Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tana kallon makirar yarinyar nan shikansa kallo yaringa binsu dashi baisan mezaice ba da Yana da wurwura akan zancen girki tofa yanzu Kuma gata ga umma zubewa yayi tare da Kama hannun umma yace umma kafin na auri sadiya sai da Kika yardarmin banyi Kai tsayeba bare kice bazabinki bace ...katseshi tayi tace sanda kazo da ita nagaya maka batada tarbiyya to tin ba,aje ko inaba gashinan ta bayyana inzaka nutsu kasan inda kasa gaba to inkuma zumarta tana ibanka tofa akwai kalubale agaba,

Dan haka umarnine wannan kaje ku daidaita da amira Yar gidan babanku merasuwa (mlm tanko) dama tintini ita naso ka aura to ganin Kun rayu gudaya baka taba nunawa ita zabin ka bace shiyasa narabu dakai yanzu ko daka yarda dakarka yarda nagama magana,
Tajuya tashige cikin daki ta bassu asandare agun balle sadiya da bata taba tinanin zata bullo Mata tanan gurinba amma ta shammaceta itadin zatasha mamakinta domin sai ta mayarta abar kwatance hawayene sirara masu zafi suka kwaranyo Mata.


Dagowa yayi ya kalleta sannan ya matso ya Kama hannunta suka Shiga cikin falon karshe daya fuskanci Jan kafa take sai ya sunkuceta bai direta a ko inaba sai akan kujera yashiga goge Mata fuska tare da bata hakuri yace ummata bansan meyasameta ba kiyi hakuri da duk abinda zatayi Miki itadin cikon farin cikinace karkiga batasonki kiyi kokarin hakke Mata komai zai daidaita zatasan kedin kinasonta batasan yadda kike kokari akanta bane shiyasa amma akwai lokaci da zata fahimta kiyi hakuri.


Ajiyar zuciya tayi tace niduk wannan bai dameniba Yaya makomar maganar datayi gameda neman auranka?


Shidin umarni ne tabani dazabi taban sai ince bana bukatarsa yanzu dan haka kikara hakuri da duk abida Zaki gani.


Hannu ta Dora aka ta rusa ihu yanzu shikenan saboda tsana ko haihuwar fari banyiba za,ayimin kishiya wallahi gidanmu zantafi nagaji da tsana danasan tinfarko bata Sona bazan aureka ba ,

tinda naga mahaifiyarka nake doki domin zamowa sirikarta asheni basona akeba nashigesu nagatakaina inama bansami wannan cikinba za,a mayarni bazawara nashigesu.


Duk hankalinsa yatashi tausayi tare da soyayya suka Kara narkar Masa da zuciya sai yaji yanajin zafin abinda ummantasa tayiwa sadiyar gaskiya takurar tayi yawa shidayasan ma Bai hadasu gudayaba duk da hakan bata faruba.


Kamota yakumayi yace kigayan duk abinda kikeso Zan Miki indai Zaki kwantar da hankalinki kinji sweetheart kedin magamin rayuwatace bana hadaki da kowa Musamman danaga ajiyata atare dake.


Kuma shagwabewa tayi tace ni yanzu bana bukatar komai sai kwanciyar hankalin umma shinafi bukata,


Allah sarki da tasan yadda Kika damu da ita datayi hakuri tarungumeki amatsayin ya amma zankuma bata hakuri ,banda wannnan bakya bukatar komai ?

Idanunta tashiga juyawa Musamman data fuskanci suna daya daga cikin abinda Yake Kara shagaltar dashi gareta .

Tace ni yanzu abinda nakeso ba sabgarka bace yafi karfin shigarka Dan Haka banida bukatar komai sai Kai sai umma.

Jiyayi nan duniya ita Yake da bukata babu sama da ita jikinsa yajanyota tare da hade bakinsu gu daya jiyayi kamar Yana wata duniyar dabai taba shigaba itako dake tarko take hadawa sai tasake rungumoshi tare da bashi gudun mawa hundred percent .


Sai da yagama lugwi gwitata sannan ya Kuma bukatar tagaya Masa abinda takeso?


Tace nidin damuwata yanzu wadda take hanani bacci shine tashin da,akayiwa itayena daga gidan da sukeyin haya to akwai wani gida abayan layinnan shi muke ta shige da fuce domin mukama sudawo abin yaci tura shine abinda yafi damuna.

Karki damu nawane kudin hayar ,tasa keyimar fari sannan tace dubu darine amma yanzu akwai wasu akasa ,

Karki damu kikwatan tamin gidan zanje naji yadda tsarin Yake.

Pls share



*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*

🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN* *JINGAU*πŸ™‹





πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😨😨😨😨😨😨


πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*


🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU*πŸ™‹


πŸ…Ώ *14(N)*


🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝



*INA GODIYA DAGAREKU*

mrs naseer inayinki irin sosai dinnan nagode da kaunaπŸ’˜

Tareda Jamila dan baba Ina Miko gaisuwa🀝

Ban manta dakeba Asma kaunarki ta dabance πŸ’˜agaida yarana.

Nagaisheki fatima wakili asha karatu lfyπŸ““

Mmn jidda nagaisheki🀝

Gakuma Yar momy yata ta kainaπŸ’˜

Zainab muhammad uwata ta gariπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°

Sailuba Sully nagode alherinki ya iskeni nagode Allah ya bar kaunaπŸ’˜πŸ’˜

Ummu shahid godiyata gareki Musamman domin Jin dadin comment dinkiπŸ’ƒπŸ’ƒ

Zanyi tuya in manta da albasa hajiya fa,iza gaisuwa🀝
Kuyi hakuri masoya Kuna dayawa mahade a gaba.





Kai abin takaici wai shin haka surikai suke nidai tawa akwai damuwa tare da ita da dayarda zanrabu da ita danayi Musamman datake neman lalatamana rayuwa ,

Mita take tayi kamar zata dakeni narasa yadda zanyi inburgeta ko walwala nacika takance nasaka Mata da cikin daki na cuceshi yanzunma Akan ta tambayeshi kudine sai yadauki dari biyar yabata shine take ta fada dama kyautata dakai Bata wuce haka shima saina tambaya da dai Yar gwalce dake ta wanke ta baka kasha,

Dan Haka Nima dokace duk wata kabani wani abun kodan hidima ta inkuma zakace min hidima tayima yawa Daman bayau kafaraba kekuma dake nake zancen Yar gidan malamai masu yawo da bakin asiri kindena kallona kokuwa juyawa nayi zanshiga daki kozandena Jin mugwayen kalamanta akaina.

Biyo bayana yayi tace auga Kun maidani me dakuka barni Ni kai wato ga mahaukaciya ko too kafuta Naga cewa kayi wani zakayiwa karin ruwa shine zaka bita karshe jarabarta ta hanaka futowa zokashige katafi jarababbiya,

Haka yadawo zai futa amma makakin da zuciyarsa take shiya bashi goyon bayan yimata tini yace baba kiringa hakuri tinkan yarinyar nan tadena ganin girmanki tana hakuri dake kartakurawar tayi yawa.

Au Dan lele Ashe mace na haifawa Kai a lallai maganar mutane ta tabbata shiyasa ake cewa Inka haifi namiji mace la haifawa Ashe kuwa hakane to badaniba indai inada da rai bazan yadda da wannan tsarinba ehe .

Haka yafuta ya barta tana ta mita nikuma nafuto domin Dora girki tare da gyara gidan tin inayi ba walwala har nasamu zuciyata tayi sanyi Musamman dake aiki Yana daya daga cikin abinda Yake debe min kewa.

Irin wadannan abubuwan data ke shine yafara hadamin komai Wanda shikansa mijin yasallama ni yadena dawowa gidan sai can dare sosai inyadawo ma baya nuna dokin San kasancewa dani tin Ina jurewa har nazo gejin Dana kasa jurewa inna nemu hakki na yakance nifa sai dai kawai mukara hakuri har Allah yasa baba hankalinta yadauke akanmu yanzu Ina farawa zata fara kwalla Mana Kira gara ma ba,a faraba kema ba nutsuwa kike samu ba a firgice muke komai gara mubata lokaci.


Abinda na fuskanta Kuma yasan so ya girgiza ni sai Kuma nace zato ne banida tabbas da baya wanka da dare inzai kwanta wankansa na yamma ya Isa amma yanzu kullum yadawo sai yayi wanka tin bansani ba har nafara gani sanda zayyi wankan yakanyi komai da nutsuwa batare da nasaniba sai wata rana da mitar baba tatadani cikin dare .

Wai ni Dan lele wannan wanka da kake kullum dare kamar kwado na meye kaddai halin nakane yadawo karka sake taba Yar kowa kadakko min magana wadda akayi dama ta Isa matarka Bata ishekaba sai ka dakkon magana meye amfanin auren dakayi ka kiyayeni abinda nasaurara yadagan halinkali balle danaji nasa zancen.


Kaiiiii baba wooo ya kikeso mutum yayi karki sa tajiki Dan Allah abinda batasani ba kije ki ballomin ruwa .

Taki Mana wata uwar zatayi dab nakema da dakko make yarka kuriketa andena yima bauta sukansu rabon da kaje kayi musu hidima ankean biyu sai wannan matar me Kama da aljanu.


Zufa zufa itace take kwaranyowa tashin hankali me hakan KE nufi ?


Motsinsa naji nakoma nakwanta amma jikina rawa Yake sosai kirana Yake amma sai nayi shirikamar me bacci , ajiyar zuciya yayi daya tabbatar banjiba komawa yayi gurinta amma nadenajin abinda suke cewa .

Tashi nayi na duba agogo yanzun karfe biyu saura na girgiza kaina tare dajan bsrgo na kudindina Ina tinani lallai akwai wani Abu aboye inko hakane akwai drama dan bazan lamunci abinda nake hasasheba inya tabbata.



Sadiya ce tare da aminiyarta abin duniya yayi Mata yawa cewa take ayanzu Zan iyayin komai Alan matarnan domin haukanta yayi yawa sai na Dede tata gani take abinda nake fada karya ne aminya muje kirakani gurin duk wani malamin da Kika San zai rabata alhaji sabo ko sunanta banason naji Yana ambata ke nifa farraku za,ai musu na dindin din har kanwarsa Dan yanzu ma zancen danake Miki ya biya Mata kudin umara,

Ido ta kwalalo wadda aka Kira da amiya.

Tace ke dan manzo kina me? Sufa dama Dan gin miji haka suke daga sunga Zaka huta sai a,bude maka wuta dan haka kisaki kudi hajiyata akwai wani mezafi zafi shi zamusa yadaki Kan shedaniya kedin kece asama keda yayanki .

Mhn nifa saboda tashin hankali kotakan cikin banabi abin duniya yayi min yawa .

Ki kwantar da hankalinki komai zai normal kisaki jaka hajiyata yanzu wanna lokaci zamu.

Aini ashirye nake gone kishigo kinsan su ummana sun dawo bayan layinnan zance Masa gobe zanshiga sai muhade acan sai minyi waya kawai sai insanar miki na fito.


Baki ta nude tace yaushe ?

Satinsu biyu kenan alhaji sabo ne yakama musu ke komaima ma shiyayi harkayan abinci yakai musu gidanma zancen danake Miki sai nasa yase musu.


Hhhhh Zaki iya tawajena kedin tadabance ba aikin malam ma kinyi nasara balle teacher yasa hannu.


Karimatu ce tare da yayanta suke addu,a tin dayamma suke zaune ita da sadiya suna karanta suratul Yasin Musamman Dan biyan bukatar neman aikin shu,aibu jikinta yabata akwai alheri a sauyin dazai ballan tana da taji cewar gurin da a zashi mutumin inkayi shekara biyu kanayimasa yaro yakan sallameka kaima kanemi naka gurin shinefa kullum sai sunyi zaman karanta Yasin kafa uku sannan ta hada kananan suyi addu,a su shafa.


Aiko ba,a shura wata gudaba sai ga Kira nan daga mutumin da zai zauna gunsa Yakuma nemi da su Gane .


Dama tinda taji zancen samun aikin taje tasamo bashin shaddodi guda biyar masu Dan sauki ta bayar aka dinka Masa domin tasan inhar yaje a inda yake Dakar mutumin yadaukeshi Dan Suma sukan duba suga bame bukata suka dauka ba Dan gudun taba musu dukiya.


Dace ko anyo shi domin yakarbeshi hannu biyu Yakuma yi na, am dashi domin kamalar dsyagani atare dashi ita tajashi ga saurin tsayar masa da lokacin dazaifara zuwa shagon .


Munsha Murna Dan yi yayi kamar yagoyani haka yarikeni agaban yara Dan murna Yana min godiya Allah yayi Miki abinda kikayimin kedin macece ta gari har a aljanna Ina bukatarki domin sunnanki na karamci,
nadaga Miki kafata aljanna indai daga nine kishiga keda yayanki .


pls share


*INA BUKATAR COMMENT* *DINKU NA* *ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA*

🀝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR* *MUTANAN JINGAU* πŸ™‹








πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€


😨😨😨😨😨😨

πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*


🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹


πŸ…Ώ *15(O)*



🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝





ayau shu,aibu yaga banbanci yakara sanin kalmarnan ta Yan uba sun nuna Masa cewar baciki daya suka fitoba sanda yake yiwa Yan uwansa bayanin samun wani aikin bawanda ya nuna murnarsa sai Mita da suka Shiga yimasa tare da cewar ya Raina abinda Dan uwansu yake Masa karshe harda cewa dama inkasaka mutum a inuwa sai ya nemi matarka rana Musamman inyasan yawan samunka sai yaringa kokarin sai ya kamoka .

Tin Yana nuna musu bahakabane harsai da yagaya musu cewar kanin babanane yanemo Masa aikin ,

Aiko Naga tijara nida yarana gidannan nasu tsakanin matasa da matan auren bawanda baizo yaci mutuncinaba daga karshe ma cewa sukai tinda nagama dashi sai yarda mukayi dashi sun barmin Kuma insha allah abinda nayi Masa sai anyiwa yayana.


Kai daga karshe danaga sun ishen tinda Nima bakanwar lasa bace sai dai inba,a taba niba natada tawa tijarar da Saida ta hargitsa gidannasu .

Ni nagode Allah inhar Haka ake gamawa da mutum meye atare da Dan uwannaku Dan Allah kuce daga yau abinda Yake min yadena tsakanin ciyarwa ko tufatarwa inbanda bautar ubangiji da Zama domin Allah mezanyi da irin gidanku masu son zuciya shikansa abin gudun Daban tantance waye Shiba masu son zuciya Kuma kudina da habu yakarba agun shu,aibu da nabari yabani acan amma wallahi sai anbiyani naso kukyaleni bakusan true color Dina ba amma as from to day zamu hadu ko a inane bana shakka karkari kuce yasaken ,


Yo sai me Mara abinyi shine inyana tare da wannan zugar da Allah ya bashi shine zaiji tsoro ammybawanda ya goge da wahalar iyaliba, dazakuce abinda nayi aimin Amin nace Amin Wanda Yake tsoron tafasa shike tsoron konewa yayan iska masu sa arainasu ,


Yau na ballo ruwa domin sai da akatafka babban Bala,i acan gidansu Wanda har sai da hajiyarsa tanemi barin gidan sabida takurar da akayi Mata Musamman Dana Kara huta wutar anbiyani kudina ko inkai mutum kotu.


Dake sudin bawani zurfi sukayi da gogewa aharkar duniyarba Musamman daya kasance basuyi wani cikakken karatuba nan da nan aka hado min kudina aka kawo tare da karbadi mezafi akaina da Kuma me gidan ,

Wannan Bala,in da ake cikine yasa hajiyarsa agaba har sai da tazo gidan tana kuka tare da bani hakuri abin tausayi cin mutuncin datake bani labari anayi mata is too much ga habaici da sukeyi Mata.

Sai nake cemata hajiya mafita kawai kirawo nan Kan komai ya lafa sai insa akara gyara Miki wancan dakin kar Susa jininki ya hau Kinga yanzu kina bukatar kadaicewa kodan kisami nutsuwa.

Dafarko kinyarda tayi sai da nacigaba da rokonta kafin ta tafine shu,aibu yadawo tayi farin cikin ganinsa ni kaina namanta rabon yadawo min cikin kamala sai a Yan kwanakinnan datasani sauyi nayi murna nima tare dayimar sannu da zuwa ,guri nabasu domin sugaisa tare da Kara tattaunawa har take sanar Masa yadda mukayi da ita shima yayi maraba da hakan amma sai tace to Kuna zancen nadawo Nan shikuma megidanfa inkaishi Ina?


Sallama nayi nashiga nakai Masa abinci da ruwa domin Naga baya bukatar wanka yanzu Dan anutse taye sabanin da dayake dawowa afujajan kafa duk kura .



Maimaitawa zancena takumayi Kan yace komai nayi saurin cafewa nace hajiya Ina baban Yana gidan suke Miki haka Dan Haka kimanta kawai kizo ki huta inkika Kwan biyu sai muraki kawai kikoma.



To ai shikenan Allah yayi Miki albarka yaduba bayanki Allah yasa girmanki yayi kyau Allah yadoraki Akan yaya yanki yarabaki da wahalar surukai






πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€

😨😨😨😨😨😨


πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹


πŸ…Ώ *16(P)*

🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝



Me kike nufi Ni kikeso kicewa na,ajiye abin kunya?

Inma banfadaba Kai ka fada bakuma yau nafara jiba cutar dakaimin insha Allah sai Allah yasakamin nayi hakuri dakai da mahaifiyarka amma Baku ganiba burinku kubatamin ko hakan Mai zai dadeku dashi oho dadinta Baku kadaine dangin mijiba in wasu sun Kika wasu sai su soka tinda nasan baduk aka taru akazama dayaba .

Au kina nufi bama sanki kenan ?


To Sona kike inkai da kasoni mahaifiyarka dama nasan basona take ba duk wata hanya dazata rabamu tayi Dan haka alhamdulillah burinta ya cika sai ka bini datakardata before natafi ehe.

Au Mara kunya nibance kin rabani da danaba sai ke to kuwa Zaki tafi da mummunan sako gidanku tinda bakida mutunci irinku dama masuson raba da da uwa to ta Allah batakiba ,


Baki nahau mirgudawa Ina maganganu,aiko yazabgan Mari Wanda sai da naga taurari sun gilmani,


Ihu nakurma tare da birgima Ina neman dauki,

Dariya ta sheke da ita tace dan lele kayimin dai dai nasan kahaifu ba mace na haifawa ba kekuma Mara mutunci tashi ki hada kayanki kibar Mana gida bakar kadara .


Wallahi banyafe ba Allah yasakamin insha allah sai Allah ya bimin hakkina ko a tsokar jikinkane Allah ya futarmin da zalincin da kakemin banda sauran cutar da kukemin harsai kadakeni banyafe ba wallahi,

Lallai kinshirya barin gidan sabida takurar da akeyimiki takaryar da Kika zuba shine harda zagina to kinzagi aurenki Yar banza lalatatta,

Aiko kamar an ingizoshi yakumayo wa kaina zai. daken ,

Daki nashige na kulle kofa nace nafada Allah zai sakamin ,

Kizo kifuta Danba gidan ubanki bane kije kihuta kidawo kikarasa girbar abinda Kika shuka ,

Haka suka cigaba da tattaunawa har Saida suka gama cin mutuncinsu suka futa Niko mamaki ya isheni yaushe habibu ya koma haka ,

da baya goyon bayan cin fuskar da mahaifiyarsa takemin amma lokaci daya yajuye min abin da mamaki.


Tafi tafi layi nayin gaba sai ga shi anzo Kan su sadiya sanda suka shiga jikinta sai rawa yakeyi har Saida malamin yagano rudewarta a hankali suka Sami guri suka zauna bayan sun gaisheshi ne Yake tambayarsu (kunutsu masu karatu kufuskanci wani abu anan yayin zuwa gurin malami).


Wadda tafi rudewar yakalla yayi murmushi sannan yace Al,amuranki yarinya gasunan sun bayyana agareni ba abinda nake bukatar ji sai wani Abu danagani yaki yayewa abun akwai rudu shin menene wannan duhun meke damunki yarinya?


Tinda yafara bayani suka zuba Masa Ido ita kuwa sadiya inbanda tsuma ba abinda take tace malam me kagani kabani magani Dan Allah bansan abinda kagani ba,

Yace kifara bani amsata tikun

Nidai ba abinda Yake tafe dani sai Al,amarin uwar mijina ta ta ku....katseta yayi yacigaba da cewa duk nasan wannan domin Naga komai yanzu me kikeso ayi mata domin ita kanta ba,azaune takeba ahaka dai zakiga kamar ta Allah amma bakin halin dake gareta yayi yawa sai kintashi tsaye burikane da ita akanki ke inta kai cemikima basonki takeba ko ba,ayi hakaba?

Hakane malam ga shi bayaganin kowa inba itaba komai sai ita,


Duk nasan da haka amma kisaki jikinki zamuyi maganinta a hakanma
Dan iskokin kanki masu karfine shine samun saukinki ,
(Inkun lura anan Yana amfani da abinda tacene Yana fakada zancan nata tofa shi malami Haka yake sai ya tinziroka kafara fadar damuwarka sai ya katseka yadora a inda katsaya Wanda da mutum zai lura duk zancen dayayine yaketa maimai tasu)

Juyawa tayi ta kalli aminiya tace bakice komaiba meya kamata ayi Mata?


Yo kedata gundireki aike kikasan abinda za,ayi mata ko Kuma malam kawai kayi musu farraku Wanda ko ance suga junansu ma zasuringa fargabar haduwa.


Angama yanzu abinda Zaki Nemo shine zakaru shekararru guda biyu sai kofaton kura tare da hakoransa inhar akayi aiki dasu to kuwa duk sanda zasu hadu ba abinda zai bayyana ga fuskokinsu sai fuskar kura wannan farrakune mezafi karyashi kuwa sai Wanda yashirya.


Malam hakan yayi sannan kakaramin da na mallaka sonake injuyashi son raina ga Kuma auren da tasashi yayi shima inda hali amantar dashi zancan .


Carbi ne me dubu agefensa yaturo Mata gabanta yace Kama duk Wanda yayi Miki aciki ,

Bayan ta dauki wani kwandalele daga cikine yasa hannu yakarba sannan yayi Yan magan ganunsa bayan ya,ajiye ne yace sai dai kiyi hakuri aure ba fashi amma Kuma Nagano Miki nasara ga rayuwarki amma wani bakin duhu yagilma ciki hakan Kuma baya rasa nasaba da zancen auran sannan Zaki samu alherin haihuwa metarin albarka insha Allah mallaka kuwa kinfarata daga yau indai kinzo ashirye ,


Bamu zoba sai da muka shirya mezan bayar har kudin kayan aikin sabida ba,inda zansamo su.


Kibada kudin aikinki na farko dubu talatin shikuma wannan Zan iya karbar dubu goma Sha biyar ladan aikin Kuma sai bukata ta biya.


Haka tacake Masa kudin shikuma Yana yage baki yakarba tare da dannasu karkashin filon daya tada kafa dashi Bai Basu komaiba amma yatsayar musu da ranar komawa sannan ya shaida Mata aikinta na mallaka daga yanzu yafara aiki domin kantaje gida zai fara ai watar Mata da aikin nata akan alhaji sabo.



Inason yin magana dakai Inka gama hutawa.


Aini indai kinada wata bukata kawai kigabatar babu zancan hutu gareni indai uzurinki ne aikene ko wata bukatarce kinsan nidin nakine kekadai ba Kari.


Dariya nayi nace karkashiga sahun maza masuyin zancen da sukaga dama domin inhar namiji yadora mace kan wannan tafarkin ba lallai ta bulle Masa ba .

Haba karimata da wani zance baki yarda ba kenan ?

A ,a bayardace banyiba kawai ni banida ra,ayin namiji yasani gaba da irin wannan zancen da bazai yiwuba sabida inkayi tinani sanda Allah zai shiryo maka kaddararka ai bance anyi shawara da kaiba ko ?

Inajinki domin ninasan duk abinda Zaki fada yakan zamo karuwane ko da kuwa da kalma dayane dannasan sunanki nakaramci ya biki yakan hanaki son zuciya kinsan ance suna yakan bi mutum.


Murmushi nayi nace ba,a yabon Dan kuturu sai ya girma da yatsa.


Dan haka in Allah ya kaddaro maka kaddarar watafa kadawo kacemin me ko kuwa sai karasa yadda zakayi kazo kanamin borin kunya dazai hanamu zaman lafiya Dan haka duk dadin zancen daza muyi karka dorani a keken bera karshe inzo Ina neman yin abinda bashi kenan ba banida matsala tanan matsalar kawai itace in Allah ya kaddara maka yin wani auren karka munafunceni inkuwa hakan tafaru akwai nadama bakuma daga ko inaba sai a gunka danni da kake ganina ninasan kaina Dan haka duk wani kodani da zakayi karka Kuma zancen nikadaice ba kishiya .


Ido yazuba Mata yace karimatu kenan wato ke duk irin wannan baburgeki yakeba in ma nayi sai kin gwaleni sau tari inason yimiki wani abun amma inatsoron halinki.

Ikon god wani haline Dani karkasa jikina ya mutu dakai Mana nidai kawai nasan banyarda dazancen da nasan bahaka bane bakuma nayarda a Shiga hakina Kuma Nima Ina kokarin kiyayewa to Kuma sai me haba shu,aibu.



Dariya yayi yace to abar zancen haka meyake tafe dake?


pls share


*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*


🀝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* πŸ™‹





πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😨😨😨😨😨😨


πŸ™ *ABINDA KEFARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹


πŸ…Ώ *17(Q)*

🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝



inasauraranki me kikeso kice?


dama kan zancan dawowar hajiya ne dukkanin dakunan kaga ba,agyare sukeba sai namu dana yara Kuma kasan bazata Shiga cikinsu tazauna ba dan hakan zai Zama rashin girmamawane amma fa anawa ganin, Ina fatan kafahimceni ?


Ko ban fahinceki ba ai dole nabi karimatu danwa kike haka mahaifiyata ce fa yanzu mekikeso ayi?


Yawwa shine nakeso mutattauna akai kamata yayi acikin wadancan dakunan daba a,gamasuba daya yakamata ace angyara Mata sai ta sauka aciki kaga bamu takura mataba bare takasa sakewa,


Hakane amma nikinsan banida kudin dazance zandau harkar gini yanzu .

Nasani amma adinga godewa Allah karka Zama me saurin karaya Mana nidai innice Kai cewa zanyi to sabida natabba duk abinda mutum yasa agabansa indai bame mutuwar zuciya neba insha allah zai cimma gaci ,

balle nasan aiba futar banza kakeba baza,a rasa yancanjin dakake ajiyewa ba tinda nasan yanzu ai ba dabaceba.


Hadaransa yayi tare da kauda kai gefe ,


Waiku meyasa Mata kuke hakane daga kunga alamun mutum da naira biyar saikun bullo masa da zancan naira goma yanzu har kinfarga datara kudin dana fara yi to gaskiya nidai bazan iya gyaran daki yanzu ba harkar gini bakarama bace Dan haka niba zanyiba.


In raina yayi dubu ya baci lallai abin babbane yanzu shu,aibu kocewa nayi kabani kudin aibaka bini dabakar maganaba ballantana zancena kasan inda yadosa,


Amma shikenan dasauran lokaci bekureba zaka iya janye kalmarka gareni domin tayimin zafi inda baka
zato,
inkuma bahakaba zamu fara wasan yanzu .


Tashi nayi nabashi guri ko takaina baibi ba wani katon abune ya tokare min narasa tinanin dazanyi kawai sai nashare zancansa nahau sabgata harya fito yakamamin yadda muka Saba daga karshema tsokanarsa nahauyi yayi kudi yagujeni ,

Dariya yakeyi yace waneni ai innayi kudi karimatu kece tafarko wadda Zan waiwaya ,

Nakama haba nace sake lale Ina kabaro hajiyar dayan uwanka nidin dai wani matsayi Allah ya ajiye ni nadaban kafin Nima Inga sanda su saddiku zasu taso kozasu sharemin hawayana ,


Cikin ikon Allah wani hawaye yaziraromin nashare yasake ziraromin domin jinayi shidin bazai iya sharemin hawayenaba lallai yakamata insake zage dantse wajan kula da iyalina kodan wata rana suzamemin gata .


Matsowa yayi yakama hannayena yace me akayimiki indai kalmar Dana fadace kiyi hakuri bansan ranki zai baciba kawai nafada ne bada manufa kigoge hawayen ki karyara sushigi suzaci wani abin nayi Miki,

Gogewa nahauyi dasauri domin nikaina bansan zasu

Please Login or Register in order to submit comment