Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya rage masa mace domin duk cikar mutum da kamalarsa mutukar bashi da aure to darajarsa dole tayi 'kasa..........'Kwarai hakane a yanzu ya san cewa cikar mutumcinsa shine aure, wannan dalilin ya sanya yaji sha'awar auran a cikin zuciyarsa, sai dai kuma babu wanda ya amsawa cewa zai auri 'yarsa a cikin wa'inda suke kawo masa tallan 'ya'yansu, da kansa zai duba wacce ta kwanta masa a ransa ya aura.

B'angare d'aya ya dauka Uwale da Hamra'u sai suke amfani da daya, Uwale ganin ba zata iya zama a gidan ita kadai ba yasa tace Hamrau ta ta zauna domin ta taya ta zama, hakan yayi mata dadi mutuka domin dama tana neman hanyar da zata kusanta kanta dashi.

Itace ta d'auki ragamar kula da gidan, ta tsaftacce ko'ina har sashensa idan zai fita take 'karbar key a gurinsa ta shiga ta gyara masa ko'ina tasa turare idan taga ya cire k'ananun kayanshi a toilet ta wanke masa tas ta shanya idan sun bushe ta ninnke tasa masa a wardrobe, kullum idan ya dawo daga gurin aiki tsaf-tsaf yake samun gurinsa yana kamshin turare na mussaman, kafin yayi wanka ya fito ta shirya masa abinci da duk wani abinda zai bukata, k'wazon yarinyar da yanda take kulawa dashi da kakarsa yana burgeshi! ba tun yau ba ya gane inda ta dosa a kansa, zai iya auranta saboda kyawawan dabi'unta dama wannan shine abin dubawa a cikin lamarin aure.

'Bangaranta kuwa shawarwari take da zuciyarta kan cewa ta sheda masa tana sonsa ko kuwa ta bari ya furta mata da bakinsa, a ganinta yanzu tunda yayi kudi yafi k'arfinta shiyasa kullum take jin tsoron tunkararsa da maganar gudun wulakanci, sai dai duk sanda masifar sonsa ta isheta daki take shiga taci kukanta ta koshi, kafin ta roki Allah ya za'ba mata abinda yafi alkairi a rayuwarta, amma tayi mamakin yanda akayi Uwale tayi shakulatun 'bangaro da maganar wanda ada can baya har kayan lefe take tarawa burinta bai wuce tabbatuwar auran ba, amma yanzu kwata-kwata bata maganar, ballanatana ta bashi umarnin auranta kamar yanda tayi alkawari a can baya.

Kamar yanda gwamnati ta mutuntashi ta kuma karramashi, shima haka ya mutunta yaransa ya karramasu yayi musu alheri sosai, domin duk rabin alherin da ya samu ya sadaukar musu, a cewarsa suma suna da hakki duba da irin muhimmiyar rawar da suka taka, hakan ya sake janyo masa kwarjini da farin jini a gurinsu da sauran jama'ar gari.

*******
Yau satin sa guda kenan da fara gudanar da aiki a ofis dinsa na mussaman, Uniform dinshi ma na mussaman ne, amma yayi kamanceceniya dana Asp amma kuma akwai bambanci sosai!

Da yake yana da hikima da nazari babu wani abu da ya shige masa duhu, aikin yake kamar wanda ya shekara yana aikin tsaron lafiyar al'umma!

Wasu takardu yake dubawa kira ya shigo wayarsa dake saman tevur din dake gabansa.

Ya ajiye takardun cikin nutsuwa ya daga wayar da fadin.'' Ranka ya dade barka da aiki."

Daga daya bangaran Asp ya amsa da "Barka dai *Jan wuya!* da yake sunan da yake kiransa dashi kenan, ya cigaba da cewa." Gobe ne fa tafiyar nan."

Yayi jim! yana tunanin maganar kafin ya dan ja siririn tsaki! ya manta shaf da maganarsu ta zuwa garin kano domin kai marakunyar yarinyar nan gaban iyayenta........Yace."Ogah me zai hana ka sata a mota ta tafi ai ita din ba yarinya bace zata kai kanta gida."

Ya girgiza kai da fadin." A'a mutumina ba za'ayi haka ba, ni nayi wa mahaifinta alkawarin cewa dani da kai zamu kai masa ita, sannan kuma ba haka dokar aikin take ba, dalilin da yasa ma tuntuni ban shirya tafiyar ba, saboda na fi bukatar yarinyar ta murmure na 'yan kwanaki hakan zai farantawa iyayenta rai su kuma ji dadin ganinta cikin koshin lafiya, to alhamdullihi yanzu naga tayi kyau sosai babu rama ko wani abu wanda ya danganci haka daga gareta."

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin.'' Ranka ya dade don dai kawai ka shirya tafiyar nan dani ne amma da sai dai nace kaje kai kad'ai kawai dalili bana bukatar abinda zai sake danganta ni da yarinyar nan wallahi.''! Cike da takaici ya 'karashe maganar.

Asp na 'yar dariya yace." UMARU ban san me yasa kai da yarinyar nan bakwai jituwa ba, itama yanda kake jin haushinta haka take jin haushinka kullum bata da magana sai taka."

Da sauri yace." Tana zagi! na ko."? Asp din yasa dariya da fadin." In kaji zagi! ma d'aya kenan! shin ka san kuwa maganar da mukayi da ita kwanaki a kanka."?

Kai ya girgiza a k'untace yace." Sai ka fad'a." Jim yayi kafin yace." Na san sharri kawai tayi maka ba zaka aikata hakan ba, duk da dai zuciya bata da 'kashi kuma a lokacin hakan na iya faruwa saboda kusancinku da juna wanda dama shi shed'an burinsa kenan mace da namiji su kad'aice shi sai ya zama na ukunsu."

Tsaf ya fahimci inda maganar ta dosa, murmushin takaici yayi kafin yace." Banyi mamakin jin wannan maganar ba domin duk mutumin da yake 'kin ka, to babu irin k'azafin da ba zai yi a kanka ba, Asp wallahi tallahi! da naso keta haddin yarinyar nan da ba zata kai labari a hannuna ba, saboda na samu dama iri-iri a kanta amma sam ba wannan ne a gabana ba, burina shine na kubtar da ita, sai kuma sharri! ya biyo bayan alkairi."

Yace." Kwarai kuwa shiyasa a lokacin da take maganar na 'karyata ta domin na san ba za ka aikata hakan ba, kawai dai tana neman hanyar da zata tozartaka ne."

Yace."Shiyasa ai nace kayi tafiyarka kawai Asp wallahi kaji rantsuwar musulmi ba naso na sake ganin fuskar yarinyar nan."

Yace." A haba dai kada ka tsananta da yawa abu ne mai sauki wannan ki
'kiyayyar da kukewa junanku ta rikide ta zama soyayya irin wacce take da wuyar samu hakan na iya faruwa.

Ranshi ya 'baci da jin haka tevur din dake gabansa ya buga! murya a sama yace." Allah ya kiyaye Asp bana fatan Allah ya jarrabeni da soyayyar wannan yarinyar, kawai kayi min fatan alkairi ba irin wannan ba."

Asp din yayi mamakin yanda maganar ta fusata shi, sai ya sassauta murya da fadin." Colm dwon mana ka samu nutsuwa, wannan maganar dana nake maka a yanzu ba wai nace lallai hakan ya tabbata ba, kawai a jikina nake jin kamar akwai wani abu da zai ratsa tsakaninka da yarinyar domin anyi irin haka ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, kiyayya ce ake wacce tafi wannan daga karshe kuma sai ta rikide ta juya matsananciyar soyayya."

"Mtsssssw!!!! Yaja wani dogon tsaki kafin ya kashe wayar ya jefar saman tevur tunda ya had'u da Asp bai ta'ba 'bata masa rai irin yau ba........Shi kuwa Asp din sakin baki yayi da wayar a hannunsa yana mamakin al'amarin.


Da takaicin maganganun Asp ya isa gida, takalmanshi kawai ya iya kwancewa ya kwanta saman kujera ba tare da ya cire inform din dake jikinsa ba, rungume hannunsa yayi a kirji ya rufe idanuwansa yana hasaso kammanin yarinyar............. 'baka ce ba sosai ba, idan be manta ba tana da tsayi gami da cikar kirji da fadin kwankwanso, 'kirar jikinta kenan, tana da manyan idanu da d'an k'arami hanci wanda ke tsatstsafo da gumi ako da yaushe, wannan sune kad'ai abunda zai iya tunawa a game da ita!

Yaja tsaki! tare da gyara kwanciyarsa, har yanzu maganar ce take cin zuciyarsa! shi kam a rayuwarsa me zai yi da yarinyar da ta nuna masa tsantsar 'kiyayya irin haka, hanyar jirgi daban ta mota daban.

Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya bude idonshi tare da tsareta dasu, be tashi zaune ba yana daga kwance ya amsa mata, still idonshi na tsaye kanta, sai tace tunda suke bai ta'ba yi mata kallon kurrullah irin haka ba, duk sai ta tsargu dama ta shigo ne domin ta duba taga ya dawo ta kawo masa abinci, jikinta duk sai ya mutu sakamakon kafe ta da yayi da kaifin idanuwansa.

A sanyaye tace." Yayana sannu da zuwa ashe ka dawo."?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yun'kura ya tashi zaune yana kokarin b'alle botiran gaban rigarshi, yace." Na dawo my dear nagaji ne shiyasa ban leka gurinku ba, ina so nayi wanka na huta tukkuna."

Cike da kulawa tace." Sannu ya aikin? bari na had'a ma ruwan wanka ko."? yana kokarin cire rigar daga jikinshi yace." Godiya nake Allah yayi miki albarka." Cike da jin dadi ta amsa, kafin da sauri ta kama hanyar dakinsa, ido ya bita dashi har ta shiga dakin ya girgiza kai a fili yace." Wannan itace matar aure mai cikakkiyar tarbiya nutsuwa sanin ya kamata yayi imani ko zuria ya had'a da wannan yarinyar ba zaiyi kaico ba.

Ta fito falon ta sameshi daga shi sai vest wacce ta matse shi da gajeran wando domin ya cire gabadaya kayan jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta kunyar had'a ido take dashi, ganin haka yasa yayi murmushi ya tashi ya bar gurin, da sauri ta dauki inform din ta kai masa daki ta rataye masa kafin ta bude wardrobe ta dauko masa 'kananun kayan shan iska, ta ajiye saman gado da sauri ta fita daga dakin. tana jin wata annushuwa a cikin ranta, yau ta d'an fara ganin alamun sonta acikin 'kwayar idanuwansa....



*Free pege zai 'kare a pege 40 ga masu bukatar wannan littafin suyi payment domin karanta littafin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kada mugunta!/hassada!/ ganin k'yashi! ya hana ku biya, ku jira na sata ku karanta, wallahi tallahi hakkin wani masifa ne! bala'i ne! muyi kokarin nesanta kanmu da haram! duk kankantarta!*


*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!🏹*
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATION📚🖊️*
____________________



*37&38*
Da yake ta sheda fuskarsa suna shiga ta ganeshi, cike da farin ciki take masa barka da zuwa, ta nuna masa gurin zama da fadin." Ashe tare kake da yaran naka sannu da zuwa ga guri zo zauna." Asp ya zauna kusa da ita yana amsawa ya dora da fadin." Tare muke tafe dasu ai nace su zo su gaisheki sannan kuma ita ZINATU tayi miki bankwana domin gobe idan Allah ya nufa zamuje mu kaita gida da yardar Allah."

Tace."Eh ta sheda min hakan har na bada sakon gaisuwata ga manyan nata, ina fatan Allah ya kai ku lafiya ya kuma dawo daku lafiya."

Gabad'aya suka amsa da ameeen ya Allah.

Falon yayi shuru na minti biyu kafin tace."Duk ya iyalin naka ina fatan kowa lafiya." ? Yace."Kowa lafiya lou insha Allah gabadaya zasu zo su gaisheki." Cike da jin dadi tace."To shikkenan ina nan jina jiran zuwansu."

Tun shigowarsu shida Asp din yake a tsaye a gefen kujerar da take zaune, be kalleta ba ballantana ya fahimci yanayin da take ciki wanda tsayuwarsa a kanta ya janyo mata, k'amshin turaran jikinsa ne yake fizgarta take jin wani irin azababben feelings! ta rasa wace irin masifa ce wannan duk sanda zai kusanceta hankalinta ya kan tashi, gabadaya jikinta ya mutu ta dinga matse 'kafafunta wani irin sanyi ta keji a cikin jikinta, cikin zuciyarta take wasu irin tunane-tunane marasa kan gado............Gyaran murya yayi gabadaya suka kalleshi amma banda ita, Ya dubi Uwale da fadin.'' Ina Hamra'u ne."? Tace."Yanzu-yanzu ta shiga daki watakila ko tana wani uzuri ne."

Ya kalli Asp da d'an murmushi a fuskarsa yace." Yana da kyau kafin ka wuce ku gaisa da matata da yardar Allah."

Jin abinda yace yasa Asp din yin 'yar dariya ya bashi hannu suka tafa da fadin'' Gaskiya ne abokina hakan yayi ya kamata ta fito mu gaisa." Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba ya nufi dakin nata.

Cikin tsantsar fad'uwar gabada gami da jin wani abu mai bala'in d'aci a wuya ta bishi da kallo a lokacin da yake kokarin bude dakin, ba ta janye idonta daga kansa ba har sai daya shiga dakin, sannan ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya wacce ta janyo hankalinsu kanta, sunkuyar da kanta tayi 'kasa tana 'kokarin saisaita yanayin da take ciki, halin da ta shiga a lokacin da yake maganar ta kasa fassara shi shin wai me hakan yake nufi?

Cikin yanayi na damuwa ya sameta, ya kira sunanta ta dago kai tana kallonsa , nan ya hango b'acin rai cikin 'kwayar idonta, cike da kulawa yace."Menene yake damunki."? da yake a kusa take kuma kishi yana cin zuciyarta, sai kawai ta fashe da kuka harda shashsheka!

Hankalinsa ya tashi ya zauna kusa da ita yana rarrashinta, da kyar tayi shuru sai ajiyar zuciya take saukewa, ya rike hannunta da fadin." Waye ya ta'ba min ke."? shuru tayi ba tace komai ba, yace." Ba zaki fad'a min ba ko baki da lafiya."?

Kai ta girgiza alamun a'a. Yace."Babu daya daga ciki amma kike kuka gaskiya ban yarda ba kada ki boye min abinda ke damunki kinji my dear."

Zuciyarta ta sake karyewa kawai sai ta tsinci kanta da fadin." Yanana don Allah Menene tsakaninka da ita."?

Yayi jim yana kallonta kafin yace." Wa kenan."?

Ta kalleshi hawaye na karakaina a saman fuskarta, hannu yasa yana goge mata tare da girgiza kai alamun ta daina.

Cikin shashshekar kuka tace." Kada ka gujeni na riga na makance akan sonka ba zan iya rayuwa da kowa ba idan ba kai ba, zuciyata tana wasiwahsi cewa zaka maye gurbina da wacce 'yar sarkin daka taimaka wannan shine dalilin daya sani zubar da hawaye."

Da murmushi a fuskarsa yake girgiza kansa har yanzu hannunta na cikin nasa yace." Babu wata alaka da take tsakanina da ita, ki cire faruwar hakan a cikin ranki, bani da matar aure sai ke, domin duk kin tara abunda nake da bukata, insha Allahu kece uwar 'ya'yana."

Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, cikin tsantsar farin ciki ta kalleshi da fadin." Nagode masoyina ina fatan Allah ya tabbatar da alkairin da yake tsakaninmu." Ya amsa da "ameen ya Allah."


A 'kalla ya kai minti ashirin da shiga dakin shiru bai fito ba, shi kansa Asp din ya 'kosa ballanatana ita da take jin kamar taje ta sha'ko wuyansa ko uwar me yake a dakin oho!

A cunkushe! ta kalli Asp din da fadin " Ranka ya dade ya kamata mu tashi mu tafi wannan mutumin ya mayar damu shashashai! ya shige daki ya bar mu a zaune zaman jiransa."

Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin." Hakane nima nayi mamakin jimawarsa amma bari na kira wayarsa naji."

Uwale kuwa gyangyadi take bata ma san ma abunda ke faruwa ba.

Yana kokarin kiran wayar tasa, suka fito a tare hannunta na cikin nasa.

Har suka zauna bata kallesu ba, cika kawai take tana batsewa! wani mugun abu mai nauyi ya tsaya mata a wuya.

Gwiwa a kasa Hamra'u ta gaishe da Asp, ya amsa da fuska a sake yana janta da wasa, murmushi kawai take ta kasa hada ido dashi, gabadaya farin ciki ya mamaye zuciyarta, tayi mamakin yanda akayi ya santa har yake kiranta da amarya hakan ya sanya ta sake gazgata maganarsa.


Tashi tayi kawai ta kama hanyar fita ba tare da ta tankawa kowa ba, Nabilan ta kalli mahaifinta nata da fadin." Daddy bari muje kawai sai ka shigo." Ya mike da fadin.'' Aa ku jira ni mana saurin me kuke." duk da taji abunda yace hakan besa ta tsaya ba, ta bude kofa ta fita, ita Nabilan ita ta jira mahaifin nata har sukayi sallama cikin girma da mutunta juna.


*****
Washe gari da wuri suka shirya tafiyar, bahaushe yace sabo turken wawa, 'yan kwanakin da tayi a tare dasu ya sanya duk jikinsu yayi sanyi har dashi Asp din kawai ya daure ne domin ya san dole watarana yarinyar zata bar hannunsa, Madam dai kasa hakuri tayi sai share hawaye take a fakaice.

Al'amarin ya bata mamaki mutuka! ta rasa wane irin so matar take mata, gabadaya sai jikinta ya mutu ta rungumeta da fadin." Mommy kiyi hakuri ba mu rabu da juna ba insha Allah zan dinga ziyartar ki, bayan haka kuma zamu dinga gaisawa ta waya ki daina kuka." tana maganar tana share mata hawaye.

Hannunta ta rike da fadin" Idan kin isa gida lafiya kice ina gaishe da mamanki kuma insha Allah idan an kwana biyu zamu kawo muku ziyara dani da Nabila."

A sanyaye tace."To shikkenan in Allah ya yarda zan sheda mata sa'kon ki daga zarar na isa ."

Nabila ta fito daga daki ta same su cikin damuwa, a sanyaye ta zauna kan kujera tana kokarin magana ya k'araso gurin yana duba agogon dake hannunsa, ya kalleta da fadin." Tashi muje ko." Ta mike tana gyara mayafin jikinta, Nabila ta kalleshi da fadin." Dady zan je nima." kai ya girgiza da fadin." Ki bari idan an kwana biyu zaku shirya zuwa keda Madam." Kamar za tayi kuka tace." Dady ni nafi so naje yau." be saurareta ba ya kama hanyar fita, itama da sauri tabi bayansa domin bata so ta tsaya dogowar magana zuciyarta ta karye, gabadaya suka bita da kallo cike da alhinin rabuwa da ita.


Wayarsa ya kira ya sheda masa cewa sun fito suna jiransa.

Da yake tuntuni ya shirya tafiya sai kawai ya fito daga gurinsa kai tsaye bangaran su Uwale ya nufa domin yi musu sallama.


Fitowarsa ta dauki hankalinsu daga ita har Asp din......Yana sanye da kayan mu na hausawa shadda milk colour dinkin tazarce har kasa, sai yayi amfani da hula zannar bukar mai duhun zare, kafafunsa sanye da bakin takalimi mai gidan yatsa, agogon dake d'aure a hannunsa ma baki ne, yayi kyau sosai fuskarsa tayi kar! sai fitar da annuri take.

Kasa janye idonta tayi daga kansa suna magana da Asp yana tsokanarsa cewa yayi kyau a cikin dogwayen kaya, murmushi kawai yayi kafin ya fara duba cikin motar, sai suka had'a ido da sauri ya janye nasa yana gyara yanayin fuskarsa, babu fara'a a fuskarsa ya kalleshi da fadin." Ya za'ayi tafiyar ne."?

Asp din na 'ko'karin magana direban da zai jasu ya iso gurin, gaisuwa ya mi'ka kafin ya bude motar ya shiga Asp din yayi saurin zama a kusa dashi, ya kalleshi cike da mamakin abinda yayi wato yana nufin shine zai zauna kusa da yarinyar.

Ba tare daya shiga motar ba ya kalleshi da fadin.'' Ni yafi kamata na zauna anan gurin." Ya kalleshi da murmushi a fuskarsa yace."Akwai dalilin da yasa nayi hakan kai dai kawai shiga mota mu, tafi."

Ya jima yana kallonsa gami da hasaso dalilin da yasa zai ce dole ya kusanci yarinyar, ajiyar zuciya ya sauke bada son rai ba ya bud'e motar ya shiga da bisimillah a bakinsa.

Duk maganganun da suke tana jinsu, itama taji haushin abinda Asp d'in yayi kome yake nufi oho! dalilin da yasa kenan yana shiga motar ta kawar da kanta tana ya mutse fuskarta.


Shima bai ce mata komai ba ya mayar da hankalinshi gurin tasbihin da yake ja da carbin dake yatsan shi a ma'kale.

Jefi-jefi suke hira a tsakaninsu kafin Asp din ya juyo ya kalleta da fadin." ZINATU yau sai kwanan gida ko."?

Baki ta ta'be kafin tayi masa wani irin kallo mai kama da harara! kamar wanda yayi mata laifi, ta d'auke kanta uffan ba tace ba.

A maimakon hakan da tayi masa ya 'bata masa rai sai kawai ya fashe da dariya yana kallonta da fadin." Ke kam kin zama hukuma! sai rarrashi abu kad'an ke tunzura zuciyarki kamar ba d'azu ki ka gama kuka ba okey mu yanzu dai ba za kiyi kukan rabuwa damu ba kenan."

Ta kalleshi still dai bakin ta tabe kafin tace." Ranka ya dade meye had'a ni daku da zan zauna ina kukan rabuwa daku ni burina ma nayi nesa daku."

Ya dinga girgiza kanshi yana mamakin furuncinta, yace." Ni dai na san a'iya zaman da mukayi dake banyi miki wani abu ba ballanatana ki k'ullaceni, meye duniyar ma da kuke gaba da junanku dalilin da yasa na shirya zamanku a kujera daya domin ku gaisa da junanku duka ku yafi junanku, duk da ba wani laifi kukayi wa junanku ba amma duk kun tsangwami kanku da kanku, ke ZINATU kece 'karama ya kama kiyi wa abokin zamanki sallama ki gashe shi sannan kiyi godiya akan alkairin da yayi miki wannan shine zaman duniya."

Ta dinga kallon Asp din tana jin takaicin maganarsa, a maimakon tayi abinda ya umarceta kawai sai ta juya tana galla masa harara! wacce ta sanya shi juyowa yana kallonta ido suka hada hakan besa ta daina hararsa ba...........Yanayin fuskarsa kawai ya gyara ba tare da yace mata komai ba ya janye idonsa.

Hakan da yayi ya 'bata mata rai sosai! wato ya ma mayar da ita mahaukaciya, tsaki taja mai tsayi ta kawar da fuskarta.

Beyi niyyar kula taba amma tsakin da tayi masa yasa ya kalleta cikin shan mur! yace." Wa kikewa tsaki."?

Kallon gefen ido tayi masa ta sake jan wani tsakin! ba zato! ya matseta jikin motar! lebunan ya kama ya shiga ligwigiwitasu! hawayen azaba! suka fara sauka saman fuskarta, Asp ya kalleshi da fadin." Ka kyaleta haka mana."

Be kalleta shi ba ballanatana yaji maganarsa ya cigaba da ligwigwita leban! hannunta tasa kan nasa tana kokarin cirewa ya rike sosai! yace." Yau zanga karshen rashin kunyarki."

Asp yace." Ka janye haka tayi kuskure tana neman afuwa."

Yace."Da bakinta nakeso ta nemi afuwar idan ba hakaba to zamuje a haka ban damu ba."

Asp din ya kalleta tayi wujiga-wujiga! ta shiga hannun maza! hawaye harda majina!! dariya ta kusa kubce masa ya danne ya kalleta da fadin ." Ni zan zama sheda idan zaki bada hakuri."

Kanta ta d'aga alamun ta yarda. Ya kalleshi da fadin." Ta yarda zata bada hakurin ka saketa."

Ba lokaci guda ya saketa ba sai da ya niyya tukkuna sannan ya saketa! kawai sai ta kifa kanta jikin motar tana wani irin kuka na tsantsar takaici da bakin ciki.

Asp ya kalleshi da fadin." Baka kyauta ba, nida na had'a ku zama guri daya nayi hakan ne da kyakykyawar munufa dana san abunda za kayi kenan da ban zaunar da kai a kusa da ita ba.

Ta'be baki yayi bece komai ba ya cigaba da jan carbin dake hannunsa.

Motar tayi shuru na 'yan mintina 'kasa-'kasa sautin kukanta yake tashi tare da ajiyar zuciya.

Asp yace." Kiyi hakuri kinji ki bar kukan kada mu sauka a haka wasu su dauka wani abu ne.

Hannu ta dora saman lebanta da yayi tudu ya kumbura saboda ligwigiwatar daya sha ta kalleshi da fadin." Asp ni zaku yiwa haka ko? shikkenan yau zaku ga gatana."

Asp yace."Aa ni meye laifi na babu ruwana wanda yayi laifi ai ya san kansa duk hukuncin da ya kamata kiyi masa daidai ne amma kema ki kiyaye ki dinga girmama na gaba dake."

Bata iya ce masa komai ba taja mayafin jikinta ta rufe fuskarta dashi, gabad'aya jikinta laushi bakinta sai zafi yake, bata tsammanci rashin imaninsa ya kai hakaba ya ligwigwice mata le'be saboda tsabar mugunta har sai dai ya kumbura! wallahi ko za'a mutu ba zata bashi hakuri ba.


Shima ganin yanda ta galabaita yasa beyi wata magana ba, yana dai jin yanda take sauke ajiyar zuciya dalilin kukan da taci, har suka isa masarautar bata sake magana ba, a maimakon tayi farin cikin dawowarta mahaifarta, kawai sai ta shiga kumbure-kumburen kiris take jira ta fashe da kuka.


Maimartaba da kanshi ya fito domin yi musu barka da zuwa, direba yana parking ta bude motar ta fito, ba tabi ta kan kowa ba ta wani fashe da da kuka kamar wata kan'kanuwar yarinya

Please Login or Register in order to submit comment