Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da neman su
   Tunda antabbatar da duk yaran da suka d'auka yankasu akeyi

    Wata juwace tad'auki Anas yayi baya luuuuuuuuu..................... ✍🏻✍🏻✍🏻



Keep waiting my fan'sπŸ€”πŸ€”πŸ€—πŸ€—πŸ€—
Hallmarth πŸ’•πŸ’–πŸ’•
[04/02, 8:02 AM] Ummuh FateemahπŸ₯°πŸ’–πŸ₯°: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒ
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKINπŸƒDAKA RAINAπŸ˜πŸ€”*
_Story and written by_

*SADIYA β€’Aβ€’ UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}

πŸ…Ώ---5⃣3⃣&5⃣4⃣



...............luuuu yay yafad'i 'kasa sumamme mutanen gurin da kuma d'an sandan ne suka taimaka aka saka masa ruwa yafarfad'o bayan sun yayyafa masa



   Sosai Anas yaji wannan batun danji yay kamar yagama samun farin ciki dajin dad'i kenan arayuwarsa taduniya dan yana matu'kar san Hapsatu amman kuma yakasa fad'a mata sbd gudun karya ja mata masifa

    Sai yau yake daya sanin dabai auretaba yabar garin da itaba, dayanzu tana tare dashi


Hakadai akai ta ban baki anata yi musu jaje, su Mm Balaraba kuwa kamar mutuniyar kirki harda kukan munafurci itada Fauziyya

    Alhaji kuwa jiyay kamar ancire masa wata laka daga jikinsa, duk jiyay yarasa duk wata nutsuwar sa da kwanciyar hankalin sa 


   Balaraba kam da Fauziyya ji sukai wannan labarin yafimusu ko wane albishir dad'i dan ji suke kamar yau sallah, sai juyi suke suna shewa abunsu, kamar ba gobe




WasaΒ² saida aka had'awa kawu Anas da addu'oin samun nutsuwa sannan yadawo hayyacinsa

    Sosai yarame yayi ba'ki gaba d'aya yacanja kamar ba kawu Anas d'an gayu da kwalliyaba



Abu kamar wasa bikin Fauziyya sai 'kara sowa yake inda Jazuli babu alamar lpy atare dashi sam kullum haukar tasa cigaba take, daga ''karshema gidan mahaukata aka kaishi, dan zaifi samun kulawa acan



Tun saura sati biyu aka kai Fauziyya gidan gyaran jiki anata gwalli, duk,  'kauyen su babu wadda ta auri mai kud'i kamar ta intabiyo hanya kokai waye saika caya ta wuce sannan kawuce



" ya"yan gidan Alhaji Hamisu d'an kakah hajja sune suka dawo 'kawayen ta, dan sune suke da kud'i suma a 'kauyen




Yau ce takama ranar d'aurin aure kamar yadda yakama alissafi
   Ansha faty anci DJ angaji sosai tun jiya yau kuma za'ad'aura aurene da kuma kai amarya


   Ahanyar su ta zuwa d'aurin aure su sani 'kannen Fauziyya  suka had'u da wan mijinta b......................


**************

A6angaren su Hapsatu kuwa saida ta kammala aikin komai sannan tasallami kowa sannan tazauna akan tabarma dan jiran "Baba mlm idi"

      Yajuma sannan yafuto wajen gaf da magriba dan haka saida yaje sallar Isha'i sannan takai masa wani abuncin da ruwa yaci yasha


    Sannan tai musu shimfid'a atsakar gida dayake akwai wutar nefa dan haka suka zama idan yaranta suna nan


Saida yakammala, sannan ta bashi gurin zama yazauna, suka 'kara gaisawa sannan, yace mata Rabi'atu maiya kawoki nan garin ne keda kike aure agarin kano,  can 'kauyen rano


   Baba mlm ba rabi'tu bace  "yar tace Hapsatu wadda suke kawo muku kunu ko fura idan Ummerh ta dama


A'a dai A'a dai A'a dai, karki ce mun Hapsatu ce, itace baba

    Kuka yasaka yana tafa hannuwa yace kuma kinyi kama da ita sak dan wlh baku da maraba, keda RABI'ATU


Allah kenan mai yadda yaso da bawan sa
     Ina ita innar taki tak?
Aurene yakawoki nan?
Ina sirikin namu yake?
Tunda nazo bangan saba


    Sunkuyar da kanta tai 'kasa taji wata kwallah tacika mata idan ta, tace baba, ai Ummerh na ta dad'e da mutuwa


    Mekikace Hapsatu ban fahimce kiba , Rabi'atu d'ince tarasu, kuka ya'kara sakawa harda shar6ar majina



     Kayi ha'kuri baba haka Allah yaso, Tooo yaushe akai aurenki Hapsatu
    Baba ba aure nayi ba, zaro ido yayi yace ba aure kikai ba, mekikeyi agidan nan zaman kanki kike yi Hapsatu

   Ey, baba
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Hapsatu inashi Alhajin yake da Kakah hajja menene amfanin su dazasu barki kina zaman kanki bazasu ri'ke kiba


    Kuka tasaka tana yinsa da'karfin ta kanaji kasan tun daga 'kar'kashin zuciyarta yake zuwa, abdad'e ana danneshi, na zallar ba'kin ciki ne da 6acin rai, duk wanda yake sauraron sautin kukan ta saiyajishi acikin jikinsa sbd rad'ad'i dazafin da sautin ke futarwa


   Baba malam idii ne yace Hapsatu daina kuka kinji gaya mun meyake faruwa inji



    Babah dan Allah suwaye dangina kuma a ina suke inasan zuwa cikin su nima inji dad'in da mutane sukeji idan suna tare da 'yan uwansu


      Zan fad'a miki Hapsatu amman dafari dai kidaina kukan kifad'amun meyake damun ki inji
     Nima sai in baki labarin 'yan uwanki yanzunnan


    Rage sautin kukan tai tad'ago idanunta dasukai jaaa jaajirrr tace baba, nidai tunda nataso naganni tare da ummerh ta acikin Wannan gidan kuma ban waye dakuba sosai lokaci d'aya muka rasa BAFFA tun banda wayau daga baya kuma muka rasaka, kullum natambayi  Ummerh sai tace mun inyi hakuri zataban labarin inda kukaje, kuma BAFFANA yana kawo mana sa'ko dan yana samun labarin mu daga baya kuma yadaina kawo mana komai


     Tiryan tiryan Hapsatu tabashi labarin komai daya faru arayuwarsu bata 6oye masa komai ba har wahalar dasuka sha da kuma shekarun da suka d'auka acikin garin kaduna



    Sosai Baba mlm idiii yatausaya musu wani gurin ma saida yay kuka yace meyasa ya'auro wad'an nan ahalin, wanda ake musu take kalaΒ²,   "kwar kwasa fidda na kogo" ai indai sukai shiga saisun fitar dana ciki, in kuma babu to baka isa kashigoba


    Baba Kakah Hajja ce tasashi yay auren ai, kakah Hajja ita awa kuma
    Baba ai ita kakar muce
Inji wa yace miki
Inji Abban mu


  Hmmm πŸ€” murmushi yay yace a'a wannan batun ba haka yake ba Hapsatu


   Yaya yake Baba ban gane ba sam
Zan baki labari komai yanzu Hapsatu


    gyara zaman ta tai ta maida nutsuwarta kansa dan tanasan taji labarin Ahalinta itama


      ALHAJI IBRAHIM MAI SHADDAH
shine kakan Ummerh ki
   An haifesane agarin kano acikin unguwar yakasai alayin 'kofar mata anan ne gidan su yake


  Susu biyu iyayen su suka haifa inda suka basu ilimi da tarbiya daiΒ² misali kakan Ummerh ki yayi makarantar primary dashi da 'kanin sa musa wanda daga nan suka tsaya sai suka kama kasuwanci sosai



     Sana'ar shadda shine kasuwancin gidan kakan nin ummerh ki susu biyu suka taso Ibrahim da kuma Musa suna san junan su sosai dan idan babu d'aya to d'aya bazai iya koda zaman kasuwa bane


    Sun ginu akan sana'ar saida shadda sosai sannan Allah yay wa iyayen su rasuwa wanda hatsarin mota yakashesu ahanyarsu tadawowa daga YAMAI sunkaiwa danginsu ziyara


    Sosai mutuwar iyayen su ta gigitasu wanda kakan JAURO mahaifina kenan  yaso yad'aukesu amman sukace abarsu suci gaba da harkar kasuwancin su anan kawai


   Babu yadda suka iya dole suka barsu inda kakan JAURO yadawo kano da zama badan yana soba
   Saidan yakula da yaran d'an uwansa tunda iyayensu d'aya

   Kakan Ummerh ki shiya sha nono yabawa kakan JAURO


Yataho da JAURO lokacin shima baifi sa'an suba  inda suka cigaba da kasuwanci tare sosai suke girmama junan su wanda daga 'karshema kakan JAURO yayi aure ya auri HAJIYA TABAWA


    HAJIYA TABAWA macece mai hkrn gaske wadda bata da saka ido ko kuma ba'kin ciki akan abun wani


    Kuma duk iya abunda zaka mata bazata ta6a nuna kayi mata laifiba tsakaninta dakai addu'a kawai da kuma nasiha akan ka gyara
   Haka ta kwashi shekaru amman bata ta6a haihuwa ba har su IBRAHIM  da MUSA da JAURO sukai aure


   Basu dad'e dayin aure ba tasamu ciki inda wannan ciki shine yazama ajalinta dan tunda tasamu cikin nan kullum cikin ciwo take yau da lpy gobe babu lpy


   Randa ta haihu kuwa ranar tarasu inda tahaifi d'anta namiji aka saka masa suna NAZIRU



  Sosai su IBRAHIM suke kula da yaron nan wanda kakan Jauro badan yasoba ya'kara aure inda ya auri Kaka Hajjah


   Hjy mashid'a kenan iyayenta 'yan kano tu jiddane shiyasa idanunta suke abud'e zamΒ²


       Bata ganin kowa da arzi'ki shigowarta wannan gida yafara haddasa bala'i wanda kakan Jauro yasha yi mata fad'a da kuma takara amman bata gani


    Matar Ibrahim da musa sun haihu rana d'aya inda matar Ibrahim tahaifi namiji, matar musa kuma ta haifi mace



   Namijin aka saka masa suna Hashim, macen kuma fauxiya wadda akeceda Mamie, Hashim kuma ake ce masa Baffan
    

      Matar jauro bata samu cikiba saida aka yaye yaran Ibrahim da musa


    Sannan tasamu ciki sunyi murna sosai inda tacigaba da renon cikin ta harta haihu d'anta namiji aka saka masa idiris



   Bayan ta haihune babu dad'ewa Allah yay wa kakan Jauro rasuwa
   Inda wannan rasuwa ta girgiza wannan family sosai

    Sunyi kukan rashin baban su sosai da kuna kewarsa


   Kakan Jauro bai dad'e da rasuwaba kaka Hajjah tace tanada ciki wanda wannan cikin nata ma ba'asan dashiba yakai kusan wata 4



    Alokacin ne kuma IBRAHIN mai shadda shida 'yan uwan sa suka gida makeken ESTATE acikin garin RANO


    Wanda gidane nagani nafad'a acan suka tare suda matansu da iyalinsu baki d'aya inda suka baje gidan su nagado suka gina wani katafaren gida agurin


    Haya suka saka suka cigaba da rayuwarsu acikin garin RANO
   Tun daga wannan haihuwar da sukai basu 'kara haihuwa ba sudukan su Kamar had'in baki

   Yau tun safe kaka Hajjah take................ ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


Keep waiting my fan'sπŸ€”πŸ€”πŸ€—πŸ€—

Hallmarth ce πŸ’•πŸ’–πŸ’•
 
[04/02, 8:02 AM] Ummuh FateemahπŸ₯°πŸ’–πŸ₯°: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒ
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKINπŸƒDAKA RAINAπŸ˜πŸ€”*
_Story and written by_

*SADIYA β€’Aβ€’ UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}



πŸ…Ώ--- 5⃣5⃣&5⃣6⃣


.......... Tun safe kakah hajja take na'kuda inda bata haihuba saida ta kwana asibiti ta haifi "yara mace tana haihuwar ta kuma yarinyar tarasu


Ba'karamun ba'kin ciki tajiba narasuwar yarinyar taba wanda saida ta dad'e tana jinya sannan tadawo daiΒ²



   Haka rayuwa taci gaba kakah hajja tana kula da Naziru amman kuma wahalar dayakesha takai intaha
   Wanda daga ''karshe wajen Aunty Safiyya yakoma matar Ibrahim
    Inda tahad'ashi da danta Hashim take kulawa dasu



Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau dad'i gobe akasinsa harsu Hashim suka kammala karatun degree da matter's d'insu



   Inda aka had'a auren Hashim da Fauziyya
   Shikuma idiris ya auri wata wadda ake ce mata maryam
   Naziru kuma ya'auri karima


Acikin garin RANO iyayen su suka gina musu suma nasu makeken estate d'in suka fara tasu rayuwar mai tsafta dan bala'in kakah hajja kullum ''karuwa yake
      Suma kasuwanci suke dan iyayen su basu 'kyalesuba suna aikin gomnati kad'ay ba



   Sana'ar shadda da kuma wasu sana'oin duk sukeyi ba wasa



     Matar Naziru ita ta fara haihuwar d'an ta namiji aka saka masa sunan kawu Ibrahim
   Sai matar idiris itama ta haifi d'anta namiji itama, aka saka masa sunan kawu musa



    Saida Ibrahim da musa suka girma har sukai shekara 11 sannan matar Baffan ki tasamu ciki tahaifi yaranta guda uku biyu maza d'aya mace ake ce musu hasan da usaini ita kuma macen aka saka mata Rabi'atu
    Sosai suka taso cikin gata daso da 'kauna wanda bazai misaltuba agurin iyayen suba da kakan ninsu



    Ranar wata wata talata ranar dabazamu manta taba itace ranar da wuta takama acikin estate d'in su kakan Ummerh ki wanda da dare ne kafun motar kwana-kwana tazo gidan nan ya'kone sosai, dukkan su babu wanda aka futar da rai acikin su




   Amman abun mamakin shine wutar bata ta6a 6angaren kakah hajja ba ko kad'an itace ma ta futo take ihun wutaΒ²

    Haka akai musu sallah aka sallaci gawarsu wanda duk sun 'kok'kone sosai



      Babah Ibrahim Ashe kafun yamutu yabawa Hashim da Fauziyya dukkan takaddun dukiyarsu da komai wanda kaka hajja bata sani ba



   Kuma yace karsu gaya mata dan ba alkairi bace wannan matar ba


   Bayan sun rasu ne taji har yau ba'ai zancen dukiyarsu ba gashi sun doshi shekara hankalinta yatashi dan tai tunanin za'ai maganar kuma taji shiru



   Taso tai magana amman sai taga idan tai maganar za'ace wazata bawa tunda itadai bata ta6a haihuwa ba acikin su



   Ahaka tayi hkr ta share amman kuma daga 'kasa tanata yi musu bita da kulli danta gane ina suka ajiye wasu takaddu na dukiyar tasu



Tunda tayi bugun cikin dai duk abanza dan bataji wani labari ba



    Ranar wata juma'a da safe Naziru yatashi daciwon ciki wanda aka d'aukesa zuwa asibiti kafin suje yaras





    Ba'a dad'eba itama matar sa tarasu
Abun mamaki sai Kakah hajja tace abata d'an Naziru tari'ke sbd yanzu bashi da iyaye ita kuma bata da d'a abar mata shi



   Dafarko nida baffan ki bamu yaddaba amman saita rink'a kuka harda hawaye wai zamu nuna mata wariyar launin fata dan munga bata ta6a haihuwa ba



     Haka tacigaba da ri'ke Ibrahim awajenta tun yana d'an shekara 2 tari'ke Abban ki wanda yafara basa wahala daga farko



   Aikuwa Baffan ki ya 'ke'keshe idan sa yace tabashi d'an sa inba hakaba hukuma ce zata rabasu
   Taji tsoro sosai anan tace bazata 'karaba yayi hkr dan jan ido yanuna mata sosai akan Ibrahim



      Daga ''karshe tayi hkr ta rikesa amman kuma idan yay mata abu kad'an sai masifa da bala'i zatai tai masa
   Shekarar Ibrahim 6 agurinta tayi aure ta auri wani mai kud'in gaske bata dad'e da auren saba tasamu ciki ta haifi d'anta namiji aka sama masa suna Hamisu

      Sosai take nunawa d'an nan nata soda 'kauna da kuma sangartasa datakeyi sosai da kud'i sbd kasancewar mahaifinsa yana da kud'i
  

    Hamisu yanada shekara 10 mahaifinsa yarasu inda kaka Hajjah tayi ba'kin ciki amman kuma tayi murna dan yabar musu dukiya mai yawa

    Takama kasuwanci Kamar babu gobe
   Anan harkar kasuwancin ta tahad'u da mamar Balaraba hjy kaltum wadda ta 'kara bud'e mata idan ta tass suke bin malamai da bokaye


    Sosai suke shan sha'anin su yadda suka ga dama
     Baffan ki bai ta6a kula taba saidai daga ''karshe yad'auko Ibrahim yadawo dashi wajen Fauziyya



   Tahad'ashi shida su hassan da rabi'atu taci gaba da rainon su



   Haka rayuwa taci gaba da tafiya inda kowa yake cin gashin kansa



    Sam bama shiga safgar kakah hajja dan tunda tayi aure ta 'karo wula'kanci sosai



    Bare yanzu kuma datake zawarci
Ita irin matan nan ne masu 'karamun jiki, suci zamaninsu suci nawasu, sannan kuma tunda ba haihuwa takeba tsufanta bai nuna ba sam gakuma kud'i sun zauna mata kota ita, sai she'ke aya da kuma bariki



     Hamisu a'kasar waje yayi karatunsa na primary da secondary har university ma acan yayi shiyasa ya'kara kangarewa gashi kuma yahd'u da abokai marasa ji


   Sai suka had'u suka kangare babu wanda zai kwa6esu idan suna abunsu




Wani lokacinne ma idan abun ya ishi baffa saiya kirasa yay masa fad'a amman abanza dan baji yake ba




Daga 'karshema yafuta sha'aninsu gaba d'aya


    Baffan ki mutum ne mai yawaita kyauta da sadaka dan kullum sai anyi girkin almajirai agidan sa masu dafa musu abunci yad'auka na musamman, sannan kuma dukkan 'karshen wata sai yay rabon kayan abunci daga company sa kuma baya ta6a gajiya



   Yakan kuma shiga makarantar islamiyya da allo da boko yaga abunda basu dashi yay musu sannan kuma yad'auki nauyin karatun yara dayawa harsu kammala


    Shiya gina asibitin garin Rano dakika ganta



   Dan haka suma yaransa suka taso da wannan tarbiyyar basu da rowa ko kad'an, sannan kuma uwa uba Aunty Fauziyya itama bata da rowa sam hannunta abud'e yake




Lokacin da ummerh ki ta girma takai shekarun aure, lokacin ne kakah hajja tazo akan lalle lalle saita auri Hamisu d'anta inda Baffanki yace atambayeta tana sansa itakam tace aa batasan sa



   Ba'karamun ba'kin ciki kakah hajja tajiba  ba, alokacin taso aimata auren dole amman Baffan ki yace A'a sam shibadashiba za'ai wannan rayuwarba




     Alokacin ne kuma IBRAHIN yanunawa Baffan shifa yanasan Rabi'atu kuma itama tana sansa




Aikam babu 6ata lokaci akai auren su anyi biki nagani na fad'a inda suka tare agidan su wanda baffa yagina musu gidane babba sosai na "ya"yan.........................✍🏻✍🏻✍🏻😎





Keep waiting my fan'sπŸ€”πŸ€”πŸ€—πŸ€—πŸ€—

Hallmarth ce πŸ’•πŸ’–πŸ’•

[04/02, 8:02 AM] Ummuh FateemahπŸ₯°πŸ’–πŸ₯°: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒ
*DASHEN ALLAH*
*WRITING ASSOCIATION*


*'DAN HAKINπŸƒDAKA RAINAπŸ˜πŸ€”*
_Story and written by_

*SADIYA β€’Aβ€’ UMAR*
*{UMMUH FATEEMAH*}



πŸ…Ώ--- 5⃣7⃣&5⃣8⃣



............. Na "ya"yan manyane sosai duk wanda yashiga gidan sai yasan yashiga gida mai kyau mai rai da lpy sosai ma




Ranar da kakah hajja taje gidan banda ba'ka'ken magan ganu da habaici babu abunda takeyi


   Tana samun nasarar juya Ibrahim sosai sbd yana bata girmar uwa dan ganinta yake Kamar mahaifiyar sa


Ba'a dad'eba  tasa Hamisu yayi aure ya'auro wata yarinyar yar wani mai kud'i sosai


Inda tasaka dole sai Baffan ki yagina masa gida irin na Ibrahim acewar ai duka d'ayane


Haka yasa  akai masa shima gidan sa amman baikama 'kafar na Ibrahim ba sam anyi masa shima dai daiΒ² gwargwadon iyawarsa




Sosai wannan abun ya'kona mata rai akan yaya za'ai baza'ai masa irin na Ibrahim ba

   Amman ganin shima gidan na kece sa'ane yasata hkr kawai Amman badan taso ba


Haka akaci gaba da rayuwa inda shikuma musa yaron wajena shima yayi aure

  Baffan ki bai gajiba yayi masa gida shima mai kyau sosai inda suke zaune shida matarsa



Akwana atashi babu waha sai gashi ummerh ki tasamu ciki wanda tahaifi d'anta namiji wanda ranar data haifesa aka samu wani yasacesa da dad dare a Asibiti  sosai hankalin mu yatashi muka shiga wani irin tashin hankali, abu Kamar wasaΒ²

    Har akai satuttuka babu labarin wannan jariri sam




    Tun ana nema har aka hkr aka fawwalawa Allah komai dan yakai shekara 8 Amman ba'a gansaba hotonsa kawai muke dashi sai kuma wata sheda da mukewa Ahalinmu zarar an haifi yaro to ana masa wanka muke yiwa yaro ita abayan sa za'a yayyanka shi sau uku  amasa tabo


    Sbd koda ya6ata in aka gansa ana duba wannan shedar za'a gane sa


   Haka muka hkr muka cigaba da addu'a koza'a gansa




   Amman dai shiru kakeji
Haka rayuwa taci gaba tun daga wannan haihuwar kuma ummerh tadad'e sannan ta haihu inda tahaifeki aka saka miki suna Hapsatu wanda alokacin kuma Hamisu yanada raya 3 mata



     Musa kuma matar sa bata ta6a haihuwa ba
     Saida kika kai shekara 2 sannan matar musa ta haihu mace yarinyar ta itama kamarki tunda dukkan mu asalin buzayene Amman farare



   Duk wanda zaiga "ya"yan zuri'armu to babu mummuna kaf d'in mu dan har wasu suna cewa family'n mu family'n aljanu, sbd kyau da Allah ya azurtamu dashi




    Haka kuka taso Kamar tagwaye komai naku iri d'aya ake muku shi mukan zauna abakin wata bishiyar tsamiya nida baffan ki, dayake shi ma'abocin shan furane ko kunun tsamiya, to idan Ummerh ki tayi saita aikoku keda khadija ku kawo mana




    Anan zakuyi tawasa har sai mun tashi sannan kuma musa akaiku gida
     Tin ban iya shan furaba da kunu harna koya sosai sbd kullum ne sai ankawo mana ita




     Ranar wata asabar wadda takasance mun ba'kar rana ranar ina zaune nida baffan ki da yamma sai kawai yacemun shifa kawai so yake yabar garin nan kuma samΒ² bayasan yadawo koda wasa




   Abun yad'auremun kai amman sai nace masa meyafaru yacemun babu komai amman shidai kawai tafiya zaiyi




   Da'kar na lalla6ashi aka kwana washe gari kuwa  yagama had'a komai nashi yace tafiya zaiyi nida Mamie kakarki munyi munyi amman ina yace shi sam tafiya zaiyi kuma da yaransa su hassan


   Haka suka had'a kayan su suka tafi musa ne yashiga motar danya ja yakaisu tasha subar gari, aikuwa khadeeeja tasaka kuka saita bisu




Haka suka tafi tare inda nidai bansan ina suka tafi ba yace dai ko a ina yake idan ya nutsu zai kirani


   Ahaka muka rabu kowa yana kukan wannan tashin hankali dan agurin mu tashin hankali ne dan tunda muke dashi baya iya tafiyar kwana d'aya batare da mu ba


    Amman haka kawai baka tatan yace tafiya zaiyi kuma fur ya'kijin lallashi bare ban baki


    Haka suka tafi munaji muna gani
Bayan musa yakaisu tasha ne ahanyarsa tadawowa yayi accident yarasu



    Lokacin da mukaje gurin munshiga tashin hankali sosai dan duka motar sa takama da wuta da'kar aka ciroshi daga ciki muka d'aukesa aka kaisa asibiti


   Da'kar aka samu yadawo hayyacin sa anan ne muke tambayarsa khadeeja yace 'kin biyoshi tayi tace ita agurin baffa da kawu hassan zata zauna


   Da misalin 'karfe  11:00pm na dare yace ga garin kunan




   Sosai muka shiga rud'ani haka mukai gida dashi inda kuma har akai sadakar bakwai 7 bamuji labarin baffan kiba



  Kuma gashi bamu tambayi musa wace tasha yakai suba bare muje garin cigiya




     Wadda kika kar6o sa'ko awajenta wannan mai d'inkin itace matar kawunki musa




       Bayan tafiyar baffan ki da kamar shekara 3 babu shi babu labarin su gaba d'aya





Anan kakah hajja tafara baza nata mulkin inda bamusan hawa ba bamusan sauka ba kawai saiji mukai ankawo mana sammaci daga kotu




Mudai munsan bamuyi wani laifiba amman haka muka shirya ranar zuwa kotu mukaje
   Inda aka fara gabatar da shati'a akan Baffan ki


    Tace abunda yasa Baffan ki guduwa wai sbd yaciyo bashi ne yayi masa yawa



   Kuma ita take ta biya sannan kuma yanzu ya gudu takawo wasu takaddu wanda  ga yarjejeniya nan duk sun suna yaci bashin kuma tabiya
   Dan bamu yaddaba amman da mukaga saka hannunsa da sign d'insa sai muka yadda dan ko mafarki nake zan gane saka hannunsa




    Haka munaji muna gani aka saka gidajen sa danamu na gado nagarin kano aka siyar aka bata kud'inta

   Duk da hakan ma saida aka yanki wani gurin daga cikin gidan ku aka siyar aka cika mata kud'inta

    Daga nan kuma d'an sauran 'yan canjin dasuka rage mana muka ci gaba da siyarda shaddar mu kamar yadda muka saba




     Ana nan wata rana kakah hajja tashigo gidan danake haya tace in tashi nace mata ai kud'ina bai 'kare ba tace ita sam saina tashi inba hakaba kuma yanzunnan nima taga bayana




  Anan take gayamun dukkan abubuwan data aikata tun daga mutuwar kakan Jauro wanda tabuga tabuga danta samu ciki bata samuba sai daga baya tana ganin tasamu ta kasheshi da kuma mutuwar Alhaji Ibrahim mai shadda na wutar data kama agidan sa da kuma mutuwar d'ana Ibrahim da kuma karayar arzi'kin mu



   Anan take gayamun abunda ya'kara van mamaki nacewa itace tai wa............... ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻😎



Keep waiting my fan'sπŸ€”πŸ€”πŸ€—πŸ€—πŸ€—
Hallmarth ce πŸ’•πŸ’–πŸ’•
[04/02, 8:02 AM] Ummuh FateemahπŸ₯°πŸ’–πŸ₯°: πŸƒβœ¨πŸƒβœ¨πŸƒβœ¨
βœ¨πŸƒDASHEN πŸƒALLAHπŸƒβœ¨
WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
πŸƒALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBIπŸ—‘οΈ
Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ± Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ± Ψ­ΩŠΩ…
✨DAN HAKINπŸƒ DAKA RAENAHπŸ˜πŸ€”βœ¨

πŸ’žNAHπŸ’ž
SADIYA ABDULLAHI UMAR
πŸ’žUMMUH FATEEMAHπŸ’ž



πŸ…Ώ---

5⃣9⃣&6⃣0⃣


............. Tafad'amun abunda Ya'kara ban mamaki tace itace tai wa Baffan ki kurciya kuma bazai 'kara dawowa ba har abada

    Sbd ance bazata iya kasheshi ba kuma zai kawo mata matsala indai bata masa kurciya ba


    Shine yasata tayi masa haka, tacemun mazaΒ² inyi in tattara in bar gari Inba hakaba nima takasheni

    Babu shiri ban gayawa kowaba na had'a kayana nabar gari nida matata


    Bamu dad'e da tafiyaba kd naba tayi ciwon 'koda kuma bani da kud'i dan sainai bara nake samun inkawo muci abunci acikin kasuwa muke kwana, itama Allah yad'auki ranta saura ni kad'ay

   Allah ne yay zamu had'u dan da yaune nake saran zamu tafi legos sbd acan anfi samun kud'in bara

   Sai wani d'an uwana wanda muke bara dashi yacemun anan gidan kina bada sadakar abunci kullum kwano 30 shine nace bari inzo ko Allah zaisa nasamu

    Allah sarki Baba mlm, wlh duk tuna nina Kakah Hajjah ita ta haifi abban mu kuma bai ta6a gaya mana ba
    Amman har take cewa zata tsine masa, bayan ba ita ta haifesaba

    Aimu ada Hapsatu muna tsoron cinuwa, sbd ce mana ake duk wanda yatsine maka saita bika

    Allah sarki Abban mu babu komai haka Allah yake lamarinsa
   Komai zai daiΒ² ta insha Allah

Kuka take sosai tana mamakin irin wannan mugun halin na Kakah Hajjah amman gaskiya wannan muguwace

    Da'kar talalla6ata tadaina kukan yace taje ta kwanta shima bari yaje ya kwanta

     Haka akai kuwa
Koda gari ya waye sassafe tagama aikinta sunata yin safgoginsu
   Bintu ce tashigo itama tana tayata suka 'karasa wasu abubuwan sannan ta tafi zuwa shago, sallama taji anyi ta taso sai taga Nusaibace, aidasauri tafuto tarunguneta suka fara ihu
   Yeeeee yaushe gamo wlh kemadai kya fad'a, tunda narakaki siyan kunun aya da fankasu shikenan kika manta dabatun wata bintu 'yar kawo
    Hhh habadai wlh a'a hajiyar muce batasan ina futa wlh sam
   Toh shikenan Amman dai

Please Login or Register in order to submit comment