Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinta duk a sanyaye yanzu babbar damuwarta kada asiri ya tonu sunanta ya fito shine abinda yafi tsaya mata a rai....



*Hello my fans A hanzarta biyan kudi domin yanzu zamu shiga cikin labarin akwai kuraa!! 😄 kada ki sake ayi bbu ke 'yar uwata kada ganin k'yashi ya hanaki biya ki zauna jiran na sata wallahi tallahi! hakkin wani masifa ne!! mai girman gaske!! yi kokarin gudun haram! komai kankantarta!!!*


*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin mov ko airtal
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE

*29&30*
Kusan a tare suka d'auke idonsu daga barin kallonta, Asp din yayi magana amma shi uffan bece ba har ta gama harare-harare! ta fita daga ofis din. Ya d'an ja k'aramin tsaki da fadin." Yarinya nan babu tarbiya a tattare da ita duk kuwa da cewa ta fito daga tsatso mai kyau, ba ta gaji dattako da karamci irin na mahaifinta ba, duk da ba a garin kano muke zaune ba muna da labarin dattakon mahaifinta mutum ne mai karamci da mutunci yana aiki da hankali da ilimi yana kuma gudanar da mulki a bisa tsari na isalama."

Beso ya tanka a cikin al'amarin yarinyar ba amma ganin yanda Asp din yake jaddada maganar yasa yace." Akwai irinsu da yawa wa'inda suka dauki mulki wata tsiya idan akace mahaifinsu nada sarauta ko wani muk'ami sai su dauki girman kai su dora a kansu suna ganin babu wanda ya isa dasu, hakane maganarka mutumin kwarai yana iya haifar baragurbi acikin al'umma jarabtace kawai daga Allah.'' Yace." Kwarai kuwa wannan haka yake sai dai kawai mu roki Allah ya shirya mana zuria baki d'aya." Ya amsa da ameeen ya Allah.

Shuru na minti biyu ya ratsa gurin, cikin 'yar tsokana Asp din yace." Akwai abinda na manta ban tambayi *MAI DAWA!* ba."?
Murmushi yayi da fadin." Akwai sauran tambayoyi kenan."? Girgiza kai yayi da fadin." Tambaya daya ce shin kana da iyali kuwa.''?

Girgiza kai yayi gami da dan ta'be bakinsa.........Asp ya dan zare ido da fadin." Kana nufin babu iyali kenan."
Kai ya daga masa still da murmushi a fuskarsa.

Sai kawai ya shiga girgiza kansa da fadin." Gaskiyar magana yanda kake jarumin namiji mata hudu suka cancanta da kai amma ace ma ko daya babu." cike da alhini ya kare maganar.

Sai abun ya bashi dariya ya dan dara kafin yace." Asp matsalar mata nada yawa shiyasa nayi zamana a haka ba wai don bani da bukata ba, kawai nafi bukatar kwanciyar hankalina nayi duk abinda nake so ba tare da wani ya caza min kai ba.''

Yace." To ai hakan nan ake hakuri dasu da matsalarsu Umaru kowane maigida yana da matsalar iyali mussaman idan mace fiye da d'aya yake da ita, dole ba zaka rasa shi da matsala ba, nima matana biyu sai dai kowacce da gidanta kuma yanzu haka ina shirin yin ta uku da yardar Allah sai na cike domin ina da ra'ayin hakan."

Ya girgiza kai da fadin." Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci a tsakaninsu."

Ya amsa da "Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani."

Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata a gidanka za'a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra'ayinsa zai iya 'kare rayuwarsa da mace daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar'ba hannu biyu tare da godiya a gareshi.


****
Ke'bantacen guri aka ajiyeshi shi kad'ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa.


***
Uwale duk atamfofin da take k'uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al'kur'ani akan bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar'bu.


Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra'u da ita Hamra'un suka yanke shawarar zuwa headquarter 'yan sandan domin samun cikkenan bayani.

Sun jima a tsaye kafin wani jami'i ya sauraresu, Malam Hafi'i mahaifin Hamra'u shine yayi masa bayanin abinda yake tafe dasu.

Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin......Uwale da sauri taje tari gabansa kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin ma'aikatan dake gurin suka fara tambayar ba'asi.

Cikin kuka tace." Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo gurin nan babu wanda yayi mana kallon mutunci Allah da Annabi sunfi karfin wasa amma gabadayanku bakwa tsoron Allah."!

Daya daga cikin musulman dake tsaye gurin ne yace." Tayi masa bayani abinda yake tafe da ita.

Hanci ta fyace kafin." Tace "Mun zo gurin UMARU wanda ku ka d'aure kuna zarginsa da ta'addanci bayan ba haka gaskiya take ba."

Yace." Yi shuru ki kwantar da hankalinki ki daina kuka zanyi miki kokari yanzu." Ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta, tace."Nagode sosai Allah yayi maka albarka." Ya amsa da 'ameen kafin ya umarcesu da suje su zauna a wata rumfa.

Sai da yaga zamansu sannan ya bar gurin, kai tsaye ofis din Asp ya nufa domin sheda masa abinda ke faruwa.
Ya k'ame da sarawa kafin ya sheda masa abinda ke da akwai, kai tsaye ya bashi umarnin shigowa dasu.

Da kanshi ya nuna musu gurin zama yana musu sannu, Malam Shafi'i da 'yarsa suka zauna kamar yanda ya umarcesu Uwale kuwa kai tsaye kujerarsa ta nufa, ya dinga kallonta har ta iso inda yake ta zube gabansa kawai sai ta fashe da kuka tare da rirrike masa kafafu! kuka take sosai tana bashi hakuri.

Tausayi ya rufeshi da kyar ya iya mik'ewa tsaye sakamakon rikon da tayi masa, ya sunkuya tare da sanya hannu ya dago ta ta mike tsaye, rungumeta yayi yana rarrashin gami da bata hakuri.

Ita kuma fadi take." Ku za'a bawa hakuri ku dubi girman Allah kuyi adalci kada ku yanke hukunci akan wanda bashi laifi bashi ne wanda kuke zargi ba.

Hankici ya ciro daga jikinshi, ya goge mata hawaye yana sake kwantar mata da hankali, sai da ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya umarcesu da cewa subi bayan shi.


Kai tsaye ke'bantaccan gurin da aka ajiye shi suka nufa...........Aps din a gaba suna bayansa, yana shiga sai ya basu hanya. gabadaya suka hada ido dashi yana zaune kasan kafet da tire din abinci a gabansa tsaf dashi da nutuswa a tare dashi bashi da wata matsala bayan sararin! dake daure da kafafunsa

Hamra'u da gudu ta iske inda yake, kawai sai ta fad'a kansa tana wani irin kuka! wanda yake nuna tsantsar tashin hankalinta, itama Uwalen da kuka ta karasa gurin duk da ganin da sukayi masa cikin nutsuwa hakan be gamsar dasu ba.

Asp ya juya ya fita yana jimamin al'amarin.

Tun bayan data fad'i jikinsa yasa hannu a bayanta yana dan bubbugawa, a Hankali cikin taushin murya yake rarrashinta, ta dago kai tana kallonsa hawaye sai ambaliya yake a saman fuskarta, kai yake girgizawa alamun ta daina kukan, yasa hannu ya goge mata fuskar sosai yake mamakin irin k'aunar da yarinyar take masa, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sai dai har yanzu bata saki hannunsa ba ta rike tsam a hannunta.


Ya d'ora idonshi kan Uwale da ta dage tana kuka sai kace wacce aka nuna mata gawarsa.

Murmushi yayi tare da mika hannunshi kan fuskarta hawayen ya share mata da fad'in." Kukan bashi da Fa'idah Uwale addua zaki min."

Tace."UMARU kukan shi yake kansa yin kuma shine samun salama, amma a zahirin gaskiya muna cikin tashin hankali bamu da kowa sai Allah shine kuma zai fitar damu."

Yace."Kin gama magana tunda ki kace Allah, kuma gaskiya tayi halinta tun kafin tafiya tai nisa gaskiya ta bayyana cewa wanda suke zargi bani bane nima kuma na san da hakan saboda haka ku kwantar da hankalinku insha Allah zan fito lafiya na cigaba da rayuwa da ikon Allah."

Tace."Idan hakane mai yasa basu kwance maka wannan d'aurin ba, duba fa yanda kafafunka suke daure.

Yace."Akwai dalilin da ya sanya hakan wannan ba matsala bace kada hakan ya daga muku hankali."

Kusan a tare suka sauke zuciya da jin furucinsa suka shiga godewa Allah da abinda yayi musu.

Har yamma suna tare ya saki jikinsa sosai yana basu labarin irin gwagwarmar suka sha a dajin! tace."Kaga Umaru shiyasa kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan harkar ba mahaifinka har ya mutu da abun a cikin ransa saboda haka idan Allah yasa ka kubta to dole ka ajiye wannan sana'ar ka nemi wata domin hakan shine samun nutsuwarmu baki daya.

Domin ya kwantar mata da hankali sai ya amsa mata akan abinda take so, taji dadin hakan kuwa tay tai masa addua da fatan samun nasara akan dukkan abinda ya sanya a gaba.


*****
Ta jima a toilet din tana durje jikinta da sabulai iri-iri kafin ta dauro towel ta fito. idonta ya sauka kan tufafi wanda aka ajiye mata su kan gado komai sabo underwears sai riga da siket na wani material mai taushi, goge jikinta tayi kafin ta zauna gaban mudubi tana kokarin duba man da zata shafa a jikinta, tsaki taja tana hararar tarin kayan kwalliyan dake dressing mirror din duk ciki babu kalar man da yayi mata ballantana ta shafa a jikinta........wani lotoin ta dauka tana jujjuyashi a hannunta sai ya mutse fuska.

Ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta kallo guda kayi mata zaka fahimci cewa tana daga cikin jerin mutane masu sauki kai da daukar rayuwa a sannu, tana da fara'a sosai domin da wuya kaga bacin ranta sai in tura ta kai bango.

Fuskarta yalwace da fara'a ta 'karasa shiga dakin da fadin." Yawwa kin fito ko ga kaya nan na ajiye miki na san za suyi miki dadin sawa.''

Shuru tayi bata tanka ba. Ta kalleta da fadin." Ko dai na sauya miki wasu wannan ba suyi miki ba."?

Tsaki taja da fadin." Don Allah kin cikani da surutu haka na duba na gani okey nagode."

Ranta ya 'baci da abinda tayi mata amma sai ta danne ko alama bata nuna a fuska ba tace." Okey to shikkenan idan kin shirya sai ki fito muci abinci ."

Ta'be bakinta tayi ba tace komai ba ta cigaba da jujjuya abinda ke hannunta.

Juyawa tayi da niyyar fita daga dakin. sai ta dakatar da ita, ta tsaya tana sauraranta.

A yatsine tace." Wannan tarkacen mayukan shafawar taki ba zan iya shafawa ko daya a jikina ba domin ni ba irinsu nake shafawa ba.

Cike da mamaki take kallonta tana mamakin furucinta, tarkace!!! duk man da take shafawa babu na kasa da dubu biyar sai sama amma shine har take magana cewa ita tafi karfin ta shafa a jikinta.

Jinjina al'amarin tayi kafin tayi 'yar dariya da fadin." Lallai 'kawata kina ji da gayu amma idan ba haka ba meye laifin mayuka na ko wannan na hannunki kika shafa ya isheki." Cike da wasa ta karashe maganar..........Sai ta fusata! ta mike tsaye tare da buga mata tsawa! da fadin." Ke kin san wacece ni kuwa? da har kike min wannan banzar maganar."? Ta'be bakinta tayi tace." Ina zan sani hajiya ni dai Daddy ya kira ni a waya ya sheda min cewa zanyi b'akuwa shiyasa nake karramaki bahaushe yace." bakon ka Annabin ka."

Dogon tsaki! taja kafin ta koma ta zauna..........Ita kuma da sauri ta bude kofar dakin ta fita tana mamakin al'amarin.


Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ta kalleta da fadin.'' Ya akayi ne? bata gama shiryawa bane."?

Baki ta dan ta'be kafin tayi 'yar dariya da fadin." Na isketa ta fito daga wanka tana nazari man da zata shafa."

Cike da mamaki tace." Kamar yaya nazari duk cikin mayukan shafawar taki babu wanda yayi mata."?

Tace."Hakan take nufi."

Tana kokarin magana motsin fitowarta ya katseta duk sai suka juya suna kallonta tayi kyau sosai a cikin material din sai dai siket din ya matseta dalili tana da kwankwaso mai fadi da cika sakamakon mai kayan da nata bai kai hakan ba.

Da murmushi a fuskar matar gidan tace." Kin fito."? "Umm." tace kawai ta nemi kujera ta zauna sai wani basarwa take.

Ta kalleta da fadin." Nabila mai yasa ki ka bata wannan kayan kamar sun matseta ki tashi ki dauko mata wasu."

Tace."Mommy kin san duk kayana riga da siket ne kuma bai zama dole suyi mata yanda takeso ba tunda ta fini kiba."

Ta kalleta da fadin." Zinatu baki takura ba dai ko."?

Girgiza kai tayi da fadin." Kada ki damu hakan yayi min daidai domin yawancin kayana haka suke." Tace." To masha Allah ku tashi muje muci abinci." kusan a tare suka mike kai tsaye gurin cin abincin suka nufa.



To duk wasu bayanai da ya kamata ace gwamnati ta san dasu Asp ya harhad'a komai ya turawa maigirma governor domin ya saurara dashi da wa'inda da ke da alhakin hakan, sai dai ya sheda masa cewa ranar asabar shi da wanda ake zargi da aikata ta'addancin zasu shiga sansanin domin binkice akan sassan sannun da zai tabbatar da gaskiyar magana. maigirma governor yayi na'am da maganar ya kuma bada goyon baya akan tafiyar.


*'Yan jarida mane ma labarai suka samu abun yayatawa a gari! gidajen redio da television gami da jaridu labarin abinda suke nunawa kenan cewa ashe wanda ake zargi da *UBAN DABA!* *bashi da ala'ka da zargin da ake masa asali ma shine mutum na farko wanda ya fara karya alkadarin d'an ta'addan da ya addabi kasa da al'ummar dake cikinta, domin tabbatar da gaskiyar magana kakakin rundunar 'yan sanda wato Asp Musa Baharu zai jagoranci shi wanda ake zargi domin gudanar da binkicen sassan hannun wanda ake nema ruwa a jallo...........Sannan kakakin rundunar 'yan sandan ya shedawa mane ma labarai cewa yanzu haka akwai d'iyar Sarkin Kano mai suna Zinatu wanda ake zargin cewa wasu 'bata gari sunyi kidnapping d'inta domin samun kudi daga gurin mahaifinta, amma ha'kan su bai cimma ruwa ba sakamakon zuwan shi wanda ake zargi da ta'addanci mai suna UMARU wanda jama'a suka fi sanin sa da GOJE!* *shine wanda ya zama garkuwa a gareta har yayi nasarar tallafar rayuwarta bayan ya samu nasara akan wa'inda sukayi garkuwa da ita............Wannan shine cikakken rahoton da ya cika garin Katsina dama kewayanta.*


Duk wanda ya danganci masarautar yana cikin farin ciki sakamakon samun cikkaken labarin bayyanuwar ta............Fada ta cika da jama'a masu zuwa taya murna da fatan alkairi maimarta da 'yan uwansa fuskokinsu tamkar gonar auduga saboda tsantsar farin cikin da suke ciki a ranar yini cir masarautar babu masaka tsinke mata da maza wannan ya fita wannan ya shiga.

Gimbiya Aysha da 'yar uwata tare da 'ya'yansu su ka kasance cikin farin ciki mara misaltuwa, Maijidda ma tayi nata murnar daidai gwargwado amma ta ciki na ciki domin kasa zama tayi cikin 'yan uwanta ta nufi b'angaranta jikinta duk a sanyaye yanzu babbar damuwarta kada asiri ya tonu sunanta ya fito shine abinda yafi tsaya mata a rai....



*Hello my fans A hanzarta biyan kudi domin yanzu zamu shiga cikin labarin akwai kuraa!! 😄 kada ki sake ayi bbu ke 'yar uwata kada ganin k'yashi ya hanaki biya ki zauna jiran na sata wallahi tallahi! hakkin wani masifa ne!! mai girman gaske!! yi kokarin gudun haram! komai kankantarta!!!*


*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin mov ko airtal
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!🏹*
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATION📚🖊️*
____________________


FREE PEGE
*31&32*
Jiki a mace! ta nemi kujera ta zauna tana laluben number k'aninta wanda suka shirya 'kula k'ulalliyar dashi. Yana d'aga wayar tayi kasa da muryata da fadin." Sadiq na san dai yanzu ka samu labarin abinda ke faruwa yarinyar nan fa ta bayyana ina tsoron kada asirinmu ya tonu.''

Yace."Aunty Maijidda kada ki damu babu yanda za'ayi asirinmu ya tonu tunda yarinyar ba zata iya sheda fuskokinmu ba, don haka ki saki jikinki kiyi mu'amula da kowa lafiya kada kiyi abinda zai sanya a gane cewa muna da hannu acikin al'amari!

Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi! kafin tace."Sadiq wallahi har yanzu na kasa samun nutsuwa gabadaya hankalina a tashe yake shiyasa na kasa zama a cikin jama'a na dawo gurina." Yace." hakan kuma da ki kayi shine zai janyo cewa a gane muna da hannu a cikin al'amarin ki saki jikinki kada ki kuskura ki tona masa asiri."

Ta sassauta murya da fadin." Insha Allah zanyi kokarin ganin na boye fargabata." Yace."Yawwa hakan shine abinda ya dace dake. amma har yanzu akwai kurah fa."!

Tace."Menene kuma."? 'Yar dariya yayi da fadin." Kudin da ki ka bayar domin gudanar da aikin nayi wata bukata dasu, yanzu zaki bada wasu a biya masu hakki."

Tace."Yanzu Sadiq ina ka kai miliyan daya da rabi? cikin kwanaki bakwai kacal! fisabilillahi ba'a samu biyan bukata ba kuma sai ace sai na bada wasu kudin."

Ya 'bata da rai da fadin." Kinga Aunty Maijidda duk wannan tambayoyin basu cancanta ba domin wannan aikin yafi karfin miliyan biyar amma don kin bada miliyan daya da rabi kike surutu haba kada ki bani kunya mana kawai ni ki tura min kudin ko kuma anjima kadan nayi miki dirar mikiya."

Da sauri tace." Aa ba sai kazo ba bari zuwa anjima ko gobe da safe zan tura mak.....Katseta yayi da fadin." No! ni ban zarda a wayi gari ba, a yanzu mutanan suke bukatar kudinsu idan kuma kinfi so asiri ya tonu to."

Da sauri ta girgiza kai da fadin." Aah! bana bukatar hakan ka saurari alert yanzu." Cike da farin ciki ya kashe wayar yana tsallan murna ya fad'i saman katifarsa yana kyalkyala dariyar biyan bukata, tunda ya fuskanci ta tsorata da al'amarin, cikin sauki ya samu hanyar samun kudi da ita.

***
Jaridar Leader shirp ce a hannunsa yana dubawa, hausawa sukace labarin zuciya a tambayi fuska, annuri ne kadai yake fita a kyakykywar fuskarsa, hakan kuma shi yake nuna tsantsar farin cikin dake cikin zuciyarsa.......Shigowarta gurin yasa ya d'aga kansa yana kallonta bai janye ba har sai da ta isa inda yake zaune, ta zauna kusa dashi itama tata fuskar a sake, take gaisheshi, amsawa yayi tare da tsareta da wani irin kallo wanda ke nuna mata zahirin so da tsantsar kauna.

'Yar dariya tayi tare da lumshe ido, personality ta kirashi da suna na mussaman wanda take kiransa dashi tunfil-azal.

Da murmushi a fuskarsa yace." Aysha Kinga Yaron da zaki kira da *JARUMI! NAN."* ya fad'a yana nuna mata hotonsa dake jikin jaridar.

Ta tsirawa hoton ido tana girgiza kanta, ingarman namiji maji k'arfi kyakykwa tamkar *SADAUKINTA* murmushi tayi Ta kalleshi da fadin." Lallai ni Ayshatu na sheda cewa babu *RAGO!* ga duk wanda ya amsa wannan sunan, ha'kika wannan yaron ya cancanta ayi masa komai saboda jarumtarsa! da kuma sadaukarwarsa."

Kansa ya girgiza da fadin." Sosai kuwa Aysha na jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi wa yaron, Munyi waya da Asp Musa Baharu mun tattauna muhimman maganganu dashi na fahimta, ya kuma bani tabbas a kansa cewa ZINATU ta samu dukkanin kulawar da ta dace a gurinsa, ya tabbatar min da cewa yarinyar tana cikin koshin lafiya babu wani mugun rauni! a jikinta bayan wanda ta samu kafin zuwan shi wannan yaron da ya taimaka mata, sannan bayan haka kuma ya sheda min cewa daga zarar sun gama gudanar da binkicen daya dace to dashi kansa da yaron zasu kawo min ZINATU har gida, sosai yaron ya taka muhimmiyar rawa akanta babban abinda yafi burge ni dashi yanda yayi namijin kokarin ganin ya karya alkadarin takadirin d'an ta'addan nan! da ya addabi! 'kasa da al'ummar dake cikinta, Aysha wannan yaron jarumtarsa! har ta zarce tawa."

Murmushi tayi idonta cikin nashi tace."Ina shakku! akan maganarka ranka ya dade, domin kuwa ban yarda cewa akwai wanda yafi mijina jarumta ba, har yanzu kana nan yanda kake Jarumi! a gida kuma jajurtacce a waje."!

Hannuwanta ya rike yana jifanta da wani irin kallo.........Har yanzu Tana nan mak'ale a zuciyarsa, sam bata tsufa a idonsa, duk kwanan duniya sonta nunkuwa yake a zuciyarsa, Aysha ta zame masa jinin jiki.......... Ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta fahimci abinda yake da akwai, murmushi kawai tayi, tana mamakinsa, baya tsufa da soyayya, kullum da irin kalar soyayyar da yake nuna mata idan suka kad'aice, babu wani abu da ya samu tangard'a a zamantakewar auransu.

kusan a tare suka mike tsaye, 'kugunta ya ratsa da hannunshi, ya riketa sosai a jikinsa, kai tsaye bedroom suka nufa domin mutunta junansu.



*****
To Ranar da zasu cigaba da gudanar da binkice a sansanin *UBAN DABA!* Asp ya bada umarnin kwance masa sasarin! dake daure da k'afafunsa! 'yan jarida mane ma labarai suka cika harabar gurin, koda ganin fitowarsu sai sukayi caaa! a kansu sunayi musu tambayoyi.

Asp a takaice yayi musu bayani, shi kam be iya ce musu komai ba, mota kawai ya shiga ya zauna jami'ai biyu suka sanya shi a tsakiya, Asp shima yayi saurin shiga mota domin ya san idan ya biye musu to su ba zasu gaji dayi masa tambayoyi ba.


Tsit!! dajin babu alamun akwai wani dan adam dake rayuwa a gurin, kukan tsintsaye yafi yawa sai dai jefi-jefi suna jin kukan dabbobin dake can nesa!............binkice! suke sosai a gurin, sai dai kuma dukkaninsu a shirye suke domin Babu wanda ya saki jikinsa a cikinsu motsi kad'an zasu zabura! su juya gami da saita bindiga.

Gurin da yake tsammanin faruwar badakalar! tasu ya nufa, ya jima yana duba gurin kafin yayi tunanin cire wu'kar dake rataye a jikinshi ya fara tona 'kasar gurin da tsinin wuk'ar.

Cak! ya cire wu'kar ya ajiye a gefe ya tsuguna, hannu yasa yana tutture 'kasar data turbud'e abinda yake hasashen samunsa a gurin, lokacin da ya fito da sassan hannun yayi dai-dai da isowar Asp gurin!

Ya tsuguna kusa dashi gabad'aya idanuwansa ya zuba kan dungulmin hannun! yana jimanta al'amarin! babu shakka! wannan shine hannun mutumin da ya sanya aka zana masa hotonsa shekaru biyar da suka wuce! abinda ya sanya ya gazgata hakan, zabban zinare da azurfan dake jikin wannan zane sune jere a jikin yatsun dake gabanshi a halin yanzu.

Ya kalleshi da fadin." Yanzu na 'kara gazgata maganar ka, binkice ya k'are a kanka tunda ga sheda nan a hannunka wannan kad'ai ya isa a jinjina maka."!!!

Bece komai ba, ya ajiye sassan hannun daya riga yayi wani irin kumburi! kwanaki biyu kacal!

gefe ya matsa yana ya mutse fuskarsa, hannun har ya fara fitar da wari!

Asp ya tattara ma'aikatan gabad'aya ya nuna musu sheda! gabad'ayansu mamaki ya rufesu, dukkaninsu zuwa sukeyi har inda da yake tsaye suna 'kamewa da sarawa!! alamun jinijina!!

Asp abin ya burge shi, shima hularsa ya cire ya 'kame tare da sara masa! al'amarin ya bashi mamaki mutuka! Asp din yace." Wannan ba abun mamaki bane Cancanta ce ta janyo hakan.

A takaice dai basu bar dajin ba sai da suka tabbatar da cewa babu wani mahaluki da yake rayuwa a gurin, iya binkicensu

Please Login or Register in order to submit comment