Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kalli wayan ganin Dad ne yasa ya ijiye wayan yasan fada Dady zai fara baifito da bodyguard dinshiba, tada motar yayi yaja yana lumlunshe ido he's so tired dan driving dinan dayayi, and he's so sleepy Allah dai yakaishi gida lpy kawai.











Dakinsu ta shiga da sauri Ammi tace "meya daddar dake haka?" rasa abinda zatace ma Ammi tayi hakan yasa ta shiga kame kame kafin tace "uhmm Maman Muhammad ne ta shiga wanka saida najirata tafito fa Ammi" tai maganan tana hawa kan kujera dayake tanada tsawo tana hawa takai ta makala kwan lantarkin aiko wuta yakawo sanan ta sauko, dakinta tayi tacire kaya tadauro zani tafito, tsakar gida tawuce tadau bucket tajuye ruwan zafin da Ammi tadaura ta shiga bayi tayo wanka tareda dauro alwala fitowa tayi tawuce ta shige dakinta wani dogon rigan atampa tasaka sanan tadau hijabi tafito Ammi dake binta da kallo tace "bakiyi salla ba?" gyadamata kai tayi tana hawa kan dadduma tace "banyiba" magrib da isha tayi bayan ta idar tai shafa'i da wuturi, sanan ta cire hijabin tana sauke ajiyan zuciya ta kwanta akasa tana mikama Ammi kafafunta a shagwabe tace "wash Ammi kafana ciwo" murmushi Ammi tayi ta karbi kafafun ta daura kan cinyanta tace "raguwa kawai" matse kafafun nata ta shiga yi hakan yasa ta lumshe idanu wani mugun bacci na neman dibanta, kafeta da idanu Ammi tayi tana kara godema Allah daya bata yarinya mai natsuwa ga hankali, Aneesa is just a gift to her life duk rashin jinta inhar tace tak to ta natsu, she just pray Allah yabata miji nagari dazai kula da ita yabata all that she deserves, karasa matse kafafun tayi sanan tadan bubbugata ganin tai bacci. "Aneesa, Aneesa, tashi kije ki kwanta" bude idanu tayi dake cikeda bacci ta kalli Ammi, Ammi tace "tashi kije ki kwanta sannu yau mata sun aikatu" murmushi tayi ta mike tsaye tana tafiya ahankali tawuce, wayarta tadauka dake kan kujera ta wuce dakinta kwanciya tayi kan gado bayan tai bismillah sanan tai addu'an bacci wani bacci mai dadi yau awon gaba da ita.

_"why, why Aneesa? I trusted you, mena miki da zaki kasheni eh? I trusted you Aneesa, you are my friend, we are friends remember? I love you Aneesa, why, why, why, why, dama kin tsaneni, dama so kike ki kasheni, why Aneesa?!" yadaka mata wani irin tsawa da duka karfinshi daya rage kumfa na fita daga bakinshi, idanunshi sunyi jajir yana kakarin mutuwa hawaye na bulbulowa ta gefen idanun._ afirgice ta farka daga baccin daya kwsheta tana wani irin zufa komi na mafarkin datayi na dawo mata fresh, mutumin dazu tagani kumfa na fitowa daga bakinshi yana kakarin mutuwa yana mata all this maganganun itakuma tana gefenshi idanunta sunyi jajir sai kuka take ga ankwa a hanunta, batasan mesaba fashewa tayi da kuka sosai tana girgizakai, karan wayarta daya cika dakin yasa ta mugun firgita, da sauri tasa hannu ta goge hawayen daya bata mata fuska tamika hannu tadau wayarta dake gefen filon ta kalli screen din. "Aliyu" taga yana kira, faduwa gabanta yasake tazaro ido ta kalli time a jikin wayan 12:25Am._*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



1️⃣6️⃣

_How to subscribe_

_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting. You can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 for those dabasu da account_

_*littafin nan na kudi ne, duk wacce takaranta batare data biyaba ban yafeba, pay anan ko pay alahira, your choice 🤷🏿‍♀️ gumina ne, hakkina ne inada iko akai*_

Gudun kar Ammi taji karan ringing wayar daya cika dakin da kara tafito tace me takeyi da waya ware haka, wayake kiranta this night yasa tai picking wayar da mugun sauri hana kokarin hadiye kuka datakeyi takai wayar kunnenta batare datai magana ba, ajiyan zuciya Aliyu daya kasa bacci tun dazu dudda mugun baccin da yakeji yakasa sai tunanin ta yakeyi yasauke ajiyan zuciya ganin tadauka, murya chan kasa mai kunshe da sakonni da dama wanda shi kanshi baisani ba yace "Aneesah are you sleeping?" girgiza mai kai tayi kafin ahankali muryanta narawa sosai tace "a...a'a" tashi yayi zaune daga kan gadon jin yanda muryanta ke rawa kaman wacce ke kuka, murya chan kasa yace "Hey, are you crying?" girgiza mai kai tayi tace "a'a" jin yanda muryanta kefita yasa yaji wani irin damuwa ya dira aranshi, cikeda damuwa yace "are you sick?" "no" ajiyan zuciya yasauke jin lafiyanta kalau yace "is Ammi sick?" girgixa mai kai tayi tace "n...noo" cikeda damuwa sosai yace "why are you crying then a irin wanan lokacin eh Friend?" magana takeso tayi saikuma tafashe da kuka sosai sabida yanda ta tuna mugun mafarkin datayi, tashi hankali shi yayi da sauri yace "kidena min kuka yana dagamin hankali, talk to me" kaman bada ita yakeba ta cigaba da rera kuka ahankali, katse wayar yayi da sauri danjin kukanta yake har jijiyoyin zuciyan shi, ya lumshe ido tareda jinginar da kanshi jikin gado ya fuzar da iska, he's so damn worried sabida kukan dayaji tanayi zuciyarshi batada natsuwa, shi baimasan lokacin da zuciyarshi tafarajin damuwan wata aranshi ba sai akan Aneesa, tsaki yaja ya kalli wayan dayaketa jujjuyawa a hanunshi, sake dailing number ta yayi kaman zai katse saikuma ta dauka, murya chan kasa dake cikeda damuwa sosai yace "wats wrong with you Aneesa? Why are you crying?" murya chan kasa tace "babu komi" girgiza kai yayi yace "a'a, akwai abinda ke damunki tell me we are friends remember" yanda yake mata maganan ataushashe kaman mai lallshin ta shikuma ba lallshin yakeba yasa taji zuciyata ta natsu sosai. "tell me friend what is wrong with you? Why were you crying? Kinyi laifi ne Ammi tamiki fada?" hawayen fuskarta ta share tass kafin ahankali ta girgiza mai kai kaman yana gabanta tace "mafarki nayi" dan murmushi yayi for the first time tunda suka fara wayan yace "wat!! Mafarki kikayi kikema kuka haka?" dan murmushi yasake yi maidan sauti dayasa ta lumshe ido tabude su yace "you are one hella wired girl friend" yadanyi dariya kadan kaman ba Aliyu ba dat u hardly see him laugh, tsayar da dariyan yayi cikeda tsokana yace "tell me mafarkin mekika yi friend nima natayaki kukan to" juya idanunta tayi tareda dan turo baki a shagwabe tace "ai namiji baya kuka, kuma mafarkin tsoro ne sosai shiyasani kuka" cikin wani irin murya na shagwaba kaman yanda tayimai shima yace "frienddd come onnn is just a dream, just a dream" shiru tayi tasa hannu tadafe kirjinta heart dinta is beating way too fast sabida yanda takejin muryan shi, jin shima yay shiru kaman yana sauraron bugun zuciyan natane yasa tace "scary dream, very scary" gyara kwanciya yayi tareda jan bargo yana lallube kanshi dan sanyi yakeji gashi yakara karfin AC sosai, ahankali yace "scary how? Mafarkin is about wat?" da sauri tace "about you" hannu tadaura akan bakinta surprisingly dan bama tasan lokacin data fadi hakaba, gyara kwanciya yace "about me?" yay murmushi sosai yace "my friend had a scary dream about me, tell me about the dream, dodo nazama nazo nacinye ki kome am eager to know" girgiza kai tayi tana turo baki tace "ance babu kyau fadin bad dream" "but ai am your friend right Aneesah?" yatambayeta ahankali, faduwa gabanta yayi sabida yanda yay maganan, batasan lokacin data gyadamai kaiba tace "eh" murmushi yayi yace "alright, tell me, am all ears" shiru tayi na kusan 2min kafin tace "ni bansan meya faruba amma nai mafarkin na kasheka, but baka mutubafa amma nakasheka kumani bansan how ba, kumfa dai nata fitowa daga bakinka kana cemin mesa na tsaneka, maisa na tsaneka nakeson kasheka nikuma sai kuka nakeyi shine nafarka inata kuka" dariya yafashe dashi sosai harda dan dafe ciki, kaman zatai kuka tace "da gaske nake fa stop laughing" jin yanda tai magana kaman zatai kuka yasa yahadiye dariyan yace "okay, lemme ask you some questions" gyara zama yayi yace "kin tsaneni ne?" girgixa mai kai tayi tace "a'a, niban tsani kowaba" dan lumshe ido yayi yabude yace "kin kasheni but ban mutuba, kumfa nafita daga bakina my God wat if kumfan brush ne na toothpaste kinyi tunanin hakan?" yakara kyalkyacewa dawata yar karaman dariya, yanda yake dariyan bakaramin burgeta yakeba hakan yasa tadanyi murmushi, dan shiru yayi yace "worried not, is just a dream kinji Boldest" gyadamai kai tayi ahankali kafin da sauri tace "waye Boldest?" murmushi yayi yace "you mana my friend, Aneesah the fearless lady maima mutum zanen mage a fuska" dariya tayi mai sauti kafin tai shiru shima shiru yayi yana listening to the sound of her laughter kafin chan murya chan kasa yace "inzo gobe?" ware ido tayi tace "kazo kayi mene? Ni Ammi bata barina fita naje wurin kowa, banda hakaba gobe bananan" dan shiru yayi hakanan yaji baiji dadin maganan datayi ba, baiso taje ko ina yafison yaga koda yaushe tana gida akillace, ahankali yace "ina zaki friend?" "zanje shagon danake aiki sanan zandau permission naje nai registration din jamb" da sauri tarufe bakinta tace "laaaa banfa sanka ba inata maka surutu and is not good kaitama strenger surutu?" girgiza kai yayi yace "am not strenger, kin sanni, and I know you, you helped my sister once, and am your friend, your brother dabaki dashi from today, so allow me to do my duty okay" gyadamai kai tayi ta kwanta tareda lumshe ido, ahankali yace "inzo gobe? Inaso na sake ganin kine" ahankali tace "to bari mugani goben to idan Allah yakaimu, saida safe" takatse wayar da sauri, zaro wayar yayi daga kunenshi yana kallo jiyayi kaman ta katse zuciyarshi baiso ko kadan yadena jin muryanta, fuzar da iska yayi ya ijiye wayan ya kwanta yay shiru yana kallon saman dakinshi tunanin Aneesa yake banawasa ba, he really like the girl, yanason everything about her, he just wanna be her friend and take care of her and always support her kaman yar kanwar shi, tunanin Aneesa ya dinga yi har bacci yay awon gaba dashi.




Da kyar Ammi ta tadata da asuba tazo tai salla sanan tai karatun Al 'Qur'ani, saida gari yawaye sanan ta wuce tadauko tsintsiya ta gyaro dakunoni ta sharo tafito da sharan waje sanan ta wuce kitchen tahura wuta tasa ruwan wanka awuta sanan tadau tsintsiyan ta sharo tsakar gidan, ta gyara ko ina sanan ta koma kitchen ruwan wankan tahada ta daura shinkafar da Ammi ta dafa jiya jiya dan dumamawa tawuce tafita daga kitchen din dauke da bucket din ruwan zafi taja ruwa daga rijiya tahada tawuce daki tacire kaya tafito tadau bucket din tai bayi bata wani jimaba tai wanka tafito sanan ta shiga kitchen ta sauke abincin ta daurama Ammi ruwan wanka tazuba nata abincin a plate sanan tafito tawuce kitchen afalo ta ijiye abincin kusada Ammi sanan tawuce dakinta ta shafa mai, shiryawa tayi cikin Riga da skirt nawata maroon atampa dayay mata kyau sosai ajiki sanan taciro gogagen hijabinta maroon tafito falo kafeta da idanu Ammi tayi tanabin kayan jikinta da kallo harta karaso wajen zama kusada Ammi tayi dake kan dadduma tace "Ammi na bazaki yi karin yanzu ba muyi tare" girgiza mata kai Ammi tayi tanajan charbi hakan yasa ta shiga cin abincin cikin yan mintoci kalilan tagama ta tashi takai plate din kitchen sanan tadawo daki tadau hijabin ta tasaka ba karamin kyau maroon din yamata ba ta dau jakanta ta sagala tana kallon agogo karfe bakwai da minti arba'in da biyar tace "Ammi natafi" gyadamata kai Ammi tayi dan bataso ta katse zikirin datakeyi juyawa tayi tai hanyar fita daga dakin harta sa kafa zata fita saikuma tadawo a shagwabe tafada jikin Ammin tace "nikimin addu'a Ammi" shafa addu'a Ammi tayi ta ijiye charbin tadan buge bayanta tace "inkin karyani aisaiki nemo wata Ammin ko" dariya tasaki tana tashi daga jikin Ammin tace "Ammi nifa banida nauyi fa" hararan ta Ammi tayi takama habarta takai yatsarta gefen idonta tace "jibi kwansa a ido, bakisan idan zakisa kwalli zaki ciccire kwansa bako" turo baki tayi Ammi takarasa cire mata harda na dayan idon sanan tasaki fuskarta tace "saikin dawo to, Allah ubangiji yabada sa'a, Allah ya tsaremin ke" wani irin cute smile dake mugun karama fuskarta kyau tasakin ma Ammi tace "Ameen Ammi na, nagode natafi" tashi tashi ta wuce tafita Ammi tabita da kallo zaure tayi tabude kofar gidansu tafita tana tafiya anatse as usual tana kallon hanya tana fatan Allah ya kado wani mai keke napep danyau jinkanta take bata da karfin daddarawa har express road da kafa.
Bata wani yi nisa da tafiya ba saiga keke napep tsareshi tayi ta shiga tace "express road Malam" kunna keken yayi yace "dari da hamsin ne Hajiya" "to muje" Jan keken yayi sukai gaba har gaban shagon su yasauketa tun kafin ta sauko Yusuf security dake bakin kofa ya tsareta da ido kaman zai hadiyeta dauke kai tayi ta sauko taciro kudi ta bashi sanan ta rataya jakanta back tafara tafiya tana dosan gaban shagon nasu, washe mata baki Yusuf yayi yana binta da kallo tundaga kan kafafun ta dake sanye da black socks har zuwa kan hulan hijabin ta daya kwanta akan fuskanta, numfashin shi har neman daukewa yake sabida tsananin bugawa da zuciyanshi keyi sabida ganin ta dayayi karasawa tayi jikin kofan kafin ma ta gaidashi yarigata. "barka da zuwa Aneesa gimbiyan mata, sarauniya mai farin jini" bayabo ba fallasa tace "ina kwana" tasa hannu zata bude kofan da kanta da sauri ya tare yace "tsaya nizan bude miki Gimbiya ai ba'a barin gimbiyoyi suyi aiki da kansu baki saniba?" Yay maganan yana lashe baki yana kallonta cikeda da dan masifa tace "kabude min zanje naga Madam ne Yusuf" da sauri yace "karki damu Madam batariga tazo ba akwai abinda nakeso nafada miki ne" jitayi kaman ta kwasa mishi mari mugun haushi Yusuf yake bata hakan yasa ta kawad da kanta gefe, ko damuwa baiyiba yacigaba yace "Aneesah dan Allah sonake kibani dama naturo gidanku wlh ina bala'in sonki, wlh matukar burgeni wlh narasa yazanyi da raina kiwa Allah kibani dama naturo" juyowa tayi tamai wani irin mugun kallo tace "Yusuf kaga ina baka girman ka ko to kakama kanka, babu wani na shagon nan dabaisan kana soyayya da Fatima ba, banson rigima kadena shigar dani harkan ku kuma kacire hanunka ka matsamin na shiga shago inba hakaba idan madam tazo tace maisa banfara aikiba zancen mata kaine kahanani shiga shago tun dazu" washe mata baki yayi yana wani irin mahaukacin murmushi masifan Aneesa na masifar burgeshi dan matsawa gefe yayi yace "Allah huci zuciyar gimbiyar raina ki......" bude kofar Fatima tayi daga ciki da fushi tana ma Aneesa wani matsiyacin kallo.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



1️⃣7️⃣



_how to subscribe_

_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting. Zaki iya turo katin MTN na dari uku ta watsap number na for those of you dabasu da account*_



_littafinan na kudine duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafe mata ba, nabarta da Allah_






Tawani rike kugu cikeda masifa tace "ban fadamiki kifita harkan Yusuf dinaba ba, Aneesa banson shishigi kije kinemi saurayin ki mana saikinmin snatching" hararanta Aneesa tayi kafin taja tsaki tabi ta gefenta tawuce ta shiga cikin shago abinta so take tai sauri tai baking snacks sabida dazaran madam tazo tabarta tayi, bakery ta shiga tadau rigan aikin ta ta daura kan rigan jikinta tadau mini hijab din tasaka sanan tafara aiki, shigowa bakery Fatima tayi ta tsaya a bayan Aneesa tace "nike miki magana zaki wuce kiyi gaba abinki?" ajiye whisk din dake hanunta Aneesa tayi ta kalli Fatiman tace "Fati wlh idan baki fita daga harkana ba zan miki mugun jina jina, saurayin ki Yusuf babu abinda zanyi dashi ko shine namijin karshen duniya kifita daga harkana nagaya miki" itama ihu Fatima tayi tana mata tafi aka tace "eh, eh, kema kifita daga harkana ihu mayyar saurayi, saurayi snatcher" Aneesa zatai magana taji wayanta na kara da sauri tai wajen jakan ta tabar Fatima na surutan ta, ciro wayar tayi daga jaka ganin Aliyu ne yasa bata dauka ba ta maida ta ijiye tareda jan dan karamin tsaki tawuce ta koma ta shiga buga egg dinta da whisk bata kara cema Fatima komiba harta gaji da bala'in tafita daga wurin, cakes tafara hadawa tasaka a oven sanan ta shiga yin dough nasu chicken pie. Wuraren sha daya ta gama bakin almost 100psc tai recording ta dauko tafito takawo ma Fatima agaban kanta takoma tafito da sauran sanan tawuce backyard ta wanko hanunta da kafarta sanan tafio tanaji wayanta na ringing tasan Aliyu ne yasa batama bi takan wayan ba tawuce tafita tai sama tawuce office din Madam, knocking tayi aka bata izinin shiga bude kofan tayi ahankali ta shiga Madam ta dago daga rubutun datake ta tsareta da ido tace "Anesh na you" gyadamata kai Aneesa tayi tace "good morning ma" ajiye biron Madam tayi tana dauko wani paper tana dubawa tace "morning, why are you here? Menene yakare a store dama naga sugar yay kasa da corn flour, menene babu?" dan sosa gefen fuskarta tayi dan dagajin yanda Madam ke magana tadauka wani abune babu tazo fada, mayar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta ahankali tace "Ma, ummm dama, dama sonake naje nai registration din jamb nariga nagama baking shine nazo daukan permission dinki naje yanzun nan nadawo saina cigaba da komi" nan da nan dan annurin dake kan fuskar madam ya bace tace "dole saikinje yaune?" dan rage murya tayi tace "Baban mu yace naje yau" wani kallo Madam tamata tace "baban ku?" gyadamata kai tayi tace "eh kanin baban mu" dan tsaki Madam tayi tace "ince dan nasan babban ku yamutu, kinyi baking abinda zai isa" da sauri ta gyadakai tace "eh bazan wani dadeba tunda rana batayiba lokacin ne ake cika wurin yanzun nan zan dawo" tsaki madam takaraja dan ko kadan bata so ta tafi tace "okay nabaki 2hrs,yanzu is eleven by 1 ko highest 1: 30 kodawo kobaki gamaba dan I can't stand loosing customers due to your negligence again yau" gyada mata kai tayi da sauri ta tsaya tana jiran tabata izinin fita, buga taburin madam tayi tace "bazaki wuceba bakisan time dinki kikeci ba" da sauri tajuya tafita daga office din tawuce kasa ta shiga rigan aikin da hijab din tacire tadau dogon hijabinta tasaka sanan tadau wayarta dake kan saman jaka tana dubawa 20miss calls datagani yasa tace "20" bude wayan tayi da sauri ta shiga gabaki daya 20 miss calls din duka na Aliyu ne, maida wayan tayi cikin jaka tace "to menene yaketa kirana haka" dan murmushi tayi taunawa da yace she's his friend tawuce tafita daga dakin tace zan kiraka anjima inmun koma gida, Fatima nata kallonta kaman zata hadiyeta wajen kofa tayi da sauri Yusuf yabude mata yana kallon fuskarta yace "ina zaki Aneesa?" batare data kalleshi ba tace "inda ka aikeni" tayi wucewarta, binta da kallo yayi yarike baki dama Aneesa bata da kunya? Yatambayi kanshi kwafa yayi dan duk Fatima ce taja Aneesa dake bala'in girmamashi ta raina shi haka.









Keke napep ta tare tace "Suleja ICT center zaka kaini malam" "hamsin, hau muje" hawa tayi dan batason tsayawa ciniki da masu abin hawa har gaban ICT center taje taga students dayawa duk yan registration din jamb, kudin tabiyashi ta wuce ta shiga ciki wayarta dake cikin jaka sai ringing yake.


Ciki ta shiga ko ina dalibai da kyar tasamu taje gaban kanta daya daga cikin ma'aikatan ta gaida tace "malam dan Allah nazo registration ne yaya zanyi?" zufan daya cika goshin shi ya goge dan wajen is so crowdy dudda akwai manya manyan fankoki amma kaman bakomi wani takarda ya nunamata yace "keji ki rubuta sunan ki, za'ayi ta kiranku according to numbers ne" gyadamai kai tayi tace "nagode" tawuce da sauri wajen paper dataga wasu dalibai na rubuta sunansu tsayawa tayi abayansu suka gama sawa sanan taciro byro daga jakanta ta matsa tareda daukan paper number 178 anan zata sa suna, kambu mutane har nawa agabanta itada awa biyu madam tabata sunanta tarubuta kaman wacce ke tsoron paper duk tunani ya kasheta. "Fateema Rufa'i Mai Kwato!" da sauri ta daga kanta jin ankira full name dinta ware ido tayi ganin wani malamin su daya koyar da ita tun daga SS1 a makaranta har zuwa SS3, shine malamin further mathematics dinsu, Malam Auwal Mazimaziz haka yan makaranta suka radamai ko maganan shi ake idan kace Malam Auwal baza'a taba ganewa ba saidai kace Mazimaziz kokuma kace dy/dx daga wani bene taga yake saukowa rikeda wasu takardu da yawa a hanunshi yana kallonta dogon namiji ne handsome black dashi yana sanye dawata faran yadi kanshi da hula yana kallonta murmushi tayi sosai tana kallonshi harya karaso mutumin data tambaya dazu yaje wurinshi yabashi takardun sanan yakaraso ta inda take akunyace tace "good morning Malam" murmushi yayi shima yace "good morning Fateema" murmushi tayi tace "Malam dama kananan" dan hararanta yayi yace "look at you tunda kukai waec da Neco muka sallameku kin kara waiwayan school kizo kidubamu ne? Inda kinzo aida kin gani ai mara zumunci kawai" a kunyace tarufe fuskar ta da Hijabi ita tai mamaki ma dayake mata fara'a haka Mazimaziz ai shine the most wicked Teacher a makarantan su, ko sajent saiya sallama mishi a iya duka, gashi ko test dinshi kafadi saiyay duka sunci dukanshi a makaranta kaman ba gobe. "jamb kikazo siya?" tambayar dayayi ya katse mata dan tunanin dataje da sauri ta gyada kai tace "eh nazo ai registration amma mutane nice number one hundred and seventy something" dan murmushi yayi yana zama akan kujeran gaban kantan yace "banda abinki ai da sassafe ake zuwa dan dalibai nada mugun yawa anan" dan zaro ido tayi kaman zatai kuka tace "bansani ba ne wlh" dan shiru yayi yana kallon fuskarta yanda tai kaman zatai kuka tana kallon wajen yanda aka cika ko ina. "Fateema" da sauri ta juyo ta kallai mikewa tsaye yayi yace "lemme see you off, kizo gobe da sassafe as early as seven zansa wani yay miki, ko yanzu ma aiki yamai yawane danasa yay miki but kizo gobe as early as seven fa kina jina" gyadamai kai tayi tana binshi abaya suna kukustawa dan fita daga wurin tace "okay sir" fitowa sukayi tana biyeda shi wani irin mummunan faduwa gabanta yayi Aliyu tagani tsaye yana sanye da jeans black dawani sky blue shirt yadan bude boturin kirjinshi idanunshi sanye da bakin glass ya rungume hannunshi a kirji dayake rikeda wayarshi Samsung galaxy fold, yana facing cafe din, yan matan premises din Cafe sai kallonshi suke dan yay bala'in yin kyau kaman bature, da sauri ta dauke kai daga kallonshi kirjinta na dukan uku uku ya akayi yasan tana nan? Ya akayi yabiyota? da sauri zuciyata yace a'a bake yabiyoba hala yakawo wanan kanwar tashine itama tai registration din jamb bake yabiyoba, dan ajiyan zuciya ta sauke. "Fateema kinajina kuwa?" Malam Auwal yamata tambayan da sauri ta dago kai ta kalleshi tace "sorry sa banji mekace ba" dan murmushi yayi yace "hayaniyan dalibai ne yay yawa but gobe idan kinzo ina jiran amsan kinji" da sauri tace "amsan mene malam?" dan shiru yayi yana mata wani kallon daza'a iya kirada

Please Login or Register in order to submit comment