Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taje ta rungumeshi tana shashshaka! shi kam fuskarta ya dago yana goge mata hawaye tare da rarrashinta, Aunty Maijidda ce ta jan hannunta suka nufi sashenta tare, hakan beyi wa Safah d'adi ba, ganin yanda yarinyar tayi kamar bata gansu a gurin ba, koda yake daman dole hakan ya faru tunda ita din ta kasance mai yi mata fada gami da nuna mata kuskuranta.

Bata iya barin gurin ba sai da ta tabbatar da cewa an sauki bakin a guri mai kyau da kuma dukkan abun bukata.

Gimbiya Aysha kuwa kunya da kawaici ya hana ta fitowa tarar su, amma tana zaune labarin abinda yarinyar tayi ya isa kunanta daga bakin 'yan uwanta Hassana da Husaina wanda su d'in ma ta nuna tamkar ba jininta koda yake inda sabo sun saba da halinta amma dai abunda tayi musu a yanzu ya 'bata musu rai mutu'ka!


Sosai suka samu kulawa mai kyau kafin maimartaba ya bukaci zama dasu sai da sukaci abinci suka gabatar da sallar la'asar tukkuna sannan suka sameshi a fada shi kad'ai domin akwai maganar da yake so suyi a tsakaninsu.

Gaisuwa suka sake mikawa a gareshi kafin shi da kansa ya mika godiya a garesu akan alkairin da sukayi masa.

Asp yace."Ranka ya dade ai babu godiya a tsakaninmu da kai, domin kai uba ne a gurin mu, ka cancanta da abunda yafi haka, bayan hakan kuma kulawar da mukayi akan yarinyar nan hakkinmu ne tunda aikin mu ne kare rayukan al'umma."

Ya girgiza kanshi da fadin." Tabbas maganarka haka take Asp amma dole nayi godiya domin samun irinku masu tsoron Allah da kishin 'kasa zaiyi mutukar wahala wannan dalilin yasa na jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi muku."

Kafin Asp din yayi magana ya riga shi da fadin." Ranka ya dade kada ka damu kanka akan wannan al'amari wallahi ni abunda nayi akan yarinyar nan don Allah nayi bana bukatar komai a gurinka face addua."

Murmushi yayi yana sake jin kaunar yaron a cikin zuciyarsa, yace." UMARU kenan addua kam zan cigaba dayi muku har karshen numfashina amma ba kaji bahaushe yana cewa (yaba kyauta tukwici ba) ba don kada nace na baka auran yarinyar nan ka dawo min da kyautata ba to dana baka ita sakamakon alkairin da kayi min."

Fadar tayi shuru sakamakon maganar.

Kasa d'ago kansa yayi ballanatana ya nuna rashin amincewarsa da kyautar da akayi masa..............Jin beyi magana ba yasa yace." UMARU kodai baka kar'bi wannan kyautar tawa bane."? Asp da sauri yace." Aa haba dai! ranka ya dad'e wane mutum! kyautar mutum ba karamin al'amari bane sosai ni naji dadin wannan al'amari kuma kayi kyautar akan ga'ba domin dama bashi da aure a halin yanzu mungode sosai da wannan karamcin."

Fuskarsa cike da annuri yace." Asp ka ari bakinsa kaci masa albasa amma yanayinsa ya nuna kamar beyi na'am da wannan kyautatar tawa ba."

Yayi namijin 'ko'karin kawar da damuwarsa kansa ya dago tare da kokarin aro walwala da farin ciki yace." Ranka ya dade farin ciki ne ya hana ni iya magana, tabbas abunda abokina ya fada hakane kayi min kyauta akan ga'ba kuma na kar'ba hannu biyu nagode kwarai da wannan karamcin."

Ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Alhamdullihi Allah abin godiya, lallai babu shakka ZINATU tayi dace da miji irin wanda yake da wahalar samu ina rokon Allah ya tabbatar da alkairin dake cikin wannan al'amarin." Gabad'aya suka amsa da "ameen ya Allah."



*Free pege zai 'kare a pege 40 masu payment kawai nake da bukata idan kin san na siyan littafin nan za kiyi ba kada kiyi min magana🙏🏻*




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!!🏹*
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATION📚🖊️*
____________________


*1-NANA KHADIJA*
*2-YARO DA KUDI*
*3-GIMBIYA BALARABA*
*4-BABBAN YARO*
*5- MASHAHURI*
*6- LADIDI KWADAGA*
*7-TSANTSAR BUTULCI*
*8-SADAUKI OMAR*
*9-NIDA YAYA SADAM*
*10- 'YAR BANGAR SIYASA*
*11-DA WATA A KASA*
*12- MADADI*
*13-KWARA TABI KWARYA*
*14-GA RINTA NAN*
*15- MATSALARMU A YAU!*
*16-RUWAN DARE*
*17-GOJE!!*

_Littatafai na kenan ga duk mai bukatar karanta daya daga ciki zai samu damar karantawa cikin saukin farashi, wanda zai iya siya nake da bukata, don Allah idan ba siya za kiyi ba kada ki dauki number ta kiyi min magana NAGODE sosai masoya💞🙏🏻_



*SHAFIN NA YAU NAKU NE 'YA'YAN ALBARKA.*

_DAUGHTER💞_
*ZEEY KUMURYA*
_MARUBUCIYAR_
*(NEHAL)*💫
*DA*
_MAMAN TEDDY💞_
*MARUBUCITAR*
_LITTAFIN_
*WALI-JAM🐄* *BAFULATAN RUGA*
_DA SAURANSU_

Allah ya kara muku basira da haza'ka, NAGODE 'kwarai! Allah yayi muku albarka.🙏🏻
________




LAST FREE PEGE
*39&40*
A takaice dai basu bar masarautar ba sai da duk suka gaisa da duk wanda ya kamata, sun tafi da mamakin mutumci da dattakon mutanan, hakika kaf famliy din yarinyar nagartattun mutane ne masu hankali da sanin ya kamata, ita kadai ce ta fita zakka a cikinsu, koda yake dama haka Allah yake ikonsa, amma duk da hakan itama ba za'a rasa wani abu mai kyau daga cikin dabi'unta ba.

Maimartaba ya basu kyautar dawakai lafiyyayu gami da kayan sarauta kwatankwacin irin wanda yake amfani dasu, mussaman yasa aka kawo masa kayan farauta daban-daban domin ya gwangwajeshi, aikuwa duk cikin kyautukan da yayi musu yafi farin ciki da kayan farautar domin dama yana da bukatarsu, a ganinsa koda zai cika d'aki guda da irinsu ba matsala bace a gurinsa.

Wannan karon gabad'aya a kujerar baya suka zauna, sai da sukayi nisa da tafiya sannan Asp ya fara maganar da tuntuni take cin zuciyarsa.

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi da fadin." Asp kwata-kwata fa ni wannan al'amari be kwanta min a rai ba, kawai dai na amsa masa ne amma bana jin zan kar'bi auran yarinyar nan."

Asp ya 'bata fuska da fadin." Kada ka zama k'aramin mutum mana, ko dai har ka manta da wanda kayi magana, ba fa gurin wasan yara mukeje ba, ya za'ayi ka amsa masa cewa ka kar'bi kyautarsa daga baya kuma ka shigo da wata magana''

Kallonsa yayi babu farin ciki a fuskarsa yace." Kunyarsa ce ta sanya na amince na kar'bi kyautarsa amma kai kanka kasan tafiyarmu ba zata zo d'aya da yarinyar nan ba, naji takaici a lokaci da yayi maganar har kake cewa dashi bani da aure alhalin jiyan nan, na nuna maka yarinyar da zan aura a lokacin daka shigo gidana, tabbas ka shigo masa da maganarta ina ganin ba zai k'arfafa maganarsa ba."

Yace."UMARU mace hudu Allah ya halasta maka mutu'kar za kayi adalci a tsakaninsu, wannan dalilin yasa lokacin daya fadi maganar na k'arfafa masa gwiwa, haba mutumina ai da kunya a gabansa ka nuna k'yamarka akan jininsa, kayi hakuri da katsalandan din da nayi maka domin ni kaina nasan da cewa yarinyar akwai matsala a tattare da ita, bata da tarbiya ko kadan, to amma hakan ba zai hana a aureta ba tunda wannan matsalar kawai gareta ina ganin idan ta hadu da jajurtacce namiji kamarka to cikin sauki rayuwarta zata sauya.

Ya jima yana nazarin maganganun Asp din kafin yace." Kasan Allah a tsarina bani da ra'ayi tara mata amma ina ganin hakan ba zai samu ba, Asp ina jin tsoron auran yarinyar nan ta hana ni kwanciyar hankali, wannan dalilin yasa gabadaya al'amarin be kwanta min a raina ba.


Ya dan doki kafadarsa da fadin." Haba mutumina kai da saba gwagwarmaya da maza mai zai sanya lamarin mata ya dinga baka tsoro! wallahi babu wani abun fargaba da tsoro a cikin al'amarinsu daga zarar ka gane hallayarsu shikkenan zaka zauna dasu lafiya saboda ka cire shakku akan hakan mutumina ba tun yau ba nasha fada maka cewa mace hud'u ce ta dace da kai haba *jan wuya* kada ka bani kunya mana."

Dariya ya d'anyi ya bashi hannu suka tafa kafin ya girgiza kanshi da fadin." Asp ba zaka gane ba ne amma shikkenan kawai mu bar maganar Allah ya tabbatar da alkairi."

Yace." Yauwa abunda nakeso naji kace kenan abokina insha Allahu za kayi fari ciki da wannan al'amari.


To har bayan magariba ZINATU na tare da aunty Maijidda komai anan ta gabatar wanka cin abinci da sauransu, hankalinta da tunaninta gabadaya baya kan uwar da ta haifeta ba ballantana kuma wani, hakan yayiwa ita Maijiddan dadi dama babban burinta ta cusa bakin ciki a zuciyar Safah domin itace abokiyar gabarta tun sanda ta fahimci cewa gimbiya Ayshan tayi mata nisa, sai ta mayar bakin kishinta kan Safara'u wacce ita kuma ta mayar da ita shashasha domin duk abunda take na rashin hankali bata biye mata su taru su lalace gabadaya.

Ta dinga bugar cikinta tana bata labarin abubuwan da suka faru, da rayuwar ta a dajin gami da irin wahalhalun da tasha, da labarin zamanta a gidan Asp babu abunda ta rage, sai dai koda wasa bata fada mata irin namijin kokari da kulawar da yayi akanta ba, duk abinda zata a fad'a a kansa sharri ne, har da k'azafin fyad'e kamar yanda tayi masa a gurin Asp, gabad'aya suka had'u suna zaginsa, Aunty Maijiddan ita ke fadin." Zata shedawa maimartaba komai domin abi mata hakkinta, hakan yayi mata dadi a ranta domin ta san mahaifin nata yana saurarar maganar auntyn nata.

B'angaran Gimbiya Aysha kuwa ganin har bayan isha'i yarinyar bata shigo ba, sai ta kalli sauran yaran nata dake zaune a gabanta tace." Wannan zaman da kuke bashi da amfani domin dai kune kuka damu da yarinyar nan amma ita bata damu daku ba, da ta damu daku to da yanzu ta nemi inda kuke saboda haka ku tashi ku tafi gidajenku hakan shi yafi ku rabu da ita da mugun halinta, sannan kada wacce tayi yunkurin kiran wayarta ku 'kyaleta taje tayi rayuwa da wacce ta za'ba a madadi na da kuma ku."
Cikin rashin jin dadin abinda 'yar uwar tasu tayi kowacce ta tafi gidanta da bacin ran abun a cikin ranta.

Da yake aunty Maijiddan ce da girki a daran ta zauna tana shirya masa k'arya da gaskiya har da cewa ya dauki mataki mai tsauri a kan yaron domin yarinyar ta sheda mata cewa a yayin zamansu a dajin ya keta mata haddi."

Duk cikin maganganunta wannan ce kadai ta dauki hankalinsa, hankalinsa ya tashi da jin maganar saboda ya san hakan na iya faruwa idan shad'en ya ratsa, to amma wannan maganar ba zata sanya ya janye manufarsa ta alkairi ba, kamar hakan ma shine rufin asirinsu, duk da hakan zai tuntubi yaran domin tabbatar da gaskiyar magana.


Washe gari da safe kafin ya zauna a fada ya nufi b'angaran matayen nasa domin dubasu, gabadaya ya samesu ba yanda ya saba ganinsu ba, Safah dai tayi kokarin kawar da damuwarta har ya dan zauna sukayi hira, bangaran Gimbiya Aysha kam rigima suka tafka irin wacce sukayi shekara da shekaru ba suyi irinta ba.

Cikin tsananin 'bacin rai yace."Aysha yau ni kike nunawa da yatsa akan wani dalili naki na banza da wofi shin wai me Maijidda tayi miki kika dauki karan tsana kika dora mata, baki da kawaici akan 'ya'ya Aysha baki tausaya mata cewa ita bata dashi meye laifinta anan don ta nuna kauna akan zuriarki."

Ido jawur! tace." Bana bukatar ta a cikin al'amarina kuma ba tun yau ba na tabbatar da cewa kaine kake daure mata gindi take mana duk abunda takeso, shin itace ta haifar min 'yar da zata nuna min iko a kanta! na haifi 'yata ta lalata min ita duk hakan be isheta ba sai da ta san yanda tayi ta shiga tsakanina da ita da 'yan uwanta! bayan dawowarta har yanzu bata tako kafarta nan ba ballanatana taje gurin 'yar uwata, haka nan jiya 'yan uwanta suka gaji suka tafi gidan auransu bata shigo ba, shin kai a ganinka hakan shine dai-dai? duk abunda yarinyar nan take aikatawa da sanya hannun Matarka a ciki amma kullum sai ka dinga nuna cewa baka gane ba, to ni gaskiya na gaji da wannan al'amari zan kuma dauki mataki."!

Ganin yanda take numfarfashi! ya sanya shi sauke nasa fushin, hannunta ya rike ya jata suka zauna gefen gado a tare.

Cikin sigar rarrashi yace."Yi hakuri ki samu nutsuwa muyi magana da fahimta.'' ta kalleshi da fadin." Wane irin nutsuwa zan samu a cikin irin wannan yanayin."? hannun ya sake rikewa da fadin." Na yarda da gaskiyarki, Aysha amma kada b'acin rai ya sanya k'ima da mutuncinki ya zube kada fa ki manta kece babba a gidanan kowa yana ganin darajarki kada kuma kiyi wani abun da zai sanya mutuncin ki ya zube a idanun jama'ar dake cikin gidan nan, kibi komai a sannu a hankali."

A raunane tace." To wai yanzu ya kake so nayi? kana so na bari Matarka ta samu nasara a kaina kenan."

Ya girgiza kansa da fadin." Maijidda baza ta samu nasara a kanki ba Aysha kin zama murucin kan dutse a ko'ina kece a gaba."

Ta girgiza kai da fadin." Ban da gurinka domin yanzu Maijidda ce ke tsara maka komai kuma idan ta fadi magana dai-dai ne a gurina."

Murmushi yayi yana kallonta, ya san kawai ta fadi wannan maganar ne saboda kishi amma shi duk cikin matansa babu wacce ke tsara masa magana yayi amfani da ita gwanda ma ita takan bashi shawarwari yayi amfani dasu, amma don ya kwantar mata da hankali sai yace." Na amince da maganarki kuma zanyi wa tufkar hanci banji dad'in abunda suka aikata ba, kuma da kaina zan samesu na nuna musu kuskuransu."

Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Shikkenan tunda kace haka amma dai duk da haka ina so kayi min tsakani da matarka babu abunda ya shafeta dani da kuma zuria'ta."

Domin a zauna lafiya yace."Kada ki damu zanyi mata magana ta kiyaye shikkenan kowa ya zauna a matsayinsa." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin.'' Hakan shine abinda ya dace.

To atakaice dai bai samu damar zaman fada ba sai da ya tabbatar da cewa ya kashe wutar da take kokarin ruruwa, ya kuma yi namijin kokari gurin nunawa Maijidda kuskuranta duk irin hujjojin data kawo masa be saurareta ba, yace."Idan ita ZINATU tayi aikin kuruciya ke ya kamata ki nuna mata hanyar dai-dai, cewa taje gurin mahaifiyarta da 'yan uwanta da suka damu da rashinta, amma kema sai ki ka aikata aiki irin na k'ananun yara abunda ki kayi sam be dace ba."

Kuka ta shiga yi tana fadin." An nuna mata iyakarta akan abinda take ganin tana da iko dashi, kuma ba tayi hakan da wata manufa ba amma tunda sun juya al'amarin da wata siga daban shikkenan zata cire hannunta daga kan 'ya'yansu."

Maganganun da tayi besa yaji tausayinta ba domin idan da sabo ya riga ya saba da jin irinsu kawai dai shi ya nuna mata kuskuranta ne.

Da kanshi kuma ya shiga dakin ZINAT din tana bacci ya tasheta sosai ya rufeta da fad'a irin wannan be ta'ba yi mata irinsa ba, a take a lokacin ya bata umarnin kan cewa tayi maza taje ta nemi afuwa a gurin mahaifiyarta.

Tana share hawaye ta shirya, ya sanya ta a gaba sai da ya tabbatar da cewa ta shiga sashen sannan ya nufi fadarsa.


Da sallama a bakinta ta shiga, ta amsa tare da tsira mata ido har ta 'karaso inda take ta zube k'asan kafet kawai sai ta rushe da kuka tana takure jikinta.

Zuba mata ido kawai tayi tana mugun takaicin sangartar da take sai kace yarinya k'ankanuwa!

Tsawa! ta buga mata da fadin." Za kiyi min shuru ko kuwa shashashar banza shashashar wofi."!

Kokarin hana kanta kukan take amma hakan ya gagara yi take ita kanta takasa tantance me dalilin yin sa.

Tace." To tunda haka ki ka za'ba bani da magana dake ki tashi ki koma inda kika fito."?

Kasa tashi tayi sai dai tayi kokarin rage sautin kukan ya cigaba da fita kasa-kasa.


Taja tsaki da fadin." Kullum kina girma amma kina cin 'kasa! Zinatu ban san lokacin da za kiyi hankali ba, ya kamata ace wannan abunda ya faru dake ya zama izina a gareki amma sai gashi kamar kin 'karo wani iskancin a inda ki kaje, to don baki mutun tani ba sai me? Allah dai yasa bake kad'ai na haifa ba ballanatana bakin cikinki ya kasheni! ina da wasu bayan ke kuma zan iya yafewa Maijidda ke babu abunda ya dameni."

Cikin reshin kuka tace." Mammah don Allah kiyi hakuri wallahi duk abunda ya faru dani tsautsayi ne, kuma ina jin tsoron zuwa a gurinki kiyi min fada shiyasa na zauna gurin aunty Maijidda."

Tace."Don Ubanki tsautsayi ko son zuciya? na dauka ranar da al'amarin zai faru sai da kowa ya hanaki fita amma ki ka fakaici idanuwanmu ki kama hanya ki ka fita ai naso wa'inda suka sace ki sun kasheki kowa ya huta."

Ta dago kai tana kallon mahaifiyarta da mamakin jin furucinta.

Tace."Eh ki kalleni da kyau! ni nayi wannan furucin saboda duk wani wanda zai zama annoba a cikin al'ummah to bashi da wani amfani a duniya rashinsa shi yafi alkairi."

Yanzu take kukan gaske hawaye masu tsananin zafi suka shiga sharara a saman fuskarta! tunda take da mahaifiyarta bata ta'ba ganin bacin rainta ba irin na yau ba, har tana mummunan fata a kanta da rayuwarta gabadaya duk sai jikinta yayi sanyi.

Numfashi ta sauke kafin ta cigaba da cewa." Shekarunki ashirin da hudu a duniya ya kyautu ace yanzu kin nutsu kinyi hankali kin fuskanci abunda yake gabanki amma kullum ke kina daukar kanki yarinya saboda mahaifinki yana sonki yana biye miki da dukkan abunda kike so, kin zauna shirme da shashanci 'yan uwanki na dakin mazajensu har da zuriarsu, 'kawayenki wasu daga ciki duk sunyi aure suna zaune lafiya da mazajensu, ke kuwa hakan baya burgeki kullum burinki ki sanya suttura masu tsada kiyi ado da gwalagwala ki shiga motar da kike so ki zaga duk inda kike so kina takamar cewa ke 'yar mulki ce duk mazan da suka zo da niyyar auranki ki sai ki kore su to me zai sanya mutane ba zasu d'ora ayar tambaya a kanki ba."?

Shuru tayi tana auna maganar mahaifiyartata, tabbas duk abunda ta fada a kanta gaskiya ne babu abunda tayi mata kazafi a ciki, manya mutune masu kudi da muk'amai daban-daban sun zo da niyyar auranta amma duk ta koresu saboda ta ganin kamar auran zai tauye mata rayuwarta, a yanzu kuma maganganun mahaifiyar tata sun jefeta cikin rud'ani mai tsanani ashe kallon 'yar iska tantiriya jama'a suke mata.


Ta katse mata tunani ta hanyar fadin." Daga yau sai yau babu ke babu Maijidda mutukar ni na haifeki na rabaki da ita ban hanaki gaisheta ba amma kada ki kuskura ki sake shiga sashenta ballanatana wata mu'amula ta had'aku, duk wani abu da kika sani naki ne to ki tura a dauko miki kada na sake ganin kafafunki a sashenta, bayan haka kuma ki tashi kije sashen 'yar uwata ki nemi afuwarta akan irin abubuwan da ki kayi mata, idan kin gama da wannan to d'aya bayan d'aya ki kira wayar 'yan uwanki ki gaisa dasu, har shi babban yayanku Magajin sarki wanda ki ka dauki karan tsana ki ka dora masa har kina gaba dashi saboda yana nuna miki hanya mai kyau, to shima ki nemi number sa don yanzu haka yana Egypt ki kirashi ki nemi gafararsa, wannan kadai za kiyi ki faranta min rai."

Ajiyar zuciya ta sauke murya a dashe! tace."Shikkenan Mammah zanyi duk yanda ki kace amma don Allah kema kiyi hakuri ki gafarceni ki kuma dena yi min mugun baki."

Girgiza kai tayi da fadin." Tunda kike shaid'ancinki na ta'ba jifanki da wata muguwar kalmar."? girgiza kai tayi da fadin " A'a." tace." To yanzu ma raina ne ya 'baci da al'amarinki, idan kina bukatar albarka to kiyi gaggawar gyara kuskuranki sai mu samu zaman lafiya da juna."

A sanyaye tace."Insha Allahu zan kiyaye amma kice kin yafe mun." jim tayi na 'yan mintina kafin tace." Na yafe miki Allah ya shirya min ke shirin addinin islama Allah kuma ya baki miji nagari wanda zaiyi jimiri da hakuri dake da halayenki."

A zuciyarta ta amsa da "Ameeen ta dan samu sassauci kad'an, da kyar ta yunkura ta tashi tace. "Zan shiga gurin Mommy kamar yanda kika bukata." Shuru tayi ba tace mata komai ta bita da ido har ta bude kofa ta fita.


*****
Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin, ta dan samu sassauci daga gurin mahaifiyarta, suna zaune lafiya wani sa'bani bai sake shiga tsakaninsu ba, kuma tana kokarin yi mata biyayya daidai gwargwado sai dai har yanzu mahaifiyar tata bata wani saki jikinta da ita sosai ba, A gurin Safah kawai ta samun walwala dan wani sa'in ma can take yini, wannan ce damar da ita Safah din ta samu take k'ara nusar da ita hanya mai kyau kuma take kwadaita mata son aure a cikin zuciyarta, sai dai kuma inda gizo ke sa'kar a yanzu bata da wani tsayayye a hannu lokacin da take kan ganiyarta take dasu rurutu amma duk ta koresu, a yanzu dai da zasu dawo da tantance nagartacce a cikinsu, ba kuma ta tunanin neman daya daga cikinsu a ganinta kamar hakan zubewar mutunci ne, ta san dai yanzu labarin dawowarta ya isa ace yaje kunnuwan masoyanta to tana zuba ido duk wanda ya damu da ita a cikinsu zai kawo kansa daga nan sai ta fitar da gwani.

Sai dai kuma a ranar tunaninta ya rushe dalilin hukuncin da mahaifinta ya yanke mata, be fito fili ya sheda mata abunda ke zuciyarsa ba, amma yayi mata hannunka mai sanda cewa mutukar bata fitar da miji a cikin satikan daya bata ba, to lashakka shi zai aura mata wanda yayi ra'ayi.

Tabbas mahaifinta yana tsananin sonta irin son da bayayi wa sauran 'ya'yansa amma ta sheda cewa shi din kaifi d'aya ne, a haka yake baya ta'ba yanke hukunci ya janye, ita a ganinta kamar hukuncin yayi tsauri da yawa, har yaushe ta dawo da za'a d'ibar mata sati biyu ace ta fito da mijin aure kamar akwai rashin adalci a cikin al'amarin.

Ta samu mahaifiyarta da maganar cewa sati biyu yai mata kad'an tayi masa magana ya 'kara mata sati biyu ya zama wata daya, Gimbiya Aysha ta nuna sam babu ruwanta a cikin maganar dalili ta riga ta san abunda yake rufe wanda ita Zinat din bata san dashi ba..........da ta samu Safah da maganar itama cewa tayi babu ruwanta kawai dai tayi kokarin ganin ta fitar da miji kafin lokacin daka a bata ya cika, sosai ta shiga cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa tunani kaf ya ta'allaka a gurin neman mafita, babu yanda za'ayi tabi wani daga cikin samarinta nada tace yazo ya aureta wannan zubar da mutunci ne, tsintar kanta tayi da tashin tsakiyar dare domin neman zabin Allah, duk da bata da wani cikakken ilmin addini, a hakan take gabatar da nafila ta zauna saman dadduma tana salatin Annabi kafin ta mika kukanta ga mai kowa da komai.

*****
To kamar yanda suka tattauna maganar commissioner of police da Asp abunda ya faru kenan, domin a daran ranar da ya dawo ya bukaci zama dashi..................Suka fara tattauna maganganu kamar gaske sai dai kuma tafiyar ba tayi tsayi ba suka samu sa'bani dalili bambacin ra'ayi, a take gurin ya nuna masa cewa shi din *Jan wuya!* ne tafiyar su ba zata zo daya ba, ya nusa masa cewa bashi yakewa aiki ba 'kasar sa yakewa aiki don haka bai isa ya gindaya masa wasu sharud'a wanda suka sa'bawa dokar aiki ba. mutukar yana bukatar tafiyarsu tazo dai-dai to kowa ya zauna a matsayinsa.

Sosai commissioner din yayi mamakin yaron, koda yake tun yana can ya samu labarinsa da kuma irin alakar dake tsakaninsa da Asp Musa Baharu wanda ya zame masa kadangaran bakin tulu, babu shakka ya sake ya bar wannan ala'kar ta cigaba da

Please Login or Register in order to submit comment