Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hear for yourself, banda hakama who do you think you are to talk to me in such manner nafika matsayi da iko akan Rauda, am her Mum's elder sisters first son, and her husband to be, ko ubanka yasan da hakan so back off please, ke Rauda let's go" yay maganan yana tahowa yazohar gaban Aliyun yasa hannu zai jawo Raudan cikin wani irin fushi Aliyu ya kwasheshi da mahaukacin mari. "Tau!" da sauri Aliyu yarike hanunshi sabida zafin da hanunshi yadauka ya murza hanun kaman zaiyi kuka yace "aauchhhh" yana yarfe hannun, yanda yayi saida yasa Khamis fashewa da mugun dariya dudda marin ta shigeshi dan har gefen fuskar da Aliyun ya mara yay ja abunku da fari, da yatsa ya nuna Aliyun dake yarfe hannu yana yatsine fuska yace "wanan ne, wanan ajebotan kuka kira yay protecting naku daga ni? wanan malalacin namijin daya rako maza duniya wanan maza matan dayamafi mace yauki kaman kubewa ne kuka tunanin can beat me up?" hannu yakai yafara bude boturan gaban shaddan riganshi yace "zan nunama u have messed with the wrong guy ni haifaffen dan kwari ne ba girman turai ba, girman tasha, kar har purewater na saida a park" fashewa da kuka Rauda tayi dan tasan Ya Aliyu bai iya fadaba ko kadan ta jijjigashi tace "Ya Aliyu mugudu please" itama Aneesan jikinta rawa yafara ganin Khamis cikakken dan tasha ne kam yana magana kaman dan wiwi, riganshi ya zare ya yar akasa ya matso gaban Aliyu ahaukace yasa duka hannayenshi ya daki kirjin Aliyu da saida yay baya kaman zai fadi yace "kai ubanka yaci ubanka kaji, dan babar ka nataba kanwar taka uban me zaka iya? Eh nace ubanme zaka iya?" Khamis yay maganan kaman dan daba yana hura hanci, Aliyu ya kafeshi da ido he really do not know how tayaya ma zai fara fighting dinshi ba, indako yasani daya kusan kashe yaron nan, cikin kuri yay pointing Aliyun da yatsa yana murmushi ya kalli Aneesa da Raudan dasukai zuru zurun barinma Rauda dake kuka wiwi za'a dakinmata yayanta yace "do you all see what am saying, bakazo shigarma kanwarka dat I was trying to rape bane? Then beat me up now Aliyu, are you scared Mama boy? Beat me mana, kawa Allah ka dakan, baku ganiba matsoraci bane, kai" ya dungure ma Aliyun goshi da yatsa Aliyu yasakeyin baya, Khamis ya nunamai yatsar shi ta tsakiya yace "f**k you Aliyu, I said f**k you mezaka iya? Daken mana kaji tsoro ne eh? Eh malalaci?" yanda yakema Aliyun daya tsaya kikam yana kallonshi tijara yamugun sosa ran Aneesa saitaji kaman tai kuka dan daga ganin yanda Aliyu ya mareshi da farko ya shiga yarfe hannu zaka gane baida karfi kona sisi, kallon yanda Rauda ke kuka sosai abayanshi take alamun batada hope zai musu dukan tsiya sanan yama yayan nata dukan tsiya shima hakan yasa taji wani karfi yazo mata da bata taba jin irin that kind boldness ba in her life, cikin wani irin izza ta shiga gaban Aliyu tana taku dai dai tana clapping hands dinta cikin isa da takama tana clapping din tana kallon fuskan Khamis din dake kallonta kaman yanzu yafara ganinta, tsayar da tafin tayi tace "kasan mesa nake tafa maka?" tai wani murmushi ganin baice komiba kawai kallonta yake kaman wani wawa tace "wani zubin idan kare na haushi idan kai tafi saikaga yadan natsu" cikin fada yace "nikike cema kare?" cikin dakewa ta nunamai yatsa tace "quit, am still talking" samun kanshi yayi dayin gum ganin yar yarinya namai magana kaman uwarshi, tace "what differentiate human being da animals is ability to think and reason which bakada duka biyun you are just a dog malam which yayan mu bazai taba iya biyema yadawo kaman kaiba ko?" tadan juyo for the first time ta kalleshi idanunshi da nata suka sarke faduwa sosai gabanta yayi tadan kyafkyafta ido sau biyu pink lips dinta sukadanyi rawa ahankali tace "ko?" gyadamata kai Aliyu yayi batare dayasan yamayi ba, juyar da kanta tayi tace "kai mailafine bagaremu ba kadai har agun Allah, sanan kanada bakin zage zage kana turashi kanaso yabiye maka kuyi fada, wai intambayeka man do you know who is a Man?" wani matsiyacin kallo tamai ganin yanda yasaki baki yana kallonta tace "A Man baya tsayawa yay physical fight da kowa dan physical fight dangrades one's level, banda haka a Man is someone who has control over his heart ayayin dayake cikin tsananin fushi which is abinda yayi yanzu, kazaci kana ihu kana cika kana batsewa kana tunanin by d time dayake so yaci ubanka you can match his level ne eh?" tamai tambayan tana hura hanci daya kaman wata boss tana kallonshi, dan murmushi Aliyu yasaki for the first time ya rungume hannayenshi a kirji, ganin har lokacin Khamis din baice komiba ya tsaya yana mamakin tane yasa tace "and yanzun nan zan nunamaka idan yatashi yace zai ci uban naka u can never match his level of power, kwabaka zaiyi kaman yanda ake kwaba dibila tsaya kagani" tai maganan tana tsugunna wa a wurin duk suka bita da kallo kasan dake bakin Gate din ta kwasa da hannunta dayawa batare da duksun luraba dan hijabinta yarufe mata hannu sundaiga ta tsugunna mikewa tsaye tayi Khamis din nabinta da kallo hannunta tadaga un expectedly ta watsamai kasan a fuska aiko suka shiga idanunshi biyu, ihu yayi. "wayyo Allah na, wash Allah idanuna, sainaci durun uwarki yarinyar nan" yayo kanta yana sosa idanunshi dayakasa budesu tsabagen kasan data sakamai a ciki matsawa gefe tayi da gudu ta kalli Ya Aliyu dake binta da kallo tace "Yayan mu yimai shegen duka ramama kanwarka abinda yamata bazai iya ramawa ba idanunshi cike suke da kasa" ware manyan idanunshi Aliyu yayi yana kallon this wired girl, gyadamai kai tayi da sauri tace "ka zaneshi, daddaki azzalumin" jin daga ta inda take magana yasa Khamis yay wurin yana murza ido yace "dan uwarki ubanwa yace miki koni makahone zai iya tabani ne wanan ragon" dawowa tayi kusada Aliyun ta kallai tace "yimai lilis u can do it, zo zan nuna maka inda zaka dinga duka ajikinshi zokaga" tai gaban Khamis din dake bubbude kafa yana sosa idanu kaman mahaukaci tsabagen azaban kasan dake cikin idon, ta nunama Aliyu cikin shi daya fara dan tara teba dama babu riga ajikinshi tace "zoka naushi nan" turashi Rauda tayi tace "muci ubanshi Ya Aliyu ka rama mana" ahankali Aliyu yadaga kafa yana kallon Aneesa dake nunamai cikin Khamis kaman wawa yakaraso kusada inda take yana kallonta still, zare ido tayi tsabagen jin dadi zasuci ubanshi tarage murya kaman mai shirin gulma tace "yauwa naushi nan".







Tanunamai gefen cikin Khamis, farin hanunshi Aliyu ya kalla ya dunkule ahankali yana kallon Aneesan data cije lebe irin ya dunkule hanunnan da kyau dinan tana kallon hannun tana nunamai cikin Khamis din dake sosa ido, daddagewa Aliyu yayi yabugama Khamis uban nishi aciki atare daga Aliyun har Khamis din sukai ihu harsaida Aneesan takoma baya da gudu dan tsoro sabida ihun da Aliyu yayi yana yarfe hannu kaman zaiyi kuka ya kalleta yace "it's hurt, ahhhh, aucchhhh, alottt" sosai yake yarfe hannu hakan yasa ta matso ahankali tana leken Khamis din daya zube akasa dan naushin ya shigeshi gashi yakasa bude ido balle yarama, tsayawa kusada Aliyun tayi dake yarfe hannun nashi dayay jajir tasaka yatsa abaki tana cija danso take suci uban Khamis sosai, kalle kallen compound din ta shiga yi kafin idanunta su sauka kan rigan Khamis din dayacire ya yar da sauri tai wurin rigan tsugunnawa tayi ta dauka ta shiga wurga rigan tana kaman lilo dashi rigan ya shiga kanannadewa danso take tamaida rigan dorina, binta da kallo Aliyu yake yana murza hanunshi harsaida tagama tazo gabanshi da sauri ta mikamai dorinar rigan tace "gashi yayan mu, rama mana da wanan tunda baka iya fadaba, yimai shegen duka da wanan" tamikamai rigan, karban rigan yayi yana kallon fuskarta, nunamai Khamis din tayi tace "zaneshi karka ragamai, ko akotu irinsu bulala tamanin ake musu kaima yimai 80" da sauri ya kalleta yace "80?" kallonshi tayi akaro nabiyu idanunsu yakara sarkewa faduwa gabanta yayi hakan yasa ta kyafkyafta ido sau biyu ta gyadamai kai batare data iya magana ba ta kawad dakanta, ahankali Aliyu yakarasa inda Khamis din yake azube yana sosa ido ya daddage ya shaudamai ihu yayi. "Aliyu wlh idan idanuna suka bude saina kasheka dagakai har shegiyan na..." zubamai nabiyu Aliyu yayi da karfi hakan yasa Rauda ta rungume Aneesa cikeda murna suka shiga tsalle kaman sunsan juna Aneesa harda tafi wani masifar dadi takeji fiye da tunanin mutum, cigaba da dukanshi Aliyu yayi da rigan sunamai tafi itada Rauda harya yarda rigan ya zauna agefe yana haki yagaji, da sauri ta kalli Rauda tace "ina zuwa bari kuga" da sauri tabude gate tafita jakanta tabude ta ciro wani kwababben bakin lalle da mai saida lallenta yahada mata as sample dan kafin tasiya saitasa ya dama mata tadanyi Zane kadan a hannunta ta wanke dan taga iya bakinshi dan kwanaki tasai lalle ko kadan baya baki dudda hydrogen din datake zubamai, shigowa tayi da sauri rike da ledan lallin ta kalli Aliyu tace "Yayan mu daga shi ka zaunar dashi kaga" kasa mata musu Aliyu yayi Yajuya yadago Khamis din da karfi ya zaunar dashi, tace "yauwa rikemin hanunshi tabaya" tsayawa abayanshi Aliyu yayi yarike hanunshi gam, da kyar Khamis dabaya iya bude ido ke magana yace "wlh duk kun shiga uku koba yauba yau ranan kuc...." bai karasa maganan ba Rauda tazare flat shoe kafarta tai bugamai abaki aiko sai jini, dariya sosai Aneesa tayi dayasa dimples dinta lotsawa tana kallon Raudan tace "dama kinada karfin nan tuntuni kiketamai kuka matsoraciya" takarashe maganan tana dariya sosai kafeta da ido Aliyu yayi ko kyafta ido bayayi kaman ance ta kalli gabanta suka kara hada ido shiru tayi ta saukar da idanunta kasa tadan matsa gaban Khamis din sosai kirjinta na bugawa tana gyara bakin ledan lallen, ahankali ta shiga zanamai bullen mage tundaga gefen bakinshi har zuwa wajen sajenshi uku uku sanan taja wani dogon layi tundaga kan hancinshi har zuwa goshinshi shidai Khamis sanyi sanyi da waiwayi waiwayi yakeji akan fuskarshi amma yarasa me akemai, fashewa da dariya sosai Rauda tayi ganin abinda Aneesa tamai harda bubbuga kafa akasa kaman ba itace tagama kukaba da barkakken riganta, mikewa tsaye Aneesan tayi itama tana kallon fuskanshi ta harari Rauda cikeda murmushi tace "am happy you are now smiling nidai nagudu gida, you guys should run for your lives, kugudu kafin idanunshi subude" ta kwasa da gudu tabude Gate tafita da sauri Rauda tabita tana kwala mata kira tace "baiwar Allah, baiwar Allah baki fadamin sunanki ba to" juyowa Aneesa dake kwashe kayanta nakasa awajen Gate din tayi ta kalli Raudan tai murmushi tareda rataya jakanta akafada tace "sunana Nana Fateema" "can we be friends? Inason ki sosai you are so bold wat a fearless lady, a ina kike? Inane gidan ku? Anan Suleja kike?" Rauda tai maganan tana karasowa gabanta murmushi tasakeyi zatai magana idanunta suka sarke dana Aliyu dake tsaye jikin Gate yazuba mata idanu hanunshi zube a aljihun riganshi yana kallonta sosai gabanta yafadi, dan kyafkyafta ido tayi tana kallonshi kafin ta juya da sauri tama Rauda waving hannu tace "bye Friend" daidai lokacin keke napep na zuwa tareshi tayi ta shiga ciki sukai gaba dukansu tsayawa sukayi a inda suke sukabi keke napep din da kallo har yafita daga layin.
[11/02, 05:11] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



9️⃣


_How to subscribe_

_*Zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting*_


_*zaki iya turo katin MTN 300 in baki da banki ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya*_







For a moment harta manta da matsalan datake ciki dasuke magana da Aneesa not until lokacin da keken data shiga ya bacema ganinta, juyowa tayi ahankali hada ido sukayi da Aliyun dayamata wani irin mugun kallo da baitaba mata irinshi ba kafin yafito daga cikin gidan yay wurin motarshi da sauri tabishi bude mota yayi ya shiga hakan yasa tabude dayan side din ta shiga tana kallonshi batada burin daya wuce yacemata wani abu amma saibaice ba, kunna mota yayi batare dayace mata komiba hannayenshi duk ciwo sukemai yaja motar, sosai taji jikinta yawani irin mugunyin sanyi hakan yasa ta saukar da kanta kasa gabanta sai faduwa yake, da azababben gudu yakejan motar Haryakai kai gidansu uppan baice mataba wani mahaukacin horn yadanna daya daga cikin sojojin gaban Gate yazo yabude musu Gate din yaja motar cikin gidan a tsakar gida yaga Dad sai zirga zirga yake yana sanye da jallabiya mai ruwan goro dayake yau weekend baifitaba yana gida, ganin motar Aliyu yasa tun kafin motar yay parkin yay wurin motar, daidai Aliyu yay Parking yabude motan yafito ranshi abace, tsareshi Dad yayi yadaura duka hannayenshi akan kafadarshi yana nazarin fuskanshi cikeda tashin hankali yace "Son kakirani kana cewa menene menene, banma gane mekake cewaba sai kuma ka katse wayan, were you attack? Nasaka bodyguard bin bayanka gashinan kuma kadawo, wat happen to you Gadanga na iyye? Ya akayi idanun ka sukaija hakk...?" kasa karasa maganan yayi sabida sauka da idanunshi sukayi kan hanun Aliyu, yanda yaga hanun Aliyun yay jajir kaman ya kone da ruwan zafi yasa da sauri yasaki kafadar Aliyun yakamo hanun yarike arude yana kallo yace "wat happen to your hand Son? Maiya sameka, talk to me Aliyu? Me haka hanunka yay jajir where you attack?" Dad yay maganan kaman zaiyi kuka dukya birkice, ganin yanda Dad din ya rude yasa yadan yatsine fuska tareda fizge hanunshi yace "am fine Dad don't worry am fine" yay maganan yana bin gefen Dad yay dayan side din motar, Dad yabishi dasauri yace "don't tell me you are fine Aliyu, mai ya sameka idanunka sukai ja haka hanunka yay ja shi...."cikin fushi yabude kofar motar, lekowa Dad daya biyo bayan Aliyun yana tambayanshi maiya sameshi yayi ganin Rauda zaune kan kujeran gaban motan rigan ta abarke sai rirrike wurin barkewan take da hannu, babu dan kwali sai kuka take gefen fuskarta ya kumbura suntun hakama bakinta, idanun ta sunyi jajir sai wani kukan take ganin Daddy, hadiye wani miyau mai daci Dady yayi cikin wata irin muryan mamaki yace "Rauda?" ya kalli Aliyun yace "tareda Rauda kuka fitane, but you went out alone, a ina ka ganta? Maiya sameta haka? maiya faru? You guys should answer me ha'a" dan cizan lips Aliyu yayi yasaki ahankali yace "I was on my way going to Momma's place Rauda takirani dawani number crying wai Khamis was trying to rape her, da kyar nagano inda take a Suleja....." nan yabama Dad duka labarin daga farko har kashe ranshi duk abace yace "Dad ba cousin dintaba kowa who the hell that Khamis is I've cancelled their marriage, bazan taba bari my sister to marry that kind lowlife of a being that could stood so low har yay kokarin molesting mace ba" cikin bala'in fushi Dady ya kalli yanda take babbaka kuka yace "dan gidanku kimin shiru anan kafin na kikkifeki da mari, ubanme yakaiku har Suleja? Iyye ubanme yakaiku har Suleja, ba wajen mamarshi Mamanki tacemin zai kaikiba, yawon banza kika fara Rauda? Yawon banza?" girgiza ma Dady kai tayi da sauri wasu sababbin hawayen nabin idanunta tace "Dady wlh Mama tace mai wai yakaini yawon bude ido sai dare zai dawo dani, ni kuma tace dole saina bishi dankar nazauna agida Ya Aliyu nanan wai wurinshi zani, shine yakaini gidan" tafashe da kuka sosai mai tsumma zuciya, cikin wani irin tsananin masifa da fada Dady yace "ni Khamis zai lalata ma Y'a, yarana yama haka?" ya kalli Aliyun da Raudan da duk sukai wani iri barinma Aliyu kana ganinshi kasan yau yay abinda bai tabayiba, Dady yay kwafa cikin tsananin jin ciwon yanda Khamis yataba mai yace "zai gane kurenshi, Allah dawo da Kareematun ai zata dawo gidan nan tasame ni, tashi kiwuce ciki ki chanza kayan nan kiyi wanka zan kira muku likita yazo yadubamin ku wlh saiyasan yatabaku, wlh kuwan" yay maganan yana rike habar Raudan yana kallon yanda gefen fuskarta da wajen kunenta yay suntum, sakinta yay ahankali yace "sannu kinji, tafi dakin ku kiyi wanka ki chanza kayan nan kizo falona" gyadamai kai tayi tawuce tana tafiya ahankali.










Dad ya juyo ya kalli Aliyu da duk yay wani iri ji Dady yayi kaman ya kurma ihu, hanunshi yakara kamawa yana kallo cikin dan fushi yace "why will you fight him eh? You would have called me danai contacting police headquarter na Sulejan koda i can come on time da nasa a tura police akamashi adaure shi, why will you fight him eh Aliyu?" Dady yay maganan abin namai masifan ciwo dan yasan waye d'an shi, ganin yanda Dady yayi yasa ya fizge hanunshi yana yatsine fuska yace "am fine Daddd, okay, am fine, bari naje nai wanka" yay hanyar shashin shi Dady yabi bayanshi da kallo cikeda tausayin Aliyun for the first time yau yaga jarumta a idanun Aliyu yasan hanun nan namai zafi amma yaki nunamai hakan saidai yace he's okay he's fine, dan murmushi yayi yace "Allah rayamin kai Aliyu na" yay kwafa yy hanyar shashin shi shiko Khamis mai rabashi dashi yau sai Allah dan wlh yay kuskuren taba Aliyu daya sani dashi yazo yataba fess zai iya yafemai amma Aliyu ko wlh saiya ramama marayan yaron shi yasakeyin kwafa ya shiga ciki.





Bedroom dinshi dake hadadden kamshi ya shiga ko ina a gyare dan cleaner shi yazo ya gyara, maida kofan da sauri yayi yarufe harda murza key dan yasan Dady zai iya biyo bayanshi hanunshi dakemai masifan ciwo ya shiga yarfewa kaman zaiyi kuka in fact duka hannayen ma kemai ciwo baitaba wani punching punching da mutum ba in his life, shi yanama shiga mutane ne balle har wani abu physical fight dazaisa yay exchanging punch da wasu yahada shi, cijan lips dinshi yayi ya shiga cire kayan jikinshi yabarsu anan kasa ya tsallekesu yay bathroom wanka yayi da ruwa mai zafi sosai yafito sanye da bathrobe akan gadonshi ya zauna kafin yawani irin fada kan gadon yana sakin ajiyan zuciya, lumshe ido yayi yana kara lumewa cikin lallausan katifar shi while relaxing all his nerves and body. _"wai in tambayeka mana do you know who is a man? A man baya tsayawa physical fight da kowa dan physical fight downgrade one's level, banda haka a man is someone who has control over his heart ayayin dayake cikin fushi which is abinda yayi yanzu"_ wani irin murmushi daya bayyana all his 32 teeth out Aliyu yayi. _"kazaci kana ihu kana cika kana batsewa by the time dayake so yaci ubanka you can match his level ne eh?_ murmushi yasakeyi idanunshi a lumshe yaja filo daya ya rungume tight kaman zai fasa filon murya chan kasa yace "who is this Fearless Lady? Who are you Boldest?" "Aliyu, Aliyu, Gadanga" kaman daga sama yaji ana tapping nashi ana kiran sunanshi bude ido yayi da sauri abu yaji ya shigan mai ido hakan yasa yamaida idon yarufe da sauri, Dady dake tsaye a kanshi yasa hannu yana kakkabe feather filon yace "sai murje filo haka filo harya fashe bakada lafiya ne, cikin ka naciwo ne, tundazu nazo ina kiranka baka amsaba saida nadauko spare key nabude na shigo, bude idananun to na kakkabe maka" ahankali yabude idanun yanabin gadon da kallo yanda yafasa filon da abubuwan shi duk suka zuba akan gado, hanunshi Dady ya kama yace "stand up, stand up" tashi yayi daga kan gadon Dady yabude muscle and tissue pain killer balm din daya shigo dashi ya lakato yakamo hanun Aliyun zai shafa kaman Aliyu zaiyi kuka yace "Dadddd" "kai kamin shiru anan" ashagwabe yace "Dad but this balm is smoky hot, too peprish natuna shi idan naji ciwo da ina yaro shikake samin, ni gaskiya karka samin am fine" rike hanunshi dayake shirin fizgewa Dady yay kyau yace "idan nasa ka goge stubborn boy, give me the other hand jor nagani" ya saki hanun daya shafamawa zai karbi right hand din yashafa, turamai baki Aliyu yayi yamika mai karba Dady yayi yace "and on Monday zakai resuming office and take up your responsibility am I clear" "uhmm" yafada ahankali, sakin hanun Dad yayi yace "jeke saka kaya to yaron Dadyn shi" Dady yay maganan yana murmushi hanyar wardrobe dinshi yayi shikuma Dad Yajuya yafita daga dakin.






_Suleja_
Motar datagani Honda pake kofar gidansu yasa taji gabanta yafadi ahankali tafito daga keke napep din taciro kudinshi naira dari tamikamai karban kudinshi yayi yaja keken yay gaba, ahankali take daga kafafun ta tana kara kakkabe hijabin dayay butu butu da kasa ta shiga gidan da sallaman ta, ahankali tana kallon tsakar gidansu da aka shimfida babban tabarma wasu maza magidanta guda biyu zaune kan tabarman duk sun kafeta da ido saikuma Ammi datagani zaune kan yar kujeran tsakar gidan abakin kofar dakinsu idanunta sundanyi ja sosai kaman wacce taci kuka tagodema Allah, ganin yanda Aneesan ta tsaya chak ita bata gaidasuba ita bata karaso cikin gidaba yasa Ammi tace "bazaki shigo ki gaida Baffofin kiba kin tsayawa mutane aka kina kallon mu kaman kinga dodanni" dan murmushi tayi akunyace dan yanda taga idanun Ammi yasa ta manta da kowama dake tsakar gida kanta akasa ta shigo har cikin tsakar gidan gaban tabarman su ta tsugunna tana wasa da bakin hijabin ta ahankali tace "ina kwana Baffa, ina kwana Kawu" mutanen duk kamaninsu daya saidai kana ganinsu zaka gane wa da kani ne daya yafi daya manyanta babban cikin ne wanda suke kira da Baffa wanda tunda ya shigo yake kallonta ahankali yadaura hanunshi saman kanta yana kallon fuskanta yace "Fatima, zauna dakyau" yay maganan yana kallon yanda ta tsugunna sabida karta gaji, gyara zama tayi ta zauna kan tabarman inda yake nunamata da kyau tana gyaggyara hijabi ganin ta natsu yasa yace "tuntuni mukazo mahaifiyar ki tacemana kinje kasuwa mun tsaya mugakine kafin mukoma kadunan, ya kike Fatima?" kanta akasa tace "Alhamdulillah Baffa ina lafiya" kunyanshi takeji sosai bana wasaba, murmushi yayi ya gyadamata kai yace "Allah yamiki albarka kinji ko," gyadamai kai tayi tace "Ameen Baffa, nagode" gyadamata kai yayi shima yace "ki kula da kanki kinji, ki tsare mutuncin ki, ga mahaifiyar ki nan kidinga mata biyayya kinji, in sha Allah zan kokarta nadinga zuwa akai akai ina dubaki ko dayake mun riga mun gama wanan maganar da mahaifiyar ki" dayan magidancin ya kalla yace "mikomin wanan jakan Sani" yar babban jakan dake kusa dashi magidancin yadauka yamikamai karban jakan yayi yabude ciki kwalin waya na Tecno pop2 yaciro yamika mata yace "ga wayanan nakawo miki kome kike bukata ki kirani kinfadamin kinji koda bandashi duk randa Allah ya horemin zanyi miki, sanan ga wanan" yasaka hannu a aljihun riganshi yaciro kudi yan dubu daidai har na dubu bakwai ya mikamata, ahankali tasa hannu ta karba yace "naji amfara registration din jamb kije kibiya muga ya Allah zaiyi kafin nan dawani tsayayye yafito mu aurar dake, kije kibiya cikin satinan dan naji ance idan kabiya dawuri ana turaka center a garinku ko Sani?" gyadamai kanin nashi yayi yace "eh hakane Yaya" kallonta yayi yace "masha Allah kije kiyi kinji, gakuma wanan" ya kara mata dubu uku yace "ki ajiye kidinga kashewa ahankali ahankali kinji Fateema, Allah yamika albarka, Allah yamiki albarka, dawata matsalan?" girgizamai kai tayi ahankali tace "babu Baffa, nagode Allah saka da alkahairi, Allah amfana" murmushi yayi sosai yace "bakomi kidena min godiya Fatima ni mahaifinkine so kidenamin godiya kinji, zamu tafi yanzu kome kikeso ki kirani kifadamin ga wayanki

Please Login or Register in order to submit comment