Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shanya.


Bayan sungama cin abincine sukayi sallah sai ta dan dimama musu ruwa domin yin wanka dan garin iska na kadawa haka takamasu daya bayani daya tayi musu tayi musu ita Kuma nana tana shafa musu Mai tare da saka musu kayan islamiyya basu Shari awa daya da dawowaba har sun kammala shirinsu yaran gwanin Sha,awa dukkaninsu suna tsaye domin tafiya Nana ce bata fitoba suke jiranta ganin batada niyyar fitowane yasa karimatun takwalla Mata Kira amsawa tayi batare da ta fito ba,

Girgiza Kai tayi tareda mikewa domin binta cikin dakin tana lura da ita tinda ta dawo batada walwala bakuma yarasa nasaba da zancen ko na makaranta ne ,


Sanda tashiga dakin tana tsugune tana lalube cikin Jakarta kudi take hadawa Yan goma gomane birjik da Yan biyar da Yan ashirin agabanta tanayi tana goge hawaye dasike tarar mata

Nana kifuto kutafi kinasawa suna makara shiru tayi sanda taga tana goge hawaye tare da goge majinar hancinta.


Wani abin nayi Miki dakika shigo daki kina kuka ?


Niba kuka nakeba .

To meye kike kenan ko wani abin akayi miki
naga tinda Kikashigo kike fushi kigayamin abinda Yake faruwa , wannan kudin Kuma dasuke gabanki nawaye ?

Shiru tayi batare da tace komaiba ita kanta dan bayar da zata yine tana tausayawa umman tasu dawainiyarta tana yin yawa amma dole sai Dole shiyasa ma takan jure horon da ake Mata narashin biyan kudin term Akan lokaci.

Magana nake Miki inkuma bani da muhimmanci Kan lamarin ki sai inkyaleki.


Dama Kan kudin term ne kullum sai ance inkawo kowa ya biya Ni kadai ce ajinmu ban biya ba yauma koroni akayi to Dana futo titi nayita tsayiwa bansami abin hawaba shine wani malami yazo wucewa ya ganni atsaye sai yasani gaba yamayar dani yace gobe inkawo inba hakaba kar nazo,


Gauron numfashi taja tare da furzarwa tayi murmushin Yake tace auke wannan ne yasa ki fushi kina mace har Dan wannan abin zaisa ki karaya ai ita mace kullum da dauriya akasanta yazamana duk inda Kika juya Zaki jure Amma dan Dan wannan har kike fushi tashi kutafi gobe in Allah ya kaimu babanku zaije sai ya basu abinda yasamu inkuma Basu samu ba sai ya basu hakuri insha Allah duk za,abayar har na kannanki ending this month insha Allah.


Goge fuskar tayi ta amsa da Amin .


Af wannan kudinfa nawane nagansu tirmis a gabanki?

Kudina ne nake tarawa na makaranta Wanda nace miki zamuyi yayin mauludi.

To mezakayi dasu kike ebowa keda Zaki tafi makaranta kinbar Yan uwanki atsaye sai kinsa anyi musu bulalar makara saboda Allah.


Jiyane akayi musu bulala amakaranta sabida basuje da kudin wataba shine damuka taho hanya nace musu zanbasu yau sukai inada kudi agida kirgawa zanyi nagani inzasu Kai sai nabasu inbasu kaiba Kuma ko mutum biyu sai na bawa .


Ido ta zuba Mata tarasa ta inda zata fara komai nema Yake ya kwance Mata inta bullo tanan sai wani abin ya bullo tacan.


Tace nana karkiyimana haka nasan ke yanzu kinfara hankali ko na boye Miki wani abin dolewani Zaki fahimta Daban shigo dakinnan ba Haka Zaki tafi da wadannan kudaden kibasu bansani ba ?

Zaki fara nunawa Yan uwanki gazawarmu ne duk fadi tashin da akeyi dominku yatashi awofi kenan,

Shiru tayi nadan lokuta tare da zubawa yar tata Ido ta hango karaya atare da ita domin kwayar idonta ta nuna balle datayi la,akari da hawayen dake satata a idonta.

Tace ba kuka zakiyi minba magana nakeso kiyi domin inji tabakinki.


Bahaka nake nufiba nidai kawai basu zanyi nasan in sun gaya miki yanzu bakida kudi hankalinki ne zai Kuma tashi shiyasa Zan basu amma bada nufin hakaba kiyi hakuri umma

Shikenan amma karki Kuma haka in ma basun zakiyi kiringa gayamin sai ingaya Miki yadda,zayi shi yaro indai Yana da iyaye baya girma komai zayyi sai yayi Shawara karki Kuma yankewa kanki hukunci kowane irine batare da kingaya minba ,


Ki tashi kutafi kice da malaman zanzo da kaina in anjima nakawo musu .


To umma inba fushi kikayiba kibasu wadannan sukai ko Basu kaiba inyaso inkinzo din Kya cika musu ( tasan dai karshenta ban hakuri zatayiwa malaman kafin asamu akai).



Toke nana Wanda yaje yakai irin wannan kudin biyar da goma ai yanemowa kamsa abin magana yadda wasu malaman suka lalace sai kiji ansa muku suna Akan wannan kudin Basu San da yadda aka hada kudinba gara Baku kaiba da dai Yan hamsinne to da sauki wani yanzu aciki inkuka Kai yaringa kiranku Yan biyar da goma.


Dariya sukayi tare sannan suka fito suka tafi suna muntafi ita Kuma tana yimusu tinin addu,ar fita daga gida sannan ta bisu da addi,ar allah ya kiyaye ya kuma tsareminku, mutuncinku ,kimarku lafiyarku ,sukuma suna amsawa da amin.




Bayan suntafine tacigaba da kujiba kujibarta daki tashiga ta hau bincike wata tsohuwar wayar shu,aibu ta dakko domin yadena amfani da ita ta Dade da lalacewa shine ya ajiyeta da yara sun fara Wasa da ita shine ta dauke ta adanata ,juyata tashigayi tana cewa kozasu siya masu way gata dai da kyanta afuska bansaniba ko za,asiya , haka tadauki waya ta bugawa shu,aibu domin neman iznin fita Gaya Masa takeyi zata makarantar su nana sabida matsalar kudin wata harta ke cewa kozasu Sami wani abun sai arage kodaga bayane acika.


Wai wai wai ita yafara ambata yace anya ko zasu samu toow sai dai ko innadawo din za,a duba amma kije kibasu hakuri za,a biya insha Allah.

Haka ta ajiye wayar jikinta asalube dan duk sanda yayi Mata irin Haka jikin mutuwa Yake kumayi kullum mutum ba karfin gwiwa atare dashi kullum babu haba haba abin Yana neman yin yawa .


Sai Kuma waji wani tinani yashigeta toma mezai bata mutumin da kullum sai ya Kare karfin aljihunsa kafin yabar gidan nemannan dai shine tinkan ya aureta Abu days ake samu gashi har sun tara yara akan kadami guda Aiko hakuri yazama dole inhar tana neman kwanciyar hankali gareta da yayanta dashi kansa mijin Musamman domin bashi karfin gwiwa gurin nemi musi abinda zasi saka abakinmu salati.

Goya nana Fatima tayi ta kulle gidan bakin titi tayi gurin masu Saida ways Basu tayi tace su siya naira dubu da dari daya aka siya ta kirgi Yan ashirin na naira dari ta hada suka Zama dubu da dari biyu dama dari biyune kudin watan aiko saigashi take ta biya tare da Kara basu hakuri najinkirin dasukayi gurin biya.


Alhaji sabo ne azaune gefen ummansa yamayi Mata sannu da jiki adole take amsawa kodan tseratar da sadiya daga kagen cutar datayi Mata.

Yace amma kannaki yadenako ?


Yadena dama Rashin baccine Kuma yanzu sai godiya tinda nafarka sai naji kamar cirar Kaya .

To allah ya Kara sauki,

Amin Allah yayi maka albarka ya tsareka daga dukkan abin ki nasarari Dana boye.

Yanajin dadin adduar nan ya tabbata addu,ar mahaifiyarsa ce take bibiyarsa dukkanin wani abu dayasa agaba Yana ganin haske duk sanda zaizo ya gaisheta sai tayi Masa wannan addi,ar sanda sukaje aikin hajji yanajinta dukkanin wata addu,arta akansu ne baiji tanayiwa kanta addu,aba saisu sai mahaifinsu har sai da yazubar da hawaye saboda irin feeling din dayaringa ji atare dashi kauna ce zir ta mahaifiyarsa.


Sadiya ce tashigo cikin mutunci da mutuntawa ta tsuguna ta gaisheta tare da yimata yajiki abincine a hannunta nakarin kumallo har kwai ta soyo Mata sukasaka ta a gaba Saida ta ci duk wani motsin umman takanyi Mata sannu kotace wani abun ne umma ko kanne haryanzu haka taringayi Mata sanabe iri iri har yatashi yatafi yabarta agurin Yana futa tafara yatsina fuska takuma janyo abinci tace dama nawane nabaki Danni nadena girki da kowa inma za,a koma kitchen a koma Danni ba baiwa bace ko kisashi ya nemo Mana me aiki ehe ta murguda bakin rashin kunya .


Sadiya tanan Kuma Kika bullo ?

Tokiyi kigama zanga karshen wasan naki danii zakiyi niba kishiyarki bace ko kishiya inkana neman girma da mutunci Jan girmanka kake bareni da ko kinci galaba akwai ranar kindillaci,


Tana cikin maganarne alhaji sabo yashigo yaji karhjen zancen amma baiji farkon ba tambaya Yake meyake faruwa yaga kamar ranta abace yake,

Bakomai tace tambayarta yakarayi takuma cewa bakomai ganin bazata fadaba sai sadiyar wadda tajike da gumin fargaba tayi murmushi tare da mikewa tama me bawa umman hakuri tace kyii hakuri bansan ranki zai baci ba umma amma Zan kiyaye insha allah shigewa tayi tafita tare dasa hannu afuskarta kamar tana share hawayen.


Binta yayi da kallo sannan ya kalli umman yace wai menene umma Yake faruwa mnhh bakomi kaidai Allah ya kiyaye Allah ya tsare minkai jeka kasuwa Rana tanayi.


Bai tafiba sai yabi bayan sadiyar domin yanason yaji kome ke faruwa sun daure Masa Kai daga umman har ita sadiyar.



Bara muleka wani gidan miga wata wainar suke toyawa.

Zainab taci kuka takoshi tarasa yadda zatayi da surukar tata ita kyautatawa tanayi Mata amma duk bata futa yanzunma cin mutuncinta tagamayi sabili da tasa sabon dinkin da tadade tana tara kudi domin yinsa.


Hartake ikirarin saita rabata da dannata in ma sawa tayi malamai suka asirce matashi to ita zatayi maga ninta har Ni zaku munafunta jiya nagama cemasa yasiyo min takalmi yace zai siyomin memakon yabani kudin kafin yafuta shine yayi fucewarsa kekuma shine kikazo kina giftani da wannan dankareriyar atamfar wadda Koda bansan kudin kayaba ta tasawrwa dubu goma to kuwa ko ya dinkan irinta ko Kuma yabani takin a budamin ko inbawa amina tasaka.


*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA*

🤝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* 🙋





🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀


😨😨😨😨😨😨


🙏 *ABINDA KE FARUWA* 🙏

*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*
🤝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* 🙋

🅿 *12(L)*
🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🤝



Batare data saurare taba ta futo tawanke fuskarta sannan ta koma taci gaba da shirinta,

bikin kanwarta akeyi Wanda tinda akasa ranar bikin tafara tanadinsa Kuma cikin ikon Allah duk wani shiri nata ta kammalashi kama daga anko tare da gudun mawa abinda yafi dagawa sikar tata hankali bai wuce ganin kayan da,akadinga futa dasu daga gidanba Wanda batasan sanda akatarasuba ballantana da Zainab din tace Mata tata gudun mawarce aiko tinda ga sannan tace Ina wuta tasaka ta ballan tana Kuma dake akwai Yan korafe korafe.


Amma Kuma dazatayi tinani ita Zainab din mace ce meneman nakanta tinda tawayi gari agidan mijinnata tafara sana,ar Mai da sauran tarkace hakan yasamo asaline daran da aka kawota.


Bayan tarwatsewar angwaye ne bayan ciye ciye da barkwanci tsakaninta dashi anan Yake shigar Mata da duk wani abu dayake so da kuma Wanda bayaso sannan yagaya Mata dukkanin wani nauyi da Allah yadora Masa zayyi kokarin kiyayewa ammafa bai dorawa kansa hidimarta ba kamar ta kudin mota ko Kuma sauran bukatuntaba nayau da kullum sannan ya jaddada Mata mahaifiyarsa da zasu rayu tare yace in Kika mutuntata kin nemowa kanki daraja agurina inko Kika mayarta abar wulakantawa todai akwai matsala.


Tinda yagaya Mata haka ana wayar gari da Yan uwanta sukazo ganin daki ta Gaya musu yadda sukayi aiko sukace bakiga tazama ba kidage kiyi sana,a kodon kitserewa sa,a tare da mutumcinki

Uwa Kuma indai Kai dan mutuncine ai Dole kamutuntata balle da annabi yace kagirmama furfura ko ta arnece Kinga kuwa ai duk wata uwa uwace balle Kuma ta miji.

haka sukaje gida sukayiwa mahaifiyata bayani da yammako sai ga jarkar manja data mankuli an aiko Min dashi su Maggi dasu kayan kulla kulle .

tidaga nan tafara sana,a ta banida matsala ga wata sabga tawa sai dai yaga inayin abunna ,

Kuma ina mutunta mahaifiyarsa Dan wani lokacinma sai kaga kamar har tsoronta nake domin batayi Min da dadi shi kadai ta haifa tanasonsa sosai danko sunansa Bata fiya fadaba sai dai takirashi Dan lele .


Habibu shine sunansa dukkanin wata biyayya Yana yimata ammafa Bai Isa yashiga daki shida matarsa suyi shiruba haka zata hankada labule sannan tace najiku shiru nace lafiya ,

Sai dai yayi Yake yace hutawa nake ,

To ita Zainab din metake kin kume adaki kifuto kitayani hira da dan aikace aikace,

Ina hakuri da ita yanzunma hakance tafaru before in shirya dake shidin ma,aikacin lafiyane yakan Dade a waje baishigo ba wani lokacin sai nayi bacci Yake dawowa,

komai dare yadawo zai tasheni to nayi iya kokarin na yarage dare sabida ana Shiga hakkina.

Bana jurewa ace ina bacci zaizo yatasheni yayi sex dani abin is not easy ba abinda nake fahimta ballantana dana fuskanci kamar uwar mijinnawa wato baba tana saka masa Ido .

Sau tari innazo zanyi wanka after yagamayin sex din nakanci Karo da ita abandaki ta futo ko Kuma nafuto na tarar da ita tanajiran futowata ita tashiga tashiga .


Kin yardar danayi dashi ne dadare yasa yau munayin sallar asuba ko azkar Bai barni nayi ba yanemeni da farko naki dan Ina tsoron baba karta dagamana labule nunamin yayi bazai iya hakura ba shiyasa na nemi yajirani Ina zuwa.


Dakinta natafi a hankali na daga labulen da zummar Inna cikaro da ita nagaisheta inko tana bacci shikenan dama Hala nakeso.

Aiko tana kwance a Kan dadduma da alama lazimi takeyi bacci ya sureta ,

A hankali nasaki abulen nakoma daki cikin sauri sauri nake kokarin yayi yagama gudun karta farka ,har sai da yagano kaguwa ta daya dagani .

Inda Allah yarufa asiri muna cikin daki ba ,a falo muke ba yayi nisa danemarwa kansa mafita domin iya karshe yakai inbanda Kiran sunana ba abinda Yake tare da rukunkumeni hakanne yasa nasaki jikina Dan nasan yakusa zuwa matsaya ,

Bamuyi aune ba sai magana mukaji a falo naji tsoro sosai kirjina yayimin nauyi Ina gudun karta karaso ciki zanin gadon nakuma janyowa narufemu ruf duk da kokarin tashin danakeyi Bai kaleni Kuma Jin maganar ta baisa yamikeba.

Nace ku har yanzu Baku tashiba ga shida takusa kufito haka lada ya isa,

Na rada Masa a kunne ka dagani kar baba tashigo ,Aiko you yayi kamar bayajina .

Magana take cikin masifa au har yaushe akayi Daren bare gari ya waye danake tashinku kunajina Baku fito ba Kun fito ko kuwa yau ninazama abar wulakantawa sabida mace dama take taken Dana kikeyi kallonki nake shine yau Kika fara tanan.


Badanyasoba yadaga ni Yana zufa .

Niko aguje nadaura zani tare da saka hijabi nayo waje tsugunawa nayi Ina gaisheta a wulakance take amsawa sai yanzu kikaga damar fitowa uban me kike adakin?


A,a dama lazimi nakeyi shiyasa ban amsaba shikuma bacci yake amma Naga yanzu yatashi Yana hanyar futowa.


Kikace lazimi kikeke a,a zikiri kikeyi dama bawani abune yakawoni ba tashinku zanyi ko Kun makara ashema har sallah kunyi to ai shikenan sai kifuto ki dora mana abin Kari ,

Kai Kuma kana Ina ?


Gani nan karasowa ,yawwa dama Kai Kuma tini nakeyi maka natakalmin dajiya nace kasiyomin nace ko kudin zaka bani nisai na siyo.

Ki bari Zan siyo Miki dama inaso insiyo takalman inkuma kudin kikeso sai inbaki.

Tofa shine sanda zai futa tariga tayi bacci shinefa yayi daidai dagama shirina natafiya gidan biki aiko tace Ina wuta tasakani.


Sadiya wai meyake faruwa ne bangane mukuba keda umma bafana bukatar wata matsala tasamu balle ace tagurinki tafuto ?

Hawaye ta share tace bakomi Koda wani abunma ai umma uwa tace tayimin nuni ne ga kuskurena nice bana ganewa amma zuciya tace take gayan dai dai nakeyi amma bazan karaba .


Niban ganeba mekike matane kigayamin kar kiyi Wasa da hankalina.

Adan tsorace taja baya tace tasha gayamin inkana gunta nadena Shiga sabida mene nima bansaniba sannan Kuma tace Bata bukatar abinci na nabarta zata dafa dakanta sabida wai namallakeka itama Ina neman na mallaketa,

Amma dan allah kayi hakuri karkagaya mata Zan kiyaye insha allah duk abinda tace zanyi kokarin yi mata shikansa girkin Zan dauki karamin gas dina nabata tinda tafiso da kanta maybe nawa baya yimata dadi ne sai hawaye sharrrr ni umma in bata daukeni uwa ba ai banida amfani domin niyanzu banida uwa sama da ita.


Shiko yakasa cewa komai abin yabashi mamaki amma yaushe ummansa ta koma haka Koda Yake yasha ji ana zancan wasu surukan ko umman itama tana daya daga cikinsu ne,


Ganin yatafi tinanine yasa ta Kuma shagwabewa tare da matsawa jikinsa hannunsa ta Kama tace haba alhaji na karka damu zanyi yarda takeso ai uwace kasan Kuma uwa yarda takeso haka akebinta sannan karka nuna Mata kaga bataso kasani tinda taki gayamaka kayimin wannan alfarmar banaso ranta yabaci.


Gauron numfashi yaja sannan yace shikenan basai kin bata nakiba zansiyo Mata komai
har kayan abincinma tinda akafara haka banason wani abin Yakuma faruwa,


Daka bari kawai taringa diba a kitchen sabida barnar kudin kartayi yawa gawasu kayan abincin basai ansiyo wasu.

Mikewa yayi tareda janyo ta jikinsa ya matseta jiyake tagama Masa komai data iya jurewa hantarar ummansa kaunarta ce takuma kwaranya cikin zuciyarsa yace kiyi hakuri ummatace Kuma nayi mamaki datayi haka amma bakomai kinji my sweetheart.


Shu,aibu ne yashigo kamar korarre kafar nan futufutu dagani ansha tafiya hannunsa ledar braed ce tintimeme daya hannun ledar pure water ce nana ce ta tashi da sauri ta karbi ledar tare da yimar sannu da zuwa haka daya bayan daya suka dinga yimar sannu da zuwa daga daki karimatu ce ta daga labule ta futo tana yimar sannu da zuwa gefen da akayi Masa shimfida ya dosa ya zauna ita kuma ruwa tahau zubawa takai Masa bandaki tare da komawa daki ta dakko Masa doguwar riga .


Bayan yafito daga wanka ne yatarar an ajiye masa abinci shinkafa da Miya ce taji kayan lambu haka yayita sur muka loma kamar Wanda ya wuni bai ciba ,tana gefe tana kallonsa tausayi mijinnata Yake bata tasan karshanta tin Karin kumallon da yayi agida bai kuma sa komai acikinsa ba dan tasha tambayarsa inyana rawar jikin cin abinci yakance wallahi tinda nafuta inbanda ruwa ba abinda nasa acikina Inna nuna damuwata yakance to nida bakudi ajikina dame zansiyi abincin naci sanda Kuma za,a sallameni da intsaya siya gara intaho gida inci kinga kudin dazan siya sai akara agida asiyi wani abun.


Please share other groups

*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*


🤝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU*🙋






🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀🤦‍♀
🤦‍♀


😨😨😨😨😨😨


🙏 *ABINDA KE FARUWA* 🙏


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*
🤝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* 🙋



🅿 *13(M)*


🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🤝



wannan hali namijinnata shiyake Kara Masa daraja a idonta inta yunkura da niyyar yimasa bore Akan al,amuran cikin gida da mafi yawansu yariga yasakar mata takanyi duba ga irin matsin dayake ciki tare da takura gashi Kuma Allah ya horemasa matashi itadin wani lokacin zafine da it's Musamman da abubuwan sukayi Mata yawa hatta akan yara inbata tsawatar musuba sai dai yabisu da Ido shikansa wani lokacin inyayi abu sai ta nunamar badaidai yayiba Wanda shikuma agurinsa daza,akaleshi daidai yayi wannan Yana daya daga cikin abinda yasa Yan uwansa na ubanci suke juyashi ,


Anan gun daya ci abinci ya bungore da bacci baccine nagajiya Dan ko saurayen dasuke binjikinsa Sina neman kwayakwayan dazasu haifar da iri bai san suna binsaba haka namatso Ina karkade Masa saurayen inda sabo na saba haka ce kullum take faruwa yanzu karshenta sai cikin dare Zan tasheshi yashige ciki ya kwanta Yana tafe Yana hada hanya bashida ma kuzarin dazai nemeni don yin sex inma Allah yasa baccin yasakeshi haka zai lallaba yayi abinda zai iya Wanda Ni agurina dashi gwara babu innayi magana yace dukkanin gabobinsa ciwo suke Babu abinda zai iyayimin karshe Inna takura muzo muna fada Dan ba iyawar zaiyiba ya wuni atsaye Yana kula da kasuwancin wani shiko mekayan Yana zaune Yana karbar kudi Babu tausayin zauna ka wuta incigaba da kula.


A Dan tsakanin Allah yasa mukasami salary cikin amincewar Allah naje nabiyawa yara kudin makaranta sannan nashiga kasuwa nayo Mana cefanan dukkanin kayan danasan zamu bukata haka Kuma nasiyo musu katan din Bobo guda biyu da rabi haka nake siyansa duk wata ba kullum nake basu sai ranar Friday kowa sai inbashi guda daya nakan soya musu wani abinda zasu hada dashi ban daukarwa kaina karyar kullum sai nabasuba hakan ma nakanyine sabida karsunayin tinanin sun fita Daban da sauran yara insukace min wasu kullum suke zuwa dashi muma kiringa bamu kullum sai dai nayi murmushi nace kuringa godewa Allah da abinda kuka samu nasan acikin makarantar bakowane yake zuwa dashiba ko?


Sukance hakane kuwa.

To kunga kenan kudin sai kuyi hakuri da abinda kuka samu tinda wadancan ma suna hakuri da rashin basuda shi.

Wani abin farin cikine yatin karomu domin kanin babanane yakirawoni yakemin zancan yanaso inturo Masa shu,aibu akwai wani aiki da aka samu inyana bukata insha allah za,a Sami alheri,

Aiko dasaurina na amsa Masa da cewa zayyi baba yanaso .

Bakece Shiba ki turominshi inya amince zanbada sunansa temporary ne dai ba permanent ba yardarsa itace.

To nace tare dayomar sallama nataho Ina cike daurna natabbata alharinne domin wancan Kiran dayayi Masa shine yazama tsanin dawowarmu gidannan .


Can gidansu nazarce domin gaisheda iyayansa ahanya natsaya nasiyi goro manya manya tare da sabulun wanka naso na debo musu anamu tokuma nariga nafito shiyasa Naga gara na siyadin .

Sanda nake dukkanin su suna tsakar gida Dan har kannensa sunzo gidan da Yan dakinsu dakuma Yan dakin abikan zaman hajiyarsa.

Haka nabisu daya bayan daya Ina gaidasu sannan nabasu kayan danazo dashi godiya ko waccensu tayimin sannan natashi nashiga dakin sirikartawa ganin nashigane yasa itama ta biyoni sake gaisheta nayi sannan nabata nata alherin da nazo dashi naira dubu daya nakara Mata nace gashi hajiya kyasai wani abun ,

Allah sarki godiya tayi tayimin Wanda har Saida naji kunya halinsu daya da danta basa Raina alheri ko Yaya Yake sai sungode maka.


Muna cikin hirane daya daga cikin kannen nasa tashigo tanayimin habaici niko bajurewa nakeyiba yadda tagayan Hala zangaya Mata.

Da dariya tashigo sannan tace a,a matar yaya Ina Kika baroshi kinsan shi yanzu ganinsa sai ancike form Musamman dayazama sai yarda akayi dashi.

Dagowa nayi Ina kallonta sannan nayi murmushi nace ai basai kin tambayeni Shiba duk sanda kikayi niyyar ganinshi kinsan inda yake domin kinfini kusa dashi.

Rike baki tayi tace ni awa danafiki kusa kuwa aibazan tamba yekiba Kinga inada abinyi ba inyi nan bareki gayan Mara dadi.

Dariya nayi tare da daga sauti Dan taking nace

Kece ko Mara aikinyi da kina da aikinyi Aida baki damu da damuwar waniba ,

nidin dake bana tagumi da habar wani ai Kinga sabgata nake wanki ko da kike zancansa sai dai kiyi hakuri ki kauda Idonki inkinga bazaki iyaba kice Allah yayimin abinda nayi Masa inafata kingane.

Yo Allah natuba matar yay....hajiya ce the tsawatar tace tashige tatafi nikuma tabani hakuri tace karki damu duk meneman sa,a Yana tare da ita nasan duk abinda Yake faruwa Allah Yana tare daku zai Kuma duba Al,amarinku kikara hakuri.

Tofa abinda Yake Dan kwantarmin da hankali kenan da mahaifiyarsa ta yarda dani da badan hakaba abin yawa zaimin.



Zubawa kayan da,akashigo Mata dasu Ido tayi wato sadiya tarantse sai tayi Mata Karantsaye ko to kuwa zatayi maganinta zatasha mamakinta ,

Tana tsaye agurin tilin kayan girkin da akashigo Mata dasu sai ga sadiyar nan tataho tana yatsina tare da tsartar da Miyau wai ita me ciki ummance ta kalleta tace sadiya salonki yayi kyau amma nawa bazai Miki dadiba amma har yanzu kofa a bude take Zaki iya hakuri ki karbeni a matsayin uwa in kinyi taurin Kai Kisha mamaki.


Kallonta tayi kallo me cike da tsana tace nice kofata take abude Wala Allah in Kika bar gidannan kikabarni nasake nida mijina tofa Zan iya kyaleki da danki inko kikayi taurin Kai Zaki rasa Wanda Zaki kalla kiji dadi ,tajuya tacigaba da yatsina tana tofar da miyau

Sai Kuma ta juyo tace au da akwai fa mardiyya kinama da gatanki Zaki iya yin yadda Kika so.


Suna nan tsaye har me gadi ya bude Masa get yashigo Basu jiba sabida kowa akwai inda hankalinta yayi sai ganinsa sukayi Yana tin karosu yitayi kamar Bata ganshiba tashiga matasar hawaye tana cewa umma ba laifina bane kiyi hakuri ciki Kuma nima bansan alhaji bai gaya Mikiba da danazo tinsannan nasanar Miki kiyi hakuri karki hadamu domin Yana mutun taki bazai yarda ace kingaya Masa irin wannan maganar ba yaki yarda dan Allah umma narokeki.


Turus

Please Login or Register in order to submit comment