Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinsu.... A dai-dai wannan lokaci ne Abbu ya futo daga gida yana sanye da fararan kaya kar dasu wandon shi ya d'angale sosai kana ya taje gemun shi hannunsa guda rike da dadduma d'aya hannun kuma yana rike da asuwakinsa. Cikin nutsuwa ya fara dube-dube daga inda yake jin tashin kid'an, can kan hanya ne a nutse ya fara tafiya yana tur da dab'iar matasan wato ko wane musulmi ya niyyata ga zuwa massalaci domin ya samu rabo a duniya da lahira amma su sun kunna kida sun cika unguwa babu maganar suje massalaci su bi jam'i babban abunda ya 'bata masa rai kuwa shine ganin da yayi yara mata da iyayen su duk sun le'ko waje suna kallo don rashin hankali wasu ma babu mayafai a jikinsu.


Sai da tazo daf da shagon Mubson ya fahimci a ciki kid'an yake tashi ji yayi kamar ya to she kunnen sa saboda yanda kid'an yake masa k'irjinsa har amsawa yake yi, kallon kofar shagon yayi yaga yara 'kananu masu shirin zuwa massalaci da Wanda ma basu shirya ba sunyi cincurindo a kofar shagon. Takaici ya kamashi ya rasa wane shaid'anin yaro ne a cikinsu ya tsiro da wannan shirme Dole yayi wani Abu akan al'amarin wucewa yayi da sauri domin tsayuwar shi a gurin yanzu bata da amfani dole idan an sakko ya tsaya ya tsawatar musu ko da zasu jefe shi ne.



Yana 'kokarin tsallaka titi ita ma tana 'kokarim tsallakowa a take ta shiga hankalinta ta dai-dai ta nutsuwar ta, ta tsallaka a nutse tace"Abbu na dawo." Fuskarshi babu alamun wasa yace." Masha Allah kiyi maza ki wuce gida kinji ko kada ki kuskura ki tsaya gurin kid'an can idan kika tsaya sai na 'bata miki rai."


Kanta a 'kasa tace"To Abbu sai ka dawo." Gaba tayi tana waiwayen shi har ya tsallaka titi taga yana 'kokarin shigewa massalaci sannan ta wuce zuciyarta cike da so da kaunar mahaifin nata.



Sai da ta shigo layin nasu sosai ta fara jin sautin kid'an na shiga jikinta muryar shi na 'kara tashi cikin *Wa'kar shi ta Kwalelen Ku* Hanifa ta dinga jin wani iri a jikinta tsigar jikinta ta fara mi'kewa sosai take jin dad'i wak'ar da yanayin muryar mawa'kin mai dadin sauraro.

Inda tafa wasu mata sun tsatstsaya suna hirar mawa'kin itama nan taje ta tsaya tana sauraran su gefe guda kuma tana jin shigar wak'ar jikinta Ita nan wai so take ta 'kare sai ta tafi gida, amma da ta kare sai taji wata ta 'kara shigowa Sam takasa barin gurin ta ma manta da maganar da Abbu yayi mata.




*MASHAHURI!*


_BintuUm@rAbb@le_









*15/12/2019*
[12/16, 9:51 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*






*FREE PEGE*




*5*



*DEDICATED TO:*
*Husaini 80k*



Hanifa ta shagala a gurin sam ta manta da gargad'in da Abbu yayi mata hankalinta da nutsuwar ta duk basa tare da ita suna can sauraron muryar Khalid cikin wa'kar shi mai taken *'Kwalelen Ku* tanan tsaye har aka sauko daga massalaci jama'a suka fara dawowa gidajan su masu shaguna suna bude wa domin cigaba da Sana'oin su, Abbu ta hango daga can nesa gabanta ya yanke ya fad'i! da sauri! Ta shige soron gidan da take tsaye tana zare ido addu'a take yi cikin zuciyarta Allah yasa Abbu bai ganta ba,

Abbu kuwa tun daga nesa ya gane Hanifa da Lokacin da ta shiga cikin gidan da sauri duk a kan idonsa, sosai abun ya bashi mamaki! Tunda yake da Hanifa bai ta'ba yi mata magana ta sa'ba ba sai yau saboda irin tarbiyar da ya bata sosai 'yayan shi suke ganin girman shi da bin umarnin sa, yana wanannan tunanin ya 'karaso gurin.... Abbakar ne ya futo daga shagon yana 'kokarin shiga gidan su Abbu ya dakatar dashi.


Abbakar ya sunkuyar da kansa domin yasan yanzu Abbu din zai cika shi da 'kauli da ba'adi Allah yace." Annabi yace tsaki kawai yake ja cikin zuciyarsa yana fad'in"Mutumin nan d'an sa'ido ne wallahi.


Abbu ya kalli Abbakar a nutse yace." Malam Abubakar yanzu ya dace wannan abunda kuka yi ? Lokacin sallah kowa ya niyyata domin zuwa gaishe da mahallicin sa Ku kuma a lokacin kuka kunna kad'e-kad'e domin kuja ra'ayin al'umma zuwa gare Ku, Wa'iya zubbulah ha'kika shad'ain ya ribace Ku gami da 'kawata muku duniyar ta inda har kuka shagala cikin duniya kuka mance cewa kud'in bayi ne ma'kaskanta gurin ubangiji ku, subahanallahi wa'iya zubullahi! Abbakar yana da kyau Ku gane mecece duniya Ku daina biyewa son zuciyar ku sannan Ku daina biye wa lalatattun abokan da zasu kai Ku su baro ku su hanaku samun rahamar ubangi........."Sai dai idan kaine zaka hana mu mu samu rahama daga ubangijin mu."! Abbu da Abbakar da jamar gurin suka juyo da sauri suna kallon inda suka ji maganar ta futo.


Wani 'karamin romot dake ri'ke a hannunsa ya danna gurin yayi tsit! Sautin 'kidan ya daina tashi.


Yana wata irin tafiya ya 'karaso gurin dasu Abbu suke tsaye ya soka hannunshi guda cikin aljihun wandon dake jikinsa Wanda ya zamana shi ba gajere ba shi ba dogo ba 3Quarter a turance ido cikin ido yake kallon Abbu Wanda shima ya zuba masa nasa idon cike da d'umbun mamakin sa!



Khalid d'in yace." Ina ruwan ka? Me ya dame ka damu da rayuwar mu kai kenan kullum cikin wa'azi da fad'ar Allah yayi hani da abu kaza da abu kaza, kuma irin ku kun fi aikata sa'bon Allah amma sai ku fakaice da Allah don ha'inci."


Guri yayi tsit! Jama'ar da suke gurin suka zubawa Abbu ido Wanda yake jin ina ma 'kasa ta tsage ya shiga ciki ya huta da wannan ba'kin ciki, gefe guda kuma jama'ar gurin mamaki suke yi da ganin ba'kuwar fuskar matashin yaron da yayi tsaye 'kerere a gaban Abbu kamar zai mare shi.


Hanifa dake cikin soro a 'boye ta futo da sauri jin irin 'kus-kus din da jama'ar gurin suke yi ta'ki ta 'kare.


Khalid ya cigaba da cewa''Ya shaik yana da kyau ka kama mutumcin ka tun kafin ya gudu ya barka babu yadda za'ayi ka zuba mana ido ko kuma kace dole ga irin rayuwar da zamu yi, baka ciyar damu sa'anan baka suturtamu don haka baka da hurumin da ka isa kayi wata magana akan mu da rayuwar mu, naji kana wata magana cewar Abbakar ya daina biyewa lalatattun yara kar su lalata shi, ina fatan cewa ba ka manta da abunda ya faru tsakanina da kai a shekarun baya ba,wannan karon na kyaleka amma ka kuskura ka sake min shishshigi cikin al'amura na nayi al'kawarin sai na lalata maka dukanin wani farin ciki da jin dad'i dake dashi a duniyar nan."!


Guri yayi tsit! Kowa yana mamakin rashin kunyar yaron gashi ba d'an unguwa ba d'ai-d'ai kune daga cikin jama'ar gurin suka gane ko d'an gidan wanene suma da sauri suka bar gurin saboda suna jin tsoron kada sunan su ya futo.


Cikin tsananin ba'kin ciki da takaici Hanifa ta 'karaso gurin ta rike hannun Abbu tana kuka tace"Muje gida Abbu."


Abbu da jikinsa yayi sanyi a gurin Saboda ganin yanda jama'a suke nuna shi suna zind'an sa ya 'kara kashe masa jiki domin ya lura sam jama'ar da suke gurin basa ganin laifin yaron sai nashi Saboda kawai yayi hani da aikata 'barna shine suke zind'an sa kamar Wanda ya aikata zina.


Hannun Hanifa ya rike sosai ya kalli Khalid din dake tsaye a Kansu mhar Yanzu hannunsa guda na cikin aljuhu yana yiwa Hanifa wani irin banza kallo, yanzu ya 'kara tabbatar da cewa yarinyar 'yar shi yayi al'kwarin duk sanda mutumin ya 'kara shiga sabgar shi sai ya huce fushinsa akan 'yar tashi domin ya 'kunsa masa ba'kin ciki.



Abbu yace." Yaro kayi a hankali da duniya wallahi zakace na fad'a maka duk abunda kayi sai anyi maka irin shi Allah ya gani ni na futa." Abbu na gama fad'ar maganar shi yaja hannun Hanifa suka bar gurin zucuyoyinsu cike da bakin ciki.

Khalid kuwa bayansu ya bi da 'kaskantacan kallo yaja tsaki kana ya koma ciki shagon Mobson babu abunda ya dame shi

Abbu da Hanifa tafiya kurrum suke yi zuciyoyin su babu dad'i ko kad'an ga wani irin kallo da mutanan unguwar suke musu kamar wasu 'barayi Hanifa ta kar'bi daddumar hannun Abbu ta rike suka shiga cikin gidan.


Ammi na zaune a tsakar gida tana yanka alayyahu taga sun shigo gidan dukanin su fuskar su babu walwala cikin zuciyarta tace babu shakka akwai abunda ya faru.


Mi'kewa tayi a nutse ta bi bayan Abbu da ya shiga d'akin sa, Hanifa kuma ta zauna gurin da Ammi din ta tashi ta cigaba da yanka alayyahun Zuciyar ta na tariyo mata wala'kanci da 'kaskancin da Khalid yayi wa Abbu, zafafan hawaye ne suka fara kwaranyowa daga idanunta, wula'kancin da Abbu yake fuskanta a cikin unguwar nan yayi yawa idan da Abbu zai yarda da shawarar ta da ya amunce sun bar unguwar domin watarana zuciyar ta tana iya bugawa Sam basu da sakewa a unguwa kullum cikin fargaba da rashin sukuni 'bako ma yafi su daraja cikin unguwa yafi so sakewa wai wane irin Abu suka yi wa matane ne?



Tana yankan Alayyahu tana kuka haka Ya Nasir da Hafiz suka yi sallama suka shigo cikin gidan. Ganinta tana kuka ya d'aga hankalin Nasir da sauri ya 'karaso gurin yana fad'in"Autar Ammi menene uhumm? Daina zubar da hawayen nan yana sani fargaba da tashin hankali. "


Ammi ce ta futo daga d'akin Abbu babu yabo babu fallasa tace"Sannu Ku da zuwa yau kun shigo da wuri." Hafiz yace." Wallahi kuwa Ammi da wuri muka taso don a babban masalacin juma'a na gidan sarki muka yi sallahar juma'a."


Ammi tace"Shiyasa mana to Ku shiga ciki Ku huta a kawo muku abunci." Nasiru ya mi'ke tsaye yanayin fuskarsa duk ta sauya ya kalli Ammi d'in a tsanake yace." Ammi me aka yiwa autar ki ne take kuka. "?


Cikin danne ba'kin cikin da take taso mata a zuciya tace" Yanayin rayuwa ne Nasiru yanzu suma suka shigo ita da Abbu cikin b'acin rai abunda da dai kasani yana faruwa a unguwar shine ya 'kara faruwa, Ammi ta kwashe duk abunda ya faru ta fad'a musu.


Nasiru Uban 'yan zuciya yace." Ammi idan ina numfashi a duniyar nan wallahi babu Wanda ya isa ya ci mutumcin Abbu in kyaleshi ba tare da na d'auki mataki a kansa ba, wannan din da ake magana a kanshi komai kud'in ubansa da mukamin sa bai dame ni ba sai na 'bata masa rai a gaban mutane kamar yanda yake kokarin tozarta Abbu a bainar Jama'a shima sai mun had'ashi da hukuma domin duk gagaran sa bai fi 'k'arfin hukuma ba."
Yana gama maganganun ya nufi kofar futa a fusace!


Gyaran muryar Abbu yaji daga cikin d'akin da yake cikin nutsuwa da kamala Abbu yace." Nasiru zo nan..............






*Shin Wanene Khalid kuma wanene mahaifin sa?*

*Wanene Abbu Kuma menene Ala'karshi da Nasiru?*

*Wane Abu ne ya faru tsakanin Abbu da Khalid?*


*MASHAHURI!*

Yanzu aka fara larabarin



*16/12/2019*


_BintuUm@rAbb@le_
[12/17, 12:00 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*




*FREE PEGE*




*DEDICATED TO:*


*HAUWA S ZARI'A*
_Mmn Uswan_
*RAHAMA UMMU FARISA*
_Ladingo 'yar Ilu_
*BILKISU ABDULRAHAMAN*
_Mrs Habib_



*6*





Asalin Abbu d'an jahar gombe ne bafulatani ne usul gaba da baya suna da yawa sosai cikin dangi amma kuma ba a guri daya suke ba duk sun rabo garuruwa wasu aiki ya kaisu wasu naiman kudi ya kaisu amma dai duk da haka suna zumunci a junan su.


Abbu da Dan uwanshi Amadu su biyu mahaifiyar su ta Haifa a gurin Baban su kuwa su Tara ne maza hudu mata biyar matan duk sunyi aure suna gidan mazajan su suna rayuwa mai kyau da kwanciyar hankali Saboda irin tarbiyar da suka samu.


Abbu tunda ya taso yake da tsantsane gami da kula kan addini komai cikin nutsuwa yake yin sa yana ganin ba dai-dai ba zaiyi magana ko da kuwa Wanda ya girme shi ne, aikuwa wannan d'abiar tasa yasa mutanan garin nasu suka sanya masa suna da d'an izala Abbu tun bayason sunan haka ya hak'ura ya rabu dasu suna kiran shi da sunan Dan Izalah sunan Abbu kwata-kwata sai ya 'boya a gari Idan ba kace Munzali d'an Izalah ba to ba a gane wa, Asalin sunan Abbu na Gaskiya shine Munzali a, Yana da shekara ashirin da biyar mahaifin sa ya rasu wata bakwai tsakani mahaifiyar sa ta rasu itama to bayan komai ya lafa ne yayi sallama da sauran 'yan uwanshi ya nufo kano makaranta, ko da ya iso kano babu inda ya dira sai unguwar d'orayi nan ya siyi gida maidaidaci ya zauna shi kadai ya cigaba da rayuwar sa kullum da daddare idan ya dawo daga gurin sa'anar shi zai shiga makaranta Malam Jafar Mahmud Adam ya dauki karatu, bayan an tashi ya koma gida Lokacin akwai waya a gari ya siyi karama Nokia kusan kullum sai ya kira 'yan uwa sun gaisa.
Ko da Abbu ya shiga kasuwa Jama'a sai Ku fara yi masa wani kallo na daban ganin sai ana hira dashi k'arfe sha biyu da rabi nayi ko k'arfe daya zai mike da sauri yaje ya dauro alwala kadan daga cikin mutanan ne masu bin shi jam'i a hankali Abbu ya dinga Jan ra'ayin wasu zuwa gare shi, wasu na ganin mutumcin sa wasu kuwa kullum cikin zaginsa suke suna fadin"D'an Izalah mugun bawa."! Abbu bai ta'ba tanka musu ba idan ya shigo kasuwar dukanin su sai ya bi kowa bakin shagon sa ya gaisa dashi. Sana'ar Abbu itace sai da takalam soso a cikin kasuwar wambai dake jahar kano Alhmdullahi Allah ya sanya masa Albarka sosai yana siyarwa Kuma ya bada sari, take Abbu ya suyi fili maidaidaci a unguwar shagari Quartes cikin hikima da sanin meye rayuwa ya fara ginin shi mai sauki duk da ya fuskanci cewar unguwar akwai masu hannu da shuni wannan bai dame shi ba.


'Kokarin shi yaya za'ayi a sirin shi ya rufo kullum cikin yiwa 'yan uwanshi aike yake alkairi iri-iri babu Wanda baya yi musu katsam! Ya samu labarin rasuwar babbar yarsu da suka mayar a matsayin uwa. Cikin tashin hankali Abbu ya nufi garin nasu na Gombe cike da alhinin rasuwar Addah Halima sosai suke girmama ta saboda karamcin ta a gurinsu

Bayan sadakar bakwai ne Abbu yayi nufin komawa gida wani Kawun su da yayi musu shaura ya tsayar dashi da maganar aure dole abbu yabi umarnin Kawun shi, shi kuma ya fada masa cewar yayi masa mata 'yar gidan Iiman ce Yarinyar sunan ta Halimatu.


Jin cewa yar gidan Liman ce yarinyar kuma sunan su d'aya da Addah Halima sai ya amunce kawai..... Nan Kawu yace." Amma dole zaka yi hakuri domin ba budurwa bace tayi aure wata uku kenan da futowar ta mijinta yayi mata sakin wulakanci shine nake so ka aure ta."


Abbu yace." Na amince Kawu idan tani ne gobe a d'aura aure idan na auri bazawara nayi juhadi kuma na aikata sinna domin manzo Allah (Slw) shima da bazawara ya fara Kawu ina so gobe a d'aura mun aure da ita.


Aikuwa kamar yanda Abbu din ya fad'a haka akayi dake juma'a ce ana saukowa daga massalaci aka d'aura auran Abbu da Halima cikin aminci da yarda juna.


Abbu yace." Baya bukatar komai domin duk abun buk'ata ya zuba a cikin gidan shi kawai zai tafi da matar sa ne kano, haka akayi da zasu tafi Abbu ya umarci Nasiru Dan Addah Halima mai rasuwa cewa ya shirya ya bishi domin ya fara nuna masa harkoki Kuma yana so ya sanya shi makaranta.


Ko da Nasiru ya Sanar da mahaifin sa take ya amunce yayi Abbu fatan alkairi tare da addu'ar Allah ya taya shi rikon Nasiru. Haka suka nufo garin kano cike da kewar 'yan uwansu, mussaman Halima da take tunani irin zaman da zata yi a garin da bana su ba, ita kanta tasan zata sha kadaici

****

Abbu da matar shi Halima suna zama na gaskiya gami da bin dokokin aure kamar yanda Ubangiji ya umarci ma'aurata da suyi sosai Halima take jin dadin zama da Nasiru yaron yana yi mata biyayya sosai a lokacin yana da shekaru tara a duniya Halima ta haifi d'a namiji Abbu ya sanya masa suna da Hafizu komai Abbu yayi ya tsaya tsayin daka akan iyalinsa cikin ikon Allah ya kammala gingin shi, da kanshi ya shiga Sabon gidan nasu yayi saukar al'kurani mai girma kana suka tare a gidan daran juma'a babbar rana.
Farko zaman lafiya ne ya wanzu tsakanin Abbu da ma'kotan sa tsawon shekaru goma kenan Lokacin an haifi Hanifa tana shekaru tara Al'amarin Abbu ya 'kara tsananta akan su babu sakewa a cikin unguwa ita kanta Halima idan wani Abu ya faru cikin ugunwar sai dai taje cikin dare kullum tana cikin k'aton hijab da safa hakama Hanifa kullum ciki hijab kuma duk makarantun da suke zuwa na Ahalil sunnah ne kullum Abbu ya dawo daga kasuwa zai zauna da yamma kofar gidan shi yayi ta karatun LITTAFIN addini Lokacin ne kuma yaran unguwa zasuyi ta nuna shi suna dariya ko Kuma kaji suna tsokanar sa da 'Dan izaha wawa ne jakin banza la'ananne."! Abbu yana jin su bazai ce musu komai ba.

A hankali wasu daga cikin matasan layi suka fara zuwa daukar karatu gurin shi shi kuma yana sake wa dasu ya koyar dasu yanda zasu inganta rayuwar su da addinin su.

Haka Abbu yayi ta hakuri da jama'ar unguwa Lokacin su Nasir da Hafiz suna can Sudan karatu can Abbu ya tura su domin samun ingantaccan ilimin addini don haka basu San abunda yake faruwa ba, sai Hanifa a lokacin babu wayo daga baya kuma da ta fara wayo sosai ta fara jin ciwon abunda akewa mahaifinta to da yake yarinya ce Mara kwarafniya da son hayaniya sai dai kurrum tayi kuka ko kuma ta zauna kusa da mahaifin NATA tana bashi hakuri sai dai yayi murmushi kawai yayi ta nusashe da ita yanayin rayuwa ne.
Wata ranar juma'a da Abbu bazai ta'ba mancewa da ita ba a shafin rayuwar sa shine ya shirya tsaf domin zuwa massalaci juma'a na cikin gari domin yau yana son ya zauna sosai yayi azkar kafin fad'uwar rana shiyasa yake so ya tafi da wuri, Yana sanye da sabon yadinsa toyobo fari tas! Dashi hannusa rike da dadduma ya futo yana gyara hular sa mai raga-raga kamar ta larabawan k'asar saudia hular fara ce kamar yadin jikinsa.

Ammi ta futo daga d'akinta hannunta rike da kwalabar turare mai saukin kudi tazo ta fesa masa a jikinsa da daddumar hannunsa kana tayi masa fatan dawowa lafiya. Abbu yayi mata sallama ya futa daga gidan yanajin 'kaunarta cikin ransa, a nutse yake tafiya har ya 'karasa bakin titi yana jiran abun hawa, Allah bai kawo ba gashi yana gudun lokaci ya kure kar ya rasa sallah sai ya fara tafiya da k'afarsa yana tafiya yana tasbihi cikin zuciyarsa.... Wata motar fara tas! Ta fafaro da gudu daga wani layi dake gaba dasu sosai motar tayo kan Abbu da yake kokarin kauce wa motar gashi gefe da gefan shi ruwa ne a kwance a gurin kasancewar lokacin ne na damuna bai an karaba motar ta tawo da gudu tabi ta cikin kwantaccan ruwan dake gaban shi duk ya 'bata masa jikinsa gabaki d'aya!! Abu yabi jikinsa da Kallo cike da takaici da kyama domin ga warin kwata nan tabbatae cewar ba ruwan sama bane hade yake da ruwan sama, Motar yabi da kallo yana jinjina rashin rad'a da rashin tarbiyar Wanda yake cikin motar! Gani yayi motar ta dawo da baya har zuwa inda yake tsaye, Mintuna biyu tsakani Wanda yake cikin motar ya futo Abbu yabi yaron da kallo cikin mamaki! Ganin da yayi wa yaron take ya 'kiyasta a ransa cewar bai fi sa'an Hafiz ba, A hankali yake tafiya har ya 'karaso kusa da Abbu ya fara watsa masa wani irin kallo na rainin hankali...................













*17/12/2019*



_BintuUm@rAbb@le_
[12/17, 10:31 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*



*FREE PEGE*




*DEDICATED TO:*
*MY MOMYS*

*Momy FATIMA MUSU*
_Nijar_
*Momy INDO AMADU*
_Katsina_


*Ha'kika kun cika iyayen 'kwarai kuna da mutukar girma a gurina wallahi ina alfahari da sanin da nayi muku a rayuwa ta Ubangiji Allah ya saka muku da alkairin sa Allah ya 'kara lafiya da nisan kwana kwanciyar hankali da zaman lafiya, Allah ya albarkaci zuri'arku baki d'aya👏🏻 d'iyar ku tana alfahari daku.*
_______________________



*7*



Abbu ya kalleshi cikin kyakyawan lafazi yace." Haba samari irin wannan tu'kin akwai had'ari a cikinsa, mussaman idan akan titi ne don Allah ka kiyaye ko don gab....."Kaga dakata malam."! Khalid ya katse shi cikin izgili da nuna waye Kai.


Abbu ya bishi da kallo cike da mamaki! Khalid ya cigaba da cewa"Babu babban shashasha irin ka! Ya za'ayi kana ganin mota tundaga nesa baza ka kauce ba sai ka tsaya kalle-kalle don tsabar kidahumanci da 'kauyanci irin naku kawai ka tsaya kan hanya sai kace hanyar ka kai kad'ai."!


Abbu yayi shiru yana mamakin halin da d'abiar 'yayan wasu masu kud'in Sam basu da tarbiyya tabbas ba sai an fad'a ga alamu nan sun nuna yaron D'an gata ne ko ga yanayin suttuarar jikinsa da ita kanta motar da yake ciki.


Tsaki! Khalid yaja ya juya zai tafi Abbu yace." Yaro wannan abunda kayi min a yanzu ya nuna min cewar baka San darajar iyayen ka ba kuma tabbas tarbiyya bata isheka ba, ko ban haife ka ina da kamar ka ya cancanci kayi min haka? Duba fa kaga yanda ka 'bata min jiki da gur'bataccan ruwa."



Khalid ya juyo da sauri yana watsa masa kallon raini yace." Ka haife ni ne."!? Abbu yaji maganar wata iri shiru yayi yana binshi da kallo, Khalid din ya cigaba da cewa"Idan kana jin ciwo da takaicin abunda nayi maka kazo ka rama idan kuma baka rama ba ni zan rama."


Abbu bai fahimci

1 Comments On MASHAHURI
avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

39901

Please Login or Register in order to submit comment