Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanan suka nufi hanyar komawa gida. A cikin mota Farid ya sanar da Ummi yanda suka yi da Sadiq jiya akan Nana, Ummi kuwa bakin ta har kunne tsaban jin dadi.

Ummi na zaune a dakin ta tana waya da mum dinta, daga dayan bangaren mummy take cewa "idan na gan nagama abin da nake yi then I'll attend the wedding, munyi magana da Haj Saratu (Ammi) tace suna Abuja already" "Ae mummy yau suka tafi, mu kuma gobe zamu tafi" mummy tace "toh Allah ya tsare, ki dinga addua'n tsaro daga duk wani abu Mara kyau, sanan ki dage da yima dangin mijin ki biyyaya, be smart and prayerful okay"? " toh mummy Nagode Sosai, Allah ya kara girma" bayan sunyi sallama, Ummi taje dakin ta, ta fito da wani foreign medium sized akwati pink and white color mai kyau sosai ta saka Abaya da English gown guda biyu aciki, Lace din da zata saka dinner sai ankon atampa na kamu sai kuma lafaya na Arabian night, sanan ta zuba turarukan ta kala uku: Qaed Al Fursan, Hayatti Rose scent sai kuma velvet oud, bayan ta saka su sai ta sa takalman ta half shoe masu tsini duk na companyn fendi kowane da jakan shi, sai kuma flat shoe guda biyu da bathroom slipper mai kyau, sanan ta zuba gold jewelries dinta kala hudu sai brush & toothpaste, shower gel da kuma bathing sponge tana gama hada akwatin tayi zipping dinshi ta bar shi acikin closet din. Dakin su ta shiga gan Farid yana waya da Ammi yana tambayan ta ya hanya, ta amsa mai sanan ta tambaye shi Ummi ya mika mata wayan "Assalamu Alaikum Ammi ya hanya" "Wa'a Alaikum salaam daughter mun isa lafiya" "Masha Allah Ammi ya kuka samu yan Abuja"? Ammi tace " yan Abuja suna lafiya, duk suna jiran zuwan ku, I hope kin ci abinci"? Tace "ae ammi naci" "toh daughter ki dinga kula sanan Kar kiyi wani aikin wahala Kinji" tace "toh ammi Nagode, ki gaida su Rayyana" ammi tace "zasuji suna chan wurin Nabeelah" "toh ammi sai anjima" suka yi sallama ummi ta katse wayar. Farid yace "uhm, daughter din Ammi, I'm jealous irin wanan kula haka" dariya ummi tayi tace "muje in hada maka kayan ka, kagan har na hada nawa yana chan daki" mikewa yayi ya rungume ta ta baya suka shiga closet din.

Yan Abuja kuwa ana ta shirye shiryen biki da za'ayi the next day. A yau ne kuma su Ummi da Sadiq suka isa Abuja, a gidan Baban Nabeelah kowa yake sauka, su ma chan suka je. Bayan sun gaisa da kowa, sauran dangi da basu samu zuwa bikin Ummi ba duk sun gan ta kuma suna son ta. Ummi na tsaye gaban mirror a wani babban daki mai kyau Sosai, komai na cikin dakin white and golden. Knocking akayi da sallama, Ammi da Ihsaan suka shigo, Ihsaan tana rike da tray din abinci da drinks. Ajiyewa tayi bayan tayi ma Ummi sannu sanan ta fita ta bar Ammi. "Daughter, ga chicken pepper soup da nan bread kici" murmishi Ummi tayi ta sunkuyar da kanta tayi mata godiya sosai, Ammi ta bata rai tace "daughter na lura har yanzu baki sake jiki dani ba" matsawa kusa da Ita tayi taja ta jikin ta sanan ta cigaba da cewa "banason kina min kallon surukar ki, I want you to take me as uwar data haife ki, duk abin dake damun ki ki fada min, ki zama free dani kinji daughter" rungume ta Ummi tayi Sosai, Ammi taji dadin hakan da tayi, a hankali ta sake ammi,"Oya zauna kici abinci, sanan akwai mai lalle tana nan tare da kawar Nabeelah suka zo daga Sudan, har tayi masu Nabeelah da su Nana, yanzu ke kika rage" Zama Ammi tayi Ummi ta zuba abinci sanan ta zuba ma Ammi, Sosai Ummi tasha pepper soup din, sunyi suna hira da Ammi abin birgewa.

Suma gamawa suka sauka kasa. Zaro ido ummi tayi tana kallon Inna dake yaga cinyar kaza tana ci, Ammi ta matso kusa da Ita tace "muje ki gaida Inna" da mamaki Ummi tace "Ammi Yaushe Inna tazo" "tun ranan da muka zo" daga hakan suka karasa parlon Ummi taje wurin Inna ta gaishe ta "Inna wai meya kawo ki nan" sake baki Inna tayi tace "Allah ka raba mu da mugun ji, Amina kike ko Aminu ina ruwanki da abin daya kawo ni nan. Dama chan nasan zaki min bakin cikin zuwa habuja shiyasa na kama bakina ban ce miki zan bi ku ba kuma ai ba laifi bane idan nazo bikin jika ta" Ummi ta kwashe da dariya tace "yaushe Nabeelah ta zama jikar ki" "ai toh da na kowa ne yar nan" mutanan dake parlon dariya suke suna kallon Inna da jikar ta. Nana dasu Rayyana ne suka shigo parlon, suka nufi kofar kitchen,Inna tabi Nana da wani shegen kallo kafin tayi kasa da murya tace ma Ummi "meye wancan figaggiyar takeyi anan kuma, So kike mijin ki ya miki kishiya da Ita, kamata yayi tun yanzu ki tarkata ta ki maida Ita Kano" Ummi tace "ae ai ku biyu zan tarkata in maida Kanon" daga haka ta mike taje garden inda za'ayi mata lalle, tabe baki Inna tayi ta cigaba da cin Kazan ta.

Karfe 9:48pm, Farid yana zaune da Ammi a wani karamin parlor mai kyau suna magana. "Okay so kai da Sadiq ne zakuyi booking hotel" yace "ae Ammi munyi booking already tare dasu Sultan da Jabir" (sauran cousins dinsu) tace "okay wane hotel din" "transcorp Hilton ne ammi" "oh okay ashe ma ba nisa, nan nan ne" yayi murmishi, ammi tace "toh dare nayi, kuzo ku tafi" sallama yayi mata ya fita daga parlon. Wani corridor yabi da zai kai shi dakin da Ummi take, tsaye ya gan ta da hijabi, tana jera kayan kwalliyan ta akan dressing mirror. Murmishi tayi mai ya maida mata ya karasa inda take ya rungume ta yana shakar kamshin dake tashi a jikin ta, "what's under this"? Ya fada murya kasa kasa yana kokarin daga hijabin. Inna na zaune a parlor tana kallon tashan dadin kowa, mutane daidai ku ne a parlon, Ihsaan ce ta fito daga dakin da suke tare da Nabeelah zata wuce kitchen Inna ta kira ta " yar nan zo ki kai ni dakin da Ummi take" sai tayi kasa da murya tace "kinsan gidan biki ba'a rasa mayu, ai kinga ba zai yu ina kallon TB (TV) ba jika ta tazama abin kallon mayu, kar su sama cikin ta ido ko kuwa, barin ma da naga tun karfe shida da rabi da ta je daki bayan angama mata lalle bata fito ba" murmishi Ihsaan tayi ta karba jibgegen jakan Inna (acewar Inna, wai baza ta bar jakan ta a daki barayin gidan biki su sace mata ba) hanyar dakin suka nufa, Ihsaan na gaba sosai Inna na bayanta. Daidan kofan Ihsaan ta tsaya, ganin cewa a bude yake kadan, bada tunanin komai ba ta tura kofan, da sauri ta koma baya tana dafe kirji, Inna ce ta karaso tana cewa "Meye kike dafa kirji kaman mai ciwon zuciya" bata jira amsar ta ba, ta tura kofan ta shiga dakin, ido hudu tayi da Farid da Ummi da suka shiga duniyan Soyyaya, ajiye ta yayi akan babban dressing mirror din tayi wrapping legs dinta around his waist sai zabga kiss suke yi. Hijabin Ummi na hango yayi yamma😹 kaman daga sama suka ji muryar Inna tana cewa "yau ni Yakwalo naga jaraba a wurin yaran Zamani, yanzu Faridu so kake ka danka mata wani cikin akan wanda take dashi, ke kuma jarababbiya kika biye mai ashe laulayi bai ishe ki ba" ai tini Farid ya sake Ummi, Ita ma ta sauka daga kan dressing mirror suka tsaya kaman wanda suka ma sarki karya. Inna ta cigaba da cewa "inace uwar ka tace a otal (hotel) zaka kwana, toh jarabba kenan ya tsayar da kai ko meye" Ummi ko cike take da jin haushi da takaicin Inna sai hararan ta takeyi, Ihsaan kuwa tana labe bakin kofa tana kallo (nace su Ihsaan radio mai jini, an samu rahotu). Farid ya sosa keyan shi yana murmishi, yama rasa mai zaiyi duk kunya ya lullube shi cewa yayi "Inna sai gobe ni zan tafi" bai jira amsar taba ya juya zai fita, karo yaci da Ihsaan data juya da sauri ta nufi dakin su, Farid ya bita da wani shegen kallo, ya fita daga gidan gaba daya. Ummi kuwa tabe baki tayi ta shiga bayi Inna ta bita da harara tana cewa "wuhuhu an kusan yin abin kunya a gidan biki" daga haka ta fita daga dakin.

Su Nabeelah suna hira a daki suka gan Ihsaan ta dire a daki kaman an jefo ta tana dafe kirji. Nana tace "Lafiya haka, daga kije ki dauko ruwa shine kika dade haka" Ihsaan tace "ina lafiya kuwa" sanan ta kwashe komai ta fada musu, dariya duka suka yi amma banda Chuchu "ke komai kika gani sai kin fada, ai Allah yasa Yaya Farid ya ganki ya koya miki hankali kila bakin zai dinga shiru, da wani shegen bakin ta kaman an shafa ma bunsuru Jan baki mtcheeew" Ihsaan ta harare ta tace "ta Allah ba taki ba" daga haka taje ta kwanta.

WAI INA AUNTY SHATU, NAJI TA SHIRU

✏📖

Aunty shatu na zaune akan gado tare da Sajida tana cewa "Wlh tun ranan da Nana tazo bata kara dawowa ba kuma bata kira na, idan na kirata lamban ma baya shiga" Sajida ta sauke ajiyar zuciya tace "kaman fah da gaske take data ce abar zancen nan, gashi kuma baki san gidan ba bale ki san ya ake ciki" "Wlh Sajida bansan gidan ba, shakaran jiya dana je ganin Hadiza bata ce komai akan ummi ba" Sajida tace "toh da kyar idan Nana bata yar da maganin nan ba" "toh yanzu mai Zanyi" Sajida tace "komawa zamuyi wurin tsohon chan, Kice mai yayi miki aiki, ya Zubar da cikin Ummi, bayan wannan sai a san yanda za'ayi da lamarin Nana" aunty shatu ta gamsu da maganar Sajida daga haka ta mike suka fita gurin bokan.

Bangaren su Ummi kuwa, yau ne ranan kamu. Ummi ce zaune ana daura mata dankwali bayan an gama mata simple makeup mai kyau Sosai, ta saka atampa mai tsada sosai white mai touch of red anyi mata dinkin fitted skirt da 3 quarter gown na A shape, ta saka takalmin Hermes red color sanan ga gold jewelries dinta simple masu kyau, bayan an gama daura mata dankwali ta yafa Chantilly veil dinta Shima red color, ta dauka wayar ta ta nufi Kofa makeup artist din tabi bayan ta sanan ta sa key ta rufe dakin (acewar Inna wai ta dinga rufe kofa, Kar barayin gidan biki su sace mata kaya). Sauka tayi ta nufi babban parlon, wurin cike yake da mata daga yara har tsofaffi gaishe su tayi ta nufi kitchen kowa kallon ta yana yabon kyan da tayi. Ammi dasu Rayyana tare da wasu masu aiki ne acikin kitchen din, jin an bude kofan kitchen din duk suka juyo su gan waye ne "wow, Masha Allah daughter, you're so beautiful" cewar Ammi, murmishi Ummi tayi su Rayyana ma sai yabon kyan datayi suke "kai sis irin wanan kyau haka, Wlh idan Yaya ya gan ki da kyar zai yi bacci yau" Rayyana ta fada cike da tsokana tana dariya, Ummi tace "ke ko, ai zan gaya mai abin da kika fada" "laaa sis ki rufa min asiri" tini su Ammi da sauran yan matan suka fita daga kitchen din ya rage su Ummi da masu aiki, suma fita suka yi daga kitchen din suka Nufi compound inda akayi Jere, mutane dayawa ne a compound din kowa na harkan shi, sai raba abincin gargajiya akeyi kala kala, ga amarya Nabeelah taci kwalliya tayi kyau Sosai anata daukan hotuna. Nana kuwa dasu Chuchu suna chan gefe sai zuba rawan kalangu suke yi ana musu liki. Ummi da sauran kawayen amarya sai hotuna suke yi, ana cikin haka ne wayan Ummi ya fara ringing ganin Farid ke kira yasa ta nemo wurin da ba hayaniya sanan ta dauka "Assalamu Alaikum baby" yace "Wa'alaikum Salam baby's baby and baby's mummy, duk ke kadai" murmishi Ummi tayi tace "I miss you so much" "I miss you more my love, anjima zamu zo nida Sadiq" "okay baby Allah ya kaimu" suka cigaba da hiran su sanan suka yi sallama. Lokacin magrib jama'a suka fara tafiya, lokacin isha kowa ya watse ya rage yan gidan kawai. Su Rayyana da Zeenat da Zulaikha (cousins dinsu) ne a dakin da Ummi take, sai hiran su suke yi. Nabeelah,Nana da chuchu suna kasan carpet suna cin samosa, Rayyana, Ihsaan da Zeenat suna faman goge makeup dinsu, Ummi da Zulaikha kuma suna kan gado suna kallon 'Keeping up with the Kardashians' a iPad din Ummi. Wayar Ummi dake charging a gefen Ihsaan ne ya fara ringing lekawa Ihsaan tayi, ganin anyi saving number da 'Abyaad💋' ta cire wayan daga charging tana mika wa Ummi tana cewa "sis, Abyaad na kira fah" tana murmishi kasa kasa, Chuchu kuwa hararan ta tayi. Ummi na daga kiran Farid ya sanar mata suna waje, bayan ya katse kiran ta mike ta saka hijabi mai yadin mecedes purple color sanan ta saka wasu takalmin minisou shima light purple mai shegen taushi ta dauka wayan ta sanan ta kalli Nana tace "Heyysss sis zo ki raka ni" turo baki Nana tayi tace "ooo nifa na gaji gasu chuchu nan su raka ki mana" "ke malama banson wulakanci, minti nawa ne ki tashi ki zumbula hijabi mu wuce" mikewa Nana tayi tana kunkuni ta yafa jersey scarf din Rayyana dake kan gado suka fita daga dakin. Ummi.ta kalle Nana tace "saura kuma kije kina mai hade haden ran nan naki, zo muje dakin da kuke ki fesa turare" suka Nufi dakin, ummi ta fesa mata turaruka kala kala "wai sis ba raka ki kawai zanyi ba sanan kuma waye kike magana wai" Ummi bata kula ta ba, ta cigaba da gyara mata zaman gyalen ta sanan ta kalli takalmin kafan ta "ba dai da bathroom slippers zaki raka ni ba" daga haka ta nufi wurin shoe rack dinsu ta zaba wani flat shoe white color na Hermes ba tare da tambaya kona waye ba, bayan ta shirya Nana suka nufi compound din gidan. A cikin wani karamin hut dake cikin garden din gidan Ummi ta hango su, Nana dai taga Farid amman bata gane wake zaune a gefen shi ba Sabida wurin akwai dan duhu. Karasawa suka yi, Ummi ta gaisa da Sadiq, Nana ma ta gaishe su. Ummi ta ce ma Farid "babe zo muje kaci abinci" Sadiq ne ya kalle su yace "au nice baza'a min tayin abinci ba ko" Ummi tace "Nana zata kawo maka ai" daga kai Nana tayi tana kallon ta, Ummi kuwa hararan ta tayi taja mijin ta suka yi gaba. Fita suka yi daga compound din suka nufa mota "baby ina zamu" cewar Ummi, bude mata kofan motan yayi ta shiga sanan ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace "baby I'm pressed" rufe kofan yayi ya zagaya ya shiga mota yana kallon ta ya kashe mata ido itama ta mayar mai. Faxx supermarket suka biya tukunan dan Ummi tace tana son chocolates daga wurin kuma suka nufi Transcorp Hilton hotel. Room 119 suka shiga, dakin da Farid yake lodging kenan, daki ne mai masifan kyau komai tsaf ga kamshin turaren Farid dake tashi a dakin. Cire hijabin tayi folding dinshi, ya rage daga Ita sai wani dark blue body con da kuma ash hula, jikin ta sai kamshin bakhoor take. Zama tayi akan ottoman tana hamma, Farid kuwa kallon ta yake kaman zai cinye ta, yana kallon cikin ta da bai fara fitowa ba sosai kasancewa cikin Ummi 3 months ne yanzu. "Stop staring at me like that" inji Ummi, murmishi Farid yayi ya cire kayan jikin shi, ya kai su closet sanan ya karasa wurin gadon ya hau ya kashe musu wuta. Janyo Ummi jikin shi yayi yana shakan kamshin gashin ta. Kissing dinta ya fara yi a hankali sanan ya cire mata rigan ta sukayi cuddling juna, a haka bacci ya dauke su.

Bangaren Nana da Sadiq kuwa, bayan su Ummi sun tafi, Sadiq ya kalle Nana da kanta ke kasa yace "come on princess kizo ki zauna" Nana ta daga kai ta da kalle shi tace "no, never mind bari na kawo maka abinci" daga hakan ta nufi kofan baya da zai kai ta kitchen. Tana shiga kitchen din taci karo da Inna dake damaNanaa "Ina wuni Inna" nana ta gaishe ta "da ban wuni ba zaki gan ni anan ne Iyye" daga nan ta tabe baki, Nana ta nufi wurin warmers din da akwai abinci, ta dauko plates sanan ta fara dishing abincin, Inna ta sake baki tana kallon ta, chan tace "yar nan kiji tsoron Allah. Gidan ku dai na san ba kya ci haka, ba dazu dazu na ganki kina faman cika cikin ki ba, so kike ki karar musu da abinci wato an samu bati ko. Toh ko ni nan da jika ta take aure a dangin su, ni na kawo fura ta tun daga Kano, nono ne dai ban samu na kawo ba nace sai nazo nan. Toh dana zo na ba wancen yarinyar mai aikinsu Naja take kowa na bata dari biyu Ita nace ta siyo min nono. Kinga ko ba kudin Uban kowa bane" murmishi Nana tayi sanan tace "Inna ba abinci na bane daman, na dan uwan su Yaya Farid ne" Inna ta zaro ido tace "dan uwan su kika ce, shine kika tsaya kallo na baki kai mai tuntini ba, toh yi maza ki hada masa ki kai" Nana ta fara hada abincin sanan ta fita daga kitchen din, Inna kuma ta cigaba da dama furan. Ihsaan ce zaune kusa da Sadiq "Yaya ashe kazo shine kaki kira na ko" murmishi yayi yaja mata kumatu yace "ba gashi kin gan ni ba" Nana ce ta karaso wurin ta ajiye tray din akan table sanan ta kalle Sadiq tace "Bismillah, ni zan koma ciki" "thanks but ba kiyi serving dina ba" ya fada a dan shagwabe, karaf Ihsaan tace "ai ko ni zan yi serving dinka Yaya, Nana ki wuce kawai ki huta" Nana tayi murmishi tace "Noo, bari in cika lada na kawai" Ihsaan ta tabe baki. Nana ta gama serving Sadiq sanan ta koma cikin gida. Tana shigan parlor, Inna ta gani a zaune tana shan furan ta tana kallon dadin kowa. "Sannu Inna" cewar Nana "ke banason munafurci, atoh banda munafurci kin saba gaishe ni ne Iyye. Toh idan ma furar ke shige maki ido, toh ki cire tun wuri don billahilazi ba wace zan ba fura ta, koda kuwa Ummin ce da take jikata balantana ke da ban hada komai dake ba, babu dangin iya balle na uba". Ihsaan ce ta shigo ta same su, Inna na ganin ta tayi shiru ta washe baki chan tace "yar nan, ni kam ina Ummi, ni fah tunda ta shige ciki ban gan ta ba" "ai Wlh Inna dazu Yaya ya kira ta, taje ta same shi, haryanzu dai bata dawo ba" Inna ta sake baki tace "au toh haka abin ya zama, toh Allah dai ya kyauta" murmishi Ihsaan tayi ta wuce dakin su, Nana ma ta bita a baya bayan Inna ta gama bambamin ta.

9:20pm Ummi ta tashi daga bacci jin ana ja shafa mata gashin ta. A hankali ta mike tana kallon Farid tace "we slept off, what's the time"? Wayar shi yayi tapping ya nuna mata time. Zaro ido tayi tace "Na shiga uku, maiyasa ka barni nayi bacci haka, now it's late. Meye zan fada masu Ammi"? Murmishi yayi yace "sai kice you were together with your husband" hararan shi tayi ta mike tana cewa "ka maida ni plsss". Shiryawa suka yi ya maida ta gida, har bakin kofar parlor ya raka, yayi pecking dinta sanan ya juya ya nufi gate. Ummi ta bude kofar tana leka ciki, ta gan wutan parlon a kashe sanan ko ina shiru alaman kowa ya kwanta. Shiga tayi bayan ta cire takalman ta, ta rike a hannu sanan ta fara tiptoeing sabida kar aji ta. Ta kai tsakiyar parlon kenan aka kunna wutan, juyawa tayi a firgice tana kallon Nana dake kallon ta itama. Murya kasa Sosai Ummi tace "Wlh kin bani tsoro" dariya Nana tayi, ta mata alama suje sama, ta kashe wutan. Suna shigan daki Nana tace "daga kuje ki bashi abinci yaci shine kuka fita kika dade ko sis" ta karasa maganar tana turo baki, Ummi tace "ai nima abincin ce" ta kashe mata ido ta fara kokarin cire hijabi.... Nana kuwa ta sake baki tana kallon Ummi, "Heyysss why are you staring at me like that"? Cewar Ummi, Nana tace "ah ah sis ai kin fi karfi na" dariya suka yi, Ummi ta tambaye ta ya suka kare da Sadiq, Nana tace mata ta bashi abincin daga nan ta koma cikin gida. Sake baki Ummi tayi tana kallon ta kafin tace "amman Wlh ke dai sai a slow, yanzu barin shi kika yi. He came because of you ne fah" Nana ta turo baki tace "Na fah ce miki suna tare da Ihsaan" Ummi ta harare ta, tace "And so what idan suna tare, is she not his cousin, amman Wlh you can spoil show for Africa" Nana ta kara turo baki tace "Ni fah sis ba kya so ki fahimce ni ne kawai. Kuma according to Chuchu, tace Ihsaan tana son Sadiq din and besides ba son shi nake yi ba, ni nafi son Yusuf dina" Ummi taja tsaki tace "waye kuma Yusuf, muna maganar Sadiq taya zaki kawo mana wani Dan daba cikin zance" Nana bata kula ta ba, ta kwanta akan gado tace "ni dai zan taya ki kwana yau" mikewa Ummi tayi ta tace "kya ji dashi" daga haka ta wuce shirya kwanciya, sanan ta kashe wuta suka yi addu'a suka tofa, suka kwanta.

Washegari bayan sun idar da sallahn asuba, Ummi tayi wanka ta shirya cikin turquoise blue color material gown, tayi kyau sosai, daga haka Ita da Nana suka fita daga dakin. Dakin da Inna take suka shiga dan gaishe ta, zaune suka same ta akan darduma tana ta faman gyangyadi ga charbi a hannun ta. "Inna ina kwana" Ummi ta gaishe ta, a firgice Inna ta bude ido, tace "amman ke kam Aminu ya haifa jaraba" Ummi ta tabe baki, Inna ta cigaba da cewa "kina fah ganin cewa ina addu'a, kawai ki shigo min daki gatsau babu sallama ki katse min addu'a" Ummi ta kalle Nana dake ta murmishi kasa kasa tace "Ina har sau uku mukayi sallama muka ji shiru, da muka shigo kuma gyangyadi muka ga kike yi" Inna ta fara matsar kwalla tana cewa "Wlh Aminu ya haifa jaraba, yanzu Amina bakya tsoron Allah zaki kalle ni Kice ina karya, taya zaki gan ni ina lazimi kice gyangyadi nake" Ummi da ta sake baki tana kallon Inna tace "Wlh bazan bi taki ba" daga haka ta mike ta fita daga dakin Nana na biye da Ita. Daga wurin Inna, dakin da Ammi take suka wuce don gaishe ta. Ammi na zaune kan gado tare da Aunty Turai. Sallama suka yi kafin su shiga dakin, suka gaishe su cikin ladabi Ammi ta amsa musu da fara'a itama aunty Turai haka. Daga dakin suka sauka kasa dan taya yan matan gidan hada breakfast. Bangaren aunty Shatu kuwa, bayan Ita da Sajida suka isa wurin bokan, ya ba aunty Shatu wani garin magani yace "wanan garin da kike gani nan mai karfi ne Sosai. Zaki kona shi acikin kasko, idan ya fara hayaki zaki kira sunan yarinyar da ake aikin a kanta sau uku, sai ki fada abin da kike so ya faru da ita, daga nan aikin zai isa wurin ta" daga haka suka gode mai suka fita daga zauren. Tana isa gida kuwa tayi yanda tsohon ya fada mata. Bayan

Please Login or Register in order to submit comment