Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali irin naki kin mayar da kanki yar aiki bayan baki da tabbacin zai aureki.

Tace."Zabbah! duk abinda kika fada hakane babu karya ina san UMARU kuma ina rokon Allah yasa ya zama uban 'ya'ya na, bayan haka kuma duk wata bauta da nake masa ra'ayi na duk surutun da jama'a za suyi akan hakan bai dameni ba."

Ta girgiza kai da fadin." Shikkenan ai tunda kinyi nisa duk abinda zan fada miki a yanzu ba zaki fahimta ba, saboda haka muna zuba ido muga yanda za'ayi wannan auran.

Shuru kawai tayi bata sake magana ba, ita Zabbah ce keta surutu tana bata labarin saurayinta wanda zata aura uffan bata ce ba har suka rabu da juna.

Cikin kunci da damuwa ta shiga gidansu, nan ma ta iske wani bacin ran don mahaifiyarta fada ta rufeta dashi sosai tace."Ina ji ina gani kinfi karfina Hamra'u! saboda kulafucin namiji kullum da gari ya waye hankalinki na wani guri kisa kafa ki fita ki barni da aikin gida, kina can kina bauta a wani gurin, to wallahi nagaji ba zan hanaki ba tunda ke ki kasa kanki amma ba zaki kara fita ba sai kin gama min aikin gida."

Daki kawai ta shige tana kokarin danne kukan dake kokarin kufce mata, wai shin da wane bala'in za taji? ko'ina babu sassauci, bata samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai a gurin Uwale ita kadai ce ke kwantar mata da hankali, amma ita kanta wacce ta haifeta kullum habaici take mata akan wanda ta kwallafawa rai! kowa yana ganin laifinta bayan itama ba ita tayi kanta ba, Allah ne ya halliceta ya sanya mata soyayyar wanda bai san ta nayi ba, dole idan ya dawo ta cire kunya ta sameshi da maganar ko ta san matsayinta..




*Don Allah idan ba sayan littafi zaki ba kada ki dauki number ta Nagode🙏🏻*



*Ga mai bukatar Sadauki Omar 1k zai tura domin samun damar karanta littafi biyu Goje sadauki Omar return*
*#500 via 0542382124......Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari Katin airtal ko Mov
Aa
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________




_*INA MAFITA?*_

_*Matsalar dai guda daya ce data addabi tsakanin ma'aurata rashin hakuri da juna, wanda shike haddasa fitintinu masu yawa, ma'aurata shifa aure gabad'ayansa ibadah ne, jin dadinsa kadan ne, to mai yasa ba za'ayi hakuri da juna a mayar da hankali gurin ribatar ladan dake cikin auran ba*_

*WA YAFI LAIFI*?

_*Shin wa yafi laifi a tsakanin ma'aurata biyu wato mace da namiji? ni dai ba zance ga wanda yafi laifi a tsakanin ma'aurata ba, saboda i dan akayi duba na tsanaki za'a fahimci cewa kowanne bangare da nasa laifin. a matsayina na mace bana goyon bayan 'yan uwana mata akan matsalar data shafi zamantakewar aure wanda kullum ta Allah sai na samu sakon da ya danganci wannan maganar da nake a yanzu, hankalina ya kan tashi idan naji yarinya karama auran fari haihuwa daya biyu kai wata ma auran beyi shekara ba zata kira waya ko ta turo sako tana kuka a taimaka mata da shawarwari yanda zata zauna lafiya a gidan auranta, haka zalika daga b'angaran mazan ma ina samun irin wannan sakkonin cewa baiwar Allah matata tana karanta littatafai na hausa amma bata daukar darasin komai karshe ma tarbiyar tace take lalacewa sakamakon karance-karance littafan da kuke rubutawa. ire-iren wannan sakkonin ba zasu lissafu ba, shin wai ta yaya marubuci zai lalata tarbiya? a ganina marubuci har in dai ya san abinda yake bai cancanta da a kirashi da mai aikata 'barna ba."*_


FREE PEGE

*11&12*
Tun bayan tafiyarsa farauta, Uwale ta samu 'kafar yawo, wanda idan yana gari ko nan da can baya bari taje a cewarsa ta tsufa abinda yafi cancanta a gareta ta zauna a gida ta huta, tunda shi yana iyakacin bakin kokarinsa gurin daukar dawaniyarta da duk wani abu da take bukata na yau da gobe.

Ita kuma a nata bangaran haushin abinda yake mata take, ta dingi mita da surutai tana fadin ba zata zauna zuciyarta ta mutu ba sai ta fita ta nemi kudi kodan bada gudumawa idan sabga dangi ta tashi,

Hakan ya sanyashi
yanke hukunci a duk sanda zai fita sai ya sakar mata kare a gidan ya rufe kofar daga waje yayi tafiyarsa.

A ranar yini take d'aki bata fitowa saboda yanda Allah ya zuba mata tsoron kare a rayuwarta, idan ya dawo gidan sai ta fashe da kuka tana fadin." *UMARU* saboda bani na haifeka shine kake azabtar dani, ka san sarai bana san kare amma saboda mugunta zaka sa min kare sannan ka rufe kofa ka tafi yawo to babu shakka wata rana zaka dawo ka samu gawata."

Sai yace."Uwale idan kina so mu shirya dake ki daina dillanci domin kuwa kina zubar min da mutunci a gari, ni mutum ne mai zuciya da gudun magana bana son jama'a na ganin gazawata a kanki."

*"UMARU* Ba zan daina dillaci ba saboda itace sana'ar data ci da kai ta shayar da kai har ka kai munzali, sannan kuma kana maganar zagin jama'a kai yanzu *UMARU* wane irin zagi ne jama'ar gari ba suyi maka irinshi ba, babu fa wanda yake maka kallon mutumin kwarai mai daraja, kowa yana maka kallon banza tare da kiranka da sunaye masu muni! *B'arawo* *'Dan ta'addah!* duk saboda wannan harkar daka jefa kanka a cikinta, Mahaifinka da bakin cikin hakan ya mutu dalili irin zagi da habaice-habaicen da mutanan gari ke masa, bana rana dayan biyu bakin cikinka ne ya kasheshi."

Duk sanda zata fad'i wannan maganar hankalinsa yana tashi mutu'ka, shi fa har yanzu bai ga illar abinda yake aikatawa ba, na farko bai ta'ba tare wani a hanya ya k'waci abunsa ba, na biyu tunda yake ba'a ta'ba kamashi ya haura wani gida yayi sata ba, na uku bai ta'ba yiwa yarinyar wani fyade ba, abu na karshe shine baya muggan! shaye-shayen da zai janyo masa zubewar kima da mutunci, abunda ya sani shine yana busa Sigari sa'i da lokaci sai shan Shisha da ya zame masa masifa, wannan abu biyun sune abunda ya san yanayi bayan haka azimi sallah akan lokaci basa wuceshi, a ganinsa zagin da jama'ar gari ke masa k'in gaskiya ne, babban abin mamaki kuma duk sanda yayi nisan kiwo dashi da jama'arsa ma'ana suka fita farauta, to duk sanda ya dawo gari da yawa masu zagin nasa sune suke zuwa su gurfana a gabansa domin kar'bar maganin sanyin da yake guzurin zuwa dashi.

Ita kanta Uwalen matan da suke zuwa gurinta kar'bar magani suna da yawa, wani sa'in yana kallo zata zabga kudi masu yawan gaske sai sun nemi alfarma a gurinsa sannan take sassauta musu, amma shi anasa b'angaran 'karamar sadaka yake kar'ba wani sa'in ma kyauta yake bayarwa yace sadaka ayi wa Annabi Salati dubu, Uwale tayi ta jin haushin hakan, idan ya fita sai ta samu buhu mai zurfi ta shiga dakinsa ta kwashe rabin maganin ta boye a karkashin gadonta, idan ta samu sarari ta fita cikin gari ta siyar akan kudi masu yawan gaske.

Wannan dabi'ar ta kakar tashi tana b'ata masa rai, mutuka idan yana so ya tsoratar da ita akan ta daina abinda take sai yace." Uwale shifa aljani ba'a wasa dashi kuma wannan magungunan da nake zuwa dasu ba a banza nake samu ba, musulman aljanu ne suka lamunce min da hakan domin kin san kowane bawa da hanyar abincinsa to nima bani sukayi domin na taimaki jama'a idan kika wuce gona da iri zan barki dasu."

Sai ta tsorata ta dinga rokansa kan cewa ya basu hakuri ta daina abinda take, yace shi babu ruwansa taje ta nemi inda suke ta basu hakuri ba maganarsa bace, kuka irin na tsofaffi take sawa ta rikeshi ta hanashi fita tace lallai sai ya basu hakuri sannan zai futa. sai ya fahimci tayi laushi sannan sai yace tayi shuru ya basu hakuri sun hakura amma kada ta sake aikatawa,

Zata amsa da cewa ba zata sake ba, amma cikin ikon Allah idan aka kwana biyu zata manta ta cigaba da sayar da magani da tsada tana boye kudin a cikin adaka a cewarta da kudin zata hada masa lefen auransa.

***********
Kishingide suka sameshi a gurin hutawarsa, ya mike zaune tare dan gyara zama ido ya tsira musu har suka samu guri suka zauna kafin su gaisheshi, ya amsa still idonshi na tsaye a kansu mussaman mutuniyar tashi da yake hango rashin walwala a tare da ita, koda yake tunda al'amarin ya faru gabadaya walwala da farin cikinsu ya gushe duk abinda suke karfin hali ne.

Gyaran murya yayi kafin yace." Idan kaga wata to za kaga zarah Aysha Safara'u wannan tafiyar taku tana burgeni."

Babu wacce ta saki fuska a cikinsu, domin kuwa suna ciki dashi sakamakon hade kai da yayi da matarsa suna daukarsu a matsayin marasa tawakkali.


D'aya daga cikin hadimanta ne yaje ya sheda mata cewa yanzu - yanzu ya gansu sun nufi gurin hutawar Maimartaba

Da saurin gaske ta shiga daki ta shiryo ta fito kai tsaye can ta nufa, tana sauri taje ta riski abinda ya kai su bayan itace da girki.


Tunda ta doshi gurin take hangoshi gabadaya hankalinsa yana kan wacce ta tsana a cikin matan nasa fuskarsa akwai alamun sassauci da rarrashi, gabadaya ma kamar ita kadai ce a gurin babu Safah.


Ta isa gurin da sallama wacce bata fito sosai ba.

Ya amsa yana kallonta kafin ya kallesu da fadin." Kuna ji 'yar uwarku na muku sallama kunyi shuru."

Safah ta amsa a ciki Aysha kam ko kallonsa ba tayi ba ballanatana 'yar koran nasa.

Ta samu guri ta zauna tana ya mutse fuska da fadin." Ranka shi dade barka da dare."

Ya amsa "Barka dai Maijidda ya hidima." Ta amsa "Alhamdullhi."

Gurin yayi shuru na 'yan mintina kafin gimbiyar ta kalleshi babu fara'a tace."Ranka ya dade wannan magana iyakacin nida kai da 'yar uwata muka tattauna bana son wani yaji abinda ya shafeni da zuriata."


Ya 'bata rai da fadin." Aysha wannan wace irin magana ce? shin ita Maijiddan bare ce a cikinmu."?

Ta d'aga masa hannu da fadin." Allah shi gafarta maka tunda na fara maganata kaji sunan Maijidda a bakina."?

Ransa ya baci mutuka, yace." Ki sauke hannunki idan ba hakana ranki ya b'aci zaki nuna min abinda zanyi ne? ko kuma zaki hanani iko da abinda na haifa? dake da ita Zinat din da ita Safa da Maijiddan duk ikona ne to ke baki isa ki tsara min yanda zanyi ba."

Maijidda ta fashe da kuka da fadin." Ranka ya dade na rasa me yasa har yanzu matarka bata kaunata, meye laifina ? me kuma nayi mata? haihuwa dai Allah ke bayarwa ba wani ba, nima ban cire rai ba."

Tausayinta ya rufeshi, sassauta murya yayi yace." Maijidda kada ki sanya damuwa a ranki nida na aureki nafi kowa sanin halinki babu wanda zai kawo min jita-jita a kanki na dauki maganarsa, maganar haihuwa kuma kada ki cire tsammani, zaki haihuwa da izinin Allah, bayan haka kuma baki da shamaki da zuriata zaki iya yanke hukunci akansu ba tare da na daga kai na kalleki ba."


Gabad'aya suka kalleshi a lokacin da yake wannan maganar, Aysha gaza hakuri tayi tace." Ba zai yuwu ba ranka ya dade ana duba nagarta da cancanta kafin a yanke hukunci babu wani d'a da zan haifa na amince ya dauki wannan matarka taka a matsayin me kaunarsa duk mutumin da ya fito da kiyayyarsa a sarari a kanka be kamata kayi rayuwa dashi ba.

Gabadaya sai suka rasa inda maganarta ta dosa, ta mike tsaye tana gyara lifayar dake nade a jikinta, sunkuyawa tayi da fadin." A tashi lafiya." Bakinsa ne ya mutu kawai ya bisu da kallo a lokacin da suka kama hanyar fita, Ya girgiza kai yana jimanta al'amarin wato dai har yanzu Safa taki zama cikkakiyar mai 'yanci a gidan auranta, tana biyewa Aysha suna zuwa har gabanshi suna masa rashin kunya, to babu shakka zai sa kafar wando guda dasu.


***********
Washe garin ranar da ciwon ciki ya tashi, yaransa suka kewayeshi suna masa sannu, yana kwance idanuwansa a lumshe yake amsawa, daya daga cikin rayan nashi, yace." Allah ya taimaki *Mai dawa!* ga magani na had'a maka." A hankali ya bude idonshi ya dora kan 'kwaryar maganin dake hannunsa, ya mutse fuska yayi ya mayar da idonsa ya rufe da fadin." Alba ka ajiye wannan maganin ka matsa min lemon tsami guda shida."
Da sauri yace." An gama ranka ya dade.

Ya dan sauke numfashi tare da sake rintse idonsa shi kadai yasan irin ciwon da marar shi ke masa.

Alba ya k'araso gurin cike da bin umarni yace." Allah yaja zamaninka ga abinda ka bukata.

Ba tare da ya bude ido ba yace." Nagode Alba kuna iya tafiya Allah ya bada sa'a." Suka amsa da ameen kafin su bar gurin sai da sukayi yi masa kirari kamar yanda suka saba.


Kimanin minti biyar da tafiyarsu ya tashi da kyar, ya jima yana yamutse-yamutse kafin ya dauki matsatstsan lemon tsamin ya shanye tas, ya ajiye ya koma ya kwanta, yana danne saman cikinsa.


Tayi mamaki da gari ya waye be zo ya dubata kamar koda yaushe ba, kawai tashi tayi a bacci ta samu ruwa cikin kwarya da asuwaki sai manya manya ayaba da mangwaro a gabanta.

Ta wanke bakinta da fuskarta, dama can ibadah bata dameta ba domin data dameta da duk yanda za tayi sai tayi ta gabatar da sallolin da suke kanta.


Yunwar da takeji bata tsammanin Ayaba da mangwaro zasu kawar da ita, taja tsaki tana harare-harare a gurin da babu motsin kowa sai ikon Allah.

Jikinta ta duba tayi fututu! fatar jikinta duk ta bushe tayi datti! ta dubi qunar da duk ta bushe tana mata kaikayi, ruwan hawaye ta goge tana tunanin jin dadi da irin rayuwar da take ciki amma lokaci kankanki rayuwa ta juya mata baya.

Kullum idan za ta kirashi da *'Barawo* zai kalubanceta kan cewa shi ba *'Barawo!* bane to idan ba haka ba waye silar zuwanta wannan kasurgumin dajin."?

Ta girgiza kai cikin qunar zuciya ta kudiri aniyar irin rashin mutuncin da za tayi mata huce takaicinta.


Ayaban kadai ta iya ci ta dauki kwaryar ruwan ta shiga tsakanin bishiyu kayanta jikinta ta cire tas ta wanke jikinta, gurin wankan ta jike rigar data zame mata garkuwa, bata damu ba kawai tasa breziyya ta mayar da wandonta ta fito a haka, taja ta tsaya tana dube-dube a gurin.

Babu motsin mutum sai kukan tsintsaye da alama yau ma sun fita sun barta a dajin ita kad'ai.

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke taja tsumman zanin ta dan daure tsakain cinyoyinta kafin ta nemi saman wani kuttuturun icce ta zauna tana tunanin halin da iyayenta ke ciki na rashinta, ta san mahaifinta sai yafi kowa shiga tashin hankali rashinta a kusa dashi.


Ya kai minti arba'in cikin halin ni 'yasu kafin Allah ya sassauta masa, ya mike zaune da kyar! duk da halin da yake ciki hankalinsa na kanta burinshi ya tashi yaje ya duba halin da take ciki.

Ya mike babu kuzari a jikinsa, kai tsaye gurin da take ya nufa...................Rintse idonsa yayi da karfi yana Auziya a fili sakamakon ganin da yayi mata ita ba tsirara ba ita mai tufafi domin breziyar dake jikinta bata hanashi ganin kamai ba........"Subahanallah !
Ya jima a tsaye a gurun yana kiran sunan Allah! kafin yayi namijin kokarin bude idonsa yayi ya'ki da shaid'an da kuma zuciyarsa ya durfafeta babu alamun wasa a tare dashi............





*Don Allah idan ba sayan littafin nan zaki ba kada ki dauki number ta kiyi min magana abubuwan da yawa Nagode🙏🏻🤝🏻*



*Ga masu bukatar sadauki Omar 1k za'a tura domin samun damar karantawa littafin tare da Goje! sadauki Omar return*
*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* katin mov ko airtal.
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE

*23&24*
*Biyu da rabi na sulusin dare!*
Cikin firgitaccan yanayi ta tashi zaune tana kiran sunan Allah! hakan ya janyo farkawarsa dama can bashi da nauyin bacci, zaune ya tashi kafin ya rike hannunta dake wani irin rawa, yace."Menene Aysha."? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka ta rungumeshi tana girgiza kai da fadin." Zinat ce ranka ya dade yarinyar nan na cikin mugun yanayi Allah ya nunan hakan a mafarkina."

Sake rungumeta yayi a jikinsa cikin sigar rarrashi yace."Aysha mafarki ba gaskiya bane kada ki gazgata abinda ki ka gani, bana tsammanin cewa mafarkinki zai tabbata, jikina yafi bani cewa yarinyar nan tana a raye kuma daf take da ta dawo garemu da ikon Allah."

Kallonshi tayi hawaye na tsere a saman fuskarta tace.''Ranka ya dade koda Allah ya nufa yarinyar nan ta dawo gida bai zama lallai a sameta da cikakkiyar lafiya ba ka san dai yanda duniyar nan ta lalace da rashin gaskiya wannan shine babban tashin hankalina."

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Kada ki fadi haka Aysha! zuciyarki ta dinga halarto miki alkairi akan yarinyar nan! adduarki a gareta karbabbiya ce a gurin Allah, kada ki yarda zuciyarki ta yarda da wannan mafarki ki dauka cewa k'anzon kurege ne, a yanzu abinda zakiyi ki faranta min shine ki tashi kije ki dauro alwala ki gabatar da nafila a gaban ubangiji kana ki mika masa kukanki."

Ta sauke ajiyar zuciya da jin sassauci acikin zuciyarta, a hankali ta zame jikinta daga nasa ta sauka daga gadon ta nufi toilet domin daura alwala.

Tana fitowa shima ya tashi ya shiga ya daura alwalar ya fito, lokacin har ta tayar da sallar, jallabiya da gajeran wando ya sanja kana ya gyara dadduma shima ya tayar da tashi sallar.


******
Tun bayan daya sa'ba ta a kafad'a suke buga artabu a tsakanisu, rikon tsauri! yayi mata yana gudu tare da tsallake manya-manyan dutsina da ita a kafadarsa! tayi duk wani kokari gurin ganin ta ceci kanta abun yaci tura! domin mutumin mugun basamude! ne wanda cizo da yakushi basa shigarsa! dukansa take tana cizo duk ta dauke masa fata amma ko ajikinsa, ya riketa katamau! yana gudu! burinsa kawai ya kaita gaban ogansa ya san hakan zai faranta masa rai.

Hakan ne ya kasance kuwa, Ogan nasu yana cikin bacin rai! mai tsanani sakamakon rashin samun nasara! bai ta'ba fuskantar irin hakan ba sai a wannan lokacin, kai kawo kawai yake gurin ya rasa abinda yake masa dadi! ............Amma zuwan babban yaron sa da yarinyar ya faranta masa rai! mutuka, sai kawai ya kwashe da wata 'yar iskar dariya kafin yayi wani irin tsalle! da juyi na jin dadi, ya zuba mata kwala-kwalan idanuwansa!

Bakinsa kawai yake lasa, jikinsa na wani irin tsuma! komai na yarinyar yayi cif da cif! bata da makusa, cikakkiyar mace irin wacce ya jima bai kwanta da irinta ba!

Gurin ya tsit! gabad'aya yaransa sun zagayeta motsin kirki ta kasa, kanta ne ma yake juyawa a gurin, dishi-dishi! take kallonsa har ya karaso inda take zube!

Ya tsugana kusa da ita, sai tayi saurin janye jikinta, ya sha kunu; tare da matsawa jikinta, ta sake janyewa tana watsa masa mugun kallo!

Mahaukaciyar dariya yayi! ya cigaba da lasar lebansa, yana bin sassan jikinta da wani irin kallo na tsantsar sha'awa! Hannu ya kai jikinta, a zabure! ta fitar da hannu ta bashi kyakykyawan mari a fuskarsa! ko gezau! beyi ba sai dai yaransa da suka zabura! sukayi kanta!

Ya daga musu hannu da basu umarnin matsawa baya.

Suka matsa can nesa suka bar shi da ita, zaman dirshan yayi a gabanta ya mika mata tafkekiyar fuskarsa dake cike da kasumba! yace. " Idan hakan yana miki dadi ki sake aikatawa." Ya fada yana sake tura mata fuskar.

Tsaki mai tsayi taja! ta matsa nesa dashi! ya rarrafa kan gwiwarsa ya cimma inda take! kafafunta dake daure da takalmi ya tsirawa ido, babu abunda yafi tafiya dashi irin shara'ban kafafunta, ya kai hannunsa gurin yana shafawa da lumshe ido, janye kafarta tayi da fadin." Allah ya isa!!
Ya bude idanuwansa da suka rikice! da zazzafar sha'awarta!

"Ni kikewa Allah ya isa."? yafada yana nuna kirjinsa.

Ba ta amsa ba, wani irin kallon banza take mai, ya lumshe idonsa ya bude da fadin." Ina sonki saboda kinyi min, ban ta'ba amfani da mace na maimaita ba, amma gani guda da nayi miki naji cewa kece zaki zama mahadin rayuwarta, shekaru sun ja ya kamata ace nima na ajiye k'wai a duniya kece zaki zama uwar 'ya'yana, kinzo hannuna babu wani mahalukin daya isa ya rabani dake."

Maganganunsa suka dinga amsa kuwwa! a kunnanta, ta tsira masa ido tana mamakin furucinsa, kallonsa kawai take ta rasa yanda zata fasaltashi, shi ba mutum ba ba aljan ba.

Ya mike tsaye a kanta! saurin kauda kanta tayi gabanta na lugudan duka!

Blet din dake daure a kugunsa ya fara kokarin kwancewa, tayi saurin tashi tsaye! dariya ya fashe da ita, kafin ya cire blet din ya jefar dashi ya zame wandon............"Innalillahi- wa'ina ilahi raji'un! abinda ta ambata kenan, ta rintse idonta da karfi! tunda take bata ta'ba ganin tsaraicin namiji ba sai a kansa, yanda yake mara fasali to hakama gabanshi yake tamkar na mahaukacin doki!!

Wandon ya mayar jikinsa, yana kyalkyala dariyar hauka kafin ya fizgo kafadarta! fuskarta ya rike a cikin tafin hannunsa, ta rufe idonta gam! bata son kallon mummunar fuskarsa.

"Ina fatan kin shirya zama tare dani! masoyiyata nayi miki alkawarin baki dukkan wani jin dadi na duniya! gwarzo ne ni akowane fanni! na tabbata cewa ba za kiyi nadama da kasancewarki a tare dani ba."

Zuciyarta ta dinga tashi sakamakon warin bakinsa, fuskarta ta fizge! da karfi ta matsa can gefe tana numfarfashi! yawu ya cika mata baki! yana zuwa gurin da take ta fesa masa yawun a fuskarsa!

Ya sanya hannu ya shafo yawun yana lashewa! amma kuma fuskarsa ta rikide da alama yaji haushin abinda tayi masa.

Sai da ya lashe yawun tsaf! sannan ya kalleta, ta tsorata da yanayinsa, sai ta sunkuyar da kanta, a kausashe! yace." Wannan shine na farko kuma shine na karshe kada ki sake maimatawa idan ba hakaba zan ladabtar dake.

Ta cire tsorosa da fadin." Wawa!! kafara ladaftar da kanka kafin ka ladaftar da wani."

"Wawa!! kalmar tayi mai ciwo! sosai a ransa sai kawai ya dingi maimaita kalmar a fili yana zagayeta, ta dinga binsa da kallo duk inda yayi, ya shammaceta yasa mata kafarsa ta fadi a kasan a gurin! turmusheta yayi ya danneta iyakacin karfinsa! bakinta yake kokarin sumbata tana kautar da kai yana bin duk inda ta nufa, be fasa maimaimata maganar ba! suka dunga bugawa! domin duk yanda yaso hada baki da ita ya gagara! ta gumtse bakinta gam!!! sai ya zama kamar mahaukaci sai rawar jiki yake babban burinsa yaji yana shan bakinta.................Ba zato! ba tsammani! yaji saukar kibiya a gadon bayansa!!

Ya gantsare! tare da zabga ihu!! a zabure! ya mike tsaye! ya fizge! kibiyar ya jefar jini ya fara tsiyaya! tashin hankali kenan! waige-waige yake a gurin yana mamakin yanda akayi hakan ta faru.

Cikin zafin nama! ya mikar da ita tsaye sai numfarfashin wahala take, ya rike hannunta katamau! yana sake dudduba gurin!..................!

Wani abu dake daure a hannunsa ya murza!

Please Login or Register in order to submit comment