Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinajina
   Ummm
Oya kalleni
   'Daga kanta tai amman idanta arufe suke
    Kibud'e idanki mana
A'a kayi hkr
    Sunkuyawa yay yad'auki bra d'inta yami'ka mata yace saka
   Amsa tai ta saka idanta yana zubar da hawaye sosai
   Rigarta yamayar mata sannan yagyara wandonsa
   Kallonta yay yace daina kukan nan
Shiru tai yasaka tongue d'in sa yalashe sauran hawayen

      Hijab d'inta yasaka mata
Yajanyota tadawo jikinsa yace wannan 'kawar taki da kikaga muna magana da ita basanta nakeba
   Gaya mata komai daya faru yay sannan yace Allah babu wadda ta ta6a canja mun tunani da lissafi lokaci d'aya sama dake


  Randa nafara ganinki natabbatar da ina sanki
    Dan Allah kidaina kula kowa
Zan tafi makaranta gobe nabaki amanar kanki inkika kula wani wlh ban yafe mikiba
     Kuma kibawa wannan yaron hakuri inba hakaba wlh duk abunda nai masa ke kika janyo
   Dan wlh zan iya kisa akanki

Zaro ido tai atsorace tace kisa kuma
   Kina mamaki ne, to kidaina
Amman inkika d'auka wasa gobe yazo kifuta wlh zakiga d'anyen aiki, ina fatan kin fahimta
    Ummmm
Oya muje
    Bud'e kofar yay ahankali yafuto itama ta futo saida yaga ta shiga ciki sannan yazauna azauren dan bazai iya shiga ba ahaka duk ta tashi amike take sosai



   Haka yazauna yana le'kenta saida yaga tashiga d'aki sannan hankalinsa yakwanta dan yaga Hapsatu tana kiching tana aiki

    Saida Fahat yazo sannan suka shiga shiya d'aki yashiga direct bai zauna tsakar gidaba

   Itadai tunda abun yafaru takejinta awani yanayi nadaban kuma batasan menene yasaka  ba

   Da'kar tasamu bacci yad'auketa
Awajensa shima hakan ne takasance gwara itama babu ciwo
   Shikuwa da matsanancin ciwon mara ya kwanta sai juyi kuma dayake tayi

   WASHE GARI
Haka koda ta tashi sam batasan ta had'a hanya dashi dataji muryarsa take 6oyewa

   Koda saurayinta yakiratama 'kin d'auka tayi
    Test tai masa akan yayi hkr anbada ita, baiji dad'iba ko kad'an amman sai yay tunanin kodai jan ajiii take masa


     Yau ko tsakar gida saida sand'a take futowa Hapsatu ta tambayeta lpy tace lpy qlu


    Shikuwa yayi sintiri yakai goma shaaa amman baigantaba

   Koda kaliss tazo yay tunanin zata futo sutafi Makaranta amman saitai 'karyar ciwon kai

      Har lokacin tafiyar Nauphal yay amman bata futoba, kuma daya shiga d'akin saita shige bathroom 🛀 sosai yadamu yakira wayarta akashe kuma



    Saida suka futo rakasa su Hapsatu sannan Fahat yace ina Nusaiba take
   Hapsatu ce tace tana d'aki kanta naciwo tad'an samu baccine datasha magani

     Ok toh mutafi
Shidai Nauphal kasa jurewa yay harsun tafi yace yayi mantuwa yakoma gidan


   Lokacin daya shiga gidan tana tsaye abakin 'kofar d'akin su da wasu ka..................✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻



Keep waiting my fan's🤔🤗🤔🤗


Hallmarth ce 💕💖💕
👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔*
_Story and written by_

*SADIYA •A• UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}

🅿---


8⃣3⃣&8⃣4⃣



.............Da wasu kayan baccin ta riga da wando, do gone wandan har 'kasa
   Batasan ma yafutoba dan doguwar sumar kanta take gyarawa tanata tajeta


    'Karasowa wajen ta yay yakauda kansa daga kallonta yace shine kika 'ki futowa kirakani ko


   Jitai gabanta yafad'i taisaurin tattara gashinta awaje d'aya ta d'ago kanta tana kallonsa atsotace



   'Daki tainiyyar komawa yace Uuuu'ummm karki shiga babu abunda zan miki

    Tambayata anan shine meyasa kika 'ki  futowa kirakani, kuma duk yau ban ganki koda atsakar gida ba meyasa


     Shiru tai
Yace ba tambayar ki nakeba
  Kai nane yake ciwo
      Ummm, sannu



Yanzu muje kirakani
   Bazan iya tafiyaba sbd yanzuma ruwa zan zuba masa kozanji sau'ki


   Ok tom shirya sai muje asibiti ko
A'a nidai katafi kawai zan je daga baya idan Ummerh tadawo daga rakakaaa


     Yayi kyau
Matsowa yay kusa da ita
  Itakam sai jaa baya take yana 'kara matsota, saida takai 'karshen bango sannan yasaka hannunsa yatokareta yakalli cikin idanta yace kalleni




    Kallonsa tai, amman suna had'a ido tasauke kanta 'kasa dan bazata iya kallon cikin idan saba


      My wife to be in sha Allah, kinajina
Saida taji wani dummm sannan tadaure tace, Ummm

    Good girl
Zan baki amanar kanki, kinji ko
  Karki sake ki, 'kara futa babu ni'kaf


    Sannan kuma karki 'kara kula wani d'a namiji koda wasa, idan naji labarin hakan ranki zai 6aci



     Sannan banasan yawo atsakar gida babu hijab
   Koda bana nan akaremun dukiyana, akulan sosai da ita, kinajina



   Ummmm
Good
   Duk abunda kike da bu'kata ki kirawoni kinji ko
    Sannan banasan yawan 'kawaye d'aya ta isheki kinji


   Kimun al'kawrin zakiyi Dukkan abunda nace miki kinji
     Shiru tai
Yace bakice komai ba
   Ummm tace


Toh amman ai bakice kinyi al'kawrin ba, zakiyi komai dana saki
   Hmmm I promise you I will do everything that you positioning me to do


     Hmm Allah yashiryeki
Yanzu babu rakiya
  Nace maka bazan iya zuwabafa


Yanzu zantafi har tsawon 2years hubbi amman bazaki rakaniba
   Kika sani ko Acan ma in mutu bazaki sake gani naba


   'Dago kanta tai dasauri jin abunda yace wai yamutu
    Girgiza masa kai tayi idanta nacikowa da kwallah tace Uuuu'ummm


    Bakyasan in mutu
Ummmm
Meyasa to
   Shiru tai
      Murmushi yay yace saboda kinasan yaron mijinki ko
    Tureshi tai tajuya masa baya



'Dan takowa yay yace ko 'karya nayi
   Shiru tai masa

   Yace toh nizan tafi, hubbie taaa
Adawo lpy Allah yatsare ka yakaika lpy yadawo dakai lpy
     Wowwwww ngd sosai dear
Shammatar ta yayi yasakar mata kiss awuyanta yace byeeee


     Wani numfashi tasauke dan ba 'karya taji Wannan kiss d'in sosai

    Juyowa tai ta kalle sa yana futa daga gidan
     Acikin nafef yasamu su Hapsatu sunata jiransa

   Kallonsa tai tace waimeka manta naga baka d'auko komai ba
   Ummerh banganshiba fa
To menene shi d'in
   Ummerh...... Ummerh...
    Fahat ne yay saurin cewa ko P-cap d'inka kaje nema
    Ummm.... Ummm....  Ita naje nema
To ai nad'auka tana cikin kayana inasantane
     Ok amman baka gayamunba
Nasan kanasantane shiyasa na'ki gaya maka

   Itakam Hapsatu kallonsu tai kawai tayi Murmushin dan tasan ba haka zancen yake ba


   Amman tunda sun nuna sunajin kunyar sanar da ita bari ta kyalesu karsu dainajin kunyarta kuma


   Haka suka kaisa tasha yahau mota sannan suka dawo bayan sunga tashin su



    Koda suka dawo Nusaiba takammala gyaran gidan tana ta sallamar masu siyan abunci wanka tashiga tabar mai Mm suwaiba agurin tunda tazo


     Aikin suka cigaba dayi ita da Hapsatu dan haka ake wuni kullum tun daga safe har dare



     Washe gari suka raka fahat shima yatafi makaranta duk da tasa acikin garin take

   Haka ma........
   ****************


Wazan gani su doctor faruq ne suka futo da waliyyansa

      Shiga sukai cikin gidan harda wani namiji wanda a'kalla zaiyi 47-48,kyaky kyawane ajin farko shima


     Shiga sukai cikin gidan suna kallon gidan sosai azauren gidan suka tsaya ganin Alhaji yana shirin futowa

   Yana kallonsu gabansa yafad'i nuna wani yafarayi acikinsu hannunsa yana karkarwa sai kuma yafad'i yasuma



   Salati suka fara suna d'aukar sa zuwa cikin gidan su kuma wakilan doctor faruq suka futa



    Anjuma kafun Alhaji yafar fad'o kallonsu yay yace ina yake
   Waaaa fa baba, inji doctor faruq

Wannan saurayin yana ina
    Wanene baba
Wanda naganku tare yanzu
   Sun futa ai
Dan Allah kiramun su
   ''ko'karin tashi yafarayi
A'a baba kahuta bari inkira makasu
     'Daukar wayarsa yay yace dasu Alhaji magaji su shigo
Ok gamunan
   Kashe wayar yay sannan yamaida dubansa akansa yace gasunan zuwa


    Toh zama yay yana zubda kwalla acikin ransa sai ro'kon Allah yake Allah yasa hasashensa yazama gaskiya


  Suna shigowa
Yaga babu shi aciki, harzaiyi magana sai yagansa yashigo
   Dasauri yatashi yarungume sa yasaki kuka

   Mamakine yakama su
Shikansa Ibrahim mamakin yake dan dai baisan saba bai ta6a ganin saba amman kuma yarungume sa
   Ba nuna 'kyama ko wani abu shima yarungume sa yana bubbuga bayansa ahankali yaji gabansa yana tsananta fad'uwa



    Sakinsa yay yakalli doctor faruq yace doctor Wannan d'anane wlh d'anane ba 'karya zan mukuba Allah d'anane shi


    Sosai abun yabawa kowa mamaki amman sai sukace haba baba daga ganin yaron mu sai kace d'ankane Wannan d'an mune kuma jininmu family'n mu



   Shid'in gudan jinin d'an uwanane
Meyasa zakace haka Baba


Wlh Alhaji wannan d'a nane kuma ni nahaifesa
    Zan iya nuna muku shaida idan baku yaddaba


   A'a bari akira baban sa tukunna dan abun da d'aure kai


    Kallon faruq yayi yace kira baban ku maza, kace masa muna san ganinsa agidan Alhaji Ibrahim mai shaddah kaji


  'Daukar wayarsa yay yakira shi kamar yadda aka umar cesa haka yafad'a


   Lpy meyafaru faruku naji kamun irin wannan kiran
   Daddy, Uncle ne yace ince maka haka
   Ok yana ina, bashi wayar
Mi'ka masa yay kamar yadda yace


   Amsa yay yagaya masa komai daya faru, jummmm yay kafun yace gani nan zuwa
    Aransa yace wannan shine ranar wanka ba'a boyon cibi




  Tashi yay yakalli hajiya habiba yace mata kishirya muje idan su Alhaji Ibrahim mai shaddah

   Inna lillahi mezamuyi musu
Hjy tashi muje kawai

Tashi tai tafara Shiryawa
Shima yashirya sannan suka futo
   Mota suka hau driver yakaisu har 'kofar gidan nasu dan sunga Motocin suma agurin



    Tun kafun su futa hjy habiba tasaka kuka tana fad'in shikenan yau za'a'kwacemun d'ana


    Da'kar Uncle sulaiman yalalla6ata tayi shiru sannan suka shiga sallama tai tashiga sannan aka basu izinin shigowa



   Shiga sukai suka zauna a d'akin Alhaji, yasaka anas yakawo musu ruwa da lemo dama

   'Karowa akai harda cincin
Amman babu wanda yaci ko yasha

   Zama Uncle Sulaiman yayi itama hjy habiba tazauna

   'Kara mai maita musu komai akai kamar yadda Uncle yagaya masa


   Kallonsu yay yace naji kuma nafahimta, shikuwa Ibrahim In banda kuka babu abunda yake dan yakasa gane komai


    Tashiyay yadawo kusa da daddy Sulaiman yace daddy kagaya musu gaskiya niba d'ansu bane


     Kuka daddy yasaka dan tausayin d'an nasa sosai

   Dakewa yay yakalli Alhaji yace, Alhaji Ibrahim wace shaidace kake da ita wadda kace zaka nuna

   Tashi Alhaji yay yabud'e durowar sa yad'auko.....................✍🏻✍🏻✍🏻

👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔*
_Story and written by_

*SADIYA •A• UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}

🅿---


  8⃣5⃣&8⃣6⃣


............Tashi yay yad'auko wata jaka sannan yarufe yadawo yazauna

     Bud'ewa yay yad'auko wani pic d'in sa na ranar da aka haifesa ansaka masa kayan sanyi a asibiti ne ma yana kwance kusa da Ummerh'n sa


   Mi'ka musu yay yace wannan hotonsane lokacin da aka haifesa da daddare


    Kallo sukai sannan Ibrahim ya amsa yaga tabbas yanada wannan photon amman nasa akwai mom d'in sa agurin ba wannan matar bace sannan kuma dasu daddy agurin dawasuma



    Kallonsa yamaida kan daddy Sulaiman yace dad wannan hoton iri d'ayane danawa amman kuma anawa babu wannan matar saidai ku dasu mom



   Kwallace tazubowa daddy Sulaiman yace kayi hkr d'ana yau zan gaya maka abunda naita 6oyewa sama da shekara 47


   Kallonsa su Uncle sukai da mamaki dansu kansu basusan komai ba


********************************

    FLASH 📹 BACK  🔙

......Akwai wata ranar laraba wadda bazan manta da itama mun taho da family na zamuzo garin kano akan hanyarmu ta zuwa sai motata tai facii


   Sai nai parking agefen titi natsaya ina jiran wani abun hawa yazo wucewa in hau motarsa inje cikin gari inkai faci

   muna tadai zaune shiru kuma gashi ita uwar d'akin nawa bazata jure zaman motaba dan bansan bata da lpy bama saida muka taho, sbd tanada tsohon ciki
   Sannan kuma awatan ta na haihuwa muke

       Wani mai mashing ne yazo wucewa natsayar dashi, shiya taimaka mun muka kunce tayar yakaini akai faci sannan muka dawo muka sakata


   Amman gamamakina sai naga babu hjy habiba amotar dan nai tunanin ko bacci tayi abayan mota


    Dan haka saida muka gama na lura, gayawa mutumun nayi nan muka juya dan nemanta

    Hangota mukai tana tahowa da yaro ahannunta sai kuka yakeyi sosai yana 'karawa

    Kallonta nai da mamaki kuma ga cikin tanan ajikinta amman kuma gayaro ahannunta

     Saida ta 'karaso nace mata ina kika samo wannan d'an

    Sai mai machine d'in yace aikam dai a ina kika samo sa

     Zama tai acikin mota sannan tace mun
   Bayan tafiyarku ba'a dad'e ba naji inajin  futsari saina sauko nazagaya dan inyi futsari
    Bayan nagama sainaji kukan yaro kamar an muntsilesa
    Dabazan jeba sbd nai tunanin ko aljanune tunda gurin jeji ne sosai

   Amman saina daure nafarabin sautin kukan yaron
   Abakin wani ruwa nagansa an kwantar dashi wanda da alama ba'adad'e da haihuwar saba

     Saina d'aukosa nafuto daga gurin inata sauri inzo ince maka kutaho masa da madara sainaganku kuma



   Toh Alokacin mukace da mutumun ko in basa yaron amman saiyay fafur yace a'a sbd bashi da aure

   Sai  nace kozai kaimu wajen mai gari
   Yace a'a shibaisan mai garin wannan unguwarba
   Nandai yace kawai bari ya amshi number wayar mu koda zaiji masu d'an saiya kiramu

   Muma muka amshi tasa

   Saina sallamesa nabashi dubu 30 yatafi mukuma muka shiga mota

   Zamu cigaba da tafiya sai hjy habiba tacemun karmu sauka a family house 🏚 d'inmu mutafi gidanmu kawai


   Haka na amsata koda muka shigo garin kano agidanmu muka sauka dayake sharad'a


   Bamu dad'e dasaukaba itama tafara na'kuda dan haka na d'auketa zuwa d'akin haihuwa nan akaita fama abu kamar wasa saida takai wajen 12:30pm sannan ta haihu d'anta namiji

    Bayan komai yalafa angyarata itada baby sai muka yanke shawarar inkira "yan uwana ince musu habiba tahaifi 'yan biyu



   Haka kuwa akai nagaya musu ta haifi 'yan biyu kuma suka yadda


    Saboda shaida yasaka bamu sauya maka kayankaba mukai hoto dasu

    Haka taci gaba da shayar daku amman tunda muka tsinci Ibrahim bayashan nonon habiba saidai madara kawai

    Bayan suna da kwana uku sai Allah yayiwa d'anmu rasuwa munyi kewarsa sosai
   Amman babu yadda zamuyi haka Allah yaso sai muka rufe sirrinmu muka cigaba da kula da Ibrahim


     Saida Ibrahim yacika shekara 6 sannan habiba ta 'kara haihuwar d'anta namiji sai muka saka masa UMAR ake kiransa da faruq




   Haka muka cigaba da rayuwa muna d'an binciken sirri ko zamuji ina iyalan ka suke amman shiruuu


   Anan nan sai akamun canjin gurin aiki nakoma England 🇬🇧 da zama tunda muka tafi bamu dawo Nigeria 🇳🇬 ba saida mukai shekara 27 sannan muka dawo


   Muna zuwa sai faruq yace shi agarin Rano yakesan muzauna sbd yanasan yarin'kayin aiki a asibitin nan danya tai makawa marasa lpy garin



  Haka akai muka tare atsohon gidan mu sai muka saka aka fara gina mana babbar estate Acan saida aka kammala sannan muka dawo



     Haka muka cigaba da zama gaba d'aya family d'inmu
    Amman kusan koda yaushe muna bincike wajen ganin mungano ina family d'inka suke



   Lokacin da faruq yazo mana da zancen auren sama Ibrahim baya GARI da tare zasuzo, dan cemana yay "yar gidan Alhaji Ibrahim mai shaddah zai aura


    Saida d'aurin aure yarage saura kwana 1 sannan mukaji ashe "yar da yake ri'ko ce "yar Mm balaraba dangin bala'i, shine muka rasa yadda zamuyi akaucewa wannan auren, sai kawai mukace muce muku faruq ya6ata kawai sai afasa auren bayan haka da d'an kwanaki sai muzo  muyi muku jawabi akan dalilinmu


    Toh shine fa su Uncle d'insu waliyyansa kenan sukace zasu taho sai sukace faruq yabiyosu
     Sai shima Ibrahim yace zashi, sai suka taho gaba d'ayan su


   Sosai abunda Uncle sulaiman yafad'a yasaka Ibrahim da alhaji kuka dan sunyi masa ri'kon Allah da Annabi basu ta6a nuna masa wani mugun haliba ko kuma su nuna masa wani abu nacewar basu suka haife saba



     Alhaji ne yace Tabbas wannan shine 'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔 Tabbas zai tsone maka idooo

     Allah mai iko


Akunnen Mm Balaraba akai komai dan anfuto da ita tsakar gida tasha mamaki sosai da sosai


    Abunda sukai gashinan duk taji dan itada kakah Hajja suka kai jaririn nan bakin ruwan nan suka ajiyesa sannan sukai tafiyarsu


    Kuma harda su amasu neman sa suna kukan munafurci



      Alhaji ne yace kosuwaye sukai mun haka bazan yafe musuba har abada wlh dansun cutar dani sosai

       Fashewa da kuka yay
Ibrahim yataso yarungumesa yana kukan shima


     Da'kar suka samu sukai shiru sannan Alhaji yace wa Ibrahim babana inga bayanka

   'Daga rigarsa yay saiga wannan SHAIDAR TASU TA FUTO RAMMM
   Yawwa kunga shaidar danake nuna muku, sannan akwai ta ajikina ma bari in nuna muku


   Haba Alhaji aibasaika nuna ba komai yatabbata Ibrahim d'an kane dan haka babu abunda zamuce mu



   Sallama akai ana saka kuka kuma muryar namijine babba kuna

   Futowa sukai dasauri suna kallon bakin 'kofar d'an gidan Alhaji H................ ✍🏻✍🏻✍🏻




Keep waiting my fan's🤔🤔🤗🤗

Hallmarth ce 💕💖💕






Keep waiting my fan's🤔🤗

Hallmarth ce 💕💖💕
👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔*
_Story and written by_

*SADIYA •A• UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}

🅿---


  8⃣7⃣&8⃣8⃣


.................'Dan gidan Alhaji Hamisune yaketa kuka yana kiran Alhaji


   Futowa yay yace lpy meya faru kuma, kaka Hajja ce da daddy sukai accident ankaisu asibiti


     Salati suka saka sannan suka futo motoci suka shiga sukai asibitin acan suka tarar da an'ki amsar su ance sutafi cikin kano bazasu iyaba

    Doctor faruq ne ya'karasa ya saka aka shiga dasu cikin OPERATION ROOM

   Sun kwashi sama da awa 5 akan su kafun aka samu nasarar ceto rayuwarsu


  Sun jigatane sosai dan shi Hamisu yasamu karaya 5 acinya dai gocewa dayay ahannunsa da kafad'arsa

   Fuskar sa kuwa in kaganta bazaka iya ganetaba sam dan ta murzu


    Kaka Hajjah kuwa ta samu gocewa a'kugu sannan kuma 'kafarta guda d'aya ta cire dan wata mutar ce ta murje mata ita tass da hannunta guda d'aya
      Sai kuma spinal cord d'inta data samu matsala
       Ta bugu akanta sosai dan da'kar aka samu aka tai maka mata jini baije kwakwal wartaba

       Saida sukai mata tankwall sannan aka samu nasarar yi mata aiki

     'Dakin hutu aka kaisu sannan aka dawo dan biyan kud'in aiki dana magungunan su


    Uncle sulaiman ne yabiya komai sannan aka cigaba da kula dasu

   Sai bayan Isha'i sannan suka dawo gida inda akabar matar Hamisu tana kula da kaka Hajjah shikuma babban d'anta yana kula da baban sa


    Uncle sulaiman ne yace dama munzone muce abar wannan zancen auren nasu Umar dan gaskiya bazan bari d'ana ya auri dangin wannan matar ba



   Babu komai gaskiya nima bansan haka sukeba dabazan kawo kubama daddy

    Hakadai aka bar magana aka basu sauran kayan lefen su
   Amman uncle sulaiman yace a'a abarsu sun yafe taci gaba da amfani dasu


   Tafiya sukai Alhaji yanata musu godeeya, nan Ibrahim yace bazai tafiba zai zauna awajen mahaifinsa nanda 2weeks sannan yadawo

   Basuyi masa musuba suka barsa anan suka koma gida hjy Habiba banda kuka babu abunda take


    Saida Ibrahim yayta bata ha'kuri sannan taha'kura
    Suka tafi


   Suna shiga gida Mm Balaraba tafara kuka tana cewa Alhaji kayafeni kozan samu salama acikin rayuwata

    Kallonta yay da mamaki yace meya faru Balaraba lpy kuwa, ni babu abunda kikai mun

    A'a Alhaji baka sanibadai amman dai ina 'kara neman afwaraka dan Allah tun kafin ingaya maka


   Mezaki fad'amun inajinki
Zama yay shida Ibrahim akusa da ita dan 'kafarta d'aya tafara wari amman dai haka suka zauna sbd tana zubar da wani ruwa ne



    Kallonsa tai tafara basa labarin abunda kakah Hajja ta aikata masa tun daga mutuwar kakan sa har zuwa mutuwar iyayen sa da rabasu datai shida 'yan uwan sa, dakuma yadda suka sace Ibrahim suka kaisa cikin dajin duk tagaya masa


   Sosai Alhaji yake kuka shida Ibrahim musamman mutuwar iyayen su wanda tasakawa wuta tacisu sosai kafun aka tai makesu


  Dakuma kakansa data rin'ka bawa guba yanaci harta kasheshi


    Yama kasa yi mata magana dan baisan ma ta ina zai faraba idan yace zaiyi maganar, shiyasa yay shiru saidai hawaye gashi tarabasa da matarsa da "ya"yansa ko a ina zai gansu ALLAHU A'ALAMU

     Balaraba kitashi keda "ya"yanki kubarmun gida nasakeki saki 3 kutafi Allah yasakamun abunda kukai mun keda Kakah Hajja bazan yafe mukuba kun cutar dani sosai

     Anas da Fauziyya da suke tsaya suna jinta kuka suka saka Anas harda fad'uwa dan tunani yake shin sud'in musul maine ko kuwa
   Anya akwai zuciya acikin 'kirjinsu
Yayi nadamar kasan cewarta mahaifiyar sa sosai yake kukan ba'kin ciki

    Sallama sukaji anyi
  Juyawa sukai dan suga waye
Abun mamaki wasu mutanene guda uku da j............. 


***********************

..........Hakama Nusaiba ta dage wajen zuwa Makarantarta tamaida hankalin ta sosai wajen karatun ta

   Ga soyayya dasukesha mai tsafta itada Nauphal



A6angaren saurayinta muktar kuwa saidai zumunci kawai dan tagaya masa yayi ha'kuri anbada ita


     Awajen Ummerh ta kuwa bata ta6a sanar da wani tana wannan makeken gininba nagani na fad'a

   Part 4 tai ko wanne ya amsa sunan sa, sai makeken Restaurant data bud'e akusa da gurin

   'Dayan gurin ne data siya aka fara gina musu asibiti bata yi nisaba tasa aka tsaya dan a'karasa wancan gine ginan sannan



     Wasa² Fahat yakammala karatunsa yayi komai harta nema masa aiki dan daddy Nusaiba ne yashige masa gaba yasamu aikin


    Shima Nauphal saura wata 10 sukammala karatunsu

   Sosai yake kewar Nusaiba amman basa d'aga musu 'kafa ko kad'an dan lokacin wayama bashi dashi wani lokacin ma sai suyi kwana biyu basuyi waya ba


      Awajen Hapsatu kuwa ankammala mata ginin gidan ta tsap kowane part yasha gyara ansaka masa komai na bu'kata abunda yarage kad'anne acikin gurin kaya masu tsada ake zuba mata akowanne 6angare

   Sannan tazuba ma'aikata kota ina suna kula da gidan yadda yakamata



    Wani lokacin ma bata samun damar zuwa ganin abunci saidai ma'aikata suyi kawai


   Manya²'n masu kud'i suke fakawa siyan abuncin ta kota ina sunanta yad'aukaka daga gari² ake bata Oder abuncin dinner kona paty



    Sosai tayi kud'i naban mamaki, harta gyarawa Baban Bintu da abokin sa gidansu tazuba musu kayan more rayuwa


  Amman abun mamaki ita ta'ki tashi daga wannan gidan sam saidai gyarashi datakeyi kawai


    Komai Nusaiba takeso tanayi matashi babu abunda tanema tarasa ita kanta yanzu takoma makaranta Hapsatun

    Kuma tana fuskantar komai sosai yadda yakamata



     Fahat da Bintu sun d'inke dan abun yana bata mamakima dan ita tunanin ta kaliss yakeso amman saitaga ashe shi Bintu yakeso



      Har ankai kud'in nagani inaso, da kuma kayan saka rana


     Motar Mom d'in su Nusaiba ce tai parking a'kofar gidan su Hapsatu tana mamakin yadda gurin yake cike da manyan masu kud'i da alhazawa suna cikin rumfar cin abunci ga manyan motoci kashi²

   Gurin dabata sanshiba dazatace ba gurin bane dantasiye gurin gaba d'aya ta maka gida da gurin cin abunci makeke

    Sosai abun yake bata mamaki sosai dan gani take kamar a film ne sbd shekararta ta biyu kenan rabonta da gurin amman yasauya sosai

  Abunda bata ta6a tunani ba
WANNAN SHINE 'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔



    Sakkowa tai tana yatsine fuska tana kallon su gaban tane yafad'i ganin............✍🏻✍🏻✍🏻


Keep waiting my fan's🤔🤔🤗😬

Hallmarth ce🥰😘😍

[04/02, 8:03 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨
✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨

💞NAH💞
SADIYA ABDULLAHI UMAR
💞UMMUH FATEEMAH💞



🅿---


8⃣9⃣&9⃣0⃣


...............Gaban tane yafad'i ganin mahaifinta da kuma daddy'n Nusaiba agurin sunacin abunci sosai hankalinta yatashi


   'Karasawa tai wajen amugun fusace takallesu, cewa tai amman dai anyi asara wlh, SAGIR yanzu anan kakecin abunci sbd ta6ewa karasa a ina zakaci abunci sai gurin nan


   Mahaifintane yakalleta yace meyake damunkine ke waya kawoki nan wajen


   Babah ka kyaleni da wannan tambad'ad'd'en mana inji uwar me yazoyi nan gurin

    Kiwuce nace kitafi bakyaji nane
Wlh babu inda zani saidai mutafi tare daku dan wlh bazanje ko inaba

   Mahaifintane yakalleta yace in kika 'kara magana d'aya anan saina tsine miki


    Kallonsa tai tace kadad'e baka tsinen ba indai akan SAGIR ne wlh babu inda zani saidai mutafi tare kanaji nako


  Nace bazaku tafi tareba tare kuka zo, kiwuce nace

   Bazan wuceba wlh babu inda zani
Kallon SAGIR yay wanda kunya ta isheshi yasunkuyar da kansa 'kasa yace muje SAGIR

   Kama hanya sukai suka tafi tazo tasha gabansu tace kashiga motata mutafi gida wlh idan ba hakaba saidai mutafi tare duk inda zaku


   Mutanene suka farayi musu zobe dan haka yace tashiga motar ta shima yashiga tasa saisu tafi gidan gaba d'aya


   Amman 'kememe ta'ki tace saidai driver yaja tasa sushiga tata sutafi tare
   Dan kar yazubar da mutuncinsa yasaka yashiga suka tafi tunkafu mutane sugane me ake ciki sosai



   Jan motar tai sukai gidansu inda shima babanta yake bunsu abaya har suka isa

Please Login or Register in order to submit comment