Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna jiran fitowar Hassana, daddy ya kalli Momy "anya yarinyar nan tana cikin Hayyacinta kuwa? "Saboda me kafad'i haka Alhj, saboda yanda ta shigar da 'kara kotu gashi har ana shirin zama na farko gobe batare data nemi shawarar yin hakan ba,

Murmushi Momy tayi "ai Alhj aikin gama yagama,tunda taji zata iya sai mu barta mugani.
Fitowar Hassanace ta katse masu maganar dasukeyi, cikin ladabi tasamu guri ta zauna, sannan tayima Daddy sannu da zuwa.

Suduka shiru sukayi na tsawon minti biyu kafin daddy yafara magana, "Hassana munji abinda kika aikata, amma amatsayinmu na iyayenki yakamata ki shawarcemu kafin ki yanke shawarar, ita shari'a da kike gani sa6anin hankali ce, kuma idan baka iya kama 6arawoba sai 6arawo yakamaka.

'Dagowa tayi ta kalli iyayen nata da fuskarta wacce Hawaye suka gama wankewa tace "dan Allah daddy da Momy ku gafarceni akan rashin shawartarku danayi, yanzu ba abinda nake bu'kata agareku sai addu'a inashaAllah naji ajikina nice da nasara, "To Allah ya bada sa'a "Ameen, ta amsa sannan ta kalli daddy, kuma dan Allah daddy ina Neman wata Alfarma agareku, "muna jinki daddy yafad'a, "inaso duk zaman daza'ayi a kotu yazama tare zamu tafi daku.
"InahaAllah zamuje Hassana kada ki damu kedai kije kiyita addu'a.

Nagode daddy, sannan ta kalli momynta Momy nagode, kuma inaso kuma ku tayani da addu'a.



Zuby kuwa tana zaune gidansu itada 'kawayenta tana nunamasu d'inkunan data amso daga gurin d'inki, tana gayamasu ranar dazatasa kowane kaya, 'kawayen nata kuwa ba abinda suke sai zuzutata suna yaba duk wani abu data fad'amasu ta tsara...

Ba zato ba tsammani kawai sai ganin yansanda sukayi gabansu, kusan su takwas mata hud'u maza hud'u,
Zumbur zuby tami'ke tsaye dan ba 'karamin razana tayiba kad'an yarage tasaki fitsarin wando.

'Daya daga cikin yansandan tace "zuby ko, munzo mutafi dakeU office d'inmu zaki amsa wasu tambayoyi.

Zuby ido ya raina fata zata fara masu gardama suka hankad'a 'keyarta tanaji tana gani aka sata a mota 'kawayenta kuwa duk sun fito sunyi cirko cirko, hakan yaba sauran yan unguwa damar tsayawa suma suna kallo, haka akaja motar zuby kuwa ba abinda take sai raba idanu.








Love u all my Fan's πŸ‘„πŸ‰
[4/15, 6:55 PM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................52





Jabir zaune yahad'a hannuwansa duka biyu ya tallafi kumatunsa da alama yayi nisa cikin tunani, a zuciyarsa yana ganin gangancin Hassana da wannan mummunan hukuncin data yanke na maka zuby a kotu batare da tanada wata kwakkwarar shedaba.

mama ce tashigo hannunta d'auke da kula da plate ta ajiye gabansa sannan takoma ta bud'e d'an 'karamin pridge d'inta ta d'auko ruwan pure water me sanyi guda biyu ta d'ora a plate takawo gabanshi ta ajiye, zama tayi d'an nesa dashi tare da zuba mashi idanu wani irin tausayinshi ya tsirga mata, tana matu'kar tausayama d'an nata shikuma haka Allah ya jarabeshi da rashin dacen mace tagari wacce duk wata harkallar da'ake ciki yanzu Itace sila, kuma gashi bata duniyar ma baki d'aya.

Wata nannauyan ajiyar zuciya tayi sannan takira sunanshi "jabeer... Firgigi yayi ya kalleta kamar Wanda yafarka daga bacci, sannan ya amsa "na'am mama.
"Tunanin me kakeyi haka? Ajiyar zuciya yayi sannan ya maida dubansa ga mahaifiyar tasa "mama Dole inyi tunani abubuwa da dama sun d'auremin kai nayi tunani nayi nazari amma ban hango wata kwakkwarar hujja da Hassana zata kai zuby 'kara ba.

Shiru yad'an ratsa na kimanin mintuna biyu sannan mama ta sauke ajiyar zuciya "to Jabir yazamuyi da wannan Al'amari tunda sunriga sunyi 'kara ai bakin al'kalami ya bushe mudai fatanmu Allah toni asirin koma waye ya aikata wannan mummunan aiki.
"Ameen jabeer ya amsa yana matukar jin ciwon abinda yafaru dashi arayuwa, sannan yajawo kular abinci yafara zubawa dan rabonsa da cin abincin kirki tun lokacin daya gane Hassana ba ita bace ainafin matarsa Hussaina.

Haka yafara cin abincin kamar yana cin magani badan yanajin dad'insaba Haka mama tatasashi gaba tana rarrashinsa har yad'anci da dama sannan yakora da ruwa me sanyi.


** ** **



A 6angaren Zuby kuwa tun anar da police suka angiza "keyarta Zuwa office d'insu suka shiga tuhumarta da tambayoyi amma fir ta 'ke'kashe 'kasa tace ita batasan kome game da kisan Hussaina ba. Haka yan sandan sukayi ta fama har suka gaji suka tattara kome suka ajiye suna jiran ranar daza'a fara gudanar da shari'ar a kotu.


*kotu* πŸ”¨

'Katon d'akin gudanar da shari'a yacika ma'kil da jama'a maza da mata yan kallo dakuma wad'anda shari'ar ta shafa. Zuby kuwa tana tsaye Inda ake ajiye wad'anda ake zargi a kotu, sai raba idanu takeyi, gefe ga d'ansandan dake tsare da ita,
yan kwanakin datayi a kulle har fatar jikinta tayi duhu sai 'kuraje dasuka firfito a jikinta wad'anda suke nuna alamun tasha cizon sauro ga wata irin rama datayi


Guri d'aya kuma momy ce zaune Sai Hassana gefenta wacce tunda tashigo d'akin shari'ar take faman karanto duk wata addu'a datazo bakinta dan neman nasara gurin ubangiji.

Daddy shima suna zaune a kujerar gaba yayinda Jabir yake kujerar dake bayanshi,
Kotu tagama cika mutane an kaure da surutu kowa na fad'in albarkacin bakinsa, shigowar Al'kali yasa mutanen gurin yin shiru tare da mi'kewa, haka Al'kalin ya isa mazauninsa ya zauna sannan sauran jama'a suka zauna, wani littafi dake gaban Al'kalin ya bud'e yayi wasu yan rubuce-rubuce sannan yayi gyara murya yace "afara gabatar da 'kara ta farko.

Me gabatarwa ya mike tare da wata takarda a hannunsa yafara karantawa kamar haka "shari'armu ta farko shine wacce Hassana mansir company take 'karar 'kawar yayarta Zubaida wacce akafi sani da zuby akan tana zarginta da kisan gillar da akayima 'yar uwarta kuma abiyar Haihuwarta wato Hussaina mansir company, bayan yagama karantawa yakoma ya zauna.

Al'kali ya kalli Zuby yace kece Zubaida? Zuby ta gyad'a kai kamar 'kadangarwa tace "Eh nice ya mai girma mai shari'a, Alkali yace kokinada lauya Wanda ze iya kareki tace "inadashi, nanma Al'kali yayi "yan rubuce-rubucensa sannan yace ina lauyan wanda ke 'kara da kuma lauyan wacce ake 'kara.

Lauyan Zuby ne yafara mikewa yafara gabatar da kanshi sannan lauyan Hassana shima yagabatar da kanshi.






*Kuyi ha'kuri kufara da wannan inshaAllah kafin kome ya dai-daita, kuma inaso zanyi amfani da wannan dama inmi'ka dumbin godiyata ga masoyana a duk inda suke nagode da kulawar da kuka nuna agareni najina da kukayi kwana biyu shiru kuna ko'karin kirana dan jin lafiyata, banida bakin dazan godemaku sai dai ince Allah saka da Alkhairi ya'kara dan'kon zumunci*
[4/17, 8:55 AM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................53




Al'kali ya gama yan runbuce-rubucensa sannan yafara magana "ko lauyan wacce ake 'kara yanada abin cewa.

Lauyan zuby ya mike "inada magana ya mai girma mai shari'a, da farko inaso in tabbatarma wannan kotu me Adalci zuby ba ita bace ta kashe Hussaina, kodan Idan akayi la'akari da 'kawancen dake tsakaninsu dakuma aminci da yarda da juna, bayan wannan an tabbatar da marigayiya Hussaina batada wata 'kawa bayan zuby, kuma Kowa yasan zuby yasan kyawawan halayenta bazata iya koda kashe 6era ba, barantana mutum, kuma 'kawarta aminiyarta, saboda yarda da ita dakuma kyawawan halayenta yasanyama mijin ita marigayiyar yayi kwad'ayin aurenta Wanda a halin da ake ana saura kwana goma a daura aurenta ita Hassana tayi 'kararta akan tana zarginta da kisan yar'uwarta wacce batada wasu kwararan shedu,........ Yana kaiwa nan ya russuna yace "nagode ya mai girma me shari'a, sannan yakoma ya zauna.

Bayan Al'kali yayi rubutu, sannan yad'ago yace "ko lauyan wacce ke kara yanada abin cewa, sai lokacin lauyan Hassana yami'ke ya'kara gabatar da kanshi sannan yafara magana.
"Ya mai girma mai shari'a inaso inyima wacce ke 'kara wasu yan tambayoyi, Alkali yace "anbaka dama, "kotu na bu'katar ganin Hassana a gabanta, wani mummunan fad'uwar gaba Hassana taji sannan tami'ke tana karanto addu'oin samun nasara abakinta.

Bayan tatsaya inda aka umarceta lokacin lauya yafara jera mata tambayoyi tana bashi amsa, karshe yace Hassana to ko zaki iya bayyanama kotu dalilin dayasa kike zargin zuby akan kisan 'yar'uwarki? Hassana tagyara tsayuwa tace "itace tasameni har gida tafad'amun lokacin ina zaune gidan jabeer amatsayin matatarsa marigayiya Hussaina, kuma sannan ta gargadeni akan in gaggauta barin gidan da ita yadace da ta zauna amatsayin matar gidan sannan kuma tayimani kashedi da idan na kuskura nafad'ama wani nima zata kasheni.

Lauya ya'kara jefarta da wata tambayar "taya akayi kika zauna gidan jabeer amatsayin matarsa alhalin kuma yana auren 'yar'uwarki?

Wani irin kuka ya kwacemata dan tunowa datayi da abinda yafaru da ita na *AUREN TAGWAYE* dasukayi itada yar'uwarta, ahankali tasa hannu tashare hawayenta sannan takwashe labarin abinda yafaru kaf tsakaninta da marigayiya Hussaina tundaga had'uwarsu da Hafiz har zuwa lokacin da taro'keta akan tanaso ta zauna gidanta amatsayin ita akan cewa zataje bikin 'kawarta Wanda zubyn ce takitsa mata haka kuma tayi sa'a Hussainar ta amince shine tayi amfani da wannan damar takasheta dan tasamu damar aure mijinta, wannan shine iyakar abinda nasani.

Lauyan ya kalli al'kali wanda yake rubutu acikin littafinsa yace "inaso kotu tabani dama inyi wasu 'yan tambayoyi ga mijin marigayiyar, alkali yace "anbaka dama.

Haka kotu ta umarci ganin jabeer, shima bayan yan tambayoyi da'akayimasa yaba kotu labarin iya abinda yasani tundaga aurensa da Hussaina dakuma zaman da Hassana tayi agidansa amatsayin ita marigayiya Hussainar. Daga kan tambayoyin da lauyan yayima Jabeer yajuya gurin Al'kali yace nagode ya mai girma mai shari'a, sannan yakoma ya zauna.


Lauyan Zuby yami'ke yana gyara rigarsa, yace "ya mai girma mai shari'a labarin da wacce ke 'kara ta bayar kwata-kwata beda nasaba da abinda ake 'kara Kanshi, saboda haka ina ro'kon wannan kotu mai Adalci datayi watsi da wannan shari'ar kuma sannan abima zuby hakkinta akan 'kazafin kisa da aka li'kamata wanda batajiba bata ganiba.

Al'kali yace "ko lauyan wacce ke 'kara yanada wasu 'karin bayani? Lauyan Hassana yami'ke yace "babu yamai girma mai shari'a, bayan Al'kali yayi yan rubuce-rubucensa sannan yadago ya kalli Al'ummar dake cike ma'kil cikin wannan kotu yafara jawabi


"Abisa shedu dakuma bayanai da lauyoyi suka gabatar agaban kotu, kotu ta gamsu da bayanan kowane 6angare dakuma shedun dasuka gabatar saboda haka kotu tayi watsi da wannan shari'ar saboda batada makama, sannan kotu taba zuby damar d'auka 'kara akan 'kazafin kisa da aka li'ka mata.

Wani irin kukan takaici Hassana tafashe dashi dan jin abinda al'kali yafad'a, Zuby kuwa wani shu'umin murmushi tayi, take kotu ta kaure da surutun jama'a Kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

Al'kali yabuga teburin dake gabansa sannan kotu tayi tsit, yana shirin cigaba da jawabi kawai sai ganin wani matashin saurayi sukayi yashigo kotun yana cewa "nine sheda na 'karshe wanda zan war-warema kotu kome da kome akan wannan case din.

Nanfa kallo yakoma kan wannan matashin sunayin ido hud'u da zuby gabanta yayi wani mummunan fad'uwa, Jikinta yafara kyarma wata irin zufa ta keto mata, Hassana kuwa kallonsa takeyi tanaso ta tuna inda tata6a ganin wannan fuskar amma takasa tunowa.






Love u all my Fan's.
[4/19, 1:45 PM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................54





Baki d'ayan hankalin mutanen dake cikin kotun yakoma kan wannan saurayin daya shigo yana fadin zebada sheda, Hassana kuwa mamakine yakamata azuciyarta tace " toshikuma waye wannan ? meya sani game da mutuwar 'yar'uwata,? anya akwai wata sheda daxe bada wacce zatasa Al'kalinnan ya saurareshi tunda har abinda nafad'a besa ya yarda cewa zuby takashe Hussainaba.


Muryar Al'kalince tadawo da ita daga tunanin datake, jitayi yana fad'in "saurayi daga ina? Kotu tanaso tasan ko kai waye kafin kabada sheda agabanta.

'Kara dai-daita nutsuwarsa yayi sannan yafara magana "sunana *Hafiz* kuma ni saurayin Marigayiya Hussaina ne, wannan kuma friend d'inace yafad'a yana nuna Zuby.
Amma ita sona take kuma batada burin daya wuce in aureta, nikuma a lokacin bata gabana saboda ko d'an iska yanaso ya auri mace tagari ba irin zuby ba wacce tagama watsewa a titi, kwatsam saita fahimci muna soyayya da 'kawarta marigagyiya Hussaina, muna cikin wannan halin mahaifin Hussaina yayimata aure saboda ganin ta 6ullo da wasu Halaye marassa kyau.

Haka dai yacigaba dabada labarin iyakar abinda yasani dangane da mutuwar Husssaina kuma ya tabbatarma kotu zuby itace takashe Hussaina saboda tanason ta auri mijinta dan ganin cikin irin jin dadin datake dakuma yanda mijinta ke Sonta.

A lokacin nikuma nabukaci da muhad'a kai idan ta auri jabeer ta kasheshi ta kwashe dukiyarsa tadawo muyi aure dan inada tabbacin babu wani namiji datakeso sama dani, jabir najin haka besan sanda yakalli zuby ba yana jin wata muguwar tsanarta cikin zuviyarsa, dama tun can ba sonta yakeba.

Hafiz yacigaba da magana shine tanuna rashin amincewarta, nikuma alokacin na kunna mata recording din danayimata lokacin datake jaddadamin ita takashe Hussaina, nan take ta tsorata dajin wannan recording dan nayimata barazanar muddin bata amince da bu'katataba zan dam'ka wannan recording hannun hukuma, shine tacemin inbata kwana biyu zatayi shawara.

Ranar data nemeni dan gayamin shawarar data yanke ranar tazubamin guba a lemu dan kada natonamata asiri, Allah yasa inada sauran numfashi 'kanwata takaini asibiti da taimakon lokitoci nasamu kaina, shine nasa 'kanwata tabugama Zuby waya tafad'a mata cewa namutu, tunda aka sallameni daga asibiti na tattara kayana nakoma garin Kaduna gurin abokina, ina can nasamu labarin wannan shari'a shine nazo dan inbada sheda yanzu hakama saukata garin kenan nawuto nan.

Yana kaiwa nan yayi shiru, mutane suka fara kallon kallo ana magana 'kasa-'kasa Kowa nafad'in albarkacin bakinsa, Hassana kuwa mamakine yagama rufeta, haka Momy da daddy, Zuby kau raba idanu kawai takeyi duk illahirin jikinta kyarma yakeyi, zufa tagama rufeta kamar wacce aka she'kama ruwa.



Bayan surutun yad'an lafa Al'kali kuma yayi 'yan rubuce-rubucensa yad'ago ya kalli Hafiz yace "Hafiz kozaka iya gabatarma kotu da wannan recording din dakace ka d'auka lokacinda Zuby take jaddadama itace takashe Hussaina, Hafiz yace Eh ranka shi dad'e yasa Hannu aljihu yaciro wayarsa ya kunno inda recording d'in yake wani mutumi dake zaune gaban Al'kalin ya amshi Al'kali yabashi dama sannan ya kunna mutane sunyi tsit ana saurare bako shakka muryar zuby ce lokacin datake cewa _of course bazan tsaya ina jayayya dakaiba nina kashe Hussaina saboda tashiga gonata_ mutane najin Haka suka d'au salati wasu suka fara Allah wadai da halin Zuby.

Saida Al'kali yabuga teburin dake gabansa sannan kotun ta saurara, "Abisa shedun da kotu tasamu tagamsu da cewa Zuby itace takashe 'kawarta Hussaina dan tanaso ta auri mijinta, saboda Haka wannan kotu me Adalci ta yankema Zuby hukuncin kisa ta Hanyar rataya, muna fata wannan zezama Izna gamasu Hali irinna zuby.

Wani irin murmushin farinciki ya subuce daga bakin Hassana tafad'a Jikin momynta tana kukan farin ciki.

Zuby kuwa wata mahaukaciyar 'kara tasaki tana kuka tana tsinema Al'kalin wai beyi hukuncin tsakani da Allah ba

Haka kotu ta watse zuby na hauka tana zage zage da fizge-fizge aka angiza 'keyarta cikin ba'kar mota wacce ake saka masu ba'kin hali irinnata.






Love u all my Fan's
[4/23, 6:35 PM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................55




*Bayan Wta Daya*
Jabir ne zaune a office dinsa tunani barkatai acikin zuciyarsa, a wani 6angaren kuma na zuciyarsa soda 'kaunar Hassana ne ke d'awainiya dashi, tunanin irin zaman dasukayi yakeyi, Lallai Hassana macece waccce kowane namiji zeyi fatan tazama mallakinsa, kuma uwar yayansa.

yarasa wace hanya zebi ya bayyana mata irin tsananin sondayake mata, jiyayi zaman office din ba dad'i saboda haka tattara takardun dake gabansa yayi ya ajiyesu tare da rufe office din, kai tsaye inda ya ajiye motarsa yanufa yabud'e yashiga sannan yasa key yatayar da motar yad'au hanyar gida, zuciyarsa cunkushe da tunane-tunane.


'Kofar gida ya ajiye motarsa, sannan yafito, da nusaiba suka had'u cikin fara'a da sakin fuska take gaisheshi, "yaya jabeer sannu da Zuwa, "yauwa ya amsa sannan ya tambayeta ina zaki haka? Cikin ladabi tabashi amsa "nan 'Kasan layinmu zanje gidan kitso, "owk to adawo lafiya, yafad'a tare da wucewa kai tsaye cikin gidannasu, da sallama yashiga, mama ya iske zaune tana sauraren redio, jin sallamarsa yasa tarage sautin redion tare da amsa sallamar "kaine yanzu da rana nan, tafad'a tana kai dubanta gareshi, lokacinne kuma ta fuskanci akwai damuwa tattare dashi, bissmillah zauna tafad'a tana tura mai kujerar dake kusa da ita.

Fridge yanufa yafara d'auko ruwa me sanyi sannan yadawo ya zauna tare da sauke wata ajiyar zuciya, ruwan yafasa yafara sha, ahankali yaji wani sanyi na sauka a zuciyarsa, saida yakarasa shanye ruwan sannan ya kalli mama ya gaisheta cikin girmamawa, bayan ta amsa, shiru yad'an ratsa na kimanin minti biyu, sannan mama ta numfasa tace "da alama akwai damuwa tattare dakai, shin miye damuwarka kafad'amin amatsayina na mahaifiyarka idan inada maganinta zanyima idan kuma babu inbaka shawara, idan itama bazatayiba zan taimakama da addu'a domin babu abinda ya gagari Allah.

Hakane mama, ba wata damuwa bace tafe dani, inasone Hassana ta maye gurbin 'yar'uwarta amma kwata-kwata nakasa tunkarar mahaifinta da maganar.

Murmushi mama tayi me d'auke dajin dad'i tace "ni kaina na jima inayima kwad'ayin auren Hassana yarinya me hankali da ladabi da biyayya, ga girmama nagaba da ita, abinda yasa banyima maganaba Dan ina tsoron kada kabi za6ina kuma a maimaita yar gidan jiya, watakila bakada ra'ayin hakan, amma yanzu tunda ka furta da bakinka kabar kome a hanuna inshaAllah kome zezo da sau'ki.
"Kamar da yaushe Alhj yake gida zanje ni insameshi,
"eh to yana komawa gurin 'karfe biyu na rana sai yakuma fita 'karfe hudu na yamma.
"Kada kadamu inshaAllah gobe zanje gidan dakaina,

Cike dajin dad'i jabeer yayima mamanshi godiya, haka suka d'an ta6a fira, saida yaci abinci sai bayan azahar yabar gidan, zuciyarsa cike dajin dad'i dan abinda mama tafad'a mai gani yake kamar yasamu Hassana yagama.


A 6angaren Hassana kuwa tun ranarda aka yankema Zuby hukunci a kotu take jinta cikin wani farinciki, dan jitake kamar da hannunta tad'au fansar kisan da'akayima 'yar'uwarta.
Wani 6angaren kuma na zuciyarta tsananin son jabeer da 'kaunarsa ke d'awainiya da ita, dan d'an zaman dasukayi da jabeer ta fuskanci halayensa akwaishi da tsananin ha'kuri, ga yawan ibada, wasu hawaye taji sun zubo mata Wanda ita kanta batasan dalilin fitarsuba, tasa hannu tagoge sannan tad'aga hannuwanta sama tafara rokon Allah,
"ya Allah ka mallakamin jabeer amatsayin mijina, yazamo uban yayana, Allah ameen tafad'a tare da saukar wasu sabbin hawaye a kumatunta.

Kusan kullum haka take fama da dawainiya da soyayyar jabeer acikin zuciyarta tarasa Wanda zata fad'amawa kota d'an samu sauki dan ita dama bata cika kwashe-kwashen kawayeba, sai kuma ga abinda yafaru da 'yar'uwarta ta sanadin 'kawa tarasa rayuwarta, itakam ta tsani 'kawa duk yanda take.





*ina Baku ha'kuri na rashin samun typing akai-akai, kunsan jiki da jini, akace yauda gobe sai Allah*


Love u all my Fan'sπŸ“
[4/23, 7:26 PM] Zee Elkaseem: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*



*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»



Page......................56




Washe Gari Hassana ce keta kai kawo tsakanin falo da kitchen, kallo d'aya zakayimata ka tabbatar tana cikin nishad'i haka kawai yau ta tsinci kanta da jin wani matsanancin farinciki, yanzuma girki tagama shine take jerawa kan dining, bayan tagama takoma tagyara kitchen ta goge sannan tawuce d'akinta kai tsaye toilet tashiga tashe'ka wanka, sannan ta d'auro Al'wala dan ganin lokacin sallar azahar yayi, tana fitowa ta zura wata doguwar riga tare da saka hijab ta shimfid'a abin sallah, saida ta kammala sallar tayi addu'o'inta tashafa sannan ta isa gaban dressing mirror tafara shafa wani cream me dadin 'kamshi sannan ta murza powder a fuskarta tashafa kwalli tashafama lebenta man le6e.

Wadrope tanufa kai tsaye ta d'auko wasu riga da siket na material orange colour d'inkin yayi matu'kar kyau bakamar datasaka ajikinkta, sai jikin nata tare da Hasken fatar jikinta ya'kara fiddo da kyan material d'in.


Kitchen tanufa tazubo abinci tare da d'auko robar ruwa me sanyi, da madarar holandia takoma d'akinta tafaraci zuciyarta wasai kamar wacce akayima albishir da gidan Aljanna, bayan ta kammala cin abincin ta d'auki plate ta maida kitchen tana mamakin kanta yanda yau taci abinci me yawa haka kamar ba itaba, wanda rabon dataci abincin kirki tun ranar data zauna gidan jabeer amatsayin 'yar'uwarta sai kau yau, a zuciyarta tace anya ba wani abu ke shirin faruwa daniba......



Tana cikin wannan tunanin taji tsayuwar motar daddy, tananan hartaji shigowarsa falo sannan tafito tayimashi sannu da zuwa tawuce d'akinta, binta yayi da kallo da alama akwai abinda yake tunani dangane da ita.

Momy kanta ta lura da hakan, itace tadawo dashi daga tunanin dayake ta hanyar 'kar6ar jakar hannunsa tawuce d'akinsa, shikuma yabi bayanta, ruwan wanka tafara had'a mashi saida yayi wanka ya canja kaya zuwa masu sakai-sakai sannan suka fito zuwa dining, Momy da kanta tazuba masu sannan suka fara ci.

Bayan sun kammala cin abincinne Momy ta kwalama Hassana kira, da sauri tazo tace "gani momy.
Momy ta umarceta data kwashe kayan dasukaci abinci, "to ta amsa sannan tafara kwasa tana kaiwa kitchen saida ta kammala ta gyara gurin tsaf, sannan takoma d'aki wayarta ta jawo ta kunna data best group dinta tashiga na *Ciwon ya mace* ta iske su *Mmn Ummi da Mmn zee da Momyn ramadan da Ameena PA* da dai sauransu anata raha itadai mutanen grouf din na matu'kar burgeta, sallama tayimasu suka amsa, nan fa Ameenoo tafara "oyoyo ga 'kawata, nan Hadiza tace kaji shishshigi 'kawarki ko

Please Login or Register in order to submit comment