Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wai in tura mishi account number" aunty shatu tayi kuri da ido, tana kallon Ummi kamar zata hadiye ta, Inna kuma ta fara kuka, sai kuma ta Saki Kabbara tace "Allah mun gode maka". Mummy tace "Ummi lefe har na 12 million sanan maimakon su hada kawai da kansu, sai sun turo kudi ne, ba gwara ki ce musu su hada ba, ko ya kiga gani Nadeeyah" Inna ta Saki baki tana kallon mummy, sai tace "ke dai Hadiza wata sa'in kina abu kaman baki waye ba, ai yanzu iyayen mace ake ba kudi su hada mata kaya kawai, salon a bar masu miliyan sha biyu su cuce min jika, su ki siya mata abin da ya kamata. Su turo kudin kawai, zamu siya mata kaya na gani kuma na fada, wanda babu wanda zai ce Ita ba diyar baban ta bane, ai tunda Allah ya tsameta daga cikin mu ya mayar da Ita cikin masu kudin kasan gaba daya, Ita ma za ta dinga yi kamar yar sarki. In sha Allahu kayan da zamu siya mata sai ya girgiza su, yanda babu wanda zai raina min jika ta a gidan. Ana gama hada kayan kuma Za'a hada ni da dreba in kai gidan, nima zan kara duba biyar Ita akan Kudin, idan an kai sai ace musu kayan miliyan sha biyu ne da dubu biyar" Nadeeyah tace "kwarai kuwa Inna hakan za'ayi, kaya kam sai dai wanda bamu gani ba" mummy tace toh shikenan, a aika kudin zuwa account din Nadeeyah kawai, Nadeeyah ki ba Ummi account number dinki" Nadeeyah ta ba Ummi account number har ta tura ma Farid, kan ka ce mene Nadeeyah ta gan alert. Su aunty Shatu kuwa, sun zama yan kallo, sai bin su kawai suke da ido, mikewa aunty Shatu tayi ta nufi dakin ta cikin sauri, ta dau wayar ta ta kira kawar ta Sajida. Sajida na dagawa aunty Shatu ta saki kuka tace " na shiga uku Sajida na lalace, Wlh tun da nake ban taba girgiza irin ta yau ba fah. Yanzu aka aiko miliyan sha biyu daga gidan Alhaji Nagoda wai a hada wa Ummi kayan lefe. Gashi dai na shawo kan Nana ta yarda wai zata aure shi, amman Wlh sajida na rasa yanda Zanyi, gashi bikin na ta matso wa" Sajida tace "karki damu kanki Shatu, na tabbatar maki cewa aikin malamin nan zai ci, ai ce min yayi, ko sunyi aure baza su samu kwanciyan hankali ba kuma yace min Nana sai ta samu alaka dashi" jin hakan yasa aunty Shatu ta washe baki tace toh shikenan,daga nan su kayi sallama.

✏📖

Su Noor tare da Nadab da Yaya babba(yayar mummy da Nadeeyah) suka yi sallama suka shigo. Tuni gidan ya dau hayaniyar su. Dukan su suka gaida Inna cikin ladabi, ta sa masu albarka kafin ta wuce daki. Ummi kuwa dasu Noor harda Nana suka wuce dakin ta suna hira. Noor tace "su Ummi zadukzama Mrs, God when"? ta karasa maganar tana turo baki, duk suka kwashe da dariya, Nana kuwa ta labe a jikin gado kamar wace tayi sata, chan dai ta mike ta fice daga dakin, Nadab tace "Wancan ba yarinyar cousin dinsu mummy bace" Ummi ta gyada kanta, Noor tace "I don't like her yarinyar tana da raini, look at how she was just staring at us" suka dinga hiran su, suna maganan anko.

Saura kwana biyu bikin Ummi, tuni kuwa gidan ya fara cika da jama'a. Aunties din Ummi from both sides suna gidan da wasu cousins dinta. Amman wasu zuwa suke su yini Sannan su wuce da yamma. Daga bangaren su mummy, Nadeeyah, Noor da Nadab, Sannan Shatu da Nana, dasu yaran yaya babba masu suna: Kamila,Deejah,Mimi da Hajjo Sune suke kwana a gidan. Daga bangaren daddy kuma, Yaran kanwar shi masu suna: Amina, Zainab da kuma Walida Sune suke kwana a gidan, sai kuma Zahra da Iftihal. Duk yan matan sun shaku da junan su sosai, they became friends amman banda Nana. Suma basa son ta sabida tana yawan yi musu raini kuma su basu yarda su dauka shirme ba. Tun ana wata biyu bikin Ummi aka fara mata gyaran jiki, wani kyau tayi irin na amare.Kasancewar a gida ake yi mata gyaran shi yasa bata fita balle ta shiga rana. Fitowa tayi daga bandaki domin tayi wanka bayan an gama mata gyaran jiki. Noor, Nadab da Iftihal ta gani suna gwada ankon lace dinsu, Zahra kuma da yaran Yaya babba suna saka wa Ummi wasu kaya a wardrobe dinta, Amina, Zainab da Walida suka shigo da trays guda uku dauke da abinci da drinks kala kala. Ummi tana gaban mirror tana shafa kwallacha da wasu turarukan ta, tace "toh yan mata, gobe zamu sa lalle, Noor ta kira one of the best henna artist in town, su uku zasu zo don muna da yawa sanan Inaso mugama da wuri" suka dinga hiran su suna cin abinci. Su Inna da sauran manyan matan suna ta zirga zirga na biki. Samirah kuwa sai jabgan aiki takeyi, sanda aka karo masu aiki guda hudu kafin ta samu saukin lamarin. Tunda aka fara hayaniyar biki, aunty Shatu bata samu natsuwa ba, kulum bata gida, tana nan tana bibiyen malamai akan lamarin Nana. Yau dai biki saura kwana daya chuk! Baki suna ta zuwa, ana ta sama da kasa haka ma a gidansu Farid. Samirah ce ta shigo dakin Ummi tare da sallama tace "aunty Ummi, wai aunty Nadeeyah tace kizo" Ummi tace "okay ina zuwa" daga haka Samirah ta fita. Walida yar gidan kanwar daddy tace "toh amarsu tashi ki wuce, kila wata nasihan dai za'ayi maki" Ummi ta fita, taje dakin dake downstairs, ta shiga tare da sallama. Aunty Nadeeyah na zaune kan carpet da kwalin magungunan mata wanda tasa aka hado daga Maiduguri, Ummi ta karasa ta zauna kusa da Ita. Aunty Nadeeyah ta bata wani cup wanda yake dauke da daya daga cikin magungunan tace "oya kwankwada ki bani cup din" Ummi ta tsuke fuska tana kallon abin da ke cikin cup din "ni Dallah kina bata min lokacin" cewar aunty Nadeeyah tana hararan ta, Ummi ta kapa kai har ta shanye, Nadeeyah ta zuba mata wani, Shima ta shanye tass sannan ta bata gumban kwakwa taci, gumban yayi wa Ummi dadi Sosai, daganan tayi mata wasu nasiha Sannan ummi ta fita ta koma sama.

A bangaren su Farid kuma, cousins dinshi maza wanda suka yi aure suma suka sa shi a gaba suna yi mai nasiha. Farid ya kosa gari ya waye, dadi kuwa kaman zata kashe shi. Ammi ce take ta kaiwa da kawowa Ita da yan uwan ta mata da kuma yan uwan Alhaji Nagoda. Su Rayyana suma suna ta fito da kayan bikin suna hadawa da takalmi da jaka da zai shiga. Ana ta hidimar biki, duk wani abu na ci da sha a wurin biki, yana hanun ammi da kanwarta aunty Turai.

Tabarkallah, Ummi tayi kyau na fitan hankali ranan da aka fara bikin, kwana hudu akayi ana biki(Walima, Bridal shower, Arabian night da Daurin aure) kuma kowace rana da shigar bikin ta, Ummi tayi kyau harta gaji, haka su Iftihal da sauran kawayen amarya sunyi kyau. Biki ta amshe sunan biki, biki irin ta manyan kasan. Convoy din motoci guda bakwai akayi da aka tashi kai amarya gidan ta. Sun isa gidan su Farid suka sako daga motan, su aunty Nadeeyah da su kawayen amarya suna biye da Ummi. Rayyana ce ta hango su ta shiga bangaren Ammi da wuri dan sannar masu cewa an kawo ummi. Su Ummi suka shiga gidan da sallama, Ammi da yan uwanta da sauran abokan arziki sunyi farin ciki Sosai. Anyi budan kai, Ammi ta sa masu albarka, daga nan aka kai Ummi bangaren ta. A bangaren Ummi su aunty Nadeeyah da wasu gwagwonin Ummi suka yi mata nasiha tare da yi musu fatan alkhairi, daga nan kowa ya tafi ba wanda aka bari bayan Ummi ta sha kuka.
Bude kofan yayi a hankali ya gan matar shi a zaune tana danna wayarta ta. Shigowan shine yasa ta daga kanta a hankali sannan tayi smiling. Farid ya karasa inda Ummi take zaune ya sa hanun ta acikin nashi yana kallon kwayan idanuwan ta yana fada mata kalaman Soyyaya mai shigan zuciya, hugging dinta yayi sannan ya fara kissing dinta, kafin suka mike, kowa yayi alwala sannan suka gabatar da sallah. Bayan sun Idar ne Farid ya kawo kazar amarcin daya siyo, bayan sun gama ci Ummi ta kwashe plates, Farid kuma ya dauke cups din suka kai kitchen ta wanke sannan suka koma daki. Daga nan kuma.....hmm.

Karfe 4:50 na asuba Farid ya tashi, ya kunna side lamp dinsu, yana kallon Ummi yana murmishi, kissing dinta yayi ya cigaba da kallon yanda ta shige jikin shi tana bacci. A hankali ya fara shafa mata bayan ta har zuwa waist dinta wanda ta saka masa Jigida. Bude idanuwanta tayi a hankali tana kallon shi kaman zatayi kuka tace "dan girman Allah da Annabi kar ka min komai, wlh nagaji, duk jiki na ciwo yake yimin" Farid ya danne dariyan da ta bashi, ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace "ba komai zanyi miki ba Wifeyyyy, amman I can't resist you" Ummi ta harare shi tana kokarin mikewa da sauri amman ta kasa, sai tayi a hankali ta tashi, ta yaye duvet din ta lulube kanta dashi ta nufi kofan bathroom tana bude kafafuwan ta, ganin haka yasa Farid ya mike da sauri ya dauke ta sama ya shiga dasu bandaki, ya tara ruwan zafi a jacuzzi, ya saka disinfectant Sannan ya saka Ummi acikin Ruwan, daga hakan kuma ya fita daga bandakin ya je ya cire zanin gadon su dan akwai few blood stains. Ba dadewa ba ya koma cikin bandakin ya kara chanza wa Ummi ruwa sannan yayi musu wanka, ya fito da Ita daga cikin ruwan suka yi alwala, ya dauke ta ya ajiye ta akan gadon su, ya shiga closet dinta ya saka jallabiyan shi sai ya fito mata da wata skimpy dress da kuma hijabi. Ummi ta shafa turarukan ta sannan Farid ya sa mata kayan ta tare da Hijabin, ya shimpida sallaya ya daura ta a kai sannan ya fita dan zuwa masallaci. Ummi na idar da sallah ta koma kan gado ta fara baccin wahala, da ka ganta kasan a gajiye take. Wuraren karfe 6:20 Farid ya dawo daga masallaci. A hankali ya bude kofan ya gan tana bacci, closet ya shiga ya cire jallabiyan shi, sannan ya dawo ya hau kan gado, ya lulube su da bargo ya rungume ta har bacci ya dauke shi. Wuraren 9:30 ya tashi, ya gan ummi tana sanye da wata hadaddiyar atampa, wanda aka dinka mata fitted gown da ya fito da figure 8 dinta, ta daura dankwalin ta simple kuma yayi mata kyau, ga hanun ta da zoben zinari kala kala, ta yafa gyalen ta, ta dauka wayarta zata fita Farid ya tambaye ta "baby ina zaki"? tace "zanje side din ammi in gaishe ta" Ummi ta karasa wurin shi tayi kissing dinshi a hankali tace "good morning babe" Farid ya lumshe idon shi yana murmishi yace "good morning sweetheart, jira ni muje tare" daga nan ya mike suka fita daga dakin ta suka wuce nashi, ta shiga closet dinshi ta fitar mai da kayan da zai saka, ya saka...Kaii Farid yayi kyau Sosai, Ummi ta tsaya tana kallon shi tace "babe just wait a minute" ta bude wayarta ta fara daukan shi hotuna. Masha Allah, Farid akwai kyan ruda mata. Farid ya kama hanun ta suka fita daga side dinsu suka nufi side din Ammi. Ammi kuwa tayi farin cikin ganin su, bayan sun gaisa Ammi tace "daughter kizo muje dining muyi breakfast, daman har ina cewa Ihsaan ta kawo muku breakfast, sai kuwa gashi nan Kunzo" dukan su suka je dining suka yi breakfast.

A kwana a tashi, har ummi tayi wata uku da auren ta. Tuni Ummi har tayi resuming school, kasancewa yau sati, Ummi tana bangaren Ammi, Farid kuma yau sati daya dayayi tafiya akan business. Ummi kuwa tun da safe da ta tashi take jin jikin ta ba lafiya. "Ammi wlh bani da karfi, jiri nake ji" cewar Ummi, Ammi tace "toh Ummi taya zaki samu karfi kin ki cin abinci" "Wlh Ammi bazan iya cin komai ba zanyi amai" Ammi ta sauke ajiyan zuciya, chan ta mike ta wuce dakin ta, fitowa tayi rike da wayarta tana kiran Dr Aisha family doctor dinsu. Dr Aisha ta daga wayan tace "Assalamu Alaikum, Hajiya ina wuni" ammi ta amsa mata sai tace "Dr kizo gida ki duba mana mara Lafiya" daga nan suka yi sallama. Ganin Ummi ta kwanta akan kujera yasa tace "Ummi zaki iya tashi kije daki na ki kwanta, yanzu likita zata zo ta duba ki" da kyar Ummi ta mike ammi na taya ta suka shiga dakin ta, Ummi ta kwanta har ta fara bacci Sannan Ammi ta koma parlor ta zauna. Wayan Ammi ya fara ringing, ganin cewa Farid yake kira ta dauka da sauri suka gaisa, yace "Ammi ina Ummi, ina ta kiran wayarta bata dauka ba" tace "Son Ummi tana nan side dina, tun da safe bamu gane kanta ba, she's very weak kuma bata iya cin abinci sai tayi aman shi. Na kira Dr Aisha she's already on way, zata zo ta duba ta" yace "Subhannallah, ammi tana kusa ki bata wayar"? Tace "bata kusa and besides she's sleeping" yace "okay daman na kira in fada maki zuwa anjima zan shigo gari" tace "Hm Farid nasan halin ka, I hope kagama duk abinda ka keyi a chan because banaso kusamu problem kai da baban ku akan business" yace "Ammi na gama, ai munyi waya da daddy kuma yayi confirming komai" Ammi tace "toh shikenan, Allah ya kawo ka lafiya" daga nan suka yi sallama. Sa'adatu ta shigo fada wa Ammi Dr Aisha tazo, ammi tace "ki shigo da Ita mana" ba da dadewa ba sai ga Sa'adatu ta shigo da Dr Aisha, suka gaisa da ammi sai tace "Hajiya ina mara lafiyan"? Ammi tace "tana daki muje ki gan ta" Dr Aisha ta bi Ammi zuwa dakin ta. Suna shiga dakin Dr Aisha ta karasa wurin Ummi dake kwance tana kallon ta, ta taba goshin, taji jikin ta ya dau zafi sosai, mikewa Dr Aisha tayi tace "Hajiya tun yaushe ta fara rashin lafiyan"? Ammi tace "gaskiya yau ne dai na lura, da yake ba side dinan take ba" a hankali Ummi ta bude idanuwan ta tana kallon su, ganin haka yasa Dr Aisha tace "okay, Hajiya dan Allah ki dan bamu space" ammi tace "oh okay, I'll be in the parlor when you're done" daga haka ta fita daga dakin. Dr Aisha ta kalle Ummi da kyau, ta rike hanun ta a hankali tace "sannu kinji" Ummi ta gyada mata kai. "when last did you see your period" cewar Dr Aisha, Ummi tace "It's been a month and a half now" Dr Aisha tace "daman kina dadewa kafin ki gan period dinki ne" Ummi tace "A'a, this is the first time" Dr Aisha tace "good, now explain to me how you're feeling" Cike da karfin hali Ummi tace "I'm feeling dizzy, sannan idan naci abinci sai nayi amman shi" daga hakan sai tayi shiru Dr Aisha tace "okay dear kwanta abinki" Dr Aisha ta fita ta je ta samu ammi a parlor, ta zauna kusa da ammi tace "Hajiya ina mijin ta"? ammi tace "ai baya nan, yayi tafiya amman yau zai dawo inn sha Allah" Dr Aisha tace "okah Allah ya kawo shi lafiya" Ammi tace "amin, yanzu dai mai ke damun ta" Dr Aisha tana murmishi Sosai tace "Hajiya congratulations kin zama kaka, amman naso inyi mata pregnancy test kafin in fada maki, but duk symptoms din pregnancy na gani a jikin ta" Ammi ta dinga kallon Dr Aisha chan dai tace "Toh Alhamdullilah, mun gode Allah" Dr Aisha tace "bari inje mota in dauka PT test strip" daga haka ta fita, ba da dadewa ba ta dawo rike da test strip din, ta shiga dakin Ammi ta fada wa Ummi yanda zata yi amfani dashi sannan ta taimaka mata taje bandaki. Bayan wasu mintuna Ummi ta fito rike da test strip ta mika wa Dr Aisha sannan to koma ta kwanta, Dr Aisha ta fita daga dakin tana murmishi, ta kara congratulating ammi sannan ta wuce don siyyan allurai da zatayi wa Ummi. Bayan tafiyan Dr Aisha, ammi ta shiga dakin.

✏📖

Bayan magrib, Farid ne ya shiga side din Ammi ya tarar da Ita da su Rayyana suna kallon TV su Rayyana suka gaishe shi suka bar parlon ya gaida Ammi cikin ladabi, jin Ammi tayi shiru bata ce komai akan Ummi ba yasa yace "Ammi ina Ummi take" tace "ban sani ba, ka bar ta ta huta mana daga zuwan ka ko abinci baka ci ba" ya dan sosa keyan shi yace "toh Ammi, amman meye ke damun ta"? Ammi tayi mai bayanin komai, wayar Ammi ne ya fara ringing, Alhaji Nagoda ne ya kira ta tazo bangaren shi. Ammi ta mike ta fita, ganin haka yasa Farid ya fara bude dakunan dake side din amman bai gan Ummi ba, ya nufi dakin Ammi ya bude. A kwance ya gan ta tana bacci, ya sauke ajiyar zuciya ganin Ummi kwance akan gadon. Karasawa yayi, ya zauna a gefen Ummi yana kallon ta ya rike hanun ta yana murmishi, daidan lokacin Ummi ta bude idanuwan ta a hankali, duk jikin ta yayi sanyi, gashi ko tunanin abinci tayi saita ji amai. Smiling Kadan tayi tana kallon shi, a hankali yace "baby, ya jikin ki" kasa magana tayi ta gyada kanta, dukawa yayi zai yi kissing dinta, daidan lokacin Ammi ta shigo dakin da Sa'adatu wace take rike da tray tana biye da ita. Da sauri ya mike ya fita daga dakin Ammi ta bi shi da wani shegen kallo, Ummi ji tayi kaman kasa ya bude ta shiga tsaban kunya, Ammi ta karasa wurin Ummi tace "taso kici abinci" Ummi ta mike a hankali, Sa'adatu na bude flask din Ummi taji zuciyar ta na tashi, kaman zatayi kuka tace "Ammi Wlh bazan iya ci ba, amai nake ji" a hankali ammi tace "toh zaki sha fruits, a kawo maki"? Ummi ta gyada mata kai, Ammi ta kalle Sa'adatu tace "ki mayar da abincin, ki kawo mata fruits da ruwa" daga hakan Sa'adatu ta fita. Farid kuwa bai samu kwanciyan hankali ba, gashi shi kadai a side dinsu, Ummi kuwa ta samu ta sha fruits, tayi sallah sannan tayi bacci. Washe gari Ammi ta shigo cikin dakin ta gan Ummi zaune akan daduma tace "Ummi ya jikin naki"? a hankali ta mike tace "Ammi ina kwana" Ammi ta amsa mata tace "zaki iya motsa jiki"? ummi ta gyada mata kai, sai Ammi tace "toh yanzu Sa'adatu zata zo ta raka ki side dinku ki dauko wasu abubuwa da kike bukata, za ki dan zauna a side din nan for a while don in dinga duba ki, Kinji" Ummi tace "toh Ammi nagode sosai" Ammi tayi murmishi taceb"A'a ba komai daughter" daga haka ta fita daga dakin. Bayan wasu mintuna, Sa'adatu ta shigo dakin tare da sallama tace "aunty sannu, ya jiki"? Ummi tace "da sauki, Nagode" "daman Ammi tace In zo wai zan taya ki da wani abu" Ummi ta gyada mata kai tace "Ae muje side dina" daga hakan ta mike suka nufi bangaren su. Shiga parlon Ummi tayi Sa'adatu na biye da ita, Ummi tace "Sa'adatu ina zuwa inje in kawo kayan" daga nan ta hau sama ta bude dakin Farid, taji alaman yana wanka a bathroom. Fita tayi daga dakin ta shiga dakin ta, ta shiga closet dinta ta fito da wata mini akwati mai kyau sosai, ta saka Abaya guda biyu masu shegen kyau da tsada, ta saka atampa guda biyu da underwears and kayan shafe shafen ta da turarukan ta da su shower gel. Bayan ta gama zuba kayan acikin akwatin, tayi zipping dinshi ta tsayar da akwatin, kokarin dagawa tayi taji baza ta iya ba. Fita tayi daga dakin ta tsaya a corridor ta Sa'adatu "Sa'adatu dan zo ki dauka kayan ki kai chan" Sa'adatu ta hau sama da sauri ta dauka akwatin ta sauka ta fita daga bangaren su. Ummi ta koma dakin Farid ta ga haryanzu wankan yake yi. Cire Hijabin ta tayi ta ninke, ya rage daga Ita sai skimpy dress wanda bai wuce hips dinta ba mai spaghetti hand da yayi mata kyau Sosai, ga dogon gashin ta baki wul wanda tayi twisting dinshi. Kofar bandakin ta nufa, daidan zata bude kofar Shima ya bude ta ganshi yana daura da towel a waist dinshi. Yana kallon kwayan idanuwan ta itama haka, a hankali ya janyo ta jikin shi ya rungume ta sosai, itama ta kankame shi kaman Za'a kwace mata shi. Chak! Ya daga ta sama ya nufi gado ya zauna ya ajiye ta akan cinyan shi yana rike da waist dinta, Ita kuma tayi wrapping hands dinta around his neck tana kallon shi. Murya kasa kasa tace "baby I've missed you so much" yana shafa cikin ta yace "I've missed you more Wifeyyyy. Baby I hope little Farid is not disturbing you" turo baki tayi tace "bansani ba, little Farid is so hungry Wlh" ta fada kaman zata yi kuka. Dan murmishi yayi yace "let's take little Farid out for breakfast, yau banaso mu ci breakfast din gida" daga hakan ya fara kissing dinta yana kokarin cire mata hanun rigan ta ya kai bakin shi saitin kunen ta yace "I love you baby, Allah ya barmu tare" murmishi Ummi tayi tace "ameen latest daddy in town". Daga nan ya dan lallashe ta sanna suka mike, Ummi ta shiga bathroom din domin tayi wanka, Farid kuma ya shiga closet dinshi ya shirya daga hakan ya je dakin Ummi ya shiga closet dinta ya dauko mata wata Abaya pink and white mai kyau Sosai, ya dauko mata wata Chanel handbag white da takalmi Shima white, ya hada mata da inner wears ya fita daga dakin ya shiga nashi. Daidan lokacin daya shiga itama ta fito tana daure da towel taga kayan ta a hanun shi tace mai "Aww, so thoughtful of you, thanks baby" daga hakan suka shiga closet dinshi tare, ya zauna kan wata hadadden sofa yana danna wayar shi, Ita kuma tana aikin shafa kayan shafe shafen shi a jikin ta, minti minti yake satan kallon ta. Ummi ta gama yan shafe shafen ta tasss! Sannan ta saka kayan ta. Ba karamin kyau Ummi tayi ba, kayan ya karbe ta sosai. Farid na kallon ta yana hyping dinta kaman zai cinye ta Ummi cike iyayi irin na yan mata tace "you can't believe this sexy young babe standing before you is your wife ko"? yace "babe kin hadu ne over wlh" Ummi tayi murmishi tana kokarin shiga Snapchat a wayar ta, tayi musu mirror selfie masu shegen kyau. Daga hakan Farid ya dauka key din Brabus dinshi suka fita daga dakin suka sauka kasa. Ummi da Farid sun hadu ba kadan ba, gasu young couples.
Wani restaurant mai tsada sosai ya kai ta. Parking yayi suka fito daga motan suka shiga tare. Sai kallon su akeyi don sun birge mutane. Waje suka samu suka zauna wani dan matashi da ke aiki a wurin ya kawo masu menu ya tafi. Farid ya kalle ta yace "baby kiyi mana choosing abin da za muci sai kiyi mana placing order" tace toh, chan dai ta daga kanta tana kallon shi tace "then who will pay the bills"? yace "my wife of course" tace "and if I don't pay"? yace "you're a woman ai you can wash dishes" dariya tayi ta kira waiter din ta nuna mishi abincin da suke so daga nan ya wuce. Kallon ta Farid Yayi yace "I see you ordered expensive food, wife ita cash madam ce" murmishi tayi bata ce komai ba, haka Farid ya dinga tsokanar har aka kawo musu abincin su, suna ci suna hira har suka gama, suka bar restaurant

Please Login or Register in order to submit comment