Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sandunan rake na raba na ba kowa Goggo tace bazata sha ba wai ita likita ya hanata shan abu mai zaki.
Muna zazzaune muna shan rake sai ga almajirai suna shigo da kwalaye muka bisu da ido, kowa yayi shiru sai da suka kare Awal ce “shin daga ina aka aiko ku ne Tanimu?”
“Yallabai Bellon gidan Waziri ne, yace wai a kawowa mara lafiya, da yamma zai shigo ya dubata in ba damuwa” ya fiddo wata jaka fara tas, shake da kaya yace
“wai wannan na Atine ne”.
Baba ya mike yace “yana ina? Ba za’a karbi kayan Atine ba, amma na maras lafiya an gode. Abinda yayi ma kadai ya isa, Allah ne kadai zai biya shi, don haka ku maida mai wannan”.
Sani yace “haba Baba! Bello don wa yake wa Goggo wahala, ba don Atinen ba? Ba kuma a mayas da hannun kyauta baya”. Baba ya murmusa yace “Sani, tunda nace a mayas, to a mayas”.
Sani ya san Baban mu sarai, mutun ne mai kaifin basira, tabbas akwai abinda ya hango. Shi da kansa ya dauki jakar ya nufi dandalin hirar su, aka sanar da shi Bello ya je kiran Maimartaba, can ya zauna jiran shi.

Inna ta saki baki tana kallon ikon Allah, Auwal na bude kwalaye yana yiwa Baba bayanin locozade ne maras lafiya ke sha don maida kuzari, katon na madara peakta ruwa da katon din milo kayan shayi ne, Heinz-beans wake ne na gongoni. Wannan mai kwaya kwayan na cikin kwali sukari ne, shikuma wannan tang na kwalba lemu ne irin lamurje, ake zuba suga da ruwa a sha. Wannan na zungura-zunguran gongoni dankalin turawa ne aka sarrafa haka, sai magungunan Goggo da likita ya rubuta da za’a sallameta.
Baba bai ce komi ba, sai ma cewa yayi a hada su yadda suke a kai karkashin gadon sa, in aure Allah bai yi nufin sa ba, ina zamu nemo su?
Ni kan kaina a duke yake, tsoro da fargaba sun cika ni, ji na nake kamar wata bare a cikin su, kamar kuma wadda ta aikata wani gagarumin laifi. Ina kallon sanda Inna ta kyafta ma Atika ido suka mike suka shige daki.
Baba da Awal suka nufi masallaci don bin jam’in sallar Magriba. Nima na mike na zubawa Amarya ruwan alwala ita da Goggo, nayi alwalah na yi sallah na kara nemawa Goggo sauki wurin Ubangiji, na kuma rokeshi, idan tarayyar mu da Bello, akwai alkhairi a ciki, ya cire mun masifar tsoron shi da ke gallaba na, ya tsayar min da hankalina wuri guda.
Har muka yi Lisha, shiru ban ga Atika ba, Amarya ta kare tuwon dawa miyan zogale ta kira ni in kaiwa Inna, in kuma kira Atika mu ci. Kamar yadda mukasaba.
Nayi sallama ba’a amsa ba, suna can kuryar daki inda na jiyo sheshekar kukan Atika, sai muryar Inna kasa-kasa
“kiyi shiru abinki, Atika na ki bar asarar hawayen ki a banza da wofi, su aureshin in gani, ai ba tun yau ba nake gaya miki mutanen nan basa kaunar zaman mu a gidan nan amma kin yi sautun mahaukaciya da ni, kin nane a gindin su, ke kenan Atine sama Atine kasa ke mai ‘yar uwa, ai gashi nan ta nuna miki karshen ‘yan uwan taka tayiwa kanta miji mai ido da kwalli.
Ko bakya son shi tunda har naji zancen, dole ke zaki aure shi, wannan shegiyar afiruwar a gidan saraki? Kirji kaman danmalele, kugu uwa an tatsile kuliya bisa kwalta, ke kuma a gidan manomi, waye Jibo? Ai bazata sabu ba.
In dai akwai boka, Mallam da bori a duniya BELLO BAZAI AURI ATINE BA, sai ke, ko kuma duk ku rasa”.
Muryar Aika "wallahi Inna ni in baki sa ya soni ba, sai dai in mutu ba aure, wallahi shikadai nake so Inna, duk cikin samari na babu kamarsa, mai kyau ne dan birni ne kuma mai ilmin bokon nan irin na radiyo, ke baki ganshi ba fa….” “nace na ji ya isa, Atika, ASIRI FA GASKIYA NE, wallahi kin ji na rantse miki daga Atine har Amarya, sai sun bar mana gidan nan, sai sun…..”na gyara murya na kwarara sallama sukayi tsit, ya tsumma cikin mai.
Atika ta leko jikin ta a sanyaye idanun ta sun yi ja tace “au, ke ce, baki shigowa? Tun yaushe kike tsaye?”
Nayi murmushi “abincin Inna ne na kawo, ke kuma in kin gama kukan kizo mu ci namu”.
Na kwanta rigingine ina tunanin maganar su Inna, wata zuciyar nace dani in fadiwa Goggo da Amarya. Nasan Inna bata da imani ko miskala zarratin duk abinda ta furta zata yi, to sai ta yi shi hankalin ta ke kwanciya, amma sai nayi wani zuzzurfan tunani sanda Liman ke ce mani.
“A kowane hali kika tsinci kanki, ki rike Allah, ki sanyawa ranki cewa yana tare da ke a duk inda kike”. A kwai kuma sanda yake yi mana nasihar munanan aiyuka masu kai mutum wuta, yace
“ku guji munafinci. Cikin kaba’irai shima babba ne, wanda Allah (SWT) yayi wa ma’abotan sa tanadin wutar jahannama, inda yake cewa “Innal munafiqina fid-darkil asfali minan-nar” ya kuma ce “fa bash-shirhum biazhabin azeem”.
Atika tace da shi a lokacin wai
“MEYE MUNAFUNCI?” Yace “shine;
-Yi da mutane (cin naman mutane)
- Hada husuma tsakanin mutane
- Daukar zancen wani ka kaiwa wani
- Zunde, yafice da kifce duka munafinci ne
- Zama da mutum da zuciya biyu.
Kenan in na fadawa su Amarya, nayi munafunci har kala biyu, na dauki maganar Inna na kaiwa Goggo; na hada husuma tsakanin su. Ban kuma amince babu wanda ya isa yayi min abinda Allah bai kaddara a kaina ba.
Shawara ta karshe da na yanke shine in yi shiru, in yi addu’a Allah ya kare mu duka daga sharrin su, in kuma san irin zaman da zanyi da Atika a yanzu…
“ke Atine! Ke Atine, kina inane?”
Sani ke kwala mun kira tun daga can tsakar gida, na yunkura kenan ya shigo ya russuna ya gaida Goggo da jiki, ya soke kai yace
“Goggo, Yallabai Bello ne zai shigo dibaki” Goggo ta mike zaune Sani ya sanya mata filo don ta ji dadin kishingidar, ya shiga kauda shirgi a hamzarce duk sai ya bani dariya.
Nayi murmushi mai fidda sauti ya juyo yana hararana
“ke dai wallahi kazama ce, dibeki don Allah, kuma baki san kinyi manyan baki ki tashi ki dan gyaggyara ba, a’ah, sama-tsami tsaka-tsami ko koyi da Atika bakyayi, shiyasa baki da samari sai shegen jin kan tsiya, shima dai Yallabai ban san me ya gano jikin wannan afiruwar ba…”
Goggo ta sunkuci kwanon tasar da ke kusa da ita ta jefe shi da shi tace
“dan nema, ai sai ka je ka gaya masa wannan bayanin naka. Shi yasan me ya ganin, haka a kazamcen kuma a afiruwancen.
Yanzu ne kake ganin Atine na Afiruwa amma Sani, na rantse, na kuma na rantse bazaka samu mata ya Atine na ba.
Ka bawa Atine shekaru uku a gidan Bello za ka sha mamaki”.
Sani ya fita yana dariya na hade rai, na cika nayi fafam kiris nake jira in fashe, da kyar ta lallabani in je in dauraye jikina, in sa kaya mai wanki, na nufi dakin Amarya inda kayana suke.
Gabadaya gidan mu ya gauraye da turaren shi mai sanyin dadi. Sun dade suna tattaunawa da Goggo, sannan Inna ma ya je har dakin ta ya gaisheta ya aje masu rafar ‘yar murtala sabbi kar.
Ina kuryar dakin Amarya ina jiyo gaisawar su duk na rikice na dabarbarce kamar kullum naji muryar Bello, ina jiyo Amarya na tambayar wanda suke tare yace babban aminin shi ne, tare suke karatu can Jos, a Bukuru yake sunan shi Muhammad. Tace ashe maigidanne, Mamman ko?” Sukayi dariya.
“Mama ai nima Mamman din ne, a can Jos, Muhammad nike, ainihin sunan Muhd. Bello” ta jinjina girman mai sunan tasa masu albarka tace
"ka dinga hakuri da Atine, sai a hankali zaku saba, tace tsoron ka take, kuma dama dai halin ta wani iri ne sai Goggonta" kai ya dukar, cike da kunya. Muhd. din ne ya amsa "to Mama".
Suna fita tana kwallan kira tace in dau kudinnan in mayar mai bazata amsa ba, ba kuma ta sigar rashin da'a ba. A dan filin da ya zama zauren mu, jingine suke jikin buhunan kalwa, basu ko damu da warin kalwar ba, na russuna na gaida abokin da alama mai barkwanci ne yace
“naqi in amsa Atine, ya zaki gaida Muhd. Jos, baki fara gaida Muhd. Karaye ba? Bayan a dalilin shi kika ganni?”
Nayi shiru, kaina a sadde ina dan murmushi.
“Atine, kuma sai aka dawo da ajiya mai ita bai ce akawo ba, kin kyauta kenan?”
Da kyar cikin ‘yar siririyar muryana nace “wane ajiya ne?” “Rigar sanyin Dan Karaye mana?” “Wane dan Karaye?” “Au, baki san shi ba?” “Da na san shi ba zan tambaye ka ba” “to dago dubar ni, in nuna maki Dan Karaye”.
Kamar wata doluwa, wai sai na dubeshi har ga Allah, ni da zuciya ta daya nake magana.
Ashe shi tuni har ya canza wuri sai muka hada ido hudu da Bellon da ke rikita ni. Idanuwan shi lumsassu ne, kuma manya tamkar nawa, bakin zanen idon shi har wani kyalli yake na musamman cikin hikimomin Ubangijin halitta.
Wani irin kallo ne da shi mai jan hankali da ban sha’awa, ban iya na dauke kwayar idanuna ba kazalika shi din, Dan Karaye, kokari yayi ya sarke kwayan idanun mu sarkewa mai ban mamaki. Ke da gani kinsan ya saba yi wa mata, ba ni ce ta farkon ba. Kallon da ko kin ki Allah, dole ki fada a tafkin kaunar shi…

Ni naga Bello mai kyau ne, amma ba wannan ne ya razana ni ba; tsabar kwarjini da cikar zati. Ingarman namiji ne tako’ina, Bello Waziri bai da makusa. Dogo na hakika, mai ginannen kakkarfan jiki, ga wani lafiyayyen saje da ya aje tun daga gefen kunnuwansa har zagayen lafiyayyen bakin shi, lebba gareshi masu sulbi da sheki bakake sidik. Shi ba fari ba shi ba baki ba gashi nan dai ruwan kasa mai daukar ido.
Sanye yake da Jabba (kayan sarauta) kufta da wando na wani rantsatstsen yadi ruwan madara, wani irin budadden takalmi ne a kafar sa, wanda ya tona asirin, lafiyayyun yatsun shi da sullubebiyar kafar shi tamkar bai taka kasa, gashin kansa baki wuluk sai sheki yake kazalika bakar daran dake kanshi, gassun ta na reto a wuyan sa. Ta ko’ina nasan Bello ba tsarana bane, koda yake nima wai ina da kyau inji Goggona? Oho.
Tafin Muhd, har tsakar kan mu, gabadaya muka juyo muka dubeshi, idanuwan mu jazur; so kenan, ke aiki a tsakanin mu. Dan Jos yace
“a’ah Atine! daga cewa ki dube ni, in nuna maki Dan karaye, sai ki dulmiye gabadaya? Ya dace in kauce hakannan, don naga Dan Karaye bai son fadin son a gabana. To an ce dai kallo in ya wuce daya, biyu haramun ne na barku hakannan”.
Bello bin shi yake da ido kamar ya ga mahaukaci sabon kamu yace “Atine, na aiko maki da sako kika ce a maido mun kayana? Don sun yi kadan, ko don har yanzu kina jin tsorona?”
Na harare shi kasa-kasa
“ina jin tsoron ka fa kace, akan me?” Yayi murmushi “na ji ne daga bakin da ba zai mun karya ba” “ ni wallahi bana tsoron ka, da ina tsoron ka ashe da ban rama zagin Uba na da akai ba”.
Yayi murmushi a karo na biyu “to tunda baki tsoro na, kuma ki na son in yarda baki tsoron, shin yaya sunana?” “Dan Karaye mana?” “Ai kin ji tsoron kenan, wannan ba suna bane don ko ke ‘yar Karaye ce, amman ai Atine ce, don haka ya sunana?” “Na manta” ya sake murmusawa ya kashe zancen ta hanyar russunawa ya tura min jakar dazu gabana
“Atine, ba’a maida kyautar miji, don haka kada in kara baki abu ki maido mani, kina ji na?” Ya dan fiddo ido na kara tsorata don haka ya saki, ya koma zolaya.
“Kyauta yana kara dankon kauna, bana yiwa kowa kyauta sai wanda yake (so special) a gareni, sai dai sadaka. Na fahimci baki iya karatu ba, don haka ki ba Awal ya karanta maki abin da na rubuta, doguwar wasika ce.
Akwai hotunana a ciki don ki karen kallo, ko akwai wani abu wanda yake wani nakasu a tattare da ni, don nagane har yanzu ana so, ana cillawa kasuwa ne.
Zan koma Jos, bazan dawo ba sai da kayan auren mu. Amma Atine, bazan samu koda gaisuwa ta mutunci, daga matan da nike so da aure ba, daga Atinen da ta sani aure ban shirya ba?”
Wani tattausan murmushi ne ya subuce min, wai na sashi aure bai shirya ba. Meye shirin, bayan suna da kudi, suna da muhalli mai tsabta? Oho! “Me zan ce maka to?” “Ina son ka Muhd. Bello” nayi hamzarin kai tafukana na rufe fuskana cike da matsananciyar kunya, ina girgiza kai alamun “a’ah banda wannan”.
Ji nayi ya matso gabana na kara rudewa, daddadan kamshin shi, kwarjinin shi, jinin mulkin shi da cikar zatin shi sun mani mayafi na runtse ido da karfi, tattausan yatsun shi yasa ya dago habana ya dubeni sosai da murmushi “kada ki tsorata, child, ke ‘yar shilla na ce, Atine, ba abinda zan maki illa RAINO, rainon ki zanyi har sai kin zama kaza, sannan…” ko me ya tuna?
Yayi saurin toshe bakin shi da tafukanshi, ya maida hannuwan shi aljihu, ba zai wuce tunanin Atinen yarinya ce karama kuma ‘yar kauyen su ba, da kyar in ba kara tsoron shi zata ji ba.
A duk sanda yake tare da yarinyar, mance shekarunta yake, rayuwar barikin Jos, ba daya take data kauyen su Karaye ba.
“I am sorry, Atine yi hakuri na tsorata ki wasa nake maki, kai dan Jos!” Muhammad ya shigo “mu je ko?” “ Ina fatan an sayi bakin? Atine me zaki bani in kai tsaraba Bukuru wa Inna na?”
Na dube shi a sanyaye “bani da komi Muhd. sai daddawa da muke yi da KALWAR Baban mu, sai kuma citta, masoro, kanimfari, citta mai kwaya, borkono da zogale. Ban sani ba ko Innar ka zata so?”
“Sosai kuwa, don Innata bata girki sai da kayan kamshinnan da kika ambata, hakanan ma’abociyar cin zogale ce da yin miyar sa, wallahi kin ji na rantse, ko dan Karaye?”
Yayi tsaki ya soma tafiya yana cewa “kai dai surutun ka Muhd.is tooo much…., talkativesoldier, try to remember alwayz Atine is too young!”
Na juya ina kunkuni na shiga dakin Amarya “kai ni Amarya yau Allah ya hada ni da mai kwadayin tsiya, wai lallai sai na bashi tsaraba, gashi gallele ko mai zai yi da ‘yan shirgin kauyen mu oho, yanzu haka ma zubdawa zai yi a lambatu” tace “ke kuma marowaciya ba, da mai rowa ai gwara mai kwadayi, da kyar ma in akwai masoron ke dai hada ki bashi, son ki fa suke, mai son ka kuwa ai ya gama maka komi. Ko ya dauka, ko ya zubar, ruwan sa.”
Ina jin tashin motar su na kinkimo jaka na nufi dakin Goggo, Goggo tayi murmushi, “har an soma cafko toshi” nayi dariya “ni ban ma iya budewa ba, bari Sani ya shigo” dan halak din ban rufe bakina ba najiyo gyaran muryar shi yana surutun su na ‘yan bal, ya shigo yace
“eye, Afiruwar yarinyar nan da farin goshi take, a’ah su Afiruwa yau an aje tarihi” Goggo ta kwada mai maficinta yana dariya yayi kici-kicin kauyancin sa shima da kyar ya bude, har wani karfen da ake turawa gareta, ga tayoyi kanana sai kace wata mota, (trolley), turamen atamfofi ne Ingila sunan ta inji Goggo, har turame uku, sai wasu irin dogayen riguna masu kyau baka, ruwan hanta da ruwan hoda da aka yi su da wani irin yadi mai santsi, daya hula ce makale ragowar biyun mayafai ne da su, sai wasu lesussuka masu taushi da daga ganin su zaka kimanta tsadarsu, kore kalar lemun tsami da aka yiwa yarfen fararen fulawoyi da ja mai rastin baki, takalma kafa biyu marassa dunduniya hade suke da jakunkunan su masu dan banzan kyau, sai manyan turaruka ban san abinda yake rubuce jiki ba, na zare wasikar da wani sukunbiyan abu kamar littafi wanda na fahimci hotuna ne aciki.
Ban bari Sani ya buda su gaban Goggo ba don kunyar ta nake ji. A yau har da takardun kudi, bamu kirga ba, nace bazan taba komi a ciki ba, tun da Baba ya hana, ba mu san abinda yake hangowa ba, sai hotunan sai takardar.
Can uwar dakin Amarya na shige, duk suna tsakar gida suna hira. Tun jiya na lura Atika bata gidan, Inna tace wai ta tafi gidan kanwarta Tani data haihu, haihuwar fari, sai bayan arba’in zata dawo.
Ni kan daga ji nasan karya ne, me Atika zata yi wa mai haihuwar fari? Oho su suka sani.
Na bude abin nan mai kama da littafi (album) ba komi bane ciki sai hotuna, da alama babu wanda aka dauka cikin Karaye sai ko can wajen karshe tare da Muhammad a fadar Maimartaba Sarkin Karaye. Ya tura zungureriyar wasikar a can kasan hotunan, komi ya fito hannun Bello kamshi daya yake yi, na rasa dalili.
Na fiddo takardar na rika jujjuyata a hannuna cike da matukar son sanin abinda ta kunsa. A yau ne na yi dakacen inama na je makarantar boko, dafa wai na karanta kyawawan rubutun da ke cikin takardar nan na fahimta, shine yace in ba Awal ya karanta mani? Ba zan bashin ba, illa in bi Awal din ya koya min har na iya kana in karanta da kaina.
Na farke wasikar, doguwar takarda ce da aka yarfawa rubutun gwanaye a fannin boko. Na cigaba da juyata a hannu na gaban ta da bayanta. Shin me ya hana Baba sanyamu makarantar nan ne don Allah? Idona ya ciko taf da kwallah.
Na tattara na boye, na koma dakin Goggo na kwanta lamo, a bayan ta, naji jikin ta zafi rau. Nace “Goggo jikin ki zafi” “to ya zan yi Atine? Jiki da jini ai dole ne”.
Tayi shiru, zuwa can tace “Atine na yi wa Allah godiya ina kan yi masa ma, daya hadaki da miji irin wanda nake maki addu’ar samu tun zuwanki duniya.
Wato miji nagari mai kaunar ki tsakani da Allah, don in da ba don kauna ta tsakani da Allah ba, babu yadda za’ayi Bello ya zo gareki. Sai dai tun daren da na fara samun sauki, nayi maki istikhara ta kwarai, abinda na gani wai mijin ki yana nesa, gashi kuma naga Bello da gaske yake.
Allah shine masanin gaibu, don zancen nan da nike maki yanzu Waziri na shirin turawa Maimartaba zancen aure, duk da nauyin shi da ya ke ji na kin amincewar Bello auren Fatima diyar Maimartaba.
Abinda nake so da ke, Atine kada ki bari wata baraka ta bullo daga gareki, domin yanzu mahassada sun saki gaba. Dama auren irin su Bello sai mai gagarumar sa’a, kuma jaruma.
Ki zama jaruma Atine ki jure rayuwar duk da kika tsinci kanki a gaba, mai dadi ko akasi. Ina ji ajikina, rayuwar ki Atine mai wahala ce daga farko mai dadi ce daga karshe.
Atine cikin ko wane irin hali, kada ki butulcewa ATIKA, kada ki gujeta, kuma kada ki cuceta. Atine rayuwar talaka gabadaya cikin wahala take. Cikin ko wacce irin daukaka da kika samu kanki a duniya kada ki boye Babanki MAI-KALWA NE.
Da arzikin kalwar kika ci, kika rayu har kika kawo matsayin duk da kike. Kada ki taba barin abinda zaki iya yau, ki ce sai gobe, hakan shi ke kawo da rabon wani. Yau naki ne, gobe na wanin ki ne.
A duk abinda zaki yi Atine, ki zama mai karfi kuma mai gaskiya.
Gaskiya da karfi, sune kyawawan sutturar TALAKA. Kada ki karbi alfarma, sai dai taimako a inda ya dace. Ki guji duk wani abu da zai saki jin kunyar mutane, gara ki mutu da ki bar ABIN KUNYA.
Ki zama mace tagari a gidan aure, wadda zata taimakawa mijin ta da karfin ta, lafiyar ta da aljihun ta koda yana da shi. Sirrin ‘ya mace a gidan aure sune girki, kyakkyawan raino, tsafta da kame kai. Atine ki kula da kanki. Kwanta kiyi barci, Allah ya bamu alkhairi”.
To amma na kasa barcin, illa kara mannewa jikinta. Maganganun ta ke yawo da juyi a kwanyata sai tsakar dare kan in samu barci yayi awon gaba da ni.
Na farka ana kiran sallar Asubahi na tashi Goggo ta mike, muka zaga mukayi alwallah muka tadda jam’I a dakin Baba. Tun dai raka’ar farko Goggo bata dago ba, na kaddara hakan da addu’a takeyi doguwa. Har muka sallame ba wanda ya kula, domin dai ta saba nisan kiwo a sujjada.
Gari ya soma wayewa alfijir ya keto Goggo na duke cikin sujjadar ta. Amarya ce ta sha jinin jikin ta, ba lafiya ba, domin Goggo raka’a daya tayi, yaya za’ai ta katse jam’I haka kawai?
Sai ta kai hannu ta dafa Goggo, kamar jira take wani abu ya shafeta, sai ta kwanto sharaf, tsakiyar dakin.
Ban taba ganin mutuwa ba, amma kallo daya na yiwa Goggo a yau nasan Goggo na, ta amsa kiran mahaliccin ta.
*****












K
wanaki uku muna amsar ta’aziyyar Goggo, a kullum ka’ida ne sai ankawo abinci lafiyayye cikin fanteku safe, rana da dare daga gidan Waziri. Tun ranar rasuwar da Waziri a ka yiwa Goggo Sallah. Matanshi da ‘ya’yan shi duka masu aure da marassa aure kwansu da kwarkwatarsu sun zo mana ta’aziyya dukkansu sukan ce,
Bello yace a isar da sakon ta’aziyyar shi, yana zana jarrabawar karshe ne daya kare zai zo.
Bayan share makoki da kwana biyar muka ga Inna na sauke kwallayen ta da bamba, almajirai na fita mata da su, duk matan gidan ita kadai ce mai jere. Tace da Baba wai bikin diyar aminiyar ta Jummai ne ya tashi zata yi mata gudunmuwa.
Inna sarkin rowa, da ko auren kanwarta da suke ciki daya, Tani, bata bada ko sisi ba ita ce mai sauke kwallaye domin auren ‘yar aminiya, shikan Baba mun lura kwanan nan wani ‘yar tsoro ne tsakanin shi da Inna, komi ta fadi, jiki na rawa zai amsa. Wani abin mamaki har akayi rasuwar nan aka share makoki babu Atika, ba labarin ta amma ban ji Baba ya ce komi ba.
Kwanaki biyu bayan haka ta kulle dakinta ta tafi, bata ko ce mana ga ranar da take sa ran dawowa ba.

Auwal ya shiga shekarar shi ta karshe a sakandire, shi kuma Sani dama tuni ya daina, Rabi’u ya shiga babbar sakandire aji daya. Auwal yazo ya gayawa Baba ance duk mai son shiga jami’a, dole sai ya sayi wani fom waishi (Jamb) ya cike naira dubu da dari biyar. Hankalin Baba ya tashi ainun, ko jarin kalwar gabadaya za’a hada bai fi na naira dubu biyu ba, gashi yana son Awal da karatun nan kwarai da gaske, don ba karamar amfana muke da shi ba, ko wasika aka kawowa dayan mu shi ne mai karantawa, shine mai fadin tsarin shan magani yadda likita ya fadi.
Rashin lafiyar Goggo da kaita asibitin birni, Auwal ne ya yi wa likita bayanin abinda ke damun Goggo kasancewar shi Bayerabe. Haka a asibitin larabawan da Bello ya maida su duka Awwal ke fadawa Sisters (malaman asibiti) abinda Goggo ke cewa.
Na kawo shawarar a fidda sauran kayan kullin Goggo kasuwa a saida tunda tun bayan rasuwar ta babu wanda ya kara zuwa siya. Baba ya yarda da shawarata can kuma yayi tunani ya ce kaya na magadane, rabawa za’ayi a basu, Allah ne gatan mu, ya kuma dogara gareshi yasan bazai bar shi ya tabe ba.
A satin su Inna suka dawo a tare, kai da ganin su kasan cike suke da farin cikin wani abu, Atika ta daina kulamu kwata-kwata abinda zamu ci wannan kansa nema yake ya gagaremu, domin kasuwar kalwa ta kara wulakanta a dai-dai wannan lokacin da kan jama’ar karkara ke kara wayewa da sana’o’I masu gwabi. Da shiga birane

Please Login or Register in order to submit comment