Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matattun macizai da mesa tare da sauran dabbobin da suka farauto,
Abun ya dinga bata mamaki ganin sun daga wani lafcecan maciji sun sanya wuka mai kaifi sun rabashi gida biyu, suka tsire shi a jikin wani itace kafin su barbada masa gishiri da wani abu ja da alamar manja ne sannan suka sanyashi a wuta suna gasawa.

Hankalinta yayi bala'in tashi, karni da wari duk ya cika gurin zuciyarta ta dinga hantsilawa saboda tsabar kyankyamin abunda suke.

Tana nan zaune tana kallon ikon Allah suka gama gasa maciji nan wanda bai sani ba sai yace bushashshan kifi ne suka fara yankarsa da wuka suna ci hankalinsu a kwance.

A gurin ta dinga kyalaya amai duk sai da ta amayo mangwaron data sha, taja gefe guda tare da toshe hancinta.


Sai da dare ya tsala sosai sannan kowa ya nemi makwanci, yana sanya kafarsa yaji ya taka abu cabal! yayi saurin kunna fitilar hannunsa yana dubawa, aman da tayi ne duk ya bata kan shimfidar, tana rakube a gefe guda bacci ya dauketa.

Yaji takaicin bata mai shinfida da tayi yaja tsaki tare da samun ruwa ya wanke kafarsa ya dawo yana tunanin inda zai sanya hakarkarinsa ya kwanta ba don bacci ba.

Kusa da ita ne kadai babu kazanta kuma baya so ya kusanceta gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, domin har yanzu yanayin be bar jikinsa ba.

Kawai sai ya yanke shawarar zuwa gurin yaranshi domin samun matsuguni, tsakaninsu babu wata tazara mai tsayi kuma yana da tabbacin babu abunda zai sameta, rigar jikinsa ya cire ya rufa mata a jikinta sannan ya bar gurin.


Da yake baccin ya dauketa a cikin tsoro da fargaba yasa ta dinga munanan mafarkai da namun daji sun biyo ta zasu cinyeta sai ta farka a gigice! tana kwalla ihu! da fadin." Kura ce! kana inaaaa! *GOJE!!* zata cinyeni."!
Gabadaya suka tashi tsaye da shirin ko ta kwana, amma ba subi bayansa ba, shine ya cimma inda take tsaye sai rawar dari take a tsaye.

Yana zuwa ta rungumeshi, tsam! tsam! tana wani irin kuka da fadin." Kura ce ta biyo ni."!!!

Ya dinga nanata mata addua a kunnuwanta har ta samu nutsuwa, ya zaunar da ita, amma fafur taki zama wai dole sai sun zauna tare. ta rike masa hannu katamau!

Shi kam taushin hannunta da dumin da yake shine yayi masifar sanyayyar masa da jiki,

Babu zato babu tsammani ta janyoshi duk karfinsa, sai ya tsinci kansa a zaune a kusa da ita, yayi mamakin hakan mutuka

A maimakon ta saki hannunsa, tunda yana kusa da ita, sai ma ta sake shigewa jikinsa, tana boye fuskarta a kirjinsa dake waje babu riga sai singlet.

Tsigar jikinsa ta tashi gabadaya ya rasa nutsuwarsa, so yake yafi karfin zuciyarsa amma ta kanainaiyeshi, ta hana shi tsira da mutuncinsa.

Haka suka wanzu har asubah! tana makale a jikinsa, ta hanashi sakat daga yayi motsi zata zabura! ta matseshi, tana goga masa sassan jikinta.

Da kyar ya iya furta magana." Sai ki sakeni haka asubah tayi babu wata dabba da zata zo ta cutar dake."

Kanta ta cire daga kafardarsa tana kallonsa da jajayen idanuwanta tace."Kayi wa Allah da Annabi ka hada tawagarka mu bar dajin nan! duk abunda kuke bukata mahaifina zai baku kada ka cutar dani ko kuma wata dabbar tayi sanadiyar rayuwata.

Ya jima yana mamakin furucinta ashe tana da hankali irin haka.

Sai shi ma yayi mata magana irin ta samu hankali yace."Bana bukatar komai a gurin mahaifinki, kuma ki daina dora zarginki akaina ni ba 'barawo bane Allah ya nufeni ne da na taimaka miki."
Yana kare maganarsa ya nufi bakin kogi da asuwaki a hannunsa, kallo ta bishi dashi har kurewa ganinta kafin ta girgiza kai tana tunanin wani abu akansa.


Sai da gari yayi haske sosai sannan ya dawo gurin dunga nesa yake hangota a kwance rigingine, ta dogare kafafunta a kasa cinyoyinta a waje amma ta suturta gabanta, saurin dauke kansa yayi har ya karasa gurin be sake kuskuran kallonta

Ya dauki rigarshi data cillar masa ya rufa mata a jiki, baya so yana ganin abinda zai tayar masa da hankali.

Ai da sauri ta cire rigar ta cillar da ita can tana ya mutse fuska, zaune ta tashi tace."Idan zaka kwana kana rantsuwa cewa kai ba dan ta addah bane ba zan yarda ba wallahi."


"Ke baki isa nayi rantsuwa a kanki ba, kuma idan kika sake kirana da wannan sunan zan nuna miki ta'addanci na."!
Yanda yayi maganar shi ya tsorata sai tayi shuru amma bata fasa yi masa kallon banza.

Ya dauki rigarsa data jefar yana girgiza kansa ya rasa wace irin yarinya ce me manta alkairi ina laifin wanda ya suturta ka.

Rigar ya sanya a jikinsa, can kasan makoshi tace." Kazami kawai." Yaji abinda tace amma be tanka mata ba, ya juyo, tayi saurin dauke kanta, janyeta yayi kan daddumar ta fadi kasan gurin, ba tare da ya saurareta ba ya bar gurin da daddumar a hannunsa.

Ta ciji yatsa tana bin bayansa da mummunan kallo.

Daya daga cikin yaransa ne ya karbi daddumar ya wanke tas ya shanya kan wata bishiya.


Ya umarcesu da suyi shirin fita shima tare zasuje don baya tsammanin zai zauna da yarinyar tana 'bata masa rai bayan masifar data jefashi a ciki.

Be saurareta ba ya hada kan tawagarsa suka fice ba tare data sani ba, hankalinta ya kai kololowa gurin tashi, lokacin data fahimci ita kadaice a cikin dajin sai ta raina kanta da wayonta, tana kuka ta kama hanya ta cire tsoro da fargaba kokarinta ya za'ayi ta fitar daga kanta daga cikin masifa.


Aikuwa kanta ne ya juye! a maimakon tayi baya sai ta dinga gaba, tana kutsawa cikin dogwayen bishiyu na kuka da tsamiya nan ta dinga arba da manya manyan birai iyaye da 'ya'yansu, hankalinta ya tashi, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, gwagwgwan biri! ido sukayi da wani kato ya tsufa sosai! yana zaune duguzun-duzugun jikin wata narkekiyar bishiyar kuka!

Da baya da baya ta farayi kafin ta juya a sukwane tana falfala gudu hade da kiran sunansa *GOJE!!* shi kuwa Gwaggon birin nan dariya yayi da ya fahimci tsoronsa take sai ya kudiri aniyar tsokanarta, ya fara bin jikin bishiyu yana tsalle yana mata dariya har ya dura a gabanta.

Zubewa tayi tana daga masa hannu yawun bakinta ya bushe "Don Allah kayi hakuri! wayyo Allah na wayyo na shiga uku kuka ta dinga yi hawaye da majina sunyi kaca kaca da fuskarta.

Daya bayan daya suka kewayeta iyaye da kakanni! da alama sassaninsu ta shigo bata sani ba.

Kanta ne ya dinga juyawa a gurin kafin ta fadi, suma tayi, ba tare da bata lokaci ba wannan dattijon birin ya dauketa yasa a kafada, kataf-kataf ya fara tafiya da ita iyalinsa suka rufa masa baya.


Dabaru irin nasu sukayi mata ta dawo hayyacinta koda ta bude ido ta ganta a tsakiyarsu, sai ta mayar da idonta ta rufe jikinta sai karkarwa yake, su kuwa suna zazzaune sai cin manya manya ayaba sukeyi suna gurnani da alama zantuka suke a tsakaninsu.


Sai gefin magariba suka dawo, hankalinsa ya tashi lokacin daya duba sama da kasa be ganta ba,

Dajin ya shiga yana yana sasssare mattatun itatuwan da suka cika gurin, ya fito da sarewa yana busawa tare da cigaba da ratsa cikin dajin.

Zumbur! ta tashi zaune jin busar sarewar na kusanto gurin da suke, daga can nesa ya tsaya yana hango tawagarsu tana tsakiyarsu sai kace 'yar tsana saboda kankanta.

Kai tsaye gurin ya nufa yana cigaba da busa sarewar dake bakinsa, tsakiyarsu ya shiga yayi wani irin tsugo gaban dattijon birin nan yana me cigaba da busa abinda ke bakinsa,

Murmushi yayi ya dora hannunsa me cike da gashi da farata zako-zako a hannunsa a saman kansa, kafin ya cire ya nuna masa ita, yana gurnani!

Kansa kawai ya girgiza ya nufi inda take, hannu ya mika mata ta mike tsaye kafafunta sai kyarma! suke a haka suka bar gurin.

Saboda fargaba da mutuwar jiki yasa gabadaya kafafunta sukayi sanyi da kyar take iya jansu, bakinta ya mutu murus! tsabar tashin hankali binsa kawai take duk inda yaja ta, b'angaransa kuwa yana sane yaki goya ta saboda tayi bala'in bashi haushi, ya tabbata idan wata dabbar ce sai yasha mutukar wahala kafin ya samu damar fito da ita daga cikinsu idan sun barta da rai kenan.
Wannan Gwaggon birin sun saba dashi sosai duk sanda zasu shigo farauta dajin basu da matsala dashi da iyalinsa, wani sa'in ma har kyautar ayaba mai yawa suke basu.

Cikin mawuyacin hali suka karasa gurin da suka yada zangon ya jefar da ita ta fadi kasan gurin, zaune ta mike tana kallonsa ya juya mata baya gabadaya jikinta yayi sanyi domin ba tayi tsammanin zata cigaba da rayuwa ba.

Cikin wani irin amo! taji maganarsa. "Kada ki kuskura ki sake barin gurin nan dana ajiye ki domin kuwa yin hakan na barazana da rayuwarki, babu inda yake da tsaro a cikin dajin nan fiye dana nan gurin, idan kika sake fita yawo to ba zan sake yunkurin ceto rayuwarki ba, yau kwananmu biyu sai kuma munyi sati guda kafin mu koma gida don haka ki kiyaye rayuwarki kibi umarnina kuma mutukar kina bukatar cigaba da rayuwa.''

Kuka ta fashe! dashi ra rarrafa ra rike kafafunsa, " Kada kace haka mana! ka tausaya min a matsayina na mace mai rauni ka fitar dani daga wannan dajin ni ba zan iya sati a guda a cikin wannan tashin hankalina ba, wallahi komai kake bukata mahaifina zai maka ka taimakawa rayuwata."

Yanda take kuka tana rokonsa sai ku dauka mutuniyar kirki ce, haka take dama a duk lokacin da zata ganta cikin wata ukubar takan gigice ta saduda amma daga an kwana biyu sai ta koma baya.

Kafafunsa ya cire ba tare daya ce mata komai ba ya bar gurin, Hakan da yayi ya 'bata mata rai! sai kawai ta kullaceshi a ranta, ta kuma kudiri aniyar wani abu a ranta zata tayar masa da hankali wanda zai daga
Masa hankali dole ya kaita gaban iyayenta........



*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* Katin Mov ko airtal
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE
*5&6*
Kwanciyarta da kamar mintina goma bacci ya kwasheta sai dai baccin beje ko'ina ba dafin kunamar ya fara yawo a sassan jikinta, a gigice ta tashi zaune gabadaya jikinta ya dauki rawa ga wani irin gumi da yake karyo mata! rikicewa tayi ta rasa inda zata sanya ranta taji dadi.

Gurin ya karaso, yana tambayarta, abunda ke damunta, da kyar ta iya bude baki tayi magana.
Bece komai ba ya bar gurin, halin da take ciki besa ta bishi da kallo ba, har ya dawo kanta yana kasa wannan karan kuka ya samu ta nayi, ta dan bashi tausayi kadan, amma bai nuna a fuska ba.

Ya bude gwangwanin Milo din dake hannunsa, wani abune mai duhu a ciki, da alama magani ne aka kwaba da mai, ya kalleta da fadin." Zaki iya nuna min gurin da kunamar ta cijeki."?

Wani irin kallo ta tsawa masa, ta dauke kanta, ranshi ya baci ya daka mata tsawa da fadin" Taimakonki fa zanyi kike min kallon banza kin san wanene a gabanki kuwa."?

Hannu tasa ta goge fuskarta ta daure zugin dake damunta, cikin rashin tsoro tace." Sanin wanene kai bai dameni ba, na dai san ka amsa suna biyu wato *barawo* kuma dan *ta'addah."!*

Ya tsira mata idanuwansa masu kaifi! yana mamakin maganarta, *'barawo kuma d'an ta'addah!* tunda yake a duniya babu wanda ya ta'ba kiransa da sunan *barawo* sai ita, kalmar *d'an ta'addah* kuwa yana ji tana yawo a gari a kansa.

Ya girgiza kansa cikin yanayin maganarsa yace." Wannan shine karon farko da aka ta'ba kirana da wannan kalmomin a gaban idona, kiyi kokarin kiyaye harshenki kafin ki bar hannuna, *GOJE!* nake ba'a kawo min wargi duk tsagerancinki ni zan daidaitaki.

Ta kalleshi a wulakance kafin tace."A hakan? babu tarbiyar! ka fara daidai ta kan............'Barin makauniya yayi ya fuskarta, a take hancinta ya tsinke da jini, tasa hannu ta dafe, jiki na kyarma! take kallonsa, fuskarsa ta rikide da zallan bacin rai!

"Zaki janyo nai miki mugun rauni a gurin nan, babu ruwana da kowace masarauta kika fito, ki sani ba'a nuna ni da yatsa ban karya ba! sannan ba'a jayayya dani, kuma bana magana biyu, *Billahil-lazi hurramanu!* duk sanda kika kara fadin wata mummunar magana akaina sai na illataki."!

Shuru tayi jikinta yayi bala'in mutuwa ganin yanda hancinta ke zubar da uban jini shine abinda yafi zaburar da ita.

Ta kalleshi, yana safa da marwa a gurin, tace." A kan me ba zan kira ka da wannan suna ba? ka sato ni a gaban iyayena domin su baka kudi. akan me ba zan kiraka da *'Barawo* ba me kake bukata? da ka kawoni daji ka ajiye kana azbtar dani, kamar ni *Zinatu* wacce ta gaji sarauta gabada da baya ina rayuwa a wannan kazantaccen gurin, tare da kai makaskanci to saurara kaji da kyau! wannan jinin da ya zuba, be zuba a banza ba, wallahi sai kayi daka sanin zubar dashi."!

Hannu d'aya yasa cikin aljihun jins din dake jikinsa, ya dan sunkuya tare da dogare gwiwarsa, fuskarta ya dago da hannunsa, yana kallonta tana kallonsa, yace."Daga wace masarauta kika fito naga kina girmama kanki kina mutunta kanki, duk wanda ya gaji saurata baya kambaba kanshi kamar yanda ke kike, ina so ki sani zargin da kike a kaina kar ki gazgata, Allah ya kawoni ne tareda jama'ata domin na taimakeki, kuma zan taimakaki bakin kokarina, amma ni zan koya miki tarbiya.

Magana za tayi ya sanya yatsunsa biyu ya murje fatar bakin...........tsam! ya rike lebunan yana ligwigiwitawa, kukan zucci kawai take, jikinta yayi mugun sanyi, yana sakin bakin ta silale a gurin, yaja tsaki da furta "kalankasa kawai."!

Zanin dake nannad'e a jikinta ya janye duk tana jin abinda yake amma tsabar yanda jikinta yayi tubus, ta kasa hanashi sarrafata.

Bai damu da kallon wasu sassan na jikinta ba, domin gabad'aya babu wani feelings a tare dashi, tunda yake sai yace babu ranar da wata mace ta ta'ba tayar masa da hankali duk zubi da kirar dake gareta, Asalima yakan jima bai shiga yanayi na bukata ba, shiyasa auran baya gabanshi, wanda uwar rikonshi wato kakarsa Uwale keyi masa surutu akan hakan.

Da kanshi ya lalubi inda kunamar! ta harbeta ya shefe gurin da magani, ganin duk yaran nashi sun bar gurin yasa ya bude mata jikin domin qunar tasha iska.

Har ya gama abinda yake a gurin bata daina zubar da hawayen takaici ba, tayi turr! da wannan rayuwar da take ciki, a tunaninta hanya ba zata iya had'awa dashi ba, sai gashi w *Kazami- Bagidaje!* irin sa yana ganin sirrin jikinta. tana ganin wannan ko hadimanta (masu yi mata bauta) sun fishi kyawun gani sai gashi a banza yana yin yanda yake so a kanta ya tatta'ba jikinta babu tsoro ko shakka a tare dashi hawaye masu zafi ta goge tana jimanta al'amarin.


Taji dadin maganin sosai domin tana tsaka da tunanin hanyar da zata bi domin kubutar da rayuwarta bacci mai nauyi ya dauketa.

*****
Kana ganinta kaga bafulatana, doguwa ce sambal kyakykyawa a fuska, gata fara tas! ta tara duk wasu abubuwa da da namiji ke bukata amma hausawa sukace wai Dan Adam tara yake be cika goma ba, Hamra'u bata da cikkar kirji hakanan kuma babu baya a tsaye take kamar muciya da zani, sai dai akwai tarbiya da kunya irin ta fulani.

A nutse tayi sallama a gidan, Uwale dake uwar daki ta amsa, da fadin.'' 'Yar halak yanzu nake maganarki a zuciyata.

Murmushi tayi ta cire takalminta, ta shiga dakin, Uwale na kurbar kunu ta mika mata kofin da fadin " Bisimillah."
Girgiza kai tayi tana murmushi tace." Ai daga gida nake kuma sai dana karya kafin na fito.

Dariya tayi irin ta tsoffi tace." Hamra'u kenan wai me yasa duk sanda zan baki abu sai kice daga gida kike ko dai kankyamina kike ne."?

Da sauri tace."Aa Wallahi ba haka bane Uwale na koshi."

Tace."To ai shikkenan duk ya mutan gidan."? Tace."Suna nan lafiya lou alhamdullhi babanmu yace a gaisheki da kyau.''

Tace."Ina amsawa ai a cikin satin nan nake so nazo gidanku mu gaisa sai kuma *UMARU* Yayi tafiya gashi zai dauki sati guda bai dawo ba.

A sanyaye tace."Yanzu fa nake shirin tambayarki ina yake shine zakice yayi tafiya kuma sai yayi sati zai dawo."


Tace."Eh haka yace min da zai tafi kin san dai yanayin al'amuranshi, wani sa'in ma har wata guda ya kanyi yana gwagwarmaya a daji"

A raunane tace." Ni wallahi ba naso yana irin wannan yawace-yawacen tsoro nake kada 'yan fashi su kasheshi ko kuma namun daji su cinyeshi."

'Yar dariya tayi tana sud'e kofin kunun data gama sha tace."Sai dai kiyi hakuri Hamra'u wannan mijin naki yayi nisa addua kawai zaki dinga yi masa.

Tace."Kullum inayi masa addua tare da sauran jama'a." Tace."yawwa hakan yana da kyau, sannan ki cigaba da hakuri insha Allahu, hankalinsa zai karkato kanki."

Idonta ya cika da ruwan hawaye, tace."Uwale sai nake ganin kamar baya sona tausayina kawai nake gani a kwayoyin idonshi.

Tace." To in banda abinki Hamara'u ai sai da so ake tausayi, da baya sonki ba zai tausaya miki ba."

Shuru tayi tana nazarin maganar, itafa tunda take dashi babu wata kalmar so daya taba furta mata, asalima yana kiranta da kanwata, amma bai taba cewa Hamra'u ina sonki ba, sai dai yana tsananin bata kulawa komai take bukata idan tayi masa magana kai tsaye yake mata, wannan dalilin yasa iyayenta da ita Uwalen suke ganin kamar sonta yake, ajiyar zuciya ta sauke ta kudire a ranta cewa idan ya dawo zata cire kunya ta tambayeshi matsayinta a zuciyarsa.

Hamra'u 'yar kanin Uwale ce, tun tana yarinya Allah yasa mata so dakaunar Goje tun be fahinta ba har Allah ya fahintar dashi, be ajiyeta a wani matsayi na daban ba face wanda take dashi a zuciyarsa, gabadaya tunda ya taso baya da ra'ayin soyayya, shiyasa baya fahimtar tarin 'yan matan dake k'aunarsa, Samari da yawa a karkarar tasu suna kishi dashi, a cewarsu sai kace shi kadai ne namiji ko wacce budurwa bata da magana sai tasa, ransu yana baci mutuka, suna kuma bala'in kishi a kan haka, ita kanta Hamra'un akwai wanda yake mutuwar sonta amma fafur taki amince masa ita dai Umaru takeso wanda bata da tabbas a kansa..............

Uwale, kayan dillacinta ta dauko ta nada gammo ta dora aka, tana gyara yafan mayafi take fadin."Hamra'u ni zan fita dama a irin wannan lokacin nake samu na nemi halalina idan kin gama gyara min gidan ga kwado ( dan mukulli) akan taga ki kulle gidan ki bawa Tasallah ta ajiye min."

Tace."Uwale inace Yayana ya hanaki yawon dillaci nan kuma kin san Babana ma baya so me kike bukata ne a duniyar nan."

Tsaki taja da fadin." Sai kiyi kuma kinga tafiya ni babu wanda zai hanani neman kudi." tana gama maganarta tasa kai ta fita daga gidan.
Hamra'u girgiza kanta kawai tayi idan da sabo ta saba da hakan , a nutse ta mike ta fara ayyukan dake gabanta....

***********
*WAIWAYE*
K'allo d'aya nayi masa na fahimci wanene a gabana, ko da yake koda zanyi shekara d'ari ba tare da na sanyashi a idona ba to ba zan mance kammaninsa ba, *Sadauki Omar* kenan Sarkin dake kan karagar mulki a jahar *Kano* Adalin sarki wanda al'ummarsa ke jin dadin mulkinsa.

Yana nan a yanda kuka san shi tsayayye! kuma jarumin namiji! kamanninsa suna nan sai dai alamun girma da ya baibayeshi amma a tsaye yake da jarumta babu abunda ya samu nakasu a cikin halayensa da d'abi'unsa.

Yana tsaye a tsakiyar babban falonshi hannuwansa goye a banyanshi yana kai kawo a gurin, kallo daya kayi masa zaka fahimci yana cikin damuwa.


Cikin nutsuwa da kamala tayi sallama be juyo ba ballantana ya amsa sallamarta,
kai tsaye inda yake ta nufa, sai na bita da kallo, ina hasashen a inda na san fuskarta, Gimbiya *Aysha ce fa* zuciya tayi saurin tuna min ita

Cike da dumbun mamaki nake kallonta tana sanye cikin laffaya milk color da adon zaiba kafarta sanye da takalmi rufaffe irin na sarauta, ban hango wata tawaya a tare da ita ba domin kuwa jikinta ya nuna alamun hutu da jin dadi sai dai alamun shekaru sun tura hakan ma sai ka 'kura ido a kanta sannan zaka fahimci cewa ta kwana biyu a duniya.

Hannunta ta d'ora kan kafadarsa, a nutse ta kira sunanshi *"Jarumi."* be juyo ba ballantana ya kalleta, sai ta dora kanta kan kafad'arsa, hawayen da take boyewa suka kufce, wai shin ya za suyi da wannan ibtila'in da yake kokarin ruguza musu farin cikin da suke ciki na tsayin shekaru masu yawa................




*Ga wanda bai samu damar karanta Sadauki Omar ba, zai tura 1k domin samun damar karanta littafi biyu tare da Goje! Sadauki Omar return*



*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* Mutanan Nijar zaku turo min katin Mov ko airtal na Dala dari.
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE

*15&16*
Sosai ta kwanta jinya sakamakon artabun da sukayi ita dashi, jikinta yayi mugun tsami! ta shar'be! a guri guda da kyar take iya motsa hannu saboda tsabar sanyi da jikinta yayi, al'amarin bai tashi tsananta ba sai da dare ya tsala tukkuna, ta kasa rintsawa gabadaya jikinta ya dauki ciwo! ga wani irin kaikayi da ciwukan jikinta keyi.
Kuka ta dinga yi tana jan hanci! ita kam wannan bala'i bata san ina zata kai shi ba.

Can cikin baccin daya dan fizgeshi ya dinga jin shashshekar kukanta, zumbur ya mike zaune, dama babu wata tazara a tsakaninsu, ya d'auki fitilar dake gefansa ya kunna yana daga inda yake zaune yake haska gurin da take.

Hannu tasa ta kare fuskarta ta sake takure jikinta tana cigaba da zubar da hawayen azabah!.

Ya karaso gurin da fitilar a hannunsa, ya dudduba ko'ina babu wani abu. tsugunawa yayi a gabanta yana duba fuskarta, hannu tasa ta doke fitilar ta fadi. a take ta mutu gurin yayi duhu! ya lalubi fitilar yana kokarin gyara batir din, amma ina ta rikice! yayi-yayi ta kama taki, haka ya hakura ya ajiyeta kafin yace." Kukan me kikeyi ko wani guri yana miki ciwo a jikinki."? Shuru tayi masa, ya sake maimaita maganarsa, uffan ba tace masa ba.

Sai ya yun'kura da niyyar barin gurin tayi saurin rike gefan rigarsa, a rikice tace."Jikina ne duk yake ciwo ko'ina babu dadi."

Yanda yaji tana magana a rikice da alamun kuka ya sanya ya gazgata maganarta, bece komai ba ya sake yunk'urin tashi. Ta rike gefan rigarsa da kyau! yaja! taja! sai ya juyo yana kallonta, da k'yar ta mike zaune kafin tace."Kada ka tafi kayi wani abu wallahi zan iya mutuwa."

Yana da tsananin tsausayi mussaman akan 'ya mace! sai duk jikinsa ya mutu, ya koma ya tsugana yana dan ganin shatin fuskarta duk tayi wani iri idonta yayi jajawur! fuskar duk ta kumbura!.

Be iya tausasa murya ba, amma sai ya tsinci kansa da sassaita muryasa yace."Yi hakuri ki sake min rigar na samo miki magani."!

Hanci taja kafin ta sakar mai rigar ya tashi, tabi inuwarsa da kallo tana sauke ajiyar zuciyar wahala.

'Daya daga cikin yaranshi ya umarta daya had'a masa maganin ciwon jiki, da yake duk suna tafe da guzurinsu, ba tare

Please Login or Register in order to submit comment