Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dinga fad'uwa da sauri ta lumshe idonta had'e da rungume pastar 'kam a k'irjinta tana sakin wata irin zazzafar ajiyar zuciya!

Motsin shigowa taji da sauri ta bude idonta ta cire pastar hade da nannad'e ta mayar cikin jaka. Muryar Abbu taji yana kiranta, amsawa tayi ta mike da sauri ta futo daga dakin.... Kafin ta zauna yace." Maza dauko jakar makarantar ki muyi karatu kafin lokacin sallahr Isha'i."

Jiki babu k'wari ta koma dakin, kici-kicin cire pastar take yi ta jawo da sauri aikuwa keeeeeeee! ta yage taji kamar ta kurma ihu! Dai-dai fuskar sa ne ya yage. Tsayuwa tayi tana gyarawa zuciyar ta duk babu dad'i tama manta da Abbu dake jiranta sa sai da taji muryar shi yana fad'in "Tsayuwar me kike yi ne Hanifaaa."! Sannan ta dawo nutsuwar ta tayi saurin cure pastar guri guda ta jefe gefan gado yanda da tq zura hannunta zata iya dauko wa.

da sauri ta futa daga dakin Abbu yabi ta da kallo a nutse yace." Tsayuwar me kikayi."?

Shiru tayi tana sinne kai gyada kansa yayi tare da fadin"Zauna ki futo mun da littafan."

Zama tayi ta futo dasu danginsu Balaga ishmawi Minhajin musulum, Abbu yace." Bude ki fara karanta min."


A nutse ta bude littafin balaga ta fara karanta masa yana saurara idan ya samu gurin da tayi ba dai-dai ba ya gyara mata.

Haka har lokacin sallahr isha yayi Abbu yaje massalaci ya dawo su ka d'ora da karatun alk'urani sosai abbu yayi tayi mata ganin duk wasu ayoyin na cikin suratun bakara tayi kuskure wanda ada ko zai tuna mata guri kadan ne.

Yace." Wato yanzu kin daina tilawa ko ganin bana sanya ki a gabana duk lefin ba na kowa bane na Ammi ki ne a ranar Ammi sai da tasha fada gurin Abbu a cewar sa duk laifin ta, Hanifa in banda kuka babu abunda take yi Ammi kam hakuri take bashi su Nasir suna taya ta da kyar Abbu ya hak'ura sannan suka fara cin abunci Wanda ita Hanifar ji take kamar tana cin magani don dai tana jin tsoron fad'an Abbu ne da tashi zata yi baza taci abincin ba.



****

Jirgin safe Khalid ya biyo don haka 11:00 dai-dai yana gida Mamy tayi masa kyakyawar tar'ba sai lallabashi take yi shi kuma yana shagwabe wa dama d'abi'ar shi idan yana gaban iyayen shi yayi ta shagwaba yana sangarta, ya gama da mamy Kai tsaye part d'insa ya nufa cikin gajiya ya shiga toilet wanka kawai yake so yayi kafin ya kwanta ya huta zuwa 2:00 na rana wayoyinshi ma duk ya kashe su saboda jama'ar da suke takura mishi da kira hakanan kafin ya tawo sai da wani abokin ango ya nemi da yayi wa 'k'anwar shi wa'ka ta aure wacce za'ayi bukinta a sabuwar shekara me kamawa. Bayan shi kuma wani alhaji ya nemi da yayiwa 'yar shi 'yar auta wa'ka shima dai a sabuwar shekarar yake so saboda first January take cika shakaru bakwai ranar kuma zasu yi mata birthday, donshi Alhaji ma har ya tura masa ma'kudan kudi cikin accont d'insa Wanda Sam bai so hakan ba yasan Tajo ne zai bada numbar accont dinshi har kullum yana fad'a cewar wa'ka yanayin ta ne ba don kudi ba sai don ra'ayi kawai.



***

Yau alhamis babu makaranta Hanifa na kuryar daki akwance kan gadon Ammi ta rungume hoton Khalid a k'irjinta tana tunanin yaya za'ayi ta futa daga gidan domin Abbu ya san babu makaranta kuma bays Bari ta futa.

Ammi ta shigo cikin dakin zata dauki Abu dake babu wuta kuma dakin yana da duhu Ammi ta fara Neman fitila zata kunna Hanifa tayi saurin boye hotonta ta mike zaune tana shagwaba fuska tace"Ammi don Allah zanje gidan su Asalamiyya kinji."






*24/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/24, 9:14 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*



*FREE PEGE*


*21*



Ammi ta d'ago kanta tana kallonta kafin tace"Kin san dai Abbu yana gida ko."? Gyada kai tayi Ammi ta cigaba da cewa "To ki rufa min asiri ki hak'ura da zuwa gidanan domin kina gani jiya akan ki sai da yayi min fada abunda bai ta'ba faruwa ba Hanifa don Allah kiyi 'kokarin kiyi masa biyayya kamar yanda yake so, dukanin abunda ya umarce ki kiyi masa gaba zaki ci riba."


K'walla ce ta fara taruwa a idonta tace"Ammi bafa zama zanyi ba zan 'karb'o littafin nahahu ne a gurin Zan duba domin mun kusa fara jarrabawa." Ammi tace"Ke ina naki da sai kin tafi yawon aro."

Cikin 'kosawa tace"Nifa Ammi ba aro zanyi ba nawa ne zan 'karbo itama Asalamiyya a gurina take ara, kuma Ammi sai ki dinga cewa nayi biyayya ga abbu ni fa nasan inayin iya iyawa ta Amma Abbu tsaurin sa yayi yawa a kaina."

Ammi ta bude baki cike da dumbun mamaki take kallon Hanifa kafin tace"Abbu din kike fadawa wannan maganar Hanifa."?


Zumb'ura bakinta tayi tana bubbuga 'kafafu a kasa kamar yanda ta saba ta fashe da kuka Wanda dama kiris take jira."

Da sauri Ammi ta futa daga dakin tana mamakin Hanifa da sababbin halayen data tsuro dasu, aiki take tana addu'ar Allahu ubangiji ya shirya mata ita shirin addinin musulunci.


Abbu ne ya futo tsaf dashi yana sanye da da wani farin yadi mai sauki kudi anyi masa dinki dai-dai misali kanshi da hular shi wacce ya saba sawa itama fara tas k'amshin turare yake yi dai-dai ya tsaya kofar kicin din tare da fadin "Ammi ni zan wuce cikin gari gurin d'aurin auran 'yar gidan Rufa'i Wanda za'ayi shi massalaci malam jafar dake gadon 'kaya misalin k'arfe biyu na rana."

Ammi tace"Af wallahi shaf na manta da Yau ne to Abbu Allah ya kiyaye hanya ace muna yi musu Allah ya sanya alkairi. " Abbu na kokarin futa yace." Insha Allah za'a fada masu, Ammi ta juya ta cigaba da aikinta


Hanifa dake daki a zaune taji lokacin da Abbu ya futa don ha sai ta mike da sauri ta zura hijab dinta dama duguwar rigace a jikinta irin cotton din nam don wani sa'in ma da ita take bacci saboda yanda rigar ta matse mata jiki. Ammi na can ns aiki ta fuce daga gidan.


Abbu kuwa Tun kafin ya futa babban titi yara suk masa d'an kira suna le'kensa har da masu ma'kale murya suna fad'in "D'an izalah mugun bawa."!! Duk yana jinsu idan da sabo ya saba da wannan d'abi'ar tashi babban abunda ya fi dauke masa hankali shine duk inda ya kalla gabas kudu yamma arewa sai yaga hoton Mara kunyar yaron nan 'yan unguwa sun manna ajikin gidajasu da shagunan su sosai abun ya bashi mamaki girgiza kansa yayi yana yi musu fatan shiri a cewar sa duk Wannan abunda suke bidi'a ce domin aje suffar mutum haramun ne kuma Annabi ba yaso shiyasa gidashi ko tv babu balle wani hoto haka ya futa titi yana zancan zuciya da nemawa yaran unguwarshi shiriya daga gurin ubangiji.

***

Kai tsaye gidan su Asalamiyya ta nufa tana tafiya tana zancan zuci ta Riga ta gama yanke shawara akan abunda zuciyarta take bujoro mata dashi tana ganin hakan shine mafuta a rayuwar ta.

Tana shiga soron gidansu Asalamiyya ta fara jiyo maganganu na tashi da sunan ta, fasa shiga tayi ta rabe jikin bango tana sauraron su, inda taji Umman su Asalamiyya na cewa"Ai nace ni da kaina zan je har gidan nasu na sanar da mahaifinta abunda yake faruwa, yarinya kin tsatstsiya mai hankali mai son makatanta zata biyewa yaron da ya Riga ya gama watse wa a duniya tace shi take so ai duk iyaye na gari baza su bari 'yar su ta auri wannan yaron ba."

Abbakar ya 'bata fuska tare da fadin "Umma kullum ina hanaki shiga abunda babu ruwan ki kina shiga kinayin kane-kane a ciki, wai don Allah me *MASHAHURI* yayi muku kuke aibata shi? Idan hakane kinga nima zaki iya kirana da lalatacce tunda muna abota dash......Da sauri Umman ta katse ta hanyar fad'in" Ni ban haifi lalattace ba ihe! Wallahi ja kara jin ka fad'i wannan maganar sai nayi maka baki, ai nima babu abunda zance da Dan Iskan yaron nan Wanda shine silar lalacewar ka ka daina jin magana ta, jiya jiyan nan nace ka bamu muyi cefene ka hana amma dake baka da mutumcin kaje ka sayowa Hanifa indomee da wainar kwai ni yausha Rabon da naci kwandalar ka."!


Dariya Abbakar yasa yace." Umma bani da kudi da gaske tunda ba sana'a nake ba su kud'in da kike magana nayi wa Hanifa siyayyar daga hannun Wanda kike zagi suka futo shine yake bani kudi da kowane lokaci idan kina bukatar cin kudinsa sai in siyo miki nama da kayan miya kiyi miy...... Katse shi tayi da sauri tace"Allah ya kiyaye min cin kud'in Wannan yaron yo meye bamu sani ba uban nasa fa Dan chanji ne kuma duk Wanda yake Wannan sana'ar "barawo ne."!

Abbakar ya rufe bakinsa cike da mamakin mahaifinyar tasa gami da kausasan lafuzunta yace." Wallahi Umma ki daina haka kar kije ki jawowa kanki wata masifar ya mutum da sana'ar shi ki dinga ce masa 'barawo Sanar chanji sana'a ce tsabttacciya ni dai babu ruwana, Alhaji Tijjani bashi da hakuri kan komai mussaman kan danshi *Khalid* kar watarana kina gidan buki hira tayi dad'i ki zagesu sai dai kiji ki a daure."!!

Asalamiyya tasa dariya Duka Umma ta kai mata tana zaginta Shi kuwa Abbakar hanyar futa ya nufa yana fad'in "Haka kurrum kubi Ku takurawa mutum ni wallahi banga aibun Khalid ba mutumin da abun duniya bai dame shi ba, don ni har yanzu ban ga wani abun asha da yayi a garin nan b......... Tuntube yayi da Hanifa dake tsugune tana kukan bakin ciki sosai taji zafin irin zagin da Ummansu Asalamiyya take wa Khalid ji tayi kamar ita take zagi.

Cike da mamaki! Abbakar yace." Hany kece a tsuguna anan kike yin kuka."!?

Kasa d'ago kanta tayi ta kalleshi sai ya rike hannunta ya mi'kar da ita tsaye yace" Zo muje muyi magana dake ta fahimta. " babu musu Hanifa tabi bayansa waje. Shagon Mobson ya bude Allah yasa babu jama'a sosai a gurin yace." Shigo ciki."

Hanifa sai da taji fad'uwar gaba kafin ta shiga tana tunanin yau itace cikin shagon Mobson matashin saurayin da yake da d'aurin gindi a unguwar kasancewar mahaifinsa shine me unguwar shine yake yin duk abunda yaga dama a cikinta.

Kallo ta dinga bin dakin dashi kana kallon dakin kasan na samari ne masu ji da Kansu ga abubuwan kida nan iri-iri.

A raku'be ta zauna kan wata kujera gabanta sai fad'uwa yake yi, Abbakar ya zauna kujerar da take fuskantar sa yace." Hany da gaske maganar da naji gurin Umma."!?

Hanifa ta sunkuyar da kanta kasa cike da kunyar sa.

Yace." Ki fad'amin kar kiji kunyata ni zan taimake ki ne. "

Daga kanta tayi. Yace." Baki zaki bude kiyi min magana."

Kanta a kasa tace"Eh Hakane Ya Abbakar wallahi zuciyata na sonsa nayi masa wani irin so da ban san iya a dadinsa ba."

Abbakar yaji wani iri cikin zuciyarsa Hak'ika yana son Hanifa sosai Cikin zuciyarsa kuma yana mutukar son dabi'unta sosai yake da ra'ayin auranta amma shi yasan menene so a rayuwa babu shakka zai danne nasa son domin ya taimaki yarinyar duk da yasan abune ba mai sauki ba gurin Khalid din amma ya San Hanifa lafiyayyar macece kuma kyaykyawar mace wacce ba ko wane namiji bane zai iya dauke kansa daga kanta ba, zai San yanda yayi ya shawo kan Khalid ya saurari Hanifa da haka shi idan ya gani Qualities dinta da kanshi zai rike ta hannu biyu... Wani tunani yayi a zuciyar sa ya kalli Hanifa a nutse yace." Zan taimaka miki gurin ganin na shigar dake a gurin sa amma duk abunda na umarce ki kiyi min kar ki musa min hakan shine zai sa ki jawo hankalinsa kanki."

Gyada kanta tayi tace"Ya Abbakar ni Abbu fa nake jin tsoro. " dariya yayi yace." Ki rabu da Abbu munsan yanda zamuyi masa."

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya yanzu zuciyarta ta soma sauki tana ganin kamar bukatar ta akan Khalid din zata biya tunda Abbakar zai shige mata gaba


A hankali yace." Ki tu'be hijab dinki da d'ankwalin kanki zanyi miki pictures yanzu zan tura masa su ta whatsp."

Hanifa taji wani irin fad'uwar gaba idonta ya fara rau-rau k'walla har ta soma zuba tace"Ya Abbakar ban gane ba?"

Abbakar yace." Kin gane Hany kwai kina kara tambaya ta ne saboda abun da na fada ya baki mamaki ko."

Tace"Sosai kuwa Ya Abbakar ina laifi kayi min hoton a haka Cikin suttura ta sai ka tura masa."

Dariya Abbakar yasa yace." Hany baby in banda abunki idan nayi miki pictures haka me zai gani har ya kyasa ki ke dai kawai kiyi abunda nace miki."

Hanifa ta girgiza kanta tana kokarin mik'ewa tace"Gaskiya Ya Abbakar bazan iya ba domin yin hakan haramun ne da dai zaka yi min a haka ne to."

Yace." Shikkenan Hany tunda kinki yadda ni kam iya kacin taimakon da zanyi miki kenan...... Kofar futa ta nufa zuciyar ta na saka mata ta yarda ko kar ta yarda.

Karaf!!! Idanunta suka sark'e da nashi tsayuwa tayi a gurin tana jin wani irin bugun zuciya hoton shi ne manne a jikin kofar futa daga shagon yana tsaye hannuwansa zube cikin aljuhu kwantaccan murmushi ne a kyakyawar fuskar shi

Hanifa taji wani irin masifaffan sonshi ya taso mata jikinta yayi sanyi tana jin wani irin yarrrrr! A jikinta juyo wa tayi kamar wata 'yar maye ta dawo ta zauna hade da cire hijab din ta aje ta cire hular kanta yalwataccan gashin bakikirin ya bayyana hade da zubowa kafadunta muryar ta na rawa tace"Ya Abbakar kayi min indai zai so ni kamar yanda nake sonshi."

Abbakar dake tsaye yana kallonta ji yayi kamar zai fad'i ganin albarkatun kirjin hanifa da suka gigitashi a zuciyarsa yake fadin ashe haka yarinyar nan take da tsarin jiki me kyau! Chaiiii! Hadiyar yawu kawai yake kafin ya ciro k'atuwar wayar shi mai muguwar camera tsiya ya fara d'aukar ta a hoto sosai yake sata tana canza salo da gantsare-gantsare hade da kwanciya iri-iri sai da yayi mata kusan Hamsin masu zafi sannan yace." Haka ya isa Hany baby." Da sauri ta dauki d'ankwalin ta ta d'aura ta zura hijab ta zauna tana jin fad'uwar gaba."

Abbakar da ya gama tsumuwa ya kalleta da idanunsa da suka soma sauyawa yace." Ki wuce gida insha Allah yanzu zan tura masa nasan idan yaga wannan zafafan hotonan naki zai soki."

Jiki a sanyaye ta mike ta futa daga shagon Kai tsaye gida tana nufa tana addu'ar Allah yasa yace yana sonta.....




*Yanzu aka fara kafcan!!*



~Littafin MASHAHURI akwai cakwakiya mai ban mamaki sannan akwai darrusa a cikin littafin akwai soyayya me zafi duk a cikin littafin daukaka gami da shahara wannan duk na Allah ne Khalid MASHAHURI!!!!!~


_*Kuyi maza ku biya kud'in karatu domin na kusa 'kare free zan tsunduma tsundum cikin labarin kar Ku bari a baku labari.!!?*_






*24/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/24, 8:25 PM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*



*FREE PEGE*


*22*



A sanyaye tayi sallama ta shiga gidan, Ammi dake zaune a tsakar gida ta d'aga ido ta kalleta da kyau! Tace"Hanifa kin kyauta wato da nace miki kar ki futa sai da kikaga hankalina ya dauke ki kasa 'kafa kika futa daga wai me kike so ki zama ne ? Hanifa kina so ki jawo min rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin gidana ko."!


Sunkuyar da kanta tayi tace"Ammi kiyi hakuri don Allah kinga ban Dade ba ko."!? Ammi tace"Eh baki Dade ba kam Yanzu ina littafin yake."!?

Gabanta yayi mummunar fad'uwa sai ta fara inda inda! Ammi tace"Zonan."!

Jikinta a sanyaye ta 'karasa gurin zama tayi gefen tabarmar. Ammi tabi ta da kallo cikin nazari tace" Ki fada min gaskiyar inda kika je don ga alamu nan sun nuna min baki da gaskiya."


Muryar ta na rawa tace"Wallahi Ammi gidansu Asalamiyya naje."!! Ammi tace"To ina littafin."!? "Ammi ta manta shi a wai! Ta bawa wata 'yar ajinmu a ro."! Ta k'arashe maganar cikin inda inda.!

Ammi tace" Hanifa INA fatan kin janye abunda yake Cikin zuciyar ki a game da wannan yaron da kike so."!

Hanifa tayi 'kasa da kanta tana zumbiro baki!

Ammi tace"Zaki fara zumb'ura baki ko to Wallahi yanzu zakiji na fasa miki shi har sai yayi jini."!!

Kuka ta fashe dashi tana fad'in "To Ammi ta yaya zan cire shi daga cikin raina nima fa bani na d'orawa kaina ba kawai wayar gari nayi naji ina sonsa."


"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un." Shine abunda Ammi ta fada cikin aljabi da mamakin irin maganar da ta futo daga bakin'yar ta ta."

Shiru ns minti biyar Ammi ta kasa cewa komai sai mamaki da al'abi take yi ta bude baki kenan zata yi magana sallamar Ummansu Asalamiyya ta katse ta.

Ammi ta amsa mata sallamar a sanyaye!

Ta 'karaso ta zauna suna gaisawa da tambayar me jiki."

Ammi dai tace"Da sauki don bata fahimci komai ba sai da Ummansu Asalamiyya tace"Hanifa ya jikin naki da sauki dai ko."!?

Hanifa da gabanta yake dukan uku-uku tace"Da sauki Umma."!

Ita dai Ammi binsu take da kallo cike da mamaki.!

Ummansu Asalamiyya tace"Ammi gurin ki nazo."

Ammi tace"To Sannu da zuwa bari in fara kawo miki ruwa tukkuna." Mik'ewa tayi ta shiga daki.

Hanifa ta fara 'k'ananun hawaye kamar tasan abunda ya kawo Ummansu Asalamiyya gidan gabanta sai fad'uwa yake.


****

Sai wajejen uku da rabi na rana ya tashi daga bacci a gurguje ya shiga toilet yayi wanka ya futo daure da alwala ji yake cikinsa kamar anyi masa yasa ya zura wata irin d'amammiyar vest da wando 3Quaetar wayoyinsa ya kunna kafin ya shimfid'a abun sallah ya tada sallah la'asar.

Bayan ya idar da sallahr yayi adduoinsa yanda suka sawwa'ka kana ya mike daga kan abun sallahr Kai tsaye inda ya aje wayoyinsa ya nufa ya d'iba futa yayi ya nufi b'angaran iyayen sa, Mamy na zauna a parlor suna hira da wata 'kawarta da ta kawo mata ziyara ya shiga da sallama.

Mamy tace"Yawwa kinga dan halak ko dama nace miki mybe ki ganshi ya shigo yanzu."

Fuskar sa ya saki kad'an yace." Mamy Kinyi ba'kuwa ne."!? Hajiya Mariya ta bude bakinta cike da mamaki tace"Khalid ni ka manta."!?

Sosa kansa yayi yana kokarin waske wa yace." Am sorry Momy wallahi na mance." Hajiya Mariya tace"Babu shakka ka girma ka kai Munzali yanzu har ka mance da Uwar goyon ka ta unguwar tudun Maliki."

Cike da kunya ya Sosa kansa yace"Momy sai yanzu na gane ki wallahi ke dince naga kinyi haske ba kamar lokacin da na sanki ba."

Hajiya Mariya ta watsa masa hannu tana yi masa da'kuwa tace"Ta ina? Kai dai kawai kace"Kayi girma kuma yanzu al'amarin jama'a yasa ka mance damu da Nasrin dinka."

Dariya ya danyi yace." Kiyi hakuri wallahi kuna raina Momy INA Nasrin da wannan 'katon jikin nata amma ta sa'be ko."

Hajiya Mariya tasa dariya hade da gyara zamana tace"Nasrin ta dawo siririya dama ko lokacin ai yarinya ta ce tasa tayi Wannan kibar."

Murmushi yayi kawai ya nufi daining yana fad'in"Mamy yunwa nake ji pls."

Mamy ta mike da sauri ta isa daining din ta soma hada masa abunci tana yi masa fada ya kula da cikinsa.

Hajiya Mariya ta sanyo musu Baki tana fad'in "Insha Allah zan turo miki Nasrin ita sai ta dinga kula da cikinsa tunda sai kinyi da gaske."

Mamy tace"Aikuwa da kin kyauta min kawata wallahi ina jiran zuwan ta."

Khalid baice musu komai bai tun bayan zaman shi gurin cin abincin ya bude what sap Wanda yayi kwana uku bai hau ba messengers ne kawai suke shigowa ya aje wayar kan teble din ya fara cin abincin cikin nutsuwa hankalin shi na kan messages din da suke shigowa. Da sauri ya dauki wayar ganin tarin pictures da Abbakar ya turo masa hannu na kyarma ya bud'e su.

'Kwarewa yayi ya fara tari!! Ammi ta taso da sauri! Tana fadin"My son sannu sannu ayya! ruwa ta mi'ko masa cikin wani cup na tangaran tana fadin "Aje wayar ka kar'bi ruwan kasa my son."! Khalid jinta kurrum yake yi ya mi'ka hannu ya karb'i ruwan hankalin shi duk na kan pictures din hanifa Wanda suka yi mutukar gigita shi! mamy tayi wuf! Ta le'ka fuskar wayar abunda ta gani yayi mutukar gigita ta da bata mamaki!


***

Ammi tace" Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "! Bayan ta gama sauraron abunda ya kawo Ummansu Asalamiyya gurin ta. Da sauri ta juya inda Hanifa take zaune wayam! Babu ita gurin.






*24/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/25, 9:28 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*




*FREE PEGE*


*23*




Cike da damuwa gami da 'bacin rai Ammi tace"Hak'ika Hajiya Abu bani da bakin da zan gode miki kuma duk inda ma'koci yake kin kai wato da mu muna zaune sake da baki mun tura Hanifa makaranta Ashe bamu sani ba bata zuwa lallai duk inda ka kai da dubarar ka d'an yau ya fika."! Cike da mamaki Ammi ta 'karashe maganar.

Ummansu Asalamiyya tace"Wallahi kuwa ni babban abunda ya fi daga min hankali da al'amarin shine wannan yaron da ta kwallafa rai ya kamata kuyi kokarin rabata dashi domin Sam ba yaron arziki bane."


Ammi tace"Insha Allah zamuyi kokari kuma Allah zai shige mana gaba."

Ummansu Asalamiyya ta mike da niyar tafiya Ammi itama ta mike har soro ta rakata kafin ta dawo cikin gidan kai tsaye daki ta shiga tasan Hanifa na cikin Uwar dakin tana shiga ta fara juyo gunjin kukan ta kamar wacce aka zanewa jiki.


****


Mamy ta kalleshi da Jan ido tace"Myson me nake gani cikin wayar ka wannan yarinyar d'iyar hausa fulani ce ko kuma d'iyar arna ce."!?

"Mamy wace yarinya."!? Ya fad'a yana kokarin bagarar da mamy din.

A kufule! Tace" Zaka raina min hankali ne hoton da nagani a wayar ka nake magana akansu ."

Shiru yayi mata yana tsakurar abincin so yake ma ya bar gurin domin ji yayi duk abincin ya ginsh eshi.


Hannu ta mi'ka masa tare da fadin"Bani wayar mu gani."?

Cike da mamaki yake kallonta Mamy zata yi masa bunkice a waya lallai asirin sa zai tuno.

Ido ya tsura mata ya shagwabe fuska kamar yanda ya saba, shan kunu tayi tace"Myson ranka zai 'baci nace ka bani wayar na ga wace 'yar iskar yarinya ce wannan."

Wayar ya mi'ka mata yana fad'in "Mamy nima bansan ta ba abokiya tace kawai ta online."

Mamy ta karb'i wayar tana fadin "Kai ka sani dai." Barin gurin tayi parlor ta nufa inda Hajiya Mariya ke zaman jiran ta.


Mamy tace" k'awata duba ni ganin abun mamaki."! Hajiya Mariya ta zuro kanta fuskar wayar Mamy ta shiga ma'adan hotona already pictures din Hanifa sun bude duka sune kuma a farko nan suka fara kallonsu d'aya bayan d'aya.


Hajiya Mariya tace"Duniya yanzu ta 'baci duba don Allah yarinyar budurwa d'anya shakaf tana kokarin zubawar wa da kanta mutumcin dubi sassan jikinta kai Innaillahi."!

Mamy tayi tsaki tare da fad'in "Hajiya wannan yarinyar wallahi bakya raba d'ayan biyun tasan namiji dubi idonta fa kamar na mashaya ai duk inda take bata futo gidan mutumci

1 Comments On MASHAHURI
avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

39901

Please Login or Register in order to submit comment