Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

neman na kai.
Amma duk da haka Baba bai taba cewa a taba kayan Bello ba, ko mai yasa? Wallahi oho?

****
I
na tsaye ina surfen ‘yar ragowar dawar data rage mana zamu yi tuwon dare. Sallamar Haj. Talatu ni na amsa ta, na santa baiwar gidan Maimartaba ce mai ji da kanta amma tasu tazo daya da Amarya, takan dan zago lokaci-lokaci su gaisa, tace “Saude na ciki ko Lami?” Na ce “duk suna nan”.
Ban sa me ya kawota ba, bayan tafiyar ta Amarya ta je ta gayawa Baba, ya kira mu duka ya dubi Inna da Atika yace
“tunda Atika ta kasa fidda wani cikin manemanta, kafin Allah ya fiddo wani, zataje yin wanke-wanke gidan dan Maimartaba da yake aiki a Habuja, za’a biya mu kudi naira na gugar wuri har naira dubu goma a kowanne wata. Ko na wata daya muka samu muka karba ai mun warke, ga auren Atine da ke tafe, wanke-wanken nan shine rufin asirin mu.
Ni dama nasan nayi rashin mata kuma matallafiya, Indo-Aisha. Don haka ku tallafa mani, Lami ki bar Atika ta je wanke-wanken nan ko na wata daya ne”.
Inna ta shiga keta wata iri dariya mai ban haushi tace “WANKE-WANKE! WANKE-WANKE!! WANKE-WANKE!!! Allah ya sauwake Atika ta je muku bara, kuna zaune, tayi aiki da karfin ta da lafiyar ta don amfanin kan ku.
Baka tura Sani kodago koko makarantar Auwalu dole ce? Kai da bakayi karatun ba me ya sameka a rayuwa, ga ka nan da ranka da lafiyar ka daram ina ce?
Atine ‘yar gata, mai aure gida Wazirawa, me kuwa zai hana a yo wanke-wanke domin hidimar aurenta, tana zaune; kura da shan bugu, gardi da amshe kudi.
To Atika ma Allah ya cishsheta zata yi aure gidan saraki, ai kuwa kunga ba’a turata wanke-wanke gidan surukanta ba. Atika, tashi maza mu tafi taron nan ba namu bane”. Suka tsallake mu suka wuce.
Baba ya sunkuyar da kai sabida kunyar abinda Inna tayi mishi a gaban mu shiko Awal tsananin bacin rai sai yace
“Baba ni zani je kodagon, ko kodagon laifi ne ko talauci abin kunya ne?”
Baba yace “a’ah Auwalu, ka kyale ni in yi tunani, mutuncin auren kanwarku zaka diba, bai kamata ace Yayyun ta manya da za’a karbi aurenta a hannunsu kodago suke a tasha ba, karshen tsiya kenan.
Abinda ya daure min kai maganganun Lami, ina Atikar tayi mijin har ta zartar da hukunci kan gaban kanta, bada yawuna ba?”
Sallamar yaro a zaure yace wai Yallabai Bello ya zowa Baba gaisuwa. Baba ya mike tsaye yace Sani ya je ya gaya mishi idan ya zo ya daina aike, ya shigo kansa tsaye, nan gidan su ne.
Ni da Amarya muka nufi daki, ko tatafas Amarya bata tofa a zancen nan ba. Ina jiyo kamshin raina yayi fari, duk wani bacin rai da ke damuna naji ya yaye. Daga dakin Amarya, na hango Inna da Atika sun fito a hanzarce rike da koko, tabi kofar dakin Baba ta yayyafa tabi har soro ta yayyafa, ita kuma Atika garwashi ta debo a murhu ta zuba wani turare mara dadin kamshi tamkar na bori, ga bala’in hawa kai.
Ita kanta Amarya na lura hankalin ta na kansu, ina gani tana marmasa addu’a a bakin ta, ta mike ta dawo jikina, ta kama yatsun hannuna na dama da hagu tace
“rufe idon ki”.
Ban san me take tofa min ba, naji duk jikina yayi kwari gadagar tamkar na sha ‘Daga’. Tayi shigewar ta daki.

Na hango fitowar Bello, ya kara girma ya kara kyau da ilhama. Sanya kafar shi a tsakar gidan ke da wuya ya shiga atishawa ba kakkautawa. Baba na mishi ‘Yarhamakallah’ amma bai iya ya amsa ba sabida yadda atishawar tafi karfin shi. Da kyar ta tsaya kafin ya kama kanshi da ke juyawa ya fice daga gidan da sauri tare da Sani.
Can zauren fita Sani yace “bari in kira ma Atinen, na dauka zaka shiga ku gaisa da su Inna?” Yace “No, kyaleta kawai bana jin dadi, kaina kaman an tsaga shi gida biyu. Zan je clinicin sha magani, gobe in naji sauki na bullo”.
Sani jikin shi ya mace murus, ya soma zargin, nan gidan mu Bello ya dau ciwo, shi kanshi ya ji kanshin mai hawa kai da bai san daga inda yake ba, bai kuma san ko na mene ne ba, ya dauka daga makotane, wala’Allah Bello bai son kamshin? Allah masani.
****




K
wana daya, biyu, uku, hudu biyar, ba Bello babu labarin sa. A na shiddan ne labari ya iske mu yana kwance a can wani asibiti a Jos. Na rude, na rikirkice na rasa inda zan tsoma raina inji sanyi.
Nayi kuka nayi kuka har na ba uku lada. Ina naga hanyar zuwa Jos, wa zai kaimu? Idan muka je gidan Waziri, muka ce a kaimu Jos, ai munyi karambani da zakewa da yawa.
Sati biyu bayan nan Muhammad ya aiko sallama da ni, ba karamin jin dadin zuwan sa nayi ba, don nasan hanyar gano abin kauna ne yazo, na dan gyaggyara na fita. Kallo daya yayi min yayi dariya yace
“shin tsakanin ki da Dan Karaye, waye ke kwance ne?
Kin ga yadda kikai kozai-kozai dake kuwa Atine?”
Ba wannan ne a gabana ba, a ganina Muhd. Bai damu da ciwon Bello ba sam, barkwancin shi kurum ya sanya agaba, hawaye zurrrr….suka bilbilo min nace “Muhammad, ya Dan Karaye?” “ Sai kin fadi sunan yau, in har da gaske kina son sanin halin da angon ki ke ciki”.
Tamkar in mangareshi, wannan mugun aboki ne, bai damu da Bello ba sam, yadda yake kiranshi amini. Ya ga dai bani da niyyar magana ya zama kintsatstse yace
“ki kwantar da hankalinki Atine, Muhammad ya samu sauki, yanzu haka yana gida tun jiya muka dawo….” “amma shine ko ku neme ni a jiyan? Dan Jos, baka kyauta mani ba!” “kin san Allah daya ne Atine, ba laifi na bane, ba yadda ban yi da shi ba mu zo, ya ki, yanzuma bai san na taho ba da ya hanani.
Yace wai baki damu da shi ba shine kadai yake haukansa, satin shi guda a kawance baki nemi da ki je ba bayan in har kika nuna zaki, akwai masu zuwa a kullum ba za su ki tafiya da ke ba….” “kaga ni don Allah ya ishe ni, idan naje gidan Waziri duba shi, nayi laifi?”
Muhammad yayi shiru, “tukunna kamin wannan, so nake in tambayeki wani abu, amma don Allah kada hankalin ki ya tashi, ko kiyi tunanin wani abu daban” nace “toh..” (jikina ya soma sanyi).
“A ranar da muka kare jarrabawa, kayan da Muhammad ya aikewa Yayan shi dan wurin Maimartaba ya hado mishi daga Washington D.C suka iso, muka taho Karaye, cike yake da begen ganin ki, kada ki so kiga irin tsarabe-tsaraben da ya yo miki.
Duk wani dan abin ado ya gani jikin matan Barikin Jos, sai ya ce su sayo mishi ya bawa matar da zai aura, har su ci riba da shi.
Muna sauka, ko ruwa bai tsaya ya sha ba, karewama abinci nace ya tsayani in ci, ya ki, yace na same shi a gaba, ko Yallabai bai gan shi ba ya kamo hanya ya taho.
Ya kuma dawo mana ba a hayyacin sa ba ke kamar wani wanda yai gamo. Sannan ya ishe ni da zancen wai wata ATIKA shin wacece ATIKA ko kin santa???”
Kafafuwa na sun sage, yawun baki na ya kafe, gangar jikina ya saki, kuzarin jikina ya kare nace.
“Na san Atika mana, Atika Yayata ce Uban mu daya, ba mamaki Muhammad ko kadan ban yi mamaki ba, mu bar wannan zancen don Allah Don ba shine a gabana ba. Kayi mani jagora kawai in dibo jikin Bello, shine ya dameni.
Don nasan ko ma menene ciwon shi, gidan mu ya kwasa, bai kuma kyautu in ki zuwa ba” yace “in kina ganin ba komi, mu je?”
Na koma na gaya wa Amarya zani dibo jikin, Bello, tace “haka zaki tafi ba kintsi, ba gyara Atine yaushe zaki girma ne? Kuma me za ki kai mishi?”
“Me muke da shi, shima ai ya sani Amarya, bamu da abinda zamu bashi, KALWA KO DADDAWA?”
Idanun Amarya ya ciko da kwallah, ta dauko min sabon zanin atamfar ta da bata da kamarta, kwadebuwa ce, ruwan anta, Liman ya aiko mata da ita a haihuwar Sadiya, tun sawar da tayi mata ranar suna bata kara sawa ba.
A gurguje nayi wanka na murza man kuli-kuli a sawayena da yatsuna kada a gansu furu-furu, fuskar kuwa sai tayi fayau, na murza kwalli don boye rama.
Na kawo sabon gyalena mai-barewa na yafa, ban daura dankwalin atamfar ba don haka na nannada mayafin a fuskata, sai na fito ya bakuwar babarbariya. Karo na farko a rayuwata da nayi tunanin shafa turare a jikina.
Na dauki turaren wuridin Amarya wai shi (Dan-Duala) na bulbula. Muhammad na gaba ina bin shi a baya har kofar gidan Waziri.
Ya tambayi samarin da ke kofar gidan, ko Yallabai yana ciki? Suka ce yanzu yayi baki ‘yan dubiya daga gidan Maimartaba sun wuce gidan sa na bayan gari.
Muhammad ya dubeni, “kina ganin muje, Baba ba zai yi fada ba?” “Ba zai yi ba, dubiya ne fa, na mutumin da yake matukar kauna, fiye da mu, Baba ya amincewa Yallabai fa Muhammad”.
Muna tafe muna hira, har muka kawo gidan yana gaya min asalin gidan Yayan Bello, dan wurin Maimartaba, shi ya gina shi domin sauka idan ya zo da iyalin shi, daga baya kuma ya mallakawa Bello halak-malak shikuma ya dora wani sabon ginin ajikin katangar wannan din. Ya nuna min shi da dan-alinsa.
Gidan karami ne hawa daya tsarin ginin turawa, shuke-shuke sun kawata harabar gidan sosai, motoci har biyu tabbacin da baki, na lura Muhammad ya rude, tafiya yake tamkar bai so.
A babbar kofar gilashi ya tsaya, ya danna wata ‘yar danja kamar abin kunna fitilar lantarki, muryar mace ta amsa “Yes, Muhammad, shigo”. Yace “ko zaki tsaya in kirashi waje? Kannen shi mata ne cike da falon” “muje kawai ba komi”. Cike da zargi na fada.

Bello kishingide jikin abin tada kan saraki (tuntu) daga shi sai jallabiya ruwan toka-toka ya zubawa allon talbijin ido, daga gefen shi dai-dai kan shi wata kyakkyawar farar budurwa ce mai dan jiki take sanya mai wani irin abu da aka yi da fulawa da ban sani ba a baki, ta kuma sanya mai gongonin lemu ya kurba.
Ya dubi Muhammad sannan ni, yace "kai ina ka shiga ne tun dazu ina nemanka?" Muhammad bai amsa ba sai da ya nunan wurin zama, na zauna a darare sannan yace "naje wurin Atine ne, Atine ku gaisa mana?” Na dan zamo daga cikin kujera na russuna nace “ya jiki?”
“Jiki alhamdulillahi, ina kika baro min Atika?” “Tana gida, tace a gaida ka da kyau”
Ya maida dubansa ga ‘yammatan, “ku, baku gaida baki? Kanwar yarinyar da zan aura ce, Atika” suka kyabe baki gabadaya, tareda bina da wani wulaqantaccen kallo kamar sun ga kashi, mai bashi abincin tace “na dauka itace Atikar, da nace ai tayi kankanta da aure, me zaka aura anan, abu uwa KYANDIR!” Suka kwashe da dariya shima dariyar yayi yace “me za’a kawo miki; lemu ko ruwa ko ko coffee?”
Wallahi Bello, kaman bai taba ganinaba, sai ranar. Babu wannan kallon so da kaunar da yake mani. Na mike juwa na kwasa na, na samu na dafa bango na isa ga kofa
“……ki ce Fatima na gaida Atika, tunda tayi man fashin miji, to tayi mashi kyakkyawan riko kamin in iso, zan amso abina koda a ta biyu ne” suka kyalkyale da dariya.
Muhammad ya biyo ni “me na gaya maki Atine? Bello baya cikin hayyacin sa wallahi tun a Jos, ya koma min haka…..” sai hawaye, yasa hankici ya share fuskarsa ya fyace hancin sa yace
“Atine, kiyi hakuri ki saurare ni, koda rabuwar ce bai dace mu rabu da haka ba. Za’ayi wa Muhammad addu’a zai ware, wallahi zai komo dai-dai……”.
Hawaye ne masu zafi suke fita min tarara, amman ban fasa tafiya ba shi kuma bai fasa bina ba
“…… Da yake shine autan maza, ai dole a yi masa addu’a mana, mutum lafiyar sa lau na gani da ido na kace wani a yi masa addu’a, to dama BAN TABA FURTA INA SON BELLO BA, koko na taba? Ka je ka tambaye shi”.
“Atine, ki fahimceni mana, nasan kina fa da hankali, Muhammad ba yin kansa bane,…” “……. yin kafafunsa ne, tunda ba yin kansa bane. Kaga wallahi ka rabu da ni tun ban zage kaba. Ina ganin mutuncin ka Muhammad, kada kayi sanadiyyar da sauran mutuncin zai zube, tunda nace, ka rabu da ni, ka daina bina, to ka rabu da ni.
Bazan mance kaunar da ka nuna min ba, amma maganar aure nida Bello BABU ITA HAR ABADA; WA ZAI AURI MAI KAFA KAMAR MUBURGI? KYANDIR? Ai wallahi ko ni namiji ce bazan aura ba!”.
Muhammad yace “duk naji, amma Atine, komai aka yi shi cikin fushi, sai anyi dana-sanin aikatashi”.
Dai-dai lokacin da muka kawo kofar gidan mu, na dubeshi duba na karshe
“ni ba cikin fushi na ke ba. ‘Yar uwata fa jinina Bello ya koma so? Kuma sai inyi fushi, don ni mahaukaciya ce tamkar shi? Kaga tafiyata, kada ka sake kayo aike kace in zo ko Babana, zaka ga kaskanci, na gaya maka, na kar gaya maka wannan!”.
Na juya na bar shi anan tsaye, na isa ga dakin mahaifiyata, na kama ta na rungume na shiga rera kuka mai matukar tsanani. Digar hawayen Amarya cikin kunnuwana ya tabbatar mani, taji yadda mu kai da Muhammad. Ni nasan Allah ne ya hutar da Goggo ganin wannan abin bakin ciki. Maganar ta ta fado min a ranar da zata tafi ga sarki Allah
“Yau naki ne, Gobe na wanin ki ne!”.
Kenan ba abin damuwa bane don Bello ya nuna min so jiya, gobe ya komawa wani na, Atika? Yayata da muke Uba daya? To amma ya zanyi da son BELLO WAZIRI? Daya riga ya kanannadeni ba tare da sani na ba? To wai ance in so cutane, to hakuri ma, maganine, zan hadiyi hakurin in gani? Ko zai mani maganin?
Na dago na dubi Amarya nayi murmushin karfin hali "to meye abin damuwa, Amarya? Bello ba shine autan maza ba. Ni wallahi gareni ba komi". Amarya bata ce komi ba, na share fuskana nace mata na tafi gidan Liman in gano Sadiya.
Kakata Luba na daka, nayi sallama na shiga, Sadiya ta sheko da gudu ta rungume ni, Luba ta aje tabaryar ta dubeni sosai
“wani mummunan labari zan ji, Atine meya faru, can gidan ku ko ko gidan Waziri?”
Na tube silifana na ja kujera ‘yar tsugunne na zauna “eh to, Bellon ki ya canza Luba, kamar bai sanni ba kamar bai taba ganina ba…” hawaye suka zubo min sharrrr! Luba da alama zancen bai ko dadata da kasa ba.
“Idan kika sake kuka akan Bello, ke ba jikar Limamin Karaye bace. Labari ya zo min, Lami ta sa duk kadarorin ta a kasuwa, bata a birni bata a Kauye ta rabaki da Bello ya dawowa Atika, tun lokacin mun dukufa addu’a a kanki, asiri bai ci ki ba, domin jikin ki shiryayye ne.
To idan Lami a sammako take, ni a can na kwan. Kakan ki a tsaye ya kwan, da asirin ta mai ci ne, da Saude bata kai yanzu a gidan Maikalwa ba”.
“Don Allah Luba, kada ku wahalar da kanku, ni Bello ya fice min a rai, auren ma ba zan yi ba, ko na rasa mijin aure na barwa Atika, Bello, dama ban taba furta masa ina son shi ba”.
Na mike zan tafi, Luba tace “yaro dai yaro ne, an ce kashe makiyin ka kafin ya kasheka. Idan ke baki san ciwon kanki ba, baki san muhimmancin auren irin su Bello ba, ni na sani. Jeki ku karata da saunar uwarki da rashin baki ke cutarta”.
“Ni dai nace na yafe ko dole ne?” Tuni har na kai zaure, ta dandalin gidan Waziri na wuce, gaba kadan da gidan Waziri jingine suke jikin motar Muhammad.
Bello na bulbular da hayakin taba kamar mai hada gajimare, Muhammad kuma na magana suka dubeni gabadaya. Akuyar data debe su ma bata ishe ni duba ba.
Baban mu ya dawo yana zaune yana harhada dan cinikin sa na yau wanda sulallan biyu da sisi, kwandalaye, sisi da ‘yan ficikoki sun fi naira biyar biyar yawa. Na zauna na taya shi, duk iya kokarin sa a satin, naira dari biyar ya hadawa Awal, da kyar da sudin ludayi.
Washegari ina wanka, hargowar mata cikin gude-guden gidan sarautar Karaye, na ji cikin gidan mu. Sai kuma sauke akawatuna da maraba-maraban da Kandala aminiyar Inna ke yi masu, cikin dan lokaci na ji gidan ya cika taf da matan makota, ‘yan gulma, ganin kwaf da ‘yan bani na iya.
Ban fito ba sai da na ji ficewar su kaf, akawatuna ne masu taya tun daga ta daya har zuwa ta uku, ga wata ‘yar mitsitsiyar (kit), fanteku da kwallaye shake da kayan kunshi, tsibe a kofar dakin Inna su Kandala na kwasa suna shigewa daki da su, (a wannan lokacin ba kowa ake kawowa lefe cikin akwati ba sai wane da wane). Na wuce dakin mu.
Amarya tayi zugum can uwar dakin ta. Na dubeta nayi murmushi duk da raina suya yake, wai in dan faranta mata, nasan iyaye sun fi dan su jin ciwon abinda ya same shi, tace
“Atika, Bello yace a kawowa lehe, daman ya santa ne?” Na yarfar da hannu “oho ni na sanar masu? Na san dai ganin shi da ita sau daya ne, ranar da muka fara haduwa kuma ko magana bai mata ba”. Amarya tace
“wannan abin mamaki da yawa yake, wannan duniyar cike take da rudani, tattare take da ababen mamaki. Mutanen cikinta, sun shagalta da kyale-kyalen ta basa ko, tunanin karshen su.
Atine, ki zama mai tawakkali cikin kowanne hali, ba duk abinda kake so zaka samu ba. Ni nasan kina son yaron nan ko baki furta ba amma don Allah, kisa masu ido, munafurci dodo ne, mai shi yake ci. IDAN BELLO SHI YA SAURA DA NAMIJI A DUNIYA KIN BAR SHI HAR ABADA in har ina raye.
Abinda mutum ya shuka, shi zai girba. Kin ganni nan, ban iya shige da ficen gidan Malamai ba. Takobi na da kowa addu’a. Kada ki nunawa Baban ki damuwar ki, bai san me ake yi ba”.
“Ni Amarya na yanke shawara, ki gayawa Baba, zani WANKE-WANKEN da Atika taki zuwa, zanyi wanke-wanke domin ku wadata, Awal yayi karatu, ku ci abinci maikyau. Zan kare rayuwata gabadaya a wanke-wanke, bana ko son zaman Karaye, na tsani Karaye, na tsani mutanen da ke cikin ta in banda Uwata, Ubana da Liman.
Allah ya taimaki Goggo na da bata nan, nasan da anyi tashin hankali wanda bakya so Amarya, da an bata min ranta a banza, da ta hanani tafiya wanke-wanken”.
“Allah yayi miki albarka Atine, Allah kuma ya baki miji wanda yafi Bello komi da komi”. Sai nayi murmushi kawai, na kama harkar gabana, cike da fin karfin zuciya. Amma can akarkashin zuciyata nasan nayi rashi, babba kuwa. Wanda na tabbatar cike shi sai wani babban ikon Allah (Tuna baya Shine Roko) .
****










B
aba na dawowa Inna jiki na rawa ta tare shi, “masu auren Atika, sun fa kawo lehe Mallam, bari kaga abin arziki?”
Baba ya zubawa kaya ido kaman mai ganin abin tsoro da kyama “ina Atikar ta samo wannan mijin, dan yankar kai, ko dan birni?”
Inna ta kyalkyale da dariya cikin jin dadi “dan Wazirin Karaye ne, Muhammadu Bello sunan sa, ai Atika, tayi farin goshi”. “Bello? Bello wanne? Wanda na baiwa Atine?”
Ya jero tambayoyin da bashi da yakinin samun amsar ko daya, “to dai ina jin ba shi bane, don wannan Bellon Atika yake so ka kuma je ka tambayo shi, wa ya aikowa da lefe?”
“Wai wane irin zancen banza ne kike haka Lami? Da alama baki da cikakken hankali, ya za’ayi ana neman kanwa ki ce yar ce? Ko an ce miki Atika ta rasa miji?”
Inna ta hasala “ko dai wane irin zancen banza kake? Sai ka je ka shafo labarin daga can sama inda ya sauko” Ta shiga maida kaya yanda suke. Ya tsallaketa, nitsatstsen dattijon, a nitse ya tadda Amarya
“Saude meke faruwa ne? Ku fidda ni duhu, ku yaye min duhun da kuka sanya ni”.
“Ka ganni nan Malam, tun safe ina nan zaune, ban san me ake a tsakar gidan ba” Mallam yace
"zurfin cikin ki bana son shi Saude, za ki gaya mun ne ko a'ah?"
" To zan gaya ma gaibu ne, abunda bani da masaniya a kai? Daga inda labarin ya faro can zaka nemeshi, ni ina daki, na san me ake a gidan Waziri ne?"
Ya tabbatar ba zai ji kalma ko daya daga bakin ta ba, kasancewar ta mai KAWAICI da KAU DA KAI akan duk wani al'amari daya shafi ATINE. Ya juya ya fita ya nufi neman Bello.
To zance dai ya bayyana ga baba, Bello Atika yake son aure. Yana kuma son a sanya ranar auren kurkusa domin zai tafi karo karatu Kasar Sanyi da ita. Baba a rikice ya dawo, karo na farko daya zargi Lami da asirin da ake cewa tanayi tun bayan auren su sama da shekaru sha biyar. Bai ce komi ba.
****






N
ayi sallama dauke da koko, mai cike da ruwan farau-farau. Na durkusa na gaida Baba, ya amsa ta hanyar daga kai kawai, na mika mai koko ya amsa ya kafa kai ya shanye tas, ya ajiye kokon. Ya dube ni da idon rahmah
“Atine kar ki damu, albarka na tare da ke, albarkar Uwa da Uba, ba zaki taba tabewa ba!”
Murmushi na yi, “Baba ka aurawa Bello Atika, kada ka ji nauyi na, da ni da Atika duka daya ne, ba banbanci. Na zo ne in gaya maka ni zani WANKE-WANKEN da Atika ta ki zuwa, ko a sami dan abinda za’a kai mata daki, ko a samu a biya kudin makarantar Ya Awal, zan kari rayuwata duka a wanke-wanke, domin taimaka maka Baba na”
Baba ya sa habar taguwar sa ya share ido yace “Atine ke da uwar ki tausayi kuke bani, baku dauki rayuwa a bakin komi ba. Don haka har kullum, nake addu’ar Allah YA YI MAKU ALBARKA. Duk wani abu da zai taimake ni shi kuke yi. Ku kyale Lami da diyar ta da mai kowa mai komi, “kowa ya ce gonar wani bazatayi albarka ba, tashin ce bazata yi ba”.
Kuma da muguwar rawa, gwamma kin tashi. Tashi jeki, zan nemi Talatu ta kai ki gidan aikin, dama sun matsa mani”.***

Na hade kayana tsaf, cikin kullin dan kwali. Duk wasu shirgin Bello na tattarasu cikin jakar shi har kuwa da takardar da nike ta kwakwar ajiyar ta na ba Salisu (mai bin Sani) na ce ya je ya ba Bello, idan baya gidan su ko gidan Maimartaba yana gidan sa na bayan gari.
Talatu tayi sallama muka amsa, suka gaisa da Baba da Amarya. Ta lalo kudi ‘yan dari-dari da muke jin labari an buga, ta bawa Baba, naira dubu goma, kudin da ko a mafarki, bamu taba gani ba a rayuwar mu. Kai ni

Please Login or Register in order to submit comment