Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tawa, murmushi Hassana tayi tace "Hmm kudakata aini banida 'kawa duk grouf dinnan kowama 'kawatace dan gaskiya kuna matu'kar burgeni kun iya zama da mutane.

A falo kuma momy ta kalli daddy Wanda ya maida hankalinsa kan jaridar dake hannunsa, tace "waini Alhj haka zamu zubama yarinyar nan ido tayita zama agida, kuma ita gashi tunda canma bata kula kowa barantana yanzu.

Shiru daddy yayi na kimanin mintuna biyar, itakuma Momy ta zubamai idanu tana jiran taji me zai fad'a.

Numfasawa yayi sannan yace "to me kike tunanin zanyimata kuma,?
Momy tad'an gyara zamanta "nida cewa nayi mezai hana tacigaba da karatunta kafin kuma muga abinda Allah zeyi.


Wani mugun kallo daddy ya watsama Momy wanda saida yasa hantar cikinta ta kad'a sannan yafara magana cikin d'aure fuska
"kada ki kuskura in 'karajin wannan maganar daga bakinki, koda zatakai shekara nawa a gidannan babu maganar cigaba da karatu, munanan tare da ita har lokacin dazataga dama tagfito da miji tayi aure.

Yana gama fad'in haka ya kwashe jaridarsa yawuce d'akinsa yabar Momy zaune sake da baki.






Love u all my Fan's πŸ“
[4/24, 6:32 PM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................57




Momy kuwa tunda daddy yagama magana yashige d'akinsa yabarta zaune a falo, tunani barkatai takeyi a zuciyarta tana ganin kamar shawarar data kawoma daddy batada makusa amma sai gashi yanda ya nuna kwata-kwata bazebi shawarar tataba.

Tayi zurfi cikin tunani taji kamar ana sallama a bakin 'kofar falon 'kara saurarawa tayi jitayi ankara doka sallamar mi'kewa tayi tare da amsa sallamar ganin maman jabir datayi yasa tasaki murmushi "a'a yau kune a gidannamu lale maraba sannu da zuwa, "yauwa tafad'a itama fuskarta d'auke da murmushi.

Bayan sun gaisa momy tacika gabanta da kayan sanyi, mama tazuba lemun tasha sannan ta ajiye cup ta maida dubanta ga momy "Allah sa dai Alhj yana gida dan maganace me matu'kar muhimmaci take tafe dani.

Numfasawa momy tayi kafin tace "eh yananan bari namaki magana dashi, sannan tanufi d'akin daddy kwance ta iskeshi ya kalli bangon d'akin da alama yayi zurfi cikin tunani, zama tayi bakin gadon sannan tasanar dashi zuwan maman jabeer,

Tare suka fito Alhj na gaba momy na bayanshi, zama sukayi baki d'ayansu a falon bayan daddy sun gaisa da maman jabeer nan take sanar dashi maganar dake tafe da ita na nemawa jabir auren Hassana, da kuma yanda jabeer din yasanar da ita jiya.

Murmushi Daddy yayi wanda ya nuna alamun farin ciki tattare dashi sannan ya numfasa yace "in banda abin jabeer aini matsayin d'a na d'aukeshi koshi da kanshi yafad'amun ai bazan hanashi jininaba inshaAllah babu wata damuwa, yanzu abinda yakamata shine yafara zuwa su fuskanci juna shida yarinyar,


Godiya maman jabeer tashigayi, tana yaba halin kirki da dattako irinna Alhj mansir, mutumne me tarin dukiya, amma Allah be d'oramashi girman kaiba, da raina talaka.
Haka sukayi bankwana momy tayimata rakiya har harabar gidan suna 'kara tattauna al'amarin yaran, da alama ita kanta momy taji dad'in hakan dan kowane iyaye zasuyi burin 'yarsu tasamu nagartaccen namiji kamar jabeer, mutum me ilimi da ri'ko da addini, ga kuma ri'kon amana.


** ** **

Sanye suke cikin kayan uniform kalar dark blue, matane zallah zaune suke cikin wani 'kazamin d'aki dan ba abinda ke tashi d'akin sai wani irin matsanancin wari, can na hango wata matashiyar yarinya zaune tahad'e kai da gwiwa da alama kuka take, itama sanye take da kalar uniform d'in jikin rigarta ansa number itace number ta sha takwas, wata 'katuwar mata nagani taje kanta ta tsaya ta ta6ota tana fad'in "yaya dai 'yanmata?
Ahankali wacce akayima maganar tad'ago ta kalli wannan wannan 'katuwar matar, fuskarta sharkaf da hawaye tayi wani ba'kikkirin duk ta rame, jin wannan 'katuwar matar takira sunanta "Zuby yadai yanaganki haka, zuby tasa hannu ta goge hawayen dake idanunta ta 'kara gyara zama batada niyyar yin magana.

Wannan 'katuwar matar dake tsaye ta gagga6e da wata mahaukaciyr dariya cikin muryarta wacce tafi kama data 'kato, saida tayi dariya me isarta sannan tadafa kafad'ar zuby tace "Haba zuby ke kullum kuka kamar ke kad'aice kiduba kiga fad'in wurinana kowa harkar gabansa yake amma ke kinsama ranki tunani kin'ki ci kin'ki sha duk kin lalace.

Kallo zuby tabi mutanen gurin dashi kowace kuwa harkar gabanshi yakeyi kamar ba gidan yari sukeba, sannan tamaida dubanta ga matar tace dole inyi kuka dole ci da sha ya gagareni, rai raifa nakashe, dole tun duniya inga sakayya ko zaman gidannan ma kad'ai bala'i ne.

Wata mahaukaciyar dariya matar tasake bushewa da ita "tace lallai yarinyar nan rayuwarki na 'Kazan ruwa, kowa tuba dan wuya ba lada, ni yanzu jiran lokacin daza'a sallameni kawai nake ind'ora daga inda natsaya.







Love u all my Fan's πŸ‡
[4/25, 8:13 AM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................58





Kallo kawai zuby tabita dashi dan tasan duk abinda tafad'a haka yake *Har a zuciya* na (Fiddausi so Dangi) amma itakam ayanzu tayi nadamar abinda ta aikata, gashi yanzu son abin duniya yakaita ya baro.

Suna cikin wannan maganar wannan katuwar matar taji an d'auketa da wani migun mari, waigawa sukayi bakin d'ayansu wata azzalimar 'yar sanda ce suka gani, dan Duk illahirinsu masifar tsoronta sukeyi har suna suka sakamata inspector zalima, ai da gudun tsiya wannan 'katuwar matar tabar gurin duk kuwa da uwar 'kibar dake jikinta.

Zuby kuwa saboda rashin 'karfin jiki kasa motsawa tayi daga wajen, hakan yaba inspector zalima damar wankamata lafiyayyun mari har guda biyu, dan gani take zuby ta rainata kowa na gudu atafi aiki amma ita ta gagara tashi, zuby kuwa yunwa da kishi, da rashin karfin jiki yahanata mi'kewa ganin haka inspector Zalima tasa bulala tacigaba da zabgama Zuby, saida tayimata rud'u-rud'u duk tafasa mata jiki sannan tabarta. Kuma sannan tatasa keyarta zuwa aikin dazasuyi na kwasar bola da wankin toilet dinsu mai d'auke da 'kazantu kala-kala. _Niko zee kallon zuby kawai nake tsananin tausayinta kwance a fuskata, nace lallai Zuby yau duniya tamata gwatson mage_.


*Bayan wata 2*

Shirye-shiryen biki ya kankama tsakanin 6angarori guda biyu, Maman jabeer hidima take sosai dan jin bikin take kamar shine tafarayi a rayuwa, kallo d'aya zakamata ka tabbatar da farinciki tattare da ita.

Momy kuwa dama wannan shine bikin dazatayi na farko dan lokacin bikin Hussaina ba'ayi wani shagaliba.

6angaren jabeer ango kuwa kullum cikin hidima yake dan yau saura sati bikin yariga yagama gayyatar duk wanda ze gayyata.

6angaren amarya kuwa wata 'kawar Momy ce ta d'auketa tatafi da ita gidanta can akeyimata gyaran jiki na amare, tsawon sati biyu ana abu guda tundaga kan dilka halawa, da sauran nau'ikan gyaran jiki, sai ingantaccen tsimi me kyau wanda ke gyara mace kullum tajita cikin ni'ima.

Ana saura kwana bakwai d'aurin aure Hassana tadawo gida, da niyyar saura kwana biyu bikin zata koma ayimata gyaran gashi da lalle, wani sihirtaccen 'kamshi ketashi daga Jikinta ga wani haske da santsi da fatarta ta'kara, dole ko mace ta kalleta takuma kallonta dan fuskarta har wani shek'i takeyi. Zaune take d'aki Momy tatasata gaba da wani tsimi da aka had'a na fruits tanaso ta shanye itakuma sai shatake tana 6ata fuska kamar zatayi amai, sotake Momy tabar d'akin ta ajiye.

Lokacin wayarta tayi ringing sunan Hubby tagani akan wayar, kasa d'agawa tayi tana kallon Momy.
Momy tace ki d'aga mana kinbar waya yana ringing, murmushi tayi sannan tace ina tunanin yazone dan munyi waya dashi yacemin gashinan zuwa yanzu.

Daure fuska Momy tayi minti goma nabaki kiyi ki dawo, ince nafad'amaki ya daina zuwa haka, idan kukayi ha'kuri sati d'aya yarage ami'ka mashi ke baki d'aya.

Cike dajin kunya Hassana ta d'auki wani madaidaicin hijab tasaka sannan tafita tsaye ta iskeshi jikin motarsa, batace yashigoba dan taji gargad'in Momy datace minti goma tabata, tana karasawa kusa dashi yaji wani sihirtaccen 'kamshi yadaki hancinsa, ahankali yadago idanunsa yakai dubansa gareta, yasalam yafad'a tare da sauke wata ajiyar zuciya.
Jiyake kamar ya rungumeta yahad'ata da jikinsa yacigaba da sha'kar daddad'an kamshinta

"Sannu da zuwa tafad'a cikin sassanyar muryarta, kanta sadde tana kallon kasa, "yauwa sannu dai amarya, yakike ya kuma hidima?

Murmushi tayi "Hmm hidima ai tana wurinku angwaye, "haka kike gani koh, amma ni a tinanina biki ai na amare ne.

Murmushi kawai tayi dan bataso firar tasu tayi tsayi, shiru yad'an ratsa na yan mintuna sannan jabeer yace "dama zuwa nayi inji dame-dame kk bu'kata na hidima dan naga idan nayi shiru ke bazakice komeba.

Eh ai bana bu'katar kome dan bawani bidi'a za'ayi a bikinnamuba walima kawai zamuyi, tonaji amma baki bu'katar kome na walimar?
"Eh bana bu'katar kome dan momy tagama had'a mana kome.
"Lallai Allah sakama Momy da Alkhairi amma dukda haka ga wannan kirike gurinki koda zaki bu'kata bandir d'in yan d'ari biyar yami'kamata sannan sukayi bankwana yawuce tana d'aga mashi hannu harya 'kule sannan takoma gida.






Love u all my Fan's πŸ‰
[4/27, 3:01 PM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................59





Yau yakama saura kwana biyu d'aurin auren Hassana da jabeer, yau ne kuma taje akayimata had'add'en gyaran gashi, tare da zana mata flower me kyau a hannunta, wani sihirtaccen kyau tayi dan idan ka kalleta sau d'aya dole ka kara.

Washe gari ana gobe d'aurin aure 'yan'uwa da abokan arziki da yan tsirarun 'kawayen Hassana sun taru a harabar gidan, domin walimar da wa'azi da aka shirya.

Da misalin 'karfe hud'u aka fara gabatar da wa'azin inda wata shahararriyar malama tayi nasiha kan zaman aure, amarya Hassana kuwa tasha kyau dan wata tsadaddiyar atamface Jikinta sai babban hijab data saka.

Da misalin 'karfe shidda aka kammala wa'azi aka rufe taro da addu'a tare dayima amarya da ango fatan zama lafiya da samun zuri'a tagari.

*Rana bata 'karya inji masu iya magana, sai dai uwar d'iya taji kunya*

Dandazon mutane manyan yan kasuwa da 'kusoshin gwamnati ne tan'kam 'kofar gidan Alhj mansir company, wad'anda suka halarci d'aurin auren Jabeer da Amaryarsa Hassana, wanda aka d'aura kan sadaki dubu hamsin.

Ansha shagalin biki taro yatashi lafiya, amarya ta tare gidanta mutane Kowa yanatasa Albarka.

** ** **

*Bayan Wata takwas*

Tunda tatashi take faman kuka kamar zata cire ranta, idanunta sun kumbura sunyi suntum sakamakon rashin baccin datake samu, kusan wata da watanni, kullum cikin damuwa take amma da alama damuwar tayau tafi ta kullum.

Wasu yansanda kusan su hudune suka tsaya kanta, d'aya daga cikinsu ya kwatsa mata tsawa da alama Hausa bata zauna Mashi a bakiba, "oya les go, jiki a sanyaye *Zuby* ta taso tabisu a mota aka sakata, saida akayi tafiya me nisa sannan suka tsaya gaban wani 'katon get megedi yabud'e masu get suka shige, daga nan suka ajiye motar sannan sukayi tafiya me d'an nisa wacce tasadasu da wani d'aki Wanda anan suka iske wasu 'kattin ba'ka'ken mutane tsai-tsaye sunata mazurai wani dogon bencine sai wata igiya ta zuro anyi kullin 'zarge da ita dai-dai yanda kan mutum ze shiga.

Zuby na tsaye ta d'aga kai ta kalli gurin wasu zafafan hawaye suka sauko kan fuskarta, batayi 'ko'karin gogewaba haka suka ri'ka zuba wasu nabin wasu. Wata mace daga cikin yansandan aka mi'koma wata ba'kar hula me zurfi tasaka kan zuby ciki bayan and'orata kan wannan dogon tebur, sannan aka sa'kalo kanta cikin wannan igiyar, wani ba'kin d'ansandan fuskarsa bako annuri yasa 'kafa yature tebur d'in haka yaba igiyar damar tsuke wuyan zuby tayi sama da ita, saiga 'kafafunta suna lilo tanata harbe-harbe kafin daga nan rai yayi halinsa.
*Wannan shine 'karshen muguwa Zuby maci amana, kuma yar ta'adda*


Hafiz kuwa tun bayan da yabada sheda a kotu ya tattara yanashi-yanashi yakoma kaduna da zama, ya canja hali, yazama mutumin kirki kullum zaka sameshi yana istigifari, a haka Allah yahad'ashi da wata yarinya yar mutunci cikin 'kan'kanin lokaci suka sasanta bayan wata biyu aka d'aura masu aure, suna zaune a unguwar dosa Kaduna.


** ** **

Ahankali take takawa saboda nauyin da cikinta yayimata, cikin wata shidda amma idan ka kalleta yanayin Girman cikin saika d'auka yayi wata tara,ga kumburi tana fama dashi,
kitchen tanufa dan sama masu abinda zasuci na rana.

Lokacin jabeer yayi horn megadi yabude masa get, gurin ajiye motoci yayi parking sannan yashigo gidan da sallama, shiru yaji kuma be ganta a faloba bedroom yanufa nanma bata nan, can yajiyo motsinta kitchen can yanufa isketa yayi tanata ha'kilon had'a musu jalouf din kus-kus harma ta kammala tana shirin d'aukowa takai kan dining, da sauri ya amshi kular hannunta, ya ajiye sannan ya rungomota jikinsa bayanta had'u da 'kirjinsa sannan ya d'ora hannunsa kan 'katon cikinta yana shafawa ahankali, "haba my sweet nafad'a maki baniso kina wahalar da kanki kina wahalarmin da baby, bari kigani, hannu yasa ya d'auki kular abincin yakai kan dinning table yadawo ta mi'ko mai plate yakai sannan yadawo tami'kamashi cup din fruit salad d'in data had'a yaji 'kan'kara sai ra6a jikin jug din

Bayan sun kammala wannan da kanshi yahad'a mata ruwan wanka sannan yarakata har toilet, yana zaune harta gama wanka da kanshi yashafamata lotion me sanyi sannan ya d'uko mata wata doguwar riga me saukin nauyi ta sanya.
Kama hannunta yayi ya zaunar da ita bakin gado "ina zuwa bani minti goma yafad'a toilet yashiga yashe'ka wanka yafito ya murza lotion sannan yasaka wasu 'kananan kaya riga ash marar hannu sai bakin wando three quarter, sannan yakama hannunta suna takawa ahankali kamar makaho da d'an jagora har kan dining.

Nanma be barta tayi wani aikiba, dan ko zuba abinci hanata yayi shiya zuba sannan yarika bata da kanshi saida ya tabbatar ta 'koshi sannan yazuba ftuit salad din a cup yatura mata gabanta shikuma yafara cin abinci.





Love u all my Fan's
[4/28, 8:42 AM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................60



*Na sadaukar da wannan page d'in gareki Asmy b Aliyu, Allah bar zumunci*




Bayan wata d'aya cikin Hassana ya'kara girma idan ka ganta dole ka tausaya mata dan ko tafiya da kyar take iya d'aga 'kafa, hakan yasa Maman jabeer ta yanke shawarar zatayima wata tsohuwa salame a unguwarsu data Zauna gurinta tari'ka taimakamata da wasu abubuwa, Sam Hassana kin yarda tayi da zaman salame a gidanta dan lokacin da salame tafara zuwa gidan kallo d'aya Hassana tayimata taji gabanta yayi mummunan fad'uwa haka kawai taji bata bu'katar zama da ita.

Saboda haka jabeer tasamu yana Zaune d'akinsa da laptop gabansa yana kammala wani aiki na office dinsu Wanda besamu damar kammalawa jiyaba saboda dawowa yayi da wuri yayi girki yayima 'yar'lelensa wanka da gyare-gyaren gida.

Zama tayi bakin gado tare da dafe 'kungunta tana fad'in waih Allah, saurin ture laptop dindake gabansa yayi ya rungumota jikinsa yana fad'in "meya faru baniso inji kina fad'in wash wash d'innan wlh har cikin raina sai inga kamar akwai abinda ke damunki.


Murmushi tayi "ba abinda ke damuna sai nauyin cikinnan dan ba 'karamin nauyi yakeminba, tafiyama da kyar nake iya d'aga kafa, "Eyyah sorry my wife, wlh jinake kamar cikinnan yadawo jikina in'karasa miki rainonsa da haihuwarsa.

Dariya ta kyal-kyale da ita tana fad'in "wai Allah naganka da ciki, wlh bazaka kalluba, hmm barantana kuma ranar haihuwa za'asha raki danna tabbata bazaka iya jurewaba.

'Kara rungomota yayi gabansa, tare da d'ora hannunsa kan 'katon cikinta yace "inji waye yafad'amaki, aini idan da ace maza na kar6ama mata haihuwa toda kuwa bazan bari ki haifi ko d'aya da kankiba zan nunamaki ni gwarzon namiji ne, dan yayannnan goma sha biyar dukni zan haifesu.

Zaro ido tayi tare da dafe 'kirji 'ya'ya goma sha biyar a ina..........
A cikinki mana yafad'a yana 'kara had'eta da Jikinsa.
Amma baka tausayamin kallifa wahalar danakesha amma har kake fatan in'kara irinta sau sha biyar.

Murmushi yayi "ai a ina tausayinki yasa nace sha biyar amma da a yanda nakesone sonike ki haifamin dozin biyu.
Suduka dariya sukasa Hassana na fad'in ashirin da hudu kamar dai haihuwar zomaye.

Shiru yad'an ratsa na wasu 'yan mintittika, Sannan Hassana tace "my hubby akwaifa maganar dake tafe dani gurinka.
"To ina jinki, yafad'a tare da tattaro duk illahirin nutsuwarsa ya maida gareta.

"Umm dama game da maganar salame, sai kuma tayi shiru "ina jinki yafad'a "mezai hana abarta kawai ni hankalina be kwanta da zamantaba, mezai hana Nusaiba tadawo nan ko itama ai zata ri'ka taimakamin da wasu abubuwan.

"To shikenan tunda haka kikeso haka za'ayi, Ammafa kinsan ankusa bikinta saura 3 month idan lokacin yayi tatafi tabarkifa wah kuma kike tunanin za'a samo, "Ah bani fatan inkai wata ukku nan gaba ban haihuba, kaga hakan ya nunamin baka lissafi.

"Ah inji waye nikam nike lissafi nida za'a haifama babies guda hud'u lokaci guda yazan manta da lissafi.
"To shikenan yanzu dai kaba mama hakuri kada taga kamar na raina za6inta, "Kada kidamu indan mama bazataji komeba.


: Bayan wata biyu da zuwan nusaiba gidan da misalin 'karfe hud'u na yamma suna zaune suna kallon shirin *Yan Zamani* a star time tashar dad'in Kowa dan nusaiba na masifar son shirin dan ko lokacin tana gida bata ta6a bari ya wuceta, tunda suka fara kallon shirin Nusaiba ke ba Hassana labarin na baya wanda bata ganiba, amma saita lura kamar Hassanar ba saurarenta takeyiba, dan wani lokacin har d'an cije baki takeyi alamar dai akwai abinda ke damunta, lura da nusaiba tayi da Haka yasa tace "nikam Aunty sai inga kamar yau bakijin dad'in jikinnaki kodai inkira Yaya?

Kallonta Hassana tayi tare da 'ka'karo murmushin 'karfin hali tace "a'a kada ki kirashi ba wani abu inshaAllah, "ah'ah aunty kedai kadafa aje asamu matsala Yaya yaga laifina, "Hmm ba kome Nusaiba kada ki kirashi, "to shikenen tafad'a tare da ajiye wayar kusa da ita, dan da harta d'auko zatayi dialing number jabeer Hassana tahanata

Batafi minti goma da ajiye wayarba wayar tafara ringing Alamar shigowar kira, kallon Hassana tayi batare data d'au wayarba itama Hassana ita take kallo tace "yanzu danace kada ki kira saida kika kira.......

Murmushi nusaiba tayi cike dajin kunya tace "Lah wlh aunty bankirashiba, Hassana ta harareta tace "dabaki kiraba da yaza'ayi yakiraki.

"Hmm aunty kenan aibashibane yakira kallifa kigani tafad'a tana d'ago mata wayar, ganin an rubuta True love yasa Hassana tayi dariya "Hmm Abdul dinne yakira, wannan soyayya taku kamar zaku had'iye juna Allah dai yakaimu lokacin bikin.

"Hmm aunty ai duk soyayyarmu bamu kaiku keda yayaba, "yanzu dai ki d'auki wayar kada takuma tsinkewa.
Tana d'auka yake sheda mata gashinan ya iso gidan yayan nata, nan ta sanar Da Hassana Zuwanshi "Hassna tace saiki shigo dashi ko, nibari nakoma bedroom in huta.

"A'a aunty yi zamanki zamu zauna a lambu bari dai nafita da ruwa me sanyi da lemu. Wlh aunty dan kina haka amma danace yashigo Ku gaisa tafad'a tana dariyar tsokana, Hassana tace "a hakanma sai dai idan ba'ayi niyyar gaisheniba, hmm Nusiba kenan kema duka yaushe zamu ganki hakan kada ki manta yau saura wata d'aya dai-dai.

"Kai aunty kuma dan saura wata d'aya aiba daga zuwa zanzama hakaba, "Hmm Allah dai ya nunamana lokacin Hassana tafad'a "Ameen nusaiba tace tana dariya tayi saurin barin d'akin dan kada Hassanar tace tayi rashin kunya.




Love u all my Fan's β˜•
[5/1, 4:01 PM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................Last page πŸ‘ŒπŸ»





Tunda Nusaiba tafita kamar an'karomata wani matsanancin ciwon mara da ciwon baya, tun tana daurewa harta fara nukurkusa, zuwa can taji azabar tayi yawa ta 'ko'karta ta tashi tana ta'kawa da kyar tanufi bedroom.

Tana shiga ta d'auko wayarta ta lalubo sunan jabeer ta danna kira, ringing d'aya ya d'auka dama kullum idan ze fita sai yayimata gargad'i akan dataji ciwo ko yaya takirashi.

Cikin za'kuwa dason jin mezata fad'a yace "Heelow my wife yadai?
Cikin tsananin azabar ciwo tace "wayyo Hubby na zan mutu ka taimakamin.........

Tana fad'in haka wani irin matsanancin ciwo yatasomata lokaci guda, saboda tsananin ciwo jikinta har kyarma yake, wani irin 'karfi yazomata lokaci guda tayi wani nishi mai 'karfi saigashi ta santalo santalelen d'anta, kamar kuwa yana jira ya kyanyara kuka, duk abinnan dake faruwa a kunnen Jabir Dan lokacin data kirashi tsananin ciwo yasa bata kasheba tasaki wayar.

Shikuma can 6angaren yanata magana kawai said jin kukan jariri yayi, a firgice yatashi yanufi motarshi da sauri,

Tuki yake amma gani yake kamar ba tafiya yakeba, dan gani yayi kamar an'karama gidan nisa,

kasa daurewa yayi, wayarshi yajawo yakuma kiranta tana d'auka takara akunne kamar azabar dataji dafarko ta'karaji nanma wani nishi tayi saiga santaleliyar yarinya, tana fad'owa ta kyanyara kuka, shima namijin datafara haihuwa kukan yake.

Jabir yaji and'au waya yanata hellow hellow yaji shiru sai kukan jarirai yakeji, ai take ya'karama motarsa gudu.



Nusaiba kuwa lokacin sukayi sallama da Abdul d'inta yatafi danta shedamashi tabaro auntynta kamar batajin dad'i.

Aiko tana shiga tundaga falo tafara jiyo kukan jarirai ai dagudu tanufi d'akin dataji kukan tana zuwa tafad'a d'akin batare da tunanin komeba.

Toxali tayi da santala-santalan baby's sunata tsala kuka, Hassana kuma tana dur'kushe kusa dasu lokacin ko cibi ba'a

Please Login or Register in order to submit comment