Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ace ki kulle kanki a d'akiba kuma kina cikin damuwa waye zaki fad'awa kiji dad'i.
Ga kuma jikin naki har yanzu be gama warwarewaba.


Jin maganarsa yasa ta'kara fashewa da kuka, da kamar bazata tanka ba barantana ta bud'e amma sai wata zuciyar tabata shawarar ta bud'e kawai.

Haka tatashi jiki ba laka ta bud'e 'kofar, ganin yanda idanunta suka kad'a sukayi ja, ya tabbatarmashi da ta dad'e tana kukan, wani irin tausayinta ya dira a zuciyarshi, kama hannunta yayi suka koma cikin d'akin ya zaunar da ita gefen gado sannan shima ya zauna dai-dai wannan lokacin kuma idanunsa suka sauka kan trolley data had'a kayanta ciki.

Juyowa yayi ya kalleta da mamaki a fuskarsa, yace "wannan jakar kayanfa lafiya dai.
Shiru tayi dan batasan irin amsar da zata bashiba.
Saida yakuma tambayarta karo na biyu tare da ru'kota yana 'ko'karin had'a jikinshi da nata,

Saurin kwacewa tayi tare da mi'kewa tsaye tafashe da wani sabon kukan, tana ja da baya kamar tana tsoron jabeer d'in.

Da mamaki shima ya mi'ke yana tunkararta "Haba Hussaina danmi kike guduna baki 'kaunar inta6a jikinki ko kad'an amatsayina na mijinki...........


"Kaiba mijina bane jabeer, haka kuma niba matarka bace, matarka ta mutu tsawon wata ukku dasuka wuce,

"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un jabeer yafad'a "Hussaina anya kina cikin hayyacinki kuwa, nine yau zakice ba mijinkiba,
ba shakka lallai 'kila kinfara irin shaye-shayennan na zamani.......

"Ko d'aya jabeer ban ta6a shan komeba, kuma dukkan abinda nafad'ama cikin hankalina nake......

Yanzu zanbaka labarin abinda baka saniba, koda kuwa yin hakan nima ze zama 'karshen rayuwata kamar yanda 'yar'uwata tabar duniya.

Wani sabon kuka tafashe dashi, saida tayi me isarta tayi shiru dan kanta batare data samu me rarrashintaba, saboda jabeer yariga ya shiga wani hali, so yake kawai yaji asalin gaskiyar abinda tafad'a wanda zesa ya yarda cewa ita ba matarshi bace kamar yanda tafad'a.

Nan ta kwashe labarin abinsa suka ahirya tsaf da Hussaina lokacin tana raye, na zamanta gidan amatsayin Hussainar wanda daga tafiyarne bata dawoba sai dai aka kawo gawarta, amma bata gaya mashi wacce takashe Hussainarba, sannan kuma bata gayamashi cewa gurin tsohon saurayinta tajeba, tadai gayamashi taje bikine kamar yanda ita Hussainar tagayamata.

Saukar wani wawan mari taji a fuskarta, wanda har saida taga wasu taurari, dafe kuncinta tayi ta zube 'kasa tana kuka,

Shima jabeer d'in hawaye yake, yarasa inda zesa kanshi, innalillahi kawai yake mai-maitawa, yana fad'in *Allahumma ajirni fi masibati wa khalibli khairan minha*

"Hassana kin cuceni, kinsa na aikata abinda banta6a aikatawaba, amma ai Allah yana gani batare da sanina na aikataba, komiye kece sila.

Hassana dai bata 'kara maganaba tun marin dayayimata kuka kawai take tana dana sanin amincewa da 'kudirin 'yar'uwarta.

A fusace jabeer ya d'auki trolley data had'a kayan yakai mota, sannan yadawo ya figeta itama ya bud'e motar yajefata kamar wasu kayan wanki, sannan yatayar da motar yafara dokama megadi horn, da gudu yazo ya bud'e masu get jabeer ya kwashi hanya da gudun tsiya.






Love u all my Fan's 👄💞
[2/12, 12:46 PM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................47



® _TALENTED WRITE R'S GROUP_ _(TWG)_ 📝


Wani mummunan fad'uwar gaba Hassana tayi lokacin dataga jabeer yayi parking cikin harabar gidansu, amma a zuciyarta saitaji ta dake akan kome ze faru 'kara ya faru da zaman datake, wanda ita kanta batasan makomarsaba.

A fusace jabeer yafito daga motar sannan ya bud'e but ya d'auko trolley yanufi cikin gidan beko kalli inda takeba.

Da sauri tabi bayanshi tana sharar hawaye har tana had'awa da d'an gudu-gudu.

Momy da daddy suna zaune falo suna kallon labarai a tashar aljazeera, suka jiyo sallamar jabeer, daddy ne ya amsa yana 'ko'karin fita yaga jabeer d'in yashigo janye da trolley, komawa yayi ya zauna yana kallon jabeer cike da mamaki harya 'karaso yasamu guri ya zauna dai-dai saitin 'kafar Daddy yana matsar kwalla.

Cike da alamomin tambaya Daddy ke kallon jabeer, Momy ma da alama hakanne a fuskarta.

Suna shirin tambayarsa saiga Hassana tashigo da kuka share-share a fuskarta, kamar wacce aka jeho tafad'i gaban Momy da Daddy tana cigaba da kukanta.

Daddy ne yayi 'karfin halin tambayarsu "lafiya meke faruwa kukazo haka birkice, wani kuka Hassana ta'kara fasawa dan tasan yau kashetane kad'ai Daddy bazeyiba, amma ta kwammace hakan da zaman datake a gidan jabeer.

Suduka ba wanda yayi magana, shima jabeer d'in hawayene ke zarya a kumatunsa, yama rasa ta inda ze gayama Daddy abinda ke faruwa.
Daga 'karshe dai yayi 'karfin hali ya kalli Hassana yace "ki maimaita masu abinda kika fad'amin.


Daddy ya watsa mata wani kallo wanda yasa saida Hantar cikinta ta juya, sannan tayi saurin saddar da kanta tana hawaye, dan tasan babu wasa ko kad'an tattare da Daddy saboda haka batare da 6ata lokaciba ta fayyace masu kome kamar yanda tafad'ama jabeer kafin suzo nan.


Lokaci d'aya Momy da daddy suka saka salati, kafin Daga bisani d'akin yayi shiru bakajin kome sai sheshshekar kukan Hasaana, wacce jira take kawai taji anrufeta da duka, dan tasan ta caccanci abinda ma yafi haka.

Duk zafin Daddy da d'aukar matakinsa kan abu, yau kasa koda motsi yayi, sai Momy ce tayi magana "Amma Hassana baki kyautaba, itama abinda kawai ta iya fad'i kenan tayi shiru.

Mi'kewa daddy yayi tare da d'aukar makullan motarsa ya kallesu yace "kutaso ku dukanku ku sameni a mota, yana gama fad'i yayi gaba da sauri yabud'e motarshi yashige zuciyarsa cunkushe da ba'kinciki da takaici.

Minti biyar ba'ayiba sai gasu sun fito, gidan gaba Daddy ya umarci Jabeer ya zauna Hassana kuma da momynta baya.
Sannan daddy ya tayar da motar, Malam bala me gadi yabud'e masu get da sauri yana masu Allah kiyaye.


** ** **


Zaune suke gaban wani dattijon mutum Wanda kallo d'aya zakayima fuskarsa ka tabbatar da kamala da ilimi tattare dashi, dan ya ajiye sunnah a fuskarsa (gemu) bayan sun gaisa Daddy yayi Mashi bayani dukan abinda ke tafe dasu.

Malam Kasim yayi matu'kar mamakin jin wannan abu daya faru amma dayake shi addini me saukine kuma ya kawo yanda za'a warware kowace matsala saboda haka yafara yimasu bayani bayan yayi addu'a da salatin annabi (s.a.w)


"To kamar yanda kuka Sani tunda ita wannan yarinya dama ba matarsa bace bamu bu'katar ace sai yasaketa, amma tunda har wani abu na mu'amalar auratayya yashiga tsakaninsu, to zatayi istibira'i idan tagama zata iyayin aure.
*(Istibira'i yana nufin zama da wacce tayi zina takeyi a gida na tsawon wasu watanni batare data 'kara kusantar zinaba, dan ta tsarkake kanta kafin tayi wani auren)*

Nan sukayima Malam godiya sannan suka koma gida, Hassana tayi matu'kar mamakin yanda iyayenta suka kar6eta batare da sun nuna matsanancin fushi akantaba.

Tayi mamakin yanda Daddy ya umarci data wuce d'akinta tayi wanka kuma tacigaba da istigifari domin shi Allah gafurun rahimunne.

Haka tawuce d'aki sukuku kamar kazar da kwai ya fashemawa a ciki.
Tana shiga d'akin kuwa tafad'a kan gado tafashe da wani sabon kuka dan tunowa datayi da Hussaina wacce tare sukayi rayuwa a d'akinnan amma yanzu gashi bata raye.
Zuby tafad'o mata arai, a zuciyarta ta rin'ka banka mata Allah ya isa dan duk halin datashiga itace sila, sannan kuma taraba 'yar'uwarta da duniya.






Love u all my Fan's 👄🍛
[2/19, 7:07 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................48




® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝



*Bayan Sati Biyu*

Zaune yake yahad'a uban tagumi duk abubuwa sunbi sun dagulemai, ba abinda yake tunani sai tsawon lokacin da suka d'auka suna zaman aure da Hassana wadda duk a tunaninsa Hussainace wai ashe Hussainar ce ta mutu ba Hassanaba, wasu siraran hawaye suka zubo kan kumatunsa, beyi 'ko'karin gogewaba haka yabarshi yanata zuba wani na bin wani.

Sallamar da ake dokawa daga bakin 'kofar falon ce tasa yayi saurin goge hawayen dake fuskarsa tare dayin 'karfin halin amsa sallamar.

Yauma kamar kullum sanye take cikin irin matsiyatan kayan data saba sanyawa, duk illahirin surar jikinta a bayyyane take.

Da mamaki yabita da idanu yana kallonta ganin wani shu'umin murmushi datake sakarmai, kafin yayi magana ta ida 'karasowa cikin falon ta zauna kan d'aya daga kujerun dake zagaye da falon sannan ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya kafin tafara magana.


"Da farko dai jabeer ina 'kara yima ta'aziyyar matarka Hussaina data rigamu gidan gaskiya, sannan kuma ina jajantama game da cin amana da suka 'kullama tsakaninta da 'yar'uwarta sukasa kayi *AUREN TAGWAYE* batare da saninkaba.

Ta numfasa sannan taci gaba da magana "kada ka damufa da wannan Allah be ta6a kama bawansa da laifin da besaniba _(niko zee nace kaji su zuby kamar ansan Allah)_

Jabeer kuwa tunda tafara surutunta 'kala be cemataba ita kad'ai keta zuba shikuwa binta kawai yake da ido.

Tasowa tayi daga inda take zaune tana wani girgiza tana rangaji harta 'karaso gabanshi ta dur'kusa.
"Jabeer akwai wata magana danazo da ita amma bansan ya zaka d'auketaba.
Tayi shiru tare da zubamai mayataccin idanunta alamar tanason jin tabakinsa kafin tacigaba.


"Ina jinki kawai jabeer yabata amsa atakaice sannan tacigaba damagana,

"Jabeer na dad'e ina dakon soyayyarka acikin zuciyata tun kafin ka auri Hussaina, ganin tana aminiyata yasa na ha'kura ban ta6a nunamaba, domin masu iya magana sunce ana barin halak kodan kunya, amma yanzu tunda babu ita, kaga zaka iya aurena in mayema gurbinta, kuma..........

Saurin d'aga mata hannu yayi "dakata dan Allah zuby, yafad'a cikin 'kunar rai, dan tunda tafara magan-gamunta jiyake kamar tana watsa mashi garwashin wuta acikin zuciyarsa.
"Kada ki kuma tunkarata da wannan maganar danni yanzu ba abinda ke gabana kenan ba, zuby kisani na tsani rayuwa da wata mace a yanzu saboda haka kada kisa ran zan iya rayuwa dake.......

Murmushi tayi "Hmm nasan ciwon abinda Hussaina tayimakane yasa ka furta wannan kalamin, amma mata ai mune abokanin rayuwa, babu namijin da baya bu'katar mace kusa dashi matu'kar yanada cikakkiyar lafiya.....


"Fita dan Allah, ki fitarmin daga gida kina 6atamin lokaci, yafad'a yana nuna mata 'Kofa,

Murmushin takaici Zuby tayi a zuciyarta tace "wannan wane irin zuciyane dashi tun bayan wata biyu dasuka wuce naketamai hannunka me sanda dan yagane ina sonshi, gashi har yau na bud'a baki na gayamashi sirrin dake raina amma gashi yana nuna halin ko inkula akaina, tabbass akwai aiki babba agabana.......


"Get out, maganar jabeer ce tadawo da ita daga dogon tunanin datake, wacce har saida tayi 'yar'karamar razana, sannan ta kalleshi ta jefeshi da murmushin takaici kafin tasa kai tafice daga gidan.


Tana fita yabi bayanta, megadi na zaune bakin aikinsa, ganin jabeer yasashi tasowa yana mashi barka da fitowa, fuska ba annuri jabeer yace "daga yau idan ka kuma barin wannan yarinyar shigowa gidannan bakin aikinka...

Me gadi yayi saurin dafe 'kirji tare da fiddo idanu waje, jin an ambaci aikinsa, jiki na kyarma yace "inshaAllah ranka ya dad'e hakanma bazata faruba.
Be tsaya sauraronsaba yakoma cikin gidan, yana Shiga falo yafad'a kan kujera, tinanin rayuwar da yayi da Hassana tafad'o mashi a rai.














Love u all my Fan's 👄🍧
[2/19, 8:15 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................49



® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝



Tundaga wannan lokacin Zuby ke zarya gidan jabeer amma koda wasa me gadi baya barinta Shiga, idan zatayi juyin duniyar nan be barinta, data gane haka saita koma zuwa office d'insa, nanma Haka ya gargad'i ma'aikatan gurin da kada akuma barinta tana shigowa, haka kuwa akayi dan akwai ranar datazo tundaga bakin get megadi yahanata shigowa, tayi magiyar tayi duk iya dabararta amma yahanata, kawai saita samu guri ta zauna tana kallon masu shiga da masu fita har bayan azahar bataga fitowar jabeer ba sai gurin 'karfe ukku sannan motarshi tafito, hannu rafara d'aga mashi Alamar ya tsaya, shi kuwa bemasan tana gurin ba.

Ganin be gantaba yasa tayi saurin tsaida me napep tanunamashi motar jabeer tace yabi bayanta,

Shikuwa besan tana binsaba, kai tsaye hanyar gidan iyayensa yanufa, dai-dai 'kofar gidansu yayi parking sannan yafito duk kan idanunta ya gaggaisa da mutanen dake gurin sannan yashige gidan nasu.

Bata fito daga napep d'inba wani yaro yazo wucewa takirashi, take tambayarsa ko nanne gidansu jabeer?

Yaron yabata amsa atakaice sannan ya wuce, nan ta umarci me bapep daya kaita gida tagaya mai unguwar suka d'au hanya.


*Bayan kwana biyu*


Zuby tsaye bakin titi jikinta sanye da riga da zani na atamfa wanda rabon datasaka kaya irin wannan harta manta, sai kuma madai-daiciyar hijab d'inda tasanya wacce ta sakko mata har iya gwiwa.


Me napep ta tsaida, sannan tafad'a mashi inda ze kaita, suna isa ta hango motar jabeer a 'kofar gidan haka ya tabbatar mata da yana cikin gidan, zaure ta tsaya tana fargabar shiga amma haka ta dake tayi ta maza tayi sallama, Maman jabeer dake duke bakin gurin tana alwala ita ta amsa sallamar.


Cikin ladabi zuby tashiga gidan, Maman jabeer tabita da idanu da Alamar tambaya tattare da ita dan bata ta6a ganin zuby ba.

Ganin yanda Zuby ke kakkare fuska da Alamar jin kunya yasa Maman jabeer d'in tayimata iso har d'aki, bayan sun gaisa take tambayarta "yarinya bangekiba,

Murmushi Zuby tayi "dama jabeer ne yace ze kawoni mu gaisa, to shine mukayi waya nake fad'amashi inanan gidan yayata nan 'kasan layinku sai yake sanarmani ai yana nan gidan in'karaso mu gaisa, takare maganar tana saddar da kanta 'kasa alamar kunya, dan tunda tazo bata yarda sun had'a ido da Maman jabeer d'inba.

Aiko Maman jabeer najin haka ta fahimci inda zancen yadosa, wani irin farin ciki ya lullu6eta, dama kullum fatanta be wuce jabeer d'in yayi aureba.

Kusan minti sha biyar Zuby na zaune tana jiran ko jabeer ze shigo amma be shigoba, hakan yasa tayi sallama da mama tace zata tafi.

Mama tace "tun yanzu baki bari jabeer d'in yashigo masallaci yaje, cike dajin kunya Zuby tace "ba kome mama sauri nake wallahi islamiyya zani nagama har lokacin yafara wucewa.

To ki gaida gida ki gaida mamanki kinji, "to zasuji inshaAllah tafad'a sannan ta fice daga gidan.

Bakin 'Kofa suka had'e da jabeer yana 'ko'karin shigowa gidan, ganin Zuby tafito daga gidan ba 'karamin tayar mashi da Hankali yayiba,

"Zuby meya kawoki gidanmu,? Ya tambayeta yana 'karemata kallo dan ba 'karamin kyau shigar datayi tayimata ba, murmushi tayi tace "meko ze kawoni idan banda tsananin so da 'kaunar danikema.

Dur'kusawa tayi gabanshi idanunta na zubar da Hawaye, "Dan Allah jabeer ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wallahi ina sonka ina 'kaunarka tsakani da Allah, nasan kasan zafin so, kasan rad'ad'in so, dan Allah kada kacema ummanka baka sona, dan nasamu kar6uwa a wajenta d'ari bisa d'ari dan Allah kaima ka kar6eni kamar yanda ta kar6eni.


Ganin yanda take kuka tana mashi magiya gashi hartasa hankalin mutanen gurin yafara dawowa kansu yasa wani irin tausayinta ya dirarmai a zuciya besan lokacin daya kama hannuntaba yabud'e mota ya sanyata sannan shima yashiga suka d'au hanya.

Tunda suka tafi ahanya yake aikin rarrashinta, amma ta'kiyin shiru saida ya amsamata daya amince ze aureta, wani irin dad'i ya lullu6eta, tunnan tafara zumud'i tana sanar mashi da bata son asa bikin nesa idan sonsamune ayi kome nanda wata biyu.






Love u all my Fan's 👄👍🏻
[2/19, 9:42 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................50



® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝



*BAYAN WATA UKKU*

Hidima ta kankama sosai dan ahalin yanzu saura kwana goma d'aurin auren jabeer da Zuby, 6angaren jabeer be wani farinciki dan jiyake kamar tilastashi ake auren zuby amma ko kad'an babu dai-dai da kwayar zarra na sonta acikin zuciyarsa,

Ita kuwa Zuby ta dad'e da sanyama ranta zama matar jabeer, tuni tafara tsara yanda za'a gudanar da program d'in bikin itada 'kawayenta, maganar gayya kuma ta dad'e da gama gayyato duka abokaninta maza da mata, program kusan kala bakwai ta tsara za'ayi a cewarta yanzune jabeer zeyi aure na kece raini saboda haka sati guda cif za'ayi ana gabatar da shagulgulan auren.

** ** **

Hassana ce kwance d'akinta, duk abin duniya yabi ya dameta ba abinda take tunani sai tsawon lokacin data d'auka gidan jabeer, cikin wannan zaman dasukayi ta la'kanci halayensa da dama ciki kuwa hada tsananin ha'kurin dake gareshi.

Juyi tayi ta gyara kwanciyarta zuwa rigin-gine ta 'kurama silin d'in d'akin ido tsananin so da 'kaunar jabeer na 'kara mamaye zuciyarta.

Wani 'kawataccen murmushi tayi, sannan tatashi zaune ta d'auko wayarta chat ta hau tana dubawa, wanda rabon data hau and'au lokaci me tsawo.

Best group d'inta tafara shiga na *Ciwon 'ya mace* tana duba d'umbun message d'inda ta taras kwatsam idanunta sukayi kaci6is da hotunan wasu amarya da ango da aka turo ana gayyatar duk wanda yasamu damar halatta, ganin yanda aketa maganar bikin da kuma yanda ake fad'in kalaluwan program d'inda za'ayi yasa taji tana sha'awar bud'e hotunan amarya da angon dan taga yayan wani hamshakinne ake gagatawa haka.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tashiga furtawa lokacin da idanunta sukayimata kaci6us da hoton jabeer da zuby.


Take wani irin gumi ya karyo mata, a hargitse tami'ke ta sanya hijab d'inta sannan ta sanya ni'kaf da safar hannu data 'kafa, sannan ta 'kara d'auko wayarta ta 'kara kallon hoton jabeer da zuby ta 'kara kallo Sannan tafara magana kamar Zuby na jinta "'karya kike Zuby, wallahi 'karyarki tasha 'karya baki isa ki kashemin 'yar'uwaba kuma ki auri mijinta wallahi saina d'au tsatstsauran mataki akanki.
Tana gama fad'in haka tafice daga gidan batare data nemi izinin Momy ko Daddy ba.


** ** **

Zuby kuwa kud'i ta amsa masu yawa daga hannun jabeer tasiyo kaya kusan kala goma wad'anda zata sanya gurin bikin, kowane kaya da jakarsa da takalminsa, yau sukayi da telanta zataje kar6ar d'inkunan saboda haka waya tafarayimashi ta tambayeshi ko ya'karasa, yacemata yagama ita kawai yake jira.

Wata 'katuwar hijab tasaka sannan tafita, dan tunda tasamu tashawo kan jabeer ta daina shigar banza, koma Tayi saita saka 'katuwar hijab.

Minti ashirin ya sadata da shagon *USMAN FASHION* Wanda ta yarda kuma ta amince da d'inkinsa dan babu wani tela dazemata d'inki taji dai-dai idan bashiba, ya kware a d'inkin mata, danshi baya d'inkin maza, lokacin data shiga shagon saida Hussaina tafad'o mata a rai dan itace ta nuna mata shagon telan sune nan daddy ke kawo masu d'inkinsu duka harda na momy.

*Wannan tallace ga babban tela USMAN FASHION shagonsa nanan cikin garin katsina sabon layi bayan tsohuwar refabulik Hotel, d'inkin mata zallah na Zamani atamfa, material, shadda, yakeyi, duk me bu'katar 'karin bayani zata iya tuntu6armu ta wannan no* 👇🏻

07037112229

*Usman Fashion yataso me maida tsohuwa yarinya* 👗👘💃






Love u all my Fan's 👄🍛
[4/13, 9:58 PM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................51



® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝



Bayan angama Had'a mata d'inkunan jabeer tayima waya akan yazo ya d'auketa, 'kofar gidansu ya sauketa sannan yaja motarsa yayi gaba da tsan-tsan kiyayyarta a cikin zuciyarsa,

Washe gari ya rage saura kwana tara d'aurin auren zuby da jabeer,
Zaune yake d'akinsa yahad'a uban tagumi hannu bibbiyu ba abinda yake tunani sai yanda ze zauna da Zuby amatsayin matarshi, ko kad'an bayajin sonta acikin zuciyarsa dai-dai da kwayar zarra, dan dai mamanshi kawai data nuna tsananin son auren shiyasa ya amince, besan me zuby tarika gayamataba kokuma takemata harta yarda da ita d'ari bisa d'ari kuma ta matsamashi akan sai ya aureta.

Wani guntun tsaki yaja gami da gyara zamanshi yajawo remote ya kunna TV lokacin ana labaran 'karfe takwas

*Da farko ga kanun labaran, ayau ne shugaba muhammadu buhari ya sauka gida Nigeria daga tafiyar da yayi zuwa 'kasar England, Gobene Al'kalin babbar kotun jihar katsina ze gabatar da shari'a tsakanin wata matashiya me suna Hassana Mansir Company inda take 'karar 'kawar 'yar'uwarta Zubaida wacce akafi kira da Zuby akan tana Zarginta akan kisan 'yar'uwa*.

A firgice jabeer ya mi'ke tsaye, yana mai-maita kalmar "Zuby takashe Hussaina, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, komawa yayi ya zauna hankalinsa a matu'kar tashe,
"Wannan bala'i dame yayi Kama? Anya zuby zata iya aikata kisan kai, meyasa Hassana takai zuby 'kara akan abinda batada kwakwkwarar sheda akansa, amma ita tasani Allah kaimu goben masu iya magana sunce duk wanda yace ze had'iye gatari sai asakar masa 'kota.




Da dare bayan daddy yadawo daga gurin aiki, bayan yasamu labarin shigar da 'karar da Hassana tayi, saboda duk illahirin garin ya d'auka Kowa Allah Allah yake gobe tayi suje kallo.

Momy yasamu zaune a falo ta buga uban tagumi, bayan tayimashi sannu da zuwa yake tambayarta "ina Hassana? "Tana d'akinta, momy tabashi amsa a ta'kaice, "kiramin ita, "to kawai tace ta mi'ke tanufi d'akin Hassana, Zaune ta isketa kan abin sallah da Qur'an a hannunta tana karantawa, domin samun nasara akan shari'ar daza'ayi gobe.

Da sallama Momy tashigo, bayan ta zauna gefen gado ta kalli Hassana "kizo daddynki na kiranki, "to ta amsa sannan tarufe Qur'an lokacin Momy ta dade da baro d'akin, a falo suka zauna itada Daddy

Please Login or Register in order to submit comment