Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwada sallama daga falo da gudunta tafito tana nagodewa Allah lallai Allah yanasona daya kawominke aminiya ,


Itako aminiya wani irin kallo take Mata tace ya Haka mejego ?

wannan wanna irin jegone duk kinyi wani iri?


Tace kedai zauna kiji ayau basai gobeba nakeson ayimin kowana irin aikine

sonake kije gurin malam yaraba mardiyya da gidannan na har abada tare da umma da wannan tsinanniyar ameeran sonake yayi musu korar kare.




*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA*


🀝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* πŸ™‹








πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😨😨😨😨😨😨



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*


🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹



*πŸ…Ώ31(E FOR EMAIL* )



🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION* 🀝




aminiya ce zaune gaban malam tana Kara Masa haske shikuma Yana dorata tana hawa ,har Yake cewa ai ita wannan mardiyyar inba,atashi tsaye akanta ba to kuwa zata Zama matsala Dan dama bason sadiyar takeba ,

yakara da cewa badan itama sadiyar atsaye take ba da tini tasa yayan ta yasaketa Dan duk wani gun boka da malam tasani Dan Haka yanzu aikinnamu kasashi zamuyi dole akara Shiga tsakaninsa da uwar tasa domin aikin da mukai yadanyi sanyi inkuma akasake tofa kwabar zatayi ruwa Dan Yana dawowa hayyacinsa komai zai iya faruwa,

Game da kishiyarta kuwa ai sai tayi nadamar shigowa gidan zamuyi Mata aikin da sai ta gudu da kafarta sannan duk wani abu daya fara yawo akansa agame da ita zai manta in kuwa yasake lekawa gareta to kuwa kice aikin danayi karyane Nina tabbatar Inna rabasu sun rabu har abada,


Nan dai tacake Masa Rabin kudin data wawuro ta watsa sauran a aljihunta kulla kulle ne guda uku yace daya a binneshi a kofar gidan daga ranar da akasaka mardiyya tabar Kara zuwa gidan daya Kuma abar bada abakin kofar dakin ameera dayan Kuma umma za,a watsawa adakinta inhar tasheka tabar gidan kenan har abada sai dai anemota ko Bata bataba to kuwa gidan tabarshi kenan,

Tace to malam itama ameeran tabisu kawai ,

Yace bar wannan kwallon shegen kwanyarta karfi gareta wannan ma dazaku zuba kuyi addu,ar yasameta inkuma Bai sameta ba kudawo dashiri mezaki akwai Wanda Zan hada inkuwa akayi amfani dashi to kuwa shida Kara kusan tarta sai anbashi umarni Kinga kuwa abin dakamar wuya,


Jikina asalube na wuni Dan komai Dakar nakeyi bansan inada saka Abu araiba sai da wadannan abubuwan suka faru ballantana da malama ramla ta Kuma kashen jiki da labarinta tare da cin fuskar daya biyo bayan sadaukarwarta ga megidanta,


Hajiya ce tazaunar dani take tambaya ta shin ko wani abun nadamunkine?

Murmushin karfin Hali nayi nace laaa Babu komai hajiya kawai dai Yar gajiya ce Kuma nasaba da haka ballantana in Rana tatake dinnan sai kiga abin sai a hankali ,

Kallona tayi ta gyada kanta tace nidai abinda zance akara hakuri juriya da kauda kai shidai namiji sunansa kenan ayyukan sa yawa garesu inyaso kayi dariya sai kaji Nan duniya bayakai inkuma yaso yasaka akasin haka sai kaji kamar kagudu kabar ladanka,hakan bashi zai Sagar maka da gwiwa ba, azama zakasa domin koyaushe kazama cikin farin ciki shi baiki kadawwama abacin raiba Dan haka nidai nasihata gareki yata akara hakuri duniyarma nawa take ita Kuma aljanna nemanta basauki gareshiba ,sai Kuma takautar da zancan kamar ba ita tayi ba tace kingama abincine naga yara suna hanyar dawowa daga makaranta amma kamar baki doraba,


Sunkuyar dakaina nayi Dan sai nauyinta Yakuma Hawa kaina danniyata da ita da jikokinnata suzauna da yunwa har sai yadawo yanemi abinda zai Basu suci,

Nace yanzu Zan Dora kotaliyace ,namike Ina cewa iceko hajiya kinacin taliya kar indafa Kuma bakyaci?

Yo badoleba ai Dole inci a lokacinnan har wani zabine dakai Akan abinci,

dama Allah yadubemu badan halinmu ba Yake ciyar damu Aida danmune da halinmu Aida tini ko buzunmu baza,aganiba kedai Allah yasa mudace,


Duk munci mun koshi sai megidan ne can gefe Yana juya abincin Dana zuba Masa dayagaji da juyawane Yake cewa wai menake gani kamar taliya da manja kinsan bacima tabace yaza,ayi kidafamin taliya in ma itan kikeso kidafa sai kiyi me Miya ko jallof amma Ni wannan mezanci da ita Kai saddiku zonan kadauke bazan iyaciba karkuma akara dafamin taliya in cizakuyi saini adafan abinda zanci,

Hajiya ce tamangantu tace karshenta taliyar kabayar shiyasa katarar da ita dabaku iya godiyaba ga Wanda ya kyautata muku ba yarinyarnan tinda tadawo take kaiwa tana dawowa amma shine kabita da sakamako,


Yoni ko ajikina Daman inasane nayi hakan Yana cewa bayaci najanyeta nakara barbada Mata yaji nabi takanta Kuma ko kallo Bai isheniba naci gaba da sabgata , saddiku ne Yake cewa umma wallahi nidai gobe bazani makarantaba yauma anti ross harta koromu uncle yabata hakuri gashi ankusa fara exam ko kudin term bamu biyaba gakuma kudin exam shima,


Juyowa nayi Zan Masa magana yo aitini ma yabar gun yashige daki cikin takaici nace kace zankawo insha allah sukara hakuri ,

Yace umma kidena zuwa makarantar mu muma abbanmu yadinga zuwa Kinga kowa babansa ne Yake kai kudin makaranta mukuma abbanmu baya zuwa ,

Nace to zaije yakai kubar zancan haka badan mungama Shan iskarba namike nasa nana tayi musu shimfida nace kowa yayi Shirin kwanciya Haka nashiga dakin hajiya nagyara Mata inda zata kwanta nasa Mata net nace Zaki kwantane hajiya kosai anjima Naga da sauro?


Tace Ina Zan zauna duk Kun gudu Kun barni Nima gara intashi dama tin dazu nake gyangyadi,nayi Mata sai dasafe Nima nashige daki ,


Bayan nagama Yan abubuwan dazanyine nayo alwala domin inyi sallar isha ,

Addu,a nake tare da sadaukar da Kai gurin Allah Ina neman daukinsa Ina neman mataimaki domin dukkanin wani hope danake dashi Yana neman rushewa,


Yana gefe Yana sauraran radio nikuma Ina lazimi tare da wasiwasin insakemasa magana koza,a dace Aiko zuciya ta debeni nadan matsa gareshi nace in ba damuwa inason yin magana da kai,


Rage radion yayi yace inasauraranki ,


Dama Kan maganar kudin term din yarannanne kaga yakamata abiya musu domin inbanda alfarma kasan lokacin biyan yayi da,azo ana korosu aigwara koyane Adan rage yafi shirun narashin biyan,

Shiru yayi tare da dauke kansa gefe,

Nace Ina magana kayi shiru,

Wani dogon tsaki yaja yace za,a biya,

Nikuma duk haushi ya isheni amma haka naba zuciyata hakuri nacigaba da magana,

Nace to yanzu dan Allah inba,a biya yanzuba yaushe za,a biya kaga sati biyu yarage ayi hutu gashi ko kudin jarrabawama ba,a biyaba,

Afusace yajuyo yace to inbance Miki Zan bayarba mekikeso ince ,babun zankira kokuwa shekaruna Zan kirga nabaki ,

Aiko nafusata Nima nace inbaka bani shekarunkaba ai kabani wadanda kake tarawa haba nagaji nagaji yaka keso nayi da raina ko sokake zuciyata tabuga kana tabuka wani abunmana amma kasakar min yara komai Ni komai ni bawani taimako to kuwa wallahi dasake inba hakaba Nina gaji Zan dau matakin danaga zaifishsheni,


Au gori zakiyimin kidau abinda yafi mataki ma iya kokarina inayi amma burinki ki kureni menene banayi naga Nima Ina iya kokarina inkinyima wa kikayiwa yayanki Ina ruwana ballema mekike yimusu dazaki sani gaba kina neman kureni haba karimatu kirabu Dani Haka kinfara takuramin dazancanki haba,badamar kiga Ina hutawa sai kin batan nishadina nariga naganeki duk sanda Kika ganni zaune Ina nishadi sai kin batan Rai tome kikeso nayi kuka kikeso nazuna inayi kome,


Nice zakace menakeyi nice nake Bata maka farin cikinka kayimin adalci kenan nidin nidin shu,aibu ko kowa zai Fadi haka nazata Kai bazakace hakaba hawaye masu zafi tukullumin bacin rai sai motsi nake narasa yadda zanyi ,na ce tsakanin makarantar islamiyya Kota boko ko sittira dasauran abin bukatu duk bazaka iya Tina alherina garekaba,

Ai kaji aikaji tsiyar badai Akan school fees kike wannan ba todama yadda mukayi dake Zan bada namutum daya alokacin to yanzunma Zan bayar ajirani,

Aiko nakuma fusata nace tsakanin sanda kace zaka ringa bada na mutum daya zuwa yanzu kataba bayarwar ko ka taba bayarwar Naga tin suna su uku kafadi haka jataba bani kosau daya yanzun su nawane nace sunawane banaso karike abinka Allah zai dubemu zai Kara rufa Mana asiri,

Wai ke duk wannan abun da kikeyi na menene kike Abu kamar Mai iska nidin meye banayi musu naga ko Abu Zan basu cewa kike nabaki Zaki Basu kodama da manufa kikeyi Dan kigayamin maganar banza,

Me kake bani inbasu naira biyar din ko goma ko Kuma taken dakake siyo musu,

Naja majina domin kuka nakeyi bakadanba yau shu,aibu yagirgizani kalamansa sunyimin zafi sosai,nace wai nice karshena yazo a haka yau shekarata goma Sha biyar Ina aikin gantali a hanya duk Dan narufa Mana asiri Ashe aikin banza nake,Ashe kaidin bakasan inayiba nace shu,aibu yau Ina neman danake yakene nazata dabana Mora maka komai Dana Tara gidaje da filaye a wannan sana,ar tawa Amma dame natsira da tijararka wayyo ni πŸ€¦β€β™€lallai *ABINDA KEFARUWA* yau yazo gareni,

Jinayi yajanyoni jikinsa ,Aiko kamar yajonamin shokin Haka naji Dan yanzun bana bukatarsa kusada ni kukana shine saukin abinda zanji,

Yace to Wannan kukan Kuma nameye goge hawayen ai na ce zanbaki niba Haka nake nufiba kece Kika dauki zancen dazafi,


Nadago kaina nace Babu komai shu,aibu Haka rayuwar take na tabbata bazaka taba Zama bango abin jinginataba , nagada hannu sama Ina hawayen me sheshsheka nace Allah kazamo gatana Allah kabani juriya yadda nakekan bautawa iyalina Allah kasa Suma su kyautatamin Allah karkabasu ikon sabamin bazan jureba Allah, Allah kasani kabani yaya yena atafin hannuna tare da yimin biyayya Allah kafinni sanin abinda nakeso ,

Aiko nakuma dafe goshina domin yau nayi kukan Daban tabayiba zuciya nakeji kamar zata Faso kirjina tafuto dama inada alwala zuwa nayi nawanke fuskata nakoma Kan sallaya ,gashidai sallah nakeyi amma kukanake mesauti bawai kukan zuciba,


Kuyi hakuri zuciyata tayi rauni wallahi nikaina kukanna dagaske naci gaba labarin Nina ya girgizani😭😭😭😭😭

*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO* *NACIGABA*


🀝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU*πŸ™‹







πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😨😨😨😨😨😨😨



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™



*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*


🀝 *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹



*πŸ…Ώ32(F FOR* *FANS* )




🌈 *KAINUWA WRITERS* ✍🏾 *ASSOCIATION🀝*




dukkanin tinanina yakare domin ba abinda yanzu nake tunawa sai kalamansa ,

Shikuma sai faman kame kame yake wai nayi hakuri Shiba abinda Yake nufiba kenan rainane yabaci shiyasa nagaya Miki wannan maganganun amma ainasan kinayi Ni ai ba Wawa bane dazance bakya taimakamin ,

ba saina fito nafada agaban kiba ai Ina yabonki ko agurin abokanaina ba inajin yadda nasu matan suke musuba nasan kedin tadabance bako wacce mace bace zatayimin abinda kikeba,

Kuma zakiji dadi insha Allah kicigaba dayimin addu,a zanbaki mamaki munkusa mu huta insha Allah yadda nasaki kukannan sai nasaki dariya kinji karimata sarkin karamci kidena kukan haka,


Uhm nace ai kagama bani mamaki narokeka idan dawani agaba kakyaleni haka nayau yawakilci koma wanne mamaki zaka bani ,

Baki ganeba Ina nufin sai kinsha mamakin alherin dazai biyo bayan kyautatawarki gareni,


Baya najuya Masa nacigaba da istigfari da hailala amma har wannan lokacin bandaina zubar da hawayeba,


Dake bansamu nayi bacci da wuriba sai da namakara Haka natashi fuskata duk tayi luhu luhu idona kuwa yayi jajir fatar idon duk tadago sama dakar nake bude idon hajiya naje nagaisar nadan matsar Mata da Yan kayayyakin gun sannan nashiga kitchen ruwan zafin Dana dafa tin Jiya nadakko najuyeshi sannan nasirka Zan musu wanka bayan munshiga bandakine naga ba sabulu ba makilin ,


Nana nakwalawa Kira wadda take hada musu abin Kari ,

Bayan tazone nake tambayarta nace Ina abbanku ?

Tace Yana falo Yana goge Mana kayan makaranta,

Nace au sunkawo wutarne ?

Tace e kina Shiga gurin hajiya suka kawo,

Kije kice Babu sabulu da makilin yabaki kudin za,a siyo, turus tayi tana kallona Dakar nakuma dagowa nakalleta nace jeki Mana lokacinmu Yana wucewa nagaya Miki Kuma dukkanin abinda zakiyi kiringa amfani da lokaci kodan kici moriyar rayuwar,

Tace umma meyasameki?

Me Kika gani ? yisauri kije bakomai ,matsowa tayi kusa dani tace bakiga inda fuskarki tayiba idonkima yayi wani iri tace umma kuka kikayi ko?


Aiko kamar jira nake sai ga hawaye sharrrr yakuma zirarowa dama Kuma bai tsayaba tinda natashi Yake zubowa sai dai infaki Ido ingoge,


Aiko itama saita rungumeni takama kukan yaranne sukayi cirko cirko suna kallona gefe daya nana Khadija ce ta taho tana kuka dakkota nayi na rungumeta nacigaba dasharar fuska nace kije kikarbo asiyo lokacinmu natafiya goge hawayenki ,

Tace umma Bari inbayar asiyo inada ragowar kudin makaranta na najiya da shekaran jiya

Nace kije dai kikarbodin Nima inada kudin ba Babu bane kice Masa yabaki asiyo,

Saddiku kune yace umma kuka kikeyi?


Murmushi nayi nace wani abune yafadamin Ido ,yace kuka kike Mana ga anti nana nanma tanayi shima sai yakama Aiko sai gani da yara kowa Yana sharar ido duk abinda muke hajiya natsaye tana kallonmu labulen tasaka tare da ajiyar ziciya tace lallai shu,aibu da gyara acikin gidanka har yanzu Kuma ban Gama fuskantar meye matsalarba Dole dai indan Kara zuba Ido kodan daukar mataki.


Wannan Rana dai Haka mukayita agida nida yara Dan ban iya shiryasuba balle sutafi Dole narungumesu mukashiga dakinsu mukayi jugum shikansa break din sai wajan Tara darabi kowa yayishi shikuwa megidan sai Kame kame yakeyi dannadauke Masa Kai yau ko Karin safe bansaurareshi dashiba balle inkaimasa ,

yau ko hannu ma a aikin gidan naki bashi fuskar yasaka duk abinda yadakko zaiyi nakance yabarshi yanzu zanyi har sai da hajiya tace keko barshi Mana yatayaki tinda kunsaba Haka inyabar Miki ai aikin yawa zayyimiki,


Dole nashiga daki nakyaleshi Aiko kannafito yagama komai har wankin yara kusan igiya biyu yayi ragowar nema dake lokacin futarsa yayi yabarsu bayan yatafi kasuwane nafito tsakar gida hajiya natarar tana karasa Wanda yabari Aiko dasauri nayi kanta nace haba hajiya ai zankarasa inake Ina wanki ai sai dai ai miki,

Nakada naraya tabarshi tace ,sai tayi aibasata nayiba inkoma inkwanta in huta kozansami nutsuwa dole nahakura nabarta Amma sai nace nana tabar abinda take tata yata,


Wajan karfe dayane naji sallamar su malama rukayya dafara,ata na amsa musu amma duk sai suka bini da kallo, dolene duk Wanda yaganni ya Kuma kallona, yanayina bamai kyau bane domin kumburin fuskata yabayyana sosai kowa Kuma yagani yasan naci kukane nagode Allah rakasu nayi suka gaisar da hajiya sannan muka Shiga daki,


Ko kunyar idona basujiba ta cigaba dazuba Masa ruwan alwalar shikuma Yana karba danaga abin kamar da iskanci sai na saki labulen nashiga nace it's Kuma wannan wacece?


Shiru yayi sai da nakuma maimaitawa yace bakuwatace ,nace nasani domin ga,alamu nan Ina nufin metazoyi ?

Dubiya tazo Kuma wannan tsayayyar da kikayiwa mutane tamece kije kicigaba da abinda kikeyi bagurinki tazoba,


Kace me?

Dan kayi bakuwa kace natafi tijarani zakayi yayi kyaukallonta nayi itada abokiyarta,


Sai wani fari take suna kallon juna suna murmushi,

Nace Dole kiji dadi sabida KE za,a nuna min iyakata Dan Haka kicigaba da jiyyarsa inhar kedin Yar halak ce ,batadaice komaiba sai kallonta dayayi yace kutashi kutafi kinji kuyi hakuri da abinda tayi muku kunji nagode kigaida babattamu ,

Aiko natsare hanya tare da kamo hannunta sannan na nunata da Dan yatsa nace kinyi nafarko kinyi nakarshe Dan Haka duk randa Kika dawo Zaki Gane kurenki inkunne yaji,


Babace tata ho tana fada kefa ba,a hada hanyar arziki dake saikin nuna hali ita wannan din kisan wace ?

to uwar yarsa ce Dan haka kinutsu kisan inda kanki Yake basa,ar yinki bace Banda ma kaddara ta wada Aida tini itace agidannan to dake Allah yayi sai Yar tafara zuwa kantazo gidan shiyasa abubuwa suka biyo baya Dan Haka inkinkayi Wasa zata maye gurbinki Yar nema,

Ni banfahimci zancantaba nidai nasan saurayi na aura Bai taba cemin yayi aureba balle ace har da ya to Kuma tace dake Yar Allah ya nufa ta fara zuwa kafin auran tome hakan ke nufine?


*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU* *INHAR KUNASO NACIGABA*

🀝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* πŸ™‹






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment