Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinci sai dai yandabaru dake jego nake bana rabo da kunun gyada wuni nakeyi shansa dake na koyawa nana ma shansa itama intaji yunwa shinakan bata.


Dake bame muguntar ciyarwar bane wani lokacinma biyar agida take masa ya auno mana Yar gwangwani hudu Kuma da ka kalleshi kasan yaci wuyar tafiya nakance abban nana amma dai akafa kataho ko ?

Sai dai yayi murmushi yace to yaza,ai abinne sai addu,a kasuwar tazama abinda tazama.

Danayi wani tinani sai naga shidin inbanda wahala ba abinda yakeci mutumin dazaije kasuwa akafa yadawo akafa kuma ya wuni Yana maka bauta ace baisamu abinda zai hau motaba ko abinda iyalinsa zasuci su wadataba aiko wahalace ciki zalla.


Wataran nakece masa mezai hana asami wadansu Yan kudi kaima ka Kama shagonka .

Kallonna yayi tare da daukar saddiku dake cinyata yace karimatu bakisan abinda kasuwar Tamu take cikiba yanzun ana ganin kayi wani motsi na cigaba sai a kwantarka dan abinda kake futa kana samowa iyalinka ma sai ya gagareka .

Nace to ai in akace ahaka zamu cigaba da rayuwa ko akwai kalubale megirma tin yanzun komai Yana gazawa balle ace munkara tara yara kaga Allah ya bamu dama tin farko Kuma kayi watsi da ita yakamata yanzu mugina iyalinmu kodangaba kana gani fa dukkanin Yan uwanka sundareka amma ka fahimceni karkayi min mummunan zato.


Ina nufin dukkanin su bawanda bazai iya ajiye abincin shekara agidansa ba amma Kai sun kwakumeka karkashinsu ya kamata ace kaima yanzu kaci gashin kanka shekararku nawa tare bakada cigaba kullum dan uwanka kakewa nema inda yare suka fimu kenan dasune da tini sun yayeka kaima ka yaye wani amma kullum in ya hango cigabanka sai ya dukunkuneka ya Kuma danneka karkashinsa kayi tinani iyalinsa kake ginawa ba nakaba Kuma inda duniyarnan tazama daga kwauri sai gwiwa ko bayanan ranka inhar baka raine mu da tattalin rayuwarmu ba Babu mebi takanmu.


Amma kayi tinani .

Ajiyar gwauron numfashi yayi yace za,a duba Amma kinsan banida kudin da zanja jarin .

Nace indai kudine bazasu gagaraba kabari inkoma aiki zansami dashi inshiga saina baka amma fa kasanni banida dadi nima kudi nawane bakuma kyauta nabakaba kafin kakarba zamuyi yarjejeniya kullum inkadawo daga kasuwa akwai abinda zaka cirarmin na ajiye har Allah yasa kabiya ni in Kuma kayimin halin maza zakaga true color dina domin guminane nabaka aro domin cigabanmu Kuma zance ne nidakai karkayiwa kowa zancen har hajiya mu bashshi atsakaninmu .

Gadiya yayimin tare da amincewa da batuna .

Nace kwana biyu bamuje nagaida hajiyaba Allah yasa kaje kaima danna fuskanci kamar kwana biyu baka zuwa ?



πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€


😨😨😨😨😨😨

πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™

*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAUπŸ™‹*

πŸ…Ώ *7(G)*


🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝




Sadiya ce kwance ta lula duniyar tinani a haka take Jin wata murya na tashi alamar sallama akeyi tin tana jiyowa anesa har sallamar ta matso kusa da ita .


Dafata taji anyi tare da cewa keko aminiya meyayi zafi ?

Kuma kuna fadawa duniyar tinani bare Kuma mu,


Gyara Zama tayi tare da yin kwafa tace kedai bari nida uwar sabo ne tana neman hakkemin nida mijina amma kan ya Kira suna na sai yakira sunanta ko dawowa yayi Kan yashigo nan wai sai yaje yakai Mata abinda yashigo dashi ko nidin yakan nuna bakowa bace in uwarsa tananan ke kamarma tsoron nuna ni Yake matsayin matarsa intananan kefa wallahi sai naci durun uwart....karki karasa batta taci darajar haifo mikishi datayi .


Dama tin zuwana nafarko naga yadda yake Mata nasan dakwai matsala sanda nayi miki magana gwaleni kikayi har kina babassa ce ita ta haifi abinta to yanzu aikinga idi randa kikaga mudi Kuma Kya neman shawara yarage gamai Shiga rijiya.


Yo ai ba mudi ba niba abinda banganiba har talle nagani Kuma wallahi sai ta bar gidannan ko Taki ko taso ita lokacin da tayi rayuwar aurenta waya takurata nifa yanzu ko wani abinne mukeyi ke ko dariya ce tayi yawa saboda takura sai yace rage murya saboda ummata kinji wani fi,ili abinci sai yace sai yaduba intaci najirashi sannan zaici inko ya durkusa gananta kamar Yana neman hantsilawa saboda risinawa Niko jinake kamar nahadiyesu wallahi Dan so ma danake masa jinake yaja baya saboda takurar uwarsa .


Ke yishiru akwai hanyoyi har sai kince ya Isa aikin sanni kin San halina bana daukar irin wannan kina ganin yadda nayi maganin tsohuwar nawa mijin yanzu da lada akace su hadu gudaya ma bazasu iyaba saboda tini nasa na zaure yayi musu farraku.


A,a safiya nidai bazan iya
zuwa gun malami ba nidai inda wata hanyar kigayan .

Hhhhh tayi wata shegiyar dariya ,tace bani kunnanki.

Matsowa tayi kusa da ita tayi mata wasu maganganun a kunne,

Ahayye ke Yar gari dake za,a kinsan Allah itace simple way din dazanbi zataci kwal u...keee

Nace Miki taci darajar haifo mikishi batta kawai da takaicin dazata kunsa .

Keni banmiki albishirba cikinefa dani .

Allah tawan ?

Wallahi da jiya kikazo da baki sameniba Ina asibiti sakamakon mashsharar danake fama Ina zuwa akayimin test sai ga Dan baba ya bayyana nasati uku amma bakiji murnar da yayiba a waya amma abin takaicin da yadawo sai yayimin fuskar shanu Dana magantu wai ummansa yakejin kunya.


Bar dan ....kinkusa maganinta .



Megadi ne aguje da buta tare da redio a hannunsa Yana kokarin kaiwa ga wawakeken gate din daya Kara kawata gidan har sai da redion ta subuce Masa garin sauri .



Horn ake tayi tindazu gashi yana toilet sakamakon shidin ma,abocin Shiga bandakine hakan yasamo asali da sabuwar cimar daya samu wadda Bai sababa shine dayaci takan rude Masa ciki Musamman ma da abincin baya dahuwa ake bashi bakuma dan bata iyaba ne matar gidan tsabar muguntace tasa sai ya kusan dahuwa sai ta ibarwa sirikarta tare dashi me gadin domin tace mijinta ne a hakku data dafawa abinci,

inkuma da Yan wulakancin dasukafi wannan akanta takance bazata dafaba.

Bayan bude gate dinne wata zungureriyar mota taturo hancinta bakowa bane sai alhaji sabo bayan yin fakin dinsa me gadine Yakuma bazamowa ya bude Masa kofa tare da risinawa domin kwasar gaisuwa Yana kokarin karbar jakarsane ta bayansa ake gargadinsa wai Kai har sonawa zance maka wannan aiki nane kai dai katsaya a gadinka.




Murmushi alhaji sabo yayi yace ke kuwa sadiya Banda abinki ai temaka Miki yayi bakya ganin nace Miki da ummata ce take tarena Inna dawo yanzunko ganin kina tare dani yasa ta hakura tabar Miki kema sai kiringa yin hakuri da taimakon baba ko ya Kikace?


Wani tukullimine ya tokare Mata daya ke mata zancen ummansa komai ummansa komai ummansa zaku gane shayi ruwane .

Afili kuwa murmushi tayi tace ai umma uwace Kuma tasan yanzu fadar tawa ce shiyasa dama dan baka da mekula dakaine .


Suna tafe suke Wannan zancen Kuma tanayi ne dan ta janye hankalinsa har yamanta dashiga gurin ummantasa daga bisani tafuskanci hankalinsa yayi can aiko kamar ta kurma ihu.

Yace muje induba ummata ,

Murmushi tayi tace ka kyaleta yanzu nadan bata fanadol tasha Kuma tace kar atasheta sabida kanta ne Yake ciwo .


Da damuwa afuskarsa yace Aiko bazan iya tafiya ba sai naganta bara indan dubata .

To Kuma Inka taba kofa Taji motsi ta farka fa kaga kakuma sa ummata kanta ya amsa dan Allah ka kyaleta in kayi wanka sannan ta farka sai muje mukuma dubata.


Hakadai yabita badan yasoba .


Suna zuwa ruwan wanka ta hada mar sannan tagabatar mai da abinci dakar yaci domin Yana tinanin ko ummansa taci har sai da ya tambayeta .

Tayi murmushi tare da juya kwayar idonta harsai da yadokantu gareta tace ai kasan bamu Saba cin abinci ummanmu bataci ba kafin nabata maganin sai da nayi kokari taci har Saida tayi gyatsa don haka kaima cika koshi.

Kadan yatsakuri abinci dan hankalinsa Yakoma kanta Musamman data dameshi databe tabe Haka ya biye Mata sai gasu a other room bayan komai yai normal takara matseshi yadda bazai iya mikewa ba ,

Batare datasani ba shima biye Mata yayi nan da nan bacci yayi gaba dasu.


Itako ummansa tin shigowarsa ta jiyoshi takuma ji sanda take kokarin hanashi zuwa gunta tin tana zuba Ido har sai da bacci ya kwasheta batare da yazo ba.


*INA BUKATAR* *COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*

🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAUπŸ™‹*






πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€

😨😨😨😨😨😨

πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™

*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹


πŸ…Ώ *8(H)*

🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝



Hajiya amina ce kwance tinanin duniya ya isheta tin misalin karfe uku tafarka tasaka wannan ta kwance wannan.

Tarasa meke Mata dadi itadin macece mekawaici akalla intace zata dauki mataki Kan sadiya bazayyiwa sadiyar dadiba.

takanyi tinanin inhar tace zata rabata da sabo tokuwa itama tata Yar dake gidan nata mijin baza ayi Mata uzuriba shiyasa take yin hakuri da duk wani cin Kashi datake mata hannu tadaga sama tana yimar addu,a Musamman datake hango irin musibar data kunno Masa Kai dan sadiya alamu sun nuna zamansa da ita bashida alheri Musamman yadda take gani da Jin take takenta.




Tinani tashigayi na irin wuyar dataci da yayanta.


Su biyu ta haifa sabo shine babba sai mardiyya tazarar shekara biyune atsakaninsu sabo Yana dan shekara goma Sha biyu mahaifinsu ya rasu bayan share makokine dangin babansu suka nemu tafiya dasu ,


Alfarma ta nema abarmatasu dake Suma basu zafafaba sai suka amince abubuwa da dama ne sukasa tace abarsu gunta batun yauba tasan ko mahaifin sune ya nemi taimakonsu sukance Suma nema suke Kai ko rashi yatashi dashi yadau kwano a matsayinsu na Yan uwansa yace azubo Masa abinci to tabbaci hakika ko sunbayashi sai gori yabiyo baya.


Sukanje duk juma,a su gaishesu ko lomar abinci bata hadasu ko angama dafawa insunje akan mayar da murfin tukunyar sai sun tafi sannan aci.

inko akaga basannan zasu tafiba akan ringa cin abincin cikin hikima yadda dai baza,a zuba musuba ,

Suma dake yarane masu nutsuwa in rabo yarantse an zubo sukance akoshe suke to tin Yana darai kenan balle da kasa ta rufemar Ido.

Rayuwa ta wahala mun dandanata tin Ina Yan saide saide muna cin abinci sai da yazama mun cinye jarin aka wayi gari abinda zamuci ma Yana gagararmu sai Kuma na lura wannan hadisin Yana yawo akanmu yadda tsuntsu Yake wayar gari bashida me bashi Kuma yakan wuni a koshe.

Duk Wanda ya wayi gari a Kano yasan gidan hajiya mariya,

indai kanada matsalar abinci ko almari to kuwa inkadaurewa layi da cunkoso tare da turmutsutsu to kuwa zaka samu agidan sadakace sabida Alla suke rabawa ,

tonima nan nake buga sammako bayan nasallamesu sun tafi makaranta nakanje nabi layin masu karbar abincin sadaka innakarbi na safe nakan dawo gida inbasu suci sannan sun dawo daga makaranta nikuma inya ragu sai inci ragowar bayan munyi sallar azahar sai sutafi Islamiyya nikuma sai inkoma karbo Mana na dare shima nakan Kai magriba bandawoba nakanzo in taddasu a kofar gida suna jirana .


bayan nazuba Mana abincin munci nakan rage wani domin su samu suyi Karin kumallo dashi ,

Zuwan nawa sai Allah Yakuma kawo Mana dauki domin innaje gurin karbar abincin nakan zauna muna yin hira da almajirai Mata dake gurin dake gurin unguwa ce ta alhazawa haka zasuyi ta Miko sadaka muna karba wannan kudin nakan tarasu domin bukatun yau da kullum yazamto yanzu indai matsala ta taso ko ta rashin lafiya ko ta makaranta banida damuwa domin Ina tara Yan kudadena.


Anan Allah ya hadani da wani mutum me sunbo tanko shima zuwa Yake karbarwa iyalansa abinci yadda yake cemin shima yara ne dashi guda uku sai kanwarsa dake kula dasu itama bakarfi ne da itaba bazawarace shine Yake futa Yana samo musi dan abinda zasuci .

yace lokacin danake da dan jarina haka zankasa Kuma in kwashe kinsan mutanamu mune muke durkusar da kanmu memakon kayi kokarin siyan kayan da talaka yakasa kodan yasami na abinci amma Ina sai katafi siyan nawanda yafi karfin ci dasha ,

yace ba irin buga bugar da banayi ke daga karshe natsaya akan kayan gwari aiko dake jarin bawai Wanda zai ja hankalin jama,a bane kaina.

sai aka wayi gari albasar ta dafe tsabar dadewar datayi ba,asiya ba suko su timatir haka nadinga watsarwa danaga basarki sai Allah ragowar kayan gida nakai sukayi Miya dasu Haka nakoma bawan ba kanin ga iyali haka na hakura hakurin dole nake tahowa nan tin daga burget da kafa nake zuwa karbar abinci gurinnan Kuma nakoma da kafa.


Bayan mun daidaita andaura tare da cewa ajalanne sadakin ba lakadanba .
yakan je yasamo abinda Allah ya bashi agidan muci dan sukansu yayan nasa sawa nayi suka dawo nan na hada danawa itakuma kanwar tasa dama akwai mesonta rashin inda zai Kai yayanne ya hanata aure to kuwa ana kwasominsu itama tayi aurenta shi Kuma gidan dama nasune sai yazuba Yan haya ciki nikaina auren dolene gudun kar awayi gari sunan yayana ya bace ya koma yayan mace don kadan daga aikin mutananmu ga inda yakamata suyi magana amma bazasuyiba sai inda ba,a sasuba.

Rayuwa muke cike da godiyar Allah domin komai atakure yake duk inda bawa yajuya badadi amma inbanda haka ace duk cikar unguwa arasa Wanda zai tallafawa marayun Allah Koda da lomar abinci ne Koda Yake ABINDA KE FARUWA KENAN sai dai ka leka waje kaga anfuto da abinci an zubawa akuya memakon abawa mabukata niko rubabban aka bani zaimin amfani ko wankewa nayi in shanya innayi wani tinani sai ince to wandama yakasa baka loma daya inashi Ina baka Wanda zaka shanya haka .


Da wuya tayi wuya sai nakoma wankau ban ritsa wata inayiba sai ga kanta a hannuna gashi banason yarannan maraici yatabasu shikansa megidan yanzu yakwan uku baikarbo Mana abincinba sakamakon masassarar dake damunsa inda Allah ya temakeni nasa yayan sundan fi nawa girma sukan saka hannu muyi wankin tare .

A haka sabo da mardiyya suka gama makarantarsu.
. dama su nasa yayan basayi Kuma ban dorawa kaina wahalar sasu ba dannauyin sai yayimin yawa.


Tafi tafi saiga sabo da mardiyya sun kammala karatunsu na secondary ammafa mun doku dan sai da aka wayi gari sutturar sawa tagagaremu amma cikin amincin Allah innadan Tara kudina nakanje wanbai indan tsinto musu kayayyaki .


Shidai sabo ya kafe sai yacigaba da karatu Kuma ban hanashiba nadai bishi da addu,ar neman sa,a da Kuma huwa cewar Allah.




*INA* *BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*

🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU*πŸ™‹



πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€


😨😨😨😨😨😨


πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA* πŸ™‹


πŸ…Ώ *9(I)*



🌈 *KAINUWA WRITERS*
✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝




Asanda yasa kansa karatun asannan matsatsi Yakuma zuwa rayuwarmu.

Asannanne dukkanin yaran dake gabana suka girma Kuma kowacce tana bukatar abin amfani narayuwa danma wani gida dake daura da gidanmu sun nemi da nabasu yarinya daya taringa zuwa tana Mata dan aikace aikace sai nagayawa megidan ,


Babbar cikinsu wacce take da hankalin sosai ita take zuwa aikatau din da haka muke rage wasu abubuwan Dan matar gidan takan bata Yan tsummo karanta dasu suke da yin gayu ,

cikin amincewar Allah komai ke gangarawa shi Kuma sabo yakan je yayi turin ruwa akalla kullum yakan Sami dubu daya ita Mike tarawa har Allah yasa akasami kudin registration sai ga sabo yafara zuwa University intakai cemuku dai ahaka yayi karatunsa in Yana da lakca yakan hakura da turin kurar sai ya Sami interval sannan yakeyi cikin amincewar Allah ya kammala a hankali cigaba Yake zuwar Mana domin yanzu duk na airar da yaran dake gabana daga mardiyyar har yayan malam tankon danake aure.

asannan Kuma dukkanin wani cigaba yakara zuwarma na dan wuyar da mukaci da yan zun alamu sun nuna muna dad da ketaresu domin sabo yasami aikinyi bakuma nagwamnati ba wani iyamurine yadauke shi Yake kular Masa da kantinsa cikin aminci suke zaune in lokacin tashi yayi kullum Yana bashi dubu daya ga taimakon dayake Masa na sutturu da abinci basuyi shekara biyu ba yafara yimasa zancen sallama .


Yace lokaci yayi dazan sallameka kaima kazama ubangidan kanka akwai kudade danake tara maka kullum inkatashi daga tsarin shago sannan akwai alherin dazan maka domin naji dadin Zama dakai Kai me amanane baka cutata.


Sanda zai sallameshi million biyu yabashi da mota sannan ya zuba Masha Kaya ashago yace yabashi halak malak.

Zokuga umma ranar har suddaja tayi saboda godiya ga Allah .

Aiko kudin dayake tarawa yadakko yase katon fili,

Inda kudi akwai aiki gini yayi amma bai gina gaba dayaba sai yaginawa ummansa iya gun da zata zauna kafin Kuma acigaba , ranar dazasu koma gidan suka tashi da mummunan zance domin gawar mlm tanko akashigo musu dashi ansami wani yabugeshi ya gudu.


Banida caji kuyi hakuri da wannan.



*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*

*DAGA* *ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU*









πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€


😨😨😨😨😨😨


πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™

*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*


🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹

πŸ…Ώ *10(J)*

🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝




Sunyi kuka sunyi jimami domin sunyi rashi yatsare musu abubuwa da dama Musamman dayakasance yana tare dasu ya maye musu gurbi dayawa Wanda ko danginsu dasuke dolensu basuyi musuba walau na uwa ko na uba dan sanda yakamata su rungumesu bawanda yake lura dasu ko ta tarbiyya bare na abinda zasuci malam tanko yasha sasu suje su gaida dangin nasu amma ko sunje sukan nuna dasu da babu duk daya .


Bayan anshare makoki da mako daya suka tare agidan kafin sutafine tayi magana da dangin malam tanko akan zaman yaran gurinta to dake sudin sunsan yakamata daman ko lokacin da matarsa ta rasu sunso daukarsu shine dai yaki haka suka tattara yaran suka tafi dasu .


Tayi murna tayi farin ciki bata taba tinanin samun sauyin rayuwaba sai gashi Allah ya musanya Mata da mafificin alherinsa domin duk inda tarbiyya take tsakanin sabo da mardiyya sunsameta sannan ga wannan tagomashin da Allah yayi musu .
basu ritsa shekaraba agidan mardiyya tasamu miji cikin kankanin lokaci akayi bikin batare da bacin lokaciba asannan shima taringa yimasa nuni da yayi kokari yasamo matar aure.


Yakance nifa umma ba yanzu zanyi aureba .

Sai tayi dariya tace toni dai yanzu abinda yaragemin kenan auranka nake fatan Allah ya nunamin .

Zanyi karki damu sonake sai nagama ginin gidannan gabadaya,

To ai wannan mesauki ne mezai hana gidanmu da muka taso kasashi akasuwa sai kakarasa ginin da kudin .

Bayan ansiyar da gidanne ya hada da wasu daga cikin kudin gurinsa aka karasa sannan ya zuba mata kujeru da Yan tarkacen gida .


Duk dai a runtsin Allah ya hadashi da wata yarinya sunje siyan Kaya gurinsa aiko tinda taganshi ta makale masa musamman data shi yaro ga kudi Kuma Yana juyawa shima Kuma dama ya kyasa.

har yafara zuwa gidansu zance tin anan tafara fuskantar irin matsalar dazata fuskanta akalla yaje zance kusan so biyar gidansu bakuma shi da hirar komai sai ta ummansa tin tana biye Masa har tafara Jin haushi takuma fara Jin tsanar matar .

Wata rana yazo yake ce Mata tashirya gobe zaizo suje ta gaisa da ummansa.


Aiko da misalin karfe biyar yazo ba bata lokaci suka tafi gidan
tarya hannu biyu umma tayi Mata tayi Munna da kawota dayayi ta Kuma yaba da hankalinta .


Sai dai kanta tafi sai ta fuskanci irin kallon wulakancin da sadiyar take Mata tare da taunar cingam na rashin kunya har wani hurashi take inyayi billi sai ta tauneshi haka zai bada Kara karasassss.


Bayan yakaita gida yadawo umman tasa yatarar tayi tagumi cikin dagin hankali Yake tambayarta meke damunta?


Ajiyar zuciya tayi sannan take cewa niko sabo wannan yarinyar ko tadace dakai ?


me Kika gani ummana?

Shima ya tambayeta ,


Nayi Mata kallon Mara tarbiyya da farko yarinyar ta kwantamin daga bisani nafuskanci kamar batada tarbiyya.


Murmushi yayi yace haba umma Allah lafiyayyi yace domin ko Ido bata yarda mu hada da ita karshenta shedanne danyaga kin yaba shine zai tinzira minke Allah ki kwantar da hankalinki batada matsala.


Ahaka aka cigaba har Allah yasa yaje gurin Yan uwan mahaifinsa yanemi alfarmar sukai Masa kudin aure sunso su hanashi amma da sukayimar kallon tsaf sai sukaga baya neman tallafinsu aiko jiki na rawa suka karba bai barsuba sai da yabasu har kudin mota tare da kudin dazasusa a aljihunsu sai ko aka hau kirarin addu,a ga mahaifinsa .


Murmushi yayi tare da yin sallama garesu ya koma inda yafuto.


Abinda Yake damun sadiya Bai wuce ganin mahaifiyarsa tarigata Shiga gidannan ba Tasha tsara rayuwarta akan ita kadai zata rayu da mijin ta Bata yarda da iskancinnan nadangin mijiba baza,a takura mataba tayi aurene Dan ta huta bawata Yar kwal
uba dazata rabesu bare azo a hana su walwala bakuma ta bukatar ko wace tace zatazo tashiga hurumin gidanta bare azo ayi Mata kafafar wanane kodan Yar babatane balle su uwar miji suji labari tamafi tsanar ace uwar mijin da zata aura tana raye karshen matsalar kenan in suna hira da kawayenta sukanyi shewa suce nifa uwar miji inda kikasan ciwon dan yatsa haka nadauketa, hhhhhh ke da sauki ma nifa da,ace Ina da uwar miji gara infasa auren ,Medan dama damance takance ni banida matsala da ita matsalar dayace ace tashiga hurumina tofa anan labarin zaisha banban .

dan haka suke da iko kana tare da mijinka cikin kwanciyar hankali sai kaji yace abinda yasa kikaga ban siya Miki ankonnan ba babatace take bukatar wasu kudi shiyasa to Kuma sanda Zan baki sai akasami akasi shine nabata kudin daxanbaki kidan jinkirtamin zuwa wani lokaci toko kunga ai akwai matsala ,shewa suka sake sawa tare da addu,ar Allah yarabu da ciwon ulcer Allah yasa ta kwanta dama Kan mu isketa.


To Kuma sai gashi ita gida daya ma zasu zauna
Inda ta lura Kuma baya hada babar tasa da komi dan ko maganar ta zayyi sai ya kwantar da muryarsa duk saboda girmamawa.


Ansha shagali cikin farin ciki amarya ta tare sungudanar da daransu cikin kwanciyar hankali Dan har makara sai da sukayi hakan Kuma bai hanashi kokarin tayar da itaba domin Shiga kitchen tare da jaddada Mata ummansa tana jiran break fast domin ya lekata da ya idar da sallah har sannan barcin gajiya take shiyasa yakeso kafin tatashi sai dai tatarar da abinci daga sirikarta.


Hakane yasa ta kullaceta domin yadda take karantawa a novel ba hakace tasameta ba memakon tafarka taga ya girka Mata ko Kuma ita umman ta Aiko Mata dashi amma sai sabanin haka ace ita kamar ita amarya ba a temaka mataba har za,ace ta tashi ta girka.



Dafarko taso takai zuciyar ta nesa tana kula da ita Musamman dataga duk duniya bashida farin ciki sama da ya kyautata wa ummansa sai taga abin Yana neman wuce gona da iri abinci bazaici ba sai yaje yaga in taci sannan zaizo ya zauna yaci komai baya bawa muhimmanci sama da ita shiyasa itama taga fa intayi sake za,ayi ba ita.

Ajiyar zuciya tayi tare da juyawa zuwa daya hannun idonta yayi jajir tabbas inta bari sadiya tayi galaba Akan danta to kuwa zuciyarta tana iya bugawa.


Karimatu ce take bawa yaranta umarnin kowa yacire uniform dinsa yasa a ruwan omon data jika.


*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*


🀝*DAGA ALKALAMIN YAR* *MUTANAN JINGAU* πŸ™‹







πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€


😨😨😨😨😨😨


πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™

*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*
🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹

πŸ…Ώ *11(K)*


🌈 *KAINUWA WRITERS✍🏾 ASSOCIATION* 🀝



daya bayan daya sukaringa cire kayannasu suna sakawa acikin ruwan omo wannan yazame musu jiki dake tana rigasu dawowa takan dawo gida daya saura sukuma sai daya da kusan rabin suke dawowa,

tana shigowa gida take zazzaga omo cikin roba ta zuba ruwa duk Wanda yadawo takanyimar tinin cire Kaya yasa aciki ita Kuma nana tana dawowa before sutafi Islamiyya saita wankesu

Please Login or Register in order to submit comment