Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san Allah ne kad'ay zai cece su agurin ta, da'kar idan bata kore su daga aiki ba

   Suna shiga phalon da ita sukai tozali tana zaune akan kujera 'kafa d'aya kan d'aya abunta tana ta cin apple
    'karasa shigowa sukai suka russuna agabanta, kallon su tai awula'kance tace lpy meya faru ina kuma Nusaiba take
    Am..... Ammm... Am... Tana nan shigowa, Amm.. Amm... Amman abunda yafaru shine ta'ki amuncewa da sa'konki, kwashe dukkan yadda sukai yayi ya gaya mata, amugun fusace ta tashi tace sam wannan ai zancen banza ne yaza'ai ace mace kamata ta tura da sa'ko amman akasa samun amsa mai dad'i, kutashi maza kuje kugaya mata wacece ni sannan ta fad'i kuma Ada din kud'in datakeso zanna biyanta duk wata

   Hjy wlh mun gaya mata amman tace a'a muyi hkr wannan ma abunda takeyi ya isheta rufun asiri
     Whatt kutashi kuje na sallame ku maza tunda har anrasa mai kawomun farin cikin "'yata acikin ku dan haka ku 'kara mai maza nabaku minti 5 kubar gidan nan
   Dan Allah kiyi hkr wlh bazamu sakeba ko ina ne zamuje mu samo mata duk wadda takeso amman karki rabamu da aikin mu, Outtttt, tafad'a da 'karfi
   Babu yadda suka iya haka suka futa daga gidan dan idan suka tsaya zata saka ayi musu korar karene
     Zama tai tana lila 'kafa akan kujera tana tunanin yadda zata kaya atsakanin su da Nusaiba dan tasan cewa zatai  abarta tana siyan abuncin gidan, ita kuwa bazata bari tanacin abuncin wannan ma'kas'kancin gidan ba

   Abakin 'kofa Nusaiba ta had'u dasu suna shirin futa da jakun kunan su ahannu, kallonsu tai tace ina zaku kuma Aunty safiyya, hjy ce takoremu, akan me, gaya mata duk yadda akai tai, sbd wannan Za'a kore ku sai kace ku kuka hanata zuwa, Maza ku koma bakin aikin ku, zanje in sameta
   Toh hjy mun gode
Kallon 'kawarta tai kalisat, tace muje kalis, ok Nusy
   Atare suka shiga phalon suna tafe suna hira harda tafawa, da Sallama akan labban su suka tura 'kofar phalon, tana kishingid'e akan kujera abunta tana kallon TV

    Zama Nusaiba tai kusanta, kalisat kuna ta gaidata, Amsawa tai da kulawa tace, a'a kuna tare kenan, eyyy mom yau kun'ki zuwa school ko, mom babu abunda sukeyi ai shi yasa, ok tom kunde'ki zuwa kawai amman ana karatu tunda ba hutu kukai ba
    Sallama hjy safiyya tai tashigo, kallon ta mom tai da tambayoyi fall bakinta, daga ina kike,  waya dawo dake, me kikazo yi kuma, uban wa yabaki damar shigomun phalo

   Mommmmm wannan tambaya haka Wacce zata amsa daga ciki, ni na bata dama nace su koma bakin aikinsu, Amman daughter yaya zakiyi haka bayan kinsan duk wanda nasa aiki ya'ki yimun "'karshen sa kenan

   Nasani mom amman kibarsu kawai, toh kefa yaza'ai da cin abuncin naki, mom na hakura basai naciba, really, yes mom, ok thank you dear, all is for you my dear mom,murmushi tai, itakam Nusaiba tashi tai takama hannun 'kawarta sukai part din ta

  Ajiyar zuciyah ta sauke tace Allah yasoki, tashi kiban guri, tafiya tai itama part din datake ajiye kayan ta danta maidasu inda suke

    **  **   **

Agida kuwa koda suka tafi aikin gabanta  Hapsatu taci gaba dayi dan ita bazata tafi tabar aikin ta da takeyiba da yaranta ta tafi wani gurin ba
     Koda suka dawo tagaya musu duk abunda yafaru sunji dadin yake hukuncinta

  Haka rayuwa taci gaba da tafiya, inda malamun su Nauphal yacanja masa guri yakai sa ss3 akan yadda yaga Yanada 'kwazo sosai

   Itakam Nusaiba asace take turawa asiyo mata abunci Agidan su Nauphal
  Akwan atashi babu wahala yanzu Nauphal yazana jara bawar sa inda result dinsa yay kyau sosai
   Gashi kuma Fahat yashiga aji na biyu a mkrntrs
    Komai yana tafiya dai-dai
Inda Nauphal yasamu gurbin karatun sa na Likita amakarantar zariya, sosai yake kewar "dan uwansa da Ummerh bada himma yay sosai dan ganin ya cimma daci akan abunda yazo nema
   Suna waya shidasu kusan kullum babu fashi, sosai Hapsatu ta dage wajen ganin tayiwa yaranta addu'ar Allah yakare mata su ya tsare mata su daga dukkan Sharri

Yau tun wuri suka kammala komai dan babu mkrnt kuma akwai wani taro da za'ai na gwamnoni, kuma ambada hutun 7week's
    Nauphal yadawo gida shima sunyi kayan siyarwa sosai suma
   Futowa yay danya bud'e shagon yayan sa, yana budewa yashiga yafara tartare shi yana sharewa
   Sallama akai da tattausar murya mai d'aukar hankalin mai sauraro
   Juyowa yay anutse dan ganin mai mgn wata kyakykyawar yarinya yagani wadda bazata wuce shekara 15 ba amman komai nata nagirma yabayyana kallonta yake, tanata mgn amman baisan tanayiba
   Saida 'kawarta ta ta6ashi sannan yace ammmmmm mezan baku, sweet ibon guda 10 sai kabamu chocolate guda 10 biskut guda 10, ok, zubo musu komai yay yamika musu, kud'in ta mika masa tana had'e rai amsa yay shima ya had'e nasa ran dan bayasan raini sam
    Basu canji yay yajuya abunsa duk da yanasan 'kara kallon ta koda sau d'aya ne amman yaga kamar tanasan kawo masa raini ne
    Tafiya sukai suna hira, kalis ce tace Nusy kinfayi kasuwa, kasuwar me ban gane ba, wannan kyakykyawan guy din ya 'kyasafa, 'kyasa me wlh Allah yakiyaye ni inso wannan yaron, yaro kuma, ey mana wlh naraina sa sosai ma kuwa bakiganshiba d'an 'karami dashi dukafa bai wuce 19-20 ba
   Aaaa kinganki waike ko wanne irin saurayi saikin raina sa, ey haryau banga dai-dai ni ba wlh
    Ok yayi nikam yamun sosai zance masa ina sansa, ta6 wlh wannan zubar da ajin badani ba yasin da bazan 'kara kulakiba, meyasa , sbd ma kar ayi kwatance dani ace ni'kawar nice, hhhh dariya kalis tasaka suka tari d'an sahu suka tafi
    Shikam Nauphal kasa nutsuwa yay yana ta kallon su harsuka hau d'an sahu suka tafi sannan yad'auke lulu eyes d'in sa daga kansu
   Zama yay yayi shiru yana nazari, Fahat ne yazo bakin gurin yabe my man, man, man har sau uku amman baisan anayi ba, ta6ashi yay yace ummmm yadai ko wata ta sacemun ruhin d'an kaninane
    Murmushi yay yace haba Allah yakiyaye kawaidai ina tunanin yadda zanji inna kammala degree dina ne shine yasa nake tunani
   Bude masa 'kofar yay yashigo yace brother wai menene gift d'in dazaka ban idan na gama
   Ummmmm hmm ummm zan maka aur...............


Hallmarth ce 💕💖💕
  👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔*
_Story and written by_

*SADIYA •A• UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}



🅿---4⃣7⃣&4⃣8⃣

............... Aure kuma yayah🤔🤔
Yesss😉😉😉yakaji abun zai bada citta koh, nidai ban girmaba wlh
    Hhhhh😀 saika girma tukunna, toh idan kagirman nayi maka auren
     Haka sukaita hirarsu, amman Nauphal yakasa man tawa  da kyakykyawar fuskarta sam da murmushinta


      Hapsatu ce tale'ko tana kiran Nauphal dan ya'karasa sauran aikin zata futa ta amso sa'ko


   Shiga gidan yay ita kuma ta futo suna mata adawo lpy, tunda tashiga d'an sahu gabanta yake fad'uwa amman takasa gane dalilin hakan ko kad'an, addu'a dai take dazarar taji hakan



    Wani gurin majalisa ta isa inda baban bintu yake 'karasawa tai suka gaisa yabata takaddun taduba sosai sannan tami'ka masa jakar hannunta ya amsa tafiya sukai ita kuma takoma gida


Ahanyarta ta tafiyane tahango wasu manyan motoci nagani na fad'a masu shegen kyau

     Kallonsu take gabanta yana tsananta fad'uwa kamar daga sama tajiyo muryarsa wanda bazata ta6a mantawa da itaba, yana fad'in arage glass d'in bayasan iya iskan AC kad'ay


Waigowa tai tagansa yana murmushi duk da girma yabayyana sosai atare dashi amman hakan bazai hana ta gane saba

   Kwala masa kira tafarayi BAFFA...... BAFFAAA...... BAFFFAA.......
   Kallon mai nafef d'in tayi tace dan Allah kabi bayan wad'an nan motoci

   Naaaaameeeee hjy kina da hankali ma kuwa, ai wad'an nan security d'in nasa kashemu zasuyi wlh


Kinsan wanene ma kuwa
   Nidai kabisu dan Allah

Ai wlh saidai kisauka dan bazan saida rayuwata ba
   Wad'an nan security masu yawan tsiya ai in muka bisu ko gawarmu kare ma bazai shin shina taba bare kuma mutum

      To wai waye shiii
Auke baki sani bama kikesan in bishi
  Gaskiya kina ruwa kusa da kada🤔🤔🤔

   To wannan duk cikar Nigeria da batsewarta babu mai kud'in sa ko kad'an
  Kuka hapsatu tasaka
   Yace kinga kiyi hkr nan garin da'anga kina kuka za'a kamani, ace sato ki nai
    Wai waye ma naki tukunna
Shiru tai masa batace komai ba har suka isa inda zata sauka, kud'in sa tabiya sannan ta koma gida


   Duk jikinta babu 'kwari tana zuwa ta tarar da Nauphal yana duba wasu littattafan sa sallama tai tashige d'aki tacigaba da kukan ta

   Nauphal hankalinsane yatashi, yabi bayanta yana kiran sunan ta
    Ummerh..... Ummerh....... Ummerh... Lpy meya fatu, keda wa, waya ta6aki

  Fahat ne yashigo dan shima yana mata magana dan yaga idanta yayi ja, amman yaga bata kulaba tayi Gida kawai, shine yarufe shagon yabi bayanta


   Haka suka rufar mata da tambaya amman taki basu amsa suma kukan suka saka mata sannan tayi shiru tafara lallashinsu tana basu hkr

  Nauphal ne yace ummerh waito me aka mikine, Nauphal baka sanshiba BAFFANA NAGANI
    ummerh baffan ki kuma waye, kakana Wanda yahaifi ummerh taaa
    Ummerh a ina kika gansa

Basu labari tai tsap sunji haushin dabasu bita ba dasai sungansa

   Fahat ne yayi ta lallami, yacewa hapsatu Ummerh kinsan ana babban taro, kibari zamu 'kara ganinsa tunda sai anyi kwana uku ana taron


Da'kar yashawo kanta sannan ta tashi aka cigaba da safga
   Wasa² har an kammala taro har tsawon kwana 3 amman Hapsatu bata 'kara ganin saba
    Haka taha'kura ta fawwalawa Allah komai tana cigaba da addu'a Allah yabayyana mata shi
    Tanasan taje tayiwa Abbansu magana akan tarihinta amman tanajin tsoro sosai, dan karya yi mata korar kare


   Sosai suka samu ribar dabasu ta6a samu ba tunda suke arayuwarsu dan sunyi ciniki kamar ba gobe


Yaune yakama Nauphal zai kammala hutunsa sosai yakejin ba'kin cikin rabuwa da family'n d'insa Da kuma kewarsu tun kafin yatafi gasoyayyar Nusy datadamesa amman hakadai yake daurewa sbd bayasan raini sam atsarin rayuwarsa


   Haka yashirya suka kaisa har tasha yahau mota yatafi, dannewa kawai yake amman saida yay kukan zuci

    Haka suka koma suma suna ta kewarsa, Fahat ma makaranta yatafi abunsa, dan Hapsatu hostel takama masa sbd karatun taga in ana mkrt yafi, agida yana shan wahala ga makaranta ga aikin dayake tayata, gakuma zaman shago, dan haka kawai saita kama masa hostel yana kwana acan sbd ta sau 'ka'ka masa

      Sai gidan yarage daga  Hapsatu Sai masu tayata aiki, da kuma Bintu datake zaman shagon


    Ribar dasuka tara, ta'kara had'awa taje wajen baban Bintu ya'kara mata hanya tasiya wani filin, kuma duk kansu d'aya akusa da juna amman manyane sosai tasiya


    Yau da wani irin sanyi aka tashi wanda, da'kar Hapsatu takeyin aiki, tana kammalawa, tafara gyaran gida, buga 'kofa tafarajin anayi, kamar kartaje sai kuma taje


Wani tsoho tagani yanata karkarwar sanyi, da'kara yake iya bud'e idan sama, atsorace tagansa tace da'karfi babaaaaaa malammmmm idiiiii luuuu....................... ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻



Keep waiting my fan's🤔🤔🤗🤗🤗
Hallmarth ce💕💖💕

[04/02, 7:59 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔*
_Story and written by_

*SADIYA •A• UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}


   🅿---4⃣9⃣&5⃣0⃣

..................luuuu tai tafad'i 'kasa wad'anda suke tayata aiki ne sukayo kanta dan suma suna gaf dashigowa

    Rabi'atu...... Rabi'atu...... Tashi karki mutu kinji tashi dan Allah,kuka yasaka yana jijjigata

Dasauri suka  taimaka mata sukai suka shiga da ita gida, ruwa suka yayyafa mata sannan tadawo hayyacinta


   Ganinsatai akusa da ita tace Babaaaaaa malammmmm idiiiii kaine dagaske bagizauba

   Nine mana rabi'atu kidaina kuka karki 'kara shiga wani halin kinji
   Toh baba, saida tad'an huta sannan ta tashi tayi masa masauki ad'akin zaune tunda akwai katifa da ledar tsakar d'aki aciki, ban d'akin tsakar gida kuma akusa da d'akin yake



     Sawa tai aka kai masa ruwan Wanka da kayan Nauphal da man shafawa
   Aikam wankan yashiga yayi sannan yashirya saigashi yayi kyau abunsa
     Abunci ta ajiye masa mai rai da lpy sannan takoma bakin aikin ta

   Koda ya kammala ce masa tai Baba ka kwanta kad'an huta kafun zuwa anjima mayi magana

   Haka ya amsata yakwanta dan yana bu'katar hutun sosai, rabonda yasamu Wannan gatan tun suna tare da BAFFA aminin sa kuma d'an uwansa tunna 'kuruciya


    ************
A6angaren Fauziyya kuwa tadaku kamar babu gobe dan Jazuli yalakad'eta kamar babu gobe
    Da'kar take iya ganin gabanta haka ta tashi takuma cigaba da aikin gidan


Tun daga ranar yakafa doka akan duk wanda ya'kara gani a "yan uwanta to abakin aurenta

     Haka tacigaba da rayuwa cikinta sai girma yake 'karawa, abun na mata ciwo, inda gari yad'auka, ai da cikin shege tayi aure dama



    Yau tun safe takejin ciwon mara sosai taketa daurewa dai amman abun babu, sauki
   Gayawa Jazuli tai yayi mata banza yacigaba da al'amuransa daga 'karshema gidan yabari hankalinsa akwance

   "Yar tsitsinta tad'auko takira Anas tagaya masa bata da lpy sosai kuma gashi tanata zubar da farin ruwa mai yawa

  Direct gida yaje yad'auko mama Balaraba, yawuce tamajalissar su Jazuli yace yazo sutafi

Dayake yasan halin Anas bayasan raini shine kawai yasashi yabisu

   Gida sukaje suka d'aukota acikin d'an sahun sa, sukai asibiti da ita
    Da'kar suka amsheta danta galabaita sosai, haka suka kwana amman Fauziyya bata haihuba
    Na'kuda takeyi kamar me, amman kuma saita taso kamar zata haihu saita Lafa


   Wasa² saida Fauziyya tayi kwana uku tana ibada, amman bata haihuba, daga 'karshe ma doctor faruq yace amata CS kawai
    Anfara had'a kud'in aikin ne, ciwon ya'kara tashi, doctor yace bari su shiga da ita d'akin daza'ai mata aikin


Shi kansa Jazuli saida yatausaya mata, yatafi had'o yan canjinsa dan ahad'a abiya kud'in kayan aikin


Suna ciki ana 'ko'karin fara had'a kayan aiki akad'auke wuta
   Haka doctor yafuto yace musu indai ba'a kawo wuta ba nan da awa d'aya ba to gaskiya zaiyi wahala tarayu


Sosai mama Balaraba tasaka kuka tana neman dan Allah yatai maka mata yaceci ran "yarta

     Ana cikin wannan halin wata nurse tafuto da gudu tace da doctor faruq Sir kazo Dasauri
  Juyawa yay yashiga cikin d'akin dasauri samu sukai har kan yaron yafara futowa

   Da'kar suka tai maka mata ta'karasa haihuwa amman saida akai mata 'kari, wani kanne ya"kara danno kai, tai maka mata sukai nan ma ta haifosa

   Namiji da mace ta haifa, inda Allah yatai maketa kamar su d'aya da Jazuli sakk

   Ita kuwa atake alokacin tabar numfashi, dan duk jikinta yasaki saboda tsabar wahalar datasha


       'Ko'karin ceto rayuwarta suka fara dan ta wahala sosai, sukuma yaran aka fara gyara su, gaya musu akai ta haihu "yan biyu mace da namiji


   Sosai gaban Mama Balaraba yafad'i danji tai dama yaran sun mutu, dan bala'i bama d'ayaba biyu
   Kai nikam naga takaina ni Balaraba, kuka tasaka tanata yi tana 'karawa, babu mai lallashi


   Dan Anas ana fad'a masa yajuya yatafi dan siyo musu kayan da za'asa musu, yayi musu siyayya sosai yakawo aka shirya yaran cikin kayan sanyi green ☘ da white sunyi kyau acikin kayan


Ita kuma yasaka Jazuli agaba sukaje aka d'auko mata kayan sawa, dan ko takan Balaraba Bai biba bare tasaran zai bata hakuri, dan gani yake abunda suke aikatawane yake dawo musu


Saida Hapsatu ta kwashi tsawon sati 5 kafun ta warware sosai jikinta yayi kyau tayi lumi mi abunta sbd Anas yana bata kulawa ita da yaranta

   Amman tun daga wannan lokacin data haihu har kawo yanzu basa magana da Mama Balaraba dan ita tsoronsa takeji sbd yadda yake had'erai inya shigo


Shima Jazuli sosai yake kulawa da iyalansa dan yanasan yaran sosai

    Yau Fauziyya tayi sati na 6 a asibiti amman dinkin nata bai warkeba dan haka doctor faruq yace abari ta 'kara sati biyu in sha Allah zai warke



Haka kuwa akai kafun sati biyun ma yawarke, aikuwa ana sallamar su suka wuce gidan su Mama Balaraba acan tayi wanka tayi dukkan jegonta inda jarabar "yan unguwa ma ta ishe su, kullum ba'a rasa mai zuwa ya'kare musu zagi


   Saida Anas yatashi tsaye sannan suka samu sukuni, kusan kullum cikin kuka Balaraba take na wannan haihuwar da Fauziyya tai


    Yau tun wurwuri tagama komai aka yankawa yaran hakika akan barsu da sunan su hasan da usaina
    Ad'an dafa abunci aka raba, sunyi taro amman ba sosai ba, dan komai rabun abun ma Anas ne yayi matashi




Kullum baya gajiyawa dayi musu hidima, in kagansa kamar bashi da damuwa

     Amman a'kasan ransa kuma tunanin inda zaiga hapsatune da 'kaninta kullum yake damunsa dan duk inda zaije cigiya yaje, har gidan redio da TV duk yake amman shiru, yana damuwa sosai dan duk Jazuli yabasa labarin komai daya faru


   Bayan an kammala suna ba'a watse ba saida aka kusa dambe da'kar aka shawo kan abun aka samu sauki

  Alhaji kuwa baban su Hapsatu yadamu sosai da wannan d'ibar albarkar da ake masa agidan sa kullum


   Hakadai yake hakuri dan babu yadda zaiyi


Yau tun safe Balaraba ke shiri ita da Fauziyya suka goya yaran suka kama hanyar gidan Boka



Babu 6ata lokaci suka isa wannan 'kasurgumun jejin suna isa cikin bukkarsa

   Yafara she'ka Dariya yana shewa harda tafawa hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh  😁😁😀😀😀😂😂😂😂😂

   Kun 'Kara so alokacin daya dace sosai ma kuwa, kuzauna kuzauna
   Zama sukai nan yafara labarta musu cewa, ai anan Jazuli yazo ya amshi maganin mallaka wanda shida Fauziyya mutu ka raba, kuma yace kar'abashi mai la'kanin dazai karye


   Kunyi sakaci dan bazata iya auren likitan nanba kuda nace muku tana haihuwa kuzo ko kuma ke kizo


Ai mlm babu natsuwane dan batai haihuwar kwanciyar hankali ba

     Mun sani ai dan mu muka rin'ka jaa mata rai dankarta haihu da wuri sbd tasa6a mana umarnin mu


  Toh yanzu boka menene abunyi
Hhhhh😀 ai abunyi d'ayane saidai ahaukata Jazuli saitayi wani auren amman idan ba haka ba tofa wannan auren bazai mutuba


Amman meyasa kai masa wannan aiki
    Hhhhh😀 Hhhhh😀 Hhhhh😀 kud'ifa zai bamu da jini tayaya bazamuyi masa aikiba
   Jini kuma?
Ey jinin haihuwarta yakwaso mana wanda kukace yazubar toshiyakawo mana mukuwa mukai aiki mai kyau



Toh gaskiya ahaukatashi sannan kuma akarkato da hankalin likitan nan yadawo kan Fauziyya sbd ayi ai auren nan muhuta

Zanyi aiki amman saidai kubari aure saita yaye yaran nan nanda wata 14  ai ayi aure


Aa mudai ayi auren in yaso komai ayishi daga baya
   To zanyi amman kuma saikinje kin kwanta da d'an tsito
    Dan me?
Abunda kunnen ki yajiye miki, inba hakaba kuma, kutashi kuban guru
   Zanyi ranka yadad'e duk yadda kace haka za'ai babu matsala


Toh tashi kishiga yana jiranki, saiku tafi daga baya, tashi tai tashiga d'ayar rumfar, tana ta sauri sbd ayi awuce gurin


   Dagataje sai tagansa yana zaune haihuwar uwarsa ba komai acikin jikin sa yana jiranta
   Tunowa tai dawahalar datasha rannan babu yadda ta iya haka ta 'karasa dan tasan idan tajuya sai yayi sau uku

    Tana zuwa tacire nata kayan, babu wani wasa ko wani abu, kawai far mata yay aikuwa ihuuu kawai kake jiyowa



  Fauziyya ce ta mi'ke zata shiga d'akin, Boka yatareta yace kina shiga kema saina kwanta dake kuma shima haka, dan bayasan yana aiki ashiga wannan yasa6awa dokar mu


Gaba tai abun....................... ✍🏻✍🏻✍🏻



Keep waiting my fan's 🤗🤗🤔🤔
Hallmarth ce💕💖💕

  
[04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 👑👑👑👑👑👑👑👑👑
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔*
_Story and written by_

*SADIYA •A• UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}




🅿---5⃣1⃣&5⃣2⃣


............... Gaba tai abunta harta kusa 'karasawa kuma saita fasa tajuyo,  sbd tasan mahaifiyarta jarababbiya ce amman kuma tana kuka dawa wannan d'an tsiton to ina kuma gani da bankaita jaraba ba

   Dawowa tai tazauna, Boka yafara dariyar mugunta Hhhhh😀 Hhhhh😀 Hhhhh😀 Ashe kinajin tsoro shegiya dakin je ai dayanzu munyi maganinki babu 6ata lokaci


Hhhhh😀 Hhhhh😀 Hhhhh😀 Hhhhh😀 dariyar ce tacika gurin sosai har tana yi mata amsa kuwa akunnen ta, haka ta hakura amman badan tana soba saidan babu yadda zatai tana jiyo ihun mahaifiyarta


   Saida Balaraba takwashi kusan awa 1h sannan yakammala, saida ta huta sannan da'kar takamo hanya tana jan 'Kafa ta futo, tanata sharar kwallah



Magun gunan su aka had'a musu sannan suka kama hanya suka tafi gida da'kar suka isa gidan


   Babu 6ata lokaci suka fara aikin da nakan dutse yasakasu, sunyi komai kamar yadda yace sannan suka koma suka sanar dashi, yace toh su jira nanda kwana 7 komai zaiyi yadda sukeso
    Sannan yabasu wani magani yace suyiwa likitan farfesu susaka masa aciki, idan yazo, yanaci shikenan zance ya'kare dan kuwa baza'ai wata ba zai turo


Haka kuwa akai dan bayan kwana 7 komai yayi inda Jazuli yafara hauka harda bin mutane da bololi


Nanfa mama Balaraba tayi tsalle ta dire akan saiya saketa, aikam da dance masa kasaki Fauziyya saiduka baya bada amsa saidai duka kawai


    Haka dai tarinka shiga tana futa har aka raba auren nan, ba'adad'e da raba aurenba dan watanta biyu aikam sai ga doctor faruq nan

   Yasamu Alhaji yace yanasan auren "yarsa Fauziyya, yakuma gaya masa bayasan ad'auki lokaci
    Amsa masa yay ace amman yabari ta gama iddah kafun nan sai ayi maganar auren


  Ahaka suka rabu inda aka yi masa farfesu kamar yadda Boka nakan dutse yalabarta musu


Yaci kuwa sosai, aikam sunji dad'i ba kad'an ba
     dan suna ganin burin su yakusa cika akan sa

    Bayan wata d'aya da tafiyar doctor yadawo su Mm Balaraba ma anzata aiki baiyiba


     Saigashi da manyan ledoji da kud'i yakawowa Fauziyya, itakam sai yau'ki take tana wani rangwad'a alamar ta isa d'in nan
     Saida tagama yau'kin sannan taje, doctor faruq kuwa kamar zai haukace sanda yaganta haka yayta zuba yana yaba kyan ta(wanda nikam dana ganta kamar nayi kuka dan rashin had'uwa😙😙)

     Wasa² soyayya mai 'karfice tashiga tsakaninsu inda take samun kud'i yadda take so tayi mai ta'kara fari, gashi tasha, shaka fashe tayi wata irin 'kiba sosai

    Anas kuwa tun abun nabashi mamaki har yadaina, yazuba musu ido kawai dan dai yasan wannan abun bana Allah bane
   Babu abun da yake damunsa kamar rashin jin labarin Hapsatu dabaiyiba


     Yau tun safe su Mm Balaraba ke shiri ita da Fauziyya dan yaune za'a saka ranar auren su akuma kawo lefe dakud'in nagani inaso


  Sai wajen 12:09pm sannan suka iso Alhaji da kakah hajja sai gyaran gida ake anata gwalli za'a "yarsu zata auri mai kud'i
    Shidai Alhaji sbd kar kaka hajja tace zata tsine masa yasa yakeyin wasu abubuwan amman badan ransa yanasoba
    Kuma abunda yafi d'aga masa hankalinsa shine yanasan yatambayi ina su Hapsatu suke amman saiya kasa kwata²


    Koda family 'n su faruq sukazo sun raina wannan gidan da faruq yaketa rawar 'kafa akansu
    Saida sukaga amaryar ma sannan sukai dana sanin zuwan dasukai, dan waye baisan family d'insuba wajen bin bokaye da malamai har la'kabi ake musu da "ya"yan Allah bani sbd dukkan su halinsu d'aya



   Hakadai sukai duk abunda yakamata inda suka kawo lefe akwati 8 da bakko guda 2 anzuba kaya sosai
      Nan aka saka sati biyu dan haka faruq yace kuma yace kar akawota da komai yasaka komai acikin gidan sa



In kukaga Fauziyya abun saiya baku mamaki sosai dan babu kunya tazo tanata dudduba kayan tunkan ba'kin sutafi



Haka aka tafi da ita abaki anata zaginsu
    Itakam ko ajikinta saima shewa take da bud'a



   yarone yayi sallama, aka amsa yace kawu Anas yana nan
   Akace ey
Yace ana sallama dashi awaje
   Toh, kace waye
Futa yay, bai dad'eba yadawo
   Ance wai ansamu labarin wanda yagansu zasu hau mota subar gari
    Suwa fa inji Mm Balaraba
Anas ne yafuto dasauri yace A'a wannan zance nane
   Muje ko tasa yaron yay suka futa daga gidan ashirin yabashi yace ngd kaji yaron kirki

  Amsa yay yana ta murna yace angode kawu

    Yana futa yaga wani mutum abakin kofa dasauri ya'karasa suka gaisa

    Mutumun ne yace yawwa wannan yarinyar daka bamu cigiya anganta amman kuma wanda yaganta yace ansaidasune gawasu mutane
    Masu siyan yara a garin Abujah

Mekace wannan yarinyar fa tacikin wayata
   Tabbas ita nake nufi dan har hotunan su yanunamun suna cikin adai-daita za'asiyar dasu kuma dama mai adai-daitar Saida yara suke shida mahaifiyar sa, suna zaune ne atashar kaduna, kuma sunyi hatsari sun mutu gaba d'aya
   Shine nazo in gaya maka maka dan kar ka cigaba

Please Login or Register in order to submit comment