Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta share hawayen dake bin kumatunta sannan ta kalli jabeer cikin dasashshiyar murya take magana "Nifa ba wani abu bane ke damuna kawai ina tunanin 6atan "yar'uwatane yau kwana biyu ko labarinta ba'a samuba.

Tana kaiwa nan tafashe da wani sabon kuka, jabeer har cikin ranshi tabashi tausayi sosai janyota yayi jikinsa yana rarrashinta, da dabara tasamu ta kwace kanta tanufi kitchen domin had'a masu breakfast.

** ** **

Daddy zaune daga bakin gado kallo d'aya zakayimai ka tabbatar da tsananin damuwar dake tattare dashi, Momy kuma nakan abin sallah tana lazimi idanunta fall da hawaye ro'kon Allah kawai take Allah bayyanar mata da d'iyarta aduk halin datake ciki,

Wayar daddy dake jone jikin socket tana chaji tahau ruri alamar shigowar kira, ko motsawa beyiba barantana yad'aga haka ta 'karaci ringing d'inta harta tsinke aka kuma kira karo na biyu nanma beyi niyyar d'agawaba, dan ko kallon wurin beyiba, Momy ce ta kalleshi tasa hannu ta goge hawayen dasuka gangaro kan kumatunta tace "Alhj wayarka fa tana ringing, shiru yayi kamar beji maganar datakeba, magana ta'karayimashu lokacin da kiran wayar ya'kara shigowa karo na ukku "Alhj yakamata ka d'aga wayarnan dan da alama kowaye yadamu daya gayama kowace mgana ce saboda wanda yakiraka dai-dai wannan lokacin 'karfe shidda na safiya yakira baka d'agaba yanace yanata kira kasan maganar nada matu'kar muhimmanci, tana rufe bakinta wani kiran yakuma shigowa karo na biyar, Momy bata jira daddy ba tanufi inda wayar take ta d'auko ta danna ok sannan ta mi'kamai ba musu ya kar6a yakara akunnensa batare daya kalli sunan wanda ke kiranba.


"Assalamu Alaikum aka fad'a a d'aya 6angaren, me maganar bejira jin abinda Daddy ze fad'aba yacigaba da magana
"Sunana Ahmad turaki comusioner of police, ina fata dai muna magana da Alhj manair company?
"Eh dashi kake magana daddy yabashi amsa a ta'kaice.
Zaku iya zuwa babbar headquarter mu ta police domin tabbatar da wata gawa da muka tsinta kota d'iyarkace.

Saurin mi'kewa tsaye Daddy yayi yana yana salati "to shikenan ganinan zuwa bekobi takan Momy ba ya suri key d'in motarsa jikinsa dagashi sai jallabiya, silifas yazura a 'kafarsa yana shirin fita, momy tabiyoshi tana tambayarshi "Alhj lafiya? Beko sauraretaba yawuce hankali tashe.

Fad'awa Momy tayi kan gado tafashe da wani irin kuka me ban tausayi "ya Allah ka bayyanamin Hassana Allah sa duk inda take tana cikin aminci da kariyarka ya ubangiji, wani sabon kuka ya kubce mata.

Daddy na isa headquarter police bayan sun gaisa da comusioner nan yahad'a daddy da wasu police guda hud'u suka nufi babban asibitin dake garin kai tsaye matuare (d'akin ajiye gawa) suka nufa nan aka jawo dorowar da gawar Hussaina take, Daddy na ganinta yafashe da kuka kamar 'karamin yaro, nan ya tabbatarma 'yansandan d'iyarsace lokacin duk kamanninta sun canja fuskarta ta kunbura ga jini daya gama wanke mata jiki.

Nan yansandan suka shiga rarrashin Alhj "kayi ha'kuri Alhj inshaAllah zamu tsaurara bincike sai mungano Wanda ya aikata wannan mummunan laifi, dan bincike ya nuna ankashe marigayiyar ne ta hanyar dukan da akayimata aka.

Daddy kasa magana yayi sai kuka kawai dayake, haka aka d'auki gawar Hussaina cikin motar police d'in aka nufi gida da ita.







Love u all my Fan's 👄😭😭😭
[2/2, 9:05 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................37



® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝



Momy kuwa tun bayan fitar daddy Daga gidan gabanta keta fad'uwa takasa zaune takasa tsaye.

Jin 'karar bud'e get tayi da sauri tatashi tanufi 'kofar fita daga falon zuwan harabar gidan, ganin motar me gidanta tare data police yasa tayi saurin komawa ciki tare da dafe 'kirjinta saboda jitake kamar zuciyarta zata fad'o saboda bala'in fargaba.

Jin annufo falon yasa fad'uwar gabanta ya yawaita, bata ankareba kawai sai gani tayi anshimfid'ar da gawar Hussaina tsakiyar falon, tana kai dubanta gareta taji duk illahirin wasu jijiyoyin jikinta dake aiki sunyi tsaye cak, kafin ayi wata magana sai ganin Momy akayi 'kasa ba alamar numfashi tattare da ita.

Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Daddy yari'ka furtawa da sauri ya d'auko ruwa ya yayyafa mata, nan akayi nasarar dawowar numfashinta bakinta d'auke da salati.

Nan Daddy yacigaba da yimata nasiha yana rarrashinta da 'kyar yasamu ta nutsu ba abinda take maimaitawa a zuciyarta sai salatin annabi.

Ranar kafin ad'au wani lokaci labarin mutuwar Hussaina ya bad'e gari dandanan gidan Alhj mansir yacika da 'yan'uwa da abokan arzi'ki wasu na zubar da hawaye wasu kuwa sunyi jugum-jugum. Amma duk a tunananin mutane harma da daddy da Momy Hassanace ta mutu.

** ** **

Hassana zaune tana duba wani littafi na addu'oi kad'an-kad'an tayi try number Hussaina wai ko Allah zesa tashiga dan tanaso tagayamata Halin datake ciki, amma kamar kullum dai akashe ake cewa.

Jabeer ne yashigo jikinsa a sanyaye. haka kawai yana shigowa Hassana ta tsinci kanta da wata mummunan fad'uwar gaba.

Kallonta yayi ya matu'kar tausaya mata sannan yace "ki tashi yanzu zamuje gida daddy yana nemanmu, jitayi fad'uwar gabanta ya tsananta lokaci guda hawaye ya wankemata fuska a tunaninta jabeer yakai karartane.

Tasowa tayi jiki a sanyaye ta dur'kusa gaban jabeer "dan Allah kayi ha'kuri indai wannan maganarce nayima Al'kawari wlh zan gyara.

Wani irin tausayinta ya'kara mamaye zuciyarsa "a'a ba wannan maganar bace ban dad'e da isa office ba daddy yakirani yace muzo yanzu nidake nikaina bansan ko miye dalilin kiranba, haba tanajin haka wani sabon tashin hankali ya ziyarceta jikinta yafara kyarma kad'an yarage tasaki fitsari dan bako tantama tasan asirinsune ya tonu kan abinda suka aikata itada 'yar'uwarta nasanya jabeer yin *AUREN TAGWAYE* batare da saninsaba, innalillahi kawai tacigaba da furtawa acikin Zuciyarta, ahaka tanufi bedroom ta bud'e wadrope ta d'auko wata doguwar Riga ta canja kayan jikinta sannan tasaka hijab med'an girma wacce ta tsayamata iya gwiwa, plate shoe tasako sannan tafito falo ta iske jabeer na jiranta, yana ganin fitowarta yayi gaba tana biye dashi har gurin mota yabude gurin driver ya zauna sannan itama yabud'emata gidan gaba ba musu tashiga, amma duk illahirin jikinta kyarma yake dan kallo d'aya zakayimata ka tabbatar da bata cikin nutsuwarta.

Ahaka har suka 'karaso 'kofar gidansu tundaga nesa tahango dandazon Al'umma haka yacanjamata tunanani Zuwa wani daban "to wannan iyayen mutanenfa meke faruwane "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.

Hankalinta be'kara tashiba saida tashiga harabar gidan nanma cike yake da jama'a maza suna jiran afito da gawa, cigaba tayi da tafiya dai-dai 'kofar dazata sadata da falon gidan taga wasu gun-gun mata zaune sunyi jugum-jugum sai d'aya daga cikinsu ta nuna Hassana tana cema sauran matan "wannan itace Hussainar marigayiyar, d'ayar tace "oh itace wacce akayima aure kwanakin baya, d'aya tace itacefa Allah sarki mutuwa me yankan 'kauna lalle wannan yarinya tayi rashi Allah bata ha'kuri da dangana.........

Dai-dai wannan lokacin Hassana tanemi numfashinta tarasa sai mutanen dake gurin sukayo kanta anata salati aka kinkimeta akayi ciki da ita.

Dai-dai lokacin kuma aka fito da gawar Hussaina domin kaita makwancinta.





*Anan inso inja hankalin Al'umma akan mutuwa, yanzu abinda aka gane shine da ance wane ya mutu sai mata suje su cika gida wasuma ba dangin iya bare na baba, kuma Alhalin lokacin ana kimtsa gawa irin haka na jawo matsaloli da yawa, da zarar ka mutu 'yan'uwanka da iyayenka sha'kikai ake bu'katar suje ga gawarka bawai mutanen unguwaba, ba'ace kada mutane suje gidan suyi gaisuwaba amma ayi ha'kurin kauda mamacin, mata inajan hankalinku da kunyi gaisuwa ga wad'anda akayima mutuwar kutafi gidajenku shine mafi Alkhairi agareku kada azauna zaman gulma da cin abincin gidan mutuwa. ALLAH SA MUDACE ALLAH KUMA YASA MUCIKA DA IMANI ameen*
[2/3, 10:16 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................38



® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝



Nan fa aka Shiga wani sabon tashin hankali ganin Hassana kwance ba Alamar numfashi tattare da ita, Momy kuka take tama rasa inda zata dosa saboda tsabar rud'ewa.

Sai kusan awa ukku sannan Hassana ta farfad'o lokacin 'Karin ruwane ke shiga jikinta, ahankali tafara bud'e idonta ido biyu sukayi da 'kanwar babanta Haj Uwani tana mata firfita, ganin ta bud'e idonta yasa tafara jeramata sannu.

Bin robar 'karin ruwan dake hannunta tayi da kallo, tunanin 'yar'uwarta tafad'omata arai "yanzu shikenan Hussaina tamutu nashiga ukku, ya zanyi da 'kullallen al'amarin data barni cikinsa, yazanyi in tunkari iyayena da mijin 'yar'uwata da wannan 'kazamin Al'amarin damuka aikata.

Fashewa tayi da wani irin kuka me ban tausayi, tana 'ko'karin tashi daga kan gadon, saurin ri'keta Haj Uwani tayi tare da rarrashinta.

"Kiyi ha'kuri Hussaina dukkan me rai mamacine, addu'a kawai zakibi 'yar'uwarki da ita, dan ita tafi bu'kata akan kome "Allah ji'kan Hassana yakai Haske kabarinta Allah toni asirin wad'anda suka aikata wannan mummunan aiki akanta, Haj Uwani tafad'a tana share hawayen fuskarta.

Hassana kuwa kwance tayi, tayi lamo akan gado tana sauraren yanda Mama Uwani 'Kanwar daddy take kwararo addu'a akanta bayan ita tasan ba itabace ta mutu, amma babu damar tafad'i, hawaye yacigaba da kwarara daga idanunta ba 'kakkautawa. Ahaka Momy tashigo d'akin hannunta d'auke da cup, ganin Hassana na kuka ya 'kara d'aga hankalinta itama kad'an yarage tafashe da kukan da kyar ta rarrashi zuciyarta, ta daure tami'kama Haj Uwani cup d'in hannunta "gashi tunda tatashi 'kara ta daure ko tea tasha kota d'an samu 'karfin jikinta.

Nan Haj Uwani kar6i cup din ta tada Hassana zaune tana 'ko'karin bata tea d'in tana 'kin kar6a da kyar tasamu tasha Rabin cup takoma ta kwanta da tunani barkatai cunkushe a kwalwarta.

*Bayan sati d'aya*

Hankali yad'an kwanta mutane 'yan'uwa na kusa dana nesa kowa ya koma gida, gidan yarage daga Momy sai Hassana wacce tundaga ranar da'akayi rasuwar tazo bata komaba saboda har yanzu jikinnata ba 'karfi duk tabi ta rame ta kod'e.

Washe gari ranar kwana takwas da rasuwar Hussaina Momy da Hassana na zaune, Momy na aikin rarrashinta akan taci abinci dan duk yinin yau batasa kome acikintaba, daddyne yashigo gidan da sallama, Momy ta amsa masa sallamar tare dayimashi sannu da zuwa, kallon Hassana yayi yaga yanda tarame ta kod'e cikin sati d'aya duk ta fita hayyacinta, har cikin ranshi ya tausayamata dan yasan ba karamar sha'kuwa tayi da 'yar'uwar tataba, sai dai al'amarin ubangiji ba ruwanshi da sha'kuwar dake tsakaninka da mutum idan yatashi d'aukar rayuwarsa.

"Hussaina, daddy yakira sunanta.
Gabanta yafad'i sannan ta juyo ta kalleshi tare da amsawa, amma kanta sadde 'kasa dan bata yadda su had'a ido dan gani take idan suka had'a ido da daddy ze iya gane cewa ba Hussaina bace.

Daddy yacigaba da magana "inaso kitashi ki shirya dan munyi waya da mijinki yanzu haka yana kan hanya zezo ya d'aukeki sai kitashi ki shirya kikoma d'akin mijinki kicigaba da biyayya, kinga dai abinda yafaru da yar'uwarki saboda haka kicigaba dayimata addu'a Allah kai haske kabarinta, yana gama fad'in haka ya wuce d'akinshi, Hassana kau fashewa tayi da wani irin kuka tafad'a jikin Momy tana maida numfashi sama-sama.

Hankalin Momy ya masifar tashi ganin yanda Hussana ke kuka ga numfashinta na fita sama-sama, amma ba yanda zatayi dan tasan tunda Daddy yariga ya furta takoma tofa ba fashi saita koma yau d'in, saboda haka jiki a sanyaye Momy tatashi ta taimaka mata tayi wanka, tana fitowa tad'an shafa mai sama-sama sannan tacanja kayan jikinta zuwa wata doguwar Riga, bata dad'e da gama shirinba suka jiyo tsayawar motar jabeer a harabar gidan, kafin jabeer yashigo ciki daddy yafito ya umarci Hassana data tashi sutafi kada ta 6atamai lokaci.

Haka ta mi'ke jiki ba laka tanufi harabar gidan tana tafiya tana waige jitake kamar takoma tasanar da daddy gaskiyar Al'amari amma data tuno da irin zuciyar daddy sai tsoro yakamata, dan tasan tsaf itama ze iya aikata inda 'yar'uwarta tatafi.

Ahaka ta isa gurin motar jabeer na ganin tahowarta yashige mazaunin driver tare da budemata gidan gaba tashiga ya tayar da mota me gadi ya bud'emasu get suka d'au hanya.







Love u all my Fan's 👄👌🏻
[2/4, 4:46 PM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................39



® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝



Tun a mota Hassana ke faman kuka har suka iso gida, jabeer nayin parking tafito tanufi cikin gidan dagudu tana 'kara fashewa da kuka, tana shiga falo tawuce bed room tasa key tarufe 'kofa

tarufene dan bata bu'katar jabeer yabiyota yace ze rarrasheta, fad'awa tayi kan gado tacigaba da rizgar kuka Kamar zata cire ranta.

Tunanin Hussaina yafad'omata arai yanda suke kome tare, ba abunda ke rabasu ko bacci basu yadda yarabasu har tayi aure amma gashi mutuwa tarabasu, zaune tatashi ta d'auko wayarta tana kallon Hotunan dasukayi itada Hussaina lokacin suna gida wasu sabbin hawaye suka kwararo a idanunta, tafara surutai kamar wacce ke magana da wani a kusa da ita tana kallon wani hoto na Hussaina "sister mesa kika tafi kika barni da 'kulallen Al'amarin da bansan yanda zanyi in warwareshiba, Hussaina ina kikaje aka rabaki da rayuwarki, me kikayimasu suka kasheki, ya Allah ka toni asirin kosu waye suka aikata maki wannan abin.

Cillar da wayar tayi gefe takoma kan gadon ta kwanta tacigaba da kukanta,
Bata tashiba sai 'karfe bakwai da rabi na dare lokacin wani matsanancin ciwon kai ke addabarta, a daddafe tatashi tashiga toilet ta d'auro Al'wala ta rama sallolin da'ake binta daga magrib har isha'i tadad'e tana lazimi kafin tashafa takoma kan gado ta kwanta, tunani barkatai takeyi a zuciyarta tace "ni yanzu yazanyi in fidda kaina cikin wannan sar'ka'kiyar......






Bayan kwana goma tunda Hassana tadawo gidan jabeer bayan rasuwar Hussaina bata yadda su had'u da jabeer.

Kalacin safe saitaji fitarshi take fitowa tasamu abinda zata sama cikinta, dukda ba wani abincin kirki takeciba hakanan take tutturwa, da rana zata fito tayi abinci tajera a dining sanan ragyara ko'ina na gidan ta share hadda d'akin jabeer d'in, tana gamawa take ibar wanda tasan ze isheta daga lokacin har dare sannan takoma d'aki bakuma Zata 'kara fitowaba sai gobe idan taji fitar jabeer d'in

Tun jabeer na rarrashinta akan tafito ta daina zaman d'akinnan har yaha'kura ya kyaleta ganin tunda yake magiya ko saurarensa batayi sai dai duk ranar dayayimata magana yajiyo sautin kukanta.



: Bayan sati d'aya tana zaune d'aki kamar yanda tasaba tanajin lokacin da jabeer yafita saboda haka da sauri tafito tahad'a abinda zataci, dankali da kwai tasoya sannan tahad'a tea cikin cup tadawo palo ta zauna tafaraci, bawani dad'insa takejiba dan yau tashi tayi da wata irin kasala ga tashin zuciya dake addabarta, ahaka tasamu ta tuttura dan yunwar jinta takeyi, tana gama cin abincin kuwa yafara tu'karta da gudu tanufi toilet tafara she'ka amai, saida ta amayar da duk abinda taci sannan taji sau'ki-sau'ki

Nan take kuma wani irin zazza6i yarufeta, tafara kyarma kan gado tafad'a sannan tajawo wani 'katon bargo ta kudundune dukda uban zafin da akeyi a lokacin.




*kuyi ha'kuri yau namaku typing kad'an, da bazanyiba ma ganin mutane sun matsamin yasa nayi, muhad'u a page na gaba*




Love u all my Fan's 👄🍍
[2/6, 9:28 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................40





® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝




Jabeer be dawo gidan ba sai bayan sallar azahar kamar yanda yasaba dawowa, da sallama yashigo falon kai tsye d'akinshi ya wuce yafad'a toilet yayi wanka danya kwaso gajiya sosai, bayan yafito daga wankan ne ya murzama jikinshi mai sannan ya canja kaya zuwa 'kanana marassa nauyi, falo yadawo kai tsaye dan yakwaso yunwa sosai yasan ze tarar da abinci kamar yanda yasaba.


Falo yadawo kai tsaye ya doshi dining area amma bisa mamakinsa sai yaga wayam bako cokali gurin barantana yasa ran abinci, cike da mamaki yashiga kitchen nanma ganinsa yayi tas ko ina a share a goge ba alamar andafa wani abinci cikinsa, cike da mamaki yadawo falon sannan yanufi d'akin Hussaina nocking yayi ahankali duk da yasan ba bud'ewa zatayiba, hannu yasa yad'an murd'a handle d'in 'kofar da mamaki kawai sai gani yayi kyauren ya bud'e, ahankali yashiga d'akin yari'ka dubawa inda ze ganta can idanunsa sukayimai tozali da ita tana kwance kan gado ta kudundune a bargo tanata makyarkyata kamar wacce aka she'kama ruwan 'kan'kara, duk zafin da akeyi a garin.


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un jabeer yafad'a tare da nufar inda take kwance, zama yayi gefen gadon tare da bud'e bargon yana kallonta sannan yakai hannunsa kan wuyanta, jin wani irin zafi yayi rau ajikin nata, "subhanallah zazza6i Kike amma baki gayaminba sai ki zauna da ciwo ajiki, kitashi mutafi asibi,


: Bejira mezata fad'aba yanufi wadrope ya d'aukomata hijab, da kanshi ya taimaka mata ta sanya hijab d'in sannan suka nufi mota da sauri jabeer yabud'emata gaban mota ba musu ta zauna sannan ya zagaya yashigaazaunin driver suka d'au hanyar asibiti.

Bakin wani private Hospital suka tsaya me suna *Allah Bamu Lafiya* dake cikin garin katsina jabeer da kanshi ya taimakama Hassana tafito daga motar suka nufi cikin asibiti, suna zuwa kai tsaye aka bud'emata file sannan aka turasu gurin likita, bayan yan tambayoyi da likitan yayima Hassana itakuma tayimai bayanin duk abinda takeji, nan take likitan ya danna wata 'yar karaurawa saiga wata nurse tashigo, ta rissina gaban likitan cikin ladabi, ya nunamata Hassana "kije da ita kiyimata wannan gwaje-gwajen yafad'a yana mi'kamata wata takarda, "owk sir tafad'a tare da amsar takardar sannan takama hannun Hasaana suka nufi lab, nan aka ebi jini sannan tanunamata toilet tabata wani d'an konkoni na roba ta umarceta datayo fitsari anan, haka Hassana tayo fitsarin takawo sannan takoma kan wani benci Wanda masu jira ke zama ta kwanta ta kudundune cikin hijab d'inta dan har yanzu wani irin sanyi takeji,


Kusan minti talatin suna jiran result ganin yanda mutane ke 'kara yawa yasa jabeer matsawa kusa da Hassana yace "ko muje inkaiki gidanmu tunda kusane ni sai indawo injira sakamakon dakuma magungunan daza'a rubuta.


'Daga mashi kai kawai tayi, alamar hakan yayimata dan dama ita tamatsu dasubar wannan asibitin ganin yanda mutane suketa zuwa gashi gurin zama ma yana neman gagarar wasu itakuma ga wani irin sanyi datakeji.


Da taimalonshi suka isa gurin mota, bud'emata yayi tafara shiga sannan shima yashiga yatshi motar suka tafi, kasancewar ba nisa tsakanin asibitin da gidansu jabeer ba'a d'au wani lokaciba suka iso, bakin 'kofar gidan sukayi parking sannan suka fito, suka nufi cikin gidan Ahankali Hassana take tafiya tana biye da jebeer, yanayi yana waigenta har suka isa cikin gidan suka kwad'a sallama Umman jabeer daga d'aki ta amsa, dai-dai lokacin 'kanwarsa nusaiba tafito daga wanka ta kai dubanta garesu cike da fara'a "Lah Yaya jabeer ashe tare kuke da aunty Hussaina, jin an ambaci Hussaina yasa Umma Fitowa daga d'aki tana masu sannu da zuwa, takai dubanta ga jabeer baka cemin tare kuke.

"Eh wlh mama daga asibiti muke shine nace bari inkawota nan tad'an huta kafin agama gwaje-gwajen daza'ayi.

"Subhanallah, Umma tafad'a meyasameta? Ta tambaya tana 'karema Hassana kallo wacce ta saddar da kanta ta'ki bari su had'a ido da Umma, amma hakan behana Umma tagano wani Abu tattare da itaba, murmushi tayi me d'auke da farin ciki, sannan takama Hannun Hassana suka nufi d'aki tanata jera mata sannu.











Love u all my Fan's 👄🍉
[2/7, 10:32 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻



Page......................41



® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(RWG)_ 📝


Jabeer ne zaune gaban likita, saida likitan yayi wasu 'yan rubuce-rubuce sannan yafad'a mashi ainafin abinda ke damun Hassana, sannan yabasu shawarar hanyoyin daza'abi domin kare lafiyarta,


Nan jabeer yayi godiya sannan ya sayi magungunan da'aka rubuta ya wuce gida.

Da sallama yashigo gidan, zaune ya iske Hassana da kwano a gabanta d'an wake ne Mamanshi tayimata shine takeci dan ba 'karamin dad'i yayimataba, dai-dai lokacin nusaiba tafito daga d'aki cikin kayan islamiyya kalar ruwan 'kasa, cikin ladabi ta isa kusa dashi "yaya harka dawo? "Eh nadawo nusaiba ina mama take ? "Tashiga nan makwabta zata kar6oma Aunty Hussaina kunun aya, tunda kashigo ni bari na wuce islamiyya dama nafara latti baniso inbar aunty ita kad'ai shiyasa nad'an jinkirta.

"To shikenan maza kitafi ga wannan kihau napep dan kiyi saurin zuwa yafad'a yana mi'komata d'ari biyu hannu biyu tasa ta kar6a sannan tayi godiya tawuce.

Kujera jabeer yajawo ya zauna gaban Hassana suna fuskantar juna "sannu ya jikin naki,? "Da sauki, tafad'a tana cire Hannunta daga kwanon d'anwaken, buta ta d'auka tanufi bakin maguji domin wanke hannunta, jabeer yabita da kallo har cikin ranshi yake matu'kar tausayamata ganin yanda tarame sai wani uban fari datakara.

Umma ce tashigo da sallama, dai-dai lokacin Hassana tagama wanke Hannunta zata mi'ke Umma tayi saurin kamata ta mi'ke tana ri'ke da ita har kan tabarma datake ta zaunar da ita, tana jeramata sannu a zuciyarta kuma fall da farin ciki ganin takusa samun jika.
Dai-dai lokacin kuma aka kira sallar la'asar saboda haka jabeer besamu damar yin wata magana da maman tashiba yad'auki buta yayi Al'wala ya wuce masallaci.


** **

Please Login or Register in order to submit comment