Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah yasa kafi haka
  Ameen ngd sosae
Juyawa yay yakama hanayar barin tashar
     Taba dadeba aka saka mota nan aka fara loda kayanta sannan suka shiga ita da Nauphal xama tae tana dan dudduba kafarta da take mata xafi gani tae duk taji ciwo sosae akafar


     Sae wajen 6:00am Sannan motar tafiya KADUNA tacika suka kama hanya
    Kudin mota akace musu tadauko xata bayar sae wani mutum akusa da ita yace aa bari in bayar
    Kallonsa tae taga bata san saba amman yabata kudin mota godeeyah tae masa
    Yace babu komae
Haka sukaeta tafiya vasu suka isaba sae wajen 10:30pm sannan
   Suna sauka aka sakko mata kayanta dauka tae tayi shiru tana tunanin ina tace akaeta tunda ita batasan ko inaba
     Bakin wata inuwa suka xauna tacewa nauphal tsaya anan in samo maka abunda xakaci  kaji dan kirki
     Toh Ummerh saekin dawo
Tafiya tae wajen wata mae koko da kosae ayar rumfarta tace abani koko da kosae
    Toh na nawa
Kokon 50 kosan 100 fanken 50
   Dari biyu tabata kar6a tae tafara daura mata kosan tae da panke sannan tadauki leda xata saka mata Kokon aciki
    Hapsatu ce tace aa kixubamun aroba yanxu xamusha acan mukawo miki
     Toh dan Allah inkunsha ki kawomin dan 6ata suke wlh
    Toh in sha Allah amsa tae taje wajen Nauphal tashimfida xanin data goyo nauphal dashi  sannan tace xauna yaraon kirki inkawo maka ruwa kawanke hannun ka
    Toh Ummerh ai nayi alwala yanxu nayi sallah da wannan ruwan na butar can dana gani

    Toh inga hannun naka mana
Nuna mata yay
    Tae murmushi tace toh xauna kasha kaji

    Xama yay yace Ummerh musha tare kinji Ummerh ta
    Toh saka hannu tae tafara cin kosan tana shan Kokon

    Koda suka gama tashi tae takae mata robar
   Har wajen 12pm lokacin ma babah mai kosae tagama wanke wanke takeyi dakanta
    Hapsatu ce taje tace mata dan Allah koxan iya yimiki wanke wanke
    Aaa aaa barshi kawae
Kawo intayaki toh
Mika mata tae tacigaba da wankewa ita kuma tana saka sauran kayan acikin shagonta
     Haka har suka gama
Hapsatu ce tace mata dan Allah babah ina xan samu gidan haya Koda daki dayane da bandaki

    Aaaa kajimu da tsiya wani irin gida keda baku da  matsugunni kika kamo hanyar xuwa KADUNAH IYEEEE 🤔 🤔 🤔
      A'a dolece tasani xuwa babah
Toh muje gidana daganan sae afara nema muki........
   🍃🍃🍀🍀🍃🍃🍀🍀🍃

   *DASHEN🍃ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*
*DAN* *HAKIN* 🍃 *DAKA* *RAINAH😏** 🤔

             Nah
  💕Ummuh fateemah💞

🆓 *page*
   Page 2⃣9⃣&3⃣0⃣


*Wata* katuwar motace tadaki wannan nafef din nasu ta cillasu can cikin dajin daga gefen wata bishiya
    Ko minti uku basuyi dafadawa gurin ba bala da baba mai kosai suka fara yunkurin futowa aikuwa kafun sukarasa futowa nafef din yakama da wuta gaba daya saici yake
   Ihu suke suna neman tai mako Amman babu kowa agurin koh alamar motsin mutane babu bare susaka ran ceto.......


Wata motar hayace tazo wucewa hapsatu tasa hannu tana tsaydata Amman ko sauraran su basuyi ba suka wuce abunsu

   Komawa sukayi bakin Titin suna jiran ko xasuga wata tazo wucewa
    Suna zaune sukaga wuta ta kama bawwww
    Dasauri takama hannun yaran tace kutashi mutafi wuta
   Dahanzarinsu suke tafiya gashi duk sun gaji sosai gurin data saba kwanan anan taje ta kwanta ita da yaran
    Basu dadeba bacci yadaukesu suduka dan amugun gajiye suke

   Basu suka farkaba sai da gari yawaye Nauphal ne yafara tashi yaga ummerh sa akwance tana bacci
    Murza idonsa yayi yace ummerh nah kece ummerh
    Jin ana shafa mata fuska yasata bude ido cikin Sauri tana mikewa tsaye
    Ganin Nauphal ne yasata murza nata idon itama dan ganin shine ko kuwa gizau yake mata

    Shidinne dai wata muguwar runguma takai masa tana kan kame shi gam ajikinta kamar za'a kwace mata shi
    Kuka suka saka atare dan sun rasa mezasuyi idan ba kukanba
    *FAHAT* dayake bacci kukansune yata sheshi yazauna yana kallon ikon Allah dan shi dai yakasa gane musu
    Duk da yafi Nauphal girma dan zaikai shekara 15 Nauphal kuma yanzu yake 13 banbancin kadanne

   Shima hapsatu kamosa tayi tarungumesu gaba daya tanaci gaba da kukan sosai saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru

    Cewa tai kujirani anan inje in samo mana ruwan alwala kunji
    Toh ummerh
Tafiya tai tasamo musu ruwan alwala dayake babu nisa da jama'a fiyo wata tasiyo musu Leda daya sannan tadawo alwala sukayi sannan sukai sallah tanajin kunyar yin sallah gari yayi haske amman yanzu babu yadda ta iya haka tayi tanata istigfari

    Ce musu tayi mukoma can dinnan ko kuma muzauna anan dan niyanzu tsoron mutane nake

    Cewa sukai A'a muzauna anan kafun musamu gurin zama
    Toh bari inje in siyo mana abunda zamuci
   Tafiya tai cikin garin tana duddubawa har taga inda ake shinkafa da miya ta tsaya ta siya musu ta dari biyar sannan ta siya ruwan shayi dauri uku da bread sannan tadawo
    Zama sukayi sukaci suka koshi sannan tace muje gidan wanka muyi ko
   Kunga mafi kyau shiga cikin mutane neman inda zamu zauna

    Aikuwa haka akayi gidan wanka sukaje sukayi wankansu tadauko kayan *Nauphal* tabawa *FAHAT* yasaka itama tasaka wasu kayan suka daure wanda suka cire aleda suka saka abakkonsu

   Shago taje ta siya musu takalma da man shafawa sannan suka shafa
    Shiga suka farayi cikin garin suna dan zazzaga garin *KADUNA* kozasuga inda yayi musu sukama haya

   Wani mutum suka gani yatsufama sosai suka gaidashi sannan sukace masa dan Allah suna tambayar shin ina xasu samu gidan haya agarin nan koda mai daki dayane da ban daki
   *Babah sa'idu* yakallesu yace 'yata inake ina iya kama haya
   Tace Babah zan iya insha Allah
Yace to shikenan ni dillaline ina bada hayar gida amman muje kiga wanda suke ahannuna kozasuyi miki saiki za6i daya daga ciki

    Toh *Baba* muje tafiya sukayi mai dan nisa kadan sannan suka shiga cikin gari sosai unguwace ta jama'a
    Nan yafara nuna mata gidajen kowanne da mutane acikin sa sannan kuma yakaita wasu Gidajen
    Sukuma daya mutum dayane aciki dayan kuma mutum biyune aciki amman matsalar duk vandaki dayane dasu

  yace toh acikinsu wanne ne yayi miki
Toh baba duk sunyi amman matsalar ta bandakice wlh Baba daso make dasan samune ko zamu samu mai ban daki daban
   Ey Yar nan zaku samu amman da tsadafa sosai dan duk wadannan gidajen dana nuna miki dukkansu dubu 10 ake biya duk shekara
   Amman mai ban daki daban da phalo da daki biyu da kicin shikuma dubu 20-30 ne duk shekara
    Yakike gani shidin zankaiki ko kuwa
Toh baba muje in gani
   Nafarkon da sukaje d'aki biyu, ban d'aki, kicin, babu phalo kuma part biyune kowa da nasa shine dubu ashirin #20
   Shikuma dayan d'aki biyu, phalo, ban d'aki, kicin sai dan karamin tsakar gida shikuma part 4 aciki shine me dubu 30# kuma akwai mutane aciki guri dayane ba'akama ba inda ya nuna mata

    Toh gurin yayi amman itakam tsoron mutane take sosai dan haka yasa tace suje dayan wanda bashi da phalo suzauna kawai tunda shi kofar shiga part dinkama daban take data daya 6angaren kuma akwai katanga data shiga tsakaninsu kowa kofarsa daban
   Nan taza6a tace masa nan yayi Baba bari muzauna anan kawai
   Toh shikenan amman kinsanfa nan dubu #20 ne koh duk shekara
   Ey baba zan biya yanxu bari in baka rabi zuwa nan da sati biyu zan cika maka to shikenan

    Shiga sukayi da kayansu taduba tadauko masa dubu goma acikin kudin ta sanann tafuto tace gashi Baba
   Yace A'a Yar nan bari in kira dayan abokina sai mu amsa kinga saboda yanayi na rayuwa yau kaine gobe ba kai bane ko yakikace
    Hakane kam
Wayarsa yadauko yacdanna kira wata number aka dauka nan yayi masa jawabi sosai yadda zai gane sannan yace gashinan zuwa
   Bai dadeba  yakaraso nan akayi komai akan idonsa
   Nan sukace taciko dubu biyar kawai tarinka biyan dubu shabiyar 15 duk shekara taji dadi sosai kuwa
   Baba sa'idune yakalleta yace yata kije asibiti aduba miki kafar nan taki dukta kumbura gashi taja ruwa ko kuma kiduba kiga ko sartse kikayi
   Toh baba IN SHA ALLAH zanduba in gani kafun inje koda chemins ne
   yace mata yanxu kingani kowa yanada nasa shaidun koh ke da danki daya da Malam baba
   Nima nida danki daya koba hakaba
Kinga hakan yafi kai waye
   Ey Babah ngd sosai
A'a karki damu ai duk wanda yataimaki wani shima Allah zai tai makesa
   Hakane kam ngd
Sosai Allah yasaka da alkhairi
   Ameen tafiya sukayi itakuwa Hapsatu suka fara duba yaya zasu fara aikin gidan yanzu
    Cewa su Nauphal tai ina zuwa kujirani zanje in siyo mana tsintsiya da allura in duba wannan kafar
    Toh Ummerh saikin dawo
Toh ngd
   Futa tayi taje wani shago data gani acan bayan unguwar su tasiyo abunda duk zasu bukata sannan tadawo gidan
    Lokacin sukam harsun fara futo da "Yan tarkacen da suke cikin dakin harda wasu kodaddun labulaye da tar kacen kwanuk da tukwane da farantai da wasu fasassun robobin ruwa da kuma jarka guda 6 yalaye nazuba ruwa

   Cewa tayi toh wadannan kayan banamu bane amman bari inje in gayawa Babah sa'idu cewa munga kaya yaya zamuyi dasu

   Toh ummerh kibari muje mugaya masa mana
   A'a kubari inje dan yanzu nikam tsoron garinnan nake sosai wlh
   Toh ummerh
Futa tayi tana futa tag...........


***     ***      ***

A6angaren su *Balaraba* kuwa haka suka koma gida babu wani farin ciki ko kwanciyar hankali atare da ita
   Koda gari ya waye sun shiga tashin hankali sosai dan dukkan tashoshin garin Rano lungu da sakonsa saida suka duba amman babu su Hapsatu babu dalilin su ko kuma alamun su

   Hankalinsu yayi matukar tashi dan Alhaji daya dawo yatambayi Hapsatu
   Sun rasa mezasu ce masa
   Kawai sai fauziyya tai katsa landan tace muma bamusan inda ta tafiba
   Tun jiya mun kasa bacci sbd nemanta da muke
   Wlh mun gaji da halin wannan banzar yarinyar ta tafi yawon karuwancin ta sanann tabarmu da nema haka kawai
      Kema dai kyafad'a haka kawai muyi tafaman wahala akan karuwa
   Wlh mama wadda batasan ciwon kantaba ma kuwa wadda bata da aiki sai karuwan..........
   Wani wawan mari aka dauketa dashi wanda yadauke dukkan wani jinta kanta ankara aka kara dauketa da wani marin saida yayi mata kwarara guda 4 sannan yakyaleta shima ganin tafadi kasane hancinta yana futar da jini shine yasashi kyaleta
   Duka yakai mata da kafa yana fadin akwai wanda yakaiki karuwanci ne eyeee
   Tunda anriga angur6ata miki rayuwarki
   Kuma kisani wlh dukkan sharrin da ake kullawa akan Hapsatu kanku zai koma
    *WLH IN GAYA MIKI*
*DAN HAKIN DAKA RAINA* *SHINE ZAI TSONE MUKU IDO*
   Karkuyi tunanin kuna cutar da ita da kaninta dan ganin bata da kowa
   Toh ina mai tabbatar miki da cewa Allah yana tare da su akoda yaushe
    Kuma dukkan wanda Allah yatsaya masa to bashi dasauran Kuka
    Har lokacin dukanta yake kamar jaka
Da gudun tsiya s.......


Hallmarht ce💞💖💞
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: ✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨

💞NAH💞
SADIYA ABDULLAHI UMAR
💞UMMUH FATEEMAH💞



🅿--- 3⃣1⃣&3⃣2⃣


🆓 page

   Da gudun tsiya sukayi kansa suna cewa bazaka denan dukan taba ANAS wannan wani irin haukane eyeee


Gajiya sukayi dan sunkasa kwatarta daga Alhaji har mama Balaraba sunkasa amsarta dukan ta yake kamar an aikoshi

   Balaraba ce tace wlh ANAS idan baka daina dukan taba saina tsine maka kaji narantse wlh kuma baka isa ka karyamun rantsuwata ba

   Jin hakan ne yasashi tsayawa da dukan nata Amman fa tadaku sosai dan bakaramun duka yayi mata ba
    Dan tunda take aduniya bata ta6ajin irin wannan dukan ba gashi kuma yau ta d'an d'ana

    Kamata sukayi itada Alhaji sukayi waje dan zuwa asibiti dan tahancin ta, tabakin ta, ta goshi, duk jini zuba yake
    Sannan  gawani nan yana zuba ta kasanta kamar an6alloshi
    Dak'ar take iya taka kafarta saboda muguwar azaba
    Amugun wahale take dan jitake kamar jiri zai dauketa babu yadda suka iya dole yasasu suka je chemist dan afara dubata kafun suje asibitin

   Da'kar suka shawo kan Baba iyabo yadubata sosai yayi mata kokari sosai nan yake sanar da Balaraba tana da ciki dan Allah yataimaka sun kawota da wuri dabasu kawota da wuriba daya zube

Tashi tayi amugun razane tana fadin CIII MEEEEEE............



***        ***        ***

Tana futa taga abokin Baba sa'idu gaisawa suka karayi take gaya masa kayan dasuka gani acikin dakin nan yace mata wlh matar data kama haya agidan ce tayi arziki shine tace duk kayan dasuke shiki tabar mana tofa shine muka tsinci na tsinta mukabar sauran
   Kiyi amfani dasu kawai in kina so Wanda basu da amfani kuma ki xubar
   Toh Baba ngd sosai Allah yasaka da alkairi
  Amen "Yar nan
Komawa tayi cikin gidan ta tarar harsun fara sharo dakunan da ban dakin sunata cire yanar
   Ita ma fara tayasu tayi aikin dansu gama da wuri saida suka share ko Ina nan suka kwashe sharar suka saka abuhu
   Lokacin da suka bude kichin dinne sukayi mamaki dan jerene aciki nakomai tsaf Ba'ata6a ba harda sababbin kuloli acikin sa fara dubawa sukayi ahankali nan sukaga harda shinkafa buhu 2 da taliya da maka roni
   Kayan avunci sosai ne acikin gurin harda mai doyarce dai tafara hun huna da dankali saidai 6ura da sukasha sosai
    Ce musu tai bari inje in gayawa Baba kayan dayawa sosai fa

   Sukace Toh
Tafitai gidan tayi sallama
Amsa mata sukayi nan take fada masa komai akan kayan dasuka gani sosai dana abunci
     Babane yace mata kiyi amfani dasu Hapsatu wlh muma mun samu arziki sosai acikin wannan gidan
   Wadannan Allah yayi rabon kine Hapsatu karki damu kinji
   Toh Baba ngd sai anjima
Sannan ko kinga wani abun ma karki dawo kidauka kawai
    Toh Baba
Tashi tayi danta futa kafarta ta rike gam takasa takata
   Salati tasaka
Baba Hasiyace tace lpy "Yar nan meyasameki
   Wlh Baba kafatace nakasa taka ta
Assha LAHAULAH
   BARI MUGANI
zuwatai tafara tai maka mata tazauna sannan tace muga kafar taki
    Mika mata tayi
Inna lillahi ni Hasiya mezan gani haka saikace ba mutum ba dawannan katon hakin akafa fuwanki har kusan 3 Amman kina tafiya haka nan

    Binta Binta kina inane
Ganinan Babah lpy nikam wannan kira haka
   Dauko mun matse fata da leta da kuma allura maza kinji yi sauri
   Dauko mata tayi dan aleda take ratayesu tasa asaman sip

   Yawwa daukarsu tai ta konasu da letar nan sanan tadauki wata auduga tagogesu tas
   Ahankali tafara cire mata sartsen duk inda tacire sai yayi feshin ruwa sosai
    Haka saida tacire mata su tsap sannan tafara buda gurin da allura tana yankewa da sabuwar rezar data bude yanzun
    Hapsatu jitai kamar ancire mata wani mugun nauyi daga kafarta
   Danjitae sakayau kafar tata

Baba hasiyace tace muga dayan kafar taki dubawa tayi nan guda dayane sartsen Amman yajah ruwa yakumbura sosai
    Shima matseshi tayi tana fad'in sannu kinji "Yar nan kinyi jarumta sosai
   Nan kamar tar gad'e mlm zoka duba mata dan inajin nan kam tar gad'e ne
   Toh tasowa yayi yafara duba mata
Yace ey wlh tar gad'ene kam
   Wai nikam "Yar nan a ina kikaji Wadannan ciwukan sai kace wadda tai ya'ki
    Murmushi tayi kawai batace komai ba
Sannu sukaita binta da ita sannan
  Baba Hasiya tace dan huta kafun kitafi
   To Baba zama tai tadan huta har wata gajiya taji tana saukar mata
    Takai kusan minti 40 sannan tace bari in tafi Baba
  Haba dakin kara hutawa itama kafar tasamu salama ai ko
   Bari ma in kira binta ta tai maka takai miki ruwa ki watsa ko kyaji dadin jikin ki
   Aa babah....
Wani A'a
   Kina inane Binta
  Gani nan Baba kayan make up din nan nake kwashewa
  Ok toh yiki kwashe kizo
Toh Baba
Bata Jimaba tazo
  Yawwa "Yar kirki  kawo mata ruwan dumi tadan watsa
  Ki saka mata aban d'aki
   Aa Baba bari inje aiki mukeyi nabarsu sukadai karsu zata ko 6ata nayi sufuto
Aaaaaa"aaaaaaa 'aaaaa wlh hakane kam bari inkun gama Binta takawo muku ruwan zafin kawai kuyi wankan
   Toh Baba ngd sosai Allah yakara lpy
Ameen "Yar nan
   Wai nikam yasu nan kine
Murmushi tai tace Hapsatu sunana
    A'a kice mesunan sirikatace
ALLAH yabar kauna sirika
   Murmushi ta'karayi tace amun Babah


  Futa tayi taka ma hanyar xuwa gida
Lokacin dataje gidan sun gama share ko'ina sun wanke ko ina dan tayal ne ako ina acikin gidan
   Sunsa tsunman dasuka gani sun goge ko ina ya tsane
    Kayan kiching ma sun wanke sun goge komai Doya, da dankalin dasukaga sun lalace suka futar suka saka abuhun shara
    Dan watan ta d'aya da tashi Amman saboda yanayin sanyi ga iska ga 6ura kota ko ina shiyasa gidan yayi futu futu sosai
   Yadda kasan an shekara ba'a shiga gidan ba
    Mamaki tai ganin sun gama komai har wankin kaya sunyi shaya
    Tarar dasu tayi suna iban ruwa dayake akwai rijiya acikin gidan kuma akwai guga aciki
     Wai harkun me
Mun gama Ummerh
  Sai kace wasu injina gaskiya kun aykatu sosai Allah yasaka muku da gidan aljannah
   Amen yarab Ummerh

FAHAT ne yakalleta sai kuma yace Ummerh mujefa cigiya har INDA RANKA, BBC NEW'S MUJE
   Amman shiru bamu ji bayani ba

Murmushi tai tace Allah yashirye ku wlh
  Ummerh munjefa sai kafun nashiga naji ana cewa kizauna kidan huta shine nadawo nace masa kina nan muci gaba da aikin mu

Au ainazata bakuje nemana ba
   Haka kawai kuke ta zaune
Haba mu mafara
  Dariya sukayi gaba d'aya suka cigaba da dibar ruwan tana tayasu cika wasu abubuwan
   Atare sukayi jeran kicin din dakuma sauran ayyuka
    Kallon su tai tace toh yanzu mezamu siyo muci kuma ice zaku siyo muhura wuta azaure ko kuma magal zaku siyo mana da gawayi dan naga acan kofar gidan wasu makera anayi
   FAHAT ne yace Ummerh ga gass nan aisaimu kunna muyi amfani dashi
   Gass kuma ni Hapsatu ina na iya aiki dashi ko kunnashi ban iyaba
    Hh Hh Hh ummerh ni na'iyafa wlh agida nikeyin girki kullum
   Toh maza shiga kayi
Meza'adafa ma Wai
Ai sai abunda kikace
Tohhh🙄🙄 kubaku da za6i sai nawa
  Ey mana Ummerh kifada
Toh nikam banasan komai
   Nauphal ne yace toh muyi shinkafa da wake tunda akwai
    Saimu daka yaji koh yayah
Yawwa kumafa hakan yayi mudaura
    Hapsatu ce ta tafi dakanta tasiyo barkono da salat, tumatir, kokumba, da albasa duk sannan tasiyo musu kankara daruwan sanyi leda daya, da tiara, da so6o, cotta, kanin fari da danyan kifi na dari biyar sannan tadawo gida
   Lokacin sun zuba wake
Adayan kuma sun daura ruwan zafin wanka har Nauphal yashiga yayi Fahat kuma zai shiga ta shigo
   Zuwa yay zaitayata aikin tace a'a maza kayi wankanka bari ingyara
    Tafiya yayi yay wanka yashirya
Lokacin ta gama komai ta tattare gurin ta gyara
   Itama wankan tashiga
Lokacin harya sauke abuncin yajuye akula Nauphal yakama wanke-wanke shikuma yahad'a sauran kayan abuncin yakai daki ya ajiye
    Kifin yasoya sannan yasoya man dazasu ci abuncin dashi
    Saida suka kammala komai sannan suka zauna cin abuncin ababban plate 🍽 tazuba musu abuncin suka saka hannu suka faraci
     Koda suka gama saida suka tattare komai sannan suka dawo dakin suka zauna
    Hirar su suke
Sai Hapsatu ta kalli Fahat tace nikam Fahat inane gidan ku
   Saida yanayin fuskarsa yacanja dakar ya kwa'kulo murmushi yace Ummerh meyasa kika tambayar gidan mu
    Haka kawai kuma yakamata musan gidan ku dan mumaidakai koh yakake gani
   A'a Ummerh dan Allah karki maidani gidan nan wlh banasan komawa gidan nan ko amafarki wlh
   Meya faru haka Fahat?
Kabani labarinka in babu damuwa?
Toh Ummerh bazanki gaya miki koni waye ba da kuma asalina ba..............


***      ***       ***

   A6angaren su fauziyya kam
Mama Balaraba anugun razane ta tashi tace ciiii meeeeee na shiga uku yanzu fauziyya cikine dake inna lillahi wa inna ilaihi raji'un nabani
    Tayaya akayi fauziyya tasamu ciki
Am nace ba dan Allah tayaya za'ai acire wannan cikin
   Zaro ido Baba iyabo yayi yace minana kike cewa hajiya
  Kazubar mana da cikin nan nakeso
Niii nini nii Wlh bazan iya aikin sa6an nan ba badani ba hjy
  Nace kadauka d'anka kubarmin chamist Wlh konayi maka ihu yanzu jama'asutaru
   Haka kawai ni nace d'anka yaje yayi ciki
  Tashi Balaraba tai tace katai makamun karkamun ihu yanzu zamu tafi
  Yawwa yafi dai kam
Amman kaban kudina maza kafun nama rashin mutunci Wlh kagane ko?
  A'a Baba iyabo basaikayi rashin mutunci ba yanxu zan baka kudinka nawane
  Yawwa yika kawo maza dubu biyar da d'ari tara da hamsin da biyar
  A'a nashiga uku harda biyar Baba iyabo baza'abar mun biyar dinba
  Ey bazan bari ba dan tashegen zan yiwa ragi kaban kud'ina tsaf sannan kafuta anan Wlh
   Balaraba saida ta irga masa kudinsa tass sannan takama hannun Fauziyya suka futo daga chemist din
  Kama hanya tayi sukayi wani chemist din ma nan ma babu wani sauki sai wula 'kanci data tarar
Saida sukaje chemist yakai 5 amman babu wani bayani haka suka dawo akan zasuje cikin garin kano gobe dan samun mafuta
    Mama Balaraba kuwa tashiga tsananin tashin hankalin daba'a zato bare tsammani dan ta gigice ta razana dajin wannan zancen har yakai kunnen..........


Ina ganin comment dinku masoyana ina godeeyah sosai da sosai
   ALLAH yabar kauna
Love you all my fan's 💞💞💞💞💞💞💞💖💖💖💖💖💖😘😘😘💋💋💋💖💖💖💖💖💖💖❤❤❤😍😍😍😍😍😍😘😘😘

Hallmarth ce💞💖💞
     
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨
✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
*🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️*
بسم الله الر حمن الر حيم
*✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏* 🤔✨

*💞NAH💞*
*SADIYA ABDULLAHI UMAR*
*💞UMMUH FATEEMAH💞*



🅿---

Page 3⃣3⃣&3⃣4⃣

Danjin zancen yakai kunnen Anas da kannensa shiga sukai cikin gidan ad'arare suka wuce d'akinsu

    Zaunar da Fauxiyya tai tace dan uwarki a ina kika samu ciki nace miki eyeeeee

    Uban waye yayi miki ciki
Kifad'amun nace kafin yanzunnan in yanka ki wlh kinajina ko
Cikin tsananin tashin hankali da rud'u take maganar


     "Dan tuno da maganar da likitan nan yamusu akan karta kara samun ciki dan in takara samun ciki tofa saidai tarasa mahaifarta gaba daya"


   Ma'ana bazata kara haihuwaba kwata kwata yanzu kuma gashinan tayi wani cikin wannan na 4 kenan


    Kuma ita gaskiya bata da burin "yarta taja mata abun kunya acikin garin toh yanzu yayah zatai kenan


    Haka Balaraba taita masifa tana tambayar Fauziyya wayay mata ciki amman ko ajikin ta tayi mata buruss
   Tana zaune kamar bada ita take ba

    Saida Balaraba tadauko wata katuwar wu'ka tace wa Fauziyya koki gayamun waya miki wannan cikin ko kuma na yankaki


    Sannan cikin rawar baki tafara fad'in wlh mamah zan gaya miki ki ajiye wukar nan wlh zan fad'a

    In kinga na ajiye wu'kar'nan toki tabbata kin fadamun Gaskiya wlh inba hakaba Wlh saina yankaki, kinjini koh ba kijiba

   Tunkarota tai gadan gadan da wukar zata luma mata
   Tana fad'in kin manta abunda doctor yace koh akan karki kuskura kisake daukar ciki sbd mahaifarki bata da lpy in aka 'kara yimiki abortion zaki rasa mahaifarki


   Yanzu yaya kike so inyi
Kuma dawani idon kikeso in kalli yayyenki da jama'ar gari eyeeeee

    Ma..... Ma.... Ma.... M... Mama..... Wlh wannan cikin na jaz.... ja...... z.. u.... l.. i... J.. azuli..... ne Wlh

   Jazuli.....  jazuli....  kuma bangane ba jazuli.... dana bawa kudi yayiwa Hapsatu fyade
   Eyy Eyy Wlh shine
Yanzu kuma haukar taki kan jazuli takoma
  Inna lillahi wa inna ilaehi raji'un kice hauka nake tayi nice keda abun kunya agari
   Toh wlh daga ke har Jazulin saina kasheku
   Kan Fauziyya tayo da gudun
Ihuuuu taraf ka tana fadin atai makamun jama'a
   Za'ai kisan kai Wayyo Allah n............



***      ***       ***
ALHAJI UBAH SHEHU
Shine mahaifina yakasance mutum mai tarin dukiyane
   Dan shahararren d'an kasuwa ne shi babu abunda baya siyarwa kama daga kayan abunci sutura motoci mashina da kekuna da saida gidaje yana siyan fili yagina yasiyar

   Wannan dalilin ne yasa shi yin suna acikin garin kano kota ko ina ansansa har wasu suna masa kirari da
SANA'A GOMA MAGANIN

Please Login or Register in order to submit comment