Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya nuna musu cewa d'an ta'addan! ya canza she'ka, hakan be basu mamaki! ba domin dama gabad'aya sunyi hasashen cewa babu yanda za'ayi ya cigaba da rayuwa a gurin domin ya tsira da rayuwarsa, to har yanzu dai suna nan akan bakansu zasu cigaba da gudanar da binkice a kansa, ba zasu fasa ba har sai bukatarsu ta biya a kansa.

Maigirma governor da kansa ya 'bukacin san ganin *GOJE!!* gani da ido domin tattauna wasu muhimman abubuwa.

Asp ne ya jagoranci tafiyar........shigarsu government house din keda wuya Maigirma governor ya mike daga kan kujerarsa, Asp yayi mamakin hakan sosai! koda yake yaron ya kai kuma ya cancanta da girmamawa! Governor be zauna ba har sai da suka zauna sannan ya koma ya zauna kan kujerarsa.

Cikin mutumci da girmama juna suka gaisa kafin su shiga tattauna abinda ya tarasu a gurin.

Ya jima kanshi a sunkuye yana nazari da tunanin maganganun governor a kansa. ya sauke ajiyar zuciya, cikin nutsuwa ya kalleshi da fadin." Wannan shine burina a duniya cewar na tabbatu gurin hidimtawa addinin Allah da kuma hidimtawa k'asata Najeria da al'ummar dake cikinta, amma ranka ya dad'e ya za'ayi nayi gogayya da manya-manyan ma'aikatan tsaro! bayan bani da cikkaken ilimi a kan hakan, ba zan boye maka cewa iyakaci na secondary skull ba shin dama hakan tana iya faruwa."?

Maigirma governor yayi dariya irin ta manya kafin yace." Malam bahaushe yace ta yaro kyau take bata k'arko! UMARU! ai bai cancata ka kira kanka da jahili ba, koda iyakacinka primary ka cancanta daka zauna a kujera irin ta Asp saboda jarumtarka, kayi abinda shi Asp din ya kasa dashi da wa'inda suke 'karkashinsa, sun buga! sun buga! sunyi-sunyi! Allah bai basu nasara ba, wannan dalilin ya sanya na d'auko hayar sojoji daga libiya domin su taimaka musu, sai gashi kai d'aya 'kwal kayi aikin mutum dubu! koda baka san (A) ba to ni na d'auke 'ka aiki a'kar'kashin mulki na, kuma zan biya ka albashi mai kyau! sannan kuma na baka kyautar gida da motar hawa, domin ka zauna da iyalinka a ciki."

Sai ya rasa bakin magana kawai ya zubawa Asp ido yana jimanta al'amarin, ganin ya rasa bakin magana ne yasa Asp din ya ari bakinsa domin yaci masa albasa.

Governor ya kalleshi da fadin." Asp babu batun godiya UMARU ya cancanci abinda yafi haka, godiyar ta isa haka, kai dashi duk kuna aiki kan gaskiya gami da kishin 'kasar ku, duka kun cancanci a baku lambar yabo."

Asp ya mika masa sannu cike da farin ciki yace." Mungode sosai da wannan karamci ranka ya dade Allah yasa ayi a gama lafiya." Ya amsa da "ameen ya Allah, kuma Allah ya taimake ku akan aikinku." gabadaya suka amsa da "ameen."

Hotona sukayi sosai suka sanya shi a tsakiya, sai kuma wasu da maigirman governor ya rungumeshi bayan ya bashi lambar yabo da girmamawa!! sosai ya samu kyaututtuka na mussaman daga gurin manya manyan 'yan siyasan dake gidan gwamnatin, su kansu sun jinjinawa kokarinsa,

Cike da tsantsar farin ciki da annushuwa suka fita daga gidan gwamnatin.


******
A daran ranar da al'amarin ya faru ZINATU da kyar ta iya runtsawa saboda 'bakin ciki da takaicin ganin yanda lokaci guda Allah ya daukakashi, ganin hotonsa da governor a lokacin da ya bashi lambar yabo da girmamawa ya mugun daga mata hankali, haka kawai take so ta ganshi a tagaiyare! a wulakance! amma hakan bata samu ba, babban bakin cikinta yanda taga manya mutane na girmamshi tare da kambaba! darajarsa, bata damu da kyaututtukan da ya samu ba kamar yanda ta damu da taga ya k'askanta!

Washe gari da 'kyar ta fito daga dakin domin breakfast, Asp din ya gidan be fita ba, ta gaisheshi kamar bata so, ya amsa yana nazarinta shi kansa d'abi'un yarinyar gabadaya basu bashi sha'awa, shiyasa yake so su shirya ranar da zasu kaita gaban mahaifinta kamar yanda yayi alkawari.

Ya kalleta sai kumbure-kumbure take alhalin babu abunda akai mata, da kulawa a maganarsa yace."ZINATU Ina fatan dai kina jin dadin zama damu ko."

Da 'kyar tace." Um ina jin dadin karamcinku a gareni nagode amma yaushe ne za'a sallame ni haka, tunda dai duk bukatunku sun biya."

Ya kalleta da mamakin maganarta yace." Kamar akwai abunda yake cikin ranki duba da yanayin maganarki."

Murmushi takaici tayi da fadin." Ranka shi dad'e wannan mutumin fa da kuka d'auki son duniya kuka d'ora masa bai da kirki ko kad'an! mugu! ne azzalimi! ni har yanzu ban yarda da gaskiyarsa ba."

Asp ransa ya baci da jin maganarta sai kawai ya rufeta da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, yace." Ban san wace irin kiyayya kike wa Umaru ba, shin me kike so muyi masa bayan wanda yafi haka? mutumin nan ya taimakeki a lokacin da kike bukatar taimako amma duk sanda za kiyi magana a kansa ba mai kyau bace! shin wai me yayi miki da zafi da kika tsaneshi haka."!

Cikin 'Kunci da takaici tace." Ranka ya dade mu bar maganar kawai domin duk abinda zan fada maka a kansa ba zaka yarda ba duba da ganin yanda zuciyarka ta hasala! kawai saboda na kiraye shi da macuci alhalin sunan daya cancanta dashi kenan."

Yace."Kin san Allah ba zan matsa daga gurin nan ba har sai kin sheda min irin cutar da yayi miki da har kike kiran sa da wannan sunan."

Ganin yanda ya kafe ta da idanuwansa yasa jikinta mutuwa, me zata ce yayi mata bayan alkairi, ta san ya taka muhimmiyar rawa a kanta amma haka kawai take jin haushinsa! a yanzu duk abinda zata fada a kansa sharri ne!

Ya katse tunaninta da fadin." Ke nake sauraro na fada miki ba zan bar gurin nan ba har sai naji dalilin da yasa kike tsaneshi."


Bakinta ya sub'ce gurin fadin"Saboda ya keta min haddi sakamakon kad'aicewar mu a dajin."

Ya zuba mata ido da so ya tabbatar da maganarta......."Ya keta miki haddi kamar yaya."?

Ko kunya ta sake lailayo wani sharrin......"Fyad'e yayi min." Tafad'a babu nadama a cikin maganarta.

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta kafin ya girgiza kai da fadin." Wannan shaci fad'i ne ban yarda zai aikata hakan ba."

Murmushin takaici tayi da fadin." Ai dama ba zaka yarda ba saboda jarumtarsa tana burgeka a matsayinka na babban mutumin mai rik'e da mu'kamin Asp bai kamata ace kana mubaya ga wannan k'azamin mutumin ba."

Maganarta sai ta bashi dariya, ya tsaya ya dara kafin ya mike yana duba agogon dake daure a hannunsa yace." Lallai yarinyar nan da gaske kike amma babu damuwa, wannan maganar kuma ba zan barta ba sai mun tattaunata da mutumin naki." Shuru tayi ba tace komai ba, har ya bar gurin, tana zaune a gurin suka fito tare da madam d'inshi dirarriyar mace kyakykawa da kyawun jiki sam ba za kace ta haifi 'yar shekara ashirin ba, hannunta rike da 'yar jakarshi ta rakashi bakin mota ta nayi masa fatan alkairi.
Koda ta dawo a falon ta zauna suna hira jefi-jefi ta d'an saki jikinta sakamakon mutunci da karamcin matar wanda ya janyo mata 'kima da mutunci a idonta......Sai dai kwata-kwata jininta bai had'u da Nabila ba, haka kawai ta tsani yarinyar alhalin babu wani abu da tayi mata na laifi........daidai gwargwado tana bata girma tunda ta fahimci cewa ta d'an girme mata sai take kiranta da Auntyna. hakan yana sake sanyawa kanta ya kara girma domin akwai ta da son girma, gata dai a gidan ubanta amma mulkar yarinyar take, da yake ita din mai saukin kai ce bata damuwa, domin bata mance ingantaccen hadisin nan da yake cewa "ka girmama bakon ka, wannan dalilin yasa take mata duk abinda take so, wanda ita kuma anata 'bangaran take ganin kamar ta isa ne! shiyasa take mata biyayya.....!




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!🏹*
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATION📚🖊️*
_______________



*35&36*
Cikin 'kananun kayan data ajiye masa ya shirya jikinsa tsaf, ya fesa turaranshi mai sanyi da sanyayya rai, ya kimtsa tsaf dashi, kai tsaye b'angaran nasu ya nufa cikin yanayin tafiyarsa ta gwarazan maza!

Uwale kawai ya samu a falon ta zubawa tv ido tana kallo, ya shiga da sallama a bakinsa tayi saurin kallon bakin kofar ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya ta amsa sallamar tare da maida hankalinta kansa har ya k'araso inda take zaune.

Tibin ya d'an kalla kafin ya zauna kusa da ita da fadin." Kallo kike ne."? Ta gyara zama da fadin." Gashinan dai Ina kallonsu da ido amma bana fahintar komai, yanzu nake cewa Hamra'u ta kai min tashar Arewa 24 nafi fahimtarsu duk da cewa su din ma wani sa'in suna da abun haushi."

Ba tare da yace komai ba ya dauki romot ya canza tasha sunnah tv ya kai dai-dai lokacin da marigayi malam Ahmadu B.u.k yake tambihi akan hadisan Annabi Muhammad (SAW) tace." Allah ya jikan wannan malami yayi wa addinin Allah hidima." Yace."K'warai kuwa ba iyalinsa ne kadai sukayi rashi ba duk duniya ne muna rokon Allah ya jadadda rahama a gareshi." Cikin alhini ta amsa da ''ameen ya Allah."

Gurin yayi shuru gabadaya hankalinsu na gurin sauraran malamin, har Hamrau ta 'karaso gurin kafin tace."Yayana na kawo maka abinci nan ne."?

Hankalinsa na gurin malamin yace." Eh ki kawo min nan." Da sauri taje ta shiryo masa abincin a tire ta ajiye masa a gabansa, kasan kafet ya sauka ya tankwashe kafafunsa, yana kokarin bude kwanakun abincin tayi saurin zuwa ta bude cikin nutsuwa ta zuba masa towon farar shinkafa tas dashi lailaye a leda da miyar zogale wacce taji kayan hadi tayi kyau sosai sai kamshi ne yake tashi, ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace."My dear wannan miyar wace kala ce.''?

Tana kokarin magana Uwale tace."Miyar zogale ce, ni nayi sha'awarta nace a maimakon taushe tayi mana ko baka so ne."?

Girgiza kai yayi da fadin." Ai ko bana so tilas naci domin farin cikin ku, na san kuma miyar za tayi min dadi kamar yanda nake bukata."

Hamra'u farin ciki ya lullubeta, murmushi tayi ta tashi daga gurin taje ta samu kujera ta zauna.

A nutse yake cin abincin yana yaba nutsuwa da nagartar yarinyar, duk inda ake tunanin mace ta kai, komai Allah yayi mata nutsuwa tarbiya uwa uba iya girki na zamani dana gargajiya, tunda yake cin abincinta bai taba cin karo da kuskure ba, komai yana masa dai-dai wannan dalilin yasa yake zagewa ya cika cikinsa ba tare da wata fargaba ba, ya cinye wanda tasa masa tas ya 'kara wani yaji dadin miyar sosai da sosai.

Koda ya kammala cin abincin, sai ta kwashe kayan ta nufi kicin dasu domin wankewa........Ajiyar zuciya ya sauke bayan barin ta gurin, ya janye idonsa daga hanyar da tabi, Uwale ta kalleshi da fadin." UMARU ni kuwa ina labarin wannan yarinyar."?

"Wace yarinya kenan."? Yafada idonshi a tsaye a kanta.

Tace." Yarinyar da ka taimaka mata wacce ake maganar 'yar sarkin kano ce."

'Bata fuska yayi da fadin'' Tana nan Lafiya." daga haka sai yayi shuru da bakinsa.

'Yar dariya tayi irin ta tsaffi ta dauki goro ta gutsira kafin tace."Haka kawai nake maka sha'awar auranta"

Ya kalleta da mamakin jin furuncinta, da kyar yace."Me yasa kike min sha'awar auranta bayan duk ga 'yan mata nan masu hankali da tarbiya''

Shuru tayi na minti biyu kafin tace."To UMARU kaine ai kamar mara lafiya duk macan da akayi magana maganarta sai ka 'bata ranka abinda yasa nayi maka maganar yarinyar domin naji abinda yake
zuciyarka na d'auka ko akwai alakar soyayya a tsakaninku."

Girgiza kansa yayi da fad'in" Babu kuma ki cire hakan a ranki, halin da ake ciki a yanzu shine ina binkice akan yarinyar da zan aura."

Fuskarta a sake tace." To masha Allah, nayi farin cikin hakan, amma UMARU ya za kayi da wannan yarinyar Hamra'u ta jima tana sonka don Allah kada ka watsa mata 'kasa a ido"

Murmushi yayi kafin yace."Ai ita zan aura da ikon Allah." sai ta wangale baki tana kyalkyala dariyar farin ciki ta dafa kansa da fadin." Kai masha Allah naji dadin wannan al'amari UMARU Allah ya tabbata da alkairi ya nuna min lokacin da zanga zuriarka, amma ina alfarma a gurina."

Ya kalleta da fadin." Wace alfarma kuma"? tace." Bana so aja dogon lokaci ayi komai a gama a lokaci k'ankani." Yace."Kada ki damu insha Allahu daga na dawo daga training za'ayi komai a gama da yardar Allah." tace." to Allah ya tabbatar mana da alkairi" ya amsa da ameen ya Allah."

*****
A daran ranar Asp ya umarce su ita da Nabila yace su shirya zasuje unguwa, ba a son ranta ta shirya ba, suka fito harabar gidan a tare sai cika take tana batsewa tana ya mutse- ya mutse, ita kuwa Nabila kamar koda yaushe fuskarta a sake kamar gonar audiga sa'i da lokaci ta kan yi mata magana, idan ta kama, sai taga dama take amsawa, a bayan motar suka zauna Asp din ya zauna kusa da direbansa.

Babban super market suka nufa, ya kalleta da fadin." Duk abinda kike da bukata kina iya dauka." Uffan ba tace masa ba tayi gaba tana zagaye gurin, girgiza kansa kawai yayi ya matsa can gefe tare da fito da wayarshi.

Abokin nashi ya kira, don yanzu UMARU ya zama abokinsa duk da ya girme masa, amma abota suke tamkar tare suka taso aiki yasa sun shak'u da junansu,

Cike da girmamawa ya daga wayar suka gaisa kafin Asp din yace." Ka tsammaci zuwana gurinka yanzu."

Cike da mamakin hakan yace." Ina fatan ba wata matsala bace." Yace." Alkairi ne zamu tattauna wasu batu masu muhimmanci" Yace." Okey to shikkenan sai ka shigo din" sallama sukayi kafin kowa ya kashe wayarsa.


Turaruka kawai ta iya dauka sai kayan za'ki data jida sai kace shazumamu! haka take da shan zaqi kamar me a cikin hakoranta ma akwai wanda suka dan samu matsala duk ta dalilin shan zaqi.

Tana gama tsintar abunda take bukata ta mi'kawa Nabila kwandon kayan, ita kuwa ta kar'ba ta had'a na da na hannunta, kai tsaye gurin total ta nufa da kayan, ita kuma ta fita daga gurin.......Tun kafin ta k'arasa bakin motar direban ya bude mata ta shiga ta zauna har yanzu babu sassauci a fuskarta.

Ganin fitowarsu yasa tayi saurin dauke kanta babu wanda ya tanka mata, direban ya bude masa mota ya zauna, kafin ya kar'bi ledojin hannun Nabila ya bude boot ya zuba, ba ta jira ya bude mata motar ba, ta bude da kanta ta zauna tare da bisimillah a bakinta.

Koda suka shiga barrack din direba na kokarin parking ya umarceshi da cewa ya zarce dasu gida mai lamba shida(number 6) kai tsaye can ya nufa yayi parking a inda aka ta nada kafin ya fito da sauri ya bude musu mota.

Tun sa'ilin da Asp din ya kira wayarsa ya sheda masa zuwansa ya fito ya tsaya domin tsumayinsa sai dai ganinshi tare da yarinyar ya d'an sosa zuciyarsa, amma be nuna hakan a fuskarsa ba, cikin wani irin taku na gwaraza! ya isa bakin motar gabadaya hannuwansa goye a bayansa.
Hannu ya mika masa sukayi musabaha ga juna, Nabila da saurin gaske ta gaisheshi har tana kiran shi da Uncle, ya dan saki fuskarsa ya amsa shima ya darajata kamar yanda tayi masa ya 'boye asalin sunanta ya maye gurbin sa da daughter ina godiya." Murmushi kawai tayi tana sunkuyar da kanta.............Kamar yanda ya watsar da lamarinta ita itama haka ta watsar dashi, ta dinga cika tana batsewa tana banka musu harara! tabbas da ta san gidansa ne da tuntuni ta sauka a hanya domin bata bukatar abinda zai had'ata dashi.

Asp ya juyo cikin tsare gira ya kalleta da fadin." Ku shiga ciki ku gaisa da mutan gidan, sannan ke Zinatu sai kiyi mata bayanin kanki."

Ta kalleshi da niyyar caccakarsa, yanda ya sha kunu! yasa ta d'an ji shakkarsa domin ta fahimci shima dan had'in takaici ne mybe tana iya magana ya buga mata tsawa! a gaban mak'iyinta wannan dalilin yasa tayi shuru amma a fuskarta zaka tabbatar da cewa ranta a b'ace yake, Nabila ce tayi gaba, kafin tabi bayanta tana d'acin rai!


Barin su gurin yasa gabadaya suka sauke ajiyar zuciya, suna shakkarta tana shakkarsu, tana da wata baiwa wacce ita kanta bata san tana da ita ba, koda yake jinin saurata gaba da baya yana yawo a jikinta, dole takewa mutane kwarjini a ido, dan dai ta had'u da jajurtattu ne.

A wasu kujeru suka zauna kafin su shiga tattauna abinda ya had'asu a gurin.


Da yake ta sheda fuskarta a tv da jarida yasa suna shiga ta sheda ta, fuskarta a sake take musu lale marhabun tana nuna musu gurin zama, Uwale ba dai karrama mutane ba.

Nabila ce kadai take amsawa, ita kuwa kamar kurma! uffan ba tace ba ta nemi kujera ta zauna tana bin falon da kallo, komai akwai tamkar falon shahararan mutumin daya amsa sunansa. hotonansa dake kafe falon sune suka dauki hankalinsa, uku ne d'aya yana sanye da inform wanda yayi masa bala'in kyau! biyun kuma kayan farauta ne rakwacam! a jikinsa hannunsa rike da wata gora mai lankwasa! kansa nannad'e da wani bakin yadi, gabad'aya jikinsa babu masaka tsinke damtsen hannuwansa daddaure da wasu igiyoyi! hoton ya dauki hankalinta mutuka sai kawai ta tsinci kanta da tunanin rayuwarsu a daji! tsigar jikinta gabadaya ta tashi sa'ilin data tuna sassanyar muryarsa a lokacin da yake rarrashinta idan wata masifa ta sameta, lumshe idonta tayi na minti biyu ta bude still hoton ta cigaba da kallo gabanta na wani irin fad'uwa!.

Har Hamra'u ta shigo falon tana can gurin kallon hotonsa, gaisheta take amma inaa! hankalinta gabadaya na can wani guri, Hamra'u ranta ya b'aci wata kibiyar kishi mai mugun tsini tazo ta tsaya mata a wuya!! kusa da Uwale ta zauna tana jin takaicin abun a ranta.

Maganar Uwale ce ta dawo da hankalinta, da sauri ta janye idonta daga kan hoton tana kokarin saisaita tunaninta ta kalleta da fadin" Kowa lafiya insha Allah gobe nake sa ran had'uwa dasu."

Cikin kulawa tace."To masha Allah, don Allah idan kin isa gidan lafiya ki mika gaisuwarmu gare su, Allah ya kiyaye gaba."

Ciki-ciki ta amsa da "Ameen." Ta dora idonta kan Hamra'u dake ciccin magani! kallon 'yar 'kauye tayi mata kafin taja tsaki a fili tace." Stupid girl!." Uwale ce kawai bata fahimci komai ba, Nabila da Hamra'u sunji lokacin da tayi zagin sai suka rasa da wanda take a cikinsu! Hamra'u tafi tsarguwa cewa da ita take, ba tace komai ba ta tashi domin barin gurin, ta kalleta a yatsine kafin tace." Ugly!!." (Mummuna!) da yake ta danyi karatu ta fahimci maganar, amma bata tanka ba, tayi saurin bude dakinta ta shige tana mugun mamakin al'amarin!
Ita kuwa Nabila duk wannan abun dake faruwa ba sabon abu bane a gurinta ta riga ta san hali shiyasa uffan ba tace mata ba, har ta k'araci iskancinta ta gama, Uwale dai ba jin turanci take ballanatana ta fahinceta, tas taci musu mutunci cikin turanci ba tare da wata shakka ba!


Yace."Kamar yanda muka tattauna maganar a kwanakin baya yanzu ma zan sake dawo mana da ita domin samun solution." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Ka san da cewar duk abunda yake faruwa Commissioner of police baya gari yaje taron k'arawa juna sani dashi da ta kwarorinsa, sai dai duk abunda yake faruwa yana da labarinsa, ya san labarinka kuma yana da cikakken labarin irin muhimmiyar rawar da ka taka, sai dai kuma a lokacin da ya samu labarin cewa ka fara gudanar da aiki, sai ya nuna rashin goyon bayansa akan hakan, A cewarsa lallai sai kaje kayi training domin haka dokar aiki take, banyi masa gaddamar hakan ba saboda na san yana da hujjah mai kyau! amma na sheda masa cewa umarnin mai girma governor ne hakan, duk da hakan ya nuna rashin goyon bayansa da fadin shi zai zauna da governor din domin su tattauna maganar, shine nayi maka maganar a cikin kwana biyar da suka wuce, yanzu ma ina maimaita maka, gobe insha Allah muke sanya ran zai sauka, babu shakka na san cewa zai nemi zama da kai, ina so ka kula dashi da kyau!domin shi din wani irin bahagon mutum ne mai raina tunanin mutane, a tsarinsa bai yarda da cewa wani ya fishi ta kowanne fanni ba, kullum shine wanda ya iya, sannan baya kar'bar kuskure a tsarinsa, wannan kadan kenan daga cikin halinsa, ina so ka kiyayi mu'amula dashi."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Asp tun lokacin da kayi min maganarsa ban ji wani tsoro! ko fargaba! ba (bahaushe yace fad'uwar gaba asarar namiji!!) Ni na fi so ma naje nayi training din domin nagoge! maganar halinsa kuma wannan bai dameni ba, abinda na sani shine ba zan yarda da rashin gaskiya ba! ba zan aminci a hada baki dani a cuci 'kasata ba! ba zan yarda a cutar da wani ba! ba kuma zan yarda da cin hanci da rashawa ba."! Cikin jaddada gaskiyarsa yake maganar.

Asp yaji dadin furucinsa Yace."Naji dadi sosai da wannan alkawarin naka, ina rokon Allah ya tabbatar damu akan hanya ma daidaiciya." Ya amsa da "Ameeen ya Allah."

Tare suka mike tsaye, Asp din yace." Idan babu damuwa inaso mu gaisa da Hajiyan." Cike da jin dadi yace." A haba babu damuwa mutumina muje kawai." Tare suka jera domin shiga gidan suna sake tattauna maganar.



*Free pege zai kare a pege 40 kuyi payment domin karanta labarin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, idan da akwai bukata Sadauki Omar 1k za'a tura domin samun damar karanta littafi biyu wato Goje (Sadauki Omar return) mu nesanta kanmu da haram! duk kankantarta! hakkin wani bala'i ne! kada ganin 'kyashi- hassada mugunta ya hanaki biyan kudin littafi ki jira na sata ki karanta! ki dauki nauyi kin dorawa kanki! abunda ba zai zama dole ba, idan baki da ikon biya babu lallai babu dole akan ki dauki hakkin wani gwara ki hakura!!!!*

*Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, idan kin san ba siya zaki ba don Allah kada ki dauki number ta kiyi min magana🙏🏻*




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!🏹*
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATION📚🖊️*
____________________

_Mijina kazami! ne! to ni kam sai dai nace kiyi hakuri 'yar uwa domin akwai su a cikin maza amma ba duka ba, kuma bake kadai kike da matsala irin wannan ba, amma ki sani ke da kanki kina iya gyara abinki, da wayo da dabara, zahirin gaskiya kazamin namiji nada wuyar sha'ani! duk macan da take fuskantar wannan matsalar daga gurin mijinta akwai hanyoyi masu sauki da zata bi domin gyara masa dab'iu kamar yanda takeso ya kasance!_



FREE PEGE
*33&34*
Police barrack nan ne mafi akasarin ma'aikatan tsaro suke zaune da iyalansu, a nan gidan Asp yake, haka zalika ma anan ne mai girma Governor ya mallakawa UMARU gida tazarar su da Asp din babu yawa gida biyar ne a tsakaninsu, tsarin ginin gidan mai kyau ne, plate ne mai dauke da bangare uku, kowanne 'bangare a shirye yake tsaf da dukkan abinda za'a bukata na yau da gobe, abinda kawai ya rage a gidan mace, don a ranar da ya tare a gidan ma 'yan uwa da abokan arziki surutun da suke masa kenan, cewa a yanzu Allah yayi masa komai na rayuwa, abinda

Please Login or Register in order to submit comment