Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ga kiran Iftihal ya shigo wayan Ummi "Hello babes kin shirya n " Ummi tace "ana yimin makeup ne yanzu, an kusan gamawa" "okay toh, gani nan bada dadewa ba zan shigo layin ku, Zahra ma tace yanzu ta fito daga gida" Ummi tace "toh sai Kun zo" daga haka ta katse wayar ta. An gama yiwa Ummi makeup dinta, very light makeup akayi mata but tayi kyau sosai, sai manyan idanuwanta da small lips dinta suka fito. Ummi ta nufe wurin wardrobe dinta ta fito da gown din event din wani off white, Kaiiiii kayan ya hadu sosai gashi kayan ya kamata chass, ta saka wata black half shoe mai shegen tsini da tsada, ta rike purse dinta Shima black wanda tare yake da takalmin. Makeup artist din ta daura wa ummi dankwalin ta kuma yayi kyau. Ummi ta hadu Sosai. Bayan ta gama pesa turarukan ta masu tsada ta sauka kasa bayan ta sallame makeup artist din. Ummi ta tarar da Nana wace take ta bin ta da kallo tun da take saukowa. "Toh Ummi ina zuwa haka kamar wata Amarya" Ummi ta danyi murmishi tace "muna da event a school yau ne, ina aunty" Nana tace "au, toh Allah ya tsare, umma ta fita ai" ummi tace "oh okay, bari in jira friends dina" daga nan ta zauna a parlon, Ita kuwa Nana sai kallon Ummi take kamar mayya. Suna zaune suka ji anyi sallama, Iftihal da Zahrah suka shigo tare, suma sunyi kyau, ko wace outfit dinta ya hadu, haka Nana ta dinga kallon su har suka fita daga parlon bayan sunyi mata sallama. "toh yanzu ya za'ayi, kowa ya tafi da motarsa ne ko kuma mu tafi tare a mota daya, idan yaso in mun dawo kowa ya dauke motarsa" Inji ummi, sai su Zahra suka amince Wai su tafi a mota daya. Ummi ta nufe wurin Zakariya da already yana jiran su, ta mika mai makulin wata baban mota hadadiya tace "da wanan zamu je yau" yace "okay ma'am" daga hakan, kowa ya shiga mota suka fita. Tun suna cikin mota Farid ya kira ta wai yana waje yana jiran ta, ta sanar mai ta shigo already. Dukan suka sauka lokaci daya daga motan, date dinsu na jiran su. Kowace taje ta samu date dinta, Farid na ganin Ummi, yayi saki dan murmishi ya fara walking towards her. "Wowww" ya fada yana zare Idanu, sai ya kara cewa "favorite kinyi kyau Sosai, kamar wata angel" hararan shi tayi tana murmishi tace "thank you fav ,kaima kayi kyau and I like your tuxedo" murmishi yayi yace "thanks, can we go in now" ya fada yana mika mata hannu suka shiga, sai baza kamshi suke yi. Zo ku gan yanda jama'a ke kallon Ummi da friends dinta with their dates, wasu sun saki baki suna kallo, wasu kuma suna ta hyping dinsu, wasu kuma suna tayi musu video. Wlh ko kai makiyyin su Ummi ne, sai sun burge ka Wlh. Kujerun da Farid yayi reserving ma dukan su, suka je suka zauna. Event kam yayi kyau, around 7 suka koma gida, daga nan su Iftihal suka wuce.

Ummi ce zaune a parlor tare da aunty shatu da Nana. Sallama akayi duk suka kalle Kofan, Inna ce ta shigo tana kalle kalle. Ummi ta mike da sauri da nufin runguman ta, Inna ta daga mata hanu tace "ke banson shiririta, inda kinyi kewata da gaske ai da zaki dinga zuwa ko" Ummi ta turo baki tace" Inna fah makaranta nake Kema kinsan ba sauki, Inna kawo jakan ki" Inna ta tsuke fuska ta danka mata jakan ta, tana kallon su aunty Shatu wanda suke mata kallon banza. Inna ta karasa cikin parlor Ummi na biye da Ita ta zauna tace "su kuma waye wa'enan gajiyayun babu sannu balle ya hanya" Ummi ta zaro ido tace "Inna yar uwar mummy ce fah da yarinyar ta" Inna tace "au toh taya zan sani, tunda sun tsaya kallon mutane kaman ba yan halak ba" Ummi ta kalle su aunty shatu tace "aunty, Nana kun gane inna kuwa, mahaifyar daddy" suka gaida Inna sama sama, Inna ko kula su ma batayi ba tace "ke ina maman ki" Ummi tace "ta fita zuwa gidan rasuwa" Inna tace "au toh shikenan" Ummi tayi shiru chan tace "Inna bari a kawo maki abinci" daga nan ta mike ta shiga kitchen. Inna ta ci abinci tayi nak har ta fara gyangyadi, mummy ce ta shigo cikin parlon da sallama ta nufi wurin Inna da sauri ta gaishe ta da ladabi Inna tace "tashi ki zauna yar albarka" chan Inna tace "na shigo na hadu da wasu rudadu suna ma mutane kallon uku kwabo, amman Ummi tace wai yar uwarki ce tare da yar ta" mummy tayi murmishi tace "eh Inna, Ita yar kanwan mamanmu ce Inna" tace "au toh, ni dai yanzu Yaushe Aminun zai dawo daga legas din ne, ace mutum ya kai wata biyar bai dawo ya duba iyalin shi ba, ai hakan bai dace ba Hadiza" mummy tace "Inna ai muna waya, Kema kinsan yanayin aikin shi, amman yace ba da dadewa zai dawo" daga hakan suka cigaba da wasu hirar su har magrib. Mikewa mummy tayi tace "Inna zo muje in kai ki daki" Inna ta tsuke fuska tace "sai kace wata tsohuwar banza, in ba ke ba ina ni ina kwana a gidan yara" mummy tayi dariya Sosai tace "toh, Inna ai dare yayi, bai kamata ki tasa kanki a hanya ki tafi ba, sannan ma meye aciki idan kin kwana a nan din ma" da kyar Inna ta yarda ta kwana.

✏📖

A kwana a tashi, Ummi da Farid sun fara Soyyaya har an kai ga maganan aure tsakanin su har. Farid tuni ya gama school dinshi harda service, kuma ya samu aiki a CBN sanan kuma yana running family business dinsu. Kasancewa lokacin da ya hadu da Ummi, shi final year chattered accounting student ne while ummi kuma tana 200lvl. Inna tazo gidansu Ummi ranan, ta shigo babban parlor kenan tana ta kallon bakon da ke zaune a kan kujera. Inna ta samu wuri ta zauna. Ganin Inna ya sa ya gaishe ta cikin ladabi, Inna tace "toh sannu, amman ka tabata nan gidan Kazo ko dai ka bata ne" Farid da ke kallon Inna cike da mamaki yace "A'a mama nan nazo" Inna tace "toh na dai gan ka Kaman balarabe, yan gidan duk chakwulati ne su,banda Ita matan gidan amman dai batayi hasken ka ba, da nace ko kai dan uwanta ne" Farid Yayi murmishi yace" A'a mama, wurin Ummi nazo" Inna ta kalleshi da kyau tace "toh meye hadin Ummi da balarabe kuma, amman dai kasan cewa an fara shirye shiryen bikin ta ko, Kar ya zama yaudarar ka take yi" Farid yayi murmishi bai ce komai ba, chan Inna tace "toh idan ma baka sani ba yau kasani, dan gidan Alhaji Nagoda wanda yake gwamnan CBN, toh dan shi zata aura, inkes ma baka sani ba yanzu ka sani" Farid ya dan yi dariya yace "Allah sarki mama". Sakowa Ummi tayi taga Farid da Inna a parlor, yana ganin ta ya saki wata murmishi, Inna kuwa ta bisu da ido tace "ina ganin Ikon Zamani ni Yakwalo" daga haka ta mike ta wuce sama, Ummi ta kalle Farid tace "wai meye Inna take fada maka" yace "is that your grandma"? tace "ae, Ita ce maman daddy" yace "oh Allah sarki" ya bi ko ina da kallo ganin ba kowa, ya jawota ya rungume ta. Fisge kanta tayi tana turo baki tace "A'a gaskiya banaso, gidan mu fah kake kuma akwai mutane a gidan" ya dinga kallonta with his sexy eyes irin kallon Kauna. Ganin kallon ba tsayawa zaiyi ba yasa Ummi ta mike ta shiga kitchen, ba dadewa ba ta fito da tray din drinks a hannunta samirah kuma na biye da Ita da tray din flasks na abinci da plates suka kai dining. Ummi taje wurin Farid tace "zo muje kaci abinci, mummy tana zuwa" suka Je dining,ta zuba mishi abincin da drink a cup, shi dai sai kallon ta yake yi daga nan ta zauna tana danna wayar ta. Nana ce ta sakko sai kallon Farid takeyi tana murmishi tace "ina wuni" Farid ya daga kai ya amsa mata, ta cigaba da kallon shi tana tafiya har da tuntube. Inna ce zaune a dakin mummy suna magana "Hadiza don Allah kiyi wa Amina magana ta daina kawo mana samari cikin gida ai bai dace ba" mummy ta zaro ido tace "toh Inna samari kuma, a ina kika gan hakan" Inna tace "toh yanzun nan naga wani matashi kya ce balarabe ne, cewa yayi yazo wurin Amina, ni dai na fada masa ta kusan aure sabida haka ya daina shigar sabgar ta, idan ma yaudarar sa take yi toh Allah zai saka masa" mummy tayi murmishi Sosai tace "kai Inna kenan, ai toh wanda kika gani shine surukin mu fah Inna" Inna ta rike baki tace "laaa, toh ni ina zan sani tunda ban ganshi da yan gadi ba, yanzu kina nufi shine dan gidan Alhaji Muhammad Nagoda"? Mummy tace "kwarai da gaske" Inna tayi ajiyar zuciya. A parlon, Farid ya gama cin abincin shi, Ummi kuma ta hau sama domin sallah, Mikewa Nana tayi ta Nufi dining din tana murmishi tace mai "a kara maka ne ko kuma a kawo maka small chops" daidan nan su Inna suka sako, Inna ta sake baki tana kallon Nana tace "ina ganin tabargaza ni Yakwalo. Yo dan uwar ki Shatu, ko bai koshi ba ai ba damuwan ki bane" a hankali mummy tace "Inna yi hakuri mana ga baki a zaune fah" Inna tace toh, Sannan ta Nufi dining din tana kallon Farid tana washe hakora tace "ashe dai kaine surukin namu, ai toh ban sani ba tunda ban gan ka da yan gadi ba. Ya sunan ka"? Murmishi yayi yana shafa kan shi yace "Suna na Farid mama" tace "toh Farid, Amina amana ce zan baka, ka rike min Ita hannu bi biyu, Wlh yarinyan dai tabarkallah akwai natsuwa, Kaga dai Ita kadai uwarta ta haifan ma dana kuma iyayen ta suna alfahari da Ita Sabida haka don Allah Kar ka ci amanan da na danka maka kaji" yace "insha Allah mama,zan rike amanan" sai ya kalle mummy, ya gaishe ta cikin ladabi kafin yace "mummy daman munyi magana da Abba na, insha Allahu zamu zo nextweek in kawo kudin gaisuwa" tace "toh,Allah yayi maka albarka" daga hakan ta kira Ummi tazo ta raka shi. A waje ya kalle ummi yace "babe gobe Zanzo in dauke ki muje gida ki gan ammi ku gaisa, she's so eager to meet you in person" ta dan yi shiru sai tace "toh Allah ya kaimu" ta raka shi har wajen mota sanan ta koma cikin gida.

Aunty shatu ce da Nana a daki suna magana "hmm wancan banzar tsohuwan ta ban haushi wlh, amman Umma kin ganshi ne kya ce shi yayi kanshi" aunty shatu tace "Kar ki damu zanyi maganin ta, yanzu dai magana nake so inyi maki " Nana tace "ina jin ki umma" tace "yanzu Nana kina ji kina gani zaki bar Ummi tayi aure kafin ke, Sannan kina sane dan wanda zata aura amman baki dau mataki ba" Nana na kallon aunty Shatu tace "umma wane kalan mataki kuma" Umma tace "matso kusa kiji" ta fada mata wani abu a kunen ta, Nana tayi shiru chan dai tace "amman fah, saurayin Ummi ne fah" aunty shatu a fusace tace "amman walahi anyi wulakantaciya da butulu, kina ji kina gani bamu da ko taro balle sisi, yanzu Allah ya kawo mana wanda zai fitar damu daga wahala, ki samu ki aure shi, shine ki ka tsaya yin maganar banza. Kinga Ummi dai a cikin kudi ta tashi har ta girma idan ma talaka ta aura, za su iya taimakon shi, amman ke fah, so kike ki wahala har abada, dan gidan Alhaji Nagodan guda ake magana fah" Nana ta turo baki tace "toh ni umma mai kike so Ince. Ni fah ba son shi nake yi ba, kawai yamin kyau ne, umma gaskiya ki kyale ni, Yusuf yana sona kuma ina son shi, Sannan yayi min alkawarin aure na ba da dadewa ba" cikin masifa Umma tace "dan kaza kazar ki, ni kike gaya wa hakan, yanzu wancan dan gwatan kike so har kike ce min zaki aure shi, ko ke baki fishi rufan asiri da galihu ba. Wai ke baki gaji da wulakanci da talauci ba, kina gani uban naki bai ci mai kyau, ya sha mai kyau ba ina ga har ya bamu, sannan ga jarabbaben gantali da chacha daya saka a gaba. Toh bari kiji in dai nice uwarki toh sai dai inda karfi na ya kare don sai kin aure dan gidan Alhaji Nagoda, dallah tashi ki bani wuri" Nana ta tashi piii ta fita, aunty Shatu ta dau wayarta ta fara kiran kawarta. Washe gari kuwa Ummi ta tashi around 11:30 na safe wanda bayan tayi sallahn asuba ta koma ta kwanta. Sauka tayi ta gan su aunty Shatu, Inna da kuma mummy akan dining suna jiran a kawo musu breakfast. Ummi ta karasa dining din ta gaishe su Sannan ta zauna. Inna ce ke kallon aunty Shatu tace "shatu kike ko wa, ina ce dai bayan bikin zaki tafi ko" Shatu ta hadiye wani abu tace "ae toh Inna bari mu gani dai" Inna tace "kaman ya ki gani dai, ina ce daga gidan mijin ki kika zo nan, ai dai ya kamata ki koma dakin ki yanzu, ba zai yu matar aure kamar ki da yara samari da yan mata ki zo kina galantoyi a gidan mutane ba" Samirah ce ta shigo masu da breakfast, kowa yayi shiru yana ci, aunty Shatu na hararan Inna kasa kasa. Bayan sun kamala breakfast, ummi ta hau sama tayi wanka da alwala Sannan tayi sallan azahar, ta yi shafe shafe, ta nufi wardrobe ta bude ta fito da atampa golden color embellish mai kyau da tsada, style din gown ne kaman bubu amman mai katon hannu da kuma ajihu, sannan ta kashe dauri irin ta Zahra Buhari, sannan ta saka simple earing na gold, ta yafa maroon gyalen ta na Chantilly da kuma jaka da takalmi mai tsini shima maroon. Ta fesa Bakhoor da Andaleeb, ta saka kwalli ta shafa lip gloss ta fita daga dakin. Kaii Ummi tayi kyau wlh, Inna ce ta bita da kallo tun da ta sakko tace "ke gidan surukar taki zaki haka da fuska kamar na gardi babu ko hoda" Ummi tace "Haba Inna kya ce min banyi kyau a haka ba" Inna ta Saki baki tace "ke Kar ki laka min sharri" Ummi tayi murmishi ta zauna kan kujera Inna tace "toh shi Faridu yaushe zai iso" "Munyi waya dashi yanzu, yace nan da minti goma zai iso" Inna tace "Aiyo" daga nan ta cigaba da kallon TV, Ita ko aunty Shatu sai hararan su takeyi tana nazarin abin da zata yi, mummy kuma sai danna wayarta ta keyi, Nana ma haka. Ba da dadewa ba, Farid ya shigo ya gaida su, sannan ya sanar masu cewa za su wuce, daga nan suka yi sallama.

Cikin wata hadadiyar compound suka shiga wanda yaci uban nasu Ummi. Duplex guda uku ne acikin compound din, daya na su Ammi (maman Farid), daya na baban Farid sai dayan kuma nashi. Ummi na bin Farid a baya suka shiga side din ammin sa, cikin gidan is breath taking, parlon kadai abin kallo ne, gidan babba ne sosai kuma ya hadu. Ummi dai sai kalle kalle ta keyi "babe, ki zauna let me go upstairs and inform ammi" cewar Farid. Wasu yan mata kyawawa uku suka shigo parlon, daga ganin su, yan uwan Farid ne, gasu nan real ajebotas, daya daga cikin su mai suna Rayyana ta yi wa Ummi murmishi, Ita take biye wa Farid. Baban yayarsu mai suna Laila tayi aure da yara biyu, mai biye da ita kuma shine Farid, Sai Rayyana, Chuchu da kuma Ihsaan. Rayyana ta kalle Ummi tana murmishi tace "Welcome sis,are you Amina"? Ummi ta amsa mata, duka suka gaishe ta suka hau sama. Wata faran mata da bata wuce 54 ba ta sauko, kamanin ta daya da na Farid Ita ma kamar balarabiyar, Ummi na ganin ta tasan cewa ammin su Farid ce. Ummi ta duka har kasa ta gaishe ta, ammi tana murmishi tace "tashi Kinji, Allah ya miki albarka, sannu da zuwa daughter" Ummi ta amsa mata cikin ladabi kafin Ammi ta tambaye ta "kinyi sallah"? Ummi ta gyada mata kai "toh muje dining ki ci abinci" Ammi ta kwalla ma Sa'adatu mai aikin ta kira, tazo Ammi tace "Sa'a ga matan da Farid zai aura" Sa'adatu ta kalle Ummi tace "Allah sarki aunty ina yini" Ummi ta amsa mata Sannan Ammi tace "je kira su Rayyana su zo muci abinci" Sa'adatu ta amsa mata daga nan ta wuce, Ammi ta kalle Ummi tace "taso muje dining din daughter" suka mike suka je dining, ba dadewa, su Rayyana duk suka shigo, suka zauna, Sa'adatu ta zuba ma kowa abinci da drink. Sun gama cin abinci, suna ta hirar su, dukan su suka saki jiki da Ummi, Ita ma haka, chan dai chuchu tace "Auntyn mu taso muje kiyi sallah a side dinmu" dukan su suka mike suka bar Ammi da Farid a dining, suna tafiya Ammi da tabi bayan Ummi da kallo ta kalle Farid tace "wwow Amar (sunan da take kiran shi kenan) ina ka samu black beauty, she looks so natural, kuma tana da aji gata da hali nagari" Farid yayi murmishi yana sosa keya yace "ai Ammi in dai aji ne ummi tana dashi, kadan ma kika gani. By next week zamuje kai kudin gaisuwa insha Allah" ammi tace "toh Allah ya kaimu, Allah ya tabbatar mana". Ummi ce ta fito tare da su Rayyana daga bangaren su, wucewa suka yi wurin Ammi, Ummi tayi wa Ammi sallama cewa za ta tafi, Ammi tayi mata addu'a sannan ta bata kyautan wani turare mai shegen tsada, Ummi ta gode mata daga nan su Rayyana suka rakata har wurin mota inda Farid yake ta jira ta fito. Farid ya kalle Ihsaan yace "pls ki hada min coffee ki zuba min a flask kafin in dawo" daga nan suka shiga mota suka wuce bayan Ummi tayi sallama dasu. Farid, na ajiye Ummi a gaban gate ta kalle shi tace "babe baza ka shigo bane" yace "Nah, Sadiq yace min he's in the hospital, I need to go and see him" tace "oh, toh Allah ya bashi lafiya" yace "Amin babe, I love you" Ummi ta amsa masa, daga nan ta fita daga motan ta shiga gida.

Ummi ta shiga parlon da sallama, Inna ta gani tana kallon TV, ta sa banana a gaba sai dura wa cikin ta takeyi. "Ah ah,oyoyo uwar gidan Faridu Muhammad Nagoda" cewar Inna, Ummi tayi murmishi ta gaida Inna cikin ladabi tace "Inna ina yan gidan naga ke kadai aka bari nan" Inna tace "Uwar ki tana sama, wannan gajiyayun suma suna dakunan su, tunda kika fita ba wace ta kara fitowa, ai daga ganin su kinsan bakin ciki suke yi, toh insha Allahu ba tsinanniyar da ta isa ta hana auren nan" Ummi tayi rolling eyes dinta tace "uhm Inna ni dai ki gan turaren da Ammin su Farid ta bani" ta fito da turaren ta mika wa Inna "kaii kai Ummi daga gani wannan turare mai tsada ce, kwalin kadai ya isheka kallo balle abin ciki" suka danyi maganganun su, Ummi ta dauki turaren ta ganin cewa inna ta labe shi a gefenta, ta mike ta hau sama wurin mummy. Ummi da mummy suke maganan su "ai munyi waya da daddyn ki, I told him they're coming next week to pay for kudin gaisuwa, yace weekend dinan zai shigo gari" Ummi tace "toh mummy, Allah ya kawo shi Lafiya" daga nan ta fita, ta nufi dakin ta.

Abu kaman wasa, bayan an biya sadaki, akasa ranan auren Ummi da Farid nan da wata uku. Farid da Ammin sa suke magana, Ammi tace "ya kake so ayi harkan lefen, mu zamu hada kodai mu basu kudi su saka abin da suke so" Farid ya danyi shiru, chan dai yace "Ammi gara mu basu kudin kawai" tace "okay to nawa zaka aika musu" yace "Ammi nawa kike ganin ya dace abasu kinsan it's my first time" tace "I think mu basu 12 million su hada komai da suka so na lefen, ko ya ka gani" yace "ae ammi, Hakan yayi" tace " toh yanzu zan maka transfer din 2 million, sai ka cika sauran" yace "toh ammi, Allah ya saka da alkhairi, Daddy yace duk wani biki na hall yace he'll take care of it" tace "toh shikenan Allah ya saka"

Ummi ce a parlor tare da kanwar mummy wace ake kira da Nadeeyah. Nadeeyah ke bin mummy, Ita a UK take zama da yaranta biyu masu suna Noor da Nadab tare da kuma mijinta. Jin cewa bikin Ummi ya matso shi yasa ta zo Nigeria da yaranta. "Aunty Nadeeyah saukan yaushe haka, ina su Noor"? aunty Nadeeyah tace "Wlh Ummi yau na iso, su Noor suna gidan Yaya babba, zuwa anjima zasu zo tare, ina yaya"? tace "tana sama, muje" a staircase din suka hadu da aunty shatu da Nana, Nadeeyah kuwa sai kallon su takeyi chan dai tace" Shatu kece nan, kwana dayawa" aunty Shatu tace "ae Nadeeyah ya hanya, ya yara"? Nadeeyah Ta amsa mata, daga nan suka nufi dakin mummy. Nadeeyah na ganin mummy ta ajiye jakan ta da sauri ta je ta rungume mummy. Mummy tace "Nadee ke kam kinki girma ko saukan yaushe, ina su Noor" "Yaya Wlh dazu jirgin mu ya sauka, kuma su Noor suna gidan Yaya Baban anjima zasu zo tare" mummy tace "okay,shi ne baki Sanar mana a aiko driver yazo ya dauke ki ba" Nadeeyah tace "Haba Yaya, kin manta Abban su Noor na da driver a nan. Yaya nagan su shatu, hala suma sun zo dan bikin ne"? mummy tace "Hm, zama fah suke a gidan nan, sun kai wata takwas "Nadeeyah ta zaro ido tace "wata takwas, Yaya zaman meye suke miki a gida, kin fah san cewa ba shiri muke yi dasu ba fah,ko kin manta mugun halin da Ita da yayun ta da iyayen suka yi mana ne, ni dai gaskiya yaya baki birge ni ba sam" mummy tace "Haba Nadee, ai ya wuce, Kema ai kinsan hali na ba shigan sabgar su na keyi ba" Nadeeyah tace "gaskiya yaya ana gama bikin Ummi Kice su tattara su bar miki gidan ki ya isa hakan, ai dai naga nan din ba gidan gado bane ehe, salon Shatu din ta kwace miki dan tsohon ki, kin san ta da irin rayuwar yahudawa. Wai tsaya ma tukunan, Uban mai ya samu gidan mijin nata da tazo gidan mutane da yar ta har sunyi kusa shekara" mummy da Nadeeyah suka dinga hiran su, da suka yi sallahn isha suka sauka kasa. Inna, Shatu,Nana da kuma Ummi suka tarar a parlon suna kallo. Inna na ganin Nadeeyah tace "ah ah yau gamu ga babban bako" da sauri Nadeeyah ta je gaban Inna ta gaishe ta cikin ladabi, Inna tace "ya shirye shiryen biki" Nadeeyah ta amsa mata cikin ladabi Sosai, Sannan su ma suka zauna a parlon suna kallo. Wayar Ummi ne ya fara ringing, ganin cewa Farid ne yasa ta mike ta bar parlon, Inna da Nadeeyah kuwa suka bita da kallo, chan dai Inna tace "Ina ganin bariki ni Yakwalo, yaran zamani ba kunya, ni ku ma yi auren kawai a huta, ace mutum a rana sai ya kira buduruwa kusan so dari" Nadeeyah da mummy suka yi dariya, aunty Shatu kuwa ta tamke fuska. A waya Farid ya sanar wa Ummi batun yanda za'ayi da lefen, suka danyi hiran su, daga nan suka yi sallama. Ummi ta koma parlon ta zauna gefen mummy tace "mummy Farid yace wai zasu aiko da 12 million Kudin lefen,

Please Login or Register in order to submit comment