Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register




Firgigit! Hanifa tayi tana kallon Ammi dake tsaye bakin 'kofa. Nan Ammi ta fahimci ba bacci take yi ba kuma ga yanayin ta nan duk ya sauya kamar wacce take cikin damuwa.


Ammi tace"Tunanin me kike yi Hanifa uhum? Tun d'azu ina ta kwala miki kira shiru ."?

Hanifa ta fara magana cikin sangarta kamar yanda ta saba tace"Ammi ni babu komai bacci nake so nayi ga wani irin sanyi yana damuna."


Ammi dai ba yarinya bace balle Hanifa ta ninke wa baibai gyada kanta kurrum tayi ta saki labulan ta futa tana tunanin lallai babu shakka akwai abunda yake damun yarinyar dole ta zauna da ita tun kafin Abu yayi nisa."


Jiki a salu'be ta futo daga d'akin ta d'auki wani k'aramin kaskon 'kasa Wanda Ammi take yin turarar wuta dashi kicin ta nufa ta fara d'ibar garwashin wuta a ciki.

Ammi tace"Me zakiyi dashi."?
"Ammi sanyi nake ji wallahi nasan dole yau sai nasha panodol." Ammi tace"Dole ne kuwa so nake Yayunki su dawo su kar'bo a chamis ni kaina ina 'bukatar Robb jikina duk ciwo yake yi.
Abbu ne ya shigo gidan bakinsa dauke da sallama.







*18/12/2019*

_BintuUm@rAbb@le_
[12/19, 9:35 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*





*FREE PEGE*




*11*



Hanifa tayi saurin sunkuyar da kanta 'kasa tana amsa sallama Abbu. Jinta take duk a tsarge! Ammi dake kicin tace"Abbu sannu da dawowa." Yana 'kokarin shiga cikin gidan yace." Sannu Halima sannunki da 'kokari." Cikin rumfarsu ya shiga Hanifa taji jikinta duk yayi sanyi simi-simi ta dauki kaskon wuta ta nufi d'akin. Abbu ya kalleta a nutse yace." Hanifa baki da lafiya ne kin rage kuzari a jikin ki." Ammi dake kokarin shigowa dakin tace"Ai dole Abbu duk wannan uban ruwan a kanta ya 'kare." Abbu ya mike zaune sosai yana kallon Hanifa Cikin mamaki yace." Ya'akayi kika tawo cikin ruwa."?


Cikin Ladabi Hanifa tace"Wallahi Abbu mun riga mun futo daga cikin makaranta muna tsaye kan titi ruwan ya sakko gashi masu ababen hawa sun hana mu mu tsallaka."

Abbu ya girgiza kansa yace." Dad'ina dake rashin wayo da dubara Hanifa da sai Ku koma cikin makaranta Ku bari ruwan ya dauke ." ya fad'i maganar kamar yanda Ammi ta fad'a


Kuka ta fara yi domin ba son abunda zai 'bata ran mahaifin ta cikin shashshekar kuka tace"Abbu kayi hakuri don Allah wallahi kowa ya futo daga cikin makarantar shine yasa muma muka futo."


Yace." To ko don gaba kar ki 'kara bari ruwa ya doke ki kinji ko." Gyda kanta tayi tana share hawaye. Sallamar su Nasiru ce ta katse Ammi dake magana.


Suka shigo cikin d'akin Nan Nasiru ya d'aga hankalinsa ganin Hanifa na matsar fuska ya kalli Ammi yana d'an 'bata fuska yace." Ammi nifa a gidanan an takura min kwana biyu Sai kuka ake samu."

Ammi dai murmushi tayi ta futa daga d'akin. Abbu yace." Laifi tayi akayi mata fad'a shine take wa mutane kuka." Nasiru yace. " abbu ayi hakuri don Allah a gafarce ta."


Murmushi Abbu yayi yana 'kara 'kaunar yaron lallai babu shakka Nasiru zai ri'ke masa Hanifa da amana saboda ya lura yana sonta na ha'kika a irin wannan Lokacin samun tsayayyun maza sai an tona duk rabi yanzu auran sha'awa ake yi.


Ammi ta shigo d'akin dauke da wani tire mai fad'i ta jero kayan abinci ciki Ammi macace mai mutukar tsabata da kula da gida sosai ta iya girki ko wanne Ammi duk inda ake Neman cikkakiyar mace kamila to ta Kai ta fanni komai shiyasa kullum mijinta cikin sa mata albarka yake yi yana fatan 'yarsu guda da suka Haifa Hanifa tayi koyi da irin d'abi'un mahaifiyar ta.


A nutse ta zubawa kowa nashi abunci Hanifa ta mi'ka musu sannan ta d'auki NATA ta matsa jikin bango ta jingina bayan ta tafara ya futar abunci Hanifa Sam bata damu fa cin abunci ba shiyasa kullum cikin ta a shafe duk da yake haka hallitar ta take shine dalilin da yasa ma sharp dinta ya futa sosai.


Abbu ya janyo 'karamar redion sa dake aje gefe 'kokarin kamo Tasha yake yi Don a dai-dai wannan lokacin tashar redio ta Marhaba suke sanyo Tambihi daga bakin malam Ibarahim daurawa Abun mamaki yana kunnawa d'akin ya karad'e da wa'kar *'Kwalelen ku!*
Abbu yayi saurin murd'e redio yana mamakin yau mai ya hanasu sanya tambihi kamar yanda suka saba sanya wa dai-dai wannan Lokacin.

Lokacin da Abbu ya murd'e redion Hanifa ji tayi kamar tace ya bar mata wa'kar zata ji domin Lokacin har tsigar jikinta ta fara tashi sai ta kasa cin abunci ma gabaki d'aya ita dai Allah ya sanya mata son wa'kar babban abunda yake 'kara dilmiyar da ita shine muryar mawa'kin yana 'kara burgeta!

Abbu ya fara neman tashar express redio nan ma a dai-dai Lokacin suna sanyo tafsiri daga shaik Malam Nasidi Abubukar goran dutse, nan ma wa'kar *Kwalelen ku* ce take tashi, Ammi ya kalla cike da mamaki yace." Kinji fa wani sabon mawa'ki sha'kiyi mara abinyi yana wata wa'ka gashi duk ya hana tashoshi yin abunda ya dace."

Ammi tace"Ai Abbu yanzu wa'ke-wa'ke yayi yawa a duniyar nan wallahi sai addu'a." Abbu ya gyada kansa cike da dumbin mamaki shi a ganinsa bai ga amfanin sanya raye-raye da kad'e-kad'e da tashoshij gidan redio suke yi zai fi kyau su dunga sanya karatun al'kurani mai girma wa'azi daga bakin masana malamai magada annabawa sannan su maida hankali gurin wayar da Al'umma kai su mai da hankaki gurin kawo labarain abunda zai amfani al'ummar musulmi da sanin me duniya take ciki ana tunanin yana ganin haka zaifi kyau..... A takaice dai Abbu sai da ya kamo tashoshi uku yana so yaji abunda suka saba yi a lokacin sai yaji tashin wa'kar *Kwalelen Ku* 'k'arshe dai Abbu kashe redion yayi domin shi yafi amfani a gare su baki d'aya, shi saboda tsantsenin sa tv ma bai yarda da ita a gidansa ba sai redio kawai.

Hanifa taji wani irin a zuciyarta da Abbu ya kashe redion Allah-Allah take ya gama cin abincin ya futa ta dauki redion ta kunna ko Allah zai sa su 'kara sako wa'kar, Mi'kewa tayi ba tare da taci abincin kirki ba ta futa domin wanko hannunta duk suka bita da kallo

Wanke hannunta tayi ta zauna gefan rijiya tana matse fuska hawaye ne yake so ya zobu tana 'kokarin mai dashi...... Nasiru ya 'karaso gurin tsugunawa yayi kusa da ita a hankali yace." Hanifa zaman me kike yi anan gurin."? Kallonshi tayi ta dauke fuskarta yace." Taso mu koma ciki kinji 'yar 'kanwata." Ma'ke kafad'a tayi tana zum'bura baki. Nasuru yaji wani irin yanayi a jikinsa Hak'ika yana yiwa yarinyar wani irin so a cikin jini da jikinsa yana ganin itace mahad'in rayuwar shi.

Marairace fuska Yayi yace." Ki taso kinji ko Yanzu Abbu zai futo kar ya ganki a zaune a gurin nan nasan sai yayi miki fad'a ni kuma abunda bana so kenan bana so in ga hawayen ki."

Mik'ewa tayi a nutse shima ya mik'e Yana fad'in "Muje kici abunci idan ma bakya so to ki fad'i abunda kike so ni zan siya miki yanzu kici kinji ko." Gyada kanta tayi suka shiga cikin d'akin a tare.

Khalid kuwa yana koma wa gida ya shige part dinshi a wahalce ya zube kan bed ko takalmin 'kafarsa bai cire ba rintse idonsa yayi yana 'kara tuno siffar yarinyar Lokaci guda joystick dinshi tana 'kara mi'kewa da sauri ya jawo wayar shi ya bud'e idonsa da suka koma kamar garwashin wuta saboda ja pictures din 'yan mata ya bud'o yana gani gasu nan wasu tsirara haihuwar uwarsu wasu kuwa da sitturan jikinsu gwara babu haka ya dinga kallonsu yana murkususu da sakin ajiyar zuciya, sai da yazo kan pictures din Hanifa ya 'kara jin joystick dinshi na 'kara yin 'karfi tana mi'ke wa da sauri yayi ruf da ciki ya rungume wayar jikinsa yana jin kamar Hanifa din ya rungume ya dinga wani irin nishi duk minti goma yana cikin wannan hali kana ya samu yayi realising duk ya fashe screen din wayar tashi domin 'karfin shi duka ya sake jikin wayar. Luf yayi kan bed d'in yana mamakin kanshi tunda yake kalle-kalle kallon pictures ha'de da kallen kalleni blue films da ba sosai yake yi ba, bai ta'ba samun satsyfiend irin na yau ba lallai yau ya tabbatar da cewar Yarinyar Ya Shaik shaid'aniya ce







*19/12/2019*

_BintuUm@rAbb@le_
[12/20, 9:23 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*



*FREE PEGE*


*12*


A ranar Nasiru shine ya wanke wa Hanifa kayan makarantar ta da suka jike da ruwa tsaf ya shanyan su a igiya, Ammi babu yanda bata yi ba kan ya barshi amma ya 'ki dole haka ta hak'ura ta kyaleshi ita kam Hanifa tana'kule kuryan dakin Ammi takaici duk ya ishe ta saboda kwata-kwata Abbu ya 'ki futa yau tana juyo shi Yana fad'awa Ammi cewar yau bazai futa saboda danshin ruwa, ba'kin ciki har sai da ta zubar da hawaye kafin bacci ya dauke ta.


Misalin 'karfe d'aya shaura na dare ta farka shiru gidan duk sunyi bacci a hankali ta sakko daga kan gadon ta kunna Fitilar d'akin lokacin akwai wutar NEPA Ammi take dubawa sai taga bata d'akin, da sauri taje ta dauko redio ta kunna a hankali ta rage murya sautin shuuuuuuu! kawai taji a tashar da ta kamo da sauri ta murd'a tashar marhaba Karatun Alk'urani suke yi alamun zasu rufe tashar su sai kuma gobe.

Jiki a sanyaye ta murd'a tashar express nan ma shuuuuuu! Kawai take yi, dangwarar da redion ta yi ta fad'i kasa! da sauri ta dauke ta tana tsoron kar Ammi ta futo daga dakin Abbu redion ta mayar inda take ta koma ta kwanta tana kokarin yin kuka ita duk a tunanin ta a lokacin dare baiyi ba sosai haka tayi wani irin bacci Mara dad'i Wanda yake cike da mafarkin Khalid da kuma tunanin wa'karta ta 'kwalelen ku.

Ko da ta tashi da safe sam babu wani kuzari a jikinta kamar yanda ta saba duk Ammi na lure da ita ta zauna suna gaisawa Nasiru ya shigo dakin da kayan makarantar ta a hannunsa ya goge su tsaf!

Mika mata Yayi da murmushi a fuskar sa yace." Gimbiya kin tashi lafiya." ? Bubu walwala a fuskarta tace"Ya Nasiru ka goge min unporm din ne."?

Ammi tace"Ba ma guga kadai ba har wankin shine yayi miki jiya Tunda kika jikasu cikin bokiti ki kamanta dasu abunda baki taba yi ba, na lura akwai abunda yake damun ki tun jiya."


Hanifa taji gabanta ya fad'i a yanzu ne ta tuna da ni'kaf dinta Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Yanzu yaya zata yi wace irin 'karya zata yi tasan yanzu Abbu zai futo kuma har ta tafi makaranta yana zaune dakin Umma.


Jiki babu kuzari ta shiga dakin da kayan a hannuta ta shirya tsaf ta futo ta zauna Ammi ta mik'o mata kunun gyda cikin wani jug sai soyayyan dankalin Hausa da yaji a hankali take karb'ar kunun tana addu'a Allah yasa kar Abbu ya futo yanzu, aikuwa Addu'ar ta bata kar'bu ba Abbu ne ya futo daga d'akinsa yana sanye da doguwar jallabiya fara tas da ita da hular sa fara mai raga-raga tsaf ya taje dogon gemunsa kana ganin Abbu kasan cikakken Dan a halin sunnah ne. hannunsa rike da wani littafi na addini daya hannun kuma yana goga asuwaki a bakinshi
Nasir yayi saurin fad'in"Barka da asubah Abbu."

"Barka kadai malam Nasir ka tashi lafiya".?
Abbu ya fada Yana shigowa cikin dakin sosai.

Nasir yace." Alhamdullahi Abbu dama yanzu nake so in shiga gurin ka sai gashi kuma ka futo. "

Ammi ta gyara masa gurin zama ya zauna hankalinsa kan Nasir din yace." Masha Allah gashi na futo malam Nasiru Allah yayi maka albarka."

Nasiru ya sunkuyar da kansa cikin jin dad'i yake amsawa da "ameen." Hanifa ta 'karasa kusa da Abbu din a nutse tace"Abbu Ina kwana."?

"Lafiya k'alau Hanifa kin tashi lafiya."? Kanta a 'kasa tace" Lafiya Abbu yace." Zakije makaranta ko."? Daga kanta tayi cike da fargaba yace." To Allah ya bada sa'a maza tashi ki tafi."

Mik'ewa tayi ta fara kokarin futa.Ammi tace "Ina ni'kab din naki kuma."!? Take ta sunkuyar da kanta cikin rawar baki tace." Jiya garin sauri ya fad'i a hanya."!

Abbu ya kalleta a nutse yace." Ki koma ki zauna sai gobe idan Allah ya kaimu sai kije makarantar insha Allah za'a sayi wani."

Ammi dama tasan Abbu bazai ta'ba barinta ta futa babu wannan abun ha, don haka bata damu ba,to itama Hanifar bata wani damu sosai ba ta godewa Allah sosai yanda 'karyar ta ta samu mazaunin gurin Abbu baiyi wani musu ba.

Cikin d'aki ta koma tayi kwanciyar ta ba tare da ta tube uniform din ba bacci me nauyi ya dauketa kasamcewar jiya baccin da tayi bashi da wani yawa.


A shirye ya futo daga part d'insa kai tsaye part din iyayen sa ya nufa. Alhaji Tijjani yana tsaye bakin kofar futa suna magana da Mami da Allah futa zaiyi shi kuma ya shigo parlor.


Dukuninsu suka amsa masa sallamar da duk suka maida hankalin su kansa. Ya kalli mahaifin nasa tare da fad'in"Dady yau din nan fa nake so na wuce legos akwai wani buki da aka gayyace ni."

.Alhaji Tijjani yayi murmushi cike da 'kaunar Dan nasa ya dafa kafad'un da tare da fad'in"Yaro na a ko da yaushe ni na kasance mai yi maka fatan alkairi da samun nasara a rayuwar ka INA yi maka fatan dawowa lafiya."

Khalid yace." Ameeen my dad nagode dad duk inda nake INA afahari da kai."

Rungume juna suka yi cike da farin ciki Mami na tsaye tana kallonsu fuskarta dai futar da annuri take yi. Cike da farin ciki Dady din yayi musu sallama ya futa.

Hannunshi Mami ta ri'ke suka shiga cikin had'ad'an parlor su Wanda ya gaji da had'uwa Kai tsaye daining teble suka wuce Khalid sai wata irin sangarta yake yi, ya zauna kan kujera Yana zumb'ura baki kamar wani yaro 'karami. Yace." Wai momy me zaki min ne."?

Tana 'kokarin hada masa abunci tace"gata zanyi maka saboda na San halin ka da wasa da ciki, yanzu idan ka futa yawon wa'ke-wa'ken ka kuma sai Allah mybe ma ka zauna da yunwa."

Lumshe idonsa yayi ya bude cike da 'kaunar Mamy d'insa yace." Wallahi kuwa mamy kamar kin sani yanzu ina futa studio zan nufa kai tsaye."

Mamy tace"Bukin aure ne ko na haihuwa."? Yace." Mamy wani friend dina ne d'an uwan shi zai yi aure shine wai Dole sai nayi musu wa'ka kin San wa'kar da nayi ta biyu ta cika duniya to shine tun jiya yake damuna da kiran waya wallahi Mamy nake fad'a miki tun safe jama'a suka dame ni da kiran waya mutane har ban san iya kacinsu ba ni da kashe wayoyina na huta."


Murmushi kawai tayi tace." Myson tunda ka riga ka za'bi wannan harkar dole zaka yi ta fama da jama'a dole kayi hakuri dasu ka dunga sauraron su.


Tsaki ya d'an ja hade da Sosa kansa yace." Mamy na sani wallahi kuma ni damunsu bazai sa in fasa ba, domin har kar wa'ka yanzu na fara ta saboda INA da ra'ayin ta ba don kudi ko wani abu ba.''

Tace"To Allah ya shige mana gaba." Ameen yace ya fara cin abunci cike da yanga kamar yanda ya saba ya kammala tsaf ya mike daga gurin part d'insa ya nufa domin shirya shiga studio, kafin ya wuce Lego's din kamar yanda ya fad'a




*20/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/20, 10:20 AM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*




*FREE PEGE*



*13*



Kafin sallahr Hanifa ta tashi daga nannauyan baccin da ya d'auke ta, ta tashi da wani irin 'bacin rai mara dalili haka ta futo ta shiga kicin inda Ammi take ta hidimar girka musu abincin rana.

Tana zun'bura bakinta tace"Ammi da akwai ruwan zafi."? Ammi ta d'ago kanta tana kallonta nazarin fuskarta take yi daga bisani tace"Da akwai wai ke fushin me kike yi ne tun jiya da kika shigo na fuskanci kina da damuwa."

Hanifa ta fara marmar da idonta inda gashin idonta ya fara tsane ruwan hawayen da ya fara zubo mata.

Murya na rawa tace"Ammi babu komai ni." Ammi tace"Ban yarda ba Hanifa domin ba haka yanayin ki yake ba, amma dai maza je kiyi wankan ki futo kiyi shirin makaranta domin d'azu Abbu ya kawo miki wani ni'kab din idan kin dawo sai muyi maganar."

Hanifa ta wuce ta dauko bokitin da suke wanka ta zo ta siyayi ruwan zafin dake cikin Fula's taje ta had'a band'aki ta shiga tana kwa'be kayanta tana kuka.

Tsugunawa tayi ta hade kanta da gwiwa tana kuka wani irin fleengs na taso mata Wanda ta rasa gane ko na meye ita tunda take a rayuwa bata ta'ba shiga irin wannan halin ba sai da zuciyar ta ta fara son shi, fuskarsa kawai take hangowa lokacin da ya cire mata ni'kam ita kam a yanzu bata 'ki ta sake ganinsa ba domin idonta baya gajiya da kallon kyakyawar fuskarsa, wanka tayi ta futo Ammi ta kura mata ido ganin yanda idanunta suka kumbura nan Ammi ta tabbatar kuka tayi a band'aki

Ammi ta soma shiga damuwa da lamarin tabbas abunda zai damu Zuciyar Hanifa har ya sata kuka ba 'karami bane da sauri ta had'a mata abincin cikin k'aramin plate ta nufi dakin dashi


Shashshekar kukan taji Cikin Uwar daki, tayi saurin aje plate din ta nufi dakin. Hanifa na tsaye da uniporm a hannu ta kasa sawa kuka take yi.

Ammi ta rungume ta ta baya suka zauna kan gado bubbuga bayanta take yi tana rarrashinta tayi shiru da kyar ta samu tayi shiru tace"Yi hakuri ki fad'a ko menene kiji Hanifa ni mahaifiyar ki ce insha Allah zan nema miki mafuta.


Hannu tasa tana goge fuskarta cikin shagwaba tace"Ammi ni bab....fa babu komai. " girgiza kai Ammi tayi tace"ban sanki da 'karya ba Hanifa ki fad'a min kin jiko."?

Shiru tayi tana jin kunyar fad'a mata Ammi tace"ke nake sauraro ."? Da 'kyar tace." Ammi son shi n.....shuru tayi tana jin wata irin fad'uwar gaba.

Ammi tace"To kinyi shiru ki karasa mana." Ammi dama shine ummm sonshi ne ke."! Ammi taji wata irin fad'uwar gaba ta rikito mata wato dama soyayya ce ta sauya mata hanifa lokaci guda ikon Allah lallai akwai matsala domin dai ta Dade da sanin alk'awarin da Abbu ya dauka a kanta ita da Nasiru


Jiki a sanyaye Ammi tace"Waye shi wanda kike so kika hana kanki walwala da nutsuwa saboda shi.''?

Hannu tasa ta rufe fuskarta dashi tace"Ammi nima ban San shi ba kawai dai ina ganin shine a cikin unguwar nan ko kuma in ganshi gurin Ya Abbakar yayansu Asalamiyya. "

Ammi tayi jugum! Tana mamakin wannan al'amari ajiyar zuciya ta sauke tace"Hanifa bana son Abu yayi nisa dake da wanda kike so din ina so ki cire sonshi kwata-kwata daga cikin zuciyar ki domin kin San Abbu ya riga da yayi miki miji Dan uwanki Nasiru mai kaunar ki bana son abunda zai d'aga mana hankali dani dake gaba d'aya kiyi gaggawar cire Wanda kike so daga cikin zuciyar ki shine maslaha."!

Wani irin kuka take yi tana bubbuga 'kafafunta kan gadon tace" Um!um! Ammi ni Wallahi bana son Ya Nasiru shi nake so! Nace ni dai shine Wanda nake so Ammi ni bazan auri Nasiru ba.''!

Ammi ta bita da kallo cikin d'umbin mamaki! Tunda take da Hanifa tun tana yarinya kawo wa girman ta bata ta'ba bujere mata ba akan wata magana tata komai ta umarce ta dashi da sauri take bari Hanifa tana da ladabi da gudun 'bacin ransu yanzu akan wani d'an banza take kuka har tanayi mata musu kan maganar ta tabbas akwai babban aiki a gabansu.

Ammi ta rirrike ta ganin yanda take turje-turje a kan gadon duk ta ya mutsa shimfudar gadon tace"Kinga Hanifa saurare ni tukkuna kiji abunda zan fad'a miki kiyi shiru kiji magana ta dai na kuka kiji."!!!

Hanifa na kuka tace"Ammi nifa tun wuri Ku warware wannan alk'awarin naku daku ka dauka akaina da Yaya Nasir dama ba tun yau ba na lura yana sona ni wallahi ko mutuwa zaiyi bazan aure shi ba."

Ammi taji wani irin yammm! A jikinta abunda bata saba ji ba yau shine take ji daga bakin Hanifa tace"Hanifa ni kike fad'awa magana irin wannan."?

Zumb'ura baki tayi kamar yanda ta saba ta cigaba da kukan ta.

Ammi ta gyda kanta tana tu'ajibun wannan al'amari ita Sam bata ji da ita Abbu take ji idan yaji bada'kalar dake kokarin rufto musu.

Tace"To tashi ki shirya zuwa islamiyya tunda kin ki saurara ta kin san dai yanzu Abbu zai shigo ko."

Shuru Hanifa tayi mata Ammi ta dinga kallonta cike da mamaki! A rayuwa bata yiwa Hanifa magana biyu magana daya take mata take bin umarnin ta saboda ladabi amma yanzu lokaci guda wani d'an banzan Yaro ya sauya ta lokaci guda Ammi taji tayi masa wata irin tsana! Mara misali

A takaice dai sai da Ammi tayi wa Hanifa magana ya kai sau biyar sannan ta mi'ke tana zumb'ura-zumbuarn baki ta fara sanya Uniporm din ta.




*20/12/2019*
_BintuUm@rAbb@le_
[12/20, 11:01 PM] .: *MASHAHURI!*




*Ga masu ba'katar cigaba da karanta wannan book d'in zasu biya kud'in karatu #300 kacal ta wannan account d'in.....0542382124 BINTA UMAR GT bank...... Ko kuma Ku same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Insha Allah sai in fad'a muku yanda za'ayi Ku biya*

*Mutanan Nijar kuma idan suna bu'kata suma zasu tura katin waya orange ko Airtal ta wannan numbars 90899076_88137740 dala d'ari itace a madadin 'Dari uku na Najeria, MASHAHURI MAWA'KI ko da 'kud'in ka sai da rabon ka.!!!!!*




*FREE PEGE*


*14*



Sama-sama taci abunci ta mi'ke ta futa.
Ammi ta bita da kallo tana bin plate din abuncin da kallo Hanifa ko Rabin abincin bata ci ba tazo ta dauki jakarta ta dauki ni'kaf din tana d'aurawa.

Ammi tace"Kina so ki jawowa kanki matsala da damuwa wato kina nufin wannan abincin da kika ci ya ishe ki kenan? Ina kallon ki fa bai fi loma hudu kika yi ba."

'Kokarin sanya safa take a 'kafafunta tace"Ammi na 'koshi ni sai na dawo zanci." Tana ya mushe fuska ta fad'i maganar .

Ammi tayi shuru kawai tana binta da kallo cike da mamaki har ta gama sanya safar ta futa daga gidan ba tare da tace sai ta dawo ba kamar yanda ta saba kullum idan zata tafi makaranta sai tace ammi sai na dawo ita kuma Ammi tayi mata fatan dawowa lafiya.

Ammi ta jima a zaune a gurin tana mamakin al'amarin Abbu ya shigo ya same ta, Lokacin kuma tayi kokarin dai-dai ta kanta domin bata son mijinta ya fuskanci akwai matsala.

Hanifa kuwa na tafiya hanya tana sa'ke-sa'ke cikin zuciyarta ita fa duk yanda za'ayi baza ta yadda ta auri Ya Nasiru ba domin kwata-kwata bata jin sonsa ko d'aya a cikin zuciyar ta sai dai 'kaunata ta 'yan uwanta ka.

Sai da tazo kusa da gidan su Asalamiyya sannan ta d'ago kanta gabanta yayi wata irin fad'uwa! Ganin shi tsaye samarin matasan unguwar sun kewaye

1 Comments On MASHAHURI
avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

39901

Please Login or Register in order to submit comment