Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gama ne take cewa "shegiya, ke har kin isa kiji dadi, kin tashi a gidan kudi kina auren mai kudi, gashi yana son ki, families dinshi duk suna kaunar ki, ga kuma cikin shi a jikin ki, inaaaaaa, sai dai ba ni bace A'ishatu Tanko ba"
β„Ή Wlh people like Aunty Shatu suna bani mamaki. And the irony is they'll always end up being destroyed if basu nemi gafara ba. Irin su, basu san meye kaddara ba. Duba da yanda take cewa Ummi na da this and that as if ita ta ba kanta all these things. Allah ne yayi blessing dinta, but no! Idanun Aunty Shatu sun rufu da envy da rashin imani forgetting that Allah yayi blessing kowa. Bangaren da yayi blessing dinki ba nan yayi blessing dina ba. Allah dai yasa mu cika da imani, ya gyara mana kurakuren mu. Masu irin halin aunty Shatu kuma Allah ya shirya, ya ganar dasu.


βœπŸ“–

Bayan su Ummi sunyi breakfast, suka shiga dakin da Nabeelah da kawayen ta suke ganin cewa gidan ya fara cika jama'a. Kasancewa sai da dadare za'ayi Arabian night din yasa basu fara shirin sa kaya ko make-up ba sai ma hiran su da suke tayi "wai kun gan yanda take Iyayi ne da ta gan shi" cewar Zeenat, duk suka kwashe da dariya harda tafi, Ummi tace "waye ya taba mana mata a gidan Sultan" shewa suka kara yi, Zeenat tace "wai sunanta Fatima ko Meye" ta karasa maganar tana rolling eyes dinta, Nana tace "ai toh ki kwantar da hankalin ki tunda har yace miki she was his class mate a secondary school and she's not his girlfriend" haka dai suka cigaba da hirar su har aka kira sallahn Asr duk suka nufi dakunan su dan yin sallah. Ummi tazo wucewa taji muryar Inna a karamin parlon da Ammi da yan uwanta da wasu manyan mata suke tana cewa "toh in takaita maku sanda baban su Aminu ya aure Kande yar uwa ta" su Ammi suka biye mata suna bata hakuri, rolling eyes dinta Ummi tayi ta wuce dakin ta tayi sallah. Ummi na zaune akan daduma bayan ta idar da sallah tana waya da Farid Inna ta shigo rike da cup a hannun ta. "Baby, let's talk later or sai ka zo, Inna is here" daga haka suka yi sallama.Ummi tana kallon Inna tace "Innasko sannu" "a'a rike sannun ki, da kin damu dani ai da baki zage ni da safe ba, amma bazan bi ta danyen halin ki ba. Ba dan Aminu yana uban ki ba meye hadi na dake" tabe baki Ummi tayi, mika mata cup din Inna tayi tana cewa "Ungo yi maza ki shanye ki bani kopi" Ummi ta leka cup din ta yamutsa fuska tace "Meye wanan kuma"? Inna ta washe hakora tace "Maganin tsaro ne, kinsan mijin kawata Larai babban malamin addini ne a ungwar su, toh shine na bata dubu biyu nace ta gaya ma Malam Isuhu(mijin Larai) ya miki addu'an tsaro da saukan Al Qur'ani mai girma. Toh kafin mu taho habuja ta kawo min wani gari tace a zuba maki a kindirmo kisha, babu maye ko makiyi da ya isa ya maki komai" Ummi tabe baki kafin tace "ni bazan sha ba, ke ki sha ki tsare kan ki kuma ai ina addu'a" dakuwa inna tayi mata tace "kin ci mai garin ku, ce maki akayi bana addu'an ne, kuji min ja'irar yarinya. Toh gaskiya baza ki sani asaran dukiya ba, dubu biyu na bada aka maki addu'a, sanan dari uku na ba Naja dazu ta sayo maki wanan kindirmon" dariya Ummi tayi tace "dubu biyu da dari uku kike kiran dukiya Inna, ni fah bazan sha abin nan ba, idan ma so kike a baki kudin ki zan baki" sake baki Inna tayi, ta fara matsar kwalla tace "amman dai Hadiza ta haifa jaraba, ke ana nema maki sauki kin ce wahala kike so. Baki san cewa auren da kika yi wasu na iya maki bakin ciki ba" Ummi ta tabe baki ta kau da kan ta. "Haba Amintako yar jikale ta, yar gaban goshin iyayen ta" a haka dai Inna ta lallaba Ummi har ta sha kindirmon tana yamutsa fuska "ko ke fah yar Albarka" cewar Inna tana washe hakora. Bayan fitar Inna, Ummi mikewa tayi, ta linke dadumar, ta hau kan gado ba dadewa bacci ya dauketa. 5:40 pm Ummi ta tashi daga bacci, wayarta ta jawo ta duba time. Ganin time yasa ta zaro ido tana cewa "Innalalahi wanan wane irin bacci ne haka" mikewa tayi, ta shiga bayi tayi alwala sanan ta fito tayi sallah. Tana idarwa su Rayyana suka shigo dakin "Sis, kin tashi kenan" cewar Nana, "Wlh har na makara sallah, ya nagan baku fara shiri ba" Rayyana dake zaune kan ottoman ta amsa cewa "sis kin manta cewa sai bayan Isha fah za'a fara event, ina ko muka gan ta shiri yanzu" Ummi tace "oh yes, haka ne fah" Chuchu tayi murmishi tace "sis an kai abinci dakin su Nabeelah, in deba in kawo miki ne"? Shiru Ummi tayi tana tunani kafin ta tambaya mai aka dafa,Chuchu ta amsa "couscous da chicken salad aka yi" yamutsa fuska Ummi tayi, Rayyana ta tambaye ta ko lafiya, tace "ba zan ci couscous ba wlh" Chuchu tace "rufa min asiri sis, kinga tun breakfast baki kara cin komai ba, kuma da Ammi ta tambaye ni ko Kinci abinci nace mata ae, dan Allah kici koda kadan ne, ko kuma da abin da kike so kici ne"? Ummi tace "ni para nake so inci, wanda akwai yaji Sosai" Rayyana da Nana suka yi dariya kasa kasa, chuchu kuwa kaman tayi kuka tace "sis ina zaki gan para yanzu fisabillilahi, Idan kuma Ammi tasan baki ci abinci ba, toh kashi na ya bushe dan ce mata nayu kin ci" turo baki Ummi tayi, haka suka dinga draman su Ita da Chuchu, Nana da Rayyana kuma suna tayi musu dariya. Karshen ta dai Ummi ta yarda taci couscous din kadan, lokacin Nabeelah tare da Zeenat da Zulaikha da kuma Ihsaan suka shigo dakin suka baje suna ta hira. Lokacin magrib nayi, kowa ya mike domin zuwa yin sallah, bayan sun idar ne make-up artist har guda hudu suka iso gidan, aka fara yiwa wasu yan matan dake gidan, daya kuma tana yiwa amarya Nabeelah, daya kuma tana wurin su Ammi da aunty Turai zatayi musu, sai kuma daya da take yiwa Rayyana. Lokacin sallahn Isha nayi, Ummi ta wuce dakin ta tayi wanka da alwala sanan tayi sallah. Tana idarwa, ta fito da lafayar da zata saka sanan ta fito da designers din takalmi da jaka na company Zara, wucewa tayi wurin dressing mirror, ta shafa face cream dinta na Oriflame Sweden, sanan ta fesa turaruka masu sanyin kamshi ta fita daga dakin ta wuce nasu Ammi. Ammi dake zaune ana yi mata make-up bayan an gama wa aunty Turai na ganin ta tayi murmishi tace "daughter ina kika shiga tun safe, kin ci abinci kuwa" Ummi tayi murmishi ta gaida Ammi da aunty Turai sanan ta amsa mata cewa taci abinci. Aunty Turai tace "toh, daughter ya na gan fuskar taki babu kwalliya" "daman nayi sallah ne, kuma ana yi ma su Rayyana idan an gama nasu, sai a min" daga nan Ammi da aunty Turai suka dinga jan ta da hira dan sun lura kunyar su take ji Sosai. Bayan kaman 30 minutes Ummi ta mike tace musu zata je ayi mata make-up, amsa mata suka yi suna yaba hankalin yarinyar a zuciyar su. Ummi tazo wucewa ta parlor ta gan Inna a zaune tare da wasu tsoffafi sun cika parlon da muryar su suna hira, Inna ta sha ado cikin riga da zani na embellish din atampar Vlisco, ga madaidaitun gold earrings dinta a kunne. Ganin Ummi tazo wucewa, Inna ta kalle daya daga cikin tsoffafin da suma sun sha ado cikin shigar alfarma, tace "toh Kinga wancan da zata shiga dakin chan, toh Ita ce jika ta, matar Faridu" duk suka ce Masha Allah, Ummi dake jin su, ta gaishe su sanan ta shiga dakin lokacin an gama yiwa Nabeelah da Rayyana make-up. Tana shiga, babu bata lokaci make-up artist din Nabeelah ce tayi mata,within 40minutes ana gamawa, cikin hanzari Ummi ta wuce daki ta saka kaya dan har mutane sun fara barin gidan zuwa event center. Daya daga cikin make-up artists din ne ta taya Ummi daura lafayar ta milk color, bayan ta saka wani dark blue body con aciki, sanan aka daura mata turban mai kyau Sosai, ta saka takalmin half covered mai tsayi sosai ta dau jakar ta sanan ta fesa bakhoor dinta da wasu turaruka masu sanyin kamshi... ba karamin kyau tayi ba. Wayar ta dauka ta kira Farid ta sanar mai ta shirya yace yana hanya, daga nan ta wuce dakin su Nabeelah, nan fah taga yan matan sun sha kwalliya, sun saka Abaya, Rayyana, chuchu, Nana da Ihsaan ne kadai suka yi ankon lafaya, duk sunyi kyau Sosai. Fita suka yi daga dakin suka sauka zuwa main parlor dake cike da mata tsofaffi da budurwaye masu jira a zo a kai su event center. Sake baki Inna tayi ganin irin kyan da Ummi tayi, tace "amman dai ina ganin bariki ni Yakwalo. Amina kiji tsoron Allah kiji tausayin abin dake cikin ki. Yanzu wannan uban takalmi mai shegen tsini kaman an feke pensir( pencil) kika saka gaki da tsohon ciki" kallon cikin ta da bama Za'a san akwai shi ba Ummi tayi ta turo baki, ta samu wuri ta zauna bata kula Inna ba, mutanen dake parlon kuwa dariya suka dinga yi, inda wasu yan mata kuma suna mamakin ashe Ummi matar aure ce harda ciki. Ihsaan, Zeenat da Zulaikha da wasu yan mata suka bi Sadiq kansancewa ya iso kafin Farid, ya rage Rayyana, Chuchu, Nana da Ummi wanda Farid zai kai, sai Inna da zata bi su Ammi da Aunty Turai sanan kuma wasu yan mata da kawayen amarya. Shigowa parlon Farid yayi da sallama sai kallo ya koma kan shi, yana sanye cikin dressing irin na larabawa tsak, ba karamin kyau Farid yayi ba kaman ka sace shi, kishi ne ya zo ma Ummi ganin yan matan parlon sai kallon shi suke yi, they can't just take their eyes off him. Karasawa yayi ya gaida Inna da ladabi, Inna tace "Faridu yanzu nake wa matar ka magana akan wanan dan iskan takalmi da ta saka sai kace an feke pensir, toh ni dai babu ruwa na" murmishi Farid yayi, ya kalla Ummi dake ta turo baki, Wowww! He couldn't just take his eyes off her, she looks so chic and cute, a ranshi yace "damn, that's my gurl". Rayyana ce ta dan yi gyaran murya ganin cewa idan ba'a yi hankali ba za'ayi abin kunya. Hararan ta Farid yayi ya mike yana sosa keya ya kalle Ummi yace "muje ko" mikewa Ummi dasu Rayyana suka yi sanan ya kalle Inna yace "muje Inna, motar da zai kai ku ya iso" mikewa Inna tayi tana salati tace "wa innahu min sulaimanu, halale mu bazama" kallon Rayyana yayi yace "shiga ki ce wa su Ammi motar su ya iso" daga haka shi da su Ummi suka fita. Lokacin da suka isa hall din Sheraton hotel, a cike yake tam da mutane. Hall yayi kyau Sosai ga haske ta ko ina, sai kamshin turaren wuta dake tashi ga kowa ya sha ado cikin kaya ta alfarma. Table din dasu Rayyana da wasu kawayen amarya suke Ummi ta zauna while Farid yaje inda su Sadiq da wasu abokan ango suke. Inna kuwa tana zaune a table daya da Ammi, aunty Turai sai wasu manyan mata. An danyi huduba da wasu games and other activities kafin aka fara raba abinci irin su( Mandi rice, Biryani rice, Arabian tea, Ram barbeque, Kheer, warm milk da sauran arabian dishes) kallon mandi rice dake gaban ta Inna tayi tace "amman wane irin shinkafa ne haka duk a tsatsaye kaman nonuwan maza" dariya su Ammi suka yi harda wanda suke kusa da table dinsu da suka ji Inna. Ummi kuwa sai da ta dandana komai abin ka da mai ciki. Ansha shagali sosai kafin aka yi closing event din, lokacin har 12am yayi. Parking lot aka nufa inda ake ta kokarin shigan motoci. A yanda duk wa'enda suka fito daga gidan biki suka zo, haka suka koma.

Gaban gate Farid yayi parking, su Ummi suka fita daga motar suka nufi cikan gidan while yana bin su a baya. Dakunan su yan matan suka wuce direct, Farid kuma ya nufi dakin su Ammi dan yi mata sallama. Bayan yayi ma Ammi sallama, ya fito daga dakin yaji ko'ina tsit alamun kowa ya shige daki dayake dare yayi ga kuma gajiyan biki. Dakin da Ummi take ya nufa, a hankali ya bude kofan ya shiga sanan ya rufe tare da saka key. Saukan ruwan shower yaji daga bathroom alamun wanka Ummi takeyi, ya taka har bakin kofan ya bude ya shiga. Samun ta yayi tana kokarin daura wani pink bathrobe din mink, a hankali ya karasa yayi hugging dinta, a shagwabe yace "my baby boo" itama shagwabe fuska tayi tace "yes papiii" murmishi yayi and kissed her kafin ya dauke ta suka fita daga bathroom din. Taimaka mata yayi ta shirya cikin baby pink pyjamas mai kyau sosai, sanan suka yi addu'a tare da tofa ma junan su, ya kwantar da ita tare da jawo mata bargo, yayi kissing dinta goodnight Ummi ta bishi da kallo har ya fita daga dakin. Awww Farid is just so cool and has his ways of captivating her heart.
β„Ή It's important couples su san cewa all these little things matter, su suke kara bond tsakanin couples. Ba kullum za'a je other room ba, una no dey tire ne?! Sometimes kuyi sallah tare, read the Al-qur'an together, play games together etc. Oga, sauran kuma kace "can't be me" ko kuma kace you're a man kai Ka wuce hakan, ba zai yu ka biye mata kuna wasan yara ba, blah blah blah.Kema madam ki bada hadin kai, ba wai when Oga is trying to make efforts ba ki tsaya kina hura nose kaman balloon ke wai boss lady. Toh nidai na baku hint, sauran ya shiga kunne daya ya fita daga dayan.


βœπŸ“–

Bayan fitar Farid daga dakin Ummi, parlour ya sauka sanan ya fita daga gidan gaba daya ya nufi hotel din da suke. Washegari a gidan biki, bayan yan matan sun idar da sallahn asuba, bacci suka koma. Gari na wayewa duk suka fito dan yin breakfast as usual. After breakfast suka fara normal activities din nasu wato hira da sallah kafin lokacin dinner. Ana idar da sallahn isha, aka fara shiri kaman dai yanda aka yi jiya. Ummi ta saka wani expensive black and golden color lace, tana rike da wani black ball bag kafan ta kuma sanye da black half covered heel na company din Charles and Keith, kanta kuma daure yake da turban din raw silk material. Woah guys bazan iya cigaba da fadin irin kyau da Ummi tayi ba, "damn, that's my gurl" ta fadan Farid. Ummi is just too cuuute! Kaman jiya, haka Farid yazo suka tafi event center, amma fah da kyar, dan Farid ya kusan causing musu accident tsaban yanda ya dinga kallon Ummi. Yauma hall yayi kyau sosai, ga mata sanye cikin various dinner gowns while mazan suna sanye da tuxedos kala kala, bayan anyi opening prayers, DJ ya saka old school, nan fah iyaye manyan mata suka fara fitowa suna rawa da liki. Inna dake zaune tasha ado cikin Swiss lace, dinkin Abuja bubu ta mike ta nufi wurin MC dake rike da microphone tace "Dan nan, wane irin waka ne wanan sai kace an shaqe kazar mayu, bayan ga wakan su Shatta dasu Altine Jibo" nan fah mutanen hall suka kwashe da dariya dan muryar Inna ya fito rass ta microphone din. Komawa sit Inna tayi tana faman tabe baki. Bayan iyaye mata sun gama rawa aka saka wakan zamani nasu Davido, wizkid, Ayra Starr, Young jonn, Rema, Burna boy, Kizz Daniel da suaran su, nan ma yan mata da samari suka yi caaaa suna following dance trend din kowane waka da aka saka hardai amarya Nabeelah da angon ta, Ummi ma ba'a barta a baya ba da aka saka favourite trending song dinta 'Kehlani' by Jordan Adetunji. Mikewa tayi lokacin da aka fara playing wakan taje ta janyo Farid dinta, suka je dance floor suna bin dance trend din da lyrics din wakan
'I like the way your body is i do'
'Is that too obvious'
'Okay I like your confidence'
'Oh that's what good karma is, okay'
Li'l like Kehlani is, bad just like Kehlani is, okay'.
Nan take jama'a suka fara shewa ana hyping dinsu da musu video ganin yanda Ummi da Farid suke Kehlani dance challenge cike da nishadi, ji kake "aww, osheyyy, God when". An sha rawa an gaji, kafin aka fara raba abinci in order to retain energy. Yau dai English food irin su (French fries, omelette, Vienna sausages and grills, glazed sticks, brewed coffee, cocktails and mocktails etc) Ummi kuwa taci glazed sticks ya kai goma dan abin ya mata dadi, Farid kam sai faman tsokanan ta yake wai ta cinye rabin glazed sticks din da aka hada. Bayan angama cin abinci, akayi games da karaoke sanan akayi closing prayer daga nan kowa ya nufi gida. A gajiye kowa ya shiga daki kamar dai jiya, Farid yayi ma su Ammi sallama kafin ya wuce dakin Ummi, tsaye ya gan ta da black color skimpy nightwear, kanta daure da wani ash color vintage scarf tana shafa night face cream dinta. Murmishi tayi mai tana mika mai hannu, kaman yaro kuwa yaje da dan gudun shi yayi hugging dinta yana cewa "I'm eager to go back home baby, I'm being punished, bana samun jin dumin mata ta yanda ya kamata" murmishi ta kara yi kafin tace "you're naughty" lakace mata hanci yayi yace "and you're naughtier. Baby, I'm getting late, zan wuce, do you need anything"? Kallon shi tayi kaman mai tunani kafin tace "I want to eat olives" "I think naga wani a fridge dazu, bari na kawo" cewar Farid da ya saketa ya fita daga dakin, ya sauka kasa sanan ya nufi kofar kitchen. Yana bude kofan yaci karo da wata budurwa da baza ta wuce 26 years ba, tana da dan kiba, fara ce amman ba sosai ba kuma tana da kyau daidai. Zaro ido Farid yayi yana kallon ta da mamaki, ya nuna ta da yatsa yace "Nafisa! Ko ba Nafisa bace, meye kike yi a gidan nan"! Ya karasa maganan a dan tsawace. Kallon banza tayi mai kafin tace "ni din ce, kuma bikin kawata nazo. Abu kuma yayi kyau da na gan ka because I've been trying to reach you across all platforms amman kayi blocking dina. It's high time you meet our son, dan ka na bukatan ka at this stage" wani irin kallon tsana ya watsa mata yace "are you crazy? ko wiwi kika busa ne? We've had this discussion and it's good as dead. Babu yaro tsakani na da ke, in fact bamu san juna ba. Ina biyan ki dubu dari shida every month for his upkeep yanda kika bukata idan ma kari kike so zan miki, but stay out of my life, I have a wife, I love her and I'm happily married. What happened between you and I years back was a mistake that will never repeat itself, kuma hakki na is on you because you masterminded and planned everything, Allah ya isa tsakani na dake" ya karasa maganan yana huci. Daga murya Nafisa tayi tace "wallahi, tallahi, bilahillazi ha' illa huwa baka isa ba. Yes I did what I did sabida son da nake maka and so what ai ba kaina aka fara ba, amman baka isa kace you don't know me ba, baka isa kayi denying dan dana haifan maka ba! I don't need your money anymore, ina karban kudin ka bawai dan i can't afford to take care of our son ba, ina karba ne because i want you to know that kana da responsibility akan ka apart from your so called wife, all I need is for you to show some fatherly love to your son. Wallahi kayi wasa Farid I promise you I'll mess you and your family up, just try me you son of a b!tch"!

β„ΉAna wata ga wata, waye Nafisa, kuma meye alakar ta da Farid da? Why is she saying she has a son with him? Farid ya taba aure ne bamu sani ba? Meye take nufi da "Yes I did what I did sabida son da nake maka", what did she do? Why is Farid mad at her da har ya ja mata Allah ya isa? Is she at fault da tace he should take fatherly responsibility for his son? I mean that's what every father should do right? Ga kuma madam wato Ummi, ko wane hali zata shiga idan ta ji? Sooooo many questions, and you can only get your answers in the next chapter. Sanan nasan baku ji dadin na kawo obstacle tsakanin Farid da Ummi ba, but haka rayuwa take, gbas gbos up and down, yau dadi gobe tsami. Sai dai a cigaba da hakuri sanan a dogara ga Allah. Don't forget to send your comments or reviews via this contact: 07046861910.
🚫No CALLS please just comments.

βœπŸ“–

Wani gigitacen mari aka dauke ta dashi, a tare, cikin rudewa suka juya suna kallon Ummi da basu lura da shigowan ta kitchen din ba. Daga hannu Nafisa tayi zata rama marin da Ummi tayi mata Farid ya kama hannun ta, a tsawace tace "sake ni inci uban yarinyar nan. Ni kika mara shegiya" ta karasa maganan tana kokarin kwace hannun ta. Basu ankara ba, Ummi ta kara daukan Nafisa da wani marin tana cewa "kece dai shegiya ba ni ba. Ke har kin isa ki shigo gidan mutane kina zagin maman wani, ke mahaukaciyar ina ce"! Farid ne ya fara kokarin raba fada ganin Nafisa tayi nasaran kwace hannun ta ta kaima Ummi naushi. Nan fah hayaniya ya balle tsakanin su, Farid yayi nasaran bambare Nafisa daga jikin Ummi, ya dauke Ummi ya nufi parlour da ita Nafisa na biye dasu tana bala'i. Hayaniyan dake tashi a parlour ne ya farkar da sauran mutanen gidan. Ammi ce ta tashe Aunty Turai tana cewa "ke ina jin kamar muryar su Ummi ne fah" mikewa suka yi da sauri, a atare suka fita daga dakin, daidan lokacin su Nabeelah da Inna suka fito daga dakunan su cikin sauri. "Innalalahi, Feenart meye haka"? Nabeelah ta fada cikin daga murya tana kokarin rike ta. Da sauri su Ammi suka karasa cikin parlon suna kallon Ummi dake zaune a kasa tana hawaye, hancin ta da gefen bakin ta na jini, ga kuma Farid da tissue a hannu yana kokarin goge mata tana ki tana cewa "wlh karka taba ni, don't you dare touch me"! Kallon mamaki kawai mutanen parlon suke musu. Ammi ta kalle Farid fuska a daure tace "what just happened here"? Kasa amsawa yayi, Ammi ta mai tsawa tace "da kai nake fah, meya faru"? "Ff fada suke yi Ammi" ya bata amsa, "ai wlh baza ta sabu ba, yanzu wancan mai kama da danyen gyada ta maki wannan danyen aikin? Kuma Farid sabida kai rago ne ka tsaya wata bagidajiya ta maka Jinajina da fuskar mata. Toh wlh ban yarda ba, yanzu nan zamu chaji ofis a garkame mani yar banza, zaki san jika ta kika daka yau. Ke Ihsaanu yi maza dauko min mayafi na a daki" cewar Inna tana duba fuskar Ummi. Sauke ajiyar zuciya aunty Turai tayi kafin tace "A'a mama, kiyi hakuri bai kai haka ba, a nan za'ayi ta ta kare" ta kalle Nafisa cikin dakewa tace "ke Feenart meye ya hada ki da matar Farid"? kasa magana tayi, aunty Turai ta daka mata wani tsawa da sai da kowa a parlon ya firgita "ki bani amsa, meye ya

Please Login or Register in order to submit comment