Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban ma taba jin inda aka fara bada kudin aiki ba’a fara aikin ba sai wadannan.
A cewarta wai don sun matsu da ‘yar aikin ne domin matar gidan tsohon ciki gareta bata da mai yi mata hidimar cikin gida.Baba yace
“Talatu na ba Allah, na baki amanar yarinyar nan, Atine yarinya ce karama, dole ce ta sani turata wanke-wanken nan. Domin duk halin matsin da kake ciki, gara Dan ka ya tashi a gabanka, duk wani wulakanci za’a raga masa in kana nan.
Nasan ni talakane futuk, amma ban taba zuwa wajen wani mai mulki neman alfarma ko bashi ba, don haka in aka wulakantamin Atine, bafa zan kyale ba, zan iya jure duk wani halin talauci in dai akan MUTUNCIN ‘YA’YA NA NE”. Hajiya Talatu tace
“Maikalwa kada ka damu, gidan Yallabai Magajin-Gari, babu wulakanci a cikin sa domin ‘ya’yan Maimartaba mulki da sanin darajar dan adam suka tsotsa ba dukiya ba. A tarihin mulkin gidansu kai kan ka ganau ne kuma jiyau. Tun iyaye da kakannin da suka hadu suka kafa kauyen Qaraye. Babbar masarauta (KANO) ta nannada musu rawanin Karaye. Don haka ka kwantar da hankalin ka.
Share-share ne kawai da goge-goge zata yiwa matar Yallabai kullum, sai dauraye kwanukan da aka ci abinci, bayan wannan ba abinda zatayi.
Atine zata ci mai kyau, zata sha mai kyau, za kuma ta zaga duniya ta ganta domin yanzu daga nan, Abuja, babban birnin tarayyah muka nufa can gidan da matar Yallabai take. Duk shekara zan je in dauko ta in kawo ta ganin gida Insha Allahu.”
“Wannan duk bai dame ni ba, idan naji Atine na cikin wulakanci, zan karbi ‘ya ta ne kawai a hannun ki. Maganar zuwa gida bayan shekara a barta, ni ban ce ba, sabida ina gudun surutun mutanen Kauyen mu.
Illa idan lokacin da nake ganin ya dace in mata aure yayi, zan yi maki magana ki dawo min da ita”.
Hajiya talatu tayi dariya tace “shike nan, ke fa Amarya me zaki ce?”
“Me kuwa zan ce, ban da kada wanke-wanke, ya hana Atine sallah, da sauran ibadodin da suka hau kanta?”
Hawaye suka zubo min sharrrrr! Na tausayin iyaye na, na san dole ce zata sa su TURANI WANKE-WANKE. Idanuwan su sun fada, bakunan su sun fada; neman halalin su ne.
Ni kuwa komai wulakancinnan da zan fuskanta, wanda Baba ke fadi zan jure, don cigaban samun halalin sa.

“Na bar gida, cike da kewa da kaunar ki, Inna ta, Amarya. Na bar gida, zuciyata cike da bakin cikin ki, kishiyar Inna ta, Lami. Na bar gida, zuciyata cike da kaunar, wanda bargo, ruhi, ba zai taba daina kaunar sa ba; MUHAMMAD BELLO WAZIRI KARAYE”.

Haka na rubuta da Ajami, a saman dakin Ya Awal, da gawayi, a lokacin da Talatu ke sallama da su Baba.
***













TUNA BAYA SHINE ROKO!!!
(FARKON LABARIN KENAN)
T
afiya muke, tamkar ba za’a daina ba. Nayi barci, nayi kalle-kallen gefen hanya har na gaji. Wajejen Isha’I muka shiga garin Abuja. Na bude ido na mutstsike su na dirki kallo son raina; ga fitulu kala-kala sun haske ko’ina kamar rana. Ji na nake kamar a wata duniya ta daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba.
Ga wani irin sanyi da nike ji yana ratsa kasusuwa da bargon jiki na, a cikin motar, tamkar a Aljannah na ji ni.
Direban ya dauke kan motar ya shiga wata kebantacciyar anguwa ta daban, wadda ko a Abujan nasan wannan daban ce (Ministers Hill Colarado Close). Da alama sun san direban don mu ba’a wani bincike mu ba aka daga mana kafa muka wuce.
Ya shiga keta gine-gine masu ban tsoro a gareni, kafin ya tsaya a wani gida mai katuwar kofa kamar bangon duniya, wata irin wayar lantarki ta zagaye katangar gidan gabadaya. Sojoji ne ke gadin gidan, da alama sun san Hajiya Talatu don har dago mata hannu daya daga cikin su yayi.
Muka doshi wata tangamemiyar kofar gilashi dake fuskantarmu amma ba’a iya hango abinda ke cikinta sabida duhun gilassan. Kofar ta bude da kanta (automatically).
Sanya kafata keda wuya, naji na nitse cikin wani abu mai laushi kamar katifa, ga wani irin sanyi mai ratsa kashi dake busowa hade da wani irin kamshi mai dadi, na koma baya da sauri ina haki.
Haj. Talatu tace “Atine, ki saki jikin ki don Allah, kada ki nuna mamakin komi kika gani a gidan nan, ki nuna ke kamar ba ‘yar kauye bace. Domin kin fito daga tushen Mai gidan, KARAYE. Matar gidan bata da mutunci, in kikayi wani abu da bai mata ba tana iya cewa a koma da ke”..
Jikina yayi sanyi “kin san bata da mutuncin kika kawoni baki gayawa iyayena ba?”
Haka na fadi a zuciyata. Tsallake wannan sashe, tsallake wannan falo har muka dangana da kuryar gidan wato ainahin sassan matar gidan.
Hajiya Talatu ta danna wani abu a jikin kofar, sannan ne kofar shiga sassan ta bude muka shiga. Wata murya ce ke fitowa daga cikin wata farar akwatu mai hoto, da tafi min kama da akwatin talbijin, tana fadin wani abu cikin harshen turanci (computer).
Hajiya Talatu tace “tana wanka wai mu jirata”. Nace “to ke turancin kike ji? Koko talbijin din ce ta fada maki?” Harara daya tayi mun na ja bakina na bame da mukulli.
Zaune muke tsayin awa daya, biyu har uku, ta fito bata fito ba, a raina nace wannan wanka ko daye fata? Amsa ga tambaya ta, sai muka ji motsin bude kofar ta, tana tafe da wani zungureren ciki irin na haihuwa yau ko gobe.

Na dauka zan ga wata kasaitacciyar Hajiya wadda taba arba’in baya, sai ganin mace nayi tamkar budurwa. Fara, ‘yar gajeriya, hancinta da fuskar ta duka gajerunne, idanunta mitsi-mitsi kamar ‘yar chinese sai dai ‘yar lafiyayyar fatar ta mai tsananain taushi da sheki kadai, ta isheta yiwa kowanne irin haddaden namiji yanga; musamman a wannan zamanin da muke ciki da kyawun fata shine kyau, ba kyawun halittta ba.
Tana sanye da dogon siket din Jeans wanda ya kama jinta sosai da ‘yar riga mai zanen tutar Amurka (ja, fari da shudi). Gashin kanta cure cikin wani zagayayyen abu da alama doki ne ya sammata, (ba nata bane). Ke da ganinta kinga cikakkar bahaushiya, amma ‘yar duniya, idandunanta a tsaitsaye kuma a soye kamar na soyayyar gyadar Kano (marau-marau).
Tayi ‘yar hamma tayi mikar data turo zungureren cikin ta gaba tace “wash, Talatu sai yau?” A dai-dai lokacinda ta kai dan duwawunta uwa tafin hannu cikin luntsuma-luntsuman kujerun.
Muka zube a kasa muna kwasar gaisuwa, tana amsawa a yatsine kamar dole aka yi mata, muryar ta kamar an shaketa, ta dubeni sosai tace “mike tsaye” tare da kai hannu ta toshe hancinta. Ta kare min kallo tas, daga sama har kasa, tayi tsaki tace “ina wannan ‘yar siririyar yarinyar zata iya yi mun irin gyaran da nike so a dakunana? Da wanne kazamin hannu zatayi mun wanke-wanke mai tsabta da maigidan nan zai iya cin abinci da shi?”
Talatu ta sauke kai irin yadda bayi ke yiwa iyayen gidan su cikin ladabi
“ranki ya dade, Fulani ce tace a daukota, domin ‘yan gidan su suna da tarbiyya, hakannan girman kauye ne sun saba da aikin wahala. Ki bar ganin ta haka lange-lange, babu irin aikin da bazata iya yi miki ba, wanda su maza, karti, masu aikinki suke yi miki.
Amma idan kika ga kwana biyu bazata iya ba, sai a maidata a dauko miki katuwa” tayi tsaki sabida haushin da Talatun ta bata, tana toshe da hancin ta dai tace
“shikenan, zan gwadata kwana biyun in gani, kuje falon waje zan turo Tom ya nuna mata dakin kwana, ke kuma ki kwana a dakin baki, yanzudare yayi gobe da safe zan ganku”.
Bayan Talatu ta shiga dakin da zata kwana, wani saurayi ga dukkkan alamu kabila ne, ya shigo ya dube ni
“Oya yaro muje in nuna maka daki in ji Madam” na bishi a baya, rungume da ’yan kullin kayana, ya bude wani daki da baya da nisa da sassanta, ya bani mukullin a hannu na “ga dakin ka nan, ka kwanta ka mige, ka futa gajiya ko?”
Da alamun shi mai kirki ne, nayi dan murmushi “to”. Ya sake kallo na “ yaro kayi hakuri da Madam, she is bad (bata da kyau), muma duka muna hakuri da halin ta ne, ka kula da duk abinda tace da kai, in kayi kuskure ko daya, ranka zaya baci.”
Na gyada mishi kai cikin sanyin jiki “ya sunan ka?” Ya tambaye ni “Atine sunana, kai kuma fa?” “ Ni sunana Tom. Atine, zan ke ce maka TINE, zaka amsa?” “Ba komi Tom, ka kirani duk yadda ka so” to sai gobe, ka kwana lafiya, Allah Futa gajiya”.

Na dubi daki matsakaici, an shinfide shi da jar darduma, amma bata kai taushin wadanda na gani a baya ba, haka labulayen dakin jajaye ne, masu kyau, ga wani bakin tebur (t.v stand) an daura wata ‘yar akwatu akai (talbijin), a samanta ma wani dan akwatin ne (receiver).
Akwai kofofi guda biyu a cikin dakin, daya a dama daya a hagu, na bude ta hagun; bandaki ne fari sol da shi, kamar tuwon ka ya fadi, ka tsugunna ka dauka ka ci, komi dake cikin bandakin fari ne sol.
Na bude ta daman. Ni Atine mai zan gani? Gado ne na gogaggen katako, lullube da lallausar bargo, da zanin gado mai taushi, ga filallika har guda biyu, mudubin dogon yaro da abin zaman sa (stool), ga sundukai masu taya irin na lefen Atika, babu komi cikin su, wanda ke nufin, in zuba ‘yan tsummokarana a ciki.
Na kuwa bude na jefa su ciki, uwar dakin badarduma, sai wani irin falle-falle a jere irin na bandakin, wanda na lura duk gidan ma shine har a jikin bango (tiles), wadanda in baka yi da gaske ba, sai su kayar da kai don santsi, don haka nake taka su a hankali ina kuma hadawa da kama bango.
Ban kwanta ba, na shiga bayan gidan don in dauro alwala, in sauke sallolin da ke kaina, na Maghriba da Isha’I da suka riske mu a hanya.
Banga wani famfo ba sai na jikin kwamin, mai kama da kwale-kwale, na tsaya daga gefe, ban yarda na shiga ciki ba kada inje in zame, na kunna famfon na tara hannuwana biyu, ba sai naji ruwan zafi tafasashshe ba?
Na kwalla kara iyakar karfi na, ina yarfe hannu, na ji shigowar mutane a guje, Hajiya Talatu ta daga murya tace “kina ina?” Nace “gani nan a bandaki” tace “to fito mana?”
Na fito ina haki, ita da Tom suka hada baki suka ce “lafiya?”
“ Ina fa lafiya Talatu, na kunna ruwa in yi Alwala na ji tafasahshe, don ma Allah yaso bai salube mun hannu ba???” Na fashe da kuka.
Talatu da Tom suka dubi juna, ya tambayeta ko me nake cewa, domin hausar tashi bata yi kwari ba, tayi dariya sosai ta gaya mishi da turanci, shima yayi dariya, muka dunguma gaba daya cikin bandakin.
Ya kashe fanfon dana kunna yana ta zuba yace “baka gani famfo har guda uku ne? Wadannnan guda biyu, dake cikin kwami, na wanka ne, na jikin ‘sink’ din nan, shine na amfanin da ba wanka ba.
In za’ayi wanka, in ana bukatar ruwan dumi, shine ake kunna wannan, a kuma kunna wancan na kusa da shi ya sirka shi, bayan an toshe rariyan da wannan bakin abun. A shiga ciki ayi wanka sai a bude ruwan ya fita.
Wannan da yake rufe, zama ake yi ayi bayan gida, a murda wannan, tayi floshing dinsa, wannan na kusa da shi kuma sai a hau, a murda wannan sai yayi ma tsarki, ba sai ka sa hannu ka ba, O.K?”
Na gyada kai, alamar na gane “gobe zan zo in koya ma kunna t.v da a/c, right?” Na sake gyada kai, suka fita na rufe kofar.
Na idar da sallolin da ke kaina, na rufe da nafilfili na musamman. Na daga hannu na sama nace;

“Ya Ubangiji, ni baiwarka ce, mai yawan sabon ka, dare da rana, safe da yamma, fili da boye.
Ya Allah kai ka halicce ni, ka raineni, ka bani ikon shigowa wannan gida, domin neman halak dina.
Ya Allah kaine mai kowa mai komi, Ya wanda Al’arshinSa yake sama, wanda Rahmarsa ke Aljannah, azabarshi da ukubar shi sake wuta.
Ya masanin sirrin da ke rufe, ya Ubangijin lamarina. Don sirrin dake cikin Suratul Rahman, Yasin da Waki’ah, wanda in ance LA’ILAHA ILALLAHU, yake cewa MUHAMMADUR-RASULULLAHI.
Wanda ikon Ka, mulkin Ka da buwayar Ka ya zarta duk tunanin mai tunani.
Ubangijin sammai da kassai, buwaya gagara mithali. Lallai dukkannni na, zunubi ne. Kuma kaine mai rangwame, mai gafara. Na roke Ka, Ka sadar da ni alkhairin da ke cikin zama na a wannan gida, ka nesanta ni da dukkkan sharri da abin kin da ke cikin sa. Ka bani hakuri, juriya da karfin zuciyar zama da Iyayen gida na da duk wanda nake tare da shi cikin gidan nan lafiya”.






N
a kwanta a gadon da ko a mafarki, ban taba gani ba. Na ja bargon da ko a tunani, ban taba tunano irin sa ba. Na tuno karaunin mu, na tuno salgar mu, mai cike da kyankyasai, tsutsotsi da sauro.
Na tuno ginin gidan mu; katangar ta tsage, rabin ginin ya rufta. Dukkannin mu in damuna tazo bama jin dadin kwanciya sabida yoyo.
Na tuno sauron da ke kumbura mana fata, ba yadda za muyi da shi, sai dai mu bishi da duka da hannun mu, in ba mu yi sa’ar samun sa ba, ya dawo kunnuwan mu yana mana eho, ya sha jinin mu, mun zo dukan shi mun doki kan mu.
Idan Allah ya raya ni, zan yi amfani da karfi da lafiyar da Allah Ya bani, duk da kasancewa na diya mace, in ga na fitar da Baba na daga rayuwar saida KALWA, in kai Sadiya da Jafaru makaranta, in fidda Amarya daga hawa salga mai tsutsotsi, itama ta hau tangaren.
In kai Ya Auwal, abinda ya fi so a rayuwar sa (karatun Jami’a). Na runtse idona a hankali, hawayen tausayin ahalina, shi ke zuba min, mai zafi da daci a zuci.
Yanzu dama akwai wadanda Allah yayiwa baiwar rayuwa irin haka cikin kasar mu? Basa ko tunawa da ‘talaka’ wanda ke wuni yana digar da gumi, don kurum ya samarwa iyalin shi abinda zasu ci balle su taimake shi?
Meye amfanin shuwagabanninmu, me suke yi na taimakon ‘yan kasa, musamman talakawa? Bamu gan shi ba. Sai dai su kai ‘ya’yan su yin karatun shedanci a kasar waje, su sayawa matan su, motoci na garari, su tamfatsa ginunnuka tamfar baza’a mutu ba aikin kenan.
Niko in nice da kudi, a ganina na talakawanda ke bisa hanya ne, rana tana dukan su, suna neman abinda zasu sanya a bakin salatin su. Kaico!
***



W
ashegari tunda na tashi da asuba ban koma ba, tunda kuwa na riga na saba da hakan. Na tuna su Baba nayi murmushi, nasan yau zasu samu karin kumallo mai kyau, tunda sun samu ‘yan kudin wanke-wanke.
Burin Babaaduniya shine, in yanada shi iyalinsa su ci, in bashi dashi su yi tawakkali su ciabinda yasamu. Bai san wani abu wai shi ya tara kudi ba. Ga son iyalinsa su ci mai dadi. Su ji dadi shi dai.
Sai da gari ya waye Tom ya buga min kofa na bude, ya shigo da ‘tray’ yace “Tine, ba dai har ka tashi ba” nayi murmushi “na tashi mana, tun asuba, ni bana dogon barci”.
Na tsugunna na gaida shi, na lura ya ji dadin girman da na bashi yace “kuma sai ka zauna shiru, maimako ka kuna t.v, ana programme mai kyau a B4uMovie”. Ko me yace? Wallahi oho!
Ya jona waya talbijin ta kama, ya dauko wani dan abu baki yazo gaba na “wannan shine ‘remote’, in abinda kake kallo bai maka ba, sai ka yi ta danna nan zai yi ta canzawa, har sai ka zo wanda yayi maka. Ta nan ake kunna t.v” ya dauki wani irin sa amma fari “da kin danna nan, A/C zai kama, nan kuma zai mutu, nan zai karu, nan zai ragu…..” haka yayi ta nuna min, sai da na tabbatar mishi na gane.
Yace “ka gane? To kunna mun A/C yanzu” na kuwa danna ta kama shuuuuu!. Yace “in za’ayi wanka, a wannan bandaki, ya za‘ayi?” “Za’a toshe rariyar kwamin ne, a kunna famfo wanda ake so (mai zafi ko mai sanyi), sai a shiga a cuda da soso da sabulu”.
Ya tintsire da dariya yai mun tafi guda uku “da alama zamu shirya da kai, Tine, domin kai yaro ne mai saurin fahimta, ga kari-kumallo ka nan, ni zani makaranta, sai sha biyu da rabi zan dawo, don ba ni zan daura lunch ba (abincin rana ) Ejiro ne”.
Ya juya zai fita, sai kuma ya juyo, “af, Madam tace a gaya maka, in ka kintsa kaje can falon jiya, yau zaki fara dutyn ki”.
Na bude farantan gilashin da ya aje mani, kodayake tun kamin in bude naga abinda ke ciki, kasancewar sa garai-garai.
Farantin farko kwai ne aka soya mai kauri da ayaba da dankalin turawa, dayan farfesun koda da hanta ne, sai wani abu a kwalba mai kama da ganda (Jam), sai da na diba hoton dake jiki, na fahimci a biredi ake shafawa, sai wani irin dogon biredi mai kyau da laushi.
A gefe filas din ruwan zafi ne dan karami dai-dai cikina, da sauran gwangawanaye da kwalaben da na fahimci duka a shayin ake zubawa.
Na ci iya ci na, kunnena kamar zai tsinke don dadi, sai girgidi yake. Santi kam nayi shi har na gaji, sai dai a bakina abincin ba dandano na rashin sabo.
Nayi wanka nasa ‘yar atamfar da tafi kowacce kwari cikin kayana. Ko mai ban tsaya shafawaba na bi hanyar jiya, zuwa kayataccen falon.
Na taddata tsaye tsakiyar dakin tana magana cikin wani abu, mai kama da abinda na ji Tom ya kira ‘remote’ (a wancan lokacin mutane dai-dai ke da wayar hannu a Nijeriya), sanye take da siket iya gwiwarta, rigar jikin ta iya cibinta, wanda hakan ya baiwa tirtsetsen cikin damar watayawarsa yadda yake so, abun babu ko kyawun gani.
Ban taba ganin cikin mace haka muraran a sarari ba kamar randa, sai yau. Yau ma kamar jiya, kan ba kallabi. Ke da ganin yadda take maganar, tana karkashe ‘yan kananun idanun ta, kinsan da Maigidan da ake masifar so a ke.
Abinda ma na tsinkaya zance na ne, don naji tana cewa “wallahi baka ganta ba fa, baka kirin, ‘yar siririya kamar kazar mayu, kafafunta kamar na shanshani, idanduna ribda-ribda ga tsummokara ajikin ta babu kyawun gani, hakoranta yalaye sharr, nikam tsoranta ma nake, don bata yi mun kama da mutane ba.
Tunda tazo gidan ‘atmosphere’ na gidan bakidaya ya canza, gaskiya tabi Talatu su koma, in ya so a nemo wata” ban san me ya gaya mata ba, naga ta tsuke fuska, can kuma taja tsaki tsuuuuu! Tayi wurgi da abin maganar, dai-dai lokacin da Talatu ta shigo.
Ga dukkan alamu, Talatu tayi shirin komawa KARAYE ne. Hankalina ya tashi ainun, tsoron matar ya kara kamani, gashi kuma itama tace ni nake bata tsoro. Ni kaina nasan sirinta na yayi yawa, amma ban san wani aibi a halittana ba bayan wannan.
Ta dubi Talatu “nayi magana da direbanda zai maida ke, ga wannan inji TAHEER ki sha ruwa a hanya”.
Ta fiddo rafar kudi sababbi, ta zari goma daga ciki, ke da gani kin san kwangen kudin tayi, duka aka ce ta bayar.
Talatu tasa hannu biyu ta karba ta fadi tana godiya. Tace “kamin ki tafi, ga wannan ‘dettol’ ne da ‘anticeptic soaps’, ki hada ruwa mai zafi ki zubasu a ciki, suyi kaman awa guda, kisa yarinyar nan ciki ki cudeta, musamman hannuwa, kafafu da kasan hammatarta, ki tabbatar sun fita fes, ki yi ta canza ruwan kamar sau goma.
Sannan ga wannan ‘brush’ da ‘maclean’ ki dirje yalayen hakoran nan nata ban son ganin su, zuciyata tashi take.
Direba zai kaiku saloon ayi mata yankar akaifa da wankin kai, duk wata kwarkwata da birbishin amosani, zan yi masu waya, su dirje shi.
Sannan wadannnan tsummokaran na jikin ta, da wadanda aka shigar da su daki, ki je ki tube maza-maza a fidda mun su a gida tun basu jawo min sauro ba.
Daga saloon zai kai ku boutique, ki zabo mata kayan sawa, wanda ba’a dinkawa. Idan naga zani a ciki, Ubanta zan ci. Ku tashi ku fice min a falo, saura in ga an saba umarni na daya”.
Sum-sum muka tashi muka fito, kamar an rarrade mana gwiwoyin mu da murfin kwano. Talatu na cuda ni a baho tana hawayen tausayin, tafiya ta barni da wannan mai halin yahudawa, gata dai cikakkar bahaushiya kuma musulma gaba da baya, amma kwata-kwata babu kyautayi da kyautatawa cikin al’amarinta.
Tace “Oh ni Talatu ya zan yi da amana? Ban san rashin mutuncin matar nan ya kai haka ba, ina jin labarin ta wurin bayin gidan Maimartaba da ‘ya’yan shi duka, ban zaci ya kai haka ba, me zan ce da Maikalwa?”
Ni kam ko a jikina, Babana fa za’a baiwa naira dubu goma a wata, abinda ko ma’aikacin gwamnati mai digiri, a wancan lokacin baya karbar su a farkon fara aikin sa. Babana da Innnata ne fa zasu ci jar miya, su daina dumamen tuwon dawa. Yayana Awal ne fa zai yi karatun da watakila watarana, ya hanani wanke-wanken; ya rungume mu cikin inuwar ilminsa.
To meye zai sa in ji ciwo? A karkashin ta nake, a karkashin inuwarta ne kadai zamu ji sanyi, ni da iyayena! Wulakanci yana tofo ko yana tsiro a jikin dan adam?
Ban zo don ta yabi halittana ba, sai don neman halalina!
“Hajiya Talatu na gama ki da Allah, kada ki ce da Babana komi game da halin Uwargijiyata. Ni na ce naji na gani, kome zatai min, zan iya jure zama da ita”.
Ta share fuska “shikenan Atine, nayi miki alkawarin bazan bari Maikalwa ya ji ba”.

Wani irin inji ake tura min kai, na dauka fille min kan zai yi, sai naji ashe wai cuda sumar kaina yake, aka wanke gashin tas, yasha shafe-shafe da mulke-mulken mayuka masu kamshi, in banda kamshi mai dadi ba abinda yake tashi a kaina. Mamakin da nake, wai gashi ma har yayi matsayin da za’a bude irin wannan kasaitaccen waje domin sa?
Ni kaina sai naji jikina yayi dadi, kaina yayi sayau, kaman an dauke mun wani nannauyan kaya aka, iska na shiga na ta ko’ina.
Kayan da Hajiya Talatu ke zaba, rigunane da siket sai dogayen riguna da pakistan masu dan karen tsada, domin nace mata bazan sa wando ba.
Bamu dawo ba sai bayan azahar, direba ya juya da Hajiya Talatu Karaye, ni kuma na rungumi jakar kayana na nufi dakina cike da kewar ta.
Tom ya kawomin abinci yana tamin bahaguwar hausar shi ina dariya, wai kwana daya kawai yaga nayi kyau, ga gashi mai kyalli yaga ya leko. A hankali sai ya mantar dani kewar Talatu. Ya kunna mun talbijin nace
“ni dama ka kashe ba jin abinda suke fadi nake ba, sai dai a cikani da sur-sur-sur” yayi dariya sosai
“idan kayi alkawari koya mun Hausa, ni kuma zan koya ma turanci, har da rubutu da karatu”.
“Zan koya maka mana? Hausa ba wuya, ko a yanzu ka iya hausa, matsalarka daya kana ba mace sunan namiji, shikuma namijin ka bashi sunan mace (feminine to masculine)”
“haka english, abu ne mai sauki, Tine, in har kasa kanka zaka iya”. Ya koma, jim kadan ya dawo da farar takarda da alkalami “wannan shine pencil da dan koyo ke amfani da shi yayin koyon rubutu” ya rubuta wasu haruffa daban-daban, ya kira su a nitse; A, B, C, D.
Yana fadi ina fadi har ya tabbatar na rike su a bakina. Yace in dubesu sosai in gane yadda ake rubuta kowannen su, na kuwa daddage na rubuta mai nan da nan.
Cikin dan lokaci, kirista Tom, ya

Please Login or Register in order to submit comment