Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sassanyan abu ya ratsa zuciyarta ya kuma haifar mata da yalwataccen murmushi akan fuskarta,a fakaice taci gaba da binsa da kallo,tana jin wani farinciki yana ratsata,burinta ne na tsahon wasu shekaru Allah ya cika mata shi,duk da cewa ranta ya baci a dazun da ganin irin gidan daya zaba a jjiyeta kuma tare da wata,saidai anty talatu ta kwantar mata da hankali

"Kinsan baso yake ba,ta yiwu yayi hakanne don ya baki haushin dama harkiyi wani abu da zai janyo a fasa gaba daya,dole fa saikin anjiye rashin haqurin nan,kin janyo hankalinsa a hankali a hankali,sanda zai canza miki gida ko ya rabaki da qasar ma gaba daya bai sani ba" qwarai ta gamsu da maganganunta,don haka ta ajjiye komai gefe a ranta.

Cikin salo ta amsa sallamar tasa cikakkiyar amsawa,bai sake cewa komai ba itama ya ajjiye mata ledar,ga zatonta zai qaraso koda gefanta ne yace wani abu da ita,saidai gani tayi yana shirin ficewa,muryarsa can qasa ya furta

"Gudnyt" ya tursasa zuciyarsa ta fada,duk don son ganin yayi abinda ya dace bakin gwargwado.

Gabanta ne ya fadi sanda yake gab da fita,ta daga kai tana dubansa ta madubin,zuciyarta tana bata shawarar tsaidashi,yayin da wata zuciyar ke hanata,tana gaya mata girman wannan rana a wajenta,ita yafi kamata ace an tsaida,an kuma nema kasancewarta cikin dakin,tana wannan shawarar da tattaunawar da zuciyarta har ya fice.

Kasa zaune tayi,ranta ya baci sosai,ta dinga kai kawo tana tunani a ranta,shin sassansa ya tafi ko kuwa na maimunatu?,sai taji zuciyarta taqi aminta da hasashen daketa mata yawo,don bai kamata ace sassan maimunatun ya fara sauka ba,tunda a qa'ida itace babba,ta girmewa maimunatu,ita ya kamata ta fara karbar baquncinsa,tafi maimunatu sanin rayuwa dama komai da komai da za'a tarairayi mutumin da ya jima babu mata a gefansa kamarsa,don haka ta gyara rufin mayafinta,ta kuma bude qofar ta fito.

Bata ma isa sassan maimunatun ba taji motsinsa daga sama,don haka taja birki,ta kuma koma nata sassan,girman kai yana sauko mata,tana jin ba zata iya nemansa a yau ba itama.

Yana shiga dakin ya sauke ajiyr zuciya mai qarfi kamar zai tofar harda qirjinsa,ya soma bin dakin da kallo,an qawata masa shi yadda yakeso ya kasance,idanunsa daya bayan daya suna sauka kan hotunan shaheeda da amna da amra wanda aka musu tare yasa aka gyarasu aka shiryasu a falon gwanin burgewa,kai kace idan ka kirayesu zasu amsa,zakayi tsammanin har yanzu sune ke rayuwa cikin gidan,addu'ar da baya gajiya dayi musu yayi wani abu na motsa ransa,ya wuce zuwa bedroom dinsa.

Sai daya gama duba komai daya ce a sanya masa a dakin,wanda yake buqatar ya canza masa waje ya canza masan ya ajjiyeshi inda yakeso,sannan ya fidda kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,sai ya wuce toilet kai tsaye,ya daura alwala sannan ya fito ya kuma bude walking wardrobe dake manne da bedroom dinsa ya shiga ya duba wasu navy silk pyjamas Natalya's company,ya shirya kansa wadata jikinsa da turaren da yake amfani dashi duk dare,sannan ya feshe kansa da BB hair spray.

Abun sallarsa ya shimfida sannan ya tattara dukkan hankalinsa da nutsuwarsa ga alqibla.

Unaisa kuwa kusan raba dare sukayi suna waya da anty talatu qanwa ga mahaifiyarta haj Aayah,tana gaya mata abinda yafaru,ita kuma tana shirya mata yadda zata aiwatar da komai,sun jima sosai suna tattaunawa kafin suyi sallama

"Amma dai lafiya ko?" Haj Aayah da suke kwance daki daya da qanwarta wadda bata kai ga komawa gida ba ta tambayeta

"Eh to,lafiya amma ba lau ba" abinda ya farun ta gaya mata,sai ta sauke ajiyar zuciya

"Yaron nan fa ba lafiyar kwanya ya cika ba,idan anyi magana sai kuce depression ne ya kamashi bawai ciwon hauka ba,ni tsorona ma kada ya kama min diya ya jibga,don banjin zanyi kawaici,babu yadda banyi da unaisa ta haqura dashi ba amma ta kasa haqura" murmushi talatu tayi

"Banda abinki yaaya,ta yaya yana da ciwon hauka zan goya ma unaisa baya ta aureshi,an gaya miki ciwon damuwa ne,kuma a yanzunma komai yana wucewa tunda gashi ya amshi mata har biyu,mudai burinmu kawai diyarmu tayi zarra ta zama star dinsa,don kishi da bafulatana sai an kula,shegen surkulle garesu" haka suka yita tattauna maganar a tsakaninsu a daren.

Itako maimunatu wani nutsuwa ta sauko mata bayan ta gama dukka addu'o'inta ta isa ga gadonta ta kwanta,gadon data dinga ji kamar ba nata ba,dakinma kansa jinsa take kamar an bata aronsa ne,kewa da kadaici suka dinga damunta,sosai ta dinga ji cikin ranta inama ace an bata amna,sannu a hankali idanuwanta suka dinga nauyi,bacci kuma me qarfi ya fusgeta.


*Follow my arewabooks account for more latest pages*

*Arewabooks:HUGUMA*
______________________________


*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰



32

*WASHEGARI*

Tun sanda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba kamar yadda ta saba,tana ta azkar dinta,yayin da rabi da rabi na hankalinta ke kan tunanin yadda rayuwa zata kaya mata cikin gidan.

A hankali taji idanunta suna mata nauyi,gajiyar zaman mota daga gembu zuwa gombe ya sanya bata kai ga qarasawa ba bacci yayi awon gaba da ita,ba kuma ta farka ba sai wajen qarfe tara saura na safe.

"Hasbunallahu wani'imal wakil" fa fada s sauri hamma na qwace mata,ta miqe tana linke abun sallar data tashi akai,daga nan kuma fa zarce sa bubbuge bubbugen qura duk da dakin babu abinda yayi,ta kauda abinda yake zaune ba'a kan tsari ba,daga nan ta wuce toilet kai tsaye,ta hada ruwa tayi wanka.

Sanda ta fito hudubar anty maama da yadikko matar kawu sulaiman akan tsafta da kula da kanta,duk da cewa kwatakwata qazanta ba dabi'ar ta bace.

Cikin mayukan dake jere saman madubinta ta bude wasu ta shafa,sannan ta duba makekiyar wardrobe dinta ta jikin bango.

Tsaiwa kawai tayi tana kallon tarin uban suturun da a yanzu suke mallakinta,sai takejin kamar ta zurawa rayuwa jikinta da yawa,banda haka ina ita ina wadan nan kayan da batasan ranar da zata gama sanyasu ba?,haka ta dinga dubawa har zuwa lokacin da hannunta yakai kan wata atamfa,kalarta ce ta dauki idanun maimunatu,data gwada sanyawa kuwa saita amsheta,tayi mata kyau matuqa da gaske,batayi amfani da dankwalinta ba,a maimakon hakan sai ta nema qaramin hijab ta maqala a kanta.

Bakin gado ta koma ta zauna,ta rasa abinda zatayi,sai kuma ta fada tunane tunane,abubuwan da suka faru a rayuwarta,suke ma kan faruwar,tsakiyar haka taji kamar qararrawar falon nata neman dauki,hade da knocking,tayi kamar kada ta fita,amma jin baa fasa knocking din ba ya sanyata miqewa.

Cikin nutsuwa ta fita,qafafunta suna nutsewa cikin lallausan carpet dake malale a wajen har ta iso falon ta doshi qofa,dai dai sanda yake saukowa daga samansa,sanye da wata jallabiya saqar qasar morocco,ruwan a qasa da aka yiwa ado da wani zare mai dan kauri ruwan madara,yankakken hannu gareta,don haka dukka singalalinsa dake lullube da gargasa waje yake,sumarsa tadan hargitse kadan,haka nan fuskarsa na nuna alamu na jin bacci.

Idanunsa a kanta sanda ta bude qofar yana step na qarshe,ta gane fuskar matashin saurayin dake miqo mata kwanduna dauke da fulasai masu azabar kyau

"Daga gidan dr,amma ce tace a kawo muku" sosai taji dadin karamcin amman har cikin ranta,tasa hannu ta karba tana cewa

"Kayi mata godiya,Allah ya saka da alkhairi" sai ta maida qofar ta tura ta yadda take,ta kuma waiwayo don komawa ciki ta sama musu mazauni.

Karaf idanunta ya sauka a kansa sanda yake isa gaban babban freezer dake falon tamkar ma bai ganta ba,budeta yayi ya ciro babbar gorar ruwa guda daya,gabanta ke wani irin faduwa,tsoronsa dake shaqe a zuciyarta ya motsa

"Ina kwana" ta fada bakinta yana dan rawa kadan,tana jin kamar zai mata wani mummunan abu ne,banda alamun sauti da taji da sai tace bai amsa gaisuwar tata ba,kunnuwanta na biye da takunsa sanda yake shirin komawa saman,sai tayi ta maza tace

"Ga abinci amma ta aiko dashi" shuru na wasu sakanni suka ratsa yana ci gaba da tafiyarsa,kamar bazai ce komai ba sannan tayi yace

"Madalla,an gode" yaci gaba da hayewa saman,kunnuwanta dai na biye da sautin takunsa,takun da ake yinsa cikin wani irin salo da kuma tafiya wadda jinin sarauta ke yawo a cikinta.

Sai data daina jin motsinsa sannan ta daga kanta tana duban kwandon hannunta tare dason gane me madalla da yace take nufi?,ita yanzu ya zatayi da wannan abincin?,sai ta maida dubanta ga sassan unaisa dake a rufe,zuwa zatayi ta mata magana ko kuwa ta qyaleta?,kai ta girgixa,zuciyarta tafi karkata da ta qyalesu gaba daya,don haka tayi kitchen da abincin,ta ajjiye acan,bayan ta bude ta diba iya abinda cikinta zai iya dauka,wanda duka duka cikin plate daya ta xuba komai.

Tunda ta koma daki bata sake jin motsin kowa ba,don ko data gama cin abincin sake kwanciya tayi,ita ba gwanar kallo bace bare ta dawo falonta tayi,sai bayan kusan awa biyu taji tashin mota daga farfajiyar gidan,wadda batasan ta waye ba,saidai tana kyautata zaton tame gidan ce.

Qarfe daya da ashirin na rana tana fitowa daga alwalar sallar azahar taji knocking da 'yar hayaniya,sake fitowa tayi falon,har yanzun kamar dazun dai babu kowa ba kuma motsin kowa.

Murmushi ya subuce mata sanda ta bude qofar,laila ce ita dasu hanne da hauwa,sai fa'iza da safina harda khadija,kusan dukkaninsu mutanenta ne,akwai sabo tsakaninsu sosai,abinda yasa ta sake jikinta ta kuma ji dadin zuwan nasu

"Ina fatan dai yaa ja'afar bai nan?" Fa'iza ta fada tana dan fidda idanu gami da watsa idanunta a babban falon gidan hadi da kallon stairs din,qaramin murmushi maimunatu tayi tana kada kai

"Ya fita" ta amsa musu kai tsaye,don motsin fitar motar dazun ranta yana gaya mata shine

"Na baroshi wajen amma ma fa sanda muke fitowa" safina ta fada tana zare mayafinta daga kanta

"Au to,dama wai don mufi sakewa ne" ta fadi tana dariya,ita dai maimunatu jagora ta musu zuwa sassansu,suna tafe suna gaya mata ba dadewa zasuyi ba,amma tace au dawo da wuri,kuma su hauwa da qyar idan ba anjima zasu wuce ba,zasu biya ta jalingo ne,akwai gaisuwar mutuwa da akayi da zasu fara zuwa sannan su wuce gembu.

Awa biyu kawai sukayi,amma sai taji kamar sunyi awa biyar,saboda yadda hirarsu ta dinga debe mata kewa,kowacce na qoqarin koya mata yadda zata zaun a gidan,ta kuma kama hankalin mijinta sannan ta tserewa kishiyarta,kasancewar dukansu sun girme mata,ita dai jinsu kawai take da kunne,hausawa sukace me daki shi yasan inda yake masa yoyo.

Da suka tashi tafiya sukace zasu leqa wajen unaisan su gaisa,cogewa maimunatu tayi har suka shiga suka fito,sannan tayi musu tattaki zuwa farfajiyar gidan,karon farko kenan da taga yadda harabar gidan yake,salmanu drivern abbi ne ya kawosu,tana tsaye tana binsu da kallo har suka fice daga gidan,sai ta sauke ajiyar zuciya tana jin tamkar ta bisu,cikin matuqar sanyin jiki ta dawo cikin gidan.

Tunda ta koma din bata sake jin motsin kowa ba,gaba daya gidan sai take jinsa wani iri,babu armashi babu kuma dadi,tana jin inama za'a maidata gidan abbi?,inama zaa maidata wajen anni,rayuwar can tafi mata dadi dari bisa dari.

UNAISA tun bayan tafiyar 'yan uwanta da sukazo mata bayan sallar magrib ta shiga toilet dinta ta sheqa wanka,sunyi maganganu masu tarin yawa da anty talatu,wanda ta dinga qoqarin ganin tabi kowacce shawara da umarni da anty talatun ta dorata akai.

Cikin wasu azababbun English wears ta shirya kanta, straight leg jeans da rigarsa wadda tsahonta iyakarta cinya,ta zuba turare sosai a jikinta,ta kuma wadata fuskarta da powder da lip gloss da ya qarawa lips dinta sheqi,nails polish remover ta saka ta cire tsohon nail polish din,ta sabunta da wani da yaketa glittering.

Sai data tabbatar komai yayi,ta juya gaba da baya sannan ta dauki wayarta,already tana da number dinsa,saidai bata taba gigin kira ba,ta zauna gaban dressing mirror dinta ta kara wayar a kunne sanda take ringing,tana kuma kallan fuskarta,gabanta yana dukan uku uku,don batasan da wacce fuska zai tarbi kiran nata ba.

Dai dai lokacin da yake kashingide bayan motarsa suna magana da mr husain daya daga cikin manyan ma'aikatansa,kallo daya ya yiwa wayar ya dauke kansa ya maida ga maganar da sukeyi dashi cikin ma'ajiyar motoci ta kamfanin nasa,wanda ya budewa wuta yakeson ya dawo dashi.hayyacinsa,ya kuma ci gaba da aiki fiye da yadda yakeyi a yanzu.

Al'adarsa ce haka,ba kasafai yake daga baquwar number ba,don haka da ring din ya isheshi saiya maidata silent yaci gaba da uzurin gabansa.

Da matuqar sarewa ta sauke wayar daga kunnenta,kira uku kenan bai dauka ba,sai ta yanke ta tura masa gajeran saqo kawai,don haka ta batayi qasa a gwiwa ba ta senda masa

_hello hottie,it's your wife calling you,i missed you so much today,please come back as early as possible,akwai abubuwa masu dadi dana tanadar maka....am waiting for you,urs.....unaisa_

Sanda saqon ya shigo wayar tana hannunsa yana duba wani verification code da wani company suka turo masa,zai bawa mr hussain,tsaki yaja wanda sai daya fito a fili,har sai da mr hussain ya daga kai ya kalleshi,saidai bai tambayeshi ba,shi sam yama mance dasu,tunda yasa qafa ya fice yau din duka aiki ya riqeshi,gaba daya hidimar company dinsa ne a gabansa,ko gidama da yaje amma kawai ya samu ya gaisar ya wuce,bai samu ganin abbi ba bare anni,saboda akwai sauran baqi,shi kuma bayason wannan wasan banzan da akema mutum da sunan abokan wasa.

Sai daya bawa mr hussain duk abinda zai bashin sukayi sallama sannan ya yiwa driver dinsa sign da ya shigo su tafi,sai daya tada motar suka fice a company din sannan ya tambayeshi

"where are we going sir?"

"Take me to the nearest restaurant" ya bashi amsa yana kara wayarsa a kunne,jabir ya kira,don tun dazun yaga miscalls dinsa,a sannan yayi calling urgent meeting da ma'aikatansa,daya fito kuma ya manta sai yanzu ya tuna.

Sai data kusa tsinkewa ya daga,cikin wata irin raunanniyar murya me cike da sanyi jabir din ya masa sallama,muryar data sanya ja'afar din tuno abubuwa masu yawa a shekarun baya wadanda suka shude masa,kamar shi a irin wannan lokacin da jabir din ya kirashi,da qyar ya samu ya daga,a sanda yake rayuwa da muradin zuciyarsa shaheeda.

Yayi kamar zai katse kiran,sai kuma ya dake,suka gaisa ya gaya masa uzurin da yasa ya kirashin

"Am sorry J,amma if possible please kayi postponing schedule din zuwa upper month mana,saboda ina tunanin tafiya honey moon ni da my fa'eem" wani dogon tsaki ja'afar ya sake a kunnen jabir,yana jin kamar ya raina masa wayau ne

"What nonsense are you talking about?,ina maka magana ne akan abinda ya shafi company kana min maganar honeymoon,if u r not ready to accept your vacancy shikenan fine,i can I can manage the company" daga haka ya katsr kiran cikin fusata,tamkar wani gagarumin abu jabir din ya gaya masa,yana furzar da wata zazzafar iska daga bakinsa.

Ko da yaje eatery din da drivern ya kaishi,ya kuma zaba abinda zaa kawo masan sai ya kasa ci,daga qarshe haka ya miqe ya biya abinda aka cajeshi duk da tsadar abinci a wajen ba tare daya ci wani abun kirki ba,yace su wuce gida kawai.



33

A hankali yake takawa zuwa cikin gidan,duka hannayensa cikin aljihun rigarsa,duk da yadda ya gaji amma sai daya daure ya biya ta store din gidan,ya duba kayayyakin amfanin da yace a zuba a ciki,ya tabbatar a saka komai da komai na amfanin gida na yau da kullum,sannan ya rufe,ya bulla ta qofar kitchen.

Dai dai lokacin da maimunatu ke cikin kitchen din,tana tunanin yadda za'ayi da abinciccikan da aka kawo na safe rana dana dare,tunda bai cinyu ba,daga qarshe kamar yadda taga acan gidan sunayi,saita kwashesu ta zuba a freezer.

Hannunta take daurayewa a bakin famfon dake cikin kitchen din,tana gamawa ta kashe ta juyo tana yarfe ruwan dake jiki,dai dai sanda yake fitowa daga store din,idanunsa suka sauka a kanta,cikin lausasan kayan bacci,doguwar riga baby pink da baby hijab light blue,kalar datayi masifar haskata,ta kuma fidda gewayayyar fuskarta dake nuna qarancin shekarunta,sam bata lura dashi ba,saboda idanunta yana kan hannayenta,har sai data zo gab sannan ta ankara da inuwarsa,taja baya kuwa da sauri gabanta yana faduwa,idanuwanta suka fada cikin nashi,zallar tsoron dake zuciyarta ya bayyana qarara cikin idanuwa da fuskarta.

Wani kallo yayi mata fuskar nan a dinke babu ko digon annuri,jinta tayi tamkar nutumin da zaki ya ritsa a tsakiyar jeji babu gurin kubuta,sai ta rasa me ya kamata tayi,cikin juriya da qarfin hali jajayen lips dinta suka motsa

"Sannu.....da zuwa" ta fadi a rarrabe,dauke idonsa yayi daga kan labban nata yana jan qaramin tsaki qasan ransa,yadda tayi maganar ma kawai zai gaya maka shes very young,ta yaya wai ma anni zata ce ya ajjiye kamar wannan a matsayin matar aure koda ya tashi yin auren?,wannan ba saidai a dauki buzunta ba duk sanda yace zai kaara jikinsa a nata?.

"Ungo nan" taji ya fada a maimakon amsa sannu da zuwan data yi masa,daga kai tayi a hankali tana duban abinda yake miqo matan,kafin ta saka hannu ta dauka a saman fridge din dake daura dasu,inda anan ya aje mata kafin takai ga karbar,sababbin kudi ne a daure a kyauro masu yawa,don ko da batasan adadinsu ba amma tasan cewa suna da yawa qwarai

"Idan kina da buqatar wani abu kiyi amfani dasu,banason ki nemeni,don banason damuwa da takura,take care" gyada kai tayi a hankali,sannan tace dashi sanda yake fita a kitchen din

"Allah ya saka da alkhairi" bata iya jin ya amsa ko bai amsa ba,itadai tabi bayansa itama ta fita bayan ta tabbatar yayi nesa da wajen,kudin na rungume a hannunta,saidai tana tsananin jin qyamar kudin har cikin ranta,itafa...daga randa ta ganshi yana zuqat taba shikenan kuma,bata masa kallon komai sai dan iska,mugu kuma azzalumi,biyo bayan abinda yayi mata,zuciyarta cike fal da tunanin mema zatayi da kudade haka?,me zafa buqata dasu?,da wannan tunanin ta fada dakinta ta kulle,ta isa gefan gadonta ta jawo side drawer ta jefa kudin ta mayar ta rufe.

Tunda taji motsi a sama ta tabbatar shine ya dawo,don haka ta sake duba kanta da kyau,sannan ta bude freezer dinta ta dauki sassanyan ruwa da lemo ta aza saman wani set din tray me hade da cups,ta yane kanta da wani dan yalolon mayafi,sannan ta fito.

Wani abu ya mintsini mai kama da kishi sanda idanunta suka sauka a sassan maimunatu,basu taba haduwa da yarinyar ba,basu taba gamuwa ba,ko yaya take?,tana ina yanzu oho?,taja wata qwafa kamar zata cire harshenta sanda zuciyata ta raya mata ace dai taje ta sameta tare dashi.

Har tsakiyar zuciyarta falon nasa ya tafi da ita,akwai wani yanayi na musamma tattare dashi,taci gaba da takawa a hankali ta nufi bedroom dinsa kai tsaye,saidai kuma kamar yasan wani zaya shigo masa,yana shiga kafin ya shiga wanka ya murza key,tana taba handle din ta gane hakan,dole ta koma saman kujerun alfarma dake falon,ta zauna ta dora qafa daya saman daya bayan ta kunna tafkekiyar tv dake falon,takuma canza tasha zuwa mbc Bollywood,ta samu kuwa suna wani film me kyau,saita maida hankalinta a kai,yayin da wani sashe na zuciyarta kuma yaketa wassafa mata yadda zai tarbeta,duk da tasa a ranta ba zata samu tarba me kyau dari bisa dari ba.

Cikin jallabiyya Morocco's male abaya me ruwan gold mai gajera hannu ya shirya bayan ya fito daga wankan,duk da baici abinci ba amma sam baya jin yunwa,muryar amna yakeson ji,yayin da wani sashe na zuciyarsa kuma a yau yake cike da kewar shaheedansa,ya feshe jikinsa da lallausan turaransa bayan ya gama gyara sumarsa dake samun gyara na musamman,ya dauki wayarsa ya danna kiran number ammansa.

Bugu biyu aka daga,salma ce,ta shaida masa amman tana wajen abbi,sai ya nema ta hadashi da amna,ta kuwa hadasun,yarinyar ta dinga masa hira sosai,abinda yasa ya samu relief daga abinda yakeji kenan,yadan sake shima yana tayata.

Ya kusa minti talatin tare da ita,ya samu sauqi sosai cikin ransa,harma ya samu qwarin gwiwan jin son shan coffee,don haka ya diba takardun da zai duba da system dinsa ya nufi falon.

Janye idanunta tayi daga fuskar tv din tana sakin murmushi,jarumin film din yana mata mugun yanayi da J dinta,yadda ya iya soyayya ta tabbatar J zai iya finsa,saidai shawo kansa da qwato hankalinsa abune mai wahala ta sani kuma,dai dai sanda take shirin sake maida idanunta ga film din,sai suka sauka ga babban hoton shaheeda dake rataye cikin falon,zuba ma kyakkyawar fuskarta idanu tayi,murmushin da take a cikin hoton tajiyana tabata,sake waiwaya tayi wani sashe still hotonta ne ita da twins dinta amna da amra,daga daha bangaren kuma shi da ita ne,sunyi masifar kyau cikin qananun kaya,karon farko data fara ganin wani abu me kama da murmushi saman fuskarsa,yana rungume da ita ta baya,da gani ba'a qasar nan aka dauko hoton ba,yana sanye da uniform da matuqan jirgin sama,kyau iya kyau yayishi,uniform din sun karbeshi matuqa da gaske,hoton ya fusgi hankalinta,ya kuma saka kishin shaheeda mai yawa cikin ranta,har sai data miqe ta isa ga hoton dake can wani kusurwa na falon,ta tsaya a gabansa tana sake qare musu kallo.

Da farko daya fito bai lura da ita ba,sai daya kusa isa inda ya ajjiye na'urar hada coffe dinsa take,yadan tsaya kadan,kamar zai magana sai ya fasa,ya isa inda coffee maker din yake,ya soma hada abinsa,saidai abun mamakin har ya hada ya dawo ya zauna saman kujera bata ankara da wanzuwarsa,abunda yayi masifar bashi haushi,saidai zaiga iya gudun ruwanta da nata qwaqwqwafin da kuma sanya idon.

Hannu ta sanya zata daga hoton don ganin date din jiki sosai

"Don't dare touch it" ya fada da kakkausar muryar data ankarar da ita yana wajen,tadan zabura kadan tana juyowa,idanunta suka sauka

4 Comments On GURBIN IDO
avatar
salima

2 years ago

Reply

Nice story

avatar
ibrahim-6-8

1 year ago

Reply

That's so amazing

avatar
zee-zakariyya-umar

3 months ago

Reply

I want to download the books please

avatar
zee-zakariyya-umar

3 months ago

Reply

I want to download the books please

Please Login or Register in order to submit comment