Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shiga ci, dariya Abdul ya shiga yi yace "nadaiji shege waya gayama anama abinci yanga" yay maganan yana daukan wani spoon suka shiga ci tare, he hardly eat much but because yanaci tareda wani sosai yaci abincin har Abdul na karamusu sukaci, baiwani ci pepper chicken din sosai ba yazuba juice ya kwankwada shikuma Abdul yaci tass, saida suka gama yace "this fruit kasasu a fridge Leo ni banda inda zasu shiga acikina while I clear the dining" gyadamai kai yayi yatashi ya dai bowls din yakai fridge shikuma Abdul ya kwashi plate yakai kitchen.

Gamawa sukayi sukai falo Abdul yadau jakunkunan kayan su yace "kaga kayanmu gobe zamu fita dawuri fa, mune abokan ango" tabe baki yayi yadan shafa kai yace "am sleepy sosai bangane mekake cewa, let's go to bed" waya Abdul yadauka yana gyara kwanciya kan kujera yace "kai kaje ni waya zanyi da" ya kashemai ido, tsaki Aliyu yayi yay hanyar bedroom yace "dan iska aikin kenan soyayya" daga murya Abdul yayi yace "bari kafara naka bazaka bari muhuta ba, kardai kazo kana mana kuka idan tace bata sonka" daga murya yayi daga bedroom yace "never" shima daga murya Abdul yayi daga falo yace "is a bet" tsaki Aliyu yaja yana cire rigan jikinshi yace "rubbish, why will I ever cry over soyayya? Allah kyauta" yatabe baki ya shiga bathroom yana tafiya da kyar so yake yay wanka yazo yay bacci.
Asuba tagari!!!!






_Suleja_
Shigowa dakin tayi tana gyara tsintsiyan laushin dake hanunta tana satan kallon Ammi, harara Ammi ta watsa mata tace "wai lafiya kike kallona haka?" dakin Ammi ta shiga da sauri ta ijiye tsintsiyan tafara gyara gadon saida tagama tsaf sanan ta sharo dakin tafito da sharan ta shiga dakinta ta sharoshi shima sanan tafara sharan falon Ammi sai hararanta take dan tai mata laifi tunda tai sabon wayan nan da Baffa yakawo mata take uban danne danne awayan data rasa nameme, tarasa uban me take dannawa awayan dababu komi aciki, dasafen nan ma daga ta dumama abincin kari saida taji kauri koda tafito taje kitchen abincin ya kone ga Aneesa agefe agaban murhun kan kujera tana daddanna waya bamata saniba tsabagen nisan datayi shine ta zuba mata dunddu ta karbe wayan har yanzu bata bataba saisa taketa satan kallonta tanaso ta roketa tabata amma bataga fuskar hakanba, karasa share falon tayi ta fitar da sharan tsakar gida sanan tawuce kitchen ta debo rushi ta dawo falon ta zuba turaren wuta ta shigar dasu dakunan kafin tafito da turaren wutan ta ijiye a tsakar falon tawuce tafita tsakar gidan, tsintsiyan kwakwa tadauka tana gyarawa ta shiga share tsakar gidan tana tafiya zaure dasu bude kofar gidansu da akayi yasa ta dago daga sharan da sauri wata farar yarinya ce doguwa tadan yafa dan ficicin gyale ta shigo tsayawa Aneesa tayi turus tana kallonta murmushi yarinyar tayi tace "yakuri hala na tsorataki dan Allah tambaya nake wlh tun safe muke garari a Suleja nan mun kasa gane gidan dan Allah nanne gidansu Aneesa mai lalle?" jin gidansu ake nema yasa ta gyadamata kai tana murmushi tace "nanne" wani irin ajiyan zuciya yarinyar ta sauke tana shafa kirjinta tace "Wai Alhamdulillah laaaa koma kece Aneesa mai lallen?" dan murmushi tamata tace "eh, nice" da sauri yarinyar tabude kofar gidan wani babban motane pake a kofar gidan nasu ihu tayi dagangan zauren tace "Anty nanne gidan, gama Aneesa mai lallen nan" bude kofar bayan motan akayi wata budurwa fara itama wacce tafi ta zauren tsawo da dan kiba tafito kana ganinsu kasan Ya da kanwa ne tana rike da wani hadadden designers bag na Charles and Keith da sallama ta shigo zaure. "Assalamu Alaykum" daga kai Aneesa tayi tace "wa alaykumus salam, ina kwana" tagaidata ganin babba ce, murmushi budurwan tayi tace "lafiya lau Aneesa, ashe kece mai lallen kinga wuyan damukasha kafin mugano gidanku kuwa" dan murmushi Aneesa tayi dake karama fuskanta wani irin siriintaccen kyau tace "lalle kukazo ne?" atare ya da kanwar sukace "eh lalle mukazo" "to kushigo, bari na shimfida muku tabarma ku zauna saina hada lallen mufara" da sauri yayar tace "a'a munzo daukan kine home service mukeso bamu kadai zamuyiba duk yan uwanmu na gida, tundaga Abuja aka mana kwatancen gidanku akace mana u are one of the best masuyin lalle in the whole Abuja, please home service mukeso yau za'a fara events din bikina wushe wushe za'ayi da daddare shine zakimana lalle" dan zaro ido tayi ganin yanda macen ke magana ayangance zaka gane irin yaran manyan nanne yan gayu, wasa da yatsan ta tashiga yi tace "banayin home service kuyakuri duk maison lalle a gida nakemai" daga yar har kanwar yisukayi kaman zasuyi mata kuka ahankali yayar tace "dan Allah Aneesa karkimin haka kekadai ne hope dina yau dinan am so stress out, bansan kan Abuja sosai ba hutu school kawai kedawo dani daga abroad saikuma wanan bikin nawa da za'ayi, ta ina zan nemo wata me lalle dazata bini gida tamana, dan Allah Aneesa mai lalli help me kinji sister" sosai tabama Aneesa tausayi kana ganinta kasan tagaji kam ahankali tace "to shikenan amma kuzo kufadama Ammi na, inta yarda saina biku" da sauri amaryan tace "to muje" ajiye tsintsiyan Aneesa tayi tana gyara hulan kanta dafa yau taso tai tsifa taje kitso dan gashin kanta ya tsufa amma kuma gamasu lalle sunzo, bude labulen falonsu tayi ta shiga falon da sallama suna biye da ita har gaban Ammi taje tace "Ammi gabaki nan sunce nabisu wai namusu lalle home service nace ni bana zuwa home service sunce dan Allah shine nace bari na kawo su wurinki" zama take shirin yi kusada Ammi tace "wuce kije ki karasa sharan ki" gyadamata kai tayi tafice daga dakin Ammi ta dubesu atare dukansu sukace "ina kwana Mama" cike da fara'a Ammi tace "lpy lau sannunku da zuwa" cikeda girmama amaryan tace "dan Allah Mama so muke Aneesa tabimu tamana nida dangina lalle dan Allah Mama, wlh bansan kowaba garin nan, da kyar nagane gidan nan shima kwatance aka mana yau za'a fara event din bikina wanda zan aura yau zai iso daga Chad shine za'a mai tabar damuke cema wushe wushe, dan Allah Mama kitaimaka mana" dan murmushi Ammi tayi tace "Allah ya sanya alheri yabada zaman lafiya" dan murmushi matan tayi tace "Ameen, nagode Mama" murmushi Ammi tayi tace "a gaskiya bana barin Aneesa zuwa home service lalle duk wacce keson lalli har gida ake zuwa tamusu anan agabana, sonake kome takeyi idanuna akanta tarbiyan ya mace saika saka ido sosai sanan ka kula ita kadai gareni, banso nacemiki a'a dan kallo daya namiki nagane you are so stress out, nayaba da hankalin ki ainun, zata biku amma da sharadi zaku dawomin da ita dan Aneesa batasan cikin Abuja ba, rayuwan ta komi anan Sulejan mune kin yarda?" da sauri Amaryan dawani murmushin annuri ya lullube mata fuska jin Ammi ta yarda tace "Mama namiki alkwari zansaka driver gidanmu yadawo da ita da acema lokacin am free dana dawo da ita da kaina kodan karamcin da kikamini amma zansa Baba lado driver yadawo da ita har gida namiki alkwari dama shiya kawomu yanama waje, I promise" murmushi Ammi tayi tace "shikenan karfe nawa za'a gama lallen?" dan tunani amaryan tayi kafin tace "gaskiya bansani ba Mama nida yan uwanmu ne sai kawayena guda biyu da basuma riga sun isoba dan ba'a garin nan sukeba amma dazaran tagama bazan bari ta bata lokaci ba zansa adawo da ita" murmushi Ammi tasake yi tace "shikenan nabaki amanan ta, please kisa mata ido karki bari tabar sight dinki, Aneesa wani zubin batada kai akwai neman fitina, please ku samata ido kunji" atare sukace "to Mama" duk suna murmushi ganin yanda matar keji da yarta, kwalama Aneesan kira Ammi tayi. "Aneesah" shigowa dakin tayi da saurinta duk suka bita da kallo Ammi tace "jeki shirya ki cire kayan nan, fara tattaro kayan lallen dakika siyo a kasuwa jiya kisaka ajaka saikije ki chanza kaya kizo kutafi" washe ma Ammi baki tayi tajuya da sauri tanajin dadi hakanan taji tanaso tabisu itama kodan taga family wayan nan kyawawan yan gayun yan matan kaman ma buzaye ne su, lallen ta tattaro dasu ledoji da sajen ta hada ajakanta da handglove tafito tabama Ammi, jakan Ammi takarba tana kara dubawa to make sure ta kwashi komi dan wani zubin Aneesa ta iya annoying mantuwa dazakaji kaman ka maketa itakuma ta wuce daki dan shiryawa, wani black fited gown tasaka mai kyau dan har jerin stones gareshi ta wuyan sanan tadauko wani ironed baby pink hijabinta mai hula ta zura ta zauna abakin gado tasaka safa akafa kafin ta tashi taje gaban madubin tadau kawalli ta zizara sanan tadau man baki ta shafa dayay kaman ta saka janbaki, ba karamin kyau tayiba wani irin asirtattcen kyau da only the seer kan see karamin jakanta ta rataya tafito falon hakan yasa yan mata suka mike, karasawa tayi gaban Ammi kaman zatai kuka tana kallon fuskarta, kwafa Ammi tayi tadau wayar daga gefenta tamika mata, wani irin murmushi tayi ta fada jikin Ammi tsabagen dadi tace "thank you Ammi na, bazan kara kona abinci ba kinji" gyadamata kai Ammi tayi tana tabe baki tace "common tashi kutafi kidenamin wani dadin baki, saikin dawo, ga jakan lallen" ta mika mata jakan lallen, karba tayi tace "bye bye Ammi na, kimana abinci mai dadi" yanda tai maganan yasa yan matan suka fashe da dariya, Ammi tace "aikin kenan acici kawai" murmushi tayi tareda rufe fuskarta da hijabi tawuce tafita daga dakin yan matan sukace "sai anjima Mama mun gode" "saikun dawo Allah sanya alheri" Ammi ta fada tana daga musu hannu fita sukayi daga dakin Aneesa na gaba har zuwa waje sukai wurin motar, baya amaryan tabude mata tace "shiga" shiga tayi ahankali amaryan ma ta shige, kanwar kuma ta shiga gaba suka rurrufe kofofin motar Baba lado yatada motar yaja tareda bata wuta, duk shiru sukayi sun ciciro manyan wayoyin su suna latse latse hakan yasa Aneesa tai wani murmushi irin nima inada soft touch dinan, bude jakarta tayi taciro tata tafara dannawa saikuma ta dago kai tana kallon abinda amaryan keyi awayanta ganin WhatsApp takeyi yasa takasa hakura dan matsowa kusada ita tayi tamika mata wayanta tace "Anty wai yaya ake WhatsApp dinan kinga wayata jiya Baffa na yakawomin inaso nai WhatsApp amma bansan wazai samin ba" murmushi amaryan tayi ta karbi yar tecno tana kallo tace "aiko wayan nada kyau" wani irin murmushi Aneesa tayi tace "nagode Anty, nima inason wayan wlh bansan haka touching screen keda dadi ba saida Baffa na yakawomin ita, jiyan nan nakusan raba dare ina tabe tabe, da yau nai niyyan naje shagon liti mai saida film din anguwan mu naira hamsin yake karba ya sassaka maka films awaya nace zanje asamin nima naita kallo abina" murmushi amaryan tayi ta kalli fuskan Aneesan hakanan taji yarinyar ta burgeta she's so pure at heart dan wanan wayan ne tecno takema murna haka, Allahu Akbar rayuwa kenan abinda ka raina shi wani kesamu yakasa bacci sabida tsantsan farin ciki, saisa akace kadena duban nasama dakai wanda yafika ni'ima sabida zaka kasance mara godiya ga Allah, by the time ka kalli nakasa dakai wanda kafishi saika godema Allah more and more which of the favors of Allah will she deny?? Alhamdulillah, Allah has been super good, Alhamdulillah, tasake godema Allah, dan ajiyan zuciya ta sauke tareda gyara zama tace "nagama bakida data bazaki iya downloading WhatsApp ba" hannu Aneesa tasa abaki tafito da manya manyan idanunta tace "laaaa sub ko? Kash ancene sub dari biyar dubu daya akeyi, inna koma gida nacema Ammi tabani kudi nasiyo" murmushi amaryan tayi tace "don't worry zan miki yanzu" kafin ma Aneesa tai magana tace "kiramin number ki" number Aneesa ta shiga kira mata ta tura mata katin dubu biyar sanan tamata subscription din 3gb, itadai Aneesa bamatsan meta keyi da wayan ba tadaiga tanata taba wayan, bude mata Gmail tayi screenshot din password din data bude mata dashi mai sauki sanan tamata setting up play store tai downloading WhatsApp tabude mata tsaf ta nuna mata sai dadi Aneesa keji sanan ta tura mata few movies din India datake dashi awaya wanda shine yawanci films dinta, dadi Aneesa kaman zata suma ta kudurta aranta yauko lallen dazata zanama wanga Amarya ko lallen matar sakin duniya ne sai haka.





Gamawa tayi tsaf sanan tajuyo zata bata wayan gani tayi sai leka wayan take tasa yatsa abaki tana taunawa tana murmushi tsabagen jin dadi, dariya ne ya kwashe amaryan da karfi hakan yasa akunyace Aneesa ta zare yatsan daga bakinta tana murmushi, mika mata wayan Amarya tayi tace "gashi nan yanzu saisu fara WhatsApp ko ga films nan ma duk ke kadai" cikin murna Aneesa tace "zanyi kallo yau, nagode sosai Anty, kinada kirki" gaban wani dankareren gida mai tapkeken Gate driver yay parking batare daya shiga cikiba, bude motan sukayi suka fiffito Aneesa ma tafito tana kallon wagegen gidan, fitowa kanwar tata tayi itama ta maida kofar tarufe amaryan tadubi Aneesa tace "mu shiga ciki" tabude Gate Aneesa biye da ita sai kanwar abayan su hadadden gidane babban gaske ashe saisa taga sunyi parkin a waje dan gidan cike yake da mutane da kuma canopy da aka mammakala ga kujeru mutane duk sun zauna akai, wani special canopy da aka shimfida babban rug ga pillows masu kyau jajaye sukaje amaryan tace "me kike bukata akawo miki, abinci, water drinks kokuma tea?" murmushi Aneesa tamata tace "a'a banjin yunwa abani ruwan zafi zan sa lalle ciki bayan nagama hadawa" gyada mata kai tayi ta kalli sister ta tace "ki zauna da Aneesa Nihal, lemme go and change zansa akawo miki ruwan" gyadamata kai tayi tawuce tajuya tai hanyar wani babban flat bata wani jima da shigaba saiga wata kaman yar aiki takwo flask din ruwan zafi da empty bowl karba Aneesa tayi ta hada lallen ta tsaya ya ruwan zafin a bowl ta wurga lallen ciki sanan ta shiga hada sajen yar aikin tadau flask din yakoma dashi ciki Aneesa sai kalle kalle take gidan ba karamin kyau yamata ba, wayansu matane taga sunzo an jera kwaryaye sun zauna sun fara bubbugawa suna waka saitaga Amaryan da wasu manyan mata sun fito da ita duk suna rawa suna tahowa inda take zaune itadai sai kallon culture take tana murmushi kawota wurin akayi aka zauna da ita wata babban mace tace "mai lalli fara mata" daukan lallin tayi da zuzzuba a ledan dazata amfani dashi ta ijiye sanan tadau sajen ta matsa kusada ita, ahankali ta cire hijabin jikinta ta linke gudun karya ba tashi da lalle taja handglove tasaka sanan tadau kafar tafara zana mata ja atafin kafa, guda aka farayi ana rawa, wani irin shegen lalle take zanama amaryan dan she already promise to give it her best ne amaryan nada kirki babu wanda saima lallen datake mata kallo daya yawuce saiya tsaya yacigaba da kallo lallen yay kyau ne to the extreme._*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



1️⃣3️⃣ & 1️⃣4️⃣



_Free page_

Bata wani jima akan amaryan ba dayake tanada sauri tagama mata lallen tsaf ita kanta amaryan takasa dena kallon lallen da Aneesa tamata, Subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin dayabama yarinyar nan gifted hands, murmushi Aneesan tayi tace "nagama Anty sai wane zanmawa?" da sauri kanwarta taja skirt dinta sama tace "ni ne Aneesa mai lalle" murmushi amaryan tayi tace "Aneesa kin mugun iya lalle, lallan ki bayama kama dana yan Nigeria, kina zana lalle kaman wata yar India, thank you Aneesa" murmushi tayi tana juya kanta tana zanama kanwar, kafeta da ido amaryan tayi sosai taji kawai Aneesa na burgeta she's so innocent da bazama kaji baka sonta bane, da ace tanada Yaya namiji wanda baiyi aureba da wlh saitace ga mata tamai, kwantattcen gashin keyanta dana gaban goshinta ta kalla sabida dan kwalinta yadan zamiye gashin ya kwanta sosai gadan ruwa ruwa ajiki na zufa, bakin fatarta na glowing sosai, just look at her pink lips ko ita fara bazata nunama Aneesan pink lips da yan kananu gasu so soft, tender and so moist, sai kallon Aneesan take yanda take zanama Nihal lallen tana mata fira, akwai yanda idanunta keyi idan zatai magana saikaga sunyi wani irin luuu ga bakin dogayen gashin idanunta dake karama fuskanta kyau.



Gamawa da kafan Nihal tayi tsaf sanan tajuyo ta kalli Amaryan hada ido sukayi, murmushi tayi ta kalli kafar da hannayen tace "Anty naki yabushe kin iya wankewa kona wanke miki?" da sauri Nihal datai kaman zatai kuka tace "Anty please ki wanke da kanki takarasa min nawa kafin su Umma suzo su farayin nasu" hararan Nihal din tayi tai kwafa kafin tamike tsaye tace "don't worry Aneesa karasa yimata sai kizo kici abinci kiyi salla kafin kicigaba, lado ma yaje dauko friends dina daga Airport saikiyi musu suma insun iso" gyadamata kai tayi ahankali ta karbi hanun Nihal ta cigaba da mata, batawani bata lokaci ba tagama yima Nihal tsaf ta ijiye lallen akasa tana sauke ajiyan zuciya murmushi Nihal tayi tana kallon lallen ta tace "thank you Aneesa kin iya lallen wlh, bantaba yin lalle mai kyau irin wanan ba, nagode kinji zan nunama baby idan yazo anjima" murmushi Aneesa tayi batare da tace mata komiba daidai lokacin yar aikin su ta taho wajen ta kalli Aneesa tace "muje Amarya tace nakawoki kiyi salla kici abinci" gyadamata kai tayi ta zare handglove din hanunta tadau hijabin ta dayar karaman jakanta tabi bayan yar aikin nasu sai kallonta akeyi kaman ansanta upstairs sukayi itadai sai kallon ko ina take bata taba ganin gidamai kyau hakaba wani daki yar aikin tabude ta shiga hakan yasa tabi bayanta amaryan na zaune kan gado daure da zani tanacin salad da fridge chicken akai, murmushi tayi ganin Aneesa tanuna mata bathroom tace "shiga ki dauro alwala" gyadamata kai tayi ta ijiye jakanta ta shiga da kyar dai tagane kan bayin tai abubuwan dazatayi tadauro alwala tafito babu kowa a dakin sai dadduma dataga an shimfida mata hawa kai tayi tai salla abinta ta sallame tana zaune kan dadduma ta kurama hoton pre wedding picture dinsu ido sun mata kyau, bude kofa da akayi yasa ta dago kanta yar aikin suce ta shigo dawani babban tray dake dauke da abinci almost kala hudu jellof rice ne sai moimoi mai kyau, da kuskus da miyan kubewa lafiyayyen abincin yan maiduguri sai waina d miyan taushe, baki tabude dan bata San inda zata saka uban abincin nanba jellof rice tadauka tafara ci tana kurban cold drink dinta abincin dadi hakan yasa taci iya cinta sanan ta ture tasha ruwa, bude kofa akayi aka shigo amaryan ne itada kawayenta murmushi tace "wai har kin koshi Aneesa?" gyadamata kai tayi ta kalli kawayenta tace "sun iso suzo muje namusu" kallonsu Amarya tayi tace "better kuyi yanzu kafin su Umma and her friends sufara" dunguma duk sukayi suka bita.
Haka tawuni tanama mutane lalle dabazata ma ita kirga adadin su ba salla kawai kedaga ta daga wurin kuma ko kadan bata gajiba sabida kayan dadin da aketa kawo mata tana tattaunawa, tana lallen sai kara gyara filin da za'ayi event din ake mata sai wanka suke suna saka wani anko na white and orange mai kyau, jin ana kiran magrib yasa tafara sauri tagama hanun matan datakemawa dan tafiya gida zatayi. Daidai lokacin Nihal ta iso taci gayu sosai an mata makeup tana sanye cikin ankon itama ganin Aneesa tsaye yasa tace "kin gama bazaki tsaya ki kalli event dinmu ba yanzu za'a fara fa su ango sunzo fa" girgixa mata kai tayi tace "ah a Ammi zatamin fada, tafiya zanyi" "muje to nakaiki wurin Anty makeup ake mata"
Tai maganan tanajan hanunta sukai wani flat daban inda Amarya take, babu kowa a part din sai amaryan da aka gama mata makeup ta sanya wani orange lapaya tai bala'in kyau tana waya, saikuma kawayenta dasuma sun saka anko irin na Nihal, ganin Aneesa yasa tace "baby am coming barina sallami mai lalle I will call you back" ta katse wayan ta taso daga kan gado tana murmushi tace "Aneesa kingama zaki tafi?" gyadamata kai tayi tace "eh" wani jakan souvenirs na bikin ta dauko tace "ganaki tsaraban bikin kikaima Mama" takama hanunta tasaka mata aciki sanan tadau jakanta ta bude taciro wayansu kudi yan dubu daidai ta kirga 30k ta zare ta mika mata tace "ga kudin lallinki mun gode" kasa karban kudin tayi hakan yasa takara kama hanunta tasa mata kudin adan rude kaman zatai kuka dan batasaba rike kudi dayawa hakaba tace "sunyi yawa kudin, lallen danayi baikai hakaba, please kirage Anty" duka yan matan dakin harda amaryan dariya suka shiga mata da kyar amaryan tai shiru tanunata da yatsa tace "kinga banison mu tsaya dogon zance magriba tayi nama Mama alkawari zan kula dake" ta fizge jakanta tareda kamo hanunta tacire kudin ta chusa ajakan ta zage jakan ta rataya mata a kafada ta kalli Nihal tace "jeda ita waje kicema Baba lado nace yamaida ta gida" ta kalli Aneesa da tama kasa magana tace "bi Nihal kuje amaida ke gida kinji nagode sosai ki gaidamin da Mama" gyadamata kai tayi ahankali tanaji kaman zatai kuka tace "nagode Anty, Allah sanya alheri sai anjiman ku" tadaga ma sauran kawayen hannu ahankali daga mata hannu sukayi suna atare sukace bye tabi bayan Nihal suka fita, kida sai tashi yake compound din yacika makil da jama'a gari yadan soma duhu amma ba sosai ba amma ko ina wutan lantarki ne bauuuu ya haska ka ko ina kana ganin bikin kasan bikin manya ne, hanyar Gate sukayi Nihal tafice tana biyeda ita karo Nihal taci dawata babban mata mai jiki taci gayu tasa wani lace dake walkiya, harara ta watsama Nihal din tayi tace "ina zaki baki ganin gabanki ne mara kai?" sunnar dakai kasa Nihal tayi wanan yar baban tasu Anty Hindu tacika masifar fitina, ahankali tace "Anty Hindu Anty ne ta aikeni zan kai mai lallen nan wurin Baba lado ne yakaita gida" wani mugun kallo tamata tace "ga lado chan taje tasame shi yakaita baya komi hirama yake da abokanenshi, ke come with me I want you to serve my guest banson ma'aikata suyi serving nasu, yanzun nan suka iso daga Dubai" ta kalli Aneesa datai zuru zuru tana kallon yanda katuwar matar ke masifa tace "wuce mai lalle ga lado chan tafi yakaiki" tamata pointing inda driver yake cikin tulin uban motocin dake anguwan ya zauna akan boot din mota shida wasu maza guda biyu suna hira, ta kalli Nihal tace "wuce mutafi" tai ciki waving hannu Nihal tamata tace "sorry Aneesa kije wajen ladon ai yasanki kuma yasan dama zai maidake gida, bye mungode" gyadamata kai tayi ahankali Nihal tai murmushi. "Nihal!" Anty Hindu ta leko tana hura hanci da sauri tabita tace "ganinan Anty" tawuce sukai ciki binsu Aneesa tai da kallo kafin ta sauke ajiyan zuciya gabanta sai faduwa yake duk ma wani tsoro tsoro takeji tarasa me yasa ita dayakamata taita murna yau tai lallen da aka kirgo dubu dubu har dubu talatin aka bata amma bataji ba, ajiyan zuciya tasauke tadaga kafa ahankali tafara tafiya tana dumfaran inda su Baba ladon suke, anguwan motoci sai shigowa suke ana parking ana sauka ana shiga gidan bikin, gani tayi lado ya dirko daga saman motan ya danna key yabude motan zai shiga da sauri takara sauri, gani tayi ya shiga sauran ma sun shiga yatada motar yayo reverse da gudu ta daga kafa bataso tai ihu dan mutane sunyi yawa gashi duk yan gayu ba kaman itaba datasha hijabi har kasa ba, ganin yajuya motar yasa tasa gudu amma kafin takai yaja mota dasauri rabi motar amma harya tafi hakan yasa ta tsaya chak kirjinta nawani irin

Please Login or Register in order to submit comment