Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su Iftihal sun tafi, mummy daukan wayarta tayi tana dialing wata number, daga wayan akayi da sallama, mummy tana kuka aka ce "Hadiza lafiya, mai ya faru, why are you crying"? Mummy tace "Alhaji my daughter" Kasa karasa maganan tayi tana kuka, Alhaji cikin tashin hankali yace "mai ya faru da Ummi, ina take"? Mummy ta kwashe komai ta fada wa. Alhaji yace "they're targeting my family, they're messing with the wrong ones" "who are they Alhaji" yace "don't worry, yanzu zan sa a karo maki securities, sanan ki kira wata yar uwar ki ta zo ta zauna da ke, Kar kije ko ina tukunan sai abubuwa sun laffa, Kinji ko" tace "toh, aman mai ke faruwa ne"? yace "ki Kwantar da hankalin ki, I'll take Care of everything, Ummi zata dawo gida" daga nan suka yi sallama.

Bude kofan akayi tagan wasu katai sun kai goma kuma sun saka mask, gaban ta faduwa ya dinga yi, a ranta ta sai addu'a take yi. Bayan su wani mutum fari mai uban kyau da ba zai wuce 46 years ba, yana sanye da suit mai tsada, ya saka glass, sanan ya rike wata sanda a hannu shi. Daga gani shi ne boss din. Tsayawa yayi agaban ta, sauran mazan suna tsaye a bayan shi. Ummi ta dago kanta tace "waye kai" fuskar shi a hade yace " Ke yarinya don't question me" with full confidence tace" I'll question you tinda nasan banda wata alaka da ku" daya daga cikin matasan yace" ke dan ubanki, boss din kike ma magana haka " cike da raini ta mayar mishi da magana tace" uba na dai ya fi uban ka, kuma anyi ma boss din naka maganar banza, ai ba shine Allah ba" boss ya daka mata tsawa yace" Yarinya naga kina da taurin kai, toh walahi idan baki natsu ba sai na sauke miki aljannun dake kanki" cikin kuka tace " ni meye nayi muku ni ban san ku ba" yace "bake ki kayi mana laifi ba, baban ki yayi mana"

Kansancewa baban Ummi mai suna Alhaji Aminu babba ne Sosai a EFCC inda yake aiki. He's a very strict man kuma baya cuta baya cutarwa. Wanda yayi kidnapping Ummi kuma wani babba ne acikin gwamnati mai suna Alhaji Muhammad Tahir wanda ya sace kudi over 600 billion Naira. Kansancewa Alhaji Aminu yana ta tracing dinshi for a long time ya samu yayi freezing accounts din Alhaji Muhammad kuma ya kwace most of his properties and businesses, kuma yana kokarin kama shi.

Alhaji Muhammad yace wa Ummi "Baban ki yana da abubuwa na a hanun shi, that's why nima na dauka something that's precious to him" tana hararan shi tace "Allah ya wadar, amman anyi tsohon banza,ace tsoho da kai amman bakada tsoron Allah" yace "Ke ban kawo ki nan kiyi min nasiha ba" cike da karfin hali tace "ai nasiha ya zama dole kam da irin wannan hali, ba ko tausayin yarinya kamar ni balle babba, tuuur Allah dai ya wadar gaskiya kai ta istighifari dan...." "ke! One more word from you, I swear to God I'll blow your brains out" Inji wani dan matàshi. Shiru tayi tana kallon su, hawaye na sauko wa daga idanuwanta ba dama tayi magana salon su harbe ta.

ℹNiko nace dole ummi tayi karfin hali, ganin EFCC ne suka daure mata baya

Gaban gate wata mata da yar buduruwa suna magana da daya daga cikin sabon securities din gidan su Ummi. "Kai ni fah ban son rainin wayo, Ita Hadizan bata gaya maka zan zo bane" yace "bata gaya mana ba, ki kira ta a waya ki sanar da Ita" ta bishi da harara, ta fito da waya tana dialing number. " Hadiza kina jina, wai wannan gajiyayen security naki ya hanani shigowa" mummy tace" yi hakuri shatu, bashi wayan" shatu ta mika masa wayar" Hajiya" " Ka barsu su shigo, she's my cousin and she's together with her daughter " "okay ma'am" yace, ya mika mata wayar ya bude koran. Shatu tace "dan iska sai kayi da na sanin yimin wulakanci a gidan yar uwata, Nana zo muje" ta wuce piiiii kaman zata tashi sama. Cikin parlor Shatu da mummy suna magana "Shatu Wlh ina cikin wata irin hali" shatu tace "Kar ki damu" bayan sun gama maganganun su mummy ta kai shatu dakin da zata dinga zama, dakin yayi mugun haduwa gashi girma. Daga nan ma Nana ta je dakin da aka bata. Zasu dinga zama da mummy domin rage mata damuwa. Nana ce ta sauko ta nufi kitchen ganin samirah na wanke plates tace" ke" samirah bata juyo ba balle ta amsa, cikin tsawa tace" wai ba da ke nakeyi ba kika manna min hauka ko dai kina shaye shaye ne" samirah ta juyo tace" au, ai bansan dani kike ba" Jan tsaki tayi tace "ki hada min tea yaji madara sosai, ki saka like 7 tablespoons of it, yaji Milo Sannan sugar dai dai, sai ki dafa min indomie guda biyu half done da kuma soyayen kwai guda 4" daga hakan, ta fita samirah tace" ae lalai, kaji ra'ayi Watto an samu banza". Washe gari, mummy na zaune akan dining tayi tagumi ga abinci kala kala a gabanta amman ta kasa cin kowanne, sai dai tunani iri iri. Nana ce ta sauko ta nufi dining ta gaida mummy kafin ta zauna, Shatu ta sakko suka gaisa da mummy "Hadiza na gaya maki ki daina damuwa dayawa, so kike kiyi rashin lafiya" "Shatu, this is my daughter and only child we are talking about, idan ban damu da Ita ba, dawa zan damu. Ace yau kwana yafi a kirga shiru muke ji, Alhaji kuma yace wai he's working on it, ya kike so nayi" mummy ta fada tana goge hawayen ta. "Hm, Allah ya sa mu cika da imani Hadiza, yanzu dai kar ki fasa mata addu'a" cewar Shatu. Daga nan mummy ta hau sama taje dakinta, ya rage Shatu da Nana a dining, murya kasa kasa Nana tace" Hm,umma ni fah ban yarda anyi kidnapping Ummi ba, kilan dai wata gantalin ta tafi a wani garin don irin kudin da iyayen ta suke danka mata, ai wani zai iya ciyar da iyalinsa for many years da shi" Shatu tace " ban taba sani na haife butulu ba sai yau, ke dai kulum ban san maiyasa bakin baya shiru ba, uban meye ta miki, yo dan ubanki idan ma gantalin ta tafi ba albarkacin gantalin bane kike zaune a gidan su ana miki gata yarda ake mata. A gidan uban naki da muka baro waye kika ishe shi kallo balle a kula da ke" turo baki tayi tace "uhm Umma dai abin zuciyata na fada" Shatu tace "tashi ki bani wuri dan kaniyan ki" tashi tayi piiiii ta koma parlor tana kallon TV.

✏📖

Ummi kuwa tayi butu butu, ta rame kaman ba Ita ba. Idanuwan ta sunyi baki sun kumbura tsaban kuka da rashin bacci. Bude kofan akayi tana kallon wanda ya shigo ciki, karasowa yayi, ya kwance mata igiyoyin da aka daureta dashi yace "tashi" a hankali ta mike, jiki ba kwari yace "muje" tace " ina zamu" wani shegen kallo yayi mata, ta dauke kanta ta nufi kofar ta fita. Bin mutumin tayi har inda akayi parking wani mota ya bude ta shiga Shima ya shiga ya fara tuki, suna cikin mota Ummi tace "dan Allah zan sha ruwa, I'm thirsty" kallon ta ya dan yi bai amsa ta ba, suna cikin tafiya yayi parking daidan wani karamin shago a siya bottle water mai sanyi, ya bude ya mika mata. Godiya Ummi tayi mai ta amsa ruwan, bayan ta shanye tace "you're a good person" kallon ta ya kara yi bai ce komai ba. Gaban gate dinsu ya ajiye Ummi ta sauka da sauri, mutumin yayi zooming off. Knocking ta dinga, mai gadi ko yana kankame da radion sa ya ji ana knocking. Tashi ya yi bude da sauri, Ummi ya gani tsaye, ya goge idon shi dan ya tabata ko Ita ce, sanan ya leka waje ya gan ba kowa yace mata "shigo ciki da sauri kar su dawo" Ummi ta biye mai ta shiga sa sauri. Shiko har da saka sakata. Tuni Ummi ta shiga cikin gida ta tarar da Samirah na goge goge, jin an bude kofa ta juyo, da mamaki tana kallon ummi tana mata sannu. Ummi tambaye ta "ina mummy" "tana sama tare da su aunty Shatu" ta hau sama ba kowa, ta shiga dakin mummy ba kowa, sai taji alaman cewa mummy na bandaki. Hawan gadon mummy tayi ta Kwanta. Mummy ko da ta fito taga Ummi akan gado....ta nufe ta da sauri tana kuka, Ummi ta mike tayi hugging dinta for almost 5 minutes. Chan mummy ta sake ta tana duba ta tace "Ummi ba suyi miki komai ba ko, kalla yanda kika rame" ta fashe da kuka "mummy dan Allah ki Kwantar da hankalin ki, ba gashi na dawo ba, basu yimin komai ba" mummy ta tashi ta shiga bandaki ta hada mata ruwan wanka tace "taso muje kiyi wanka", Ummi ta zaro ido tace "mummy ke zaki min" "ke banson surutu, taso nace" ta tashi suka shiga bandaki, Ummi ta cire kayan ta, ta shiga bath tub din da mummy ta hada mata ruwan zafi da kuma disinfectant aciki. Sun fi 20 minutes aciki kafin Ummi ta dauraye jikin ta tayi alwala suka fito. Mummy ta kira Samirah a waya tace mata ta kawo abinci dakin ta sannan ta sannar ma Shatu dawowar Ummi, daga nan ta katse wayan. Ummi ta saka kayan bacci ta hau gadon mummy ta Kwanta, ummi na magana "sun ce wai daddy ne ya kwace wasu properties dinsu, and that's why they kidnapped me. Apart from that basu ce komai ba mummy" mummy tayi ajiyar zuciya, sallama Shatu tayi Nana na biye da ita suka shigo cikin dakin "Ah ah Ummi barka, ke nake gani yau haka...oh Allah mun gode maka" ta karaso tana taba Ummi "aunty ina yini, Nana ya kike" Ummi ta gaishe su, suka amsa mata. Suna ta magana har Samirah ta kawo ma Ummi abinci, Ummi ta mike ta je dakin ta rike da tray din, Nana na biye da ita suka shiga dakin Ummi. Nana ko sai zare ido takeyi kamar wace tayi sata, a ranta tace "Chaap Lalai masu kudin nan akwai albazaranci, wai dakin yar su ce nan, mu ko dakin uwata bai kusan wannan kyau ba balle a kai ga namu" Ummi ta zauna akan cushion ta kuna TV tana kallo tana yan ciye ciyen ta bata kula Nana ba dan daman ba wani shiri suke ba. Ita ko Nana tayi nisa a tunanin da takeyi. Ummi ko ta cinye abincin ta tass ta sha fruits ta mike taje tayi alwala nan ma Nana ta fita daga dakin. Ummi tana kan daduma ta tuna su Iftihal ta mike don taje dakin mummy. Shiga tayi ta gan mummy na danna wayarta, mummy kaman tasan abin da ke ranta tace "Ummi yakamata ki kira friends dinki, da ba kya nan wlh ko wane weekend sai sunzo su duba ni, ranan ma sun hada ni da iyayen su akan waya suka gaishe ni" ummi tace "ai mummy abin da yasa na shigo kenan, sun kwace min wayata mummy" mummy tayi ajiyar zuciya, cike da masifa tace "amman shine da kika zo baki sa anyi blocking number din ba salon su zo suyi wani mugun abu da layin naki" "mummy yi hakuri, it skipped my mind" mummy ta mika mata wayarta "yanzu ga nawa maza kiyi calling customer care ayi blocking yanzu yanzu kafin ki kira su kawayen naki" Ummi ta kira akayi mata blocking Sannan ta fara kiran Iftihal "Assalamu Alaikum mummy ina yini" Inji Iftihal "toh mabaruka ba mummy bace" jin muryar Ummi ne yasa ta saki wani ihun murmishi tace "Ummi kece, ina aka kaiki Wlh munyi kewan ki ba kadan ba" suka dinga zuba hira, daga karshe Ummi tace bari in kira Zahra" daga nan ma ta kira zahran. A kwana a tashi, yau 2 weeks da Ummi ta dawo gida, sauka Ummi tayi ta tarar da Nana tana ta zagin Samirah, Ummi ta karasa wurin su tace "lafiya dai, ya haka ne" Nana tace "kiji min yar rainin hankalin nan, cewa nayi bazan ci wainan da tayi ba, ni ta soya min samosa kuma ta hada min tea, shine take gaya min maganar banza wai tana aiki yanzu baza ta iya ba" Ummi da ta gama ji ta zauna kan kujeran dining, ko kallon Nana bata yi ba balle ta bata amsa, sai tace wa samirah "Dan Allah ni ki kawo min waina in ci pls, ki kawo min da fruits" cikin sanyin murya Samirah ta amsa mata. Nana ta sake baki tana kallon Ummi wato ta mayar da Ita banza. Ummi ko sai aikin danna sabon iPhone 13 dinta take yi. Piiiii Nana ta wuce wurin Shatu ta fada mata komai, Shatu tace "ai wannan Ummin tana da nata bakin halin amman kar ki damu zanyi maganin ta" daga hakan ta sauka kasa ta bar Nana a dakin. Kitchen ta wuce tana hararan Ummi bata ma san tana yi ba. Samirah na ganin Shatu tasan cewa akwai problem "ke dan kaniyan ki, Watto ke kin isa da har yar gida zata Saki abu ki kiyi" Samirah cike da raini tace" wace yar gida kuma dai, banda aunty Ummin akwai wata yar gidan ne kuma aunty"? Shatu kaman zata fashe "ke ni zaki gaya wa bakan magana, amman Wlh anyi yar Shegiya munafuka" "ni dai ba yar Shegiya bace, tunda uwata na da uba kuma ya na nan da ransa" cikin fishi Shatu ta fita daga kitchen din ta Nufi wurin Ummi tana masifa "ke kuma kina ji kina gani wata bare mai aiki tana raina yar uwarki amman baki dau mataki ba" Ummi ta kalle Shatu for like 8 seconds Sanan tace "aunty ni dai ban ga dalilin da zai sa ku tada jijiyar wuya ba. Ai nasan dai Samirah baza tayi mata hakan babu dalili ba" "toh kaniyan ki nace, dage ke har Samiran" daga hakan ta wuce piiii. Ummi dakin ta ta wuce don ta shirya zuwa school bayan ta kamalla breakfast. Tun da aka sace ta, yau ne zata koma school. Wanka tayi, tayi sallah tayi yan shafe shafen ta Sanan ta Nufi wurin wardrobe dinta ta bude ta fito da wata ash Abaya mai kyau, ta saka bakin takalmi da jaka ta saka shade dinta ta fita daga dakin taje wurin mummy dan tayi mata sallama. "Oh harkin shirya zaki wuce" "eh mummy" mummy tace "toh dauka car key dinki daga wancan locker din ki mika wa Zakariya, daga yau he's your guard kuma shi zai dinga kai ki school" "toh mummy, amman why would you get me a bodyguard, I don't like it, I want to be comfortable ba sai kowa ya san cewa I come from a rich home ba" "Look Ummi I understand amman it's not safe for you to start going out alone after what happened, kuma daddyn ki ne yace, ki dinga fita da guard" "toh mummy, I get it, thank you Allah ya bar min ku" cewar Ummi, mummy ta amsa da "Allah ya tsare, a kula da kyau pls" Ummi tace "okay mummy" daga nan ta fita.

A school, Zakariya na ta bin Ummi duk inda zata and this was making her feel uncomfortable, daka gan shi kasan he's a bodyguard, yasaka black suit da black glass fuskan shi ba rahama. Sai kallon Ummi akeyi wasu na cewa ai Spoilt brat ce, wasu kuma na gulman cewa anyi kidnapping dinta, Ita Ummi ko kallo basu isheta. Ta shiga class still Zakariya na biye da Ita, ganin su Iftihal yasa ta nufe sits din da suke suka gaisa Zahra da Iftihal kaman su hadiye Ummi tsaban dadi. Iftihal ta daga kai taga zankalelen dake gefen ta, muryar kasa kasa tace "Ummi shi wannan kuma fah" Ummi tace "Wlh mummy ta hada ni dashi wai he's my bodyguard and driver" Zahra tace "ai hakan yayi gaskiya, mummy ta kyauta". Suna hira Ummi tayi shiru ganin cewa daddy na kiran ta, Sannan ta daga "Assalamu Alaikum, daddy ina yini" "wa'alaikum salaam my dear, hope you're doing fine" Ummi tace "Alhamdullilah, wai daddy har yanzu ba ka samu hutun bane, yaushe zaka zo" "Ummita kenan karki damu yar daddy very soon zaku gan ni. Dazu nayi magana da mum dinki and she said you went to school, komai dai dai ko"? Ummi tace "yes daddy, amman maiyasa ka hadani da guard, ana magana na kuma ana kallo na, I'm really uncomfortable" Daddy yayi dariya yace "yar daddy you'll get used to it Kinji, it's for your own safety" Bayan sun gama maganganu su, su kayi sallama. After first period, sun fita waje Zahra cike da tsokana tace" gobe ne fah event din, gashi baki da date" ummi ta turo baki bata ce komai ba, "wai baku shirya da Farid din bane" Inji Iftihal "mun shirya, har muna chat ma" suna magana, sai wani guy rike da rose flower yazo ya mika wa Ummi ya wuce ba tare da yace mata komai ba, sai wani ma yazo still with another flower ya danka mata ya wuce, haka again and again and again sun kai 7. Ummi ta zama abin kallo, ga hannun ta cike da beautiful roses pink and red. Tana cikin raba idanuwan ta, kawai sai ga Farid ya bilo rike da babban rose, Woahhhhh, yasaka designer English wear da shegen shade, yayi kyau, mata sai crushing suke suna kalon shi har ya nufe wurin da ummi take tsaye, ya cire shade din yana kallonta Yayi kneeling a gaban ta yaUmmiUmmi will you be my date"? Kunya kaman zai kashe ummi tace "yes I'll" tana juya mai ido ta amsa rose din. Yellow kuwa da take kallon komai, kaman zata fashe. Su Ummi da Farid kuwa fita suka yi daga department din Zakariya na biye dasu a baya, sai kallon su akeyi. School recreational center dinsu suka je, dukansu suka samu wurin zama. Iftihal da Zahrah suna hotuna a snap, Ummi kuma na zaune da Farid. Zakariya kuwa na tsaye kaman statue a bayan Ummi. Murya kasa kasa yace "Favorite, welcome, it's good to have you back" Ummi ta kaleshi kawai tayi nodding kanta, yace "Menene naga kaman you're not comfortable" tace "how will I be comfortable, kawai ka shigo cikin bainan nasi kazo kayi kneeling down as if you were proposing, gashi na lura a gaban psycho din can akayi komai, salon ta zo ta kara zagi na a kanka, ai ko Wlh this time around I won't take it likely with her if she tries such" murmishi kawai yayi dan maganan ta ya bashi dariya, cikin tsokana yace "Fisabillilahi mai tayi miki, mai yasa kike kiran ta psychopath, she's not mad and bakisan cewa she's my friend ba a close one for that matter, so kina hurting feelings dina idan kika zage ta" last kalmar shi ne ya bata haushi wai tana hurting feelings dinshi, to hell with his feelings ta hada rai taja tsaki tayi shiru. Shigowan yellow kenan cikin recreational center din Ita da friends dinta ta hango Farid da Ummi, ta nufe wurin su tana kirkiro murmishi. Tana zuwa wurin su ta tsaya kaman pole wire tana rangwada tana kalon Farid wanda shima ke mata kallon irin are you alright. Ummi ta daga kai ta mata kallon tara saura ta cigaba da dana wayarta sai yellow ta kalle ummi tace "ke kuma ya da kallo haka dai, ko kanki na hau na tsaya ne mallama" daga haka ta ja tsaki tana hayaniya tana spark, ummi tace ma Zakariya "fita da mahaukaciyar nan out of here, kaina na ciwo" ba wasting time ya janye yellow, daman ba nauyi gareta ba, su Iftihal kuwa suka yi streaks da yellow ana jan ta, Farid ko sai bin su da kallo kawai ya keyi ya girgiza kai irin Sai da tasa akayi embarrassing dinta. Mikewa Ummi tayi tana kallon Farid tace "I guess i hurt your feelings again right" daga haka ta wuce suka fita daga recreational centre din suka koma class. Ana ta gulman abin da tasa akayi yi wa yellow, suna shiga suka tarar da yellow na kuka friends dinta na bata hakuri, daya daga cikin friends din yellow tace "Kema gaskiya yellow akwai karambani, kina ji kina gani yarinyan can tafi ki kusan a kowanne bangare amma still kina shigan sabgar ta bayan ba Ita ta fara miki abu ba. Kina gani dai duk kudin Ummi bata isa ta nuna ma Farid kudi ba amman a hakan dai da kyar ya shawo kanta har suka fara abokantaka. Yellow abin da zan gaya maki shine ki cire Farid daga ranki, don naga akan shi kike wannan haukan, Farid ba class dinki bane Wlh kuma ba sonki yake yi ba, he's just being nice to you amman it doesn't mean he's in love with you. In ba abinki ba ina ke ina competing da yarinyar can, yarinya da ko kayan jikin ta kadai zai iya biya miki school fees dinki na gaba dayan semester nan. Ke ko mai kike dashi, dan Allah ki fita daga sabgar su, they're not your class kiyi hakuri Allah zai kawo wanda ya dace dake" yellow ko sai shakan kuka takeyi suka cigaba da bata hakuri.

Su aunty Shatu kuwa da yar ta sun baje kolin su, sai zuba mulki da iko su keyi kaman gidan uban su. Shigowan Ummi kenan daga school, ta tarar da aunty shatu da Nana suna kallon TV, Ummi tayi musu sallama da gaisuwa amman basu amsa ba. ko a jikin ta, ta hau sama taje dakin mummy, ganin cewa bata dawo daga office ba, ta fita ta je dakin ta, ta shiga bandaki ta yi wanka da alwala Sannan ta fito tayi sallah bayan tasa wata simple kayan gida. Ta sauka kasa, ko kallon su aunty Shatu bata yi ba taje dining tana kiran samirah. "Samirah meye kika dafa yau" "aunty paten doya nayi don shi mummy tace a dafa, nasan ba kya ci amman ban daura abincin ki a wuta ba don mummy tace in bari sai kin dawo sai ki fada abin da kikeso" Inji samirah, ummi tace "Kar ki damu ba sai kin dafa min komai ba, kije ki huta" cike da damuwa samirah tace "toh mai zaki ci, ai ba zai yu ki kwanta haka ba" ummi tayi murmishi tace "no don't worry, Zanyi ordering abinci yanzuvkawai ki kawo min fruits amman Kar kisa pineapple pls" Samirah ta amsa mata daga hakan ta juya. Su aunty shatu kuwa da suke jin komai sai mamaki suke yi ace wai bata cin paten doya, Lalai Hadiza ta bata yar ta. Suna nan zaune a parlor har mummy ta dawo daga office, Ummi ta mike da gudu taje tayi hugging dinta, mummy ta gaisa da su aunty Shatu Sannan Ita da ummi suka hau sama Ummi na rike da handbag dinta. Bayan sun shiga daki, mummy tayi wasu ayyukan ta. Ummi ta turo baki tana kallon mummy da ke Danna wayarta "ke lafiya kin kura mini ido haka" Inji mummy "toh mummy wai yaushe zasu tafi, sun fah dade, Ita aunty Shatu baza ta koma gidan mijin ta bane. Tun da su ka zo suke wulakanta mana ma'aikata all they do is sleep, eat and cause trouble all the time. Ni shiyasa ma bana shigan sabgar su" mummy tace "ranan nayi mata magana, amma gani take Kaman koran ta nake yi" ummi tace "toh mummy sai meye wannan damuwanta ne ba naki ba" mummy tace "ya isa toh, tashi ki bani waje" Ummi ta fita tana tabe baki. Washe gari, kasancewar ranan event din kenan, Ummi tayi wanka bayan tayi sallahn asuba sanan ta koma kan gado ta Kwanta. Wuraren 8:30 na safe ta sauka don tayi breakfast, tana gama breakfast ta kira makeup artist dinta. Around 10:00 makeup artist din tazo ta fara shirya Ummi, ana cikin yi mata makeup,

Please Login or Register in order to submit comment