Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta auri jazuli sai akwantar da cikin idan ankwana biyu sai atashi cikin
   Balaraba tagirgiza dajin abunda nakan tsauni yace ta'auri jazuli kuma nakan tsauni nida nakeson ayi wacce za'ai Fauziyya ta auri doctor faruq din nan
     Hhhh hhhh aikinbar gini tunran zane abunda yafi sauki kenan amman indai kinasan ta auri wannan likitan saidai kikawo ba'kin alade da mage da bunshuru

   Amman da sharad'i cewa saita auri jazuli ta haihu tukunna idan ba hakaba wannan aikin dazamuyi bazai yuyu ba
    Toh zanyi kamar yadda kace, haka suka taho duk ba'kin ciki yayi mata yawa, wai Fauziyya ta auri jazuli wannan d'an tashar da ba'asan asalinsaba, dan shaye shaye kuma
    Wannan wace irin 'Kaddarah😭 ce
Tun kafun su'karaso sukaje shagon su jazuli amman baya nan haka suka dawo badan tasoba
   Tabarwa Anas sallahun inya dawo agaya mata, ace tana neman sa
     Sai wajen karfi,  10:00pm sannan suka shigo shida jazuli, sallama sukai anan kofar daki suka tarar da su azaune
   Kallon Anas tai tace, toh ngd maza jeka , Toh mamah sai anjima
    Futa yay abunsa kallon jazuli tai tace zauna mana tsinanne, zama jazuli yay duk ya tsorata dan yasan Fauziyya tarugada ta tona masa asiri
   Zama yay ahankali kallonsa tai tace yawwa magana nakeson yi dakai
  Too...... Too........ Toooooooottttt...... tooo ina jinnnnnki mamah
   Maman uwaraka, inasan ka'auri Fauziyya sannan asatin nan nakeson ad'aura aure ku
    Aure kuma
Tabbas aurenta zakai dan bazaka zubarmun da mutunciba katozartani agaban jama'a
    Wulakanci kamar yaya kuma
Ey kaje kai mata ciki shegen gora sannan har kake tamabayar wani abu
     Ai mamah ita tazo tace in rage mata zafi bani nace tazo ba
   Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un yanzu abunda kika aikata kenan Fauziyya kinsanda kinasan hakan ai saiki gayamun in samar miki miji kiyi aure, amman saiki zubarmun da mutunci na
   Kiyi hkr mamah
Hkr'n uwarki
  Tashi kiban guri
Kai kuma ina zaka sakamun "yata dan wannan aure yazama dole sai anyishi shine rufun asirina danaku
   Toh nidai bani da inda zan ajiyeta sannan kuma bani da kud'i amman idan kece zaki kama mana haya to sai ayi wannan auren idan kuma ba haka ba saidai ahakura, dan ni nan ma gaba zanci dankar asirina yatonu
   Haba.... Habaaa..... Aibaza'ai hakaba jazuli kabar zancen tafiya
   Ninan zan nema muku haya koda d'aki d'ayane da band'aki da kicin
      Aaaatooooo danni uwatace zata gindayamun doka kawai inbi
    Toh yanzudai ka shirya asatin nan za'ayi auren nan
    Toh ni nayi nan, Tashi yay yafuta abunsa
    Mamakine yakamata tana tunanin yadda zatai haka taje tafara buga nan buga can tana neman yadda zata tara kud'in dazata kama musu haya
   


Yau yakama ranar asabar and'aura auren jazuli da Fauziyya wanda hakan yabawa su Anas da Baban su Hapsatu mamaki dan yashiga rud'ani dajin wannan auren
    Dan duk cikin su babu wanda yasan da auren saidai d'aurin aure
     Gida Anas yadawo afusace yashiga d'akin mamah Balaraba, ganin ta yay azaune tana shirya Fauziyya wadda duk ta gala baita sbd maganin datakesha na kwantar da ciki ta rame tayi ba'ki sosai
   Kallon su yay yace abunda aka fad'a gaskiyane kenan
   Mm Balaraba ce tace kamar yadda, me aka fad'a?
   D'aurin auren Fauziyya da Jazuli amasallaci
    Ey kaji dai2 kam,  menene kuma?
Kobakasan auren ne sai inji
  Aa amman dai mamah a rasa kowa za'a aurawa Fauziyya sai jazuli
   Ey mana shi tagani kuma shi take so ko zaka hana ne eyeeeee sai inji
   Yarinya tafutar da wanda take so amman kai zakace ga zance ga magana
    Allah yabaki hkr, futa yay zuciyarsa tana masa 'kuna ganin 'kannen sa yay suma duk rai a6ace suna tsaye abakin 'kofa cirko2
    Matsawa sukai shikuwa yayi gaba abunsa

   Alhajima koda yatambayeta shima d'iban albarkar tai masa haka yahakura yafuta abunsa

Kamar dai yadda yakamata haka akakai Fauziyya d'akinta kamar ko wacce mace
    Anyi mata kaya na dai talakawa dan daga gado sai kwaba da kwanon cin abunci na silba guda biyu sai copi da tukunya tuwo da miya
     Sai wajen 1:47 sannan jazuli yashiga cikin gidan abug......................




Sadiya A Umar
Ummuh fateemah
Hallmarth ce 💕💖💕


Love you all my fan's 👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧👩‍❤️‍💋‍👩💑👨‍👨‍👧‍👦💃💃💃💃💃💃💃💃💃💖💕💖
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨
✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨

💞NAH💞
SADIYA ABDULLAHI UMAR
💞UMMUH FATEEMAH💞



🅿---4⃣1⃣&4⃣2⃣


Abuge yashigo gidan yana zuwa yazube abakin gado yana tan gad'i
   Amai yarinka kwarawa abunsa yana gamawa yayi bacci agefe
   Ita kuwa data rufe kanta haka ta sakko jin wannan amai dayake kwarawa, haka ta tattare gurin ta gyara komai sannan ta kwanta tana dana sanin wannan aure
    Koda gari ya waye hakan ce ta kasance dan bai tashiba sai wajen 12:00pm sannan yayi wanka yaci abunci yafuta


Sai wajen 3:00pm sannan yadawo lokacin tayi bacci ta Tashi yafi sau akirga saitaga bai dawoba
    Lokacin daya shigo dai kamar jiya haka yashigo cikin d'akin yayi amai ta gyara ya kwanta yayi bacci da safe yayi gaba abunsa

   Kamar wasa haka jazuli yake shigowa gidan har tsawon wata d'aya bata ta6a tanka masa
   Ranar tsautsayi tace waikai meka maidani ne kamar wata 'yar aikin ka tunda nazo gidan nan saidai inyi maka wahala wannan wace irin rayuwace
    Ni kike gayawa haka eyeee
Anfad'a makan ai nayi hakuri wlh bazan iyaba
   Wata waya yad'auko mai kaurin tsiya yafara lafta mata ajikin ta saida yay mata rud'u rud'u da jikin ta tun tana iya tashi harta kasa tashi
    Saida yaga tajigata sannan yafuta yabarta agurin
   Kota kanta bai biba yayi waje abunsa yana fad'in gobe ma ki 'kara mun irin wannan maganar
    Futa yay abunsa hankali kwance
Da'kar ta iya tashi daga gurin tad'aura ruwan d'umi tayi wanka ta gargasa jikinta tad'aura girki haka da rarrafe tayi girkin ta gama sannan ta 'kara gasa jikinta sannan ta d'an kwanta wayarta tad'auka takira mamah Balaraba ta sanar mata da komai
   Aikuwa Balaraba amugun razane tace dume?
   Duka wlh mamah
Lalle kahaifu jazuli ina nan zuwa d'auka miki fansa wlh bai daki banzaba gani nan zuwa
     shiryawa tai tafuto, suka kama hanya ita da 'kannen Anas suka tafi
   Ajigace suka tarar da ita har zazza6i yafara kamata
    Chemist suka kaita anan aka dudduba aka bata magun guna sanan suka dawo
     Har suka gama zamansu Jazuli bai dawo ba ran Balaraba ya6aci matu'ka amman babu yadda zasuyi haka ta koma gida dan ranta a6ace yake tama rasa yaya zatai
   Washe garima da sassafe taje gidan amman baya nan haka ta wuni amman ko d'uriyar sa babu
     Tajera kusan kwana uku tana haka amman basu ta6a had'uwaba
   Yau kam da masifa yatashi akan bata wanke masa kayan saba sbd jiya da zazza6i ta kwana
    Amman ko duba halin da take cikinsa bai ba dukan ta yafarayi kamar an aykoshi, suna cikin haka Balaraba tashigo gidan rai 6ace tayi kansa ta fuzge bulalar wayar wutar tai ta zabga masa  tasa 'kannen Anas suka fara dukan sa da ita
    Aikuwa Jazuli yace indai suka 'kara dukan sa to sai yasaketa yanzunnan, babu arziki suka daina dukan shi, tashi yay yace, jeki gida nasakeki saki d'aya
    Dasauri Balaraba da Fauziyya sukayo kansa dansu bashi hakuri amman ina, tum kan su'karaso yay fucewarsa yaya wani yad'aukesa amashin sukai gaba
    Har dare suna jiransa amman bai dawoba
    Bashi yadawo ba sai wajen 1:47 sannan yashigo gidan abuge kamar kullum
    Kanta yayo yafara surutai anan yayi amansa ta tashi ta gyara komai sannan sannan ta gyara masa kwanciya itama ta kwanta mama Balaraba kam tana cikin Kiching anan ta kwana da gari yawaye Jazuli yashiga kicking zai ibi ruwa yaga mutum akwance aikuwa ajiye butar yay ya'karasa yafara shafa mata fuska yana fad'in dama na dad'e inasan in sha wannan ro...................


*** *** ***
Wajen su Hapsatu kuwa amaryar daddy tacigaba da masifa tana fad'in
    Nace meya kawoku cikin gidana ajiya kuka ban waya baku izinin shiga
   Hafsatu ce ta kalleta sai tace hjy mun zone mutai makeka
    Muna bada maganin mallaka ne dana farin jini, dana kasuwa
   Kai kowanne irin magani muna bayar wa har na korar kishiya
    Murmushi tafarayi tace kai masha Allah bari inzo kuwa dan kunzo a lokacin daya dace, dama ina neman magani sosai,  "da har ina cewa zanje gurin mlm mai magana d'aya ashe basai najeba ga sau'ki nan yazo"
    Haule....  Haule.... Haule...... Kina inane, Na'am gani nan hjy
   Amman kinajina dan wula 'kanci kikai shiru, bakiga ba'ki bane
   Nagansu hjy nakawo musu ruwa da lemon, okkkkkk haka kikewa ba'ki dama ko bazaki kawo musu abunciba da nama da snacks ba, sai ruwa da lemo, sai kace uban kine yake siyan kayan, a'a hjy ayi hkr bari in kawo, Banza shaa shaa shaa kawai mazakije ki kawo musu
    Tashi Haule tai takawo musu komai da aka lissafa mata
   'Kawayen tane suka dawo sukace, ai ba'ayi bamuba muma bari mudawo mu amshi na mallaka,Heeeee here heeee tafawa sukai suna shewa atare suka shigo zama sukai suma
   Amaryar daddy tace kuci mana hjy
Murmushi Hapsatu tai tace, hmmm mun 'koshi ai, bari mubaku maganin ku kawai mutafi dan akwai inda zamu da yawa, kema watace ma da muka bata magani alayin baya shine tace muzo kema tasan zaki bu'kata, ayyaaa aikam nagode
   Toh yanzu hjy nawa kuke bada na mallakar nan
   Toh yadan ganta da yanayin abunda zaku biya akwai na mallakar miji har dangin sa, danashi shikadai, dakuma na ra'kumi da akala dana bita zayy2
    Aaaaaa nikam duka za'a had'amun, toh nawane amman ai za'amun sau'ki koh tunda dayawa zan siya
   Toh hakane kibada dubu d'ari 5 sai in baki, toh shikenan bari in d'auko ahad'amun kafun in futo
   'Dadd'aura maganin Hapsatu ita da Fahat suka fara sannan suka ajiye mata aguri d'aya
   Ta amshi nakasuwama dana farin jini, shikuma dubu d'ari 2
   Suma 'kawayenta sun amshi magani sosai dan sunyi musu cinikin dubu d'ari 7, sosai suke ta musu godeeya itako amaryar daddy harda basu atamfofi guda 6 da shadda guda 4 tace mata, keda mijinki hjy
   Toh shikenan ngd sosai hjy, babu komai gashi bakuci komai ba bari ajuye muku snacks din da naman soyayye koh hjy, irin wannan tai mako da kukamun aikamata yay nima kud'anci wani abun ko kad'anne
     Toh shikenan, tsaya wa sukai aka juye musu shi , harda 'karin wani acikin babbar leda mai ba'ki da yellow aka sako musu,  amsa sukai suna godeeya
    Har lokacin zuciyar Hapsatu data Fahat bata daina bugawa ba


   Saida suka ga sun bar gidan sun shiga adai-daita sannan suka samu relief 😅 acikin ransu
    Direct tasha suka nufa dan su koma gida komai dare, Allah kuwa yabasu sa'a suna zuwa suka samu mota saura mutum 4 shiga sukai, basu dad'eba suka cika suka tafi abunsa, ahanya ne aka kawo tallar awara tasiya wa Fahat yace Ummerh a'a nikam Allah bazan iya cin komai ba sai munje gida nasan yanzu Nauphal yagama komai
    Toh shikenan nayi fushi dakai, A'a Ummerh nah kiyi hkr please 🙏
    No babu wani hkr haka zakai ta zama da yunwa bayan bakaci komai ba, Toh Ummerh kema fa bakici komai ba, aini bana iya cin abunci in muna tafiya yana damuna sosai
     Hmm Ummerh nah kenan, toh muci kad'an koh Ummerh
   Murmushi itama tai tasaka hannu tad'auki guda d'aya taci shima d'ayar yad'auka yafara ci basuci dayawaba suka 'koshi dan dama basan cin abunci sukeba su duka duk kanwar jaaa ce
    Bacci ne yafara d'aukar Fahat yad'an jingina da jikin ta yafara baccin gyara masa kwanciyar tai yaci gaba da d'aurin kayan su agaban ta da kuma tulin kud'in su wanda jama'a sukai tunanin tsummokine kawai, amman basusan dawar garin ba
   

Sai dare suka isa sbd motar su tad'an samu matsala, har lokacin kuwa Nauphal baiyi bacciba yana nan azaune atsakar gida yana jiran su
     'Dan mukulli yasa yabude 'kofar suka shiga da sallama abakinsu, Aikuwa da gudu yayo kansu yana oyoyo oyoyo oyoyo gasu yayah da Ummerh
      Rungumesa sukai suka shiga gida,shiga phalon sukai, Hapsatu tace babu wuta kenan , yace eyy Ummerh basu dad'e da d'auke taba, amman ina tunanin bada dad'ewaba zasu dawo da ita, Toh Allah yasa, kulle gidan yaje yayi suka ciccire wannan kayan dasuka saka sukai make up irin na fulani
    Yawwa dama nadafa muku ruwan wanka bari in had'awa yayah aban d'akin, d'aki, Ummerh kuma ana waje
   Toh maza d'an kirki
Tashi yay yahad'a musu ruwan sannan yadawo yahad'a kayan da suka cire acikin boket yazuba ruwa da omo yamaidasu gefe shinfud'a babbar sallaya yayi sannan yad'auko yakan abunci yakawo phalon yajere su, dama yagama aikinsa tsap dan har kayan sanyin dasukeyi na lemo duk yayi yazuba acikin freezer d'insu yakulle
     Zama yay yana shirin d'auko ruwa yasa aka kawo nefa, lokacin kuma suma suka shigo duk sun saka kayan bacci,  saida sukaci abunci suka 'koshi suka sha ruwa sannan yad'auko boket d'in dasuke had'a kwanukan wanke wanke yazubasu ya rufe Kiching yakaisu yakulle sannan yadawo, sannun kaji Nauphal yau kasha hidima, Murmushi yay yace yayah aikun fini shan wahala


Wai plan d'in mu kuwa yayi, wlh yayi aiki sosai ma kuwa, kasan tarufta sosai, kwashe yadda sukai komai yay yagaya musu, dariya sukai suka tafa,  Ummerh yanaga kinyi shiru, d'an murmushi Hapsatu tai kana tace, ni abunda yake tadamun hankali kud'in su da muka amsa, kuma da 'karyar da mukai musu akan mu masu bada magani ne
    Haba Ummerh sharesu kawai, kinsan mun aikata hakanne sbd dalili mai 'karfi inba hakaba ai ba zamujeba, kuma Allah yasani inba 'karyar mukai musu ba, Ummerh dayan zu ana labarin wasu, nadai muba,
    Kicire abun nan daga ranki kawai muci gaba da rayuwarmu kamar da, Ummerh sun kin manta irin cutar war da sukai mun, kuma Ummerh inda su suka samu damar da muka samu, naganemu tabbas babu abunda zai hana su kashemu, dan haka ki share kawai Ummerh nah
    Toh Fahat shikenan Allah ya yafe mana baki d'aya, yayi mana jagoranci arayuwarmu
    Amen suka amsa atare, kutashi muje mu kwanta kunga gobe akwai aiki sosai fa gashi inasan mu shiga mkrt ni daku sbd kusamu gurbin karatu
    Toh Ummerh tashi sukai kowa yasake d'aura alwala sukai sallar shafa'i da wuturi sannan kowa yay makwancinsa

     Tun sassafe aketa kwan-kwasa musu 'kofa, kuma antambayi waye yayi shiru yaki magana

     Dariya aka saka hhhh hhhh Hhhhh kubud'e
   Yin kasakai Hapsatu tai dan saida gabanta yafad'i, dan ta.......................





  Hallmarth ce💖💕💖

Keep waiting my fans 💃💃💃💑👩‍❤️‍💋‍👩👨‍👨‍👧‍👦👨‍👩‍👧👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦all💖💕💖

[04/02, 7:59 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨
✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨

💞NAH💞
SADIYA ABDULLAHI UMAR
💞UMMUH FATEEMAH💞



🅿---4⃣3⃣&4⃣4⃣

   Gabanta saida yafad'i dan tagane mai magana amman bata gane d'ayar ba wadda take maganar akusa da itaba

    Bud'ewa tai wazata gani abunda take tunanin dai shine Bintu ce
    Murmushi tai tace keda suwa kuma Bintu, kunji tsoro ko wlh wannan matar ce tun sassafe tahanamu sukuni wai sai tazo tasiyi fankason gidan nan da kunun ayah, wlh wata 'Kawar suce tasiya jiya takai musu yayi dad'i sosai shinefa suke ta tambaya gida2
      Aaaaa ta6 kushigo toh, aini danaji ana dariya ana fad'in bazaku bud'eba saida gabana yafad'i
    A'a bamu muke dariyar ba ai wasune suke dariya zasu wuce mukuma mukace bazaku bud'eba
    Auuu ai nai zaton kune har nad'an ji tsoro, Hhh tsoro ta6 lalle nikam abunda zai sani jin tsoro ba kad'an bane
       Shiga sukai Hapsatu tazubo mata fankason batare data tambayi ko na nawaba
    Tasako mata miya da nama, kunun ayar tad'auka roba uku ta bata
     Mika mata tai tace gashi
Da daddar muryarta mai d'aukar hankali tace nawa, a'a kibarshi kinji, meyasa, sbd nuna soyayyarki agaremu ma ta biya,  bakyasan in dawo ne gobe, a'a inaso mana, toh ki amsa, a'a goben in kin dawo sai in kar6i kud'inki, toh ngd, uhhhhhmmm😍 kigodewa Allah
    ummerh ina kika ajiyemun rigata da aka goge
    Am tana nan ad'akina kusa da kayan sawata, toh ngd juyawa yay yashiga d'akin, Bintu ce tace wa yarinyar da suka shigo, kizo mutafi mana, kin tsaya sai kallon sa kike,uhunnn, ngd Ummerh sai gobe idan nazo, toh Allah yakai mu, Ameen Ummerh, futa sukai atare sunata dariya, motar gidan su tagani abakin 'kofar gidan wazata gani mahaifiyar tace aciki, wani mugun kallo ta watsa mata, ta 'kara 'karewa gidan data futo kallo sannan tai tsaki, shiga tai tacewa Bintu ngd,jan motar akai bayan ta rufe, basu tsaya ako inaba sai, sai abakin mkrntr su wangale musu get akai suka shiga sannan aka sauketa, mai aikin tace tad'auka mata Komai sannan suka tafi, mom d'inta ko Kallon ta bataiba suka ja mota suka tafi
    Zuciyanta tana ta tsinkewa amman dai haka take daurewa, wunin ranar ahaka ta wuni tarasa meke damunta kwata2
    Koda aka tashi driver dayazo d'aukarta ita da mai aikin ta suka tafi, tana shiga gida tai wanka tashirya zuwa Makarantar dare dan tun safe mkrnt su sai yamma ake tashi ita kuma mkrntr dare haddace zasu nayar saisu tafi idan anyi sallar isha'i tunda daga Magriba ne zuwa isha'i
    Bayan tagama shiri sallah tayi sannan ta tafi abunta
  
Lokacin data dawo babu kowa aphalon sai mom d'inta sallama ta tagaidata cikin ladabi da biyayya amman yitai kamar batasan tanayi ba
    'Dauke kanta tai taci gaba da Kallon TV, shiga ciki tai tacanja kaya sannan tafuto danta bawa mom d'in tata hakuri
  Koda tadawo a'kasa kusa da ita tazauna ta'kara gaidata da'kar ta amsa tace mom kiyi hakuri dan Allah, banza tai mata, mom Allah abunci naje siyowa gidan kuma bansan tare zamu tafiba yau, kuma mom nad'ansha wahala kafun nasamu gidan
    Wani Kallon banza ta watsa mata tace, Au abinci, yanzu ke awannan gidan kika shiga siyan abunci salon wata cutar ta kamaki,  dukkan masu dafa abuncin gidan nan basu ishekiba saikin nemomin bala'i, eyeeee, ina duk sbd ke natara wad'an nan ma'aikatan,Mom Allah sun iyayin abinci, tunda nake ban ta6a samun abuncin dayamun dad'iba kamar nasu, Allah nidai mom kibarni in rin'ka siya inba hakaba Wlh bazan 'karacin Komai ba har yunwa ta kasheni
    Dafe 'kirji hyt hamedat tai tace,  Tameee, takasheki fa kikace my dear, kinsan kuwa menene kikace in rabu dake fa, haba, haba wannan ai zancene, taso maza, kamo hannunta tai tazaunar da ita akan kujera sannan tace dena kuka "yar albarka me kikeso ayi miki, Mom nidai inasan abuncin gidan su, shikad'ai kikeso, eyyy mom, cikin Shagwa6a take maganar, toh kibari zanyi mgn da manager na akan yaje gidan suyi magana asamomiki wadda zatana yi miki girkin abunda duk kikeso, dan acan zaki iya kamuwa da wani ciwon in kina zuwa, toh, mom, yawwa maza kije kici abuncinki gashinan nasa anmiki, inkika gama ci saikije ki kwanta, mom dad fa, yana ina banganshiba, bai dawoba yau da wuri sunada wani meeting shiga mutanen Turkish, ok toh mom kigaidamin shi, ok my little baby, mom yanzufa nazama babba am in Js1 a school fa, murmushi tai tace toh my auta nah, dariya sukai suduka sannan ta tafi d'akinta, addu'oin bacci tai sannan ta kwanta dan batajin yunwa sam


** ** **
  A6angaren su Hapsatu kuwa tun da su binta suka futa taji yarinyar ta burgeta amman batasan sunan taba
    Sai wajen 8:30 sannan suka futa agida suka kama hanyar mkrt dazatakai su
   Basu samu wata matsala sosai ba saboda yanada result mai kyau Fahat haka yasamu gurbin karatun sa na masters cikin kwanciyar hankali dan komai anyishi cikin sauki dan ta jajje Makarantar yafi sau akirga tun kafun takaishi
    Shima Nauphal mkrnt takaishi inda anan zaiyi ss 2-3 haka tadawo gida ita kadai tanata sauri, dan tasan yanzu ana nan ana jiranta
    Kamar yadda tai tunanin kuwa hakance tafaru mutane suna nan dan'kam yan siyan abunci damasu siyayya ashago
   Bintuce tazo siya itama tayata tai ta shiga shagon ta sallami wasu ita kuma tashiga gida ta sallami masu siyan abunci haka ta wuni sai wajen 1:00pm sannan Nauphal yadawo shiya amshi bintu ashagon bayan yayi sallah

    Washe gari kuwa tun da wurwuri sukai shirinsu suka tafi sosai sukejin dadin yanayin rayuwar tasu


***     ***     ***
   A6angaren su Mama Balaraba kuwa, lokacin da Jazuli yafara shafa mata fuskar nan lokacin tafarka dan ganin waye, Jazuli tagani atsaye akanta yana abunda yasaba, furgigit tayi, tace kai mahaukaci, matsa mun daga guri kanaji nako, amman ina shibai san ma tanayi ba cigaba yay daga inda yatsaya abunsa koda wasa bai matsaba
      Murmushi yay yace, haka kikace inyiwa Hapsatu toke zanyiwa yanzu janyota yafarayi jikin sa da'karfi, tana kwacewa, ihuuu take, dan yafara yaga mata rigarta, dasauri Fauziyya tashigo kiching d'in, tana ganin abunda yake faruwa tad'auki muciya ta rafka masa ahannunsa da dukkan inda tasamu ajikinsa, saida yaji wuya sannan yafad'i, Mamah Balaraba kuwa ai cikin sauri ta bar gurin gida ta nufa ko takalmi babu gabanta  yanata fad'uwa

   Fauziyya ma gidan takama hanya ta tafi dan bazata iyaba dawannan jarabar, kowacce rana kalar tata daban,
   Haka rayuwar Fauziyya taci gaba da dagulewa sosai take data sanin wannan rayuwar tata dakuma zalincin da suka aikatawa su Hapsatu

   Yau watanta 4month agidan jazuli amman bata sauya zaniba yadda yaga dama haka yake rayuwarsa kuma sai abunda tagani kawai

  yaune yakama zasu koma gurin boka dan yace tanayin wata 4 akoma amman Jazuli ya 'ke'keshe idonsa yace sam shi babu inda za..........
[04/02, 7:59 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨
✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨

💞NAH💞
SADIYA ABDULLAHI UMAR
💞UMMUH FATEEMAH💞



🅿---4⃣5⃣&4⃣6⃣


   ...........Yace sam babu inda zasu haka sukaita rokonsa ya'ki daga karshe dai dabara sukai suka tafi gidan su Hapsatu sukace Alhajine babu lpy taje ta dubashi, shine ya yadda

    Haka suka tafi tana zuwa wajen nakan tsauni yace ai cikin nan da aka kwantar bai kwantuba dan yanzu yakai wata 7
    Dafe 'kirji sukai atare wata nawa, yace 7 toh yanzu menene abunyi, ai babu tunda mun shimfid'a mata doka ta'ki bi, munce duk yadda zatai tayi sukwanta tare dan cikin ya kwanta amman takasa, toh yanzu babu yadda zan muku saidai ince, kutari gaba, akan aikin likitan nan amman dai kam yanzu abunda yafaru yarigada yafaru

  Kutashi kuban wajeeeee, kutashiiiiii nace ko bakwajiiiiii naneeeee
   Dasauri suka tashi cikin kuwa kafun suzo gida yafuto sosai ya zazzago dukkan abun duniya ya damesu, duk inda suka wuce sai an nuna su da baki, wasu kuma da hannu, ana zum6an su

  Lokacin data shiga gida akan idon Jazuli suka shiga dan haka yayi 'kwafa yad'auke kai
    Saida ta dawo gida sannan yabita dan yayi al'kawarin saiya lakad'.............



***  ***  ***
Dan komai yana canjawa yadda yakamata, bayan tafiyar sune wasu motoci suka tsaya abakin 'kofar gidansu, manyan mutanene suka futo daga cikin motar, babu wani 6ata lokaci aka yi Sallama abakin 'kofar gidan
   Amsawa Hapsatu tai, mai sallamar yace ana Sallama da matar gidan, toh ganinan, itadai tana amsawane kawai amman zuciyarta sai tsinkewa take, futowa tai da hijabunta akanta taga macece da kuma namiji sai yarinyar data siyi, waina da fanke jiya
      Murmushi tai tace bisimillah kushigo mana, shigowa sukai ta shimfid'a musu tabarma asoron gidan suka zauna
   Mai aikin Nusaiba ce da manager mom d'in ta
    Saida suka gaisa sannan suka d'anyi jimmm kana suka fara mata bayanin akan komai daya kawosu, na sunasan wani daga gidan yazo yana yiwa Nusaiba girki sannan kuma za'ana biyan sa naira dubu 100k duk wata
    Murmushi Hapsatu tai tace kuyi hkr wlh banida "ya mace agidan nan duk mazane kuma suna zuwa mkrnt sannan kuma ni inada ayyukan yi sosai acikin gidan nan danazo narin'ka mata, kuce da hjyr ta tayi hkr
   Rokonta suka farayi akan ta tai maka, hakurin dai ta'kara basu, akan bazata samu yi musu abunda suke da bu'kata ba, haka badan suna soba suka tafi amman da tunanin yadda za'ai hjyr su ta fuskanta dan tace duk yadda za'ai karsu sake sudawo mata babu mai aiki

   Koda suka koma gida hakadai suka shiga da fargaba acikin ransu da kuma tunanin yadda za'ai suyi mata bayani, dan sun

Please Login or Register in order to submit comment