Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 1️⃣&2️⃣



JIGAWA STATE HAƊEJIA L.G

*UNGUWAR K/AREWA*


Sanye ya ke da kayan makarantar islamiya riga da wando ash colour sai hula dark blue, riƙe ya ke da jakar leda mai ɗauke da littattafai yaro ne ɗan kimanin shekara shida, tsaye ya ke a jikin bangon wani gida na ƙasa sai share hawaye ya ke wani na bin wani, ganin ƴan islamiyarsu sun zo za su wuce hakan yasa ya juya bayansa dan baya so su ga hawayensa su rainashi.


"Kai kun ga Hizbullah prefect" Yaro ɗaya ya faɗa daga cikinsu.


"Lah wallahi shine dama nan wajen ne gidansu" Yarinya ɗaya ta ce tana washe baki.


"Aikwa ya juya bayansa kar mu masa magana dan dama shima baya yiwa mutane magana sai ya ga dama"Ɗayan yace suna ta bin Hizbullah da kallo dan ya basu baya kuma bai waiwayo ba dan duk maganganun da suke yana jinsu.Suna wucewa ya cigaba da hawayensa.



"Hizbullah dama baka tafi makarantar ba Ikon Allah yanzu akan na ce Ridallah bacci take shine ka ƙi tafiya kake kuka?" Baba Habiba da fitowarta kenan daga gida ta ce tana riƙe haɓa.


"Ai bazan tafi ba indai bata tashi na ganta ba sai dai na fasa zuwa makarantar" Yace yana share hawayensa.



"Kai jama'a na ga ikon Allah wannan wace irin shaƙuwa ce tsakaninka da Ridallah, ace saboda tana bacci ba za ka tafi makaranta ba sai ta tashi, na ga ɗazun nan ka tafi gida ka yi shirin islamiyar shine bacci ya ɗauketa amma shine kake kuka kamar dai kwana kayi baka ganta ba"


Shiru ya yi bai ce komai ba sai sheshsheka da yake ta faman yi.



"Mu je ka ganta tana baccin sai ka tafi in yaso kafin a tasoku ta tashi daga baccin" Baba Habiba ta ce tana kama hannunsa domin su koma cikin gidan.


"Au bai tafi makarantar ba?Ai dama nasan hali shi yasa na leƙo in tabbatar" Muryar Umma Sadiya ta katse musu tafiyar tasu.


"Wallahi kwa ni zatona ma ya tafi shi yasa ban biyo bayansa ba dan da na ce masa bacci take to kawai yace ya juya ya fito daga gidan"


"Hmmm ai Hizbullah da Ridallah sai Allah ki barshi ya ganta tana baccin ko ya samu ƙwarin gwiwar tafiya makarantar dan in ba haka ba ko an matsa masa ya tafi in yaje ma ba sakin jiki zai yi ba bare ya yi karatun kirki" Ummar Hizbullah ɗin tace ta juya domin komawa cikin gidan.


"Bari na yi sauri kar ya makara"Baba Habiba tace tana jansa suka yi cikin gidan, dan shi ko uffan bai ce musu ba kansa kawai ya sunkuyar yana jin duk abin da suke cewa.


Suna shiga cikin gidan ta kai shi har ɗaki, Ridallah yarinya ƴar kimanin shekara ɗaya tana baccinta hankali kwance.Baba na kai shi ɗakin ta tsaya a bakin ƙofa jakar hannunsa ya ajiye ya ƙarasa har kan katifar da aka kwantar da ita ya tsugunna a gabanta ya saki murmushi kallonta yake kamar yau ya fara ganinta sai kuma ya sanya hannu a aljihunsa na gaban riga ya fito da naira goma kuɗin makarantarsa yace.



"Wannan kuɗin shi zan siyo miki alewa da carbin malam in kawo miki in aka taso mu" Yana gama faɗar haka ya tashi yana mata bye-bye ya ɗauki jakarsa ya fito ko ta kan Baba bai bi ba ya fice daga gidan dan ya kusa makara kuma da ɗan nisa dan dai kwalta kawai zai miƙe har makarantar ba tare da ya yi kwana ba.



"Oh wannan yaro yana ƙaunar yarinyar nan ace kullum in zai je makarantar arabi ko boko sai ya shigo haka in ya taso ma, Allah raya ta, ta ga irin tarin ƙyautatawar da yake mata"Cewar Baba tana girgiza kai ta juya domin ta fita domin samun yaron da za ta aika siyan klin domin yin wanke-wanke.



Yana isa makarantar ya nufi ofis ɗin malamai ya kirawo malamin Qur'an domin shine monita kuma duk ya haddace time table ɗin ajin nasu. A kujerar gaba yake su biyu da abokinsa Bilal yana shiga ya miƙawa Bilal hannu suka yi musabiha daga haka ya zauna bai kuma cewa komai ba ya fito da Qur'aninsa, tsit ƴan ajin suka yi saɓanin kafin zuwan Hizbullah ɗin da suke ta surutu dan shi da ido kawai yake kallonsu su yi tsit kamar babu kowa a ajin dan ko sunan ƴan surutu baya rubutawa yana musu kwarjini sosai dan ba shiga harkar kowa yake ba sai dai ya yi abin da ya kawo shi gashi da mugun ƙoƙari hakan yasa ya zama mai farin jini a wurin malamai.



Malamin ne ya shigo ajin ya maimaita musu ɗorin da ya musu jiya sau uku sannan ya fara karɓar hadda daga kan Hizbullah domin shine a kujerar gaba kuma shine a farko.Tun da ya fara karatun kowa saurarensa yake yi ya iya ƙira'a gashi ko kakarewa ba ya yi har ya kai ƙarshen ayoyin da aka ɗora musu.Kabbara aka masa sannan malamin ya cigaba da karɓar hardar sauran duk cikinsu babu wanda ya bada harda irin ta Hizbullah.



Ana fitowa break ya siyi alewa da carbin malam ya sanya a aljihu ko ɗanɗanawa bai yi ba, ana tashinsu ya kamo hanya ko gidansu bai kalla ba ya shige gidansu Ridallah dan dama maƙota ne katangarsu ɗaya.Da sallama ya shiga, Baba Habiba ta amsa masa Ridallah da ke tafiya tana ta dariya ganin ta ƙware a koyon tafiya, Hizbullah kawai wurinta ya nufa yana ta murmushi itama tana hangoshi ta nufoshi tana masa dariya dan ta matuƙar saninshi dan tun da ta buɗi ido take ganinshi.



"Oyoyo ƙanwata" Yace lokacin da ya jinginar da jakarsa jikin bango ya ɗauketa sai murna take tana zillo, da yake yana da jiki dan in ka ganshi sai ka yi zaton ya yi shekaru goma ma saboda girman jikinsa.


"Ga alewarki da carbin malam"Ya bata alewar a hannunta ta riƙe tana wasanta sai ya ɓare carbin malam ɗin ya sanya mata a baki.




"Yanzu Hizbullah ace kullum ba zaka kashe kuɗin makarantarka ba in an baka sai dai ka siyo mata wani abun? Kake siyo abu marar zaƙi saboda kar rana ta kama ƙanwartaka" Cewar Baba tana kallonsu cike da sha,awa.



"Ai ba zan iya cin abu ba ban kawo mata ba, amma zan ke siyo mata biskit dan kar rana ta kamata" Hizbullah ya ce yana zaunawa akan tabarma ya ɗora Ridallah a cinyarsa yana mata wasa Baba tana tuƙa tuwo.Sai da aka fara kiran sallar magriba sannan ya yi alwala ya ɗauki jakarsa ya yiwa Ridallah bye-bye ya tafi gida ya ajiye jakar ya wuce masallaci.Ridallah kwa daƙer Baba ta lallasheta ta yi shiru dan yana ficewa daga gidan ta fara kuka.



Da daddare bayan an yi sallar isha'i ya ɗauki abincinsa ya tafi gidan Baba domin acan yake cin abincinsa tare da Ridallah, Baba ta yi ta cewa ya daina tahowa da abinci amma sai yace shi ya fi so ya kawowa Ridallah na gidansu sai shi kuma ya ci na gidan Babar.Sai wajen ƙarfe takwas da rabi idan Ridallah ta yi bacci sai shima ya tafi gida ya kwanta dan ko homework aka bashi a makaranta to a gidan su Ridallah yake yin kayansa.






Washe gari da safe wajen ƙarfe bakwai da rabi ya shigo gidan Baba da sallama dama saboda zuwansa Baba take cire sakata ta bar ƙofar a kare dan ta san ba zai iya tafiya makaranta ba sai ya biyo ta gidan.Sanye yake da kayan makarantar boko jakar makarantarsa goye a bayansa, hannunsa da flask ɗin makarantarsa mai ɗauke da abincinsa sai leda a hannunsa mai ɗauke da biredi da ƙosai sai shayi a kofi ya kawowa Ridallah bayan ya gaishe da Baba ya yiwa Ridallah wasa ya ajiye mata abincin da ya kawo mata dan ita ma shegen wayo ne da ita dan dai siririya ce bata da jiki gashi dai akwai cin abinci dan babu abin da bata ci Baba da wuri ta koya mata cin abinci. Fita ya yi yana sauri dan ya kusa makara dan dai makarantar bayan layinsu ne.





MMN AFRAH



❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 3️⃣&4️⃣




Bayan wasu shekaru

Yaro ne ɗan kimanin shekaru goma sha ɗaya riƙe da hannun yarinya ƴar kimanin shekaru huɗu, sanye suke cikin kayan makarantar boko, shi riga da wando farare sai hula yellow ta prefect ita kuma riga da wando blue sai farin hijabi.Tafe suke suna hirarsu gwanin ban sha'awa,sai flask ɗin abincin Ridallah riƙe a hannunsa.


"Ya Hizbu ni dai yau a ajinku zan zauna banaso ka tafi ajinku ka barni"Yarinyar ta ce tana turo baki.


"Haba Rida kinsan dai ba ajinmu ɗaya ba kuma in malamin mu ya ganki a ajinmu ni zai yiwa bulala, ko kinaso a dukeni?"



"A'a ni banaso"


"To in mun je ki shiga ajinku ana fitowa break zan zo wajenki sai mu je in siya miki alewa ko?"Ya tambaya yana kallonta, kai ta gyaɗa masa alamar ta yarda.



"Yawwa ƴar ƙanwata"Ya ce yana murmusawa, itama dariyar ta yi har haƙwaranta suka bayyana.


A haka suka ƙaraso makarantar lokacin ana kaɗa ƙararrrawa za a shiga aji dan ƙarfe takwas dai-dai, prefect na ta kora yara ajijuwa, ajin su Ridallah ya shiga lokacin yara ke ta shiga ajin ganin Hizbullah kowa ya nemi wuri ya zauna ya yi ɗif, ko ta kan su bai bi ba ya nufi kujerar su Ridallah yara ne guda biyu a ciki dan haka Ridallah ta ce ita tsakiya take so ta zauna haka yaran suka matsa mata ta shiga ta zauna ba dan ransu ya so ba sai da ya lallaɓata sannan ta yarda ta zauna ya je ya ajiye mata abincin a inda suke ajiye kwanukan abinci sannan ya je class ɗin su ya ajiye scul back ɗinsa ya fito suka cigaba da kora yara ajijuwa da yake makarantar a haɗe take primary & junior scul sai dai kowane da ɓangarensu.



Ana fitowa break ya je ya kamo Ridallah ya ɗakko abincinta ya zo ya zauna yana bata a baki, sai da ta ci ta ƙoshi sannan ya ci sauran, sai kuma suka je ya siyo ɓata abin da take so da kuɗin makarantarsa da nata ya haɗa ya kaso mata sai da suka zauna tana cin abubuwan da aka siyo ɗin sannan take ɗauka tana bashi a baki dan itama bata iya cin abu ta hanashi ko lokacin da ba a sanyata a makaranta ba idan aka bata abu yana makaranta sai ta ajiye masa har sai ya dawo ta ɗauka ta bashi abin da ta rage masa domin akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu bata san kowa ba sai shi sai Baba, daga ta ga bata ganshi ba za ta tafi gidansu nemansa idan kwa ɗaya bashi lafiya to ɗayan ma zai kamu da rashin lafiya.



Bayan an taso su suka kamo hanyar gida suna zuwa gidansu Hizbullah suka fara shiga ya cire kayansa ya ɗakko abincinsa suka tafi gidan Baba itama Ridallah ta cire uniform ɗin ta sanya wasu kayan sannan suka zauna suka cinye abincin Hizbullah sannan Baba ta zubo musu wani suka ci tare dan haka suke yi basa yarda su ci abincin gida ɗaya wai su ciyayya suke yi.



MMN AFRAH


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 5️⃣&6️⃣



_BIRNIN TARAYYA ABUJA G.R.A_




Wani ƙaton gida mai tafkeken get na shiga, na tsaya ƙarewa gidan kallo girma da yanayin tsaruwar gidan gida ne da ya amsa suna gida, kana kallon gidan ka san mamallakan gidan sun amsa sunan manyan attajirai.Gini ne sashe -sashe ga motoci nan bila adadin a wurin da aka tanada dan ajiye motoci wasu a buɗe wasu kuma an rufe su.

Girma da haɗuwar gidan yasa na saki baki ina bin gidan da kallo lallai wannan gidan shi ake kira da aljannar duniya! Tafiya na fara na doshi wata hanya da ta ɗan miƙe wacce idan ka kai ƙarshenta ne za ka ga ta rabu zuwa sashe -sashe, sai da na tsaya ina tunanin wane ɓangare ya kamata na fara zuwa sai kawai na nufi wanda ke gaba na.Ƙofar part ɗin na tura sai kuwa gani na shigo wani fili mai girma da wasu shuke -shuke na fulawoyi da abubuwa masu ƙawata wuri.Ƙarasa wa na yi na buɗe ƙofar da za ta sadani da babban falon.


Wani sanyi da ƙamshi mai daɗi ne ya fara ziyartar hancina, ƙarasa shigowa na yi cikin falon tsaruwa da haɗuwar falo kaɗai abin kallo ne, ban gama ganin tsaruwa da haɗuwar falon ba idona ya kai kan dinnig area inda wata mata ke zaune akan dinnig ɗin tana danna wayarta sai wani yatsine-yatsine take tana harare -harare tana yi tana kallon agogon wayar ta dan ranta sai suya yake yadda har yanzu Alhaji ba su fito ba dama duk ranar girkin Hajiya Azima Alhaji ba ya son fitowa da wuri sai ta rasa uban me suke a ɗakin matar da ba haihuwa take ba menene abin ɓata lokaci a kanta.


A hankali yake sakkowa daga upstairs ɗin sanye yake da cofee yadi mai ɗan haske ɗinkin tazarce hannunsa riƙe da agogon sa ƙirar Gucci yana ƙoƙarin ɗaurawa Hajiya Azima biye da shi riƙe da jakar office ɗinsa sai zance suke suna dariya abin su.Ƙaran takalma su shi ya maido da Hajiya Hauwa daga saƙar zucin da take.Yadda kan ta ke akan wayarta bata ɗago ba dan wani tuƙuƙin baƙinciki ne ya turnuƙe mata zuciya saboda sautin dariyarsu kaɗai sai da yasa ta ji kamar zuciyarta za ta buga.Amma da yake ta iya takunta sai ta danne abin da take ji ta ɗago kan ta tana kallonsu fuska sake.



"Barkan ku da fitowa"Ta ce musu lokacin da suka ƙaraso dinnig area ɗin.


"Yawwa barkan ki"Suka haɗa baki wurin faɗa.

Alhajin ne ya jawa Hajiya Azima kujera ta zauna lokacin da ta dawo daga tsakiyar falon da ta je ta ajiye jakar office ɗin Alhajin akan kujera, kallonta yake fuskarsa ɗauke da murmushi har dai ta zauna kafin shi ma ya sanya hannu zai ja kujerar Hajiya Azima ta yi saurin sanya hannu ta ja masa kujerar ya zauna suna yiwa junansu murmushi tamkar dai sun manta da Hajiya Hauwa da ke zaune tana hararsu ƙasa-ƙasa.


"Barka da safiya Alhaji" Cewar Hajiya Hauwa tana murmushin yaƙe dan ji take kamar ta rufesu da mugun duka tsabar takaici.


"Kin tashi lafiya" Alhajin yace cikin sakin fuska.


"Lafiya ƙalaw" Ta ce tana masa wani kallo na soyayya dan ta ɓatawa Hajiya Azima rai.


"Masha Allah"Yace lokacin da ya sanya fork zai fara cin abincin da Hajiya Azima ta zuba masa.


"Hajiya fatan kin tashi lafiya"Hajiya Hauwa ta faɗa cikin kissa.


"Lafiya Alhamdulillahi fatan ke ma haka"

"Lafiya nake"


"Masha Allah"


"Ina Iftihal ne ko har ta tafi school" Alhajin yace lokacin da yake kurɓar tea.


"Bata tashi daga bacci ba ai" Hajiya Hauwa tace tana ɗan sanyaya muryarta dan kar ya yi mata faɗa.


"Haba Hajiya sau nawa kike so na faɗa miki ki daina yiwa yarinyar nan wasa da karatun ta, ace an sanya yarinya a school amma ba za ta je ba to me kike so ta miki a gidan idan bata yi karatu ba haka jiya ma monday fa bata je ba, hatta islamiya ma bakya so ta je, gaskiya bana so kar a ƙara barinta a gida" Alhajin yace cikin ɓacin rai dan ya kasa gane Hajiya Hauwa wace irin mace ce da bata ƙaunar ƴarta ta je makaranta kullum ana ɓacin rai akan abu ɗaya.



"Allah huci zuciyarka Alhaji hakan ba zai sake faruwa ba" Ta ce tana wasa da cokali a cikin plate ɗin dan tun da ya sako maganar karatun Iftihal sai ta ji gabaɗaya abincin ya fice mata a rai dan babu abin da ta tsana irin maganar zuwan Iftihal makaranta, shi kuma ya kasa gane wa cewa bata ƙaunar Iftihal ta yi wani karatu daga na bokon har na arabiya.



"Haka kike cewa kullum amma kin kasa canjawa amma inaso ki sani akan maganar makarantar Iftihal za mu saka ƙafar wando ɗaya da ke" Ya kai ƙarshen maganar yana goge bakina da tissue, ita dai Hajiya Azima bata ce komai ba dan bata son sanya baki a abin da bai shafeta ba amma itama har ga Allah bata son sangarta Iftihal da Hajiya Hauwa ke yi musamman ma a ɓangaren karatu.


"Hakan ma ba za ta faru ba" Ta ce tana marairaice murya.


"Yanzu ma dan na ga lokaci ya ƙure har takwas da kwata kafin ace an mata wanka an shiryata amma da sai ta tafi yanzu ma" Yace yana miƙewa, domin tafiya office, Hajiya Azima ma miƙewa ta yi domin rakashi, wata uwar harara Hajiya Hauwa ta bisu da ita dan gabaɗaya haushin su take ji dan tun da ake cin abincin sai wani satar kallon juna suke kamar ba tare suka kwana ba.



"Allah tsare" Hajiya Hauwa ta ce a takaice.



"Amin "Shi ma yace ba tare da ya kalli ko inda take ba.


Hajiya Azima jakar ta ɗauka take masa baya, suka fita, a ƙofar fita daga part ɗin suka samu Sa'idu direba yana jiran fitowar Alhajin, gaishe da su ya yi cikin girmamawa suka amsa cikin sakin fuska jakar hannun Hajiya ya karɓa ya jiya ya tafi ya bar su suna sallama, sai da ta ga tafiyar su tana ɗaga masa hannu shi ma yana ɗago mata duk da akwai ɗan tazara daga part ɗin zuwa parking space amma suna hango junansu ana wangale get motar na fita Hajiya Azima ta juya ta koma ciki domin ta gyara masa bedroom ɗin nasa na upstairs inda suka kwana dan bedrooms a saman ma guda huɗu ne sai dai ɗaya wanda suke kwana Alhaji da Hajiya Hauwa ɗaya kuma inda yake kwana da Hajiya Azima kowacce da ɗakin da ya zamana shine turakar da take kwana da miji dan basa sharing na turaka sauran biyun kuma kawai dai an ƙawata su ne da kayayyakin ɗaki amma ba wai ana kwanciya a ciki.


Tana dawo wa bata tarar da Hajiya Hauwa a dinnig area ɗin ba ta koma part ɗin ta dan kowacce akwai ƙofar da za ta sada ta da part ɗin ta, sai kuku yana kwashe kwanuka, ya gaishe da ita ta amsa masa tare da hayewa sama domin yin gyaran dan ita a tsarinta bata yarda ƴar aiki ta gyara mata turakar mijinta ba saɓanin Hajiya Hauwa da mai aiki ke gyara mata.



Hajiya Hauwa rai ɓace ta ƙarasa part ɗin nata dan har lokacin bata daina jin haushin faɗan da Alhajin ya mata a gaban Hajiya Azima sai dai ta sha alwashin sai dai ya yi falansa ya gama amma dai ba za ta taɓa yin abin da yace ba ko da ta fara ba zai ɗore ba.Mai aikinta Safiya ta samu tana ta faman goge -goge cikin girmama wa Safiya ta mata barka da dawo wa amma ko inda take bata kalla ba dama ita ma bata sanya rai cewa za ta amsa mata ba dan ta san hali, shegen wulaƙanci ne da ita.



MAMAN AFRAH😍

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

💕ALAƘAR YARINTA💞

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 7️⃣&8️⃣




Hajiya Hauwa upstairs ta nufa tana zuwa ta kama ƙofar ɗakin Iftihal ta buɗe kwance ta ganta akan gado tana cikin bargo fuskar ta ce kawai a buɗe sai baccin ta take hankali kwance.Wata uwar harara take bin Iftihal ɗin da ita daga ƙarshe ta doka wani uban tsaki tare da rufo ƙofar da ƙarfi ta juya ta koma nata ɗakin, Iftihal kwa da ke ta bacci bata san abin da ake ba.Tana shiga ɗakin ta ta cire ɗaurin ɗan kwalin da ta yi wanda ake kira ture ka ga tsiya wuri ta nema a bakin gado ta zauna har lokacin ranta na ƙuna ta rasa yadda za ta yi da Hajiya Azima kullum maimakon ace Hajiya Azima ta zama bora a wajen miji amma kullum ita ce mowa ita ce tauraruwa ita ce abar so ita duk faɗi tashin da take yana tashi ne a banza, kullum Alhaji cikin ganin laifinta yake a gaban Hajiya Azima sai ya tsinkata yana mata faɗa tabbas

Please Login or Register in order to submit comment