Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamaki karara a fuskana, Ya Subhanallah! Yanzu na ga inda Jawad ya debo kyau, tsurar sa. Wannan wane irin mutum ne? Saukin kan, yayi yawa.
“Ban taho da abinda zan goya shi ba, in munje can daki zan goya shi”
“wannan towel din na kanki fa?”
Da sauri nasa Jawad a bayana, cikin kwarewa nasa Towel na daure shi kam da jikina. Jikina ya bani kallona yake yi,
“daga yau duk sanda zan ganki, in ganki goye da Dan ki a bayanki, ina son ganin mace da goyo, kin ji?”
Na gyada kai, har yanzu a kidime nake, mu ka fita.
Ejiro yana ta dariya cikin turanci yace “na so Tom ya ga wannan Dirama. Kin ganki kuwa a gaban Oga, kamar wata ‘yar mage a gaban Sa (namijin saniya)” na harare shi “ban gane ‘yar mage a gaban Sa ba?” “Ina nufin shi dogo, kuma kato, ke ‘yar mutsila” mukayi dariya.
“Amma Ejiro Ogan ku ya burge ni, baya kyamar talaka, sannan halayyar shi gaskiyar Tom ne ba daya ne da na Anti ba, kwanaki hannu na ya kai ga na Anti, cikin kuskure garin amsar Jawad, wallahi zabgamin tafi tayi wai zan shafa mata muni.
Bata taba tambayana yaya nake da rigimar Jawad ba ko sau daya. Ko a masu kudi, muIki da ilmin, samun mai irin halin shi da wuya”. Yace.
“Amma matar shi bata san da wannan ba, zan iya ce miki bai yi sa’ar aure ba. Ni zan gaya maki wanene Ogana!
Yau shekaru na sama da biyar tare da shi, ko tsawa wannan bai taba hada mu da shi ba.
Yana treating din mu asperfecthumanbeings; babu maganar bawa da Ubangidan sa, sai mutunta juna da baiwa kowanne hakkin dan uwan sa da ke kan shi.
Bata kyautata masa sam, bata kuma da lokacinsa, bayan kallo daya zaki mata ki san ita ba sa’ar auren sa bace, sai kaddara. Kullum cikin banbancin ra’ayi suke, kanta kadai ta sani da aikin bankinta.
Kin ganshi ba mazauni ba, sai yayi watanni biyu baya kasar ya dawo tana gidan kawayen ta ko ofis dinta, ba abinda ya kai wannan aikin muhimmanci a gareta, a shirye take kuma da ta ta rabu da komi, domin tsira da shi, wataran in sun soma haurawa har mu mukan ji, amma an fi jin nata, don bata da sirri ko kadan.
Allah ya hore masa iyaye, ta raba su, ‘yan uwa da duk wani abokin arzikin sa. Abokan aiki kadai ta bar shi da su” nace “to ku ina ruwan ku kuke sa masu ido, in suka koreka naga inda zaka je kayi aikin kuku kana karatu a bati”.
****








W
ashegari Anti ta tafi aikin ta kamar yadda ta saba, wato karfe bakwai, sai 10:00 Oga ya fito shima cikin shirin nashi ofis din, Tom rike da suit-case din shi. Shikuma ya ratayo falmaran din ‘Australian-Suit’ din da ke jikin shi a kafadun shi.
Da kanshi yayi sallama dakin da nake, sai da na amsa ya murda kofar suka shigo duka. Rungume nake da Jawad a kirjina, yana tai min kiriniyar sa irin ta lafiyayyun jarirai ina shan dariya.
Nayi saurin tashi zaune na zube a kasa na gaishe shi, yana daga tsaye ya karewa dakin kallo tsaf kafin ya zauna a gefen gadon, ya dauki Jawad yayi mai ‘kiss’ a kuncin shi yace
“Yello my bouncing beautiful baby, how do you dotoday?”
Tom yayi dariya ni kuwa na sake nutsuwa,
“ke bakya daura kallabi ne, kullum kuma kai ba kitso, me yasa?”
“Bani da kallabi, kitso kuma waye zai yi mun ranka ya dade?”
Yayi murmushi,
“zan kawo miki kallabi da atamfa har da shadda a dinka maki zane, don na lura kina takura cikin wadannan kayan wanda na tabbata tsarin Mubina ne, kina so?”
“A’ah ranka ya dade”
“meyasa?”
Na tuna sanda take ce da Talatu (ki zabo mata kayan sawa, wanda ba’a daurawa, idan naga zani a ciki, Ubanta zan ci).
Ni kuwa duk wani abu da za’a ci mutuncin Ubannan da bani da kamar sa, ina gudun shi, ina nesantar shi ina kuma rokon Allah yayi mun katangar karfe da shi. Ya lura tsoron Mubina nake ji bai kara maganar ba.

“Ina so ki gaya mun tsakanin ki da Ubangijin da ya halicce ki, me kike bawa Jawad tun zuwanki?”
Ban ji tsoro ko shayi ba, don na lura ba halin su daya da matar shi ba
“Kamun waken-suya neda ruwan da a ka ce kar in bashi sai yayi wata shida. Rannan yana shaquwa, na ji tsoro na bashi ruwa, data tsaya kullum na bashi ruwa da sauri yake shanyewa, amma bana bashi na famfo sai irin wanda naga Anti na sha”.
“Good (da kyau) Nanny Atine, zan sa a kawo miki buhun waken-soya. Even the swanwater boiI it.(ko ruwan swan ne ki tafasa).Da yamma Tom zai kai ki wurin Yarbawa masu yin kitso, su dinga yi miki weekly (duk sati) kin ji?”
Na gyada kai, na sake kaskantar da murya na ce
“na gode”.

Ranar wata Litinin bankin Omega an rufe shi, sakamakon gagarumar satar da suke zargin Akantocin sun masu, Anti na gida kenan, Yallabai kuma bai fita ofis ba da wuri, suna karya kumallo, take gaya mai wai cikin da take da shi ya bare tun sati biyu da tafiyar sa.
Ya kalleta kawai, “ko kuma kin barar ba? Ke dai Muslincinki akwai questionmark(?) a cikinsa, mts! Mubina, halayenki bakidaya ina kyamar su, don kwata-kwata ba ra’ayin mu daya ba, abinda na hango kenan tun farko na gaya maki bazan iya auren ki ba, kika sa Alhaji ya takura min.
Na aureki A BANA SON KI, na soki domin zuri’ar da Allah ya soma bamu kuma dole in so uwar ‘ya’yana koda na ki Allah.
Ni mutum ne mai son tara zuri’a, domin gidan mu gidan zuri’ar ne, nine Uba a gidan mu a halin yanzu amma ko kanin baya na ‘ya’ya biyu gareshi sai ni da Allah ya hada da wata irin ballagazar mace, wadda bata san ciwon kanta ba, bata san meye aure ba, waye mijin ta, me cece darajar sa gareta kuma waye Dan da ta haifa, da cikin ta…..”
Sallama nayi, ina dauke da Jawad domin ta shayar da shi, don yau bata bashi na safen ba har yanzu.
Nayi sallama ya kai sau uku basu jini ba, sai ya zamanto duk rabin zancen na ji, na juya da nufin fita wai su gama, sannan in dawo mata da Dan ta.
Yallabai ya juyo “zo, me nene?” Na dabarbarce na rikice da mugun kallon da Anti ke jifa na dashi, zani ne a jikina, na danyar atamfa super-holland, riga da zane da kallabin su, da Tom ya kawon har saiti biyar. “umh-umh dama-dama Jawad ne bai sha na safen ba” “to bata shi mana?”
Ta karbe shi kaman ta karbi kashi, idanuwanta na walainiya a jelunan kitsona da kuma zanin jiki na.
“Uban wa yace ki daura mun zane cikin gida?” Nayi tsuruuu! Kaina a kasa ban amsa ba.
“Uban Jawad, dan Kauyen KARAYE!”
Muryar Yallabai duka ta gigita mu, musamman ni, don ita nasan ta saba da halin shi, sun saba samun sabani akan barorinsa. Ta zuga tsaki ta tashi fuuu! Ta yi dakin ta bayan ta dangwarar da Dan da duwawunshi a dandaryar carpet, ya saki wani irin rudadden kuka.
Gabadaya muka kai gareshi, ni da Yallabai, nayi sa’a na riga shi dauke shi. Yace “ki je ki lallashe shi, zani ‘meeting’ Lagos. Idan na dawo zan kawo miki wani irin madaran da ake baiwa yaro in ya shiga wata shidda. Ki kular min da Jawad, ni kuma ZAN KULA DA KE!”

Daga yadda yake maganar, na fahimci ran shi a masifar bace ya ke. A daki na rungumi Jawad, a raina nace lallai ma wannan matar, ita bata san ita mummuna bace, Allah ya bata miji mai kyau take sakarci. Allah yasa kada wankin hula ya kaita dare.
Ni kadai na ke gayawa kaina. Tom ya dawo muka koma karatu.

A watanni na na biyar da fara rainon Jawad, zama da su Tom, duk zancen su turanci ne, yau da gobe tafi karfin wasa, na soma iya rubutu da karatun turanci. Tom ya kara dagewa da kawo min littattafan da zasu taimaka wurin koyar da ni sosai.
Har ya zamanto in zai fita ya samu ina barci, ko sallah, sai ya bar min note a dan takarda. Zamana a kichin tare da su kullum, yasa na kware a irin girke-girken zamani da suke yi, da amfani da na’urorin saukaka ma dan adam wahala.
Wata yammacin Litinin nace
“Tom, yau girkin gidan mu nake so in ci, ko zaka taimaka ka samo min kuka, daddawa, citta da garin tuwo?”
“Muna dai da garin semovita, tun wani tafiya da Oga yayi Britain yasa ni na sayo, muna da garin niqaqqiyar citta, daddawa ne baza’a’ samu ba. Amma zan bada sautu in za’a yo cefanen wata, ko a cikin Neja (Niger state) za’a’ samu”.
Muna maganar ne da turancin broken dana soma koyo. Shiko Ejiro dariya yake mana.Ya kawo kayan girki na tayar da ruwan miya, da kayan hadi sosai. “ ….. A dafa da mu” in ji Tom. Sai na kara ruwan miya.
A can gefe na dauki dakwalen zabbi guda uku daga cikin freezer, na wanke su na zuba a wata tukunyar dabam na dora bisa cooker, na wadata su da albasa da fresh tafarnuwa domin kashe karni, na daka kayan kamshin hausa cikin blander na zuba gishiri kadan, sai maggin knoor, guda 3 babu kayan kamshin bature ko dis.
Zabbi suka soma tafasa, duk gidan ya kauraye da wani bala’in kamshi. Wanda ba shi aka saba ji ba. Na maido ruwan miyar cikin zabbin, na kada kuka akai, ta kadu, babu gudaji ko daya, na rufe ya dahu-ya-dahu yayi lugub, har tsokar ta salibe da kanta, nasa wani irin ludayi mai yatsu na zare kasusuwan tas.
Tafasashshen ruwan banyi talge da garin semovitan ba, sabida kada yayi laushi da yawa, sai na zuba shi a haka, can anjima nasa muciya na tuke shi tsaf, daya kammalu na kwashe na rabe mana mu uku na zuba nawa a warmer da niyyar sai nayi wanka zan ci, Tom ya daura abincin dare kaman yadda ya saba.
Dirin motocin da muka ji ba daya ba, ba biyu ba, mun san maigidan ne ya dawo unexpected. Bayan ya gama da mutanen kasa ya iso sassan mu. Su Tom suka je suka kwashi gaisuwa. Ya tsaya falon Anti
“ku ina matar gidannan? Karfe shidda har da kwata yanzu, ba biyar take dawowa ba?”
Tom yayi shiru Ejiro ya sunkuyar da kai, ya kuta yace “ina Jawad?” “Yana can dakin mai rainon sa”. Samson ya shigo da katon din madara ya umarce shi da ya kaiwa mai raino, ya kuma ce ta kawo Jawad.
Ya dubi Tom “na kwaso yunwa, tun safe muna a ofis din Governon Lagos, sun bani cake ne da lemu kawai, ina fatan ka kare abinci?”
Tom ya kara nutsuwa “Oga ban san da zuwan ka ba, zan iya hada emergency sai dai…..” yayi shiru.
“Sai dai me?” “Eh to, tuwo ne mai rainon Jawad ta yi, muka ci. A yadda nasan bakin Oga na, Ba-Hausa ne, nasan zai iya ci. Domin yafi wanda nike wa Oga yana sa mun albarka”.
Yayi murmushi, “naga alama kun zama wasu too-close da yarinyar nan, to a kawon zan ci, in ka tabbatar da tsaftar sa”.
“Oga, Tine in ban ce ta fini kula da tsaftar abinci ba a yayin girki, ba zan ce na fita ba!”
Sai ya sake murmusawa, dai-dai lokacin da wayar shi tayi kara, ya fiddota daga aljihu ba tare da ya duba sunan mai kiran ba, ya kara a kunnen sa,
“…wannan kuma ruwan ki ne Mubina, ki cigaba da yi mun duk abinda kika ga dama, watarana da sadaka aka ce ki yi mun wulakanci wallahi bazakiyi ba, an ce maki na damu ne? Koki dawo, ko ki kwana wurin watsewar ki, Taheer, na tuno ki?
Yanzu ma don in ga lafiyar yaro na nazo, in sallami ma’aikatana da albashin su da yake kaina. Jibi zan koma Canada, sai kin ganni sannan kiyi mun wulakanci, Mansinar ki din banza?
Har ciwon Mansina yafi lalurar mijin ki, hakkin sa na wata da watanni, jaririn ki…idiot, stupid…., nonesense..!”
Tuni Tom ya kama gaban sa. Yana huci bisa ‘dining-table’ ya aje abincin ya koma ya dauko lemun Yallabai (prime-lady) da tambulan ya aje ya fita.

“Tine, maza gyara Babe din ki, Babansa na son ganin sa” “an ce ma sai Baban sa na nan, nake gyara shi? Dama a gyaren yake, awan sa daya da wanka, amma bari a sake sabo”.
Ya fita yana dariya.

Dinkakkiyar babbar rigar Voyel ce a jikina da fatalar ta na daura, kalar su maroon, nasa Jawad a bayana na goya, nayi sallama na taras abinci yake ci. Ko kadan ban kawo tuwo na bane. Sai na juya da nufin in ya kammala na dawo mai da Dan sa….
“…..Yaki Maman Jawad, sauko shi” na saukoshi na matsa na mika mai dan sa, ya rungume shi yana sunsunar shi. Ya lumshe ido a hankali, tsayin mintuna biyu bai bude su ba.
Can ya dago idon shi jazur kaman wanda yayi kuka.
“Zan roke ki wata alfarma. Nasan aikin ki shine raino, amma zaki dinga dafa mun abinci a duk sanda nike nan Abuja. Ni cimata ta kauye ce. Su Tom basu yi mun mai gamsar da ni.
A yau wanda kika yi mun irin na BABATA NE. Zan ninka albashin da nike baiwa iyayenki, daga goma zuwa talatin, kin amince?”
“Ran ka ya dade, ni wannan ba wani abun wahala ba ne, ba sai ka karawa Babana kudi ba. Ina tabbatar maka wanda kake bashi, ya ishe shi shida iyalinshi, na roke ka, kada ka karawa Babana kudi”.
Shiru yayi kawai yana kallona, “ke, zan kai ki makaranta. Gobe Insha Allahu, kina da hankali na lura, kina so?” “Ina so mana” “shi kenan jeki, ga madaran da nace miki za’a kawo miki, ki zuba ruwan dumi (2 litres) kullum a fidar sau uku a rana, kada ki rage kada ki kara, wannan ba’a mata karambani, don naji Tom yace kina da kankanba, kuma ki cigaba da bashi duk abinda kike bashi. Kada ki kara kawo shi wurin uwar shi wai ta bashi nono, in ta ce don me?
Ki ce nine na hana. In ta takura, ki kyaleta. Tashi ki tafi, kiyi shirin makaranta gobe. An jima za’a kawo miki duk kayan makaranta”.

Na mike gwiwoyi na a sage, zuciyata a wanke fes, da murnar zani makaranta. To gudan raina MOHAMMAD JAWAD, an yi mai yayen kwara. Mai kula da shi din wato ni, ance makaranta zani. Na san kuma ba a zuwa makaranta da kananan yara.

A wani bangaren, yaya zanyi da bala’in Aunty Mubina? Dama tace mun wai, tarani take. Ta hana ni sa zani, na roki mijin ta ya dinka mun, ta ji kuma yace na ba dan ta ruwa, tun bai kai wata shidda ba.
Kuma taji daga bakin munafikin ta (Peter) ina bashi wake. Sannan tace in bata danta ta bashi nono, in ce a’ah, Da na ne?
“Atine, a kan umarnin wa kike? Mai gida, wanda ke biyan iyayen ki, tayi miki koma ma me zata yi miki, ai dai bazata kashe ki ba, bata isa kuma ta kore ki ba, tunda ba ita ta kawo kiba, ba kuma ita ke biyan ki ba, sannan ba zaman ta kike ba, to shin don me zaki damu da ita? Ai gara a kyautatawa, wanda ke kyautatawa!”
Washegari na dage na zabga tuwon semovita, miyar danyen kubewa da ribdediyar kaza a ciki. Na hada lemun zobo da kayan kamshi masu wartsake makoshi, na zuba flavor vanilla, nasa a firji don yayi dan sanyi.
Tun safe Tom ya markada ayar kunu dana jika tun daren jiya, mai kyan ‘yar Katsina. Nayi kyakkyawa, kuma tsaftataccen kunun Aya, Tom ya diba ya kai matsayin karin kumallo.
‘Yar boko, tun 7:00 ta fice aikin ta. Nayi wanka na shirya Jawad yayi kyau cikin kayan sanyi, brown, na kasa shiryawa sai nasa kuka, ina makale da shi shima yayi lamo, a kafaduna.
Sallamar Baban Jawad na ji ba zato. Bagatatan ba tsammani. Ya shigo tare da Ejiro. Ya jingina da bangon dakin hannuwan shi duka biyu harde bisa kirjin shi. Kallo yake mana cike da sha’awa.
“Maman Jawad, bakya son school, kuma dole ki je. Bana zama tareda mai JAHILCI da matacciyar zuciya, duk wani wanda ya rabe ni ko JINI NA ne, koba Jini na ba ne dole ya je neman Ilmi”.
“Ni ba makaranta ne bana so ba; Jawad, da wa zai zauna? Bazan baiwa namiji raino ba, ko zasu yarda mu zauna tare?”
Yayi wani irin murmushin daya fiddo tsabagen kyawun kuruciyar shi,
“tun kamin inyi tunanin kai ki makaranta, na tuna Jawad, da kyakkyawar kulawar da yake samu daga gareki. Blood isthicker than water (jini yafi ruwa kauri ).
Sai dai don Da na guda daya, bazan ki taimakon mace ba, MACE AL’UMMAH wadda in ta ilmantu al’umma da yawa zasu ilmantu. Kuma mace wadda ta fito daga masarautata, KARAYE.
Karatun ki, ba ke kadai zai amfana ba har da ni. Domin Jawad daga gareki ne zai soma samun tubalan ginin rayuwar shi. Wala’Allah mai kyau ko maras kyau. Kenan ba zan so shi da mara kyau ba?”
“To yanzu ina za’a kai shi?”
“Kullum da safe zuwa karfe daya da rabi na rana, wato lokacin tasowar ki. Akwai wata gyatuma ‘yar garin Karaye, da mijin ta ya rasu a hadarin mota, bata taba haihuwaba.
Da aka yi wani kakkarfan ruwan sama a Karaye, gidan ta ya rufta mata a ka, ta gurgunce, take bara a kofar gidan Maimartaba.
Na daukota na sai mata karamin gida a Wuse, ina sawa ana kai mata abinci da kudi duk wata tare kuma da wata ‘yar uwar ta suke zaune.
To ita za’a ba Jawad har ki taso makaranta. Tunda nace ZAN KULA DA KE, tunda kina son Jawad, to matsayin ki gare ni BA ‘YAR RAINO BA, ‘yar gari na nake riko sabida Allah ”.
Yayi shiru, can ya runtse ido yace “Atine ke, na bar maki Jawad, matsayin ‘DA’ ke Uwar Jawad ce da nake biya bata hanyar aure ba. Tamkar rikon da Halimatus-Sa’adiyyah tayi wa Annabin mu. Sabida haka ki kula da Jawad kulawar da Uwa zatayi wa Dan ta, ni kuma ZAN KULA DA KE!”
***













A
bu nasu na manya ‘yan cuku-cuku, sai gani a aji hudu na firamare, gwajin da aka yi min duk na cinye na side turanci kamar ‘yar sakandire. Shi kansa (head-mastern) cewa yayi anya banyi firamare ba zan maimaita?
Oga kuwa yafi kowa mamaki, ya titsiye ni da tambaya nace Tom ne ya koya mani.

Maganar sunan da za’ayi amfani da shi yace meye sunana na ainihi? Ni kaina in za’a kashe ni ban sani ba. Yayi waya gidan su wato gidan Maimartaba, ya tura Talatu ga MAI-KALWA, ta tambayo ta fada mishi.
Washegari ni ce cikin ‘suit’ da ‘skirt’ din makarantar firamare ta ‘ya’yan masu fada ajin Nijeriya, da ke birnin tarayya, Abuja. Na daura Cambas, Tom ya ratayan School-bag. Abban Jawad yace.
“Daga yau sunan ki ZUBAIDAH MUHAMMADKARAYE”.
***
N
a cigaba da zuwa makaranta, Direban cefane, ke kaini ya dawo da ni, sannan mu biya mu dauko Jawad gidan Kulu kullum. Duk abin nan da ake, Anti bata san wainar da muke toyawa ba, tana riga kowa fita a gidan, kowa kuma na rigata dawowa.
Shakuwa mai tsanani, irin ta Da da mahaifi, ke kara shiga tsakanina da Jawad. Tun sanda Yallabai yace kar in sake kai mata shi shan nono, ban sake ba, itama kuma na lura ta ji dadin hakan. Bata ko sake tambayar yaya lafiyar yaron ba, balle ni karan kada miya. Wannan wace irin UWA ce???
Nafi maida hankali kan abincin Jawad dana Abban sa, fiye da karatun kansa. Sai dai shima ba laifi ina kokartawa. Jawad yayi wani irin girma da karfi, ya soma rarrafe, sannu-sannu sai mikewa zuwa tafiya.
Bakin shi ya soma budewa, yace min Momi, Baban shi Daddy, Tom Uncle, su Ejiro da ke yawan daukar shi duk Uncle ne a bakin shi.
Aikin da Yallabai zai je yi kasar Canada, bai fito ba sai bayan shekaru biyu. Bai tafi ba sai da ya kai Jawad makarantar rainon yara ‘nursery’. Don haka ba zancen kaishi wajen Kulu.
Ni kuma lokacin takardun jarrabawata na kammala firamare sun fito, nan ma zuke yasa aka yi mun sabida hazakar da na nuna a takardun, aka samar mun gurbi a NURUL-BAYYAN INTERNATIONAL ACADEMY ABUJA.

Sau uku Hajiya Talatu tana zuwa duba lafiyata, duk sanda tazo, tana sambarka da rayuwata ta komawa iyayena da labarin yanayin da ta ganni a ciki, na kwanciyar hankali da samun kulawa.
Sai dai tace min shi Baba ne da kansa yace in zauna, kar ta dauko ni ganin gida, har zuwa lokaci da ya tsayar da tunanin shi kan wanda yake son baiwa aure na, domin muddin na zo gida, nadawo kenan ba zai barni in komo ba.
Watan Yallabai daya da tafiya, ranar Lahadi, daga ni har Anti muna gida, yau kuma ko allurar uwa ce ta motsa oho, ta danna min intercome naje na isketa tare da ‘yar duniyar kawarta Mansina.
Ta bini da wani irin kallo, wanda nasan bazai wuce na mamakin, masifaffar canzawar da nayi ba. Ta kare mamakinta tace in kawo Jawad, Mansina ce ke son ganin sa.
Na lura da irin kallon da Mansinar ke mun, akwai magana.
Jawad na bisa gadona yayi baja-baja da motoci da jiragensa “Momi wannan helcoptern batir din ta yayi sanyi, a canza” nace to Jawad, na canza batir, nace “bakuwar Maman ka ce zata ganka, muje ko?”
Ya noke kai,
“Momi sai kin man banbu”
“wannan abu mai sauki, Jawad, zo ka hau, kai da bayan Momin ka?” Yayi dariya ya dare bayana.
Gab nike da shiga jin ana ambatona, ya sani dakatawa.
“Itace mana, mai wanke-wanken nan da aka kawo mani kafin tafiyar ki karatu Scotland, kin mance yadda tazo min; cikin tsummokara da yalayen hakora, kafafu kamar sillen kara, baki kamar bayan tukunyar mai shayi har nasa mata suna ‘BLACK’ amma dubi yadda tayi haske.
Duk kasusuwan sun ciko da tsoka, ashe dama rashin kyakkyawan abinci ne, da yake na dade banganta ba, don daga su har Abban Jawad, ba shiga harkar su nake ba.
Mansina gaskiya na gaji da auren nan, nayi kuskure da nayi tunanin Taheer shine Mr Right dina. Wani irin kidahumi ne, ban taba samun shi da irin ra’ayi na ba kwata-kwata, har yanzu baya sona.
Ya dauki son duniya, ya daura akan wannan figaggen Dan nashi, a sabili da shi yarinyar nan ke daura zannuwa irin nawa. Idan nayi magana, yace nakasa rainon Da na tayi mun ai ta cancanci hakan.
Duk tsarin zaman da nayi mata, ya rusa. Ya bata irin damar da ya baiwa su Tom a gidan nan, suna abinda suka ga dama. Kin san munyi fadan tafiyar nan da zai yi Canada, yace sai dai a tafi da ita, sabida Jawad, bai saba da ni ba.
Ni kuwa da in shiga jirgi da yarinyar nan, gwara nayi zamana wallahi, tunda na dauko ta shiga duniya, ta fita kunya, ya sanya mata kahon zuka sai da yasa ta koma kasar su.
Wallahi Mansina ina tunanin aure na da Taheer, ya kusan zuwa karshe, tun da ba shi ne autan maza ba. Bazan zauna in kare kuruciyata da mutumin da bai san ciwon kan sa ba, bai san darajar da yake da ita ba.
In kin ganshi yana dariya, to da wadannan barorin nashi ne da yake gani tamkar abokan sa.
Ba abinda yafi bani takaici irin naga Tom, yana tuka motar da mijina yake hawa wallahi ji nake kaman in yi aman zuciyata. Kin san ma abinda ke daure min kai?”
Mansina kai kawai ta girgiza ma’ana “A’ah sai ta fadi”.
“Ni dai nasan Taheer ba manemin mata bane, bakuma wani mabukaci bane cancan. Amma sai yayi tafiya har ta tsayin watanni biyu ya dawo ba wata mu’amalar kirki. Karshe ma ni ce mai nema, yana yanga yana jan aji, sai ya gama kwalani a kasar wulakanci tukunna,

Please Login or Register in order to submit comment