Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bana wasaba, she just wish tasan baban ta, dudda bata sanshi ba tasan Ammi was just the best wife he could have ever had, tanada kirki, gashi ta iya girki, ta iya kula da lura da yara, Ammi is everthing to her, she just wish zata sami second Dad dat will take care of her Ammi, ajiye jakanta tayi ahankali abakin kofa ta cire hijabin ta ta wurga afalo, sadaf sadaf ta shiga yin tafiya, ko kadan bataji shigowan Aneesa kitchen dinba dan hankalin ta yay nisa kawai jitayi an rungumeta tabaya. "oyoyo Ammi na" ajiyan zuciya Ammi tasauke tana murmushi cikeda so tana shafa hannayen Aneesan datai wrapping around her chest, ahankali tace "harkin dawo Aneesa, banmaji shigowan kiba" dago kanta tayi tana leka fuskar Ammi tace "yanzu nadawo Ammi, tashi nakarasa tuka tuwon inya salala na kwashe" girgiza kai Ammi tayi tana dauko mara daga cikin ruwan dake gefenta tace "a'a kibarshi keda kika daga wurin aiki kin gaji, ga ruwanki nan dauka kije kiyi wanka ki sa kaya marasa nauyi, jeki cire kayan kizo kijuye ruwan" gyadama Ammi kai tayi tajuya ahankali tawuce tsayawa tayi tadau jakanta dake bakin kofa sanan ta shiga daki, dakinta tawuce ta shiga, zama tayi akan gado tai shiru ko kadan batajin dadin komi gatanan ne kawai, jakanta tabude taciro wayarta tsayawa tayi tana kallon wayan kafin ahankali ta danna side button din wayan ya kunnu, tsayawa kallon wayan tayi tarasa mesa hakanan saitaji wani iri dataga batada miss call kodaya, kwanciya tayi akan gado ta ajiye wayan tareda lumshe ido wani bacci mai shegen dadi ne yay awon gaba da ita.


Shirun da Ammi taji batazo tajuye ruwan ba yasa ta kwala mata kira. "Aneesah" kwafa Ammi tayi tana daukan wata yar roba da bushashen kubewa keciki dan ta kada miya tace "hala tana chan tana daddanna wanan wayan dake dauke mata hankali" kwafa tasake yi takwala mata kira akaro na biyu. "Aneesah" shiru bata amsa ba, cigaba da aikinta Ammi tayi har aka shiga kiraye kirayen magrib, sauke komi tayi ta tattare kitchen din ta zuba na Aneesa a kwano tabarshi nan kitchen tafito ta dau buta ta zaga sanan tafito ta tsugunna tai alwala, tashi tayi ta shiga kitchen din tadauko kwanon tuwon Aneesan tafito dashi tawuce daki ajiye kwanon tayi a kasa tadau dadduma tana shimfidawa tace "kika bari na idar da salla na shigo dakin nan bakifito bako Aneesa sai jikin ki ya gayamiki" hijabin ta tadauka tazura ta kabbara salla, ganin ta sallame Aneesa bata fitoba yasa ta tashi tadau wayarta tana kunna tocula dan babu wuta tawuce dakin Aneesan, labule ta yaye ta shiga dakin tana haska fuskarta tabude baki zatai magana ganin tana bacci yasa tai shiru tareda sauke ajiyan zuciya bakaramin tausayi tabata ba ganin yanda ta kwanta kasan tagaji azaune ta kwanta kafafun ta duka na kasa sai kanta kwance kan gado, karasawa gaban gadon tayi ta zauna gefenta hannun ta takai kan wuyanta zafin dataji yasa tai tapping ta da sauri. "Aneesah, Aneesah" bude ido tayi ahankali cikin nauyayyan bacci ta kalli Ammi, da sauri Ammi takamo kafadunta ta dagata tace "tashi daga baccin nan, bana hanaki baccin mangariba ba babu kyau fa yana saukar da zazzabi, tashi kije kiyi wankan" Ammi tai maganan tana mikar da ita tsaye, tashi tayi ahankali gabaki daya batada karfi, ganin haka yasa Ammi tazage mata zip din bayan rigan ta taja zanin wankan ta daga kofar sip dinta ta taba ahankali ta karba tana kallon Ammi, cikeda dan damuwa Ammi tace "cire kayan kizo kiyi wankan bari naje na hada miki ruwan" gyadama Ammi kai tayi Ammi ta ijiye mata toculan akan gado dan taga haske tawuce tafita daga dakin tai kitchen ta hada mata ruwan wankan takai mata bayi tafito ta shigo dakin dakin nata ta shiga azaune taganta kan gado daure da zanin a kirji, zama Ammi tayi kusada ita tana sake tattaba wuyanta da hannu tace "bakida lafiya ne?" murya chan kasa tace "kaina keciwo Ammi" "sannu, muje kiyi wankan kizo kici abinci saina baki paracetamol" gyadama Ammi kai tayi, Ammi ta mike tsaye tareda dagota ganin batada karfi suka fito har gaban bayi takaita tace "shiga kiyi, na ijiye miki tocula aciki" gyadama Ammi kai tayi tawuce ta shiga tana tafiya ahankali damuwa sosai Ammi ta shiga saikuma ta daure da sauri tawuce dakinta dan nemo kwalin paracetamol din datake dashi, dakin ta shiga ta tsugunna ta jawo drawer ta ciro wani kwalin paracetamol ta tabude taciro kati daya sanan tafito daga dakin ajiyewa tayi kusada abincin ta sanan tafito danta dubata, kujera taja ta zauna agaban kitchen tana jiranta tafito daga bayin, shirun dataji batajin karan zuban ruwa almost 1 minutes yasa taji tadamu, tashi tayi taje gaban bayin knocking kofar bayin tayi tace "Aneesa wankan kike kome naji shiru" "A.....Amm...." muryan Aneesa dataji chan kasa na breaking sosai tana kiranta yasa Ammi ta tura kofan a rude ta shiga, Aneesa datagani kwance a kasan bayi kaman ma tafadi ne jikinta na rawan sanyi sosai duk kumfan sabulu jikinta tana kokarin tashi takasa yasa tama manta bayi take tsabagen rudewa tasaki salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un, Aneesa" tai maganan tana tsugunnawa agurguje ta dagota a tsorace bama ta damu da abinda ke jikinta ba tasata ajikinta ganin yanda jikinta ke rawa, tace "Aneesa, ke Aneesa menene eh?" kasa magana Aneesa tayi sai jikinta dake dake masifaffen rawan sanyi idanunta na kukkulewa, ganin haka yasa Ammi tarike ta gam da hannu daya ta sa dayan hanunta a bucket din tadebo ruwan wankan ta watsa mata ajiki ta ijiye tasaba sabulu a soso jikinta na rawa ta shiga wanke mata jikin gabaki daya dan tafadi abayi sai rawa jikinta yake da ace zata saketa da zubewa zata sakeyi akasa, agurguje Ammi ta wanketa ta daura ye jikin nata tana rike da ita tasa dayan hanunta taja zanin ta dake kan kofan bayi ta daura mata ta kwance kallabin kanta tayafa mata tundaga kai har kirji ganin sanyi takeji tarikota gam tabude kofa suka fito, daki ta shiga da ita tawuce dakinta da ita akan gado tazaunar da ita da sauri tai sip ta jawo daya daga cikin dogayen rigunan ta zuwa tayi ta dagata a inda take rawan sanyi tace "sannu kinji, sa rigan" saka mata rigan tayi tacire zanin tayar sanan ta kwantae da ita taja bargon kan gadon tarufa mata, tawuce dakinta da gudu tadauko wani bargo takara mata amma dudda haka rawan sanyin take, fita Ammi tayi da sauri tadauko paracetamol da ruwa ta shigo ta zauna gefenta dagota tayi tace "sannu, sha magani" paracetamol guda biyu ta ballo tasa mata abaki tabata ruwa da sauri ta sha jikinta narawa tasake kwanciya tana nishi. "Aaa...m" da sauri Ammi ta tsugunna tana shafa kanta tace "sannu Aneesa, zazzabin yamma ya sauka akan ki, baccin magriba babu kyau" tashi Ammi tayi tarufo window dakinta ganin sanyin yaki sanan ta zauna tana shafa kanta tana kallonta hawaye nata ruwa a idanunta. Sai wajajen tara sanan taga rawan sanyin yaragu tafara sauke ajiyan zuciya ahankali bacci yasake dauketa jikinta zafi sosai, tagumi Ammi tabuga tana kallonta takai kusan 2min ahaka sanan tawuce tadauro alwala dadduma da hijabin nata tadauko tadawo dakin Aneesan ta shimfida tayi sanan tai shafa'i da wuturi bayan ta idar tabuga uban tagumi tana kallon Aneesan dake sauke ajiyan zuciya ahankali, bataso ta tasheta dan batasan kozata tashi da rawan sanyin ba amma kuma tanaso ta tadata taci abinci, abinci ma na rage rashin lafiya, tafi awa daya zaune tana kallonta kafin dan gyangyadi yay gaba da ita.




Not edited.

_IN kika karanta baki biyaba Allah ya isa, in kinason karanta littafin nan kiyi subscribing just 300_

Yunkurin amai da Ammi taji yasa tabude ido daga dan baccin daya saceta da sauri tana kiran sunan Allah. "Bismillahi" tajuya tana kallon Aneesa dake kwance yanda tabarta tana yunkurin amai sosai amma babu abinda ke fitowa, kan gadon Ammi tahau ta dagota da sauri zafin jikinta dataji saida yasa Ammi taji tsoro jikinta yafi wuta zafi. "innalillahi, Aneesa, Aneesa menene meke miki ciwo eh? Fadamin" Ammi tai maganan tana shafa fuskarta tana rungumota jikinta, kasa magana tayi sai nishi datake sama sama kaman wacce ke shirin mutuwa bamata gane me Ammi kecewa, yunkurin amai tasake yi hakan yasa Ammi tace "babu komi acikin ki, sannu nahada miki kayan shayi kisha bazan baki tuwoba kinji, nahada miki tea? Kokuma nafita waje nasamo yaro yasiyo miki tsire da fanta?" Ammi ta tambayeta cike da damuwa tana dago kanta, jini taga yana fitowa daga hancinta idanunta na kafewa alamun tasamu. "innalillahi!" Ammi tabuga uban salati mai kama da ihu cikeda tashin hankali, saikuma ta shiga jijjigata tana kiran sunanta. "Aneesa, Fateema" ganin bata motsi yasa Ammi ta shiga kalle kalle cup din ruwan data kawo mata dazu ta dauka ta debi ruwan ta yayyafa mata a fuska tace "tashi tashi kinji bari naje na kira Abdul mai keke yakaimu asibiti" nishi tayi tabude ido ahankali hakan yasa Ammi tai cupping face dinta takirata dukta rude tace "Aneesa na, karki kara rufe ido kinji bari na kira mai keke nakaiki asibiti kinji, ina zuwa" tadau wayan Aneesan data gani agefen gado tana kunna tourch tawuce tafita hartana bugewa da kofa ta kunna haske, sillipas tasaka tawuce zaure tafita tabude kofa tafita daga gidan ganin babu mahaluki kodaya a anguwan su yasa ta kalli wayan Aneesan da sauri sha biyun dare tagani harda minti uku, hannu tadaura kan bakinta ta taushe kukan dake shirin zuwan mata ta kalli cikin gidan nasu yanzu yazatayi? Yarta mara lafiya zata bari ita kadai cikin ciwo da wanan tsakar gidan kokuma she should go ahead ta dandara gidansu Abdul mai keke ne? Hawayen daya zubo mata ta share da sauri tarufo kofar gidan nasu tareda tofa ma kofar gidan bismillah ta shiga haskawa tana tafiya da sauri danba wuta har gidansu Abdul tsayawa tayi tana bubbuga kofar gidan tana kiran su. "maman Abdul, salamu Alaykum, Maman Abdul, Abdul, Abdul" ta shiga kwalama mutanen gidan kira tana ihu, takai kusan minti bayar sanan taji kara kaman an bude kofa daga cikin gidan akace "waye da tsakar daren nan?" muryan ta narawa sosai tace "maman Abdul nice, maman Aneesa ce, dan Allah kutaimaka min Aneesa batada lafiya, Abdul zakidan tasomin yazo yakaimu asibitin General" bude kofa maman Abdul tayi tana haska fuskan Ammi da tocula tace "subhanallahi, aiko Abdul bayanan, kumama ai yadena parking keke agida agarejin su yake parking kinsan wacce yakema aiki da keken tace ya dinga parkin agareji, ya jikin nata" hijabi Ammi tadaura kan fuskarta tana kokarin hana hawayen dake shirin zubowa waje, dafa ta Maman Aisha tayi cikeda tausayinta tace "kiyakuri maman Aneesa ciwon da ba dadi sam wlh, gashi khalili na kyanda dana rakaki bakin titi munsamo abin hawa, babansu kuma kinsan baidawo daga tafiyaba, kiyakuri kinji ki dandara bakin titi kisamo abin hawa Allah yabata lpy, kiyakuri" Maman Abdul tai maganan tana zare hannun Ammi daga fuskarta, gyada mata kai Ammi tayi tajuya da sauri tai hanyar titi tana goge kwalla tana addu'a Allah ya tsare mata Aneesan ta. Abakin titin ta tsaya babu wasu motoci sai tsirarru dasuke gittawa aguje, hawaye Ammi ta shiga share wa uncontrollably sai kallon agogo take yanzu karfe sha biyu da rabi, minti a shirin da bakwai kenan databar Aneesa ita kadai agida, ganin wani mota na zuwa da gudu tasan shima zai iya cewa bazai tsayaba yasa yafada titi tana kuka sosai dataji yazomata kawai dan hankalin ta a mugun tashe yake tana dagama motan hannu alamun motar ta tsaya.



Bodyguard din Dady ne dake tuki ya kalli dayan bodyguard din dake gefenshi yace "who is that woman? Get your gun" da sauri Dady dake bayan mota yana daddanna laptop idanunshi sanye da medicated glass jin suna magana get the gun yasa yadago kai, idanunshi ne suka sauka kan matar daya hango kan titi tana kuka sosai tana musu alamun su tsaya, ganin bodyguard din yakara gudu sosai yana shirin ya kwashe ta yasa yace "slow down Jeff, slow down" da sauri yace "what if is a trap sir" cikin fushi Dady yana kallon fuskan Ammi yace "slow down, Allah shine ke kare kowa, slow down let's listen to wat she have to say, most time inna biyo ta Sulejan nan haka nake ganin mutane alot of them are the poors talakawa basuci abinci bane, let's listen if is help we can offer then we help her" Dady yay maganan yana kallon Ammi still, rage gudun bodyguard din yayi har suka iso inda Ammi take da sauri Ammi ta zagayo tana kwan kwasa glass din motar.


_Duk wacce ta karanta min littafi batare data biyaba ban yafeba wlh, saikin biyani a lahira__*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



2️⃣2️⃣




Tana share hawayen dake zubowa daga idanunta da hijabi tana leka motar ta glass duk arude tace "hello, hello, salama alaykum, dan Allah taimaka min za'ayi, dan Allah taimako nake nema, y'ata batada lafiya tana gida unconscious, please kutaimaka ma Y'ata asibiti zaku kaimu" Ammi tai maganan tana sake share hawayen dake zubowa, kallon bodyguard din Dady yayi bayan sun gamajin maganganun da Ammi takeyi yace "wind down" saukar da glass din kasa bodyguard din yayi Ammi tayi tana tsaye wajen mazaunin driver ganin bodyguard sunci bakaken suit da bakin glass, idanu Ammi tadan zaro tabude baki zatai magana bodyguard din yamata pointing baya da hannu yace "talk to my boss" gyadamai kai Ammi tayi arude takoma tabaya, hada ido sukayi da Dady dan wutar cikin motan a kunne yake, da bayan hannu ta goge fuskarta daya kara jikewa da hawaye tace "dan Allah ka taimaka min y'ata batada lpy, tana gida nabarta ita kadai, please dan girman Allah kutaimakamin karta mutu she's my only daughter ita kadai gareni dan Allah kutaimakamin, dan Allah, dan Allah" yanda jikinta ke rawa hawaye na bulbulowa daga idanunta tana sharewa yasa Dady yaji ta bala'in bashi tausayi, he just relate to her condition he just can't imagine yaga Aliyu na ciwo yana ganin rudewan shi saiyafi nata times 8, dan ajiyan zuciya ya fuxar ya kalleta yace "ina ne gidan naku?" da sauri Ammi tamai pointing layinsu tace "wanan layin ne" dan jim Dady yayi yana tunani hakan yasa Ammi tace "wlh da gaske nake ba amanan ka zanci ba, trust me my girl is dying please, dan Allah" ajiyan zuciya Dady yasake saukewa yace "alright I trust you karkici amana, shigo cikin motan" gyadamai kai Ammi tayi bata damuba dan matsalan datake ciki yafi komi ta shiga motar Dady ya matsa dayan gefen itakuma ta zauna kusada kofa tarufo kofan, Dady ya kalli gaban motan yace "let's go" ya kalli Ammi yace "nuna musu gidan" gyadamai kai tayi ta nuna musu layinsu suka shiga har zuwa kofar gidan nasu, akai parking da sauri ta sauka daga motan ta shiga gidan da sauri tana kunna torchlight din wayan Aneesan dake hanunta, dakin Aneesan ta shiga da sauri ganin Aneesan kwance akasa tana convulsing sosai ga nose dinta na bleeding yasa tai wajen da sauri ta dago kanta tana girgizawa ta kurma uban ihu. "Aneesa, Aneesa, ke Fateema haka zakimin eh? Barina zakiyi kaman babanki eh Aneesa, please don't leave me baby girl ke kadai gareni a duniyan nan, banda iyaye banda yan uwa, u are my everything Aneesa, wayyo Allah! Jama'a" Ammi tasake kurma uban ihu not knowing what to do, bama tasan metake ba.





Kallon cikin gidan Dady yayi da Ammi ta bari abude jin ihun Ammi yanadan girgiza kafa, sakejin ihun Ammi akaro nabiyu yasa yabude kofa zai fita da sauri bodyguards dinshi suka fito sukace "is not safe sir, let's go in first" baima tsaya sauraron su ba yashiga gidan ya shiga falon straight yana haska wayanshi cikeda damuwa, da sauri ya shiga dakin Aneesan dayake jin kuka sosai ya yaye labule, ganin yanda Ammi ta rike fuskar Aneesa dake convulsing sosai tana shushure kafa kaman zata mutu yasa ya shiga da sauri bodyguards dinshi biyeda shi yace "subhanallahi" tsugunna wa gaban Ammi yayi yakai hannu shi yataba wuyan Aneesa da sauri yadaga kai ya kalli bodyguards dinshi yace "get me a cold water she's running serious temperature that's why she's convulsing haka" yamikama Ammi dake kuka sosai hannu yace "lemme have her, bani ita nan" ganin Ammi bama tagane meyake cewaba yasa yasa hanunshi ya karbi Aneesan yasa finger shi yana bubbuga kumatun ta kozata dawo normal, daidai lokacin bodyguards din suka shigo da katon bucket da ruwan sanyi suka ajiye kusada shi ya kalli kofan su ya nunama bodyguard din yace "give me that wrapper" zarowa sukayi suka bashi karba yayi yay dipping zanin cikin ruwa gabaki dayanshi yaciro ya daura mata akan fuska ya kalli Ammi data rude yace "don't worry your daughter will be fine" gyadamai kai tayi tana share hawaye takama hannun Aneesan tarike gam tana kiran sunanta. "Aneesa, Aneesa tashi gani nan, kinji ga Ammin ki, bude idonki kigani" ganin bata dena convulsing dinba yasa Ammi tafashe da kuka sosai ta matse hanunta data rike gam tace "dan Allah karki barni Aneesa ke kadai gareni, banda kowa, I don't wanna be alone, kece nake gani kullum naji dadi, Fateema karki tafi ki barni kaman mahaifinki kinji" tafashe da kuka, tsayawa kallonta Dady yayi yanda take kuka sosai tanama yarinyar maganganun, ahankali ya ijiye zanin yasa hanunshi yadebo ruwan a hanunshi yay bismillah ya shafa mata a fuska yana goge jinin hancin nata yana tapping fuska, jin Ammi takirata da Aneesa yasa ahankali yace "Aneesah, Aneesah, ga mamanki nan nakiranki bude idanunki kiganta" ahankali ta shiga rage motsin hartazo tadena convulsing din saida sauke ajiyan zuciyan datake yi da karfi da karfi kaman ma da kyar take kamo numfashi, numfashinta namata wuya, ganin tarage yasa ya kalli Ammi dahar lokacin take goge kwalla yace "bani hulanta mutafi asibitin" da sauri Ammi tamike tsaye tadauko hulanta data rataya akan kofar sip takawo da sauri, karba Dady yayi yasama Aneesan hulan Ammi tamiko hannu takarbeta shima yatayata suka fita da ita daga dakin bodyguards biye dasu har waje, abayan mota aka zaunar da ita Ammi tace "ina zuwa" cikin gida takoma da sauri ta shiga dakinta kudadden Aneesan da aka biyata a lallen datayi na bikin nan ta dauko tadau jaka ta chusa ciki sanan tadauko makulli tafito da sauri ta kulle gidan da kwado sanan ta shiga motan tarufe kofan tana shashafa kan Aneesan dakeda mugun zafi gatanan ne kawai batamasan inda kanta yakeba, jikinta kaman garwashin wuta.






Wani babban private asibiti Dady yasa aka kaisu anan cikin Abuja dan Suleja babu wani asibitin kirki, suna parking kafin kaceme ma'aikatan sun gunguro gado suka cirota daga mota akai ciki da ita da sauri Ammi har zuwa gaban dakin daza'a shiga da ita aka shiga da ita zata bisu ciki a rude Dr yace "sorry Ma, don't worry your daughter will be fine" ya kalli wata nurse yace "give madam water and sit let her calm down" yawuce ya shiga ciki tareda rufo kofa, tsayawa Ammi tayi jikin kofan tana lekawa duk jikinta na rawa ganin ana janyo oxygen ana makalama Aneesan yasa ta daura hanunta abaki tarufe bakinta kuka na zuwan mata hawaye ya shiga fitowa, memory ranan da baban Aneesa ya rasu yadawo mata fresh dan shima haka aka makalamai oxygen dan he was finding it difficult to breath, hanunta tadaura akan glass din kofar arude tace "no Aneesa don't leave me kinji dan Allah, babanki yabarni please karki barni Kinji Fateema please" Ammi tai wani irin breaking down da kuka, Dady da tuntuni yake tsaye agaban receptionist yana son yamusu clearing bills dan yasan basuda wani karfi sosai ya tsaya chak yana kallon Ammi data bala'in burgeshi he so much sees kanshi in her, yadade rabonshi dayaga mahaifiya dake nunama yaranta so haka karara, jibi dai matan shi har uku, barin ma Kareema jitake kaman ta kashe Rauda kaman ba ita tahaife taba, shi wani irin mutum ne dayake bala'in so yaga mata na nunama yaransu so karara agaban kowa, saisa yakasa mantawa da Maman Aliyu yar baturiyan shi, yanda Ammi ke magana yasa yaji ta masifar burgeshi sanan ta bala'in bashi tausayi. Wani paper receptionist din ke mikomai ya daga mata hannu yace "wait am coming" ahankali yataka yakarasa har inda Ammi ke tsaye tana kuka, kallon dakin yayi yaga yanda aka sama Aneesan oxygen ana bata taimakon gaggawa, ahankali yace "karki damu Allah zai tashi kafadar Aneesa bazata mutu ba, kidena kira mata mutuwa kimata addu'a ne banji kinmata addu'a ba tun dazu" da sauri Ammi tadago jajayen idanunta ta kalli Dady kaman wacce batasan metake cewaba tace "addu'a?" gyadamata kai Dady yayi yace "kinga zomuje chan ga kujeru nan kizauna akawo miki ruwa kisha ki kwantar da hankalin ki kimata addu'a, kin zaci idan ta farka yanzu taganki ahaka idanunki sunyi jajir zataji dadi ne?" da sauri Ammi ta girgiza mai kai hakan yasa yadanyi murmushi aranshi yace kibace kawai amma batada wasu shekarun kirki, ahankali yace "muje kizauna" yay gaba, ahankali ta daga kafa tabishi abaya kujeran daya nuna mata ta zauna daidai lokacin Nurse ta fito da ruwa mai sanyi na gora takawo mata karba Dady yayi yana budewa yace "yauwa kingani ga ruwan to kisha" yamika mata Goran karba tayi tadan kurbi kadan tareda sauke ajiyan zuciya tana sake goge fuskarta da bayan hannu ganin haka yasa Dady yakoma wurin receptionist din sabida ba'a riga an gama mata treatment ba yasa basusan nawa zasu chajeshi ba, dubu dari yasa bodyguard yadauko daga mota ya ijiye musu yace abasu kome suke bukata zai dawo gobe da safe sanan yajuya zai koma wajen Ammi daidai lokacin Dr yabude dakin da Aneesan ke ciki ya fito da sauri Dady yay wurin Dr ya mikamai hannu, murmushi Dr yayi yadan duka yace "sir kaine da kanka, please let's go to my office anbarka a tsaye" girgiza kai Dady yayi yace "noo don't worry am actually about to leave ma, ya jikin Y'ata? How's her condition now?" daidai lokacin Ammi ta iso wajen kalman Y'ata da Dady yafadi yasa taji her heart was heavy, ahankali tadan kalli fuskar Dady dabaima lura da zuwanta ba yana kallon Dr, anatse Dr yace "for now we've manage to stabilize her condition, andau sample of her blood we will run some test dan munsan meya jawo mata ciwo haka" gyadakai Dady yayi yace "alright thank you Dr, please ka kula da ita sosai kome kuke bukata just let me know, am coming in the morning to check up on them, need to hurry up nima d'ana bai waniji dadi ba yasami bruises a hanunshi".






Da sauri Dr yace "hope is not serious" girgixa kai Dady yayi yace "ahhh nothing much, anyway can she see her ko hankalin mahaifiyarta ya kwanta?" Dady yay maganan yana juyawa dan yakira Ammi tazo taga Aneesa, hada ido sukayi da Ammi dake tsaye abayanshi tana wani irin kallonshi, dan murmushi Dady yayi yace "karki kara kuka Aneesa ma kaman ta warke kinajina, yanzu muje ki ganta, ai Dr she can see her ko?" dan dariya Dr yayi yace "yes sir" murmushi Dady yayi yace "muje to" har gaban kofan yaje yabude mata kofa yana kallon Aneesan dake bacci yace "karki tadata she needs this sleep nizan tafi gida" zama tayi ahankali kan kujera ta kalli Dady tace "Allah ya saka maka da alkhairi, Allah kuma ya taimakeki adukkan Al amuranka, Allah yabiya maka bukatun ka na alkhairi, nagode sosai Alhaji" washe baki Dady yayi ya bala'in jin dadin addu"o"in ta, shidai arayuwan shi yana bala'in son appreciative woman wacce bakamata wani abun kirki ba amma inta fara maka godiya saikajika on top of the world, wani sassanyar murmushi yasaki tareda dan dauke

Please Login or Register in order to submit comment