Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa ba kai ne wanda muke da bukata ba."

Girgiza kansa yayi still da murmushi a fuskarsa, Asp ya cigaba da cewa." Kayi min cikakken bayanin yanda akayi kuka samu nasarar shiga wannan guri da kai da jama'arka ina sauraranka."

Huci! mai zafi ya fesar! kafin yace." Na jima ina jin labarinsa na yawo a gari a duk sanda muka fita farauta sai mun ci karo da irin ta'addanci da yake, muna cin karo da gawarwarkin mutane bila adadin! mata da maza harda kananun yara! idan mun nausa mu ci karo da motoci irin na haya dana gida a k'one! wasu da rai wasu babu rai! mukan tsaya mu basu taimako daidai gwargwado kafin mu wuce! to wannan dalilin yasa ni d'aukar alkawarin ganin 'karshen ta'addancinsa duk da na san bani da alhakin hakan amma zuciyata bata karye ba, na zauna da yarana muka tattauna, da yawa daga cikinsu ba suyi na'am ba, sai dai kuma suka bi umarnina domin bana ajiye kara su tsallake! sannan kuma ba kai tsaye muka tunkari sansanin ba sai da muka bi matakan kariya kamar yanda yake da dabaru! da suddabaru iri-iri to muma muna dashi, domin sai da mukayi kwana biyar a dajin bai san da zaman mu ba! sai lokacin da naso ya san hakan, sosai yayi mamaki da faruwar al'amarin nayi masa bazata! kuma na fara karya alkadarinsa kenan tunda har na samu nasarar fitar masa da wani sassa na jikinsa to da ikon Ubangiji sai na gurfanar dashi a gaban hukuma."!! ya kare maganar cike da cin alwashi da cikawa kansa al'kawari!

Asp yayi murmshi mai ma'ana kafin ya latsa wayarsa serving yayi na recoding din da dauka. yasa wayar gaban aljihun rigarsa, mai da hankalinsa yayi kan rubutun da yake, bayan ya kammala ya sauke ajiyar zuciya da fadin." *JAN GWARZO! MAJA YAKI!* Yanzu zamu d'an huta zuwa anjima zamu d'ora insha Allah, bari nasa nasa a kawo maka abinci da ruwa idan kuma akwai bukatar yin wani uzuri kana iya magana."
Key yasa ya kwance masa hannu amma be kwance kafafun ba.


Ya fito da waya ya kira wani jami'i minti uku ya shigo, ya bashi umarnin kawo abinci mai kyau da ruwa da lemo." Ya 'kame tare da sarawa kafin da sauri ya juya ya fita daga ofis din cikin bin umarni.

Idonsa ya sauke kan agogon dake kafe a ofis din, daya da rabi na rana lokacin sallah yayi, sai ya mike tsaye Asp din ya kalleshi tare da tambayarsa, Uzurinsa ya fada masa, da kansa yaje ya bude masa kofar toilet din ya bashi hanya har ya k'araso bakin toilet wanda da kyar yake cire kafa sakamakon sasarin dake d'aure da kafafun!

Alwala ya d'auro ya fito, shima Asp din ya shiga ya d'aura alwalar ya fito suka tada sallar a tare............... Tare sukaci abinci har suka kare babu wanda yayi magana a tsakaninsu sai dai nazartar junansu da suke.

Asp wani jami'i ya k'ira ya umarceshi da ya shigo masa da yarinyar da suke maganarta.

Tare suka shigo ofis din ya kame tare da sarawa kafin ya fita, Asp ya kalleta tare da nuna mata gurin zama, ta zauna kujerar dake kusa dashi sai ya kasance gabad'ayansu suna fecing Asp din.

Tunda ta shigo kanshi yake k'asa sam baya so ya daga kai ya kalli fuskarta saboda tsabar yanda yake jin tsanarta a cikin zuciyarsa.

Wani irin kallon k'askanci take masa! ranta ya 'baci sosai da ganinshi lafiya lau babu duka! ko mugun rauni! a jikinsa, ita a tunanin yanzu yana nan a galabaice! kammaninsa sun sauya saboda duka! sai taga akasin haka lafiyarsa lau da nutsuwa a tare dashi fuskarsa sai fitar da annuri take irin na musulunci bayan haka kuma an kwance masa sasarin dake hannunsa.........Sai duk jikinta yayi sanyi a fakaice take aika masa da mummunan kallo! wanda take a bayan duhu domin be san abinda take ba, sai shi Asp din dake hankalce da duk abinda yake faruwa.

murmushi kawai yayi kafin yayi gyaran muryar da ta sanya shi dago kansa suka had'a ido, still da murmushin a fuskarsa Yace." *Jan wuya!! Goje kake mugun makangari sai kuree."!* Dariya yayi irin wacce bai ta'ba yin irinta ba, gabadaya suka shagala gurin kallonsa tabbas da ya san yanda dariya ke masa kyau to daya yawai ta ta, shima Asp din dariya yake yace."Na fahimci wannan kirarin yana maka dadi ganin yanda kake kyalkya dariya irin haka."

Hannu yasa cikin suman kanshi ya d'an sosa kafin ya girgiza kai da fadin." Gaskiya ne ina mutukar jin dadin hakan! da yawa jama'ata na kambaba! daraja ta ina farin cikin hakan amma ban ta'ba dariya irin na yau ba, naji dadin hakan ranka ya dade nagode sosai."

Yace." Ka cancanta da duk sunayen dana kira ka a halin yanzu, tun bayan shud'ewar zamanin maya'ki namijin duniya *ALI K'WARA* ban sake jin labari ko yin gaba da gaba da gwarzo irinka ba, *UMARU* muna sanya ran zaka maye mana gurbin wannan bawan Allah da mukayi rashi."

Ya girgiza kansa da fadin." Insha Allahu a shirye nake dana bada gudumawata bakin rai bakin fama zan kare 'kasata cikin ko wane irin yanayi."

Asp yace."Lallai kuwa idan hakan ta kasance 'kasa zata gyaru za kuma a samu sau'kin faruwar munanan ayyukan da sukayi wa kasa dabaibayi.''

Ofis din ya sake daukar shuru na 'yan mintina kafin ya kalleta tana zaune tsuru abin duniya yai mata zafi ganin yanda ma'kiyinta ya samu sake har yana kyalkaya dariya anya kuwa bukatarta zata biya a kansa........Asp ya katse mata tunani da fadin."Meye sunanki."?

Banza tayi masa ta dauke kai domin shi din ma mugun haushinsa takeji...........Ya sake maimaita maganarsa, still bata tanka ba.

Sai ya fusata! ya buga tevur din dake gabansa da karfi! yace." Ko da kurma nake magana."!?

Kawai sai ta fashe da kuka! hawaye share-share! ta d'aga masa hannu da fadin." Kaga saurara Asp ka daina buga min tsawa haka ko ubane ne kai."!?

Ya zuba mata idanuwansa da 'bacin rai a fuskarsa da maganarsa yace." Kina 'karkashin tsaro a halin yanzu duk abinda kike ta'kama dashi dole ki sauke kibi doka idan ba haka ba yanzu zaki fuskanci hukunci mai tsauri."!

Shuru tayi ba tace uffan ba, ya koma ya zauna yana mayar da numfashi! ya kalleta tare da sake maimaita maganarsa.

Cikin izzah! tace." ZINATU nake 'ya ga Saraki sarkin sarakuna arewa wato *SADAUKI OMAR!.*

Asp yayi gaggawar kallonta, ta tsira masa ido cike da tsiwa tace." Ko kana mamaki ne."? duk da akwai hakan a tare dashi amma sai yayi sauri ya basar yasha kunu! da nuna mata shi da hannunsa....."Kin san wannan."? ta kalleshi a sheke kafin tace." Eh na sanshi." yace" meye alakarki dashi kuma wane dalili ne ya kai ki wannan gurun."?

Tsaki! taja za tayi magana ya daga mata hannusa, ta kalleshi babu walwala ko ta kwabo a tare dashi, yace." Wannan shine last warning na k'arshe kada na sake miki magana kiyi tsaki ko abu makamanci haka kina k'ar'kashin hukuma! hukunci zai bi ta kanki duk matsayin ubanki dake kanki." ( Hausawa sukace dan kuka shike janyowa iyayensa zagi) ganin babu wargi yasa ta shiga taitayinta, ya sake maimaita maganarsa.

Kai tsaye tace." *'Barawo* ne shine ya sato ni daga masarautarmu domin samun makudan kudi daga gurin mahaifina."

Kallon mara hankali yayi mata kafin yace." Ya akayi kika gazgata hakan bayan kawai bude ido ki kayi ki ka tsince ki a gabansa a lokacin da wuta take kokarin cinye ki, ina tunaninki yake a lokacin?

Shuru tayi tana tunani, zata iya tuna lokacin da ta fito da daddare domin zuwa partyn 'kawarta dake murnar karin shekara daga cikin shekarunta, tana kokarin bude motarta domin shiga al'amarin ya faru, daga lokacin bata sake sanin komai ba sai bude idonta tayi tai arba dashi a gabanta bayan ya bata taimakon daya dace, amma zuciyarta taki aminta dashi har yanzu tana zarginsa.

Asp ya nuna mata shi da fadin." Wannan da ke zaune a gabanki bai cancanta da wannan sunan ba, domin kuwa ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarki! kada ki sake kiransa da wannan sunan."

Hannu ta d'aga da niyyar magana ya katseta da fadin." Duk abinda kike tsammanin faruwarsa ba zai faru ba da izinin Ubangiji muna da hankali kuma muna gudanar da aiki bisa hankali da nutsuwa saboda haka baki da hurumin magana a yanzu, binkice ya bar kanki a halin yanzu, insha Allah kuma zamu sadaki da iyayenki yau ko gobe."

Bakinta ya mutu murus! ta rasa abin cewa tsabar yanda al'amarin yayi mata bazata! ta dinga zabga musu harara tana murguda baki babu wanda ya sake bi ta kanta maganarsu suke cikin fahimtar juna kafin ya kira wayar ma'aikaci guda, yana shigowa ya bashi umarnin kaita gidansa. Ya kalleta da fadin." Zaki zauna da iyalina na 'yan kwanaki kafin mu gama gudanar da binkice. "

Kamar za tayi magana sai dai taja bakinta tayi shuru, mi'kewa tayi ta kama hanyar fita, direban yabi bayanta cike da bin umarni...........





*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin airtal ko mov
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE

*29&30*
Kusan a tare suka d'auke idonsu daga barin kallonta, Asp din yayi magana amma shi uffan bece ba har ta gama harare-harare! ta fita daga ofis din. Ya d'an ja k'aramin tsaki da fadin." Yarinya nan babu tarbiya a tattare da ita duk kuwa da cewa ta fito daga tsatso mai kyau, ba ta gaji dattako da karamci irin na mahaifinta ba, duk da ba a garin kano muke zaune ba muna da labarin dattakon mahaifinta mutum ne mai karamci da mutunci yana aiki da hankali da ilimi yana kuma gudanar da mulki a bisa tsari na isalama."

Beso ya tanka a cikin al'amarin yarinyar ba amma ganin yanda Asp din yake jaddada maganar yasa yace." Akwai irinsu da yawa wa'inda suka dauki mulki wata tsiya idan akace mahaifinsu nada sarauta ko wani muk'ami sai su dauki girman kai su dora a kansu suna ganin babu wanda ya isa dasu, hakane maganarka mutumin kwarai yana iya haifar baragurbi acikin al'umma jarabtace kawai daga Allah.'' Yace." Kwarai kuwa wannan haka yake sai dai kawai mu roki Allah ya shirya mana zuria baki d'aya." Ya amsa da ameeen ya Allah.

Shuru na minti biyu ya ratsa gurin, cikin 'yar tsokana Asp din yace." Akwai abinda na manta ban tambayi *MAI DAWA!* ba."?
Murmushi yayi da fadin." Akwai sauran tambayoyi kenan."? Girgiza kai yayi da fadin." Tambaya daya ce shin kana da iyali kuwa.''?

Girgiza kai yayi gami da dan ta'be bakinsa.........Asp ya dan zare ido da fadin." Kana nufin babu iyali kenan."
Kai ya daga masa still da murmushi a fuskarsa.

Sai kawai ya shiga girgiza kansa da fadin." Gaskiyar magana yanda kake jarumin namiji mata hudu suka cancanta da kai amma ace ma ko daya babu." cike da alhini ya kare maganar.

Sai abun ya bashi dariya ya dan dara kafin yace." Asp matsalar mata nada yawa shiyasa nayi zamana a haka ba wai don bani da bukata ba, kawai nafi bukatar kwanciyar hankalina nayi duk abinda nake so ba tare da wani ya caza min kai ba.''

Yace." To ai hakan nan ake hakuri dasu da matsalarsu Umaru kowane maigida yana da matsalar iyali mussaman idan mace fiye da d'aya yake da ita, dole ba zaka rasa shi da matsala ba, nima matana biyu sai dai kowacce da gidanta kuma yanzu haka ina shirin yin ta uku da yardar Allah sai na cike domin ina da ra'ayin hakan."

Ya girgiza kai da fadin." Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci a tsakaninsu."

Ya amsa da "Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani."

Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata a gidanka za'a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra'ayinsa zai iya 'kare rayuwarsa da mace daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar'ba hannu biyu tare da godiya a gareshi.


****
Ke'bantacen guri aka ajiyeshi shi kad'ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa.


***
Uwale duk atamfofin da take k'uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al'kur'ani akan bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar'bu.


Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra'u da ita Hamra'un suka yanke shawarar zuwa headquarter 'yan sandan domin samun cikkenan bayani.

Sun jima a tsaye kafin wani jami'i ya sauraresu, Malam Hafi'i mahaifin Hamra'u shine yayi masa bayanin abinda yake tafe dasu.

Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin......Uwale da sauri taje tari gabansa kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin ma'aikatan dake gurin suka fara tambayar ba'asi.

Cikin kuka tace." Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo gurin nan babu wanda yayi mana kallon mutunci Allah da Annabi sunfi karfin wasa amma gabadayanku bakwa tsoron Allah."!

Daya daga cikin musulman dake tsaye gurin ne yace." Tayi masa bayani abinda yake tafe da ita.

Hanci ta fyace kafin." Tace "Mun zo gurin UMARU wanda ku ka d'aure kuna zarginsa da ta'addanci bayan ba haka gaskiya take ba."

Yace." Yi shuru ki kwantar da hankalinki ki daina kuka zanyi miki kokari yanzu." Ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta, tace."Nagode sosai Allah yayi maka albarka." Ya amsa da 'ameen kafin ya umarcesu da suje su zauna a wata rumfa.

Sai da yaga zamansu sannan ya bar gurin, kai tsaye ofis din Asp ya nufa domin sheda masa abinda ke faruwa.
Ya k'ame da sarawa kafin ya sheda masa abinda ke da akwai, kai tsaye ya bashi umarnin shigowa dasu.

Da kanshi ya nuna musu gurin zama yana musu sannu, Malam Shafi'i da 'yarsa suka zauna kamar yanda ya umarcesu Uwale kuwa kai tsaye kujerarsa ta nufa, ya dinga kallonta har ta iso inda yake ta zube gabansa kawai sai ta fashe da kuka tare da rirrike masa kafafu! kuka take sosai tana bashi hakuri.

Tausayi ya rufeshi da kyar ya iya mik'ewa tsaye sakamakon rikon da tayi masa, ya sunkuya tare da sanya hannu ya dago ta ta mike tsaye, rungumeta yayi yana rarrashin gami da bata hakuri.

Ita kuma fadi take." Ku za'a bawa hakuri ku dubi girman Allah kuyi adalci kada ku yanke hukunci akan wanda bashi laifi bashi ne wanda kuke zargi ba.

Hankici ya ciro daga jikinshi, ya goge mata hawaye yana sake kwantar mata da hankali, sai da ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya umarcesu da cewa subi bayan shi.


Kai tsaye ke'bantaccan gurin da aka ajiye shi suka nufa...........Aps din a gaba suna bayansa, yana shiga sai ya basu hanya. gabadaya suka hada ido dashi yana zaune kasan kafet da tire din abinci a gabansa tsaf dashi da nutuswa a tare dashi bashi da wata matsala bayan sararin! dake daure da kafafunsa

Hamra'u da gudu ta iske inda yake, kawai sai ta fad'a kansa tana wani irin kuka! wanda yake nuna tsantsar tashin hankalinta, itama Uwalen da kuka ta karasa gurin duk da ganin da sukayi masa cikin nutsuwa hakan be gamsar dasu ba.

Asp ya juya ya fita yana jimamin al'amarin.

Tun bayan data fad'i jikinsa yasa hannu a bayanta yana dan bubbugawa, a Hankali cikin taushin murya yake rarrashinta, ta dago kai tana kallonsa hawaye sai ambaliya yake a saman fuskarta, kai yake girgizawa alamun ta daina kukan, yasa hannu ya goge mata fuskar sosai yake mamakin irin k'aunar da yarinyar take masa, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sai dai har yanzu bata saki hannunsa ba ta rike tsam a hannunta.


Ya d'ora idonshi kan Uwale da ta dage tana kuka sai kace wacce aka nuna mata gawarsa.

Murmushi yayi tare da mika hannunshi kan fuskarta hawayen ya share mata da fad'in." Kukan bashi da Fa'idah Uwale addua zaki min."

Tace."UMARU kukan shi yake kansa yin kuma shine samun salama, amma a zahirin gaskiya muna cikin tashin hankali bamu da kowa sai Allah shine kuma zai fitar damu."

Yace."Kin gama magana tunda ki kace Allah, kuma gaskiya tayi halinta tun kafin tafiya tai nisa gaskiya ta bayyana cewa wanda suke zargi bani bane nima kuma na san da hakan saboda haka ku kwantar da hankalinku insha Allah zan fito lafiya na cigaba da rayuwa da ikon Allah."

Tace."Idan hakane mai yasa basu kwance maka wannan d'aurin ba, duba fa yanda kafafunka suke daure.

Yace."Akwai dalilin da ya sanya hakan wannan ba matsala bace kada hakan ya daga muku hankali."

Kusan a tare suka sauke zuciya da jin furucinsa suka shiga godewa Allah da abinda yayi musu.

Har yamma suna tare ya saki jikinsa sosai yana basu labarin irin gwagwarmar suka sha a dajin! tace."Kaga Umaru shiyasa kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan harkar ba mahaifinka har ya mutu da abun a cikin ransa saboda haka idan Allah yasa ka kubta to dole ka ajiye wannan sana'ar ka nemi wata domin hakan shine samun nutsuwarmu baki daya.

Domin ya kwantar mata da hankali sai ya amsa mata akan abinda take so, taji dadin hakan kuwa tay tai masa addua da fatan samun nasara akan dukkan abinda ya sanya a gaba.


*****
Ta jima a toilet din tana durje jikinta da sabulai iri-iri kafin ta dauro towel ta fito. idonta ya sauka kan tufafi wanda aka ajiye mata su kan gado komai sabo underwears sai riga da siket na wani material mai taushi, goge jikinta tayi kafin ta zauna gaban mudubi tana kokarin duba man da zata shafa a jikinta, tsaki taja tana hararar tarin kayan kwalliyan dake dressing mirror din duk ciki babu kalar man da yayi mata ballantana ta shafa a jikinta........wani lotoin ta dauka tana jujjuyashi a hannunta sai ya mutse fuska.

Ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta kallo guda kayi mata zaka fahimci cewa tana daga cikin jerin mutane masu sauki kai da daukar rayuwa a sannu, tana da fara'a sosai domin da wuya kaga bacin ranta sai in tura ta kai bango.

Fuskarta yalwace da fara'a ta 'karasa shiga dakin da fadin." Yawwa kin fito ko ga kaya nan na ajiye miki na san za suyi miki dadin sawa.''

Shuru tayi bata tanka ba. Ta kalleta da fadin." Ko dai na sauya miki wasu wannan ba suyi miki ba."?

Tsaki taja da fadin." Don Allah kin cikani da surutu haka na duba na gani okey nagode."

Ranta ya 'baci da abinda tayi mata amma sai ta danne ko alama bata nuna a fuska ba tace." Okey to shikkenan idan kin shirya sai ki fito muci abinci ."

Ta'be bakinta tayi ba tace komai ba ta cigaba da jujjuya abinda ke hannunta.

Juyawa tayi da niyyar fita daga dakin. sai ta dakatar da ita, ta tsaya tana sauraranta.

A yatsine tace." Wannan tarkacen mayukan shafawar taki ba zan iya shafawa ko daya a jikina ba domin ni ba irinsu nake shafawa ba.

Cike da mamaki take kallonta tana mamakin furucinta, tarkace!!! duk man da take shafawa babu na kasa da dubu biyar sai sama amma shine har take magana cewa ita tafi karfin ta shafa a jikinta.

Jinjina al'amarin tayi kafin tayi 'yar dariya da fadin." Lallai 'kawata kina ji da gayu amma idan ba haka ba meye laifin mayuka na ko wannan na hannunki kika shafa ya isheki." Cike da wasa ta karashe maganar..........Sai ta fusata! ta mike tsaye tare da buga mata tsawa! da fadin." Ke kin san wacece ni kuwa? da har kike min wannan banzar maganar."? Ta'be bakinta tayi tace." Ina zan sani hajiya ni dai Daddy ya kira ni a waya ya sheda min cewa zanyi b'akuwa shiyasa nake karramaki bahaushe yace." bakon ka Annabin ka."

Dogon tsaki! taja kafin ta koma ta zauna..........Ita kuma da sauri ta bude kofar dakin ta fita tana mamakin al'amarin.


Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ta kalleta da fadin.'' Ya akayi ne? bata gama shiryawa bane."?

Baki ta dan ta'be kafin tayi 'yar dariya da fadin." Na isketa ta fito daga wanka tana nazari man da zata shafa."

Cike da mamaki tace." Kamar yaya nazari duk cikin mayukan shafawar taki babu wanda yayi mata."?

Tace."Hakan take nufi."

Tana kokarin magana motsin fitowarta ya katseta duk sai suka juya suna kallonta tayi kyau sosai a cikin material din sai dai siket din ya matseta dalili tana da kwankwaso mai fadi da cika sakamakon mai kayan da nata bai kai hakan ba.

Da murmushi a fuskar matar gidan tace." Kin fito."? "Umm." tace kawai ta nemi kujera ta zauna sai wani basarwa take.

Ta kalleta da fadin." Nabila mai yasa ki ka bata wannan kayan kamar sun matseta ki tashi ki dauko mata wasu."

Tace."Mommy kin san duk kayana riga da siket ne kuma bai zama dole suyi mata yanda takeso ba tunda ta fini kiba."

Ta kalleta da fadin." Zinatu baki takura ba dai ko."?

Girgiza kai tayi da fadin." Kada ki damu hakan yayi min daidai domin yawancin kayana haka suke." Tace." To masha Allah ku tashi muje muci abinci." kusan a tare suka mike kai tsaye gurin cin abincin suka nufa.



To duk wasu bayanai da ya kamata ace gwamnati ta san dasu Asp ya harhad'a komai ya turawa maigirma governor domin ya saurara dashi da wa'inda da ke da alhakin hakan, sai dai ya sheda masa cewa ranar asabar shi da wanda ake zargi da aikata ta'addancin zasu shiga sansanin domin binkice akan sassan sannun da zai tabbatar da gaskiyar magana. maigirma governor yayi na'am da maganar ya kuma bada goyon baya akan tafiyar.


*'Yan jarida mane ma labarai suka samu abun yayatawa a gari! gidajen redio da television gami da jaridu labarin abinda suke nunawa kenan cewa ashe wanda ake zargi da *UBAN DABA!* *bashi da ala'ka da zargin da ake masa asali ma shine mutum na farko wanda ya fara karya alkadarin d'an ta'addan da ya addabi kasa da al'ummar dake cikinta, domin tabbatar da gaskiyar magana kakakin rundunar 'yan sanda wato Asp Musa Baharu zai jagoranci shi wanda ake zargi domin gudanar da binkicen sassan hannun wanda ake nema ruwa a jallo...........Sannan kakakin rundunar 'yan sandan ya shedawa mane ma labarai cewa yanzu haka akwai d'iyar Sarkin Kano mai suna Zinatu wanda ake zargin cewa wasu 'bata gari sunyi kidnapping d'inta domin samun kudi daga gurin mahaifinta, amma ha'kan su bai cimma ruwa ba sakamakon zuwan shi wanda ake zargi da ta'addanci mai suna UMARU wanda jama'a suka fi sanin sa da GOJE!* *shine wanda ya zama garkuwa a gareta har yayi nasarar tallafar rayuwarta bayan ya samu nasara akan wa'inda sukayi garkuwa da ita............Wannan shine cikakken rahoton da ya cika garin Katsina dama kewayanta.*


Duk wanda ya danganci masarautar yana cikin farin ciki sakamakon samun cikkaken labarin bayyanuwar ta............Fada ta cika da jama'a masu zuwa taya murna da fatan alkairi maimarta da 'yan uwansa fuskokinsu tamkar gonar auduga saboda tsantsar farin cikin da suke ciki a ranar yini cir masarautar babu masaka tsinke mata da maza wannan ya fita wannan ya shiga.

Gimbiya Aysha da 'yar uwata tare da 'ya'yansu su ka kasance cikin farin ciki mara misaltuwa, Maijidda ma tayi nata murnar daidai gwargwado amma ta ciki na ciki domin kasa zama tayi cikin 'yan uwanta ta nufi b'angaranta

Please Login or Register in order to submit comment