Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BAYAN RAI*

Gidan daya zaba din gida ne sama dake da babbar haraba da zata iya daukan motoci goma,akwai balcony da zaka shiga wanda yake dauke da babban falo,hagu da dama na bangon falon qofofi ne guda biyu,kowacce qofa akwai babban falo hade da bedroom a cikinsa, kitchen daya ne wanda yake falon,saidai babba ne,babu wanda zai takura wani,hakanan side biyu gareshi,a falon akwai stairs da aka qawata da wasu irin makarai masu kyau,marbles ne zube har zuwa saman,inda zai sadaka shima da falo babba ne dakuna guda uku ne a saman kowanne manne da toilets dinsa,sai wani balcony din daga sama wanda zai baka daman ganin ainihin harabar gidan fetal,a qasan akwai spare din daki guda daya,sai dakunan baqi maza da na me gadi daga can wajen gidan.

Gidan yana da girma,don kowanne daki da falo babbane qwarai,hakanan yadda aka tsara ginin ya bada sha:awa ainun,saidai jabir da ya gani yaga gazawar ja:afar din,a matsayin da Allah ya bashi,duba da gidan da zai dauko unaisa

"Idan gidan bai mata ba saita fasa dani ta zaba wani fine,iya abinda zan iya kenan" ya gayawa jabir,kamar shine unaisan.

Duka kudin anty maama na lefe ya tura mata abinta ba tare daya sake wani musu ba,hakanan dukka wata zirga zirga ta samarwa da baqinsu masauki tare dashi aka yita,saidai sau tari har suje su dawo ba zakaji yace kanzil ba,lokutta mafi yawa wayarsa na a hannunsa ne,cikin abokansu guda biyun da suketa zirga zirgan tare babu wanda ya kawo komai ransa,saboda sunsan wayeshi,captain j din haka nan dabi'arsa take sun sani tun ba yau ba,magana ko surutu shine assignment mai wahalar cinyewa da zaka hadashi dashi.

Sai daya qara kwana biyu sannan ya samu ya sukunin saka time na zuwanshi gidansu unaisa kamar yadda abbi yayi masa umarni,ganin yadda yake shiga cikin sabgogin yasa abbi bai tanka masa,don yana ganin sauyi muraran da kuma qoqarin bin umarni daga wajen ja'afar din.

A ranar yayi zamanshi a sassansu kamar bashi da plan na zuwa ko ina,tab ce saman cinyarsa yana duba wasu abubuwa,sanaye yake da bawin boxer wanda ya fidda ainihin qirar tsayayyun qafafunsa dake cike da tarin gargasa,jabir ya turo qofar dakin ya shigo,a shirye tsaf cikin shadda,sai yaja turus ya tsaya

"Me zan gani?,J baka duba agogo ne?"

"What happened?" Ya tambayeshi a nutse abinsa,kamar ma baisan meke faruwa ba

"You are very stubborn manya,me yasa kakeso ayita maimaita magana daya?,just simple instruction amma ka kasa bi" idanu ya watsa masa bayan ya kashe tab din

"Yaushe na gaya maka fasa zuwa na?"

"Ai banga alama ba"

"Kamar?" Ya tambayeshi yana shafa dan qaramin gemun dake manne a habarshi,ya kuma hade da zagayayyen gashin dake kumatunsa zuws qasan hancinsa

"Gashi nan kuwa ina gani,you are sitting properly,dafa'an kamar babu inda zaka?" Yatsansa ya sanya yana bin tsahon karan hancinsa daga sama zuwa qasa,ya lumshe idanunsa kana ya budesu yana furzar da iska,sai daya sauke qafafunsa qasa daga samam glass table din da take kai sannan yace

"Okay,so kake kazo ka sameni ina ihu guri guri ina announcing ma mutane zanje naga hurul'een ko?" Idanunsa ya lumshe yana sake girgiza kai alamun a'ah

"You should remember.....ita din ba kowa bace a wajena face GURBIN IDANUN da ba zasu taba zamowa idanu ba,koda zasu shekara miliyan anan din" daga haka ya miqe a nutse yana ajjiye kayan hannunsa ya nufi toilet

"Oho dai,no matter how dolenka kaje,na baka minti ashirin ka taddani falo,idan kuma ka wuce hakan....,basai na qarasa ba"

Kusan sai da jabir yayi dana sanin fadin wannan maganar,saboda sai da ja'afar ya ninka ashirin sau uku,don sai daya dauki awa daya cif sannan ya fito,saidai ya dauki kyau iya kyau yadda ya kamata,sanye yake da wani lallausan farin yadi na maza dake da shara shara,takalmin qafarsa baqi ne dan qasar Italy,hular dake kansa tun daga nesa take qyalli kamar farin tangaran,sosai kwalliyar tabi jikinsa,ta kuma dace da yammacin,hatta jabiru sai daya yaba da adon,amma sai ya fake da qorafin dadewa da yayi,bai kulashi ba,saima seat mai zaman banza da yayi zamansa,ya fidda wayarsa yana aikawa wani client dinsu saqonni,ya kuma turawa saubam secretary dinsa saqon ya sameshi a wani eatery goben yanason su tattauna.

Cikin wata farar Rolls-Royce ghost v12 mallakin ja'afar din suka fita,suna cillawa saman kwalta jabir ya qarawa motar gudu sosai,bayan ya cikasu da ac kamar yadda suka saba amfani da ita,basa ko ji ga jikinsu.


29
_ZAFAFA BIYAR💯💕_

_ZAFAFAN LITTATTAFAI GUDA BIYAR🤌_

_YAN BIYAR MASU BIYAR DIN:_

_1-DARUSSAN RAYUWA_
_2-FADAKARWA,_ _3-WA'AZANTARWA, 4-NISHADANTARWA_
_5-TSAFTATACCIYAR KAUNA MARAR GAURAYE_

_KADA KU MANTA, YAN BIYAR DIN NA TAFE NE CIKIN TAFIYA TA KARO NA 7, SABON SALON TAFIYAR DATA FI KOWACCE INGANCI DA DIMBIN DARUSSA NA RAYUWAR YAU DA KULLUM_

_KU SHIGO A DAMA DA KU DON JIN ME KE FARUWA ACIKIN LITTAFIN *SANADIN LABARI NA*: NA *HAFSAT RANO*, LALLE AKWAI BABBAN SANADIN DA ZAI WAKANA ACIKIN ZUKATAN BIYU... DON SANIN SU WAYE SAI KU GARZAYO A DAMA DAKU._

_SHIN *BABU SO!!! (MIYA KAWO KISHI?)* NA *BILYN ABDULL* LALLE LAMARIN FA AKWAI GUMURZU. DOMIN TSAFTACEN *SO* SHI KE JANYO ZAZZAFAN KISHI A TSAKANKANIN MASOYA BIYU. KU ZO A CIGABA DA TAFIYA DA KU._

_*NAYAH....(RIBA BIYU)* NA *MAMUH GEE* RAYUWAR AYSHA INAYA NA DAUKE DA WASU SINADARAI NA TACACCIYAR KAUNA. AMMAN WANENE GWARZON DA ZAI SAMU NASARAR CAFKE WANNAN RIBA BIYU? TA KAUNAR INAYAH DA INAYAH DIN KANTA. KU TAHO MU TAFI DA KU A TAFIYAR MU_

_*FARHATAL QALB (FARIN CIKIN ZUCIYA) NA MSS XOXO* FARIN CIKIN ZUCIYA MAGANI NE NA ZUKATAN DA KE CIKIN DAMUWA. LALLE AKWAI NASARAR FARHATAL QALB GA DUK ZUKATAN BIYU DA SUKA TSINCI KAN SU CIKIN BEGEN JUNA . KU ZO MU KARASA WANNAN TAFIYAR DA KU_

_*GURBIN IDO (BA IDO BA NE) NA SAFIYYAH HUGUMA* ... SO BAYAN RAI..... KAUNA CE MARAR YANKEWA DAGA ALLAH. SU WAYE ZASU SAMU NASARAR CIKE GURBIN DA KE IDO? ZUKATA BIYU NE..KU BIYO MU DON GANEWA IDANUN KU CIKEWAR GURBI_

_DUKA WADANNAN LITTAFAI GUDA BIYAR. NA MARUBUTAN ZAFAFA NE WANDA KE YIN SU A YANZU._

_WANNAN TAFIYAR ZAFAFA MA TAZO MUKU DA TSARIN TALLACE TALLACE WADANDA ZAMU KAI MANHAJOJIN MU NA:_

_*FACEBOOK, INSTAGRAM, YOUTUBE, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES, TELEGRAM DA MA WATTPAD... MUNADA DIMBIN MASOYA DA KE BIBIYAR MANHAJOJIN SHAFUKAN MU. SU KE KUMA KOKARIN SIYAN DUKKANIN KAYAYYAKIN DA MU KA TALLATA._

_MUNA TALLATA HAJOJIN KU CIKIN FARASHI MAI RAHUSA._


Tafiyar mintuna ita ta sadasu da unguwar cikin gidan minister,sun samu tarba me kyau bayan haj Aaya ta samu sanarwar zuwansu,waje na musamman cikin gidan tasa aka kaisu,sannan tasa aka taso mata unaisa dake barci a sannan,ta fara shiryata da kanta bayan ta sanyata ta sake wanka,cikin wani material na alfarma mai dan banzan kyau da tsada.

Karo na biyu ja'afar ya sake duban agogon hannunsa,yayin da yake biye da maganar da jabir din ke masa kan dakunan da aka kamawa baqinsu sunyi kadan,za'a qara wasu da kuma yadda suka tsara event din da za'a gudanar

"Komai yayi,amma banda ni a taronku,saboda babu abinda zanje a ciki,walima ce kawai ta zama sunnah,ita dince ma nake tunanin zanje,anma fa babu tabbas itama,kada ka zura jiki da yawa" yayi dukka wannan maganar yana kallon lafiyayyen agogon dake kwance a fatar hannunsa

"Time up" yafada yana miqewa tsaye cak,sai jabiru ya bishi da kallo

"What do you mean?" Sai daya zuba hannayensa duka cikin aljihun rigarsa yana duban jabir

"Mintuna takwas nayi niyyar ware mata a yau din,kuma ta cinyesu wajen jira, you know.....i don't wait for anyone,amma dai na cika maganar abbi tunda nazo" dubansa jabir yake cike da mamakinsa,ja'afar.....ja'afar?.

"Amma dai abbi ba cewa yayi ka shigo gidan ka fita ba ko?,cewa yayi kuga juna,ka ganta ne J?"

"Na meye sai na ganta?,no need" ya amsa masa yana dage kafadarsa,sai ya juya da zummar takawa yabar wajen,dai dai sanda ta iso,cikin matuqar ado,mutum uku cikin masu aikin gidan na biye da ita da.manyan trays da aka jerawa kayan ciye ciye da shaye shaye.

Idanunta a kansa,kamar yadda fuskarta ke baibaye da murmushi

"Hello" ta fada tana waving hannayenta,murmushin fuskarta na sake fadada

"Welcome our bride" amsar jabir kena data qara ninka farincikin dake zuciyarta

"Thank you " ta amsa masa kafin ta sake maida dubanta ga ja'afar wanda har yanxun yake tsaye

"am sorry,i keep you waiting ko?" Ta fada tana murmushi,sai ya motsa kafadarsa

"Don't mind,ina cika umarni ne" gatsal jabir yaji maganar tayi masa,bai murmure daga wannan ba yaji unaisan na cewa

"Have a set please?,kaman maganan zaune tafi ta tsaye"

"It's too late......lokacin zamana ya cika,i have a lot to do,see you later" ya fada yana qetareta zai wuce abinsa.

Wani abu ne ya tsayawa unaisa a wuya,duka wannan lokacin data bata amma ko na minti uku cikakke bai kasance da ita ba zaice tafiya zaiyi?,uwa uba ma sau daya tak taga ya kalleta ya dauke kai?,tana da tarin.abubuwa masu yawa da takeson su tattauna dashi,don haka batayi qasa a gwiwa ba tabi bayansa tana tsaidashi

Cak ya tsayan,sai taji abun ya mata nauyi kasancewarta maje mai bala'in jin kai,sai itama fa tsaya tana duban ingarman bayansa take tsaye sosai tsakanin mayalwatan kafadu dake cike da siffar qarfi da cikakkiyar tsaiwa ta cikakken namiji,a hankali taga ya waiwayo,ya kuma tako zuwa gabanta ya tsaya,tsaiwar da taji ta har tsakiyar kanta,saboda tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,uwa kuma wani shegen kwarjini yayi mata,wanda ya mamayeta kota ina,qamshin lallausan turarensa ya ziyarci hancinta,sa'annan kuma hucin fitar numfashinsa data rasa me yasa yake fita da nauyi haka?,bata gane amsar tambayar tata ba sai daya fara magana,ta fuskanci cikin fushi yake,ransa ne ya baci,abinda ya bata tsoro kenan,duk da cewa fuskarsa a murtuke take cike da rashin fara'ar da dama can kowa da ita ya sanshi,to amma wannan bacin ran dake kwance saman fuskarsa bai jima da samoshi ba

"Ki kula,ki kuma yi a hankali,banason matsi ko takura,zaifi kyau ki kasance me nisantata akan yunqurin kusantata da kikeyi,stay away from me.....na gaya miki wata gaskiya guda daya wadda babu lallai a samu wanda ya gaya miki ita?" Yayi maganar yana dage girarsa dukka biyun,bata amsa masa ba saboda wani yanayi daya shigeta,shima bai damu ta amsa din ba ya dora mata

"Bana buqatar rayuwar kowacce mace da sunan matata a cikin tawa rayuwar,already na rufe wannan babin,idan kin shirya ma kuma kutsa kanki ciki...... it's okay for me" ya qarasa fada yana dage kafadunsa,sai ya juya cikin takun nan nasa mai cike da ginshira yana barin wajen.

Ko sau daya batayi yunqurin tsaidashi ba kamar dazun,sai kallo data bishi dashi qirjinta yana dukan uku uku har ya bacewa ganinta,kafin muryar jabir ta katse mata dukka hanzarinta

"Are you okay?" Ya tambayeta yanason karantar yanayinta,don baisan me ja'afar yace da itaba,kasancewar akwai tazara tsakaninsu,amma yafi kowa sanin halinsa,tabbas something bad happened,akwai abinda ya gaya mata,saboda yadda fuskarta ta sauya gaba daya ta kuma birkice.

Abirkicen ta girgiza kai

"Akwai damuwa tabbas" batayi qasa a gwiwa ba ta gaya masa maganganun da sukayi,sosai jabir yaji babu dadi,amma a zahiri sai ya kawar da hakan daga saman fuskarsa

"Karki damu,nasan J,a yanzun rashin sabo ne ya kawo yake gaya miki haka, with time zaku saba,zakiga kuma kaman bashi ba" sosai yayi qoqarin gaya mata maganganu masu kwantar da hankali,har sai daya fuskanci ta nutsu sannan ya taka mata gaban main entrance na gidan,sannan ya wuce zuwa inda suka ajjiye motarsu.

Hannu yasa ya bude murfin motar idanunsa na sauka kan fuskar ja'afar,wanda ya kwantar da seat din motar ya kuma miqar da bayansa sosai a kai,jin bude motar baisa ya motsa ba,har sai da jabir ya shigo,sannan ya bude kyawawan idanunsa da suka sauya kala a hankali ya watsasu kan fuskar jabir

"Kaci sa'a kaine,da saidai kazo ka samu empty din wajen"

"Yanzun ma me ya hanaka tafiya?,tunda kazo kayi abinda ranka yakeso?" Ya amsa masa yana dan nuna masa bacin ransa,duk da yasan ja'afar din dole abishi a sannu,saboda wata irin zuciya da yake da ita da bata iya qaramin so ko qi ba,hakanan ba qaramin riqo shaheeda ta yiwa rayuwarsa ba adan tsukin lokacin na zaman da sukayi.

Bai sake cewa jabir komai ba,sai dan qaramin tsaki da yaja yana tada seat din ya zauna sosai,tun basuyi nisa ba suna isa wani guri yace jabir din ya saukeshi qofar wani gini,kamar ya tambayeshi me zaiyi sai yaja baki ya qyaleshin,ya saukeshin ya kuma wuce da motar.


***********Dukkan tafukan hannayenta ta buda tans kallon tsakiyarsu,batasan me zata tuna ba,saidai ta samu kwanyarta fayau babu komai tun daga sanda taji ana hargowa sa hayaniyar zuwan al'ummar gombawa,ta dai tsinci kanta da matuqar sanyi da kuma faduwar gaba,wanda tunda aka fara bikin kwana hudu kenan yau cikon na biyat bataji irinsa ba sai yau,tasa ran ganin anni da amnanta cikin matan da suka iso,saidai babu daya cikinsu,kusan dukka baqin fuska ne idan ka cire anty maama wadda ita ta jagoranci tafiyar.

Ko ba'a gaya mata ba tasan cewa ayau qaramar hukumar ta gembu ta karbi baquncin manyan mutane irin wanda bata taba karba ba,jiniya da qarar ababen hawa kala kala ke tashi,hayaniyar da hatta cikin dakin da take zaune bai tsira ba,dakin dake cike da 'yammatan fulanin da suke danginta ne,duk kuma cikinsu bataga gaje ko gilmawar inna furera ba,tun ranar da za'ayi mata kamu inna fureran ta iso,da tarin sharrikanta wanda ya zame mata tonuwar asiri saboda zuwan yuuma garin,wadda da ita ake gudanar da komai,batasan inda inna fureran tayi ba tun ranar da aka silleta,umarni dai na qarshe da aka bata maimunatu tayi yaqinin shine abu mafi tsauri a wajenta da zai iya sanyata batan dabo

"Ki tattaro duk wata dukiyar dabbobi ta shatu da maimunatu dake hannunki ki kawo mana ita" bammmm!!!!.

"Alhamdlh,aure ya dauru" muryar maroqin mai babban maqogaro ta kwararo cikin gidan,ta kuma isar da saqon nasa inda yakeson ya isa,lungu da saqo na gidan,sai kuwa mata suka dauki guda,gudar data zagwanyar da duk wani qwarin gwiwa na maimunatu,ta nannade kanta da kyau cikin mudukajenta(kayan saqi na zallar lallausar auduga na musamman da matan bappa sama'ila suka tanadar mata harda na yafawa saboda wannan ranar),take taji kamar zazzabi keson kamata saboda sanyi daya fara ratsa qashinta wanda batasan dalilinsa ba,tana jin 'yammatan na waqe waqensu na fulani suna kuma tsokanarta amma ko motsawa batai ba.

Tana ji daga tsakar gida wata qanwa ga kakarsu ta wajen mahaifi tana fadin tare za'a wuce da ita da 'yan daurin aure zuwa can gombe,sunce nan da awa daya a shiryata" gabanta yayi mummunar faduwa,tana jin fargaba sosai,tana jin kamar su annin baqinta ne,duk da zuciyarta na gaya mata,bawai dasu anni zata zauna ba,zataje ne tayi rayuwa da wasu mutane na daban da batasansu ba,batasan halaye da dabi'unsu ba,bakuma tasan yadda zata fusakanci zama dasu ba.

Tana jin sanda aka gama tiri tirin hada kayayyakinta tsaf,yuuma na tsaye akai,tamkar ba daga dangin ango ta fito ba,domin tace ita din a yanzun uwace ga maimunatu bawai suruka ba,ita ta riqeta ta rakata zuwa gaban baffaninta da wadanda ke a mazaunin uwayenta a yanzu,sunyi mata dukkan nasihar da akewa kowacce diya mace a al'ada sanda ta tashi tafiya gidan miji,dukkan wannan abubuwan maimunatu ganinsu take kamar a majigin film bawai a gaske ba,kamar raqumi da akala haka take biye dasu sanda suke riqe da ita zuwa jerin gwanon motocin dake jiran fitowarta,su kuma tashi dasu zuwa gombe.

Shi daya ne cikin motar sai driver kamar yadda jabir ya tsara hakan ba tare dashi ya sani ba,zaman da yayi cikin motar ya yishi ne yana jiran fitowar jabir da yace yayi mantuwa a inda suka zauna,duba daya zakayi masa kasan cewa ango ne shidin zammm,yayi wani irin kyau na musamman cikin wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya,wadda ta lashe maqudan kudade tun daga wajen siyota har ya zuwa dinkin da aka yi mata,aikin hannu me matuqar kyau tsari da kuma tsada,takalmin sauciki kalar dark blue sosai daketa daukar idanu saboda sabunta kyau da kuma tsafta yana aje gefe,qafafunsa babu komai sai sock,gefensa ya fidda babbar rigar ya ajjye,a samanta ya cire hularsa kalar dark dark blue da ratsin light mai wani irin walqiya da daukar idanu ya ajjiyr hade da babbar rigar,hatta da links din hannun rigar gold color ya cireshi,ya nade hannun rigar zuwa gwiwar hannunsa,gargasarsa dame kwance luf ta bayyana sosai.

Wata magazine data wallafa sunayen fitattu kuma manyan kamfanunuwan gine gine a satin yake dubawa,kamfaninsu shine yazo a jeri na biyu,duba bayanan yake,amma can tsakiyar qirjinsa wani irin nauyi ne dake cunkushe a cikinsa,ranar ta yau gaba daya tazo masa ne kamar cikin mafarkai,tunda ya auri shaheeda kuma mutuwa ta rabasu bai taba tsammanin akwai rana irin wannan da zata zo ba,dukka wannan abun yanata qoqarin yaqi da abinda yakeji cikin zuciyarsa ne,amma a yau din,babu wadda ke ziyartar zuciya da kuma tunaninsa sai shadeedan,yana tuna rana irin ta yau cikin rayuwarsu data kafa masa tarihin da bazai gogu ba har abada.

Haske ne kadan ya bayyana a motar bayan an bude murfin motar,yana shirin daga kansa ga zatonsa jabir ne,sai yaji muryar mata suna fadin

"Shiga da bismillah,Allah yasa kin tafi a sa'a" wani abu ya tsaya masa a wuya sanda take shigowa motar a hankali,tana gama zama kuma aka maida murfin motar aka rufe,sai yaji driver yaja ya soma tafiya.

Shuru ne ha ziyarci motar,babu wani motsi ko kadan a cikinta illa motsin injina dake aikinsu can qasa,cikin jikinta take jin sauyin waje da yanayi tabbas ya fara daga wannan lokacin,duk da bata iya ganin komai clearly amma tasan tabbas ba ita kadai bace cikin motar.

Hannunsa ya zura a aljihun rigarsa ya fiddo wayarsa yanata qoqarin hadiye bacin ransa,shi jabirun zai rainama wayo?,yana nufin shi da ita zasuyi tafiya har ta wadannan awannin a mota guda don ya rainama kansa hankali?, numbers dinsa ya nema ya kuma kirashi,bugu biyu ya daga

"Jabir" ya ambata da wani irin sound dake nuna zallar bacin rai,saidai kuma ba wani da qarfi yayi maganar ba

Lumshe idanun
ta maimunatu dake qudundune cikin yalwataccen mayafin da aka rufa mata har ka
tayi,bugun zuciyarta dake qara bugu take qoqarin saitawa,sautin muryar ya doki kwanyarta,tamkar a cikin kunnuwanta aka furta sautin kalmar jabir din,saita hade jikinta waje daya sosai,tana jin takalminta ya zame daga qafarta,amma babu damar ta motsa bare ta maidashi,hakanan kawai takejin wani irin tsoro yana ratsata,tabbas wannan shine mutumin daya zama mijinta a yau.

"Kada kace komai,don muna tare dasu abbi,ga motarmu nan tasowa,wataqil zamu tsaya a hanya mu kwana saboda nisan tafiyar,please i beg you, don't misbehave,ka dorar da farincikin dasu abbi suka samu a yau din" magiyar jabir ta yau ta tabashi,don haka baice komai ba,amma hakan bai hanashi jan tsaki ba bayan ya kashe wayar

"Stop the car solomon" ya fada da tattausar husky voice dinsa

"Okay sir" ya amsa masa cikin girmamawa,sannan ya gangara gefan hanya ya tsaya.

Rigarsa da hularsa ya dauka ya bude murfin motar ya fice ya koma zuwa seat din gaba,sannan ya bashi umarnin ci gaba da tafiya bayan ya gyara zaman kujerar yadda zaiji dadin jingina ya zama comfortable sosai.

30

ASSALAM ALAIKUM DEARIES
BARKAN KU DA KOKARI…. KAMAR
KODA YAUSHE. WANNAN KARON MA
MUNA BARAR ROKON KU WAJEN
TEMAKAWA CHANNEL DIN SUDEIS
DAKE MANHAJAR YOUTUBE
YARO NE DAYA TASHI DA SON
KARATUN ALQURANI ME GIRMA. YA KE
KUMA KWADAYIN GADON ME SUNAN
SA SHEIKH SUDEIS. DAN ALLAH A
TEMAKA A DANNA MASA SUBSCRIBE.
A KUMA YI VIEWING DA LIKING. A
TEMAKA DA SHARING MA... JAZAKUM
ALLAH KHAIRAN AS YOU DO... "
Assalamualaikum dear sisters and
brothers.
Welcome to ummu sudais YouTube
channels?
A channel where the Holv Quran is been
recited from different Angles.
Click on this link and listen to the
Beautiful recitation that will melt your
heart
https://youtu.be/Lafgc749sK8
Your subscription to our channel is of
Great important. Please help us grow
our channel by subscribing and likitoci


30


Ko sau daya bacci ko gyangyadi basuyi nasarar fusgarta ba,hakanan ko qwaqwaran motsi batayi tsahon a wannin da suka dauka suna tafiya,hakazalika motar haka ta kasance shuru,ba zata ce ga ainihin abinda yake faruwa cikin motar ba,sai daga bisani ne tadan janye mayafin dake kanta kadan saboda ta samu damar kallon gefan hanyoyin da suke wucewa da mugun gudu.

Taraba suka wuce kai tsaye saboda su raba tsahon tafiyar,uwa uba kuma yammaci tayi lis,babu security ace sunyi tafiyar dare,don haka suka yanke sauka a wani hotel dake kan babbar hanyar da zata sadasu da gombe,kafin su iso ma tuni jabir yayi booking dakuna,don haka suna isa kowa key na dakinsu aka bashi.

Itakam tana zaune cikin motar,har zuwa sanda anty maama ta qaraso ta fiddota,ran anty maaman cike da haushin ja'afar din,ta yaya sunsha wannan doguwar tafiyar xai fita yabar diyar mutane cikin mota?.

Yana tsaye a tsakiyar dakin yana amsa waya sanda anty maama tayi knocking,ya qarasa bakin qofar ya murza handle din ya bude mata ba tare da ya tsaya tambayar waye ba,kana yaja da baya yana ci gaba da amsa wayar.

Bakin madaidaicin gadon dake shimfide da farin lallausan bedsheet,tadan duqa kadan dai dai kunnuwan maimunatun,ta yadda ita kadai zataji abinda take gaya mata

"Ki saki jikinki da mijinki,ki samu kiyi wanka da brush kafin ki kwanta,zan ciro miki wasu kayayyaki cikin akwatinki za'a miqo miki,ki saki jiki kinji ko?" A hankali maimunatu da kanta yake a duqe ta gyada kan nata,tana jin zuciyarta na wani irin bugawa,a tsahon shekarunta na goma sha shida tunda take bata taba kebewa da wani d'a namiji ba a daki daya kamar haka,balle har ta kaisu da kwana kamar haka,yau gashi za'a fita a barta da wani,wanda yake amsa sunan miji a gareta.

Juyawa anty maama tayi ga ja'afar wanda har yanzu bai gama wayar ba,sai ta kada kanta ta fice a dakin,qarar rufe qofar dakin ya sanyashi waiwayowa,don bai lura dawa suka shigo ba,ya zaci tazo wajenshi ne zasuyi wata maganar,kuma sai yaji ta fice ba tare da tace komai ba,abinda ya sanyashi juyowa kenan.

Cikin mamaki idanuwansa suka sauka ga maimunatun,kawo masa ita sukayi kenan?,lallai dai sai sun qure haqurinsa da juriyar da yaketa azawa ransa?,sai ya dauke idanunsa yana sallama da wanda suke wayar dashi,ya yanke kiran yana neman number jabir.

Bugu daya ya daga,muryarsa cike da wani irin nauyi yace

"Baku da wani extra dakin?"

"For who?" Ya tambayeshi kai tsaye,don dama yasan dole ko yaya sai ya nuna turjiya

"Ban sani ba,am asking you ne,it's simple question,just answer me bawai ka tsaya tuhuma na ba"

"Oh...oh sorry, let me ask abbi first,but dakin kadan ya muku ne?" Ya tambaya cikin zolaya izgili da neman fada,haushi da takaici ya sanya ja'afar jan dogon tsaki kana ya tsinke kiran,wai dole sai jabir ya sanyashi dogon magana ne?,baisan abinda yakeji bane?. Sai ya cilla wayar saman madubu,sannan ya jawo kujerar gaban mudubi ya zauna a kai.

A hankali ya duqa yana zare takalmin qafarsa,idanunsa suka kan farar qafarta dake dauke da dogayen yatsu

4 Comments On GURBIN IDO
avatar
salima

2 years ago

Reply

Nice story

avatar
ibrahim-6-8

1 year ago

Reply

That's so amazing

avatar
zee-zakariyya-umar

3 months ago

Reply

I want to download the books please

avatar
zee-zakariyya-umar

3 months ago

Reply

I want to download the books please

Please Login or Register in order to submit comment