Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuboba Dana hanasu balle inso yarana sugani Musamman nana datake da hankali yanzu domin wani lokacin intaga irin Fadi tashin danakeyi takancemin umma kirage wani abun abba yayi,

dawainiyar dakike tana wahalar dake gashi inkina munnar dauko albashinki sai Inga ko dubu biyar baki ragewa ajakarki.

Sai inyi murmushi ince haka dama rayuwar take gara kisaba dayawa yayinda mace tashiga dakinta dukkanin wata dawainiya tahauta,

ke awannan zamaninma harda batataba hawa kanta take danma Allah yatarfawa garina nono akwai aikinyi.

Irin wannan hirar damuke da ita shiyake tabbatar min da hankalin dayi.


Washegari bayan muntashi da asuba munyi sallah tare dayin abinda zanyi wanka nakewa yara shikuma shu,aibu Yana shafa musu Mai tare da saka musu uniform itako nana tana kitchen domin hada abun kari muryarta naji tana cewa umma ba Madara takare Kuma suger din bazai Isa ba .

Nace Mata to Ina zuwa,

Wani tinani nayi daya hanani bada kudin daza,asiyo gurin shu,aibu nadosa nakecewa Babu Madara da suger ko za,a siyo,

Dago kansa yayi takalleni yace to bara asiyo cikin mintina saigashi yadawo ,
Inacikin aikine yakecewa kuzo kutafi bakwai da rabi tayi karku makara nakara muku aikin .

Kowa ya futo nice nashiga domin daki domin inyi Masa sallama nace nafito sallameni Zan wuce kudin abincin dayasaba bani suya dakko yabani ganin Basu kaiba ne nayi magana amma sai yace kin manta nasiyo muku Madara da suger aciki Aina dauka.


Girgiza kainayi nace ok Kai yanzu Dan Allah dubu dayan yanzu kafasa kadauki dari da sitiin din dakasiyo Mana abin Kari Kuma har inzo inyi girkin dare da rana ranmu munawa haba shu,aibu ana sasanta rayuwa mana in ansamu asan ansamu tinda....
katseni yayi bayan yayi Dan karamin tsaki yace keyanzu Dan Allah kudinnan ne bazai ishekiba baki tabacewa bazai yi mikiba sai yau kiyi yadda kikasaba kawai .

Nace tom amma dai kodayake karmu makara sai mundawo .

Addu,a yayi Mana sannan muka tafi a kudin daya bani mukatsaya a kanti nadan siya musu abin makaranta sannan nadauki naira dari nabawa nana tayi kudin mota ,

Kuyi manage zuwa dare Insha Allah


pls share
*INA BUKATAR COMMENT* *DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*


🤝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* 🙋








🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀


😨😨😨😨😨😨


🙏 *ABINDA KE FARUWA* 🙏


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*


🤝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* 🙋


🅿 *18(R)*




Akwai masu aikin gini a bakin makarantarmu bayan antashi gurinsu natsaya nayi musu bayanin son azo ayimin aiki agida ,

Kwatance nayi musu nagidan danake bayan sunzo sunganine suka yi min lissafin kudin da aikin zaici bawani meyawa bane siminti guda biyu nasiya sai yashi a wunin ranar akayi aikin aka gama dama karashene aikin ,

sai rufin dakin daza ayi muna da kwano katako nasa akaje akasiyo banida matsalar rufi domin sana,ar kaninace haka nasa yazo yayimin Kan wani lokaci saiga daki yafito amma fa zancan gaskiya natike danna kusayin kat ,

haka nace abarshi banida kudin sili wannan ma Dan karshen watane anyi Mana alert gashi dama banshiga kasuwa ba haka nasa kudin agaba aka gyara dakin da hajiyarsa zata zauna.


Sanda yadawo yagani murna sosai yayi tare da yimin godiya kamar nayimar kyautar wani Abu me muhimmanci kasa shiru nayi tinda nidin bame shiru bace nace ninayi domin Allah Kuma batun yauba nace duk abinda nayi agidannan kadena godemin domin innatashi yin and jinake kamarni Allah yadorawa dan Hala nagode kadenaimin haka banaso,

Shinan baisan magana nafada ba domin cigaba yayi da godiya har Saida haushi yasa nabar gun.

Umma ce take ta faman leke domin tin Jiya dasafe rabonta datasa dannata a ido yadaizo yayi Mata sallama dazai futa harta raba gardamar kinbarin sadiya dayayi taje unguwa tun daga sannan kuma bata karajinsa ba ,


Tana kokarin futowa taje bangaren nasune taga ko lafiya sai gashinan cikin Shiga takamala da nutsuwa yashigo zubewa yayi kasa Yana gaisheta (Allah sarki uwa )sai yashe baki takeyi domin Jin dadin ganinsa ,

har nashiga fargaba danaga jiya baka shigo ba Allah dai yasa lafiya ?

Shiru yayi Yana tinanin yadda akayi jiya Bai leko ummantasa ba , yace wallahi nasha afa nakuma rasa meyadau hankalina daban shigoba.


Sadiya ce tashigo afusace tace nifa jiranka nake shiyasa nace kashige muje inkadawo kagaisheta kana batan lokaci kasan likitocin bajirana zasuyiba,

Kallo yabita dashi domin bashida abinda zaice,

Tajuya idonta tace kana kallona katashi mutafi,

Mikewa yayi bamusu yabi bayanta ko umman ma datake Masa magana baisaurara ba shikansa jiyayi kamar Ana bashi umari tinjiya Yake fama da Al,amuranta komai gadara gadara takemar inyayi yunkurin tsawatar Mata sai yaji kamar Ana bashi umarnin yin abinda takeso,

Bayani wata biyar komaima yafaru ciki ko harda faman da umma tayi na auransa Wanda badan Allah yasa da rabon aurenba dabaza,ayishi dan alhaji sabo yanzu ganinsa agurin umma sai ancike form dakaar tasamu akayi auran ,sai dai muce Allah yabada zaman lafiya,


Ayanzu ko sadiya haihuwa ko yau ko gobe tanacin wuyar cikinnan da farko kamar bazai bata matsalaba sai da abin yazo gangara takeshan fama akwai randa tatashi da matsanancin ciwon ciki harsai da aka kirawo mahaifiyarta anzatama cikinne zai futa karshe ma batasan sanda aka futa da itaba,



Sintiri take domin tarasa yarda zatayi ga bakin Hali mutum har biyu acikin gida amma Taki kiran ko daya dama umma Bata yankayanta bare Kuma kishiya dahar yau ba,a Bata mijiba itakanta batasa akaba Dan ba dadin abin tasaniba bare adaga Mata hankali.


Tin tana ciwon da dauriya harsai da tafarayi kamar zararriya dukan cinyarta tafara kafin ta cixge dankwalin kanta murkususu take kamar zatabat duniyar gata ita kadai adaki

pls share

*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA*


🤝 *DAGA ALKALAMIN*
*YAR MUTANAN JINGAU* 🙋










🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀


😨😨😨😨😨😨


🙏 *ABINDA KE FARUWA* 🙏


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*

🤝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* 🙋


🅿 *19(S)*



🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🤝




Dakar take Jan jikinta ga haihuwa tataho amma batasan yadda zata taimaki kanta ba ,

nishine yataho Mata hade da tahowar wani abu agabanta hannu tasa tashafo jinwani abu tayi kunduldul yatokare mata hankalinta Yakuma tashi ga azabar ciwo ,


Haka tayanke shawarar kiransu dan dole badan tasoba amma cikin ikon Allah takasa yunkurawa data matsa sai ta mikene tatake bakin zaninta aiko abin tausayi menakuda akasa Jikake tim inda Allah ya temake tama goshin tane yabugu,

hakan yayi dai dai da shigowar me gidan aguje yayi kanta jijigata yashiga yi amma dake ta bugu sosai ga Kuma halin ciwon daya gala baitar da ita sai tatafi luuuu,



Kaiwa Yake Yana kawowa yarasa mezayyi gashi su kansu likitocin tinda suka Shiga da ita bawanda yafito tinanin Kiran iya yanta yayi Aiko cikin kankanin lokaci sai ga Yan uwanta sun cika asibitin kowa yayi jugun jugun,


Aikin yafi karfin nurses sai da suka Kira likita babba, bayan zira safa ahannunsa yashiga dubata anan yagano inda matsalar take wato dan jinjirinne badai daiba sannan hannunsa yashige wani dan lungu acikin gabanta,

Haka yasa hannu yadinga juya dan cikin ikon Allah sai gashi yajanyoshi waje ,

Wata Kara tasa data gigita alhaji sabo da Yan uwanta can Kuma sai suka jiyo kukan jinjiri ,

Sannu doctor din Yake Mata kafin yabada umarnin a gyarata ita da jinjirin ga Kari data samu kusan guda biyar haka tanaji tana gani suka dinketa kamar kwarya( Kai yau sadiya taga banu domin manta kanta tayi)tanaji tana gani aka daureta before ayi Mata dinkin.


Bayan bakin gumurzun datasha ne akafito da ita dakin hutu aiko dangi sukayi ta tururuwar ganin me jego da dan jinjirinta,

Shiko angon karnin sai mika wuya yakeyi , yayarta ce ta hangoshi tayi dariya tace kubashi guri Mana muntsare masa abin kallonsa karya kasa hakuri yabi takanmu, Aiko meza,ayi Banda dariya,

Shiko cikin Jin kunya yakarasa ciki hannu yasa zai dauki yaron tare dayi mata sannu yayi Kuma daidai da tambayar da suka jefo Masa narashin ganin babassa tare da abokiyar zaman sadiyar,

Jiyayi kamar andaki tsakiyar kansa sai sannan ya tuna da su ,

Shaf ya manta da Suma ko tinanin su bayayi yanzu yakan shafe kwanaki bai je yaganta ba balle wata amarya da baije yaganta ba balle yakara tantance yadda take,

Wayarsa yadakko zai buga mata hannun sadiya ne yariko wayar dayake kokarin bugawa,

Cikin hawaye take magana bana bukatar kowa acikinsu domin sune silar wuyar danaci nanemi taimakonsu sanda nafara ciwon bawanda yakulani daga karshema umma cewa tayi Allah yasa na mutu nida dan, hawaye take zubarwa kamar gaske ,

Aiko dukkaninsu sukayo kanta dama bakyajin dadin Zama da ita ko kuwa?

Take dama hakuri nakeyi shikansa yasani gashinan akwai randa tace ma zata dakeni sai da nagudun gudun kartayimin illa Kuma Ni ba iya ramawa zanyiba kodan darajar danta.


Jiyake kamar yafashe saboda fushi yaji baya kaunar yaganta ma bare har yace mata wadda bata kauna ta haihu yanzu umman sace take masa haka baice komaiba yajuya afusace yafuta.

Sukuma dangi sunsamu abinyi sai aka bude babin gulmar takurar da uwar mijin sadiyar kemata harda zancan auran datayi masa kowa ya tausaya mata dimin tagaya musu cewar tinda yayi auren hakuri takeeuwarsa tasa yajuya Mata baya yanzuma Dan haihuwa tayi suka ganshi .


Tinda yakoma gida Yake fama da bacinrai yaso daurewa aje yaga mahaifiyartasa amma wani bakin ciki dayakeji akanta shiya hanashi zuwa,


Itako baiwar Allah dukkanin wata damuwa tasaukar Mata domin sanda yafuta da sadiyar taji tashin motarsa lokacin ameera tana gunta suna hira Jin tashin motar bana kwanciyar hankali bane yasa suka fito amma tini yayi gaba ,

Megadi ta tambaya lafiya ?

Anan yake gaya mata matar gidance ba lafiya addu,a tayi mata suka koma ciki batasan asibitin daya kaita ba bare suje ita da ameera haka suka hakura suka zubawa sarautar Allah Ido sanda yashigo gidan tajishi jira take yashigo taji meke akwai amma har yashare fiye da minti goma ba labarinsa,

Yankewa kanta shawarar binsa tayi ,da sallama tashiga falonnasu Yana zaune yayi tagumi cikin firgici sukayi kicibis da juna aguje ya Mike yayi cikin daki itama juyawa tayi tafita da sauri tsna Kiran innnalillahi wa Inna ilaihirraji un,

Tinanin ta gamo tayi shikansa yazata gamon yayi amma Kuma ai muryar ummansa yaji tana sallama meke faruwa ne.


Hala tashiga nata dakin tana me maimaita addu,a a bakinta ameera ce ta tareta tana tambayar ta lafiya ?


Garu tabi tadinga yin kasa domin jitayi wani Abu na yawo akanta,


pls share

*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*

🤝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* 🙋








🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀



😨😨😨😨😨😨



🙏 *ABINDA KE FARUWA* 🙏



*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*


🤝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* 🙋


🅿 *20(T)*


🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🤝

bayan kwana uku dayin aikin ne nashirya yara muka tafi gidanmu
Domin gaisheda iyayena Yan tsince tsince nayi domin kaiwa mahaifiyata sannan na tsaya a hanya nasiyawa babana kilishi,


Tayi murna daganina balle da taganni da yan jikokinta haka tadinga tsokanarsu suna yin dariya nikaina naji dadin zuwa Dan bacin ran danakeji acikin kaso hamsin yanzu babu ashirin abin da da uwa duk kokarin kiyayewar bayyanuwar bacin ran danake ciki Dana dinga kokarin yi hakan baisa takasa fahimtar halin danake ciki ba,


Tace wani abun yana damunkine karimatu?

Kallonta nayi nace ummana mekika gani?


Tayi dariya tace hoo karimatu sarkin basarwa to ai shikenan adai cigaba da hakuri yabon da mahaifinki Yake miki kiyi kokarin cigaba da zama akai yau shekara goma sha bakwai kenan da aurenki baki taba zuwa kin kawo karar mijinki ba haka shima,

Dan haka acigaba da hakuri kinji dama ita rayuwa inhar kanaso kayita da salama ka Kuma tadda ubangiji a wanke to akwai kalubale sosai dan haka sai acigaba da hakuri.

Nace ummana sai dai acigaba dayi min addu a Dan Ina bukatarta sosai
zankuma yi kokarin bin shawar warinki insha Allah Dan dasu nake rayuwa,


Bayan munyi sallar azahar ne muka shirya domin tafiya Dan inason biyawa domin taho da hajiya,

Sallama mukayi nida yarana amma sama da mutum goma zaune agun amma bansamu mutum uku dasuka amsa mana ba,

Haka suka dinga gaida kakannin nasu da kannan babansu wayanda suke zawarci dagani kasan akwai magana domin Dakar suke amsa musu Niko danayi musu gaisuwar gaba daya basufi su biyuba wadanda suka amsamin,


Dakin hajiya muka nufa akwance na hangota ta kudundune kanta nayi da sauri na budeta jikinta zafi rau kamar wuta ,

kamata nayi nana ta taimakamin muka dagata,


sakko nana Khadija nayi nasa shawul din Dana goyata nadinga daddanna Mata jikin da ruwa har sai da zazzabin yasauka,

Dube dube nahauyi domin samun abinda Zan bata taci bakomi adakin sai guntun kwaki futa tsakar gida nayi nake cewa indame abinci yasammin zanba hajiya kafin mutafi asibiti,


Munafunci dodo jiwani abu canake dazunnan nata yayan suka tafi bawanda yayi kokarin hakan saike saboda neman gindin zama to ita kanta yanzu bama ta tata balle ke uwar asugi,


Bance komaiba najuya nakoma dakin kayanta nashiga hadawa duk da bawasu masu yawa nadiba ba sannan nasa yara su samomin adai daita ,


Zainab ce take leken habibu saboda tanason tatafi gida kamar yarda yace tatafi data fuskanci bayagidan cikin sauri tahau hada kayanta domin ta tsorata da Marin daya yimata Bata hada minti biyar ba tabar gidan .


Shiko gogannaku sanda yafuta daga gidan baizame ko inaba sai wani gida dayamayar gurin hirarsa abinci matar take siyarwa bakalar namijin dabaya zuwa gun tana da ya budurwa to ita yamakalewa,

uwar tana soro tana sana,a sukuma
marasa tsoron Allah da gudun kar,ayiwa yayansu suna ciki suna shakiyanci da yammata ,


Bayan yagama cin abinci ne a gidan akahau shakiyanci da yammata ,yanason yarinyar sosai itama tana sonsa acikin hirar ne Yake cemata nakusa aikowa fa anemamin auranki,

Baki tayage tace ni awa dazanyi kishi da matarka aini wallahi tsoronta nakeji balle tinda naga gurin aikinku ba,asami wadda tayi Mata kwacenka ba nasan tafi karfina.

Yoo wace tafi karfinki Zainab din to kwantar da hankalinki da ita da Babu duk daya matar da ko cikakken nono batadashi keko nasan komai yaji Dan haka kikwantar da hankalinki kece ta gaban goshi,


Aiko taji dadin yabon dayayi mata da haka yagama kushe matar tasa sannan bayan ysji Kiran sallah ya Mike domin tafiya gida ,

Abin allah da Kuma zaluncin dayayiwa matarsa tare da karbar addu,ar ta da Allah yayi Yana cikin tafiya yazo zai Dora kafarsa Kan silaf din kwata Aiko yazame ji kake kasssss kashin kashin cinyarsa ya balle Aiko ya balle baki yana kurma ihu Allah yasa ba,agama Shiga masallaci ba mutane suka tattageshi akayi gun megyara dashi bayan bakar azabar dayasha tare da sumewar daya dinga yi har Allah yasa aka gama gyaran sannan aka debeshi akayi gida dashi,


Tagumi suka zuba anrasa me magana acikinsu tin ameera tana sauraranta har tagaji da shurun ta tabata ,


Dagowa tayi ta kalleta tace ameera meyake faruwa ne narasa abinda zance sabo yanzu yafi karfin ganina naje da kaina danne mansa sai mugun gamo danayi agunnasa ,

ashe lokaci yayi da uwa zata haifi danta duk wata wahala Tasha da abunta baka nemi daukin waniba sai na Allah ameera anrabani da dana yazanyi ?


Ita dai batasan mezatace ba domin kwata kwata Bata fahimci me umman take nufi ba dan bata taba gaya Mata komai ba yo ma har yaushe tazo gidan itakanta batasan ame take a tasan dai an daura aure ansha biki daga bisani aka kawota Wanda har yanzu batasashi a idontaba,


Yau kwanansu biyar da dawowa daga asibiti anatashan shirye shorten suna Kuma harkawo yanzu baya tinanin zuwa gun umman tasa ,barna yakeyi ta kudi kamar bada jiki aka Nemo suba Dan yanzun ma kayan dayasiyo bmata nafutar suna suke gani suna shewa.


Mardiyya ce tazo sakamakon Kiran da umma tayi Mata tasanar Mata da haihuwar Dan uwannata,


Bayan hutawar datayine suka Dan taba hira da ameera dama kosanda suka rayu gu daya tasu tazo daya take zoki rakani Inga danmu sonake inga dawa yayi kama ,


Wuri wuri tayi da Ido Dan da lada in,akace ta koma gun mejegon bazataba Bata mance abinda akayi musu ba ita da umma Randa aka sallamosu da murna suka taryesu Ana Mata sannu da jiki itako da saurinta taje tana kokarin daukar babyn tsawa aka daka Mata bakowa bace Kuma sai sadiyar sannan yayarta takarbe dacewa Ashe kunsan ta haihu to ta Allah batakuba abunda kukaso yasameta Allah ya ketararta Dan haka umma tagaida ashsha,


Jiki a mace ta ja baya ,ita ko umma murmushi tayi take abani angonnawa nagani ,

Turbune fuska tayi alamar bazata bataba yitayi kamar batasan abinda takeba tasa hannu tadauki dan addu,a take tofa masa sai ga alhaji sabo Nan yashigo niki niki da Kaya bayansa megadi ne rike da wadansu ledojin,


Sallama yayi yashigo amma sai yasaki ledojin hannunnasa tare dayin baya dasauri Yana addu,a itama suman zaune tayi sannan cikin firgici ta saki dan Allah ya taimaka uwar nakusa tariko kafarsa ,


Kowa kallonsu Yake domin shidai maboya Yake nema itama hanyar futa take nema ameera ce tariketa suka futa tindaga ranar har yau dinnan fama take ta kanta ko sunansa bataso Taki an ambata .


Mardiyya ce ta katse Mata tinanin da take tace taso muje ,


Tace kije kidawo ni umma Zan Taya Hira haka tatashi tashiga gurin yayan nata



pls share

*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*

🤝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN* *JINGAU* 🙋








🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀


😨😨😨😨😨😨


🙏 *ABINDA KE FARUWA* 🙏


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*

🤝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* 🙋


🅿 *21(U)*



🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🤝




sallama dauke a bakinta tashiga gurin yayan nata bayan gaisuwar da tayiwa mutan gunne Wanda suka amsa bayabo ba fallasa takecewa Allah yasa matar yaya ta iya haihuwa Dan inba mekama Dani aka haifaba lekensa kawai zanyi bazan dauka ba dan bazan yarda kifara da kalarki ba garama kifara da kalarmu ,



Dagowa tayi shekeke ta kalle Aiko baki fadaba balallai ne yazam kingan shiba domin baccima yake ,


Yayarta ce tatashi ta dakko jinjirin ta Mika mata ,


Tace Kai Masha Allah kin iya haihuwa zarkadi duk Wanda yaganshi inba fada akaina sai ace ninayi nakudar tafada tana dariya,


Dake ba mutuncine yawada cetaba sai tace Kinga inzakiyi abinda ya kawoki ki wuce kiyi Ni banason kitifi Dan da badan Allah yasa da kwanansa gababa da tini mutan gidan daba imanine dasu ba sun kashe minshi,


Keeeee tadaka Mata tsawa tace inzaki ci kasa to kiyayi tashuri suwaye agidan?

nace suwaye a gidan badai ummata kike fadaba gara dayar ace kishiyarki ce to ko itadinma rainonn ummace bazatayi abinda Kika ceba balle sirukartaki ,

dannaga take takenki kodama bakida mutunci bansani ba naje nazauna Ina mutunta iyayan wasu nikuma tawa tananan a wulakance ,

to ahir dinki Rami nake sai dai aganni amma ba,asan abinda yake ciki ba , inma kalarki kenan toyi kokarin sauyawa Kan mijinki yadau mummunan mataki akanki,

Kebama mijinki nidinnan inmuka daura bazakiji da kyauba,

Watace afalon tace Yoshi wanna ki ai ba mahaukacibane da hankalinsa ai yasan meke faruwa inzaki iya zuba Ido tom inkuma bahakaba kema ....turo kofar dakinsa yayi yafito Yana mutstsika Ido hayaniya nakeji lafiya?



Tayi karaf ta amshe zancen mardiyya ce daga ana zancan arziki shine ta maidashi tashin hankali kamar wata yarinya Kuma har hakuri muke bata amma kamar bazancen Wasa ba ta maidashi fada.



Ya kalli Yar uwar tasa cikin salama da kauna yace Koma kizauna bansanki da tashin hankali ba abar zancan ya isa haka.

Zama tayi suka Shiga hirar zumunci daga bisani datakeson su tattauna tace yaya kozamu Dan fita saboda akwai wani personal issue Dana keson mutattauna,


Mikewa sukayi zasu futa ta kalleshi tace alhaji ka rabuda ita ta tafi nima inason zamuyi magana ,

Kamar bada umarni haka yajuya zai koma cikin zafin nama mardiyya takamo hannunsa tajashi suka fita kokarin jansa part din umma takeyi yaja ya tirje,

.yace karki Jani Nan banason zuwa musamu wani gun muzauna amma bananba kicikani ,

Data kafe sai sunshiga sai ya fuzge hannunsa zai juya da gudu Tasha gabansa tace Yaya meyake faruwane tinda nazo nake ganin difference abubuwa agidannan anya ko lafiya?


Shiru yayi domin bashida abinda zaice sai jikinsa dayakara mutuwa,

Tace yaya gurin umma nefa nan zamu Shiga bafa wani gun zamujeba ,


Tinda nace Miki bazani ba toki rabu dani banason naganta tsoro take bani kuma ko kinsan batason sadiya agidannan ko kadan batasonta nikuma duk Wanda bayason iyalina wall... .ya Isa nace ya Isa sai hawaye sharrrr sai Kuma tadurkushe kasa tafashe da kuka dagota yayi tare da Jan hannunta domin sizaga bayan dakunan gidan ,


Tinani tayi tace mushiga dakin ameera sai mutattauna acan ,

Yace wace ameera ?

Dafe Kai tayi tace innnalillahi wa Inna ilaihirraji un sai takara ruko hannunsa yazame Mata wani soko haka suka tura kofar dakin ameera suka shiga,tagama fahimtar komai lamarin Yana bukatar addu a shikansa auran anmantar dashi take Yaya dan Allah karkatafi jirani nazo,yace Ina jiranki kiyi sauri kar sadiya tabiyo mu .


Dasaurinta tashiga gurin umma ameera take kwalawa Kira cikin sauri ta fito tana cewa lafiya kywa wannan kira ?


Lafiyar kena kedai zo zasu fita sukaji umma na magana Ina fatan dai bawata maganar zaku dakko minba tace bakomai umma inmuka
dawo Zan Miki bayani yayane Yake kiranta,


A hanya take tambayarta yanayin cikin gidan yadda taganshi it's abinda tasani tagaya mata Dan batasan komaiba Akan gidan,

tace to Kuma sai Naga kamar Yaya baisan dazamankiba a gidannan amma fa karki damu abubuwane danake tinaninsu nakeson tabbatarwa hadin kanki Kuma shine zaisa komai yatafi dai dai sannan Kuma sai kinsa juriya zadai mutattauna bayan mundawo amma kidan jinkirta Inna Shiga dakamar mintina saiki biyo bayana,


.sunci gaba datattaunawa anan take sake fahimtar duk wata hira da zatayi mar indai ta umma ce baya bukatarta,


Suna cikin hirar ne ameera tayi sallama tashiga da tsokana take amsa sallamar tana matar yaya sai yanzu Kika ga damar biyo bayana gashi har Ina Shirin tafiya to ai sai kizo kiyimin taki taryan Naga wadda tafi it's Taran bako inba hakaba insa yakaro wata .


Dariya sukayi gaba daya sannan ta durkusa har kasa tagaisheshi amsawa yakeyi Yana me Kare Mata kallo yace ameera yaushe kikazo gidan ankwan bitu ba,a haduba ya Kika barosu take kowa lafiya,

. Mardiyya ce tace yaya bakasan ameeran bace amaryarka kake tambatar Ina tabarosu ai tadade rabonta dasu,


Ya rike baki Yana murmushi yace kice kanwatace amaryar aini bansan was aka auraminba wallahi namanta dazancan auran kwata kwata ,

Sukayi dariya amma Banda ameerar wadda Tasha kunu kamar tafashe ,tofa Yaya kayi laifi wayake mantawa da amaryarsa gaskiya yau kazo kabada hakuri ko aci tararka,


Dariya yakumayi yace kaina bisa wuya na amarsu Ina Nan tafe in anjima zanzo bikoe ayimin afuwa kannawane ba dadi sai a hankali.



Itako sadiya sanda suka fita ranta inyayi dubu yabaci tinani take inhar tabari yarinyarnan tana Mata katsalandan tokuwa aikinta akwai gyara akai , shewar mutanan gun e tadawo da ita daga tinanin datake sukace Anya ko sadiya haka kikabar mutumin nan wannan bada umarni haka sai kace da da uwa bamason muna muna agaya Mana sirrin,

Ta juya Kai cike da damuwa tace in ma wani abunne ai gashinan nasami wata tana Shirin rusamin amma zataci ubanta Zan maganinta haka daibsukayi ta tattauna wa daga bisani suka tashi suka tattafi sai yazama daga sadiya sai yayarta rahane matsowa tayi kusa da it's kamarunafu ci tace kenima fa tin randa Naga sun furgita da sukaga juna nayi wannan tinanin kodai wani abun kikasa akayi musu,


Tayi dariya tace ke badan nasa anyi min aiki akansu ba ai dakema bakizo gidan kin dandali arzikin da kike cikiba yanzu da wannan sittirar daya dinkamiki kusan guda hudu gasuna harda mayafi da baki samesuba nikaina da agida Zan haihu saboda takurarta shiyasa wata amiyata tayi min hanyar arziki


Pls share

*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*


🤝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* 🙋









🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀


😨😨😨😨😨😨


🙏 *ABINDA KE* *FARUWA* 🙏


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*

🤝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* 🙋


🅿 *22(V)*


🌈 *KAINUWA

Please Login or Register in order to submit comment