min babu kallabi balle mayafi, sai na dauki tawul dina da ke toilet na yafa, Ejiro na gaba ina binshi zungui-zungui kamar wanda tayiwa sarki karya, har falon Yallabai, wanda duk gidan babu kamar sa, haka ko da wasa kafata bata taba taka hanyar ba.
Na makure can gefe. Ejiro ya russuna gefena. Ya fito daga wata kofa rungume da Jawad a kafadun shi, ban daga kai ba balle in san kamannin shi, illa ina ganin farin tafin kafar sa mai tsayi. Gabadaya falon wani irin kamshi da sanyin ni’ima ke fita cikin shi mai ratsa kasusuwan jikin dan adam.
Daya doso mu, zama yayi cikin kujera daga can nesa da mu. Suka yi magana cikin turanci da Ejiro, ban fahinci me suke cewa ba domin turancin nashi ma na ji shi ba irin na su Tom bane.
Wannan lafiyayye ne da ba broken a ciki. Abinda ya kidima ni, ya kuma sani mance a inda nike, shine muryar shi da tayi mun bala’in kama da ta BELLO WAZIRI. Karon farko da naji muryar sa suna magana da Anti, a watannin baya, a hankaIi yake magana, don haka ban ji hakan ba sai yau.
Can cikin tsakar kai na na tsinkayi sautin nashi yana cewa
“ba kya gaida mutane?”
Nayi firgigit na zabura nace
“ina yini?”
“Lafiya, yaya kike da kukan Jawad? Tun da na dauko shi yake kyanyara min kuka, sai yanzu da Allah yasa yayi barci kunnuwana suka huta”
nayi murmushi kaina a kasa
“ni baya min kuka”
“me yasa?”
“Nima ban sani ba”
“don ke Nannyn shi ce?” Nayi shiru cikin rashin sanin abin cewa.
Ya basar da zancen yace
“ina Uwar shi ta je? Bayan yau Lahadi ba aiki?”
“Tace mun zata gidan su Mansina, zata nemi Yallabai a waya”
yayi dariya har Ejiro sabida yadda nafadi sakon babu kari, babu ragi da yadda ta gaya mani.
“Bata san zan dawo yau ba? Ko don ita bata damu da mijin ta ba, balle dan ta? Yau watanni biyu bana kasar, na dawo cike da dokin su, amma rana daya an kasa tsayawa domina?”
Duk mukayi tsit, daga ni har Ejiro, ko tunani yayi a kan karan kansa, wannan ba ruwan mu bane? Oho! Yace
“O.K, zo dauke shi ki goya shi”.
Na mike cikin nutsuwa, na isa gareshi, na mika hannu ya miko min Jawad, sai na hade da hannuwanshi duka biyun, YA ILAH! Na tsorata, na kidime, na rude nace “kayi hakuri, ban sani ba” “kema kiyi hakuri, to goya shi ina gani ko na koya, nima wataran in hutar da ke!”
Na dago ido a rikice na dube shi, alamun

Please Login or Register in order to submit comment