Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min uban baban ki, lokacin ina yar amarya ta nace tazo ta taya ni zama tinda yar uwata ce shine ta min wannan cin fuskan" Ummi dai ta ki kula Inna ta mike ta shiga kitchen, bata dade ba ta fito da tray dauke da pilaf rice da shrimp sauce, gasheshen kaza da sausage rolls sai kunun Aya mai sanyi da bottle water. Ajiye tray din a gaban Inna tayi tace "Mu dai bamuyi tuwo ko dambu, ga wannan dai idan zaki ci" zaro ido da dafe kirji Inna tayi lokacin da ta gan shrimp sauce din tace "Wa innahu min Sulaimanu, Amina ashe kunama kuke miya dashi sabida lalacewa, ina ganin abubuwa ni Yakwalo" dariya sosai Ummi tayi harda rike ciki dan zuwa lokacin Inna har ta hada zufa tace "amman Inna ke down ce, a ina kika ji ake cin kunama, wannan seafood ne, shrimp ake kiran shi kuma duk dangin kifaye ne" tabe baki inna tayi tace "yo ni ina nasan miki wata shurim yar nan, amman tunda kince ba kunama bace ai shikenan" murmishi Ummi tayi cikin son kakan ta, daga haka ta nufi wurin TV, ta kunna ta saka a tashar dadin kowa sanin favorite channel din Inna kenan, sannan ta bar Inna ta hau sama. Bedroom dinta ta shiga ta sami Nana tana faman tura charger a wayan ta. Dariya Ummi tayi tace "sis ya akayi kuma mai ya faru da wayan"? Nana tace "Wlh bai yin charging ne, gashi Yusuf yace zai kira ni video call anjima" Ummi ta tabe baki tace "ke da wannan saurayin naki, ko Uban meye ya tsinana miki oho. Ga dai samari masu kyau da kudi uwa uba ga class, amman kin makale ma wannan dan daban, gashi ko waya ba zai iya chanza miki ba" Nana tayi murmishin yake bata amsa ta ba, Ummi ta cigaba "atoh ai ahir dinki, tunda ba ni zan zauna dashi ba, ni daman gab nake da raba ki da wannan shegen wayan naki, anjima idan Inna ta tafi sai muje mu siya sabon waya" Nana ta mike cikin jin dadi ta runguman Ummi tace "wow sis Nagode, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya ki" Ummi da ta sake baki tana kallon Nana tace "toh wai akan wayan kike min duk wannan godiyan, dan Allah ki daina" Nana tace "Wlh duk farin ciki ne" Ummi tace "bakomai Wlh, Yauwa kafin ma in manta, daman nace zanyi miki magana. Nace ke baki da niyyar yin jami'a ne, naga dai kinyi WAEC lokacin da nima nayi amman kuma ban gan kin fara school ba" Nana ta sauke ajiyar zuciya tace "ai sis bamuda kudin da zan shiga school ne ai shiyasa, nima ina da burin in gan kaina a makaranta, amman babu kudi" Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace "Kar ki damu, zan gaya ma wani lecturer dinmu ya samo miki admission a school din da nake, kafin muyi processing payments din" Nana da har hawaye ya ciko idon ta tace "sis Nagode Sosai, Allah ya baki duk abin da kike so, Allah ya kare ki daga sharrin makiyya, yanzu nima Maryam Abatcha University din zan fara"? Ummi tayi murmishi tace "ki gode ma Allah please and stop crying, what are sisters for, kuma ki daina min wannan kukan fah, yanzu tashi kiyi wanka dan Inna na tafiya zamu fita" daga hakan ta mike ta koma kasa wurin Inna a parlor ta sameta har ta gama cin abincin ta kai komai kitchen ta wanke har tana bacci a parlon. Ummi ta kashe TV, ta rage sanyin AC sanan ta kashe wutan parlon ta koma sama ta dauko bargo mai kyau mara nauyi ta lullube Inna dashi sanan ta koma sama itama ta kwanta.

Ummi na bacci taji muryar Inna a corridor, mikewa tayi ta fita daga dakin ta ci karo da Inna tana cewa "ni dai baki kyauta min ba sam, kawai kika bar ni a palo sai zuba munshari nake, da yanzu mijin ki ya shigo ya gan ni, ya ce min tsohuwar banza toh Allah zai saka min" Ummi dake ta hararan Inna tace "toh kina wannan magagin bacci naki kike so in tashe ki" Inna tace "kya ji dashi, ni dai daduma zaki bani da hijabi inyi sallah, in tarkata kaina in koma gidana" Ummi ta shigar da Inna dakin ta, sanan ta shimpida mata sallaya ta bata hijabi ta fita daga dakin ta koma nasu. Inna na idar da sallah ta sauka kasa ta tarar da Ummi zaune tana waya da Farid, tana ganin Inna suka yi sallama dashi tace "Inna ki dan jira driver yazo ya maidaki gida" Inna tace "oh toh yar nan, Allah miki albarka" Ummi ta amsa ta mike ta hau sama bata dade ba ta sako rike da paper bag a hanun ta tare da Nana. Ta mika ma Inna paper bag, din Inna ta leka ta gan lace mai tsada guda daya, sai atampa guda daya, manyan mayafi guda biyu, kwalli masu kyau guda biyu, turare guda biyu sai kuma kudi 50k a envelope. Inna ta fara kuka tana cewa "oh Allah na gode maka daka bani jika mai kirki, ai kin ma fiye min sauran jikoki na Wlh, atoh tunda basu damu dani ba ai, Allah ya miki albarka" ummi ta amsa mata. Suna zaune Ammi tayi sallama tana rike da basket din snacks da su zobo ta shigo, su ummi suka gaishe ta amsa sanan ta gaidan Inna da ladabi tace "Mama daman zan fita ne, shine nace bari inzo muyi sallama Kilan kafin in dawo kin tafi, ko kwana zakiyi" Inna tace "haba yar nan, sai kace wata tsohuwar banza sai in kwana a gidan jika, ai yanzu ma shirin wucewa nake yi" ammi tayi murmishi tace "toh mama mun gode da ziyara, ga wannan na motsa baki ne" ta ajiye basket din a gefen ta, Inna tayi mata addua'a sanan suka yi sallama tafita, ba dadewa ba driver yazo ya dauka Inna suka tafi.

✏📖

Aunty shatu ce zaune da kawar ta sajida a gaban wani tsoho tana cewa "Baba, ya' ta Nana ta riga ta koma gidan da zama ko, Ita da ummin suna shiri Sosai dan da muka yi waya tace min har waya mai tsada na zamani ta siya mata sanan ta biya mata ta fara makaranta a inda take karatu" yace "toh, yanzu kuma meye kike so"? tace "toh, baba daman yanzu inaso mijin Ita ummin ya fara son Nana har ya kai ga aure, sanan kuma Ummi kaman tana da ciki inaso cikin ya zube kuma Kar ta kara samun wani ciki sanan ta dinga samun matsala da mijin nata" yace "ya sunan mijin" "sunan shi Farid Muhammad Nagoda" yace "toh ai zai yu, kuma kudin ki dubu dari uku da hamsin" aunty shatu ta zaro ido, mutumin na ganin haka yace su tashi su fita cikin fada, Sajida ta saka baki tace "A'a baba kayi hakuri, za'a kawo maka kudin gobe" yace "toh ku tashi ku fita" duk suka mike suka fita da baya. A waje sajida take cewa "Allah ya soki da kin kwapsa" aunty shatu tace "toh ni sajida ina zan samu har 350k" sajida tace "sai ki sayar da zoben ki na gwal" shatu tace "kuma haka ne fah, duk da dai shi kadai gare ni, amman ni da na kusan zama surukar masu CBN din guda meye kuma gwal" sajida tace "ai shine" daga hakan suka tafi bakin titi neman adaidaita.

Ummi ce tsaye, ta saka Atampa super hollandais golden da yellow color sai kuma touch of navy blue, anyi mata dinkin fitted top long sleeve da kuma 6pieces skirt, ta yafa expensive veil dinta mai dan girma shima blue black, sanan ta rike jakan ta na Fendi golden color, takalmin ta ma haka, ta saka zoben ta na gold a kowane hanu, ga agogon ta Rolex na mata sanan kuma gold bracelet dinta. Ummi tayi kyau sosai. Nana kuma ta saka pink material anyi mata dinkin Abuja bubu, Itama ba laifi tayi kyau. Ummi take cewa "ni fa Wlh tafiya ta zanyi, Haba ace almost an hour kina shiri kuma Kinsan ina da lectures by 8:30 zaki sani latti" Nana tace "laaa sis gashi ai na gama yanzu, Wlh Yusuf yace zai shigo ya gan ni yau shiyasa nake so in danyi kyau" Ummi ta tabe baki tace "a inan zai zo, wai Maryam Abatcha, lalai da kyar a bar shi ya shigo yanda yake kama da dan daba" Nana ta turo baki kamar zatayi kuka, Ummi tayi banza da Ita ta fita daga dakin, Nana tabi bayan ta suka fita suka kama hanyar school.

Ummi na tsaye da Iftihal tare da Zahra suna hira, Iftihal tana tambayan Ummi "wai babes, Yaushe ne tafiyan ku din" "sai next week ai, da yake duk events din a Abuja za'ayi" Zahra tace "zaki dan yi skipping class kenan" Ummi tayi dariya tace "zan dan huta dai nasan zaku yimin attendance" suna cikin magana Ummi ta hango Nana da Yellow suna zuwa, ta zafi ido tace "waye wancan nake gani kamar yellow da Nana" suna tsaye har suka karaso wurin su, Nana ta gaisa dasu Iftihal ta kalla Ummi dake ta kallon yellow tace "sis, mun fito, ai bamu wani dade bako laaa har zan manta ga stepsister Ita, sunan ta Sabira" sanan ta kalle yellow tace "Sabira ga second cousin Ita da nake miki maganan ta dazu" Ummi ta kara zaro ido tace "bangane she's your stepsister ba" "ae sis baban mu daya, but why do you sound surprised"? Ummi zata yi magana wayar ta yafara ringing, dubawa tayi ta gan Farid ke kiran ta, ta koma gefe tayi picking call din "Assalamu Alaikum habeeby" daga bangaren Farid ya amsa "Wa'Alaikum salaam habibty" Ummi ta danyi murmishi tace "baby ya kake,ya aiki, I miss you so much" "I miss you more babe, kina school ne" tace "yeah muna school yanzu zamu koma gida, so babe yaushe zaku dawo" yace "very soon" suka danyi hiran su, suka yi sallama, Ummi ta koma wurin su Iftihal, lokacin yellow da Zahra sun wuce ya rage Iftihal da Nana. "Babes ni zan tafi, we'll talk later" Cewar Iftihal, Ummi ta amsa sanan Ita da Nana suka nufi wurin mota suka kama hanyan gida. Suna isa gida suka shiga bangaren Ammi suka gaishe ta bayan sun tambaye ta su Rayyana ta fada musu sun koma gidan su Nabila har sai bayan biki zasu dawo daga hakan su Ummi suka fita. Suna shiga ciki Ummi ta zauna akan sofa dake parlon tana cewa "Wlh yunwa nake ji" Nana tace "ba kin tsaya Iyayi dazun da na kawo miki wainan da na siya a school ba" Ummi tace "Wlh ni bazan iya cin wanan wainan ba" daga haka ta mike ta hau sama ta shiga daki, Nana kuma ta shiga kitchen ta daura Ruwan shinkafa kafin itama ta je dakin da take. Ummi na shiga dakin, ta yaye gyalen ta, ta zauna akan ottoman ta fito da wayar ta ta saka a charging sanan ta fara cire kayan ta ya rage daga Ita sai tight sai bra, ta kwashe kayan zata kaisu laundry basket dake cikin closet din, ta gan wutan closet din a kunne a ranta tace "ba na kashe wutan kafin in fita ba" karasawa tayi cikin closet din ta gan Farid yana arranging kayan shi acikin wardrobe din. Ai Ummi bata san lokacin data watsar da kayan a kasa taje ta rungume shi tana cewa "omg baby, what a surprise, yaushe ka dawo" murmishi yayi, ya dauke ta ya ajiye ta akan table din dake tsakiyan closet din ya fara kissing dinta sanda yayi mai Isar shi, muryar kasa sosai yace "baby tun dazu na dawo, I just wanted to surprise you" ya kai hanun shi kan cikin ta yace "how's this little baby doing" ya duka yayi kissing cikinta, Ummi na dariya tace "tare kuka dawo da daddy"? Yace "No, daddy ya tafi Tokyo" tace "oh Allah sarki, babe bari inyi wanka I'm so tired" yace "toh muje muyi tare" Ummi tayi rolling eyes dinta, Farid ya dauke ta suka shiga bathroom suka yi wanka, Ummi ta saka pajamas riga mai gajeren hanu da wando Pink and black color Farid Shima pajamas blue black color. Bayan sun shirya suka yi sallahn magrib sanan suka sauka kasa. Nana suka gani ta fito daga kitchen da tray din drinks da cups zata kai dining, zare ido tayi data gan Farid tace "laaa Yaya Farid sannu da zuwa, ya hanya" yace "Yauwa, ya school"? tace "Alhamdullilah" yace "good" yaje ya zauna akan sofa yana chanza channel din TV zuwa na kwallo. Ummi tace "sis ashe kin dafa abinci" Nana ta dan harare ta tace "ai idan na biye miki, sai yunwa ta kashe mu" Ummi tayi dariya tace "nifa ko kusa da kofan kitchen naje Sai in dinga jin tashin zuciya" Nana tace "toh Allah ya sauwake" ta karasa dining din ta ajiye tray din, tana kallon Ummi data bude daya daga cikin flask din ta yamutsa fuska "ya dai a zuba muku ne" Ummi tace "ni fah bazan ci rice da stew din nan ba" Nana ta sake baki tana kallon Ummi tace "kan uban chan, ashe ko zaki nemi abin da zaki ci" Ummi Kaman zatayi kuka tace "Wlh amai zanyi idan naci" "toh uban meye zaki ci" Nana ta fada a kufule "ni pepper soup din kan rago da yaji spice sosai nake so" Nana tace "Atoh, ai sai ki nemo ragon ki yanka, ki dafa ai dan bangan shi ba" daga hakan ta dauka plate ta fara zuba ma kanta. Ummi ta juya ta kalle Farid da bai masan suna yi ba taje wurin shi tace "babe please kayi min ordering pepper soup din kan rago, bazan iya cin white rice and stew ba, zanyi amai" Nana dake kan dining tana cin abinci ta harare ta, Farid ya mika mata wayar shi yace "gashi order what you want" Ummi ta amsa tace babe, kai fah, a zuba maka rice din" yace "Noo, anjima zanje in sha coffee a wurin Ammi" Ya cigaba da kallon football, Ummi kuma tayi order dinta.

Yau sati biyu kenan kenan da aunty Shatu da kawar ta sajida suka kaima boka 350k din daya bukata, sanan ya ba shatu wani kulin garin magani wai shi za'a barbada wa Ummi acikin abincin ta. A yau ne kuma shatu zata bawa Nana kulin maganin, da yake sunyi waya Nana tace zatazo ta gaishe ta da abban ta kasancewa aunty shatu ta koma gidan ta. Mai Napep ne ya dire Nana gaban karamin gidan su, ta biya shi sanan ta shiga ciki. Bayan Nana sun gaisa da yan gidan ta shiga dakin maman ta, zaune ta sameta a dan karamin parlon. Nana ta gaishe ta ladabi. "Yauwa Nana naji dadi da kika zo, daman na samu wani magani ne da Za'a dinga zuba wa Ummin, yanzu zan baki shi ki tafi dashi, sai kibi a hankali fah Kar su gan ki dashi" jikin Nana ne yayi sanyi, duk sai taji ba dadi dan Ita har ga Allah ta hakura, kuma ta dau alkawari cewa baza ta bar koma waye ne ya cutar da Ummi ba, barin yanda Ummi ta dauke ta kaman sun fito daga ciki daya. Maganar aunty Shatu ne ya dawo da Ita daga tunanin da take yi "ke! ba da ke nake ba" Nana ta sauke ajiyar zuciya tace "Umma wlh ni na hakura, sai nake ganin mu bar wanan maganan kawai, Kar Allah ya kama mu dashi wata rana" tsawa aunty shatu ta daka mata tace "dan ubanki ni kike gaya wa abin da Allah zai kama da, toh kinyi kadan yar banza, shashasha kawai. Duk ba ke nake so nayi wa alfarma ba, sai da na kashe har 350k zaki bude tsamin bakin ki kina gaya min maganan banza. Toh bilahillazi baki isa ki tsayar da komai ba, yar wahala kawai, gashi dai na baki kuma Wlh idan baki saka mata ba Allah ya isa tsakani na dake, dallah tashi ki ban waje" rai ba dadi Nana ta mike ta fita daga gidan gaba daya ta samu Napep, ta hau. Gaban gate mai napep ya dire Nana, ta sauka ta mika mai dubu daya tana jiran chanji, mai napep din ne ya hau fada yana cewa "daman kin san ba kida chanji shine baki yi magana tuntini ba" tace "kai Mallam ya kake daga min murya, ai hakkin ka na baka sai ka nemo chanji ka bani" haka dai suka dinga sa in sa, wani mota ne yazo yayi parking a bayan napep din. Sadiq yayan Nabeelah kuma cousin din Farid ne ya sauko daga motan, Sadiq yana kama da Farid, amman Farid ya fi shi haske da tsayi, amman a wurin gayu ba a bar Sadiq abaya ba, kuma yafi Farid fara'a. Karasawa yayi gurin su, ya tambaya mai napep ko lafiya, a takaice dai Farid yace mai napep din ya tafi da dubu dayan, mai Napep ya dinga mai godiya har ya bar layin. Nana dai da abin duniya ya ishe ta, barin Sadiq tayi tsaye ta shiga cikin gida, shiko Sadiq yabi bayanta. Nana na shiga cikin parlorn Ummi ta gan su Rayyana a zaune suna kallon TV. Rayyana tace "Nana wai ya kika dade ke fah muke ta jira, damun wuce tuntini" Nana ta zaro ido tace "ina zamu"? "saloon zamu, kin manta Ammi tace muje mu gyaran kan mu, gobe fah zamu tafi Abuja" Nana tace "laaa Shaf wlh na manta, toh bari in chanza kaya muje, tare da sis zamu"? Karaf Ihsaan tace "chaap, ai ina fah zamu tare, ai in gaya miki mun fi 30mins anan tana chan suna soyewa da Yaya, Wlh kuwa ina...." Bata karasa ba Chuchu ta mauje ta tace "ke wace irin mara kunya ce, maiyasa bakin ki baya haila iyee yar kaniya"? Narai narai tayi da ido kaman zatayi kuka, suna cikin draman nan ne Sadiq ya shigo ya gan su,Nana kuwa tuni ta shiga daki dan chanza kaya. Su Rayyana suka gaishe Sadiq, Ihsaan kuwa taje ta rungume shi tana cewa "welcome Yaya Sadiq" murmishin shi mai kyau yayi mata yace "Yauwa lil sis, meye aka miki kike turo baki" tace "Ba chuchu bace ta mauje min baki" Rayyana tana dana wayarta, chuchu kuwa sai hararan Ihsaan take, Nana kuwa da ta fito sai kallon su take, ido hudu Nana da Sadiq suka yi ta dauke kanta tace "ina yini" tana kallon Rayyana "toh na shirya, mu tafi ko" Ihsaan ta kalla Sadiq tace "Yaya Sadiq, ko zaka kaimu" yace "ina zaku" "saloon" yace "nima nazo mu fita da Farid ne, sai next time" Ihsaan ta marairace, chuchu ta matsa kusa da Nana, murya kasa kasa tace mata "wai Ita fah nan son Ya Sadiq take yi, shine fah take wani rangwada tana shishige mai" Nana tace "uhm". Sadiq ya fito da wayar shi yayi dialing number Farid, yana dagawa yace " bruh ka fito ina fah parlon ka tuntini, ka wani makale da yar mutane zaka mata wayyo" da sauri ya kashe wayar yana dariya. Ba da dadewa ba Farid da Ummi suka sauko, ta saka hijabi har kasa, Farid suka gaisa da Sadiq, Ummi ma ta gaishe shi ta nufi kitchen dan kawo mai drinks, taci Karo dasu Rayyana da suka fito daga kitchen, ko wanen su da zobo a hanun su. "Laaa sisters, ashe baku fita ba" Rayyana tayi dariya tace "uhm sister kenan, yanzu zamu wuce" Ummi ta kalla Nana tace "sis yaushe kika dawo, ya su aunty" Nana ta amsa mata,suka Nufi hanyar fita, ummi kuma ta shiga kitchen. Sadiq yabi Nana da kallo har ta fita daga parlon. Sai gab da magrib su Rayyana suka dawo, lokacin Ummi kadai ce a gida dan Farid da Sadiq sun fita. Sallaman su taji ta sauka ta gan su da manyan leathers. "Sannun ku fa zuwa sisters, wanan uban leathers din fah" Rayyana tace "Wlh sis kayan mu ne fah na biki muka amso" "Ah toh barka" chuchu tace "toh wai maiyasa baza ki bi mu gobe ba sis" "ai tare da yayan ku zamu tafi kuma shi ba gobe za shi ba sai jibi, but tare zaku da Nana" chuchu tace "okay, bari inje in huta" daga hakan ta fita, Ihsaan ta kala Ummi tace "aunty ina Yaya Sadiq, Kar dai ya tafi" "no, sun fita da yayan ki ne but zai dawo ai" Ihsaan tayi murmishi ta fita, Rayyana ma tabi bayanta, ya rage Ummi da Nana.

Daki suka wuce suka yi sallah kafin Ummi ta sauko ta shiga dakin Nana. Zaune ta sameta tana video call da Yusuf, Nana na ganin Ummi tayi mai sallama, tabe baki Ummi tayi tace "uhm, Inji mai ciwon hakori" dariya Nana tayi tace " kai sis, ni fah ban san meye Yusuf dina ya tare miki ba fah " karaf ummi tayi tace "shi har ya isa ya tare min wani abu, mtcheeew. Ai ni Wlh gab nake da raba ki da wannan Yusuf yake ko wa, in hada ki da Sadiq ko kuma Matawalle. Ga sunan dai kowa naji da class and money uwa uba ga son addini sanan kuma ga hankali da shegen kyau kaman larabawa, amman kika like ma wani shege chan yana gigilla miki karya, ni fah Wlh tun ranan da kika nuna min hoton shi ban yarda dashi ba, sai wani zare ido yake yi kaman wanda yayi sata, duk zufa a goshin shi sai kace yayi gudun tsere, wa yasan ma ko yana naso, yayi ta hada gumi yana tashi. Gashi nan dai kaman wani shugaban yan daba" narai narai Nana tayi da ido tana turo baki tace "sis Yusuf dina kike zagi haka" mikewa ummi tayi tana tsaki ta Nufi hanyar fita tace "ga Mandi rice da kuma snacks a dining nayi, sai ki fito kici" daga haka ta fita. Nana ta shiga duniyan tunani, Ita fah har ga Allah tasan duk abin da Ummi ta fada ba karya bane, amman kuma Baban ta ne ya lika mata shi sabida Yusuf yana dan kyautatawa baban da kudi irin 2k zuwa 5k. Kasancewa baban mai kwadayi ne, kuma bai damu da yaran shi ba, ya tilasta Nana yace dole sai ta aure Yusuf, tun bata kula shi har ta fara kula shi.

✏📖

10:00pm daidai Farid da Sadiq suka shigo cikin gida lokacin Ummi har ta hau sama tayi bacci, Nana kuma tana parlor tana kallon 'A tribe called Judah' a Netflix wanda akayi connecting da TV. Sallaman sune ya sa ta dago kan ta, ta kalle Farid tace "Yaya Farid sannu da zuwa" yace "Yauwa sannu" suka zauna, ta kalle Sadiq da yake ta kallon ta, Shima ta gaishe shi ya amsa yana mata murmishi. Mikewa tayi zata shiga daki Farid yace mata "where's your sister"? Tace "She's upstairs and she's asleep" yace "okay, pls can I get a cup of coffee" tace "okay" sai ta kalle Sadiq tace "kai ma zaka sha in hada da kai"? Yace " yes, please thank you" daga hakan Nana ta nufi kitchen, Sadiq yabi ta da kallo. Farid ya lura da kallon da Sadiq yake mata yana dariya yace "bruh lafiya kuwa"? Shafa kanshi yayi yace " Wlh chic din nan ta shiga raina" dariya Sosai Farid yayi yace "kai dai da son mata, ni dai bazan bari ka yaudare wannan ba" Sadiq yace "Wlh ba yaudaran ta zanyi ba, Wlh sonta nake yi, ka taimake ni mana" Farid yace "okay bruh, zan fada ma babe tayi mata magana, kasan she's her second cousin" Sadiq yace "thanks bruh, I'll be waiting" suka chanza hirar su. Nana bata dade ba, ta fito rike da tray din cups of coffee a ciki, dire tray din tayi akan carpet ta mika musu coffee dinsu, duk suka gode mata daga hakan ta shiga daki ta barsu a parlon.

Washe gari da sassafe su Rayyana dasu Ammi suka shirya tafiya zuwa Abuja. Ummi da Farid ne suka kai su airport dayake flight dinsu na 9:00am ne,

Please Login or Register in order to submit comment