Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bugawa not knowing what to do, ringing dataji wayarta nayi yasa ta kalli Jakarta da sauri zata ciro jakan tabude tacire wayarta aka wani irin danna mata horn daya mugun tsorata ta dan atsakiyan titi take, da gudu ta koma baya duk internal organs dinta na rawa ta jingina da wata mota, zip din jakarta ta zage ta ciro wayar data shiga kuka akaro na biyu ganin number Ammi ne yasa taja tai picking da sauri takara a kunne, kafin ma tai magana Ammi tace "bakisan dare yayi bako Aneesa, mena cemiki? Banace miki duk inda kike ko a ina kike kidena kaiwa magriba ba? Once kinga hudu tayi start preparing to come back home ba abinda nasha fadamiki kenan ba?" Ammi takarashe maganan tana mata ihu dayasa jikinta yakama rawa, in this world Ammi is her best friend yet babu masifa da fadan wacce take tsoro aduniyan nan irin na Ammi, intai laifi Ammi na fada har kuka take dudda batada yawan kuka amma wani zubin kafin ma Ammi tafara fadan tafara kuka tsabagen tsoron fadan Ammi. "ninake miki magana kikamin shiru Aneesa?" da sauri ta girgixa kai bakinta har rawa yake tace "Ammi wlh bahaka bane, nama fito but kafin nazo driver yafita kuma ina waje, Ammi am sorry" jin yanda muryan ta ke rawa yasa Ammi tadan sassauta karta rudata tace "to kikoma kice musu driver yafita susa wani yadawo min dake gida dare nayi yi maza" da sauri ta gyadakai tace "tom" ta katse wayan tajuya da sauri tai hanyar gidan, wasu manya manyan security har guda hudu tagani agaban gate din wanda basu dazu data fito, duk mutanen dazasu shiga gidan saisun nuna musu wani abu dabata san kome ba sai taga sun matsa musu sun wuce ciki gashi kida sai tashi yake, karasawa tayi suka sha gabanta. "Madam show us your invite?" da sauri ta kalli wanda yamata maganan kaman wacce bata iya magana ba ararrabe tace "I...n...v..ite?" gyadamata kai yayi yace "yes your event pass, show us" da sauri tace "amaryan zan gani nice mai lallen su" "we don't know dat one madam kindly leave here if you don't have invite, only invitees can grace this occasion, sorry Ma" yay maganan while sauran na duba invite din wasu suna basu wuri suna shiga, kallon abinda ake nuna musu tayi taga katin bikin amma wani hadadden dan karami ne. "madam kindly leave, this event is strictly kan wayanda aka gayyata, leave so that we will not have to force you leave" yanda yamata maganan yasa yasa tajuya ahankali, hankalin ta dukya tashi komawa tayi jikin motan data tsaya dazu taciro wayarta hanunta na rawa sosai tai dailing number Ammi tana sake shigewa dan lungun space din in between car to car dake pake a wurin, ta tsugunna ahankali, picking call din Ammi tayi hakan yasa taji wani kuka yazo mata dabatasan daga ina yazoba, sakin kukan tayi sosai hakan yamugun dagama Ammi hankali. "innalillahi, ke Aneesa, are you okay? Maiya faru? menene kike kuka? Talk to me dena kukan kinji, Aneesa menene?" cikin kuka sosai bakinta na rawa tace "Am... Ammi anhanani shiga gidan, ansa security a kofar gidan saika nuna ID card din bikin za'a bari kashiga ni bandashi basu barni na shiga ba?"




Addu'o'i Ammi takaranto aranta danji tayi tamafi Aneesan shiga damuwa, yanzu idan wani abu yasame ta ubanme zata fadama yan uwan babanta da dama jira suke batayi bama sunce tayi balle kuma tayin, ajiyan zuciya ta sauke ahankali ta kirata. "Aneesa" ahankali tace "uhm" "stop crying, kinsan sunan anguwan dakike?" girgixa mata kai tayi tace "a'a bansani ba" "kina inane yanzu haka?" cikin crying voice tace "ina lungun motocin da akai parking a anguwan kaman na yan biki ne" "okay, fito to duk wani wanda kika gani kibashi wayan nai magana dashi naji a anguwan dakike, a ina kika sami katin waya haka naga bai kareba har yanzu?" cikin kuka tace "amaryan ta turamin dazu" "okay tashi duk wanda kikagani kibashi wayan to" tashi tayi ahankali tana goge hawayen daya gama batamata fuska tafito daga lungun motar ta tsaya abakin hanyan tana kalle kalle babu kowa sai security dake bakin Gate har lokacin saikuma tulin uban motocin yan biki kowa na ciki kida na tashi da alamun event din ya kankama ne, ganin ba kowa yasa taji wani kukan yazo mata tsugunnawa tayi a wurin wayar na kunenta tarufe fuskarta da hijabi tana kuka sosai, a rude Ammi tace "menene bakiga kowa bane? Stop crying mana kina dagamin hankali wlh" gyadamata kai tayi cikin kuka tace "Ammi babu kowa" tasake fashewa da kuka hankalinta yatashi ainun bamatasan mezatayi ba, batasaba yin dare hakaba a ko ina, dama ace Suleja ne tasan ko ina dakoda kafane saita dandaro, koma bahaka ba anyhow anyhow she wi definitely find her way back home, but nan babu inda tasani, batasan cikin Abuja ba batasan ko inaba, Brain dinta yagama chuchewa. "Hi Fearless lady" wani sassanyar murya, very cool, calm yet husky murya yadaki dodon kunnuwanta, Ammi dahar lokacim take kan waya tace "naji muryan wani bashi, bashi wayan namai magana da sauri" dago kai tayi ahankali tasa hijabinta tana goge fuskarta dayan hanunta kuma tamikama mutumin da bama ta kallaba wayarta da mistakenly hanunta ya danna speaker. "Bawan Allah dan girman Allah help my daughter, batasan ko ina a Abuja ba, wanda yakamata yadawo da ita kuma yatafi, please ka taimaken badan niba dan Allah kasata ahanya, koka kaita bakin titi koka sata a hanyar dazai sadata da main road tanemi motar dazai kawota Suleja, please help a mother, am so worried, dan girman Allah help my daughter, kasamin ita a hanya dan Allah tadawo gida kar y'ata tabata kaji bawan Allah" yanda taji Ammi narokan mutum itama kanajin muryanta kasan tana cikin tsananin damuwa yasa taji wani sabon kukan yazo mata kaman wacce akama mutuwa tacigaba da kuka kaman tata takare aduniya da karfi, jin kukanta yasa Ammi tace "hello Aneesa me kuma kike kuka eh, karki damu dazaran kin fita titi zaki sami motan Suleja, inma baki samuba nima zan taho na dauke ki dakaina, bari na nemo yaron Hadiza mai keke napep na makotan mu, dena kuka babu abinda zai sameki okay kinajina, stop crying Aneesa, stop" Ammi tafada cikeda lallashi cikin kuma tsananin damuwa, gyada kai tayi tana shashshare fuskar da Hijabi tana kokarin hana kanta kukan, katse wayan yay ahankali yana kallon yanda take share fuska da Hijabi, ahankali yakai hanunshi yadaura kan hanunta dake saman kan fuskarta wani irin sanyi taji tundaga kan feet dinta har zuwa kwakwalwanta, ahankali yakama hanunta gam wani irin hannu mai taushi taji dakeda sanyi sosai, ahankali tadago kanta in a very slow and steady motion, hada ido sukayi da Aliyun dake sanye cikin wani fitinannen white magic gizna dake wani mahaukacin kyalli anmai aikin hannu a kayan, yana wani irin cool kamshi dakesa kaji zuciyarka ta natsu, da sauri ta lumshe ido dan her eyes couldn't stand haske da haiban dake tattare dashi takai almost one minute ahaka ita bata karbe hanunta ba ita batai motsi ba ita bata bude idoba shima kuma haka, hanunta dataji yaja ahankali yafara tafiya da sauri tabude idanunta, samun kanta tayi da daga kafa tana binshi gaban wani Brabus jeep dat is directly opposite to lungun motar datake tsugunne tun dazu yakai ta yabude gaban motan zai sata ciki tsayawa tayi chak tafashe da kuka sosai ta fizge hanunta tace "ina zaka kaini niban sanka ba?" shiru yayi yana kallon fuskarta kaman yasami tv batare dayace komiba itakuma sai kukan takeyi takasa kuma matsawa konan dachan sanan kuma taki shiga sunkai almost 5 minutes ahaka wayarta dake hanunshi har lokacin ne tahau kara da sauri ta kalli wayan, janye idanunshi yayi daga kanta ya kalli screen din wayar ganin sunan kan screen din Ammi yasa ya kalleta ahankali yace "get in" yanda yamata maganan ba wasa sanan kuma ba tausayi yasa tasami kanta ta daga kafa tazo har gabanshi inda yake tsaye rike da marfin motan tana share hawaye tai bismillah ta shiga cikin motan, hijabin ta data saki yafito daga motan ya kalla ahankali yatako ya tsugunna da sauri ta juyo ta kallai hada ido sukayi yana wani irin kallonta, sosai gabanta ke faduwa kaman zai fito gashi takasa janye idanunta daga kanshi kaman eyes dinshi are compelling her to look at him by fire by force, ahankali yake tattaro hijabin batare daya dena kallonta ba tattarawa yayi ya dunkule yadaura asaman kan cinyarta, da sauri ta kalli kan cinyar nata jin hanunshi akai hijabinta tagani ya tattaro ya ijiye mata mikewa tsaye yayi yamaida kofan yarufe ahankali sanan yazaga yana tafiyan nan kaman baiso yayi yabude dayan side din ya shiga tareda rufo kofar yaja sit belt dinshi yana sawa batare daya kalleta ba yace "fasten your sit belt" juyawa tayi tanajan igiyan sit belt din da karfi amma yamaki fitowa sai fama take hakan yasa ya juyo ya kalleta ganin yanda take fama da sit belt din yasa yacire nashi yataso daga kan kujeran shi ya matso da kanshi ta gabanta wani irin sakin sit belt din tayi da gudu ta makale jikin kujeran, yanda takejin kamshin turaren akan fuskarta yasa numfashin ta yafara fita da sauri da sauri kaman zata kurma ihu, hanunshi yadaura kan sit belt din yaja ahankali yana wani irin kallon fuskarta shi kanshi baisan mesa yake kallonta hakaba and anytime ya kalleta the beating of his heart use to change. "m....me ha..k...haka?" Aneesa tai maganan muryanta na breaking sosai, makala sit belt din yayi yakoma inda yake tareda sauke ajiyan zuciya he's not just himself da sauri ya kunna motar yay reverse yaja yafara gudu, ringing da wayar Aneesa yafara yasa ya kalli wayar ganin Ammi ne ya mikamata wayan yace "answer d call, tell her you are on your way".




_anan nakawo karshen free pages. Duk wacce takaran tamin littafin batare data biya dari uku ba nabarta da Allah ban yafe mataba duniya walahira_

_duk maison cigaba da karanta littafin ATSAKANIN SOYAYYA zata tura naira dari uku kacal ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461, saina saka ki a group din danake posting_

_wayanda tun kafin ma nakawo karshen free pages suka biya nagode Allah barmin ku, trust me zakusha dadi a book dinga, M Shakur mai sabon salo ce kuma kunsani Always!!!_

_ku tuntubeni kan wata magana ko business ta nan 07012181461_
[18/02, 18:01] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



1️⃣5️⃣


_how to subscribe_

_Zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting. Zaki iya turo MTN card 300 ta watsapp number na idan baki da bank_

_littafin nan na kudi ne duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafe mataba, pay anan ko pay a lahira your choice 🤷🏿‍♀️_




Fuskarshi ta kalla ganin driving dinshi yake hankalin shi nakan hanya yasa tamika hanunta dake rawa sosai ta karbi wayan tai picking takara akunne. "Aneesa kina ina yanzu?" ahankali tace "muna hanya" da sauri Ammi tace "mutumin ne zai kaiki?" gyadama Ammi kai tayi ahankali tace "eh shine" dan ajiyan zuciya Ammi tasauke tace "to Alhamdulillahi, dazaran kunkai bakin titi akwai Motocin Suleja dayawa saiki shiga kinji idan kin shiga ki kirani ki sanar dani kinji, kidena kuka babu abinda zai saman mini ke okay" gyadama Ammi kai tayi tace "tom" katse wayan Ammi tayi hakan yasa ta janye wayan daga kunenta ta ijiye akan cinyarta tana sauke ajiyan zuciya, ganin sun shigo kan titi yasa ta kallai ganin har lokacin hankalinshi nakan titi yasa tadan gyara murya danji tayi muryan ta yadishe sosai sabida kukan datayi, ahankali tace "uhhhh anan, anan kan titi Ammi na tace na sauka" dan juyo dakai yayi ya kalleta suka hada ido dan lumshe ido kadan yayi yabude kafin ya maida hankalinshi kan tukin dayake yi batare dayace mata komiba, ringing da wayarshi yayi yasa ya kalli wayar dake ajiye gefen shi ganin Abdul ne yasa baiyi picking ba dan yasan nemanshi yakeyi, saida yasake kiranshi akaro na biyu sanan yadaga wayan yakara akunne yay shiru. "where are you Leo? Nafito banmaga motanmu ba don't tell me kakoma gida, waikai wani irine eh fisabilillahi fa, he's our friend fa, haka kakeso amana ranan bikin ka eh? Duk abokanen ka suki zuwa sabida baka zuwa nasu?" dan yatsine fuska yayi yace "kacikani da surutu am driving fa" "driving? Driving to where?" dan murmushi yayi kadan yace "idan nadawo we will talk, am tired yanzu" ya katse wayar yamaida kan cinyarshi, ta gefen ido yaga sai share hawayen dasuka shiga zubo mata takeyi hakanan batasan mesa taji tana shakkanshi ba, takasa mai magana dudda batasan inda zai kaita ba, kuma gashi Ammi tace akan titi zai sauketa tahau motan dake kawo mutane Suleja, itadai yau tata takare, bata tabayin dare haka awuriba, tunanin hakan yasa hawaye sai zubowa daga idanunta suke, dan murmushi yayi yasa hanunshi a aljihu yazaro wani clean soft handkerchief dake wani cool kamshi yamika mata, kallon handkerchief din tayi kafin tasa hannu ta share hawayen dake kan fuskarta ta girgizamai kai batare data karba ba alamun a'a, ajiye mata handkerchief din yayi akan cinya yamaida hankalinshi kan tuki fuskarshi nakan hanya, sai share hawaye take dasunki tsayawa saida taga wani signboard an rubuta Suleja 20km yasa tai wani irin murmushin kuka, juyawa tayi da sauri ta kallai juyowa shima yayi ya kalleta dawani irin calm look da yatsar shi yamata pointing handkerchief din dayabata dake kan jikinta, da sauri tadauki handkerchief din ta share fuskar ta tass tareda sauke wani irin ajiyan zuciya mai kara dahar saida yaji, dan murmushi yayi ganin yanda ta natsu dataga sundau hanyan gida.

Gudu yake sosai basu wani jimaba ya kai Sulejan sanan yarage gudu yadan kalleta cikin calm voice dinshi yace "show me the road to your house" gyadakai kai tayi tasa hannu tana nunamai hanyar yanata bi har sukakai anguwan su, a kofar gidansu ta hango Ammin su tsaye sanye da dogon hijabin ta hanunta rikeda waya, da hannu tamai pointing Ammi tace "ga Ammi na nan" rage gudu yayi tareda rage karfin wutan gaban motan sabida karya haska Ammin sosai tun kafin yay parking tawani irin bude motar da gudu tai wajen Ammi data tsare motar da kallo. "Ammi, Ammi, Ammi" kafin Ammi tace ma wani abu taje da gudun gaske tai tsalle ta rungume Ammin kaman wacce tai shekara bataga Ammin nataba, rungumeta tight Ammi tayi tanama Allah godiya. "Alhamdulillah" kafin ta dagota daga jikinta takama habarta da hannu daya tasa dayan hanunta tana share mata fuska tace "Alhamdulillah Allah nagode maka, you are ok ko Aneesa na?" hannun Ammi ta rike tareda gyada matakai tana murmushi hakan yasa Ammi tasake sata ajikinta ta rungumeta, shiru yayi ya tsaya a mota yana kallonsu, looking at affection din Ammi towards Aneesa yasa yaji he just wish Mummy shi was alife to hug him like this, he miss his mum so so sooo much, lumshe ido yayi ahankali zuciyanshi namai wani irin zafi.





Ahankali yajinginar da kanshi da kujera kirjinshi namai wani irin zafi, knocking glass din motar da akayi yasa yabude ido ahankali, Ammi yagani tsaye rungume da Aneesa a gefenta, ahankali ya bude kofar shibai masan mezaiyi ba yadai sami kanshi da kasa daga fuskarshi ya kalleta zaiyi magana Ammi tarigashi. "nagode, nagode bawan Allah, yanda ka taimaki Aneesa Allah ya taimaka maka adukkan al'amuranka, Allah ya haskaka rayuwan ka, kakawo mini ita har gida safe and sound, thank you so much, may Allah reward you abundantly" kasa ma magana yayi sai gyadamata kai da yayi ahankali, ganin haka yasa Ammi tadan bugi kafadar Aneesa da kanta ke kasa tace "bakimai godiya ba Aneesa" ahankali tajuyar da kanta ta kallai har lokacin kanshi akasa dauke idanunta tayi daga kanshi ta maida kan yatsunta data shiga wasa dasu ahankali tace "nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi" murmushi Ammi tayi tace "mun gode malam saida safe, wuce mutafi Aneesa" jan hanun Aneesan tayi tasa key tabude kofar gidansu dahar ta kulle ta shiga, dan waigawa Aneesa tayi tasake kallon motar dudda bata iya ganinshi daga wurin amma saida gabanta yafadi da sauri ta shige ta maida kofar tarufe, sukai cikin gida, falo suka shiga ta ijiye souvenir da akabata akasa ta zauna kusada Ammi tana bude jakanta tace "Ammi barina saka chaji tunda akwai wuta, yautun safe bansama wayata chaji ba" ciro wayar tayi daga jaka tana kokarin kunna wayar kwan lantarkin falon yawani irin yin kara ya tarwatse da gudu tarike Ammi sabida tsoron dataji, salati Ammi tayi. "innalillahi tome kuma yasami kwan lantarkin ko karfin wutan yay yawane?" tai maganan tana kunna wutar toculan wayanta ta haska wajen wutan taga yanda yafashe, tsaki Aneesa tayi tace "Ammi dama wanan na dan dari uku baida kyau energy bulb yafi wanan yan darin dakike siyowa kyau, anmafa ce baya jan wutafa, bari naje nasiyo" tai maganan tana zage handbag dinta ta kwaso duka kudin da aka bata ta mikama Ammi tareda zare dubu daya ta mike tsaye tareda daukan hijabinta, Ammi dakebin kudin da kallo tace "wayabaki kudi dayawa haka Aneesa?" dan dariya tayi tace "amaryan tabani wai kudin lallena bari nadawo nabaki labarin abinda ya faru yau" dubu biyu Ammi tazaro cikin kudin tamika mata tace "gashi ki shiga gidan Maman su Muhammadu kice nace gashi injini" karba tayi tace "to" tawuce tafita daga dakin tana haskawa da wayanta dan tsakar gidansu dama babu fitila, bude kofar gidansu tayi tafita tana haska kudin hanunta da waya tacire dubu biyun tarike su separate sanan ta shiga gidan dat is next to them inda Ammi ta aiketa ta mika kudin tafito tana kalle kalle, idanunta ne suka sauka akan motan daya kawota ganin har yanzu motan na wurin baitafi ba, faduwa da gabanta yayi yasa tasauke kai da sauri ta dena kallon motar, tsallakawa tayi dayan side din tai wajen wani shago dayake chan gaba kadan, ta shiga tasayo kwan lantarkin mai kyau nadan dari biyar sanan tajuyo tanadan satan kallon motan tana tafiya towards there house, sosai mamaki yakamata ganin har lokacin motan na wurin tai hanyar kofar gidansu tana kallon motar, hannu tasa zata bude kofar gidansu saikuma ta janye hannun tasake juyowa ta kalli motan to kodai baida lafiya ne? Mutumin da tun dazu yakawo ta aiya kamata ace yatafi by now, in fact yamayi nisa ahanya, kasa hakura tayi ji kaman wani abu na fizganta tafara tafiya so take kawai taduba shi taga ko lafiya, ahankali take tafiya tana kallon motar kafin takarasa gaban motan taga yabude kofan motar hakan yasa ta tsaya chak takasa karasawa tadan kwantar da kanta tana lekawa, ahankali yasa kafarshi yafito daga motar yamaida kofar motar yarufe tareda jingina da motar ya rungume hannayenshi a kirji yana kallonta, faduwa gabanta yayi sosai sabida yanda idanunsu suka hadu da sauri tajuya zata koma ya kira sunanta for the first time. "Aneesah!" tsayawa tayi chak jin yanda yakira sunanta har ranta taji kiran sunan saida duka organs din jikinta suka amsa, murya chan kasa ta yanda ita kadai ne zata ijiyajin meyace calmly yace "come" sosai takejin maganan shi nazuwanma zuciyanta kaman command, kasa jurewa tayi tajuyo ahankali taa kallai, gyada mata kai yayi tareda dan lumshe ido sanan yabude su yadaura akanta, daga kafa tayi ahankali tataho wajen kanta akasa ta tsaya agefen shi kafafun ta nadan rawa sabida wani sanyi dasuke mata da batasan nameba, juyowa yayi yay facing dinta yana kallon yanda take wasa da kwalin kwan fitilan hanunta, murya chan kasa yace "ina kikaje?" batare data kalleshi ba kanta akasa tace "kwan lantarki naje nasayo" shiru yadan yi kafin ahankali yace "maisa baki aiki brother kiba yaje kika fito da dadaddare?" kanta akasa tace "uhm banda brother" "ke kadaine?" yatambaye ta immediately bayan tai maganan, gyadamai kai tayi batare datai magana ba, ahankali yace "what about your Dad?" dago kai tayi ta kalleshi hada ido sukayi da sauri ta maida kanta kasa, ahankali cikin wani irin siriruwar murya tace "yarasu" sosai kalman yarasun yadaki zuciyan shi hakan yasa yay shiru yana kallonta sai chan yace "sorry! Allah ya jikanshi" gyadamai kai tayi kaman zatai kuka dan sosai tuna mata da Baba, ahankali tace "Ameen" sukadanyi shiru batare dawani daga cikinsu yakara cewa wani abuba, dan dago kanta tayi ta kallai ganin ita yake kallo har lokacin yasa tace "in tafi?" girgixa mata kai yayi yace "No" tsayawa tayi duk tanajin wani iri yanda ta tsaya dashi danko kadan bata saba tsayawa da samari ba ita bamata dawani saurayin kirki dan batabasu lokaci. "me kikaje yi agidan bikin nan?" hanunta ta shiga wasa dashi kanta akasa tace "lalle naje yi musu" "lalle? You mean henna? Are you a henna designer?" gyadamai kai tayi tace "eh, na iya" dan murmushi yayi yarinyar nan bala'in burgeshi take bana wasaba, shidai in his life this is the first girl daya taba gani dayaji ta burgeshi, dago kai tayi ahankali kaman wacce take tsoron ta kalleshi tadan kalleshi tace "ya kanwar ka?" dan shiru yayi kafin yadan juyar da idanunshi cikin jin dadi yace "oh Rauda? Dama kin ganeni?" gyadamai kai tayi da sauri tace "eh tundazu ai naganeka, kunyi kama ai da ita saida kafita uhmm...uhmm" muryan ta ya sarke sotake tace yafita kyau amma takasa fadi hakanan taji tanajin kunyan tace mai haka, murmushi yayi sosai ganin takasa fadin abinda takeso tace mai, murya chan kasa cikeda zolaya yace "ashe kin iya kuka haka I tot mara tsoro bata kuka eh Fearless lady?" rufe fuskarta tayi da hijabi da sauri tareda yin murmushi akunyace tai gaba zata wuce dan maganan ta ya mugun bata kunya da sauri yace "wait" tsayawa tayi chak batare data juyowa ba sai murmushi take ya mugun bata kunya, cikeda murmushi tace "wat? kaga Ammi na zata zo tanemeni yanzu nan" tafiya daidai yake hanunshi zube cikin aljihu harya tako ya tsaya abayanta chak, yanda tajishi abayanta yasa taji numfashinta na neman daukewa da sauri tajuyo sukai facing juna yanda taga yana kallonta yasa taji takasa magana sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri heart dinta is beating way too fast kuma batasan mesaba sai kyafkyafta ido take, one step yakara ya matso gab da ita ahankali yace "can we be friends Aneesah?"





Ba karamin faduwa gabanta yayiba jin kalaman dasuka fito daga bakinshi, rawa lips dinta yafara tanadan zaro idanu zatai magana yamika hanunshi ya karbi wayanta dake kan hanunta ya bude ganin ba key, danne danne ya shiga yi kafin ahankali yamika mata wayan yace "take" hanunta tamiko ta karbi wayan da sauri tajuya tai cikin gida tarufo kofa, hakanan yaji ko kadan baiji dadi data tafiba kaman yabita, komawa cikin mota yayi yabude ya shiga, kifa kanshi yayi akan starring mota ya fuzar da iska he seriously don't know what's wrong with him, tun daga fitowan Aneesa daga gidan bikin tareda Nihal idanunshi suka sauka akanta lokacin yana tareda Abdul a cikin mota, Abdul yacemai sutafi yace yaje shizai shigo anjima, haka ya dinga kallonta ta mota har lokacin databi motan su Lado da gudu da lokacin data shige lungun mota da lokacin data fara kuka tana waya, shidai baisan mesa ba he just love natsuwar yarinyar, yanda take tafiya a natse, da yanda take magana a natse, da yanda muryanta ke fita so gently and innocently bala'in burgeshi yake, boldness din yarinyar use to melt his heart, bai taba ganin yarinya dat match his taste like her ba, hakanan yaji he just wanna be her friend, a girl like her is worth associating himself with, wayarshi dayay kara yasa

Please Login or Register in order to submit comment