Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝

Yo amma kinsan haka Kika barni gida zaune bawani dan temako da Zaki bani Nima inkoma gidan nawa mijin kinaganin inda nake fama da babanmu nazame mata kamar kishiya Kan zaman gidannan danake..

Takatseta tare tintsirewa da dariya tace anti Wannan gigicewa haka kwantar da hankalinAInsha Allah gobe aminiya zata dawo tayi tafiya ne ai da tini kunsan juna,

zata rakaki kuwa indai wannan teacher dinne kamar kinkoma kingama kikuma jashi inda ranki keso,


Baishiga takofar dazata ganshiba sai yashigata kofar baya tinani yakeyi wai meyashiga kansane sai yayi wasu abubuwan sai yazo yayi ta tinanin hujjar yin hakan,

ummansa ce ta wado Masa da sauri ya Mike domin zuwa gunta jiyayi wani abu ya gilma takansa Wanda yasashi dafe kannasa Zama yayi yarasa meke Masa dadi wani abu yaji yatokare Masa kirjinsa dafe gun yayi Yana Kiran sunan Allah a hankali yaji Yana samun sassauci. ajiyar zuciya yasaki da yatuno wai ameeara umma ta aura Masa amma har kawo yau wai baije yaga kalar amaryarba sai da mardiyya tajashi gun dazu tsaki yayi yace yo Ni inbanda ma ta tinamin ai shaf namanta rigingine yayi Dan yafijin dadin tinanin sannan yakara murmusawa yace lallai yau ango nake akwai shagali kenan ,

tinawa yayi da sadiya zumbur ya Mike Yana lekenta ta taga kwarjini takara yimasa wani irin tsoron tane yadirar Masa sai wata uwar zufa datake kwaranyo Masa.


Yanzu umma kinsan da wannan matsalar Amma baki taba gayanba kema ameera aikya bugo kisanar Dani kome akwai Koda bazanyi maganin matsalar ba aikwaji dadin kunsanarwa da wani,

To mardiyya abinda yafi karfinka ai sai kamarshi wasa abin ya wuce tinanin me tinani sai dai Mika Al,amarin ga Allah Dan Haka karki tada hankalinki muyi addu,a akwai Allah akwai kuma lokaci dukkanin abinda mutum yayi domin kansa kedai fatana kirike Taki uwar mijin kamar itace ni Inka mutunta uwar wani kaima sai amutunta taka Kuma shi tsoho daraja ce dashi balle wannan zamanin bakayi ba ma anmaka Allah dai yasa mudace.


Hajiya Taji jiki gaskiya domin masassarar datayi takwana biyu tabata wahala Haka nasha jinyarta harta warke Dan makaranta ma sai da nadau excuse din kwana biyu saboda inkula da ita taji Dadin hakan shima megidan yaji dadi sosai ,



A wannan kwanakin datayi kawai Ina lallaba wane tasami lafiya nikuma insami nutsuwa domin kamar akwai son zuciya cikin lamarinsa yadda nake fama da dawainiyyar yarana inbasu da lafiya nice siyan magani nice sewa yaro abinda zaisa abakinsa yaji dadi Kai duk wata hidima ta asibiti nice sai dai yayi min godiya,

to Haka ma yabarmin hidimar hajiya ko kudin mota Bai bamu ba Dana matsa masane ma ya dakko dari biyu yace muyi kudin mota abinda nasan yahadani dashi kenan shiyasa nakeso tagama warwarewa nadau mataki Dan bazai yiwuba da innayi hidimar gida nasan Babu ne yanzu ko nasan akwai sauyi ba abinda ma Yake bani mamaki sai inzai bani kudi da yakan juyemin abinda Yake dashi har sai nadau wani abin aciki nabashi yayi kudin mota yanzun ko inzai bani kudi sai yashiga bandaki ya kirga sabida karnaga yawan kudin dake gareshi wato nidin Yake neman ya manta alherina gareshi,

ko Kuma inyaga nagane shi sai yajuya bayansa sannan ya kirga abinda zai bani badai zai Bari naga kudinba sabida San zuciya irin nada namiji Dan haka nakeson nadau mataki danni bazan jure irin wannan ba yazama kamar cin fuskane agareni to meyake nufi shinakeso nafara ji sannan Kuma into Masa tini da nauyin dayake kansa bani Allah yadorawa nidin wani yanki ne natemako da aka sani gareshi Dan Haka lallai komai sai an sauya Nima macece bakuma matar wahala ba inda najure yanzu Nima gashin kaina nake nema.


pls share


*INA* *BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*


🀝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* πŸ™‹







πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€


😨😨😨😨😨😨


πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹


πŸ…Ώ *23(W)*



🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝




toke yanzu duk hakurin da baiwar Allahnnan tazo tabayar bemikiba mekikeso Kuma tayi miki Aiko bada gaske take ba kyayi hakuri kikoma kigani insun tuba da gaske Kuma ita rayuwar aure tagaji haka bakowa ce, mace ce take dacewa da abinda takeso ba Kota dace din akwai kalubale dasuke biyo baya ,



Umma wallahi tariga tace batasona gara muhakura Allah yahada kowa da rabonsa na alhairi shikansa tayata yakeyi abinda takemin Dan Haka kikyalesu kawai zasuga in inada Rana in ma banida ita zasu gani,


Haba zainaba Aiko sungama ganin ranar da kike da ita tinda gashi ita takasa jiyyarsa har tana kukan kitemaka Mata ki koma kodan kiyi jiyyar mijinki Aiko ranarki tagama fitowa,

Kije gidan aure ne, ai kome Kika ci Karo dashi ladane, lada kuwa me tsoka, Kuma dama masu iya magana sunce fini da gidan uba nafiki da gidan miji , fini da gidan miji nafiki da gidan uba ,

Dan Haka kitattara kayanki kikoma nikuma zanbiki da addu,ar neman sa,a ta gidan aurenki Allah ya doraki akansu ko Dan kuzauna lafiya,

Baki ta zunbura tace to ni nace yaje ya karye dazasu ce sai nayi jiyyarsa wayasani ma ko alhaki nane Allah ya Kara ma da ya karye din,



Alhakinki dan kunyi fada Kuma ya karye sai kice alhakinki ne ,

Wallahi alhakina nane banace Miki har marina yayiba ,Niko danaji zafi nace Allah yasakamin ko a tsokar jikinsane Aiko gaba yakuma wallahi inkarayi Masa wata addu,ar.


Hannu tashiga tafawa , tace niyasu dama bana hanaki yiwa mutum irin wannan addu,ar ba dama baki denaba Aiko ko kinaso ko bakya so sai kinyi jinyarsa tinda ke kikaja masa Allah yashirye ki yarabaki da wannan baki naki,


Haka ta tattarata tasa aka rakata gidan ranta baisoba Dan ita tagama da Yan kayansu, tana da hakuri da juriya amma inta botsare abin bakanta,


Sanda sukaje gidan dagashi sai baban ,

tana ta kiciniyar dagashi zata dorashi afo takasa,

dama takan leka waje ne inyana bukatar temako irin wannani tasami irin masu zaman majalisa su temaka Mata tosuma ganin tana damunsu yanzu sundena zama shiyasa yanzu Kan ta daga shi sai ta wahala,


Sannu suka Shiga yimasa itako dauke kanta takuma yi gefe Saida kanwar babanta tace tashi kitemaka Mata Mana Kika zuba musu ido bamu mukulin dakinnaku sai mu Shiga kafin kifito,

Mika musu nayi suka tafi domin bude dakinnawa,


Niko Dakar cikin bacin Rai nadoshe su duk yarame sai ido dama shi Abu tibar kalla gwaragwara,

Haka badan naso ba nakama matashi ta zare Masa wandon nikuma na turo Mata fodin ta daidaitashi ,

Ruwa ta tafi ebowa na tsarki ta barni dashi,

Ahankali ya kalleni yace Zainab abin har yakaimu ga haka kikasa yimin sannu da jiki,

O sannu ko to madallah,

dakasamu nadawo kaga in matsamin zakayi da magana wallahi sai na koma dama tilas akayimin nadawo sai kace Nina karyaka,oh Ashe fa alhakinane gara ma Haka wallahi duk Randa kakuma sa hannu ka mareni adduar da zanma tafi wannan ,

Na murguda Mai baki,

Kallonna kawai Yake yace Zainab ko me nayi Miki yakamata kiduba halin da nake ciki ki tausayamin ninasan abinda nakeji inhar wannan radadin danakeji alhakinkine toko nadandana kiyi hakuri badan niba kuskurene nariga nayi bazan sakeba lokacinma sharrin shedanne amma nasan bakida laifi duk laifinane Dana baba,


Hhh Allah sarki Ashe kasani katake ai shikenan inkun gyara magyara inba hakaba daidai nake Dana bar gidannan inyaso wadanda kake kaiwa zumar taka sai suzo ku hadu kuzauna agidan ,


Tashi nayi natafi dakina Daman a dakinta take jiyyar tasa tararwa nayi suna Shirin tafiya Nan mukayi sallama dasu suka tafi nikuma na haugyaran dakina inajinta tana kwalamin kiran inzo ayi Mai tsarki Niko nayi banza da it's nabi lafiyar gado,(illar takura kenan Tin mutum naganin mituncinka har sai kakoma dakai da Babu duk daya wasu surukan kenan ).


Damisalin karge takwas ne nadare dukkaninmu muna zaune atsakar gida har da hajiya wacce take cikin nishadin kasancewarta da jikokinta cikin koshin lafiya gefe daya nanace da su saddiku zaune tana koya musu homework can gefe shimfidar babansuce wacce najere Masa kayan abincinsa akai har da su lemo na hada Masa daga gefe cikin abincin kuwa dankwa leliyar jelace takifi tare da kwai guda daya aciki ,nikuma tawa shimfidar tana tsakanin tasa data hajiya,


Suna cikin homework dinne sun bude littafin maths sai ga takarda tawado daga ciki aminullahi ne yayi sauri ya dakkoπŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€


😨😨😨😨😨😨



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*


🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹



πŸ…Ώ *24(x)*



🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝



Aminullahi yayi sauri ya dakkota yace ,laaa gatakardar da aunty ross tace mukawo gida ,

saddiku ne ya kwace yace to Kai akabawa bani akace nakawoba,

Aiko yamike Yana zagaye zagaye dan kar ya kamashi yaace wallahi sai kabani ,nizan nuna kullum kullum sai adinga baka niba ,a bani ,


Nice nayi murmushi nace haba saddiku ai Kaine babba bashi yakawomin nagani inyaso sai inbaka abarka ko ba Haka ba Kai kuma sai kabawa babanku shima sai ya karanta.

Haka dai yabashi shikuma yazo yatsuguna yabani tare da Karin bayani,

Karba nayi Ina dubawa daman nasan zacan baya wuce haka kudin term suke bukata domin akalla yanzu sati kusan hudu kenan da komawa hutu ajiyar zuciya nayi daman Kuma suna cikin tsarina nace za,a kawo insha allah,

Itadai hajiya tana gefe tana lazimi,

Can sai wani tinani ya wadomin takardar nadakko nace yaka saddiku bayan yakarasone nace ungo takardar in babanku yadawo sai kubashi amma sai yagama cin abinci ,
bayana dawowa za,a bashi ba kaji dan albarka,

Karba yayi yace to umma.


Daga daya bangaren Kuma na fuskanci nana sai satar kallona take Kuma da alama magana ce abakinta ,

Nace ya akayine nana Koda wani abunne ?

Girgizmin Kai tayi nace da akwai kenan menane ko kema kudin term dinne kike satar kallona kamar za,a hanaki inya dawo kema sai kigaya masa zai baku in Allah ya yarda.



Muna cikin hira da hajiya ne Kan Al,amuran duniya da Kuma yadda son zuciya yayi Mana yawa a wannan rayuwar sai kaga mutum Kiri kiri shidin masoyin kane azahiri amma abadini bashida abin ki sama dakai har nake cewa kumafa hajiya gara ma ace kasan mutum bayasonka da Wanda zai nuna Yana sonka daga baya Kuma ashe ha intarka Yake,

Sallamar shu,aibu ce ta katsemu daga hirar da muke yaransa ne suka rude dayimar sannu da zuwa sannan ya karasa ya gaida hajiya nima nayi mar sannu da dawowa,


Bayan yaci abinci ne naje na dakko Masa matashi kozai tada Kai dashi ,

Kafin dawowa tane saddiku yaje ya kai Masa takardar biyan school fees karba yayi Yana me tambayarsa takardar mece ?

Yace amakaranta ne aka bamu Yana cikin fadane nana ma tace abba ance muma mubiya school fees, dagowa yayi ya bisu da kallo yace ai bani zaka bawa ba kugayawa ummanku Kai kuma karbi sai ka bata,


Nace a,a ai dama ninace ya baka niya fara nunawa.

Tashi yayi yagyara zamansa sosai yace ,

Yane Kikace abani?

Dama ni suke bawa koke dazaki ce subani ni mezan musu insuka bani?

nace bakai suke bawa ba nasan ni suke bawa abinda yasa nace abaka ai abayyane Yake tinda Allah yasa andan Sami sauyi neman naga yanzu ba irin nada bane gara kaima kana dan tabukawa sabida nauyin yayi min yawa hidimar akwai takura acikinta.


Yace toni dai gaskiya banida kudi balle inbiya musu bakuma zandorawa kaina abinda Allah bai dora minba dan haka innasamu Zan biya .


Kallonsa nakeyi na mamaki nace yanzu Kai dan Allah zancanka gaskiya ne kobaka biya dan yahau kankaba kabiya kodan kimarka a idon yaro,

Aiko sai yanemi ya hayayya komin ,

Tsam namike nabar gurin gudun kar su fahimci abinda Yake Shirin faruwa ballantana danaga sun fara bada hankalinsu akanmu itako hajiya ko kallanmu batayi ba balle ta tofa tata aciki,


inbanda lazimi ba abinda takeyi

Nifa duk wani tashin hankali gani nake Yana Shirin samuna wato duk takatsantsan din danake Yana neman tashi abanza wai mafa dan banzurfa faba wato ban bude Masa kofar karbar kudi aguna ba dan da abin sai yafi haka inata tinani bansan lokaci yajaba sai danaji yara sunayimin sai da safe futa nayi naje nayiwa hajiya sai da safe Zan futone take cewa akara hakuri duk da bansan abinda kefaruwa ba amma naso nafahimci wani abu zankuma yiwa tufkar hanci,


Nace a,a hajiya karkice Masa komai zanyi solving din matsalar insha Allah,

Yoni Ina nasan wata salbun me kike nufi?

dariya tabani nace hajiya Zan warware komai insha allah abin bame zafi bane.

Tace to ai shikenan Allah ya Kara Miki hakuri kinsan mazanne sai hakuri duk dadinka dasu dole sai sun bika da kalubale balle yanzu *ABINDA KE FARUWA* kenan duk inda Kika Shiga sai kiga kamar bazaki dau Al,amuran gunba wani lokacin sai kiji mace tana cewa innice wallahi bazan dau wannan abinda akewa wance ba , amma fa daza,a jarabceta da wannan abin sai kiga tajure saboda duk inda Kika Shiga *ABINDA* *KE* kenan dan haka koma menene adai inda nafuskanta kece me hakurin kikuma Kara badan Yana dana ba nake cewa kizauna kiyi hakuriba a,a shi da nakowa ne yaro Kuma sai maishi in kayi dakyau zaka ga dakyau.


Bayana nafuto daga gun hajiyane nashiga nayiwa yara addu,a duk da nasan kowa yayi before ya kwanta domin nariga nakoya musu inzasu kwanta ga irin addu,ar da asuyi haka inzasu fita daga gida ,

Daki na wada domin Nima inkwanta in huta kozan denajin abinda Yake damuna Haka nabi bayansa na lafe damuwa biyu ga wadda take neman hakkemin ga Kuma wadda dama aciki nake jinayi tsigar jikina tana tashi ballenta da mukayi gaf dagab matsawa nayi daga jikinsa gudun kar na tsokanowa kaina amma dake abukace nake dashi bandena jiba jinayi private pant dina Yana motsi ahankali nasa hannuna nadafe daga karshema rufda ciki nayi dannasan karshenta inda Yake kwasar munsharinnan ba abinda zayyimin yo ko idonsa biyu ma ba lallai ya saurareni ba domin shidin bawai me bukata bane Kuma bashida daukar Abu da muhimmanci inbukatarsa ma takawoshi baifi yadauki minti biyu ko ukuba har yayibkidan da rawar.


Ganin Zan cuci kaina ne yasa namatsa jikinsa ahankali nadinga shafashi har sai da sakona yaje zuciyarsa idonsa ya bude ya kalleni lumshesu yakarayi batare da ya saurari bukata taba Yakuma rufe idonsa ,

Nace bacci ka koma?

ba amsa jijjigashi nayi nace katashi tinda kaga natasheka ai kasan abida nakewa.

Abin haushin Mika yayi yace dan Allah kikyaleni nagaji bazan iya komaiba.


Da haushi ya isheni da zancansa ,nace dama meka iya burburin da kake yimin kamike ni wallahi nagaji Kota ina ba sauki inbanji saukinka azahiriba ace abadinima bazaka iya rarrashina da bukatata ba ,

innaga kakusanceni sai kana bukata shima wani lokacin sai inyi period inkara baka saurareniba to wallahi da sake shekarunnawa nawa daza,ace namiji yajingineni ,kagafa ni akomaima nagaji bar ganin Ina ragawa kasan nima bani da dadi....tareni yayi daga fadan danake yace darefa yafara gayara agidan ga hajiya za,a iya joyoki.


Yoni Ina ruwanna ajiyomu mana nadaice maka nagaji inbanda aikin wahala ba abinda nakema Wanda Kuma bakasan inayiba todan haka inzaka sake kasake kudinka ma da kake bani nacefane nadena karba karinga siyo komai da kanka,



Sadiya ce take ta fushi tin bayan tafiyar mardiyya yayi banbakin Taki kulashi haka sukakai har dare a haka shikuma duk wani Rashin sukuni yasameshi yarasa inda xai tsoma Ransa yaji dadi daya dametama fatattakarsa tayi Akan karyasake Yakuma lekomata daki tinda Yan uwansa sun fita Haka yatafi dakinsa ransa duk ajagule,daga karshe daya rasa mezai tashi yayi yashiga toilet yabudewa kansa shower kokayan jikinsa Bai cireba kamar tini ameera ta wado Masa arai cikin sauri yafuto daga bandakin Nan danan yashirya dasanda yafuto daga dakinsa sai da ya leka ko Ina yaga batanan daga bisani yaleka dakinta daga nesa ya hango ta tana Shirin kwanciya Aiko Yakoma da baya da murnarsa ya doshi dakin ,


Tana tsaye tana Shirin bacci Dan daga ita sai daurin kirji hannunta ruke yake da πŸ‘— tana kokarin sawa.

Kamar ana jansa Haka yakeji yayi ya Isa gareta,

Rigar yakarba ita Kuma sai nokewa take yace haba ta ango ai kima saki jikinki yau amarci nazo muci,bawata kunya sai hakuri dazan baki Al,amurane sukayimin yawa shiyasa bantina da amaryataba amma yanzu koma dai menene ayimin afuwa,

Jitake kamar ta makureshi Dan ya Raina Mata hankali badan maganar dasukayi da mardiyya dazuba da ba abinda zaisa ta saurareshi,


Murmushi tayi irnna kunya sannan tadau hijab ta saka,

Shima murmusin yasakar Mata tare da rike habarta ya daidaitata da fuskar sa yace me kike tsammani da Kika saka Wannan abun ?


Ta turo baki gaba tace nida kwanciya zanyi kikyaleni ,

Kwaikwayonta yayi yaci tonima aikwanciyar zanyi Nima kikyaleni ,

A hankali ya dinga zame hijab din daga jikinta sannan ya Kama zanin zai subale shi Aiko tazaro Ido take kaiiiii,

Yaso yayi dariya amma sai ya maze yace nidin kokin manta akwai sadakina akanki ?


Shiru tayi Masa tare da juya Masa baya shima kyaleta yayi baice komai ba rage kayan jikinsa yayi sannan ya rike hannunta hadeta yayi ajikinsa wani irin feeling yaji Wanda yaziyarci kwakwalwarsa harsai da yayi ajiyar zuciya jikinsane ya hau rawa shidai burinsa kawai ta tallafa Masa domin duk wata bukatuwa ta bayyana gareshi ita Kuma tsorone aranta Musamman datasan itadin bakowa bace ,
ga matarsa data kasa ta tsare tasan yanzuma karshenta bata San yazo ba,

Haka dai yadinga lallabata tare da kalamai masu dadada Rai har sai daya isah H Q Taji ijinta shikuma yayi kukan dadi domin a wannan daran sai da sadiya tashaida yaziyarci ameera Haka tadinga sintiri tsakanin falonta da kofar falon ameera har dakin umma sai da ta leka amma tatarar da ita bama tasan wainar da ake toyawaba baccinta take kwasa.



*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*



*DAGA ALKALAMIN YAR* *MUTANAN JINGAU*





πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€


😨😨😨😨😨😨



πŸ™ *ABINDA* *KE* *FARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA* πŸ™‹



πŸ…Ώ *25(Y)*



🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝



shiko gogannaku Yana can rungeme da amaryarsa babu komai aransa sai farinciki domin shikadai yasan abinda yaji gashi Kuma ankwan biyu dama ba,a haduba tinda cikinta yayi wata shida tasallamashi,

Gashi yanzu ameera ta ibeshi izuwa duniyarta tashayar dashi zumarta dago fuskarsa yayi Yana Kare Mata kallo ,

Koda ya rayuda ita inuwa daya baisan tana da tarin baiwa hakaba Musamman dayakaiwa dukiyar fulaninta kallo ,jikake makwatttt ya hadiyi wani tattauran miyau abakinsa ,

Yana bukatar kari sai dai yatausaya Mata Dan yabata wuya domin yayi Mata shigarka sauri har sai da tagala baitar,


Sadiya ce take ta sintiri tsakanin falonta da bakin dakin sadiya sotake tatada Bala,i a wannan lokacin amma sai rahane ta hanata tace tabari gari yawaye kokuma tayi shiru sai akara daukar mataki don inkikayi magana karshenta azo takwabe.



Yo badole ta kwabeba zasusan suntaboni wallahi sai na yimata hukunci kwatankwacin na uwarsa zasusan koni wace ,au wato inanan kwance baki sake su Kuma suna buduri,

Tashi tayi da hanzarinta tafuta kofar dakin tahau bugu tana bala,in su bude kotakarya kofar ,


Kana Ina bakin munafuki harni zaka yaudara kashige dakin wata ke Kuma zakisan kinkwana da mijina shegiya matar shige zakiga katshen auran da akayimiki kesa kwanciyar hankali har abada,


Ai alhaji sabo Bai San sanda yahan kade ameera ba aguje yatashi yahau laluben rigarsa ,itako ameera tsabar furgicin datashiga kasa gane komai tayi ga azabar bugewar da tayi agoshinta dafe take dagun itama tamike tana neman yin waje Dan bugun da akeyi tare da masifar sadiya sun mutukar daga Mata hankali,


Hannunsa dake faman rawa yasa yariketa rigar dayakarba dazu ahannunta yadaula ya Mika Mata ,

Yace yi sauri kisa sadiya ce bansan ya akai tasan inananba,

Binsa tayi da kallon bacinrai tace bazan sakaba ai ba Zina na aikataba inta isah ta shigo cikin dakin taga Nima nawa Rashin mutuncin ,

Tsugunawa yayi Yana Bata hakurin ta rufa Masa asiri kar ta Ganta ahaka,

afurgice yasake mikewa dalilin karfen datasamo tana bugun kofar dashi Wanda yatashi mutane dasama ciki ko harda umma Dame gadi kowa hankali atashe yayi waje tare da neman Karin bayani ,


Aiko kamar ankuma tinzirota tasake hawa kamar farashi har dacewa umma ce ai babbar muna fukar data hada komai,

Aciki kuwa ameera takasa ta tsare da tsiraicinta tace wallahi sai dai tashigo taganta a haka inyaso zuciyarta sai ta buga,


Zufa tare da tsoro da nadama duk singama shigarsa sai kaiwa Yake Yana kawowa yarasa mafuta,

Umma ce tayi magana take ameera zoki budemin Koda kinji bude yafuto kozata barmu mukwanta miyi bacci da safe sai ayiaganar,

Zani tadaira akirginta sannan tasa hijab kofar ta hau kokarin budeta ,daga wake kuwa sadiya ce ta saita karfen dake hannunta tanason tasaukeshi Alan ameearan ,

Ummace ta lura da hakan tatsawatar Mata,


Ina ruwanki kome nayi kishiyarki kotawa duk abinda nayi idone naki ta murguda baki ,rahane ce tajata baya gudun kar azo ayi danasani,


Shiko halin dayake ciki yafi nada tinda yaji muryar umma wani Abu yazo ya gifta ta tsakiyar kansa shikenan dikkanin wata nutsuwarsa ta kauce yanzunma arabe harke har ameeitabude kofar anti anyi ya futo yaki daga karshema cewa yayi shi tsoro yakeji waddatake maganar Nan sai ta bargun zai iya wicewa,

Sadiya ce tayirkaraf tace to ai sarakan shishshigi sai a matsa yace bayasan ganin mutum anan,


Share hawayen days zibo Mata tayi tace yanzu sabo nice abar jintsoronka ?
mutum dai yaki tsoron Allah sadiya akwai ranar kin dillanci kuma duk abinda kikeyi akwai karshensa ko badade ko bajima Musamman da Allah yayi Miki tukuici dasamun haihuwa Ina meyi Miki tini daki guji duniya babu komai cikinta sai rudani,


Kanne Mata Ido daya tayi tare da tsartar da miyau,


Abinda tatsana kenan tin tana kuruciya in aka tsartar Mata da miyau takan dau hukunci Alan komawaye Dan wannan shine karshen wulakanci takan dauki komai amma Banda wannan,


Wannan abinda tayi matane yasa tadaga hannu ta kwada Mata Mari Marin dayayi sanadin abubuwa da dama ciki kuwa harda nadama datake biyo bayan rudaddun abubuwa.





*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*

🀝*DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU*πŸ™‹



πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😨😨😨😨😨😨



πŸ™ *ABINDA KE* *FARUWAπŸ™*



*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹




πŸ…Ώ *26(Z)*



🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝



wata razananniyar Kara tasaka tare da dafe gurin datasha Marin,


Umma ce ta nunata da Dan yatsa tace wannan zubar min da miyan da kikayi kin ruguza dikkanin ayyukan da Kika dade kinayi kinyi kinyikure sadiya ,wani Dan guntun ruwane yadigo daga cikin idonta tace akwai ranar kin dillanci ranar da baki da mataimaki,



Kasacewa komai tayi domin Marin yashigeta ga banbamin fadan da umman takeyi kamar zata daketa,

Juyawa tayi zatashiga dakinta cinkaro tayi da Mai gadi da yatada Kai da hannunsa ,domin yagigita yasan gidan yadan hargitse Bai tinanin abin yakai hakaba,



Rabeshi tayi tashige batare da tasake kallonsa ba, shima juyawa yayi domin bashida abin cewa masu abin fadinma ba,a basu daraja ba balle shi megadi amma yakamata dai to........



Jin ba kowa agunne yayi kokarin fitowa amma dake ameera tana kanhanyar sai tamayar da kofar batare da yafitoba ta rufe da alama ta shirya taryan dukkanin wani shiri na sadiyar,


Bata koma bacciba sai tashiga ta hada ruwan dumi ta gyara jikinta tare da yin wanka sannan tadaura alwala,


Sanda tafito Yana tsaye inda tabarshi tausayin sane yajata izuwa gareshi tace kaje kayi wanka ga ruwancan nahada maka,


Baice komaiba sai bin hanyar bandakin da yayi ,ita kuma ta shinfida dadduma guda biyu tahau guda daya ta fara sallah Dan ko ta kwanta dinma ba abinda zata iya,


Futowa yayi daga bandakin Bai tsaya sauraronta ba ya doshi kofar futa ita kuma tana cikin yin tahiya domin sallamewa,


Bata tsaya yin addu a ba ta Mike da sauri ta rukoshi tace Yaya sabo Ina zaka adarannan bayan ga dadduma tana jiranka ,nasan koka koma bazaka iya bacci ba gara

Please Login or Register in order to submit comment