Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganowa dayayi yanzu darene a Nigeria probably hala Dad yay bacci saisa bai kirashi ba.





8:40 na dare jirgin su yasauka a Abuja, fitowa sukayi kana ganinshi kasan yagaji sosai saukowa suka farayi bodyguard dinshi biyeda shi, wuraren Tara suka gama komi suka fito ta arrival sai kalle kalle yake ya tsaya chak dan baiga wani nashiba baiga wani direban gidansu ba baiga Daddy ba, wani irin haushi ne yakamashi yamikama bodyguard hannu alamun yabashi wayarshi, karban wayan yayi dayariga ya kunna mai ya shiga dialog Dan kiran Dad dinshi, fizge waya yaji anyi daga hanunshi da sauri yadago kai wani magidanci ne kamansu daya sak dan shima farine sol alamun tsufa daya bayyana tattare da magidancin ne zaisa kawai kagane ba yan biyu bane uba da d'a ne, dudda fushi yake da Dad amma baisan lokacin dayasaki wani murmushi ba yawani irin rungumeshi ba so tight yace "Daddd dy" murmushi sosai mutumin yayi yana bubbuga bayanshi yace "na'am Aliyu na, sarkin zuciya, Aliyu an mazajena" dariya daga shi har Aliyun sukayi sanan yasake shi ahankali yana kallonshi kaman yanda yake kallonshi yace "muje kahuta kagaji da yawa karka fadi" sukai wajen mota bodyguard na binsu abaya, motoci biyune bodyguard suka shiga dayan Daddy da Aliyu kuma suka shiga motar Daddy, kwanciya yayi ya daura kanshi kan cinyar Dad yana yatsine fuska, kallo baban nashi ya binshi dashi yana mamaki yaushe Aliyu zai chanza yadawo namiji, son jikinshi da rashin kuzari is too much, hanunshi ya chusa cikin kanshi yana mishi head massage yace "sannu kaji Son kagaji sosai ko?" gyadamai kai yayi idanunshi a lumshe yace "bakaine kawani ce mutum yadawo ba, I need hot bath jikina kaman an kakkaryani Dad" "tooofah, sannu yaron kirki, muna zuwa gida zakai wanka kaci abinci saikai wanka abinka" gyadamai kai yayi a shagwabe yana sauke ajiyan zuciya yanajin dadin yanda Dad kemai headmassage din.





Agaban wani babban gida sukai horn wani soja yabude musu Gate din, tashi yayi ahankali ya zauna yana kallon babban gidan nasu da babu kowa a ciki, shiga ciki sukayi sukai parking bude musu kofar motar akayi, ahankali suka fiffito daga motan yana kallon gidan, babban gidane dake dauke da manya manyan flat flat guda hudu, sai daga tachan dayan bangaren kuma wani babban flat guda daya ne, shidai babu yanda zaiyi da Dad ne amma harga Allah baison dawowa Nigeria ba, ya tsani gidan mahaifin shi sosai, he hates this house with all his heart, dafashi da akayi yasa yadaga kai ya kalli Dad din yadan turo baki kaman mai shirin yin kuka, murmushi Dad yamai tareda sumbatan goshinshi yace "all is well Aliyu am here for you kaji relax, muje" gyadamai kai yayi suka fara tafiya bodyguard kuma nawajen mota suna fito da kayayyakin su daga boot, wata yar budurwace doguwa dabazata wuce 20yrs ba sanye dawata doguwan rigan atampa tafito daga wani daki dasuke kira da laundry tariko wani white folded zanin gado a hanunta tajuyo, ganin Aliyu tareda Dady yasa ta tsaya chak tareda bude baki cikeda mamaki danko kadan Dady bai sanar dasu zai dawoba, tsayawa Aliyun yayi shima yana kallonta da idanunshi dake cikeda gajiya, murmushi Dady yayi yace "gata wajenka nan ai banfada mataba I want to surprise her taganka kawai kaman daga sama" murmushi sosai yayi yana kallonta batare dayace mata komiba ya daga mata gira daya alamun kallon fa baki sanni bane? Watsar da zanin gadon tayi akasa tsabagen rudewa tasa hanunta takai kan saman idanunta ta murza idanun irin ta kara tabbatarwa ba gizo idanunta kemata ba sanan tabude su, tagadai still dai yana tsaye inda yake kusada Daddy dake sanye da babban riga that means Yaya Aliyun tane, wani irin ihu tayi dayacika gidan. "Yaya Aliyuuuu, Yaya Aliyu oyoyo" ta tafi dawani irin mugun gudu hakan yasa yabude mata hannu da gudu taje tai wani irin tsalle tafada jikinshi ta rungumeshi sosai her heart couldn't contain her happiness sai kuka, hakan yasa Dady yace "kagamin shagwababbiyar yarinya, kin wani dane jikinshi zaki karyamin shi saikuma ki sakinmai kuka dukshi kadai, haukatashi kikeso kiyine daga dawowan shi, cikashi" kojin maganganun Daddyn suma batayi sai kuka take bayanta ya shafa ya bubbuga alamun tai shiru, jin karan bude buden kofofi wanan nabin wanan yasa yadago kai matayen Dadyne kowacce tadan leko dakai daga flat dinta ga yara manya da kananu duk sunaso sufito suga ihun mai akeyi a tsakar gida sun hanasu fita, fuskarnan bayabo ba fallasa duk sai kallonshi suke kaman yau suka fara ganinshi, babban cikin matan ne tadan tabe baki tace "ahhhh manyan baki su Aliyu ne agarin, mutanen turai saukan yaushe ko sanarmana ba'ayi ba, hala cinye dan gwal din zamuyi maigida" tasake tabe baki tana kallon Rauda da har lokacin ke rungume da Aliyun tace "sannu da zuwa Aliyu, kekuma ina zanin gadon danace kikawo min uwar shishigi?" kafin Rauda tai magana Dad yace "ahadama Aliyu lafiyayyen abinci Kareema" dan juya ido tayi tace "haba Alhaji saida abinci yakare kasan yawan yaran gidan nan gasuda shegen ci barin ma yaran Amaryan ka, aida kafadamana zaizo dasaimu saka dashi a girki, shi yaro kasan bacin abincin yan aiki yakeba dasai ace suhadamai koyar Indomie ce, kaga kumani wash Allah" tadan yatsine fuska tana dafa kafarta tace "kasan ina fama da wanan ciwon kafan bazan iya shiga wani kitchen ba Alhaji sanyin kashi dazaran dare yayi saidai kaji kasusuwana nakiran salla" shiru Dady yayi yana kallonta baiso yay hayaniya agaban Aliyu da dawowan shi kenan baiso yatadamai da hankali da sauri Rauda ta tashi daga jikin Aliyun tace "nizan ma girki kaji yayan mu, maizan dafama?" kafin ma yay magana Kareema tace "wai bazaki wuce kidau zanin gadon chan dakika watsar akasa kije ki shimfidamin agado ba" wani mugun kallo Daddy ya watsa mata yace "kije ki dauka dakanki, girki zatama dan uwanta" Daddy ya kalli Raudan datai zuru zuru dan tsoron masifar uwarta take Yace "wuce je store ki dauko all abunda zakiyi amfani dashi kizo side din Aliyun kiyi girkin awajen" gyadamai kai tayi tace "to Daddy" tama Ya Aliyun murmushi tajuya da sauri tawuce, Dady ya kalli sauran matan biyu dasuka tsaya suna kallonsu yace "duk baku iya gaisuwa bako" ko wacce da kallan nata reaction din dasukayi da kyar sukace "sannu da zuwa Aliyu" ko amsasu Aliyu baiyiba Yajuya yay part hanyar side dinshi, Amaryan Dady mai suna Amina tace "yaro baisan ya gaida manyan Shiba saidai asa manya su gaidashi sabida sonkai, mumadai Allah bamu y'ay'a mazan nan, kuma kar wata takara kiran yarana " dan juyowa Dady yayi ya kalleta jin yanda take jefanshi da kananun magana ta shige dakinta baice komiba amma wlh duk zasuci ubansu yasan maganin su, shida sune su zuba indai kan Aliyun dudda sun haifamai yara zai iya sakin yan bura'uba yakawo nany su kulamai da yaranshi, billahillazi duk wanda zai tabamai Aliyu marayan danshi nan mara uwa sai yay yakin biafra da mutum.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



4️⃣


_how to subscribe_

_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_

_*Zaki iya turo katin MTN 300 ta WhatsApp number na sainai adding naki a group din danake posting*_



_Free page_


Bangaren Aliyun Dady yabude da wani card, ya shiga Aliyu dake tafiya ahankali biyeda shi, hadadden dakine nagani na fada, an gyara komi tsaf sai shining furnitures din keyi dan Dady yasa an gyara komi, zama yake shirin yi Dady yace "a'a Son aje ayi wanka eh dan saurayin baban shi" gyadama Dady kai yayi kaman zaiyi kuka yay hanyar bedroom dinshi daidai lokacin Rauda tashigo falon rike da katon basket data lodo all abinda zatai amfani dashi tamai girki, ganinta yasa Dady ya washebaki yace "yauwa yar albarka, shiga kitchen ki hadamai" "to Dady" tace tana leken Aliyun dake shirin shiga daki, hada ido sukayi tasaki wani murna tawuce kitchen. Sea food pasta takeso tadafamai dazaiji shrimps sosai, ruwa tasaka a wuta ta rufe pot, sanan tasa wani pot a wuta tana hada tomato sauce, ruwan na tafasa ta zuba spaghetti danya tafasa tacire, in less than 30min tahadamai hadadden spag dayaji shrimps sai kamshi yakeyi.




Wani hadadden plate ta dauko ta zubamai tasaka a tray, tabude fridge dinshi taga akwai drinks masu sanyi dat means Dady duk Yasaka an saka, tadauko drink tadaura akan tray da glasscup goran ever water tafito, yana kwance afalo sanye da pyjamas farare yay filo da cinyar Dad suna hira kasa kasa dako ita bata iyajin abinda suke cewa sai murmushi yakema Dad, karasowa tayi dauke da tray taja table ta dauramai abincin akai ta zauna agefenshi tace "ci abinci yayan mu" tai maganan tana rikemai hannu, kanta ya shafa ahankali tareda yatsine fuska yace "is too hot I can't eat it bari yahuce, ya school Angel?" murmushi tayi sosai tace "fine Yayan mu, ina 100level computer science education, ni course din wuya yakemin Yayan mu sosai" zaiyi magana Dady yamike tsaye yana gyara babban riganshi yace "bari naje na watsa ruwa na kwanta tunda kun manta dani" dariya dukansu sukayi kafin ahankali yace "good night Dad" murmushi yayi yace "yauwa Yarana, saida safenku, dazaran tafara damunka da surutu ka kadota dan kasha gajiya ga Rauda aku kuturu ce" dariya tafashe dashi taboye fuskarta abayan Aliyu tace "Yayan mu ai banda surutu ko" dan murmushi yayi yace "don't mind Dad ya iya shairi" hararan su Dady yayi yawuce yafita daga dakin, abincin ya kalla yace "go and bring another fork let's eat together" , ware ido tayi saikuma tanunamai cikin ta tace "kar cikina yafashe ni nakoshi, ci karage saina rufe nakai kitchen" daukan fork din yayi yafara ci ahankali, kafeshi da ido tayi ganin yamata bala'in kyau, rabonta dashi kusan 1yr kenan yanzu, ya kara kyau ya kara kiba, yakara cika da zati, gadan gemun daya tara dan kadan dake shining tsabagen gyaran dayakeji, sosai tai nisa akallonshi bama tasan harya gamaba saida ya dungure mata kai sanan ta farga tareda kyalkyace dariya takalli abincin tace "harkagama harya isheka dan wanan zakaci?" ruwa yadauka yakai baki yace "yeah, am ok, dauka kikai kitchen kidawo" dauka tayi tai hanyar kitchen shikuma yacigaba dashan ruwan goran dake hanunshi, dawowa tayi tasake zama kusada shi kaman zata cinyeshi tun tana karama take mugun son Ya Aliyu, shima haka yakeji da ita duk cikin kannenshi itace ta isa tazo bangarenshi ta shiga ko ina tafito, tun tana karama inhar yana nan yana daukanta sufita yasiyo mata abubuwa dayawa sudawo, ita kemai girki ta gyaramai bangaren shi, da ita kadai yake shiri duk fadin gidansu, tashi yayi daga kan kujeran da sauri ta tashi itama, hanunta yakama sukai hanyar bedroom dinshi abakin gado ya zauna ya nuna mata daya daga cikin akwatunan da bodyguard suka shigomai dashi yace "take it to your room" wani irin murmushi tamai ta tashi da sauri tai wurin akwatin, zama tayi a kasa ta kwantar da akwatin tabude, turarukan matane guda hudu adan mini fine bag, sai wani kit da sauri ta dauka ta bude agogo verosky ne da bracelet dinshi, ihu tayi dan tadade tanason abun batada shi, sauran kayan kuma riguna ne masu kyau na mata ciki da singlets, cikin tsananin farin ciki ta dago kai dan tamai godiya taga haryay bacci yana saukar da numfashi ahankali.








Murmushi tayi ta kwashi kayan ta mayar cikin akwatin ta hadasu tsaf tarufe ta tashi takaraso gaban gadon daya ke kwance ta tsugunna ta kafamai ido tana tunani, sosai takeson Ya Aliyu sama da duka yan uwanta, su 21 ne yaran Dady, Ya Aliyu shine first born agidan, itama ta girma batasan maman shiba but Anty Hajar tasanta dan tana around 6yrs ta rasu, hawan jini yakasheta, Mama ta taba fadamusu Aliyu yakusan haukacewa da Ummin shi tarasu dan ya shaku da maman shi sosai, bayan Ya Aliyu sai Maman su ta haifi Anty Hajar, sai ta haifi har maza biyu amma duk suka rasu bayan sunzo duniya, sai ita, sai kaninta dukansu mata guda 6, amaryan Dady yaranta mata guda uku, sai ta tsakiyar itama yaranta mata guda Takwas, bawasu manya bane dayake gasan haihuwa ake agidan, daga ita sai Anty Hajar ne kawai manya duk sauran yaran yarane basu wani tasaba. Deep down tausayi sosai Ya Aliyu kebata bana wasaba gidan nan kowa ya tsaneshi harda Maman su itacema oga, she's sure ayanda Mama ta tsaneshi inda zata sami hanyar kasheshi zata iyayi, ita tarasa meyay musu meya tsaya musu? Maiya kare musu wanan mugun tsana haka daga ina? Gashi baima dawani magana, bayama kulasu sabida yanda ko kaunar ganinshi basayi duk sun rabashi da kaninshi, itama da karfi da yaji tanunama Mama itafa saita kula Yayan su koda ba mahaifiya daya ta haifesu ba ubansu daya ai, kuma jini guda ke yawo ajikinsu, Ya Aliyu is just somehow that she can not even define, he's very cool saiyaga daman kulaka zai kulaka, sanan yanada fushi yanada bakar zuciya but he's always keeping calm baimaso yana fushi, gashi baida kwari komi ahankali yakeyi sanan shi mata basama gabanshi, shi kawai gashi nanne soo somehow, sa'oinninshi maza by now suna cikin kogin soyayya koma sunyi aure sun ijiye iyali shiko batamaga alamun sha'awan aure tattare dashiba ko halinsu Mama ne dayagani yasa yadauka duk haka mata keda bakin hali ya tsani aure oho but she just wish, hope and pray Ya Aliyu will meet the love of his life soon and experience that feeling of knowing someone out there is dying for you, is crazy for you, and can do anything for, love feeling is just the best ne, tarasa mesa duka matan Dady dukansu ukun bazasu soshi and hold him like a Son ba why, yanzu kenan duk yaron da mahaifiyar shi zata mutu tabarshi haka zaiyi rayuwa kowa na kyaranshi? This isn't right at all.



Tashi tayi ahankali jikinta duk yay sanyi taja jakanta tareda kashemai wutan dakin tafita ta rufemai kofan falo tawuce part dinsu, ahankali tabude kofar su gudun kar Mama taji ta maida kofar tarufe sanan tadaga akwatin dan karyay kara tai dakinsu, bamata kunna wutaba ta lallaba ta ijiye akwatin gefen gadonta ahankali kaman munafuka, fincikota dataji anyi saida tadan saki gajeren fitsari kunna wutan dakin akayi taga Yayarta Hajara ne tsaye jikin kofa sai maman su data mugun daure fuska tana rike da ita, sosai jikinta yafara rawa hakan yasa tace "M...Mama menayi?" hannu Mama tasa ta dauke ta da lafiyayyen mari ihu tabude baki zatayi Maman su tace "wlh, wlh kikamin ihu ubanki yaji ya shigo dakin nan saina miki abinda bantaba mikiba tunda na haifoki duniya" gyada mata kai tayi tsabagen rudewa tasa hannu takama bakinta tana kuka sosai mara kara, cikin mugun fushi Maman su tace "wato dan ubanki tunda Aliyu yabar garin nan nahuta yanzu yadawo kin fara, Rauda ni, ni, ni nan uwarki karimatu in tsugunna in haifoki kifito tanan Rauda" ta daura hannu gaban zanin jikinta tace "nasha azaban nakuda na kwana biyar, bayana kam har tofin yaasin akamini tsabagen yanda kika shirya karyashi kafin ki fito, sanan dakika tashi fitowan kika fito ta kafa nasha bakar azaba nice yau Rauda kike nunamin wani kasurgumin katon banzan namiji, mai kama da basamuden chan yafi ni ni mahaifiyarki, iyye Rauda? Nasaki ki daukomin zanin gado, Rauda ni zaki watsarma da wankakken zanin gadona fari kal akasa sabida kinga Aliyu, dan ubanki ciki daya kuka fito da Aliyun?" shiru Rauda tayi bata bata amsaba sai uban hawaye dake fitowa daga idanunta, cikin tsananin fushi Mama takara kamo gaban rigan ta bakinta na kumfa tace "kibani amsa, ciki daya kuka fito da Aliyu?" girgiza mata kai tayi cikin kuka tace "Yayan mune Mama" wani mahaukacin mari Mama takara sharara mata tace "dan ubanki menasha taraku nake fadamuku? Aliyu ba dan uwanku bane, babu ruwan ku dashi yanda baida uwa hakama baidaku, kuba yan uwanshi bane, haka zai karake rayuwanshi baisan dadi da soyayyan dan uwaba, ku dauka ko jini vaku hada dashi ba, yaron da ubanku ya fifitashi kan kowa na gidan nan uban me za'ayi dashi eh?" cikin kuka sosai Rauda tace "amma Mama shi aka fara haifa a gidan nan, kafin dukanmu, kuma Dady na nuna yafi sonshi ne sabida duk kunki bama marayan yaron soyayyar mahaifiya dukkun tsaneshi, maiya muku? Bai taba zaginki ba, bai taba miki rashin kunya ba, inya gaisheki baki amsawa bama kya kallonshi saisama yadena, duk kun rabashi da kowa, Anty Hajar ma bata gaidashi duk kun hana kaninshi gaidashi saidai idan sunga Dady ne zasu gaidashi, haba Mama kiji tsoron Allah, _d'a na kowane_ maiya muku eh? Idan yanzu kika mutu akamana haka yaya zaki dingaji akabari" shaketa Mama tayi ahaukace jitake kaman ta kashe ta tace "nikike kirama mutuwa Rauda akan Aliyu? Ba dangin iya bare na Kaka, saidai ke kimutu baniba kinji shegiya wacce ta debo jinin dangin ubanta mai bakin zuciya" ganin idanunta na juyawa yasa Anty Hajara da itama take mugun jin haushin kanwar nata sabida taurin kanta tazo ta cire hanun Mama daga wuyanta tace "ya isa haka Mama" cikin fushi da mugun masifa jikin Mama har barbar yake tace "Hajar ki barni na kasheta, baidai tafison wani kato akan uwarta ba, goben nan zakiji kishiyoyina sun faramin habaici na haifi munafuka, zataci ubanta ne saisa gwara ai aurenta da Khamis ta tattara tabar gidan nan ta tafi gidan mijinta nahuta inba hakaba bakin cikinta zai kasheni ne, dama Khamis din yacemin gobe zaizo yadauke ki kufita kibishi kufita dan kin gama zaman gidan nan balle kije kinama wani kato girki kega kuku yakarata chan daci a restaurant shidai da gidan ubanshi ba amma wlh bazaici abincin gidan ubanshi ba zan gyara miki zamane Rauda" ahankali Hajara trying to calm Maman su down tace "ya isa Mama kiyakuri, Bazata sakeba" dan shiru Maman tayi tana kallon yanda Raudan taduka tana kuka sosai mara kara kafin tai kwafa ta kalli hadadden akwatin data shigo dashi tace "kuma shegen akwatin nan kona shege zanyi" tasa hannu zata dauki akwatin da gudu tarike akwatin cikin kuka tace "Mama dan Allah ki barmin abuna" hannu Mama tasa zata fizge akwatin tarike gamgam tana kuka, cikin kunan rai Hajara tace "wai bazaki saki akwatin ba Rauda kanin ubanki ne yabaki akwatin, kisaki akace" cikin kuka sosai ta girgiza musu kai taki saki dan son abubuwan ciki takeyi sosai, Mama jitayi kaman ta kashe Rauda tahuta zata jibgeta Hajara tai sauri ta tare tasa hannu ta daki hanun Raudan tace "sake shegen akwatin" ta hankadeta tareda fizge akwatin tamikama Mama dan ayanda taga mama tasan zata iya jima Rauda ciwo ayanda ta zuciyan nan. Karban akwatin tayi ta kalli Raudan dake kuka kaman zata mutu tai kwafa tajuya tafita daga dakin tsaki Hajara tayi ta balla mata harara tahau kan gadonsu cikeda takaicin Raudan tai baccinta, sosai Rauda taci kuka harta godema Allah ahaka bacci yay awon gaba da ita awurin.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



5️⃣ & 6️⃣


_how to pay your subscription fee_
_*zaki turo 300 ta account dina 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_

_*for those da prefer su tura kati, you can also send MTN card na 300 ta WhatsApp number na 07012181461 saina loda nasaki a group din danake posting ATSAKANKANIN SOYAYYA_





_Free page_



Sallame salla Ammi tayi
sake kwalamata kira akaro na uku tayi. "Aneesa wai bazaki tashiba, idan kika bari nazo dakin nan sai jikinki yay tsami, kindaisan abubuwan dake gabanki yau ko" da kyar ta iya bude ido jin Ammi na masifa tana kiranta jiya taci aiki a shago bana wasaba saisa tagaji haka, dama duk jumma'a haka take uban aiki a shago dan masu zuwa party nazuwa placing order dayawa kuma duksaitayi, da kyar ta sauko daga gado har bata gani da kyau tana dafa bango tafito daga dakin tafito Ammi tabita da kallo tai tsakar gida bayi ta shiga dan lokacin har gari yasoma wayewa fitowa tayi tadauro alwala takoma daki tadau hijabi ta sanya, akusada Ammi ta tsaya ta kabbarta salla, data idar tai karatun Al qur'ani sanna ta sallame ta gaida Ammi ahankali, amsawa Ammi tayi tace "tashi kije kidaura ruwa a wuta" gyadama Ammi kai tayi ta tashi ta zare hijabin jikinta tafito daga dakin tai kitchen wuta ta kunna ta daura pot din ruwan wanka dake cikeda ruwa tadau tsintsiya ta share tsakar gidan fess sanan ta shiga dakin dakin Ammi ta tattaro ta gyara sanan tawuce nata dakin ta gyaro shima tahada da falo ta gyara tafito da dattin ta kwashe, tadawo ta kunna turaren wuta sanan tafito tasauke ruwan daya soma shirin tausa daga wuta ta daura dumamen tuwo tahada ruwa ta shiga bayi, wanka tayi tana fitowa ta sauke tuwon dayayi tasa miya sanan tai dakinta, mai kawai tashafa tadau doguwan riganta na gida baki ta zura tafito lokacin wajen 8 nasafe ta zuba abincin ta dan tasan Ammi bata breakfast early tadawo ciki ta zauna kusada Ammi tafara cin tuwon dayay dadi miyan harda wake aciki, ahankali takeci harta cinye sanan ta kai kwanon kicin ta wanke hanun ta ta dauraye baki tadawo ta zauna kusa da Ammi, da hannu Ammi tanuna mata dakinta tace "daukomin purse dina" tashi tayi tai hanyar dakin Ammi tafito rikeda wata bakar purse ta zauna kusa da Ammi tamika mata karba tayi tabude purse din ta ciro kudaden dake ciki wanda suke na Aneesan na lallen datakeyi take tara mata dubu biyarne Ammi tamika mata tace "kije kisiyo kayan lallen, sanan kisiyo handglove banson yanda kike bata hanunki haka, kiyi sauri kidawo dan nasan anjima kadan yan lallen zasu fara zuwa yau asabar kina gida" karban kudin tayi tana kallon agogon bangon dakin ganin Takwas da rabine yanzu yasa tace "karfe tara kasuwan lallin ke budewa, Ammi ki faramin tsifan kafin lokacin" tai maganan tana zare hulan kanta tulin kitson kanta datai shuku na hannu yawani zubo har gadon baya, hulan data cire Ammi ta daura ta mayar mata tace "sokike kije kasuwa dakai daya da rabi, aga nan yay kato nan yay kadan, Tara zaki fita yanzu takwas darabi minti talatin yayma kitson nan kadan, yanzu jeki fara shiryawa ne, kafin kigama shirin lokaci yayi" kaman zatai kuka ta tashi tai hanyar dakinta, sip dinta tabude tadauko wani gogaggen atamparta riga da skirt dakeda dilli dillin ja, sai ta dauko jan hijabin ta dayakai mata har guiwa ta maida sip din tarufe tacire rigan jikinta ta shiga shiryawa, riga da skirt din yay mata kyau sosai gaban madubinta taje ta shafa hodanta tadau man baki tashafa a lips din sai abin yay kaman tasa pink lipstick, dawowa tayi tadau hijabin tasaka daya kwanta a fuskarta tadau karaman jakanta tafito, baki Ammi ta tabe tace "kasuwan aka cima kwalliya haka yan mata kodai nai siriki ne akasuwan" akunyace tace "laaaaa Ammi" dariya tadanyi ta dauke kai cikeda kunya tadau kudin dake gefen Ammi tace "nifa hoda kawai na shafa Ammi" tura kudin tayi cikin jaka tayi har lokacin taki kallon Ammi tace "natafi Ammi" "adawo lpy, ki adduan fita daga gidafa, kuma adaga kafa kar aje ana yauki akasuwa hmmm" Ammi tafada cikeda zolaya, murmushi sosai tayi tasa hijabi tace "to, Ammi idan yan lalle sunzo kice sujirani bazan dadeba" "shikenan, saikin dawo, kiyi addu'an fita daga

Please Login or Register in order to submit comment