Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kare da yi mun tsaki da juyan baya.
Duk wani kyale-kyale na, bai burge shi. Duk gyare-gyaren da nake, ban gamsar da shi. Sabida Allah Mansina ina zan iya jure wannan rayuwar wulakanta kai? Ya tafi nima in tafi, ba mai neman wani, ba so balle kauna ginshikin aure?
Da haushi ya ishe ni kwanaki, dan cikin da naga yana ta bare-bare akan sa na je aka kifar da shege, tunda na gane Akuya ya maida ni, in ta zubo masa ‘ya’ya su yana kaunarsu ni ce banza.
Da nayi masa karyar ya zube, sai cewa yayi Musulunci na akwai question mark (?), gorin so kala-kala ni dai wallahi na gaji. Ba don har yanzu ina son shi ba, wallahi da tuni na kama gabana.
Duk abinda Ubana yayi masa, bai gani ba, ya manta, da bazar Uban wa ya ke rawa, bada ta Ubana ba? Idan yau nace ya bar kujerar sa, wallahi ta zauna. Don dama shekarunsa basu kai ba, Babanane ya shiga ya fita ya sa shugaban kasa ya bashi ita.
Duk son da nake mishi nasan baya mun rabin-rabinsa. Sai dai ina ji a jikina Mansina, bazan iya rabuwa da shi ba. Shikadai ne a duk mazan da nayi hurda dasu kamin nayi aure, da zai kusance ni in san da namiji ne daya san menene soyayyah?”
Ta karashe fadin maganar cikin murya mai ban tausayi.
Tsaki Mansina tayi sabida haushin da ta bata tace
“kina amfani da kayan Indonesian da nake kawo maki kuwa?”
“Har na Uwar Indonesia ma, nace maki ko Ohon sa. Ni fa nasan ala tilas yake bari na kwana cikin gidan sa, don bazan ce aure ba”.
Mansina murmushi take tana karawa. Tana kada kai tana kallon ta kamar ta ga dabba,
“ke dai ko a mahaukata ma ina jin ke ta musamman ce, har ban san sunan da ya dace in kira ki cikin jinsin mahaukatan ba. Uban wa yace maki bazai nemi mata ba a irin wannan rayuwar auren da kuke, mai kama da wasan yara?
Dadin dadawa yana turai wata da watanni ba matar aure, shi waliyyi ne koko ba lafiyayye ba?
Tukunnama wannan ‘yar rainon, da kike kira ‘BLACK’, a gidan Uban ki take Black din? Wallahi in ba kiyi wasa ba sai ta AURE TAHEER. Akwai wani sirrin kyawun ‘ya mace tattare da ita, wanda zai tunkudo, nan da ‘yan shekaru.
Irin wadannan matan Alkyabba ne ga mazajen su.Ki dubi zubin jikin ta, gashin kanta, fatar ta da wankakkun kafafunta, wallahi tana samun gyara da kulawa, wanda yafi karfin na ‘YAR RAINO.
Ki zauna ki bincika, shin meke faruwa cikin gidan aurenki? Sakacinci da wautarki sunyi yawa Mubina. Ta yaya tana kula da yaron da YAKE SO FIYE DA KOWA ki ce zai banzatar da ita?
Ke akan me ya banzatar da ke??? Zauna a hankali ki nutsu kiyi tunani. Ba wani abu bane sai Don kin kasa zama ki rainon mishi Jawad! Kin kasa zama ki goya mishi Jawad!! Kin kasa zama ki ba Jawad abinci!!! Na gaya maki, na kara gaya maki “MAI DA WAWA NE, IN DA AKE SON DAN SHI A NAN YAKE!”
“Haba-haba Mansina! Yadda nasan Taheer da kyama, ba abinda zai ci da ‘yar kauye kuma Jahila, shi da bai ko zaman awa guda da Jahili”.
Mansina ta fara kuluwa tace “’yar kauye kikace ko? Shi daga ina ya fito? Ko shi ba dan kauyen bane tunda dan Sarki ne? Jahila, baza a iya kaita makaranta ba? Na gaya maki, na kara gaya maki wannan”.
Tayi shiru, zuwa can tace
“kin ce kin gaji da auren Taheer, wallahi kikayi saken da ya sake ki, ko wanda ya kama yatsar shi bazaki samu ba.
Ba kya a jerin irin matan da mazan yanzu ke so Mubina (I’m sorry very sorry) ba cin fuskarki nake ba. Gaskiya ce tsurarta wadda a wannan zamanin dai ba kowane abokin arziki ne zai gaya maka ita ba, musamman in hannun ka da maiko kamar naki, sai dai ya dulmiyar da ke.
Abotarmu ni da ke ba yau ta faro ba, tun ajin farko a sakandire kuma tun a wancan lokacin har zuwa yau, ban huta da gaya miki gaskiya ba sabida halin ki babu mai iya jureshi sai mai hakuri, hakurin ma no.1.ba zaki samu miji irin ko kamar naki ba, da kin yi saken da ya kubuce miki. Ba nan cikin Abuja kadai ba har Nijeriya gabadaya.
A kamanni da dirin halittarki dai. Kin san in banda kaddara da rabo, Taheer bazai taba auren mummuna kamar ki ba.
Kin haifi Da, amma kowa yace Allah yai masa gyadar dogo da bai dauko uwar sa ba. Kin ce zaki iya sa Taheer ya bar kujerar shi, to sauran connections din shi da kasashen ketare fa? Baban ki nada hannun sama masa shi?
Ban taba sanin Mubina ke gaula ba ce wallahi sai yau. Tukunnama wa ya ce da ke abinda ya dogara da shi ke nan?
Kina auren mutum baki ma san hakikanin wanene shi ba, baki ma san hakikanin sana’ar sa, sai dai a zo a gaya maki daga waje, wannan ballagazanci har ina?.
To bari in gaya maki abinda baki sani ba, in gaya maki TAHEER din da har yau baki san komi a kan shi ba. Yanzu haka ya zuba manyan hannun jari a manyan kamfanoni uku a turai. Daya a kamfanin sarrafa takalma na (AndreValentino) dake Rome (Italy), daya a kamfanin sarrafa tangarayen zamani masu daraja (Crystals) dake Washington D.C, daya a kamfanin sittiru da kayan shafa dake Lisbon din Portugal.

Kina tambayar me Taheer ke yo wa a Canadan da kika ki zuwa ‘yan kwanakin nan?
Kamfanin shi na kashin kansa na sakar carpet din zamani yake budewa, zancen da nake yi maki yanzu, har sun shigo mana nan Nijeriya da wasu sabbin salon ‘rounded, squared da triangular center carpets’ da ake rububi a halin yanzu.
Duk abubuwanda kika lissafo Taheer da su a matsayin mai laifi a gareki, banga laifin shi ba ko daya, sai naki Mubina.
Maganar gaskiya, idan zaka hango kuskuren da wani yayi maka, ka fara tunanin kai me kayi masa da har ya janyo hakan? Ba ka maida naka tudu ka hango nashi ba.
A gaskiyance baki da lokacin shi, baki da lokacin Dan ki daya nuna maki yafi komi muhimmanci a gare shi, maimakon kiyi amfani da damar hakan da kika samu, ki nemawa kanki matsuguni, kiyi ta haifar ‘ya’yan har su sayo maki kaunar da kike tababar baya yi miki, a’ah sai kika tsaya rudin duniya da akidun nasara da kika ara kika yafa suka zama jagoran ki, wadanda a zahiri ya nuna maki sune yake kyama ba ke ba.
Baki bashi kulawar mata ga miji balle girma da darajar da Allah ya baiwa maza akan matansu. Ke dai kullum ke ce a sama, ke ce kika san rayuwa, shi bai waye ba. Ba ajinki bane, kin fishi, tunda Ubanki shine Ubangidan sa.
In banda karya da homa baki iya komi ba.
Kowa yasan Taheer yana hakuri dake ne kawai sabida darajar mahaifin ki, amma ba don tsoron ki ba kamar yadda kike tsammani.
Kuma wallahi komi ya faru da auren ki nan gaba idan har baki canza takun rayuwar ki ba, kada kiyi kuka da kowa, kiyi da kanki. Ki iya bakin ki Mubina, a yanzu Taheer zai iya sayen Alhajin ku da aikin sa cikin Aso Rock(presidential villa). Idan kin so ki kama auren ki, ki makalewa mijinki, ki sauke wannan jin kan naki, ki rage wannan zafin neman, banga abin da kike samu a Omega Bank, wanda mijin ki bai mallaka maki ba”.

Anti Mubina ciki ya duri ruwa, “yanzu ke don Allah Mansina ina ki kaji sirrin Taheer? Zan iya rantse maki, tunda muke dashi yau shekaru hudu, bai taba budar baki ya gaya min wani abu da ya shafeshi ba. Illa ni aiki zani kasa kaza, wuri kaza sai rana kaza zan dawo”
“a to! kin nuns kina son sani ne? Ni dai na gaya maki ki rungumi aurenki, da mijinki, a friendin need is the one who will tell you when your face is looking dirty.”
Jin sun yi shiru nayi sallama, da kyar Mansinar ta amsa na sauke Jawad, a gaban su. Ya kallesu tamkar yagaabin tsoro da kyama, ya rabe a bayana, ta taso zata daukeshi, ni kuma na mike na nufi kofa, yako biyoni a guje “Momi-Momi” ya makalkale ni yana haki kamar wanda ya ga mala’ikan daukar rai.
Na tsaya a sandare don tsoro, yau naga yaro mai manta uwarsa na ce “Mominka ce, ni bani bace” a fusace ta zo ta figeshi ya kuwa gartsa mata cizo a wuya ta cira hannu ta dauke shi da mari, kau!
Yayi taga-taga ya fado jikin Mansina, ta nemi kwayar idon Jawad, babu, itama kanta ta tsorata. Dai-dai lokacin da mai Dan, ya yi sallama, cikin Suit-Spanish.
Ya isa gareta ya daga dan shi, ba motsi. “What's the matter?” Shine tambayarsa. Na sa kai na fice, na shige dakina, na tura kofar na fada rub da ciki tsakiyar gadona na soma kuka mai tsanani.
Idan yaron nan ya mutu, bana tausaya ma kaina tamkar Babanshi. Da ya maida shi farin cikinshi abin ganinshi ya ji dadi. Bar ta ni, mai komawa KARAYE, ba wannan ne abin damuwar ba. Tunda ko da Jawad, ko babu, tilas wata rana zan koma gida.
Abin damuwar shine kaunar Jawad, da tabi bargo da tsokar jikina. Nayi ta kuka har idona suka kumbura. Ji nayi an turo kofar, dauke yake da Jawad a kafadunshi.
Shi kuma yaron, nata faman tura kit-kat a bakinshi. Tun daga bakin kofa ya saukeshi ya rugo aguje yana kiran “Momi na!” na bude dukkan hannuwa na ya shige na mayar na rufe, hawayen dadi ne suka ziraro mani suna diga gadon bayanshi.
“Shoprite muka je, kin gani Daddy na ya sai min kit-kat, ke kuma ya sayo miki 'ribbon”. Ya zaro tafkeken hair-bound cikin aljihun wandonshi, kalarshi 'brown'. Shi yana son kala 'brown' yawanci komi da zai saiwa Jawad, brown ne, nima hakan.
Na amsa cike da murmushi “to kaje kace ma Daddy, na gode”. Ya ruga ya rikeshi “Momina ta ce thank u Daddy”. Ban san me ya rada mai ba, sai ya dawo ya dare ni, ya karbi ribbon din a hannuna, ya zare kallabina, ya hada jelunan siraran kitso (Jennifer Lopez) dake kaina, ya zurasu cikin ribbon din, ya maida min dankwali na.
Ya rada mani cikin kunnuwana, “Daddy ya ce za’a baki 'thank u daddy'.
Na kyalkyale da dariya “mene ne kuma thank u Daddy?”
“Ba ke ki ka fada ba dazun?” Ya maida duba ga Uban a shagwabe
“Dad! Amma ba za'a bawa wannan matar ta can dakin ba ko? Bana sonta! Dazu baka nan ta dalla min mari, wai don kawai naki ta daukeni, ko Momi na ai kina gani ko?”
Na sunkuyar da kai bance komi ba “ki amsa masa ZUBAIDAH, anything it's, yaro bayason yayi tambaya ba'a amsa ba”.
Sai na dago a hankali na dubi Jawad da dukkan idanu, cikin murya mai nuna kashedi da tsananin tsoratarwa ga yaro karami.
“A'ah, za'a bata, itama 'Momin ka ce' ita ta haifeka ni na raineka ni 'second Mumminka’ ce. Jawad, kai ne ka cije ta ka yi rashin kunya, ba'a cizon babba. Daddyn ka yace “idan kayi wa babba rashin kunya, bazai kai ka 'Military School' ba (bazai kai ka Soja ba)”.
Sai ya kwanto a kirji na, yana wasa da sarkar wuya na. Bai ce komi ba. Abban shi yayi mana sai da safe ya juyayi ya fita, ya ja mana kofar.


Mu karasa a 2.
-Takori
Disamba, 2016



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment