Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga hall din hasken flash na wayoyin mutane suka fara haske shi hanyar da amarya da ango suka bi ita yake bi a nutse yana d'agawa mutanen dake gefen hannaun shi na dama Dana hagu hannu fuskar shi a sake take sosai, manya baki suka tare shi suna rungume shi har ya isa gurin tsayuwar shi. Amarya da ango suka taso daga gurin zaman su har inda yake tsaye suka isa a hankali suka tattaka steps suka isa gurinshi gaisawa suka yi cikin mutumci kana ango ya fara yi masa 'barin dollos tun kafin yaji ma wace irin wa'ka ya rera musu shi da amarya shi.

Kud'i ne kawai suke zubah a gurin Khalid Mc ya 'karaso gurin da sauri ya mi'ka wa Khalid din wani irin Abu Wanda kana ganinshi kasan nasu ne na mawa'ka.

Muryar shi mai dad'in sauraro ta fara tashi cikin wa'kar da shiryawa amarya da ango domin murnar shagalin sauransu.


*"Tauraruwa Zahra kin cika gimbiya, Zahra Aminiya ta iya kwalliya, Shahid kayi dace da samun abokiya, sai kayi jinjina gurin Aminiya, Zahra sarauniya ta iya kwalliya, aure dace da masoyiya Zahra ga Shahid sun dace da juna""""*


Tofaaaaa tuni guri ya hautsine da ihu! Ga sautin 'kida yana tashi sosai wa'kar amarya da ango ta fara shiga cikin jikin mutane domin wa'kar tayi dad'i mutuka

Abokan ango da amarya suka fara mi'kewa suna isa gurin ko wanne ya bude bakin jaka da aljuhu suka fara zubawa Khalid kudi a jikinsa

Kwata-kwata baka gani 'yan Dari ko Dari biyu a gurin dubu dubu ne kawai suke magana 'yan Dari biyar ma Sam basu da yawa a gurin. wasu na lika masa kudi wasu na yi masa vidio a wayonyinsu kai abundai ba'ace komai.

Yarinyar da suka had'u a cikin jirgi itace ta dunga kutsawa cikin jama'a har ta isa inda yake tsaye ta 'karasa kusa dashi ta sanya hankicif din hannunta tana tsane masa fuska dashi,


Khalid hakan bai dame shi ba saboda a inda yake tsaye a gurin wasu daga cikin 'yan da suke fakaicewa da yi masa li'ki suna zuwa ne su rungume shi su dauki hoto dashi kafin su yi masa watsin kudi hakan Sam bai dame shi ba saboda yasan a cikin garin da yake su yin hakan a gurinsu ba komai bane.


Had'addan 'yan matan da zawarawan da suka amsa sunan su ta fannin komai na rayuwa sai suka fara watsawa Jamsy kallo ganin za'kewar ta tayi yawa a gurin yarinyar da ko sutturar arziki babu a jikinta taje ta mak'ale kusa dashi wai ita gwana, haka dai kowa ma gurin ya fara jin haushin ta.
Ganin amarya da ango sun koma gurin zaman su yasa jama'a suka fara matsawa daga gurin suna komawa gurin zaman su hade da sauraran sautin wa'kar da take futa daga bakin *MASHAHURI* Alhmdullahi babu abunda amarya da ango zasu ce wa Khalid domin ya wake su mutuka ya zuba ruwan basira cikin wa'kar shi, lokacin ne kuma manya abokan ango suka fara yi masa kyauta ta ban mamaki! Kafin gurin ya nutsu a fara ciye-ciye Mc tuni ya saita komai sautin wa'kar ya fara tashi kad'an -kad'an ta ciki jibga jibgan sifikon da suke gurin.


Khalid kuwa ya zauna gurin da aka tana dar masa Wanda aka jera masa uban kayan ciye-ciye.

Madarar holandia kawai ya isha a gurin saboda yanda ido yayi masa yawa yana mamakin al'amarin mutane duk motsinsa idonsu akai mussaman 'yan matan gurin sai daukar sa a hoto suke yi da wayoyinsu

Agogon hannunshi ya kalla k'arfe goma sha daya da rabi yaga kamar wasu ma yanzu suke zuwa shi kam ya gaji tafiya zaiyi Abokin shi da yayi sanadin zuwan shi gurin shi yake nema Tajo nacan cikin jama'a tsaki yaja yana kokarin mik'ewa ta 'karaso gurin.

Jamsy ce.........................






*22/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/23, 9:38 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*




*FREE PEGE*



*18*



Jamcy ta gyara kujerar dake fuskantar sa ta zauna hade da dora 'kafarta kan d'aya zama irin na had'addan 'yan mata tayi ta wani tsura masa idonta cikin sigar Jan hankali tace"Ashe ina tare da babban mawa'ki ban sani ba, a gaskiya kayi min sosai kuma muryar ka tayi bala'in tafiya da imanina dama ni kam tunda nagan ka cikin jirgi naji jikina na bani akwai wani babban al'amari a tartare da kai, a gaskiya Allah yayi maka baiwa ba kad'an ba."


"Thank u."! Abunda yace kenan yana me kauda kansa daga kanta domin kwata-kwata baya 'kaunar ya kalli abubuwan da suke 'kokarin sauya masa tunanin a halin yanzu.


Jamsy tayi wani fari da ido cikin sigar Jan hankali tace" Idan babu damuwa zan bika masaukin ka domin in d'ebe maka kewa."


Wani irin kallo Khalid ya watsa mata yarinyar yanzu ta soma bashi haushi cikin yanayin maganar shi yace." Nagode ki sha zaman ki ni ba irin wad'annan samarin da kike nufi bane."

Cikin zuciyar ta tace" guy nan ya fiye girman kan tsiya wallahi wai budurwa kamar ni da maza suke rububi a gari har na kawo kaina gurinsa ya gwale ni...... Tana zancan zuci Tajo ya karaso gurin. Khalid ya mike da sauri suka fara tafiya da niyar barin gurin.


Jamsy kamar mayya ta mike da sauri ta tari gabansu Cikin damuwa da 'kosawa Khalid ya dafe kansa!


Tajo yace." Jamsy ya aikaine.''? Kuka ta saki tace"Tajo! wallahi tun da muka had'u a jirgi nake masa magana yana wulakantani ka dube ni da kyau ina da kyau da kyawun jiki amma sam yak'i saurara ta."


Tajo yasa dariya yana sosa kansa yace." In banda abunki meye abun kuka anan dole kiyi hakuri kamar yanda ko wace budurwa takeyi shi haka Allah yayi shi da farin jini baga mata ba ga maza ba, kiyi hakuri kawai.


Khalid ya Dan ya mutse fuskar sa tare da kallon Tajo yace." Ni na rasa me take so inyi mata tun a jirgi ta nemi numbar wayata na bata Kai kanka kasan ba kowa nake bawa numbars dina ba ita ta samu tana wani Abu."!


Tajo yace." Lallai Jamsy kinci sa'a kuma yana da kyau ki kiyaye bada numbars ko don gaba don wallahi ba kowa yake bawa numbars shi ke kinci sa'a."



Jamsy tana share hawaye tace"Ni duk ba wannan ba don Allah ka ro'kar min shi inaso in zama yarinyar shi ya zamana duk inda zashi muna tare ni bani da matsalar komai."


Tajo ya kalli Khalid yaga yana ya mutse fuskar sa yace." Ki bari mu gama wannan hidimar Insha Allah zamu yi maganar kar ki damu."

Girgiza kanta tayi kurrum tans kallonsu suka wuce ta ta bi Khalid din kallo cikin tsantsar sonsa Wanda bata San iya adadin yawan shi a cikin zuciyar ta ba.


Khalid ya shifa mota yana sauke ajiyar zuciya cike da gajiya ya kalli Tajo tare da fad'in"Wannan yarinyar wai a ina take me mugun nacin tsiya tun muna jirgi ta takura min."


Tajo yace." Friend din amarya ce itama tazo buki kuma 'yar garin ku ce."


Tab'e bakinsa yayi hade da lumshe idonsa ya mik'a wa Tajo wayarsa tare da fad'in "Duba kaga abunda ta turo mun a wayata."

Tajo ya karb'i wayar yana dariya.

Pictures din Jamcy ya gani sun kai ashirin wasu tsirara wasu babu kayan arziki Tajo yaji yana neman shiga wani irin yanayi muguwar sha'awa ta rikito masa domin duk inda ake neman cikkiyar kace Jamcy ta Kai ta ko ina.

Cikin rawar baki yace." Kai amafa yarinyar nan ta wanku shegiya da gani tana dan ta'ba harkar wallahi da kasani ka yarda ta bika ka rage zafi." Ya k'arashe maganar yana dariyar sha'kiyan ci


Khalid ya sa hannu yana kokarin karb'ar wayarsa ganin da yayi Tajo na kokarin yi masa bunkice ciki Sam baya so ya kalli hotonan yarinyar Shaik sunan da yasawa Hanifa kenan, Tajo yace." Bari inyi kallo don Allah naga wayar taka akwai.......a cikinta."


Wayar shi ya fuzge yana fad'in "Ita kadai na nuna maka meye dole sai kaga wasu kuma."!

Tajo yasa dariya yace." Shege kenan har yanzu kanan dai da halin ka ko."!?


Khalid yace." Me za'a fasa kai sai kawai Allah yayi mana me kyau kallon pictures din yana rage min zafi."


Tajo yace." Kayi aure mana ka huta da futuna." Girgiza kansa yayi yana ya mutsa fuskarsa yace." Kwata-kwata yanzu bana da ra'ayin aure wallahi domin bana son tension yanzu ina aure sai haihuwa abar da na tsana."


Tajo yace." Nima kam bana son yara wallahi shiyasa Madam tun kafin muyi aure na Sanar da ita kuma ra yarda kaga Yanzu dai shekaru hudu da auramu har yanzu bamu shirya haihuwa ba."


Khalid ya bashi hannu suka tafa kana yace." Wallahi nake fada maka duk son da kake wa mace daga zarar ta fara haihuwa Shikkenan zata rakyakykya'be jiki duk ta tsufa na tsani inga nono a zube !

Tajo ya sa dariya hade da bashi hannu suka tafa suna kyalkyala dariya cike da nutsadi. Haka har Tajo ya sauke Khalid a masaukinsa suka yi bankwana da juna Tajo ya koma gurin dinnar din don har yanzu ba'a tashi ba.


*****
Washe garin ranar Hanifa cikin nukufurci da b'acin rai ta tashi domin da kyar ma ta karya tana yi tana zumb'ura baki Ammi kuwa duk jikinta yayi sanyi ganin ma duk irin fad'an da takewa Hanifar kamar tana 'kara tun zura ta ne sai ta dawo rarrashi nan ma Hanifa ta dinga botsare-botsare taki tanka mata. Ta dauki Jakarta ta fuce daga gidan ba tare da tace mata komai ba, Ammi ta bita da kallon mamaki da al'ajabi

Abbu yana zaune a soron gidan dashi da wasu samari hudu Wanda suke daukar darasa gurin shi Hanifa tazo ta wuce ba tare da tace masa komai ba, Wanda inda da Dane sai ta tu'be takalminta ta tsuguna har 'kasa ta gaida mutanan gurun duk yawansu sannan tace"Abbu sai na dawo shi kuma yayi mata fatan alkairi da dawowa lafiya.

Abbu ya bi bayanta da kallo yana mamakin sauyawarta kai ya gyada kuruum ya cigaba da abunda yake yi.

Tun kafin ta 'karasa gidan su Asalamiyya ta hango dandazon matasan samarin unguwar suna ta manna abu jikin bango ko da ta 'karasa kusa sai da ta kusa zubewa a gurin ganin Postar ta MASHAHURI data cika bangon gidansu Asalamiyya da jikin kofafin gidajan mutane 'kofar shagon Mobson kuwa duk ita ce yana tsaye gurin dinnar hannunsa rik'e da irin abun su na mawa'ka da alama lokacin da yake wake amarya da ango aka yi masa hoton. Har da masu had'a riga da postars din suna sanyawa a jikinsu tsabar kaunar da suke masa.

Soron gidan ta tsuguna tana sauke ajiyar zuciya wani irin yarrrrrr! Jikinta yake mata ganinshi yanzu jikin hoto yayi bala'in tayar mata da fleengs ajiyar zuciya kawai take sauke wa tana jin wasu ruwan hawaye na kokarin su zubo mata.


Abbakar ne ya futo daga cikin gidan hannunsa rike da da tarin postars din kawai ya ganta tsugune ta hade kai da gwiwa Hanifa ba ba'kuwarsa bace duk inda take dole ya gane ta yace." Hanny meye kika zauna a soro ki shiga ciki mana Asalamiyya na ciki tana jiran ki."


Hanifa ta d'ago kanta tana kokarin maida kwallarta tace"Ya Abbakar kaina ne yake ciwo."

Yace." Ayya! Amma kika futo makaranta."?

Shiru tayi masa tana matsar hawaye da ya rigaya ya fara zubah."

Yace." To ki koma gida mana." Gyada kanta tayi tace"Abbu."! Abbakar yaja tsaki tare da fad'in "Ya Shaik akwai takurawa wallahi kina cuta ma bazai bari ki huta ba." Hanifa an Sosa mata inda yake mata 'kyaikyayi sai ta fashe da kuka jikinta na makyarkyata.


Abbakar yace." Wuce ciki in kawo miki magani kisha yau komai Abunsa baza kije makaranar ba kiyi zaman ki."

Mik'ewa tayi tana kokarin shiga ciki shi kuma yana kokarin futa sai ta juyo da sauri tace." Ya Abbakar."! Juyo wa yayi yana kallonta

Tace." Bani guda d'aya."

Hannusa ya kalla ganin abunda take nunawa yasa ya zaro guda ciki ya mik'a mata tare da fad'in "Ko guda dubu kike so akwai gashi."

Hannu na kyarma ta karba tare da fadin "Nagode Ya Abbakar."

Yace." Ki shiga ciki ganin zuwa mu zamuyi miki komai amma ba don halin Shaik ba."

Hanifa ta shiga cikin gidan tana jin wani irin dad'i Cikin zuciyarta ko babu komai ta samu hoton shi tana ganin zai dinga d'ebe mata kewarsa, nan nade shi tayi sosai ta cusa cikin jakarta simi-simi ta shiga cikin gidan.


Babarsu Asalamiyya na zaune a tsakar gida tana gyara shimkafa tace"A'a Hanifa jiki yayi sauki kenan."

Hanifa ta karaso jiki babu kuzari ta zauna kan tabarma dake shimfid'a tace" Umma ina kwana.?

"Lafiya Lou Hanifa ya jikin ki."? Da sauki dai" ta fada tana kokarin kwanciya lokacin kuka Asalamiyya ta futo daga daki a shirye dama Zuwan Hanifar take jira su tafi kawai sai taga Hanifa ta kwanta tana lumshe ido tace"Wannan wane irin Abu ne dallah ki tashi mu tafi kar mu makara."








*23/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/23, 10:24 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*




*FREE PEGE*


*19*



Babbar su tace"Haba Asalamiyya bakya ganin yanda ta kwanta ne tun jiya take cewa kanta na ciwo ke kije makarantar kawai domin ko taje ita babu wani darasi da zata d'auka. "

Asalamiyya tace"Wallahi Umma 'karya take yi hakafa jiya tace min kawai dai ita tasan abunda yake damunta."


Tace"Banda abunki Asalamiyya haka kurum mutum sai ya jawo wa kanshi cuta don Neman masifa tunda kika ga haka da gaske ne kawai dai nasan tana jin tsoron Abbu ne ko Hanifa."?

Hanifa ta gyda kanta tana share hawaye.

Asalamiyya ta girgiza kanta tana mamakin yanda Hanifa ta sauya hali lokaci guda ta koyi karya Wanda hakan ba d'abiar ta bace amma so ya rufe mata ido Sam bata hango abunda ake hango mata idan banda sharrin so ma ina Hanifa ina MASHAHURI lallai hanifa tana so ta jefa kanta a masifa don tayi imanin Khalid bazai taba sauraronta ba.


Cike da takaici ta kama hanya zata futa suka ci karo da Abbakar ya shigo gidan hannunsa rike da ledar indomee wacce ya sanya me shahin kofar gidan ya dafa masa da sharbebiyar wainar kwai yace." Ke Asalamiyya maza kiyi tafiyar ki Hanifa kam baza taje ba."


Asalamiyya tace"Wallahi ya Abbakar karya take yi lafiyar ta lau ni zan fada maka abunda yake damunta."

Abbakar yace." Koma meye dai nace baza taje ba ke jeki." Asalamiyya ta futa tana mamakin al'amarin.


Abbukaar ya aje ledar a gaban Asalamiyya yace." Tashi kici indomee gashinan ga kuma maganin na karbo miki kisha ki kwanta ki huta."


Asalamiyya ta mike zaune tana ya mutsa fuskarta tace"Nagode Ya Abbakar." Ledar ya bude mata k'amshin ya cika gurin .

Babarsu ta juyo tana kallon ledar indomee da manya-manyan wainar kwai har guda uku dumbin mamakin Abbakar ya kamata yanzu yanzu tayi masa magana cewar tun da babansu ya futa da wuri kuma bai da kud'in cefane ba to shi ya bada Dari biyar ayi cefane sai cewa yayi bashi da kudi shima amma abun mamaki gashi ya had'owa Hanifa kusan dariyar biyar din lokaci guda yana lallab'ata taci ikon Allah.!

"Dauke kanta tayi
ta cigaba da abunda take yi gefe guda kuma tana sauraron yanda Abbakar din yake wani kashe murya da lankwasa murya gurin rarrashin Hanifa taci Indomee ita kuma sai shank'amshi takeyi tana tsakurar indomee tana ci, sai da yaga ta ci rabi sannan ya futa bayan ya fada mata yanda zata sha maganin.

Shuru gurin yayi Hanifa ba gwanar cin abinci ba tana ganin futar shi ta cire hannunta ta mike taje ta daureye hannunta sannan ta dawo ta balli maganin kamar yanda yace mata ta zuba cikin Jakarta sannan ta dauki ledar pure water guda tasha rabi ta koma ta kwanta.


******

Kamar yanda aka sha shagali jiya to yau ma tun misalin k'arfe biyu na rana suka futa can wani kebantaccan guri wanda aka tanade shi domin shagalin buki mutanan da suka samu damar hallar dinner din yau din sunfi na jiya guri ya tumbutsa sosai da manya manya masu kudi da yan boko Khalid ya shigo gurin cikin wata irin shiga data furgita yan mata da samarin gurin gurin tsayuwarshi ya nufa tare da wasu matasan samari majiya k'arfi suka tsaya a bayan shi.

Yau wa'kar da yayiwa amarya da ango dabance ce Amarya da ango sunji dad'i mutuka ta inda suka dunga watsi da kudi kamar banza friends dinsu na taya su. Kyautuka na ban mamaki Khalid ya sha su a gurin kafin taro ya watse kowa ya kama gaban shi.


Daran ranar Tajo da wasu abokan shi su uku suka isa hotel din da yake suna janye da uban kudi cikin k'aramin buhu Khalid ya kalleshu da mamaki yake fadin"Meye Wannan cikin buhu kuka aje min a gabana. "!

Tajo yace." Kud'in ka kane gasunan yanzu zamu sa yara su lissafa su."


Girgiza kansa yayi yace." Bana bukatarsu kawai kuje Ku rabawa mabukata sanin kanka ne ni kasan ba don kudi nake wa'ka ba wa'ka ra'ayina ce."

Suka bishi da kallon mamaki! Kudi kusan miliyan biyar yace baya so lallai Khalid MASHAHURI ya ci sunan sa......








*23/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/23, 8:10 PM] .: *FREE PEGE*



*20*


Asalamiyya na dawo wa gida ta kalli Hanifa dake kwance har yanzu tace"Wallahi malam Ayuba ya shigo aji kuma anyi kiran suna jiya da yau duk baki zo ba sai ki shirya abunda zaka ce masa.


Hanifa ta mi'ke zaune da sauri tana zare ido tace"Baki fada masa uzirina ba."

Asalamiyya tace"Wane uziri zai fada masa sai dai ke kije ki fada masa cewar kin fara soyayya. "

Da sauri ta rufe bakin Asalamiyya da hannunta tana nuna mata dakinsu a hankali tace"Kar Umma taji don Allah kiyi shiru."

Asalamiyya ta bar gurin tana fad'in "Ke kika San wannan ni dai na fada miki."


Mik'ewa tayi hade da daukar jakarta ta rataya ta saki hijab din ta kana ta bude murya sosai yanda zasuji tace"Umma na tafi gida."


Ummansu Asalamiyya na daga cikin Uwar d'akinta tace"To Hanifa ki gaida Ammi da kyau Allah ya sawake."

Hanifa ta futa daga gidan tana fad'in "Zata ji insha Allah."

Asalamiyya tana kokarin cire unporm din ta tace"Umma kenan wanna cutar fa ta 'karya ce Idan na fada miki abunda yake damunta sai kiyi mamaki"!


Tana ninke kayansu tace"To ai sai ki fada min tunda dai dake da ita duk d'aya kuke a gurina amma ni nasan Hanifa baza ta jazawa kanta lalura ba."

Asalamiyya tace"Wai MASHAHURI take so shine take kwanciya da kin zuwa makaranta."


Bude baki Umma tayi tana kallon d'iyar tata cike da mamaki tace"Lallai yarinyar nan bata da hankali wato kowa yana 'kokarin samun ingantaccan namiji managarci ita kuma wannan fitanann yaron ta hango. "!? Asalamiyya ta ta'be bakinta tare da fad'in" Umma kenan to ai ba ita kadai ba kusan duk 'yan matan unguwar nam sonshi suke."


Umma tace"Hanifa dai tana bawa kanta wahala ne nasan babu yanda za'ayi Mahaifin ta ya aura mata yaron ko da shine yace yana sonta abune Wanda bazai taba yiwu ba balle ma ba shine yake sonta ba, kinga ita take cutar kanta, to tunda abun hakane ni da kaina zanje har gidansu in Sanar da Mahaifiyar ta abunda yake faruwa domin wannan shine zaman tare kinga tun Abu baiyi nisa ba sai su San yanda zasu shawo kan matsalar."

Asalamiyya tace"To Allah yasa a dace Umma." Tace"Ameen Ameen. Ummansu Asalamiyya ta jima tana mamakin al'amarin.
[12/24, 7:12 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*




*FREE PEGE*



*20*


Asalamiyya na dawo wa gida ta kalli Hanifa dake kwance har yanzu tace"Wallahi malam Ayuba ya shigo aji kuma anyi kiran suna jiya da yau duk baki zo ba sai ki shirya abunda zaka ce masa.


Hanifa ta mi'ke zaune da sauri tana zare ido tace"Baki fada masa uzirina ba."

Asalamiyya tace"Wane uziri zai fada masa sai dai ke kije ki fada masa cewar kin fara soyayya. "

Da sauri ta rufe bakin Asalamiyya da hannunta tana nuna mata dakinsu a hankali tace"Kar Umma taji don Allah kiyi shiru."

Asalamiyya ta bar gurin tana fad'in "Ke kika San wannan ni dai na fada miki."


Mik'ewa tayi hade da daukar jakarta ta rataya ta saki hijab din ta kana ta bude murya sosai yanda zasuji tace"Umma na tafi gida."


Ummansu Asalamiyya na daga cikin Uwar d'akinta tace"To Hanifa ki gaida Ammi da kyau Allah ya sawake."

Hanifa ta futa daga gidan tana fad'in "Zata ji insha Allah."

Asalamiyya tana kokarin cire unporm din ta tace"Umma kenan wanna cutar fa ta 'karya ce Idan na fada miki abunda yake damunta sai kiyi mamaki"!


Tana ninke kayansu tace"To ai sai ki fada min tunda dai dake da ita duk d'aya kuke a gurina amma ni nasan Hanifa baza ta jazawa kanta lalura ba."

Asalamiyya tace"Wai MASHAHURI take so shine take kwanciya da kin zuwa makaranta."


Bude baki Umma tayi tana kallon d'iyar tata cike da mamaki tace"Lallai yarinyar nan bata da hankali wato kowa yana 'kokarin samun ingantaccan namiji managarci ita kuma wannan fitanann yaron ta hango. "!? Asalamiyya ta ta'be bakinta tare da fad'in" Umma kenan to ai ba ita kadai ba kusan duk 'yan matan unguwar nam sonshi suke."


Umma tace"Hanifa dai tana bawa kanta wahala ne nasan babu yanda za'ayi Mahaifin ta ya aura mata yaron ko da shine yace yana sonta abune Wanda bazai taba yiwu ba balle ma ba shine yake sonta ba, kinga ita take cutar kanta, to tunda abun hakane ni da kaina zanje har gidansu in Sanar da Mahaifiyar ta abunda yake faruwa domin wannan shine zaman tare kinga tun Abu baiyi nisa ba sai su San yanda zasu shawo kan matsalar."

Asalamiyya tace"To Allah yasa a dace Umma." Tace"Ameen Ameen. Ummansu Asalamiyya ta jima tana mamakin al'amarin.

****

Tunda ta hango Abbu da su Nasir a kofar gida suna alwala sai ta hade fuskarta Tun kafin ta 'karasa ta fara zum'bure-zum'buran baki. Nasir na hango ta ya kura mata idonsa shi dai Allahn da yayi ya zuba masa kaunar Hanifa m, tana ganin irin kallon da yake mata ta dunga zabga tsaki tana watsa masa banzan kallo.

Duk ya lura da irin kallon da take watsa masa shi kuma kamar tsohon maye bai sa kallonta ba har ta 'karaso gurinsu ta d'an risina a cunkuse tace"Abbu barka da yamma."

Abbu ya dago kansa ya kalleta Cikin kulawa yace."barka dai Hanifa kin dawo." ? Kai ta gyda tana kokarin shiga gidan.


Ammi na kicin kamar ko da ya yaushe hanifa tayi sallama Jakarta ta aje gefe kai tsaye buta guda ta d'auka ta nufi band'aki Ammi ta juyo tana kallonta kana ta cigaba da abunda take yi.


Alwala ta d'aura bayan ta futo daga band'akin kicin din ta Dan kalla a hankali tace"Ammi sannu da gida."

Ammi tace"Sannu Ai na dauka baza kiyi magana ba."

Ba tace komai ba ta shige cikin dakin su. Can 'kuryan dakin ta shiga ta cire uniporm din doguwar Riga ta sanya a jikinta kafin ta shimfid'a abun sallah a nutse ta tayar da sallah Magariba.

Tana idarwa ko addu'ar arziki babu ta janyo Jakarta pastar Khalid ta cire a hankali ta bude ta tsura masa rikittun idanunta Wanda suke rikice da soyayyar sa!

'Das!d'as!d'as! Gabanta

1 Comments On MASHAHURI
avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

39901

Please Login or Register in order to submit comment