Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

miqa mata hannu,ko batayi.magana ba tasan me take nufi,shi yasa gaba daya batayi nufin amsar kudin ba,saboda tasan cewa zata raba matar da kudinta ne,ita kuma da tayi niyyar bawa ba zata mori komai a cikinsu ba,duka ta dunqule kudin hannun nata ta miqawa inna fureran,sannan ta tsugunna ta debi kayan aikinta ta fara gyara wajen bata ko waiwayeta ba.

Babu kunya babu kuma tsoron Allah ko daya a tattare da ita ta hade dukka kudaden ta irge abunta cas ta soke su tayi gaba abinta tana rera waqa,yau itakam ranta fes,mutuwa batayi mata komai ba sai rana data yi mata,banda silar mutuwar ina ita wannan dukiyar?,ina ita ina mallakar wadan nan kudade?,kudi kam sunzo mata a dai dai,tanadin bikin gajenta zata farayi tun yanzu,saboda bikin gata takeso tayi mata.

>>>>>>>>>>"sannu anni.....an gama komai ko?" Yuuma ta fada sanda take shigowa rumfarta dauke da kwanon sha da ta cikashi da damammiyar fura da nono wadda babu surkin sugar ko kadan a cikinsa

"Mun gama komai ramatu..dabbobi lafiyayyu,har sunso sufi na labaran din ma"

"Ai sunfi ma anni,sun hadu da makiyayiya mai hazaqa da iya kiwo,irin kiwon da babu ha'inci a ciki" yuuma ta fadi tana zama sosai gaban anni tana murmushi

"Ai naga alama,ko ba wata yarinya maimunatu ba?"

"Itafa,baiwar Allah" yuuma ta fada fuskarta na dan canza yanayi

"Ai tunda na shigo Allah yake hadamu,naketa ganin abubuwan mamaki daga wajen yarinyar,na jima banga me kiwo irinta ba,sannan abinda zai sake baki mamaki da ita.....wajen cinikin nan,kowacce dabba da muka nuna manaso sai datayi mana bayanin lafiyarta da sauransu,babu ha'inci" cikin gamsuwa yuuma take gyada kai

"Bata tsinta a qasa ba ai,gado ne me kyau daga wajen mahaifiyarta,Allah ya jiqan ruma"

"Allah sarki,kice marainiya ce?" Anni ta fada tana jan kwanon furar gabanta tana qoqarin budewa

"Marainiya ce,wadda aka kasa yi mata riqo na tsakani da Allah.....kinsan mahaifiyarta anni,kin tuna matar da kikaga wata balama me juna biyu a wajenta kikai sha'awarta shekarun baya can da suka shude,ta qara miki da kyautar wata akuya,akuyar da kikace ta miki albarka fiye da kowacce dabba a kiwonki?"

"Af.....af ina zan manta da wannan baiwar Allar,dama itace mahaifiyarta?"

"Itace anni" yuuma ta amsa mata tana dauko wani kwanon da ta shaqewa anni shi da dambu me dumi tana aje mata

"Allahu akhbar......." Maganar annin ta tsaya sakamakon shigowar laila tana qananun mita.

Daga kai anni tayi ta dubeta,daure take da zani daurin qirji da kuma qaramin hijab fari,sai jakar kayan wankanta dake riqe a hannunta,daya hannun nata kuma wayarta ce

"Wanne irin sakarci ne haka zaki fadowa mutane ba sallama?,banason tsiyatakun banza da wofi fa?" Cuno bakinta tayi gaba tana sauke wayar daga fuskarta tana kallon anni

"Don girman Allah anni ki karba wayar da abbi ya baki ko zamu huta da ire iren takurar su ya jabir" gyara zamanta tayi tana kallonta sosai

"To...idan kuma naqi sai yaya kenan uwata?" Hannu laila ta yarfe,bataso annin ta hutsance mata,lallabata takeson yi ta karba a wuce wajen

"Anni.....yanzu fa wanka zan shiga,ashe muna hanya daxun ya kirani banga miscal dinsa ba sai yanzu,ina daga wayar ko tsayawa amsa sallamata baiyi ba ya hauni da balbalin masifa,Ni bansan sanda ya koma haka ba wall....." Maganar tata ta katse saboda shigowar wani kiran,saita duba sannan tace

"Gashinan ma" gaba data tattar wayar harda earpiece din jiki ta miqawa anni ta juyawa tana shirin ficewa

"Wannan zaren na jiki da kika hadani dashi shi zan qaqabawa kunnena?,bada ni ba gada a maqabarta,zoki tsige abinki ki karbi naji da gayan wayar ma" dole ta dawo ta cire matan yadda ta buqata da sauri don kada kiran ya katse ta sake jazawa kanta wani sabon mita da qorafin.

*Arewabooks:Huguma*

*10*

"Assalamu alaikum" ta furta kamar yadda yake a al'adarta duk sanda zata amsa waya,daga daya sashen muryarsa ta bayyana,cikin sanyi daya sanya annin ta shanshano wani abu daga gareshi tun kafin yace wani abu

"Barka da dare"

"Dare?,a garinku kenan" daga can sashen da yake sai daya dafe goshinsa,ba zata taba yarda ta karba yadda ya bata ba sai tayi challenging dinsa

"To barka da safiya shikenan?"

"Yanzu naji magana.....barkanmu kadai" dorawa yayi da

"Kun tashi lafiya,ya jama'ar gidan?"

"Alhamdulillah,lafiya qalau,jama'ar gida mun barsu a gida,mu mun danyo balaguro nan cikin adamawa"

"da wannan qafar anni?" Ya fada murya a kwance cikin nuna kulawa

"Eh,to ya za'ayi,duk inda Allah ya tsaga sai ka taka saika taka din kafin lokacin da takun naka zai qare"

"Hakane....." Ya fada a taqaice

"Banji duriyar jafar ba" ta fada cikin zaquwa da son jin muryarsa,ajiyar zuciyar da taji jabir din ya sake sai da gabanta ya fadi

"Maganarshi na kira nayi miki anni" ya fada a sanyaye

"Menene kuma?" Ta tambayeshi gabanta yana faduwa

"Anni har yanzu dai.....har yanzun babu wani ci gaba anni,sai abubuwan sunyi kamar zasu gyaru sai su sake rikicewa"

"Kuma dai?" Ta fadi cikin tsantsar damuwa,kamar tana gabansa ya gyada kai

"Wallahi anni,yanzu haka tun jiya banga fuskarsa ba,nayi iya bakin qoqarina ma naga ya fito ko ruwan zafi ne ya sha idan ma bazaici abinci ba amma ko motsi yaqiyi bare ya bani alamar da zata gayamin yana raye lafiya lau"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kalmar da taja hankalin yuuma,ta koma ta zauna daga shirin tashin da takeyi din,ta kuma kamawa daada sukakai salatin tare.

Sosai fuskar anni ta nuna alamun tashin hankali da kuma damuwa,wannan wata matsala ce data zama kusan jarrabawa cikin tata rayuwar,saidai a yadda Allah yayi mata komai a rayuwa,ya albarkaci zuri'arta,to ta dora hakan a matsayin jarrabawar da ubangiji kan yiwa kowanne bawa don ya gwada imaninsa

"Ka kira wayarsa?"

"Ya rufeta anni,yaqi bude wayar.....amma ki kwantar da hankalinki,koda bazaice komai zan sanar dashi daga bakin qofa,awa uku suka rage ya cika awa ashirin da hudu a dakin,idan har bai bude ba ya fito zan sanarma jami'an tsaro na qasar su shigo su balle qofar su dubamin shi,duk da jikina yana bani lafiya qalau yake,tunda fitilar dakinsa naga a kunne take tun jiyan kawo yau"

"Jabir.....duk yadda zakayi ka tabbata kayi ya fito haka a dakin nan,na gaji da zamanku a wannan qasar jabir,bana jin zan barku kuci gaba da zama kamar yadda kukeso"

"Kada ki damu anni"

"Ka kula dashi don Allah,duk abinda ake ciki ka shaidamin,kada ka yarda da maganar babanku kan kada a gayamin komai,ni hakan shine kwanciyar hankali na"

"In sha Allah,i will do my best anni"

Jikinta a matuqar sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta ta ajjiyeta a gefanta,sai ta hade hannayenta waje guda

"Ya Allah.....mun tuba Allah,Allah ka kawo mana qarshen wannan matsalar,wannan damuwa Allah ka yanke mana ita gaba daya,ubangiji ka aiko mana da HASKE"

"Ameen......lafiya kuwa anni?" Yuuma ta tambayi annin cikin matuqar kulawa da kuma damuwa,saboda ta fuskanci koma wacce irin matsala ce lallai ba qarama bace a wajen annin

"Jafar ramatu,har yanzu jafar ya kasa komawa kamar kowanne irin mutum,jafar ba jahili bane....amma bansan me yasa ya kasa yarda da qaddararsa ba,gaba daya rayuwar jafar ba ita bace a yanzu,wani jafar ne na daban da dukka muke kallon an sauya mana shi,tsahon shekara uku amma komai ya kasa wucewa?"

"Jafar dai anni?" Yuuma ta tambaya tana dubanta,kai ta jinjina

"Shi.....tun daga shaheeda da amra suka rasu,bamu sake gane kan ja'afar ba,babu irin roqon Allahn da ba'ayi masa ba,ana kan yi masa ma,ba irin nasiha jan hankali da ban bakin da jafar bai samu ba,ba za'ace babu sauqi ba sam,saidai tashi danganar data zo sai tazo wani iri,duk da cewa dama miskili ne mara son magana me kuma bau dadden hali.....amma hakan baisa rayuwa ta naqasa tako ina ba,yana rayuwarsa kamar kowa,yana kuma yin dukkan wani abu daya dace da mutum kamarsa zaiyi,amma tun bayan nan jafar gaba daya ba shine tare damu ba,sai abun yayi kamar zai dai daita,sai ya sake dilmiya cikin damuwa me zurfi,na dauka zaman gidansa ke sake dagula masa lissafi......sai nasa ya tattaro ya dawo cikin gida,duk da haka babu wani canji,sai na sake tunanin kodai zaman kadaici ne?,tunda a baya shi din me aure ne?,na shiga nema masa yarinyar da zata dace dashi,ta kuma kula dashi......amma abun takaicin,wallahi ramatu yadda kikasan nayi busa a iska,baisan ma anayi ba,wannan yasa duka yaran suke kasa daurewa,saboda kowacce tana tsammanin samun kulawa da soyayya daga gareshi,to duka babu ko daya da suke samu,abinda yake sanyasu sarewa kenan,su kuma ce sun haqura......ba tare da sun duba cewa a yanzun shi din tamkar mara lafiya yake ba,zuciya da qwaqwalwarsa na buqatar magani ta hanyar mu'amalantarsa da dawowa dashi ya dawo ja'afar na asali......sannan koma meye sai ya biyo baya.....karo hudu kenan,amma dukkaninsu sun gaza daurewa zama dashi.......abinda ya bani mamaki da tsoro,yasa kuma na saare shine,wadda na nema masa a karo na shida 'yar uwarsa ce,a yadda abun ya dauko naji dadi.matuqa,saboda ina hangen haske da kuma waraka,don yadda yarinyar ta jajirce,ashe akwai mummunar manufa a ranta,dukiyarsa take hange,Allah ya toni asirinta,na gano na kuma watsa tafiyar,tunda dama shi wanda ake dominsa baima san inayi ba" shuru anni tayi tana maida numfashi,abun yana matuqar damunta da zuciya,a yanzu duk duniya zata iya cewa bata da matsala sama da wannan.

"Iyaka nazari da hangena,babu wata hanya da zamu samu yadda mukeso sai ja'afar ya haqura yayi aure,saboda jabir bazai taba dawwama tare dashi ba,shima mutum ne,aure zaiyi,don maganar da ake yanzun,watanni kadan suka rage akai masa kudi da sa rana,yau idan jabir ya tafi,shikenan haka zamu zuba idanu muna kallon rayuwar jafar ta dulmiya ta nutse a gaban idanuwanmu?" Kai yuuma ke girgizawa,tsahon wasu mintuna shuru ya baqunci dakin,kafin yuuma ta saki ajiyar zuciya

"Maganarki gaskiya ce anni,hanya daya ce tak ta fitar da ja'afar daga yanayin da yake ciki,hanyar kuwa itace,a sama masa mace mai tsananin sonsa,so fisabillahi saboda Allah,jajirtacciya da zata iya kasancewa koda yaushe tare dashi,mai juriya da zata iya daukan dawainiyarsa.....komai nisan zangon da zasu samu dashi kafin a cimma gaci...."

"Wannan shine abunda muka kasa samu har yanzu" anni ta katsi numfashin yuuma,gyara zama yuuman tayi

"A nawa tunanin kaf cikin matan da kuke nema masan,kuna sama masa ne irin matan can wajejenku,wadanda idanunsu ke a bude,suke ganin cewa 'yantattun mata ne su,wadanda zasu shiga gidan aure ne da dukka iko da isa irin wadda d'a namiji ke da ita,ba bautar aure zasuyi ba,zama ne na 'yanci da cin gashin kai" shuru ne ya sake ratsa dakin,sai hayaniya daga jama'ar dake karakainarsu daga waje jifa jifa tana ratsasu.

Sosai maganar yuuma ta ratsa anni,ta kuma sanyata zama ta dinga wareta daya bayan daya tana nazarinta,lallai yuuman tayi wani dogon nazari da kuma tsinkaye,wanda ita kanta bata yishi ba tsahon lokacin da aka dauka matsalolin suna faruwa.

Kusan rarrabuwa hankalin anni yayi kashi kashi,tana sauraren kira daga khalid,tana kuma ci gaba da nazarin maganar yuuma,tare da tunanin inda zata kamo bakin zaren,ta damu da ja'afar matuqa,tana kuma shiga damuwa ainun game da lamarinsa.


Sam hankalin anni bai kwanta ba har sai data samu tabbacin lafiya lau daga bakin jabir

"Ka bani shi jabir zamuyi magana" kai jabir din ya girgiza yana duban bakin qofar dakin da yake zaune a yanzu daura da ita,kamar wanda aka bawa gadin wajen

"Bai fito ba har yanzu anni,duk da munyi magana,amma ina da tabbacin nan da dan wani lokaci koda baiyi kiran kowa ba zaiyi kiranki" ya fada with full confidence,saboda yasan tsakaninsa da annin

"Shikenan,ka sake kula don Allah jabir"

"In sha Allah anni" ya fada shima zuciyarsa na karyewa,bayason wannan ja'afar din na yanzu,yafi qaunar ja'afar dinsa na asali,duk da dama tun asali azama da ja'afar din sai shi,duk da yadda mutane suke daukansa suke kuma kallonsa....amma zai iya cewa bai taba rayuwa da wani mutum me dadin zama irin ja'afar din ba,wasu abubuwa ne game tattare dashi da idan ka fahimcesu shikenan.

Wunin ranar gaba daya anni ta qarar dashi kan tunanin maganganun yuuma,ita kanta yuuma ta fuskanci yau din annin akwai damuwa fal tattare da zuciyarta,don ko abincin rana data kawo mata bata cishi ba sai kusan gefin la'asar,ta jima sosai tana waya da daya daga cikin yayanta.

Sanda rana ta kammala faduwa,wanda ya zamana lokaci ne na sallar magariba,annin na daya daga cikin mutanen da basa wasa da ibada,wannan ya sanya ubangiji ya bata kyakkyawan tsufa da kuna qwarin jiki,banda ciwon qafa babu abinda yake damunta,zaka zaci shekarunta basu kai yadda take fada ba.

Tana saman abun sallah tana lazumi,hannunta riqe da carbinta,ta tsakankanin labulen dakin tana hangen wulgawar mutanen gidan kowa na sabgar gabansa.

Waiwayawa tayi ga laila dake kwance tana latse latsen waya abinta sakamakon bata sallah ta watsa mata harara,ta shafa addu'arta tana shirin mata magana akayi sallama daga tsakar gidan.

Tsam anni tayi da ranta,saboda sautin muryar kamar tasan me ita,hakanan sai taji kamar ta saba jin muryar dama. Yuuma dake alwala tana wanke qafafuwanta ta waiwayo,sosai mamaki ya cikata,karon farko bayan wasu shekaru da suka shude rabon da taga maimunatu cikin gidan,don haka ta miqe cikin kulawa

"Lafiya maimunatu?" Tafukan hannuwanta dake a dunqule ta budewa yuuma,kyakkyawar sarqar wuya ta ainihin dutsen wuri da kuma murjani na asali ta bayyana

"Kun yada wannan ne a gidanmu dazu" zubawa sarqar idanu yuuma tayi,don tasan bata da ita,dutsene maj tsada wanda su kansu fulani sunsan dajarsa

"Anya kuwa?.....amma....qarasa rumfata ko anni ce,don nasan da laila ba zata saka wannan ba" kai ta gyada tana sakin siririn murmushi,sannan ta fara takawa zuwa rumfar yuuman,gabanta yana dukan uku uku,batason ta hadu daada mahaifiyar ibrahim,bare shi ibrahim din kansa,ita daya tasan irin jan kunne da kums gargadi da tasha daga wajen inna furera,ba shakka banda akwai qudurin da innar keson cimmawa ma,babu abinda zai sanyata ta kawo musu sarqar.

"Wa'alaikumussalam,shigo mana" anni ta fada tana zubawa maimunatun idanu sanda take sanyo kai cikin dakin,idanunta ya sauka ga gefe wuya da kuma kunne zuwa kuncin maimunatu karo na barkatai a yau din,ita din bata jiya bace ba kuma ta yau bace,wannan tabon tun dazu data kalleshi ta tabbatar da cewa na duka ne,to amma me yarinya kamar maimunatu tayi da za'ayi mata irin wannan dukan?,me aka saka akayi mata wannan dukan dashi?,sai taji ranta yana baci abinda.bai faru ba a yanzu.

Ita din wata irin macace da bata qaunar zalunci ko kadan,ko kai waye,ko yaya kake da ita,matuqar ta fuskanci kana da dabi'a ta zalunci yanzu zaku raba hanya.

Gaban annin ga durqusa,tasa hannu biyu tana miqa mata sarqar,anni ta miqa hannu ta karba

"Hukumullahi...ni nayar da ita,tabbas,to kinga basan ma ta fadin ba banda Allah ya tsananta rabo yanzun kin ganta kin kawomin,da haka zan yita bulayin nemanta" anni ta fada tana sakarwa maimunatu murmushi,zuciyarta da ruhinta cike da soyayya da kuma kaunar maimunatun,halayenta mabanbanta ne da halayen sauran al'umma,abar yabo ce ta gaske kuma a zahiri,godiya ta yiwa maimunatun sosai,tans juya abun a ranta ta tayar da sallah.

"Anni.....gaba daya yau tunani ya sanyamin ke agaba,komai yayi zafi maganinsa Allah anni,aci gaba dai da addu'a,wataran komai zai warware in sha Allahu" yuuma dake ajewa anni kwanon tuwo ta fada,don idan annin tazo har ta koma babu ruwanta,irin tasu cimar takeci,takan ce ko a gida rashin samun me tsaya mata da irin cimar ne yadda takeso,amma ita bata da kamar irin abincinsu.

Ajiyar zuciya annin ta sake tana miqe daya qafar tata data jima a lanqwashe ta fara yi mata tsami

"Ramatu,inajin wani abu a jikina tattare da yarinyar nan"

"Wa fa?" Yuuma ta tambayi anni tana tattara hankalinta gareta

"Maimunatu"

"Ohhh.....maimunatu?"

"Ita.....tun dazu da mukayi magana dake ramatu nake juya zancan cikin raina,da magaribar nan bayan yarinyar tazo ta kawomin sarqa ta,sai gaba daya tunani ya damfaru a kanta,na lura da irin dabi'un da nake buqata tattare da yarinyar,ta hada juriya haquri da kuma amanar da zata iya zama da ja'afar,dabi'u da kuma halayen da tabbas zata iya dawo da ja'afar yadda yake ja'afar dinsa"

"What!" Laila dane kwance ta fada cikin rata,har maganar tata taso ta fito fili

"Me anni ke fada ne?,ta manta waye ya ja'afar?,ta manta waye yaa J?,the classic and unique guy?,ya ja'afar fa ake magana da wata bafulatanar ruga?,saura kadan ta miqe ta zauna,amma sai taci gaba da kwanciya,tanason jin yadda maganar zata kaya.

Dukka idanunta yuuma ta fidda tana duban anni

"Anya kuwa anni?,bakiyi ragon tunani ba?ja'afar fa?"

"Me yasa kika ce haka ramatu?,ko hasashe na bai hasaso dai dai kan dukka nagartarta ba?" Kai yuuma ta girgiza a hankali tana juya abun a ranta,bai kamata tayi shuru ba wani abu ya kasance daga baya kuma ta zama abar zargi ba daga kowanne bangare,abu me muhimmanci ta fara gayawa anni wace ainihin maimunatu tukunna

"Dukkan abinda kika hasaso akan halayen maimunatu haka suke,yarinyar har tafi haka ma,dukka rugar nan sunsan da wannan,saidai wani baqar al'ada da jahlici gami son rai sun rufe musu idanu basa ganin wannan,bari na gaya miki wace maimunatu tun daga tushe,wanda ba kowane cikin rugar nan ya sani ba,domin kuwa,ni din,nice qawa qwaya daya tilo da mahaifiyarta keda ita a rugar nan,wadda bata da kamata,wani rikici da ya faru tsakanin gidan da gidan nan yasa bappa ya yanke huldata dasu saboda wanzar da zaman lafiya,abinda ya rabamu kenan da shatu,har zuwa sanda ta koma ga mahaliccinta" kai anni ta gyada tana bada hankalinta zuwa ga yuuma,yayin da itama yuuma ta nutsu sosai ta fara yima anni magana

"Furera mahaifiyar gaje,waddda kukayi ciniki a hannunta,mata ce ga jauro,wadda keda yara biyu dashi,macace mara mutunci ta gasken gaske,wadda ba kasafai ake tabota ta qyale ba,me son abun duniya ce da kuma masifar son 'ya'ya,asalinta bafulatanae gembu ce,jauro ne dan wannan rugar,muna zaune tare da ita tsahon shekaru,kwatsam tayi baquwa,wadda ta shigo rugar nan tare da furera da taje ganin gida,matar itace shatu,wadda tazo da diyarta maimunatu......sun shigo tare da tarin dabbobi wadda dukka dabbobin nan mallakin shatu da diyarta maimunatu ne,amma kuma a idanun kowa dabbobi na furera ne,don a haka ta gayawa kowa wannan labarin,ta shaidawa mutane cewa gadonsu dama taje gida karbowa ta taho dasu,ta kuma hado da wadda zafa dinga mata kiwo tana biyanta wato shatu,abinda zai baki mamaki,shatu ba kowace bace a wajen furera face 'yar uwarta da suke uba daya,bata da ikon musawa ko qi,saboda a sannan shatun na cikin wani yanayi na tashin hankalin rayuwa,tana neman mafaka,mahaifin maimunatu baqo ne,irin baqin dake shigowa garin na gembu saboda huldar kasuwanci da kuma yawon buda idanu,a nan yaga shatu ya kuma tsaya kai da fata sai daya aureta,a nan garin ya barta saboda ta nuna tafison zama cikin danginta,yana zuwa yana ganinta yayi mata kwanaki ya koma,mutum ne mai arziqi,don haka gida na alfarma ya ginawa shatu,ya zuba mata dukka kayan alatu da more rayuwa,ta yadda gidan shatu shi ya zama abu kwatance da kuma burin kowa cikin garin nasu,wannan ya haifar da hassada daga zuciyar 'yan uwanta da suke 'yan uba,saboda ita shatu su biyu mahaifiyarsu ta haifa a gidan,ita da 'yar uwarta sa'ade,kusan jinin dakinsu ne haka,sannan kuma da baiwar zallar kyau da Allah yayi musu fiye da sauran 'yan uwansu,itama sa'ade nata mijin me hali ne sosai,hakan ya sake haifar da zallar 'yan ubanci a tsakaninsu,saidai sunata dannewa saboda suna rabarta suna kuma samun akhairai da abun duniya daga wajenta,kasancewarta ba mai rowa ba,a haka ta haifa maimunatu,dukka alhaji na zuwa wajenta ne yayi mata satittika ya tafi,bayan ta.haifi maimunatu yake maganar zai kaita taga danginsa,saidai kuma wata tafiyace ta taso masa,wanda ya dauki tsahon watanni kafin ya dawo,koda ya dawo din kuma shima yana da niyyar kaita,har sun shirya sun saka rana,yace zai taho takanas daga kano ya dauketa. Shiri sosai shatu tayi domin zuwa ganin surukanta,ta shirya maimunatu da kyau wadda ke samun gata kamar babu gobe,itama haka,saidai haka ta yita jiran alhaji amma shuru babu shi babu dalilinsa,nata da wayar hannu bare ta nemeshi,haka tayita zaman jiransa har dare yayi ta fidda tsammani,ta sanyawa ranta qila wani abune ya tareshi,ta barwa gobe. To washegarin ma dai haka ta yita jiransa shuru babu shi babu labarinsa,haka wata washegarin,wasa wasa sai ga kwanaki nata tafiya shatu bata sake ganin gilmawar alhaji ba,abun ya daga hankalinta qwarai da gaske,tafi tafi watanni suka fara shudawa shuru babu shi babu dalilinsa,ga ciki da ya bayyana a jikinta,ita dai ta yarda da alhaj dari bisa dari,saboda iya tsahon zamata dashi tsakaninsu ita dashi babu komai sai son barka,mutum ne mai son addini da kuma kiyaye dokokin Allah,kusan a wajensa shatu tayi karatun addini mai dan dama wanda ta dinga koyawa maimunatu,duk da a sannan ta sanyata makarantar islamiyya da boko,amma kamar tasan yadda rayuwa zata juya musu,sai take zama duk bayan sallar magariba take mata nata karatun,ganin cewa yarinyar tana da budaddiyar kwanya dake saurin kwashe karatu,don tun bata isa sakawa a makaranta ba ta sanyata,tace tayi wayon acan,hakan yasa adan lokacin ta samu karatu me yawa,tana cika shekara tara zata shiga ta goma ta gama primary,mahaifinta nada niyyar yi mata shirin shiga makarantar gaba wannan abun ya faru"

*Follow my arewabooks account for more new pages*

HUGUMA



*11*


"Yau da gobe bata bar komai ba,hakanan zara bata qyale dami ba,dukka kayan abincin da shatu ke dasu wanda alhj ke jibge mata suka faru suka qare,ta fara kame kame,a sannan yan uwanta suka fahimta,sukayi mata caa,yar uwarta saade tace kada ta kulasu,ita ta dinga taimaka mata har zuwa wani lokaci,wanda kishiyar mahaifiyarsu wadda wajenta suka rayu sanadiyyar rasuwar mahaifiyarsu tun suna qananu ta tayar da borin qarya,ta tara manyan gari,ta fada musu qabli da ba'adi kan rashin dacewar zaman shatu ita daya cikin gidan,tace saidai lallai ta dawo gabanta da zama,saade yayar shatun bata qalubalanci hakan ba,hakan yayi,duk da tasan badon Allah inne tayi hakan baAmma kuma bayan giya akwai wata caca,maza maza tayi ta sanya aka saida gidan da shatu ke ciki,tunda mallakin alhj ne,ya ginawa shatun,ta tattara kudin ta siyawa shatun dabbobi ta damqa mata,saboda gudun abinda kaje yazo,babu jimawa shatu ta tattara ta koma gida ita da maimunatu,gidan da suka fara sabuwar rayuwa me cike da qunci da kuma takura,wahalhalu iri daban daban,zuciyar shatu na cike da qauna da kuma begen mijinta,jiki da zuciyarta sinqi yarda da zancan daketa yawo a garin kan cewa,mijinta guduwa yayi ya barta,tafi kowa sanin halinsa,tayi imani bazai aikata mata haka ba. Zama ya sake tsanani a wajenta sanda inne ta fahimci cikine da ita,tayi tsalle ta dire kan ba za'a haifa mata dan da bashi da uba ba,maganar data tsayewa shatu da saade a rai,ta kuma kusan haifar mata da ciwo,a lokacin saade bata kusa da ita,kasuwanci ya shillata ita da mijinta zuwa benin republic,wanda tayi matuqar baqincikin hakan,saboda sanin halin da 'yar uwarta take ciki,amma babu yadda zatayi dole tabi mijinta. Ana tsaka da wannan fa shine inna furera taje garin,ita tunda ta qyalla idanu taga dabbobin da shatu ke dasu tayi mata romon bakin ta biyota rugarsu tayi xamanta,ta kula da dabbobinta ta haihu a can babu takura. A zaton shatu ta samu mafaka a wajen yayartata,saidai tun basu kai ga shigowa rugar ba ta fara yanka mata sharuda tare da shaida mata dokokin da rugar ke dasu,suka kuma yi yarjejeniyar dabbobinta zasu shiga a mazaunin na ita fureran,idan ba haka ba zaayita kawo musu farmaki ana kashesu tunda ita baquwa ce. Ko a sannan shatu shekarunta basu fi ashirin da hudu ba,saboda auren wuri akayi mata kamar yadda aka saba.

Shatu ta shigo baquwa a rugar nan,wadda hatta da kyanta ya banbanta da irin namu,babu tausayi ko tsoron Allah furera ta maida shatu da maimunatu tamkar bayi da basu da 'yanci,shatu bauta maimunatu bauta,Allah ya zubawa shatun wani irin haquri juriya da kuma kau da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On GURBIN IDO
avatar
salima

12 months ago

Reply

Nice story

avatar
ibrahim-6-8

9 months ago

Reply

That's so amazing

Please Login or Register in order to submit comment